Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RIJIYA GABA DUBU💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part A. 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing By AA Misau
✍️⭐⭐⭐

(DUBA DA YADDA KUKE MANA LIKES AND COMMENTS ZAMUYI IYAKAN BAKIN KOKARIN MU WAJAN NISHADANTAR DAKU DA LITATTAFAN YAKI WANDA BAKU KARANTASU BA A INTERNET KO DA A ZAMANIN BAYA DA MUKAYI TYPING)

Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa..

LOKACIN DA GIMBIYA LAMRITA
Ta ji abin da Sarki Taryam ya fadi, sai
ta kamu da tsananin mamnaki garni da
Cikin sanyin jiki da sanyin murya ta
dubeshi tana mai risinawa ta ce, "Ya shugabana
me ka ke tunanin ina kullawa dangane da
Mahaifina, kuma mene ne ya sa ka biyo mu nan?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Taryan
ya yi ajiyar numfashi sannan ya dubesu duk su
biyun ya yi guntun murmushi ya ce, "Na sani
cewa yanzu kin san dalilin da ya sa Mahaifinki ya
tsani Jarumi Imhal har yake son ya kawar da shi?
Don haka ba ki da burin da ya fi ki sanar
da Jaruni Imhal komai domin ya dauki fansa a
To ki sani cewa yin hakan a gareki shi ne
babban kuskuren da za ki yi nadamar aikatashi a
rayuwarki.
Shawarar da zan baki ita ce, ki bar wannan
al'amari a cikin ranki har abada, idan har
Jarumi Imhal zai san wannan sirri to ya sani a
wata hanyar, anma ba ta ke ba.
Shawarata ta biyu da zan ba ki ita ce,
'Kada ki kuskura ki bari mutane su gane cewa
kina ran a raye ba a kashe ki ba a filin gasa,
domin idan aka san kin lalata wannan gasa ke
nan har abada, sabo da mutane za su daina sonta
da sha'awarta.
Dangane da tambayarki ta biyu kuwa, ba
wani abu bane ya sa na biyoku nan ba sai sabo da
na gana da bakon Jