Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wadannan fitilu itatuwa, dayake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai jikin su Ilaila ya yi sanyi kawai sai suka zubar da makamansu suka daga hannayen su sama, nan aka fara kallon-kallo tsakaninsu da dakarun sumame ba tare da wani mutum daya a wajen ya yi wani motsi ba.
Daga can sai suka ga dakarun sumame sun dare daga tsakiyar su Suna masu buda hanya sai suka ga shugabansu narkakken kato ya ratso yana sanye da wata bakar falmaran da farin wando buje kuma ya ratawo wani zabgegen barandami akan kafadar sa takalmin kafarsa dogone iya gwiwa kuma na fata mai daure daure, yana katon gashin baki kuma fuskarsa faffada ce sannan idanunsa kwala-kwala nd masu ban tsoro sai da wannan narkeken mutum ya iso daf dasu Ilaila sannan ya tsaya cak ya Kare musu kallo duk su taron.
Kawai sai ya bushe da dariya ya ce "Ya ku wadannan wakilai na sarkin Misira akan wace bukata ce kuka shigo cikin dajin Hailis Salas?
Shin kun zo ne domin ku kawar da mu daga cikin dajin nan ne ko kuwa kun zo ne neman yarima Ansar dan'uwan Sarki Marhat?"
Har mai hular karfe ta bude baki zata yi magana sai Ilaila ta yi caraf da ta tari numfashinta ta ce "Mun zo ne neman yarima Ansar idan yana.hannunku ku bamu shi kafin ranku ya baci idan kuma baya hannunku, ku gaya mana inda yake kuma kada ku kuskura ku yi mana karya ko ku yaudare mu."
Sa'adda Ilailal a zo nan a jawabinta sai tsoro kuma abokan tafiyarta jikinsu ya kama kyarma hatta ita kanta, mai hular karfe kuwa, su kuwa dakarun sumame mamaki ne ya kama su aka rasa wanda zai ce mata kala saboda jira ake yi a iji hukuncin da shugaba zai zartar a kanta.
Shi kuwa shugaban dakarun kurawa Ilaila idanu ya yi har izuwa tsawon wasu yan dakiku sannan kuma sai ya takarkare ya bushe da.wata dariyar mugunta lokaci guda ya murtike fuskarsa ya dubi Ilaila ya kama yi mata tafi ai kuwa sai gabadaya yaran nasa ma suka kama yiwa Ilaila tafi.
Sai da ya daina tafin sannan su ma yaran nasa suka daina tafin.
Shugaba ya ce "Wannan yarinya mai dakakkiyar zuciya haka kin burge ni, domin ban taba haduwa da mace mara tsoro kamarki ba amma yau zan ga abin da kike takama dashi kuma sannan zanga karshen rashin kunyarki. Da farko dai ina mai sanar daku cewa a cikin wannan dajin akwai rukunin dakarun sumname.guda shida, mu ne rukuni na farkobkuma mu ne muka je bayan garin ku muka sato yarima Ansar ahalin yanzu baya hannun mu mun siyar dashi ga rukuni na biyu akan farashin dinare dubu dari takwas, idan kuna bukatar shi sai ku karasa sansanin rukunin na biyu ku tambaya, yau kwana uku kenan da siyar musu dashi idan kuka yi sa'a kun same shi sai ku ba su riba ku karbe shi, idan kuma sun siyar dashi ga rukuni na gaba sai dai ku wuce garesu.
"Kafin hakan yanzu ya zaku yi da mu? Shin zaku hukunta mu ne bisa laifin da muka yi na sato yarima Ansar ko kuwa mu ne zamu hukunta ku bisa rashin kunyar da wannan abokiyar tafiyar taku ta yi mini?"
Caraf sai Ilaila ta sake duban shugaban dakarun ta ce "Mu bukatar mu kawai mu sami yarima Ansar a raye ¢ikin koshin lafiya ba tare da mun zubar da digon jinin daya ba, amma tun da kuna tunanin na muku rashin kunya ai abu ne mai sauki mu warware wannan matsalar, ni da kai za mu gwabza yaki yanzu dan baka samu sa'ar halaka ni ba acikin rabin sa'a za ku barmu mu wuce gaba zuwa ukunin dakarun sumame na biyu idan kuma ni ce na sami nasarar hallakaka to gabadaya yaranka za su zama yarana za su bi mu izuwa gaba."
Sa'adda Ilaila ta zo nan a jawabinta sai sauran abokan tafiyar ta suka kara firgita ainun fiye da koyaushe Mai hular karfe ta matso daf da ita ta yi mata rada a kunne.
"Wai shin ke wace irin wawiya ce mara lissafi da tunani ki dubi wannan narkeken katon fa ya ninka ki sau uku girma da kirar karfi ai da ganin kirar kura kinsan zata ci mutum, dole ne wannan ya zama gwarzon mayaki! ni kaina baki sami wata riba a jikina ba bare shi, Wannan ai wauta ce da ganganci kika yi mana."
Na gode sosai da addu'o'in da yan uwa kuka yi mani kuma AlhamduLillahi!
Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part F (Takun Karshe)
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Yayin da Ilaila taji wannan batu sai ta yi murmushi sannan itama ta yi wa mai hular karfe rada "Kada ki manta cewa dazu yar kashi muka gwada ni dake yanzu kuma iya yakina da makami zan nuna muku, kawai ki zuba ido kisha kallo zakiyi matukar mamaki.
Al'amarin shugaban dakarun sumame tare da yaransa kuwa mamaki ne ya sake turnuke su bisa jin abin da Ilaila tafada cewar ta amince ta gwabza yaki dashi, na tsawon rabin sa'a idan ta yi nasara yaransa sun zama nasu sai da shugaban dakarun ya ýi shiru tsawon dakika dari yana tunani da wasu-wasi a ciki zuciyara bisa sharadin da Ilaila ta zo masa dashi.
Abu na farko dai abin kunya ne ya ce yaki karbar tayin ta na su gwabza yaki a matsayinsa na gwarzon jarumin namiji, daya shafe Shekaru da yawa yana karewa maza ruhin numfarfashisu, ya zaa ce "Ya mace karama kamar wannan zan kasa tararta da yaki, abu na biyu shi ne masu iya magana sun ce idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to fa ya taka hoge, babu mamaki yarinyar nan akwai abin da ta taka shi ya sa ta tari aradu da ka, amma dai komai take takama dashi ta yi ganganci saboda dole ne na yi mata mugun kisan na gilla ma.
Lokacin da shugaban dakarun ya gama ayyana hakan a cikin zuciyarsa sai ya sauke Wannan katon barandami daga kan kafadarsa kuma ya bude kafafunsa yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya fito Ilaila da hannunsa ya kira ta taho su kara, maimakon ta taho sai ita ma ta dauko takobinta da garkuwarta tajin jina su a hannunta kuma ta gyara tsayuwar ta yafito shi da hannu kamar yadda ya kirata, koda ganin hakar sai shugaban dakarun ya fusata saboda hakan data yi raini ne a gareshi matuka.
Saboda tsananin fushi sai fuskar sa ta kama yin gatsinc, kawai sal ya falfalo da gudu izuwa kan Ilaila cikin mugun nufi da niyar kawai ya kaftara mata sara a kafada domin ya tsarge gangar jikinta gida biyu, don haka da dukkan karfinsa ya kawo mata mummunan sara, cikin bakin zafin nama ta kaucewa Saran sai barandamin ya nutse a cikin kasa, kafin ya zaro barandamin tuni Ilaila ta kai masa sara da takobinta da nufin ta fulle masa kai, cikin bakin zafin nama ya ja da baya amma duk da baka sa kaifin takobin tata ta ya Sharci kumatunsa kadan, take wajen ya dan dare jini ya ya zubo, ciki matukar mamaki ya shafa kumatunsa ya ga jini sa'adda ya dan ja da baya, al'amarin da ya ba wa kowa mamaki kenan wajen musamman mai hular karfe ashe dai yarinyar nan gaskiya take fada mini.
Lokacin da shugaban dakarun Sumamem ya shafo yaga jini a kumatunsa yaga cewa Ilaila ta sami nasarar yi masa rauni a karon farko na gumurzun nasu sai ya fusata fiye da dazu don haka sai ya daga hannunsa sama take daya daga a cikin yaran shi a ka jeho masa garkuwa ya cafeta saboda ya fahimci cewar lallai wannan yarinyar ba kanwar lasa ba ce, kawai sai ya wankame bakinsa ya yi wani irin kururuwa mai matukar firgitawa sannan ya sake rugowa izuwa kan Ilaila a karo na biyu suka rungumeni da azababban yaki cikin juriya da bajinta ya zamana cewa $una kai wa junansu sara da suka cikin zafin mama, kwarewa da jarumtaka ta ban mamaki.
Duk sa'adda ya kawo mata sara ta kare da garkuwarta sai ta durkushe kasa bisa guiwarta guda saboda nauyin saran da karfinsa amma kafin ya kawo mata wani harin tuni ta mike tsaye ita ma ta kai masa harin.
Nan fa karar haduwar makamansu ta cika dajin gabadaya. Sai da suka shafe kusan dakika dari uku da arba'in suna yin wannan bákin gumurzu amma dayansu bai sake samun wata nasara ba kuma yakin nasu kara tsamari yake ko alamar gajiya babu a tare da su, kuma kowannensu tamkar kara masa karfi ake yi babu ma alamar gajiya.
Hakan ne ya sa kowane bangare hankalinsa ya tashi saboda ko ya ya đayansu ya yĩ kuskure za a iya yi masa kisan farat daya.
Ana cikin wannan halin ne shugaban dakarun ya shammaci Ilaila ya nuna mata dadewa a sanin makama ya fyalli kafafun ta da kafarsa guda ta fadi kasa.
Kafin ta mike ya kawo mata suka a kan cinyarta, cikin hanzari ta janye kafar tata amma sai da kaifin barandamin ya dara wandon jikinta ya yanki tsokar cinyarta.
Take wurin ya dare jini ya yi feshi Ilaila ta kurma ihu sakamakon zafin da ta ji, amma kafinta a kasa tamkar an murza dan mazani kawai sai gani aka yi ta yi sama ta shallake shugaban dakarun, kafin ya juyo ya fuskanceta ta dankara masa sara a gadon bayansa.
Ai kuwa sai shi ma ya kurma ihu a lokacin da bayan nasa ya dare jini ya yi feshi. Sai da ya yi taga-taga tamkar zai fadi kasa amma ya coge a tsaya bisa dugadugansa.
A lokacin da tuni Ilaila ta diro kasa bisa kafafuwanta kawai sai ta cire bakin kyallen dake jikinta ta daure raunin cinyarta tamau.
Ko da ganin abin da ya faru sai wasu yaran shugaban dakarun suka zarc takubbansu suka yunkura za su afkawa Ilaila, amma sai shugaban ya daka musu tsawa, suka tsaya.
Nan take aka sawa shugaban dakarun ya debi wank garin magani ya sa akan raunin gadon bayan nasa, kuma aka daure bayan tamau don tsaida jini.
Kawai sai ya dubi Ilaila ya yi murmushi sannan ya ce, Tabbas ke ta musamman ce na yarda kin fini iya yaki. Yanzu kuma zaku iya ci gaba da tafiya izuwa rukuni na biyu domin kar6o Yarima Ansar amma ina mai ba ki shawara da kada ki sake yin gangancin da kika yi yanzu anan saboda su rukuni ha biyun sun fimu komai kuma ba za su ba ku irin damar da muka ba ku ba, Kawai ku je da maganar kasuwanci wato ku biya a ba kự abin da kuke bukata. Ni daga yau na daina wannan sana'ar tun da ya mace ta karya mini al kadarina."
Ko da gama fadin hakan sai ya juya, ya dubi gabadayan yaran nasa ya ce Idan kuna so ku yi gasa ku fitar da gwani a cikinku a matsayin wanda zai ci gaba da shugabanku. A je a dauko mini komai nawa a ba ni na yi sallama da ku kenan."
Batare da wata gardarmaba kuwa sai aka je aka debo dukkänin kayayyakin shugabandakarun sumamen áka daure su bisa dawakai shida aka tattare linzamin dawakan shida aka mika masa, kawai sai ya juya da dawakan ya yi gaba yana mai ficewa daga cikin dajin na Hairil Salas.
Nan take su ma su Ilaila suka hada nasu ína su suka kara gaba Ilaila na yin dingishi a sakamakon raunin da ke kan kafarta. Ba su haura dakika arba'in ba suna tafiyar sai kawai Ilaila ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya sakamakon jinin da ya ci gaba da zuba a kan raunin dake bisa cinyarta.
Lokakcin da Ilaila ta farfađơ daga suman da ta yi sai ta tsinci kanta a wani wuri mai ni'ima kusa da wata korama mai gudana, ga tsirrai a wajen kala-kala abin sha'awa, ko da ta dubi raunin cinyarta sai ta ga an dinke shi kuma an shafa masa magani.
Sauran abokan tafiyarta bakwai na can gaban koramar sun tsugunna suna wasa da ruwa. Nazima ce kadai ba ta cikinsu.
Kawai sai Ilaila ta ji motsin tafiya a bayanta, cikin zafin nama ta zaro takobinta da ke ajiyc a gefenta ta juya da sauri, sai ta ga ashe Nazima ce ta taho gareta dauke da wani dan karamin kasko wani abu na tururi a cikinsa.
Ilaila ta yi ajiyar zuciya, a.lokacin da ta dauko kufen takobinta ta mayar da ita ciki ita kuma Nazima $ai ta zo, ta zauna daf da ita sannan ta mika mata kaskon ta ce "Ungo wannan magani ne na dafin makamin da ya yi miki rauni, maza ki lshanye shi in ba haka ba kuwa wannan raunin naki ba zai taba warkewa ba."
Da jin haka sai laila ta kar6i kaskon da sauri ta kafa a bakinta a ta kama sha. Duk da cewa maganin dafaffe ne yana da zafi har yana dan kona mata harshe sai da ta shanye shi tsaf sannan ta ajiye kaskon a kasa.
■Nazima dubeta cikin murmushi ta ce. "To kawata ni ma ina mai ba ki shawarar kada ki sake yin irin wannan gangancin. Tabbas kowa a cikinmu ya gamsu cewa ke jaruma ce ta kwarai mai ban al'ajabi, amma ki daina Wasa da rayuwarki a kan wannan aikin banzan da muka fito yi tun da dai wanda muka fito nema ba jininki ba ne. Ko mu same shi ko mu rasa shi bamu da wata asara face kwadayin ladan da za a a biya mu. In ban da ma buri irin na bil'adama ko wannan dukiyar da aka ba mu ta somin tabi ai ta ishe mu rayuwar duniya"
Lokacin da Nazima ta zo nan a zancenta sai Ilaila ta kyalkyale da dariya, al'amarin da ya yi matukar bai wa Nazima mamaki kenan ta dubeta ta ce, "Mene ne dalilin yin wannan dariya ta ki?
Ilaila ta yi ajiyar numfashi sannan ta ce. "Ya ke kawata ki yi sani cewa amfanin hankali aiki da shi. Ina so ki sani cewa gabadayan dakarun sumamen dake cikin dajin nan yaran Sarki Marhat ne, zamansa suke yi kuma aikinsa suke yi, kawai raina mana hankall aka yi."
Ko da jin wannan batu sai.mamaki ya turnuke Nazima ta dubi Ilaila cikin alamun rashin yarda ta ce "Mece ce hujarki ta fadin hakan ?"
Ilaila ta sake yin ajiyar zuciya ta.ce "Kada ki manta cewa dakarun Sumamen nan da na yi fada da shugabansu yan fashi ne babu abin da suke so sama da kudi. Mene ne dalilin da ya sa ba su caje mu ba sun kwashe dimbin dukiyar da muke dauke da ita? Ina mai tabbatar miki da cewa sun sani cewa dukiyar dake tare da mu ta ubangidansu ce shi ya sa ba su nemeta ba, kuma sun sani cewa muna boye da ita a jikinmu Wanda muke nema kuwa tuni ma an kashe shi an binne gawarsa wani wajen kawai an yi amfani ne da mu domin a kawar da hankalin mutanen birnin Misira domin a yarda cewar sace Yarima Ansar aka yi tun daga shi an zabo dakarun da za su tafi nemansa.
"Karshe mu ma duk kashemu za a yi, kin ga ke nan dole mutanen Misira su hakura da zancen Yarima Ansar."
Sarki Marhat ya kashe dan'uwansa Yarima Ansar ne saboda shi ne kadai magajin karagar mulkin Misira kuma shi ne ya fi cancanta da karagar a halin yanzu bisa irin mulkin zaluncin da ake gudanarwa.
Ya zama wajibi mu zauna mu takwas din nan muyi tunanin mafitarmu a sirrince ba tare da wancan mai hular karfen ta sani ba. In ba haka ba kuwa dayarmu ba za ta koma Misira a raye ba."
Sa'adda Ilaila ta zo nan jawabinta sai Nazima ta dube ta cikin yanayi na tsoro da wasi-wasi ta ce "Ta ya ya zan iya gamsuwa da duk wadannan abubuwan da ki ka gaya mini? Kuma kí sani cewa ko ya ya mai hular karfe ta gano cewa akwai wani abu da muke shirin yi tamu ta kare. "
Ilaila ta ce Na san da hakan amma zan tabbatar miki da duk abin da na fada gaskiya ne, mai hular karfe ta san komai kuma da íta áka hada baki domin a kawar da mu, saboda ko da ace mun sámo Yarima Ansar a raye mun mai da shi Misra Sarki Marhat ba zai iya cika ragowar alkawari na na ba mu ladanmu ba."
Gama fadin hakan ke da wuya sai Ilaila da Nazima suka ga mai hular karfe ta juyo baya tà kalle su daga can bakin gabar koramar.
Wani irin kallo tayi musu na zargi, dön haka sai ta mike tsaye ta baro ragowar abokan tafiyar su shida ta taho wajen su Ilaila.
Da isowarta sai ta zauna daf da su. Ba tare da ta kallesu ba sai ta ce Wai shin hirar me kuke yi ne yanzu?"
Caraf sai Ilaila ta ce "Muna magana ne a kan hadarin dake cikin wannan aiki da muka fito da kuma yiwuwar nasararmu."
Mai hular karfe ta yi murmushi sannan ta ce "Ai ga dukkan alamu muna da nasara musamman da na ga irin kwarewarki ta yaki"
Ban taba zaton cewa za ki iya samun nasara a kan wancan Shugaban dakarun ba.
Ilaila ta numfasa ta ce "To ai wannan somin tabi ne kawai. Ka da ki manta cewa shugaban dakarun ya gaya mana cewa rukunin dakarun sumame na biyu sun fi su komai, to ya ya kuma rukuni na uku, huɗu, biyar da shida za su kasance. Kin ga kenan babu ta yadda za mu ya tsallake su har mu karbo Yarima Ansar."
Mai hular karfe ta ce "To amma ai ya gaya mana cewa za mu riski Yarima Ansar a hannun rukuni na biyun tunda bai fi kwanaki uku da zuwa hannunsu ba,"
Ilaila ta ce "Idan hahr muka riski Yarima Ansar a hannun rukuni na biyu na rantse da darajar iyayena sai na kashe kaina. Maganar banza ce da karya kuma ke munafuka ce, da ke aka hada baki domin a kashemu gabadaya. Ki fada mana gaskiyar al'amari ko kuma a yi ta, ta kare anan wajen. Wace ce ke ki bayyana mana kanki. In ba munafurci ba me ya sa hár yanzü kín ki yarda ki cire hular karfen dake kanki domin mu ga fuskarki."
A lokacin dą Ilalla tà fara wannar furucí daga muryarta ta yi kuma a fusace take yin maganar domin haka sai sauran abokan tafiyar tasu dake can bakin korama zaune sai hankalinsu ya tashi, suka taso daga bakin koramar suka zo gabansu suka tsattsaya saboda duk sun ji abubuwan da Ilaila ta fada kuma zuciyarsu ta gamsu da abin da ta fada din saboda shi mara gaskiya an ce ko cikin ruwan gumi yake yi.
Gashi a zahiri mai hular karfe ta kasa kare kanta ta yi shiru kuma ta kasa cire hular karfen dake kanta, sai kawai ta kurawa Ilaila idanu tana tunanin matakin da ya kamata ta dauka, har tsawon dakika ashirin da biyar mai hular karfe ba ta ce komai ba, kuma ba ta yi komai ba. koda ganin haka sai Ilaila ta dubi Nazima da $auran mayakan dhida tace, Ku juya ku koma da baya izuwa inda muka baro dawakanmu, kuma ba zamu bar nan ba har sai wannan shugabar tamu ta budi baki ta yi magana. Abin da nake so da ku shine ku yi gudun çeton ranku kuma kada ku kuskura ku koma cikin birnin Misira domin kuna zuwa za ayi a kamaku.
"Ko dai a kashe ku ko kuma a kai ku kurkuku a kulle bisa daurin rai da ai don kada ku tona asirin Sarki. Ita kuma wannan shugaba ta mu idan ta ki yin magana zan yaketa, sai dai ayi ko ni ko ta dole ne dayarmu ta mutu a nan. Maza ku bar nan wajen.
Ko da jin haka sai mai hular karfe ta daka wa su Nazima tsawa ta ce Idan dayanku ta kuskura ta yi tafiya ta ku daya daga nan, take za ta zama gawa. Lallai ku bi umarnina Ku sani cewa duk abin da wannan mara kunyar ta fada zargi ne a gaskiya ba.
Nazima ta yi caraf ta tari numfashin mai hular karfe ta ce "Alamomin munafurci sun tabbata a tare da ke, kuma a cikinmu babu wata jaruma mai basira da sa'a kamar Ilaila don haka mu mun amince da shawarar da ta ba mu kuma duk umarnin da ta ba mu shi za mu bi! Yan'uwa ku zo mu tafi kawai.
Nazima na gama fadin hakan sai ta mike tsaye zumbur, su ma sauran mayakan bakwai sai suka mike da hanzari su bakwan suka ruga ka gudu izuwa baya amma kuma sai suka rinka zube wa a kasa sakamakon ruwan kibiyoyin da aka harbo masu.
Nan take mayakan bakwai suka zama gawa Nazima ce kadai kibiya ta soke a kafada ta baya ta fadi kasa, amma kafin a kara harbo wasu kibiyoyin tuni ta sake mikewa zumbur ta falfala da azababben gudu izuwa cikin jejin ta 6ace a cikin duhuwoyi.
Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799
Mu hadu a kashi na biyu
Naku
Abdul'aziz Sani M/Gini
Na gode
ALHAMDULILLAHI
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

4 Comments On GWARZON SADAUKI Book 1
avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
daiy

10 months ago

Reply

Replying to maimunatu-7

Ki downloading ki karanta ko ki karanta shi anan shafinmu amma ki sani kafin ki iya downloading dole sai kinyi subscribtion na shafinmu wanda mafi karanci shinw 1k Naira

avatar
atiku

9 months ago

Reply

Zansamu complete littafan nan a pfd kuwa

Please Login or Register in order to submit comment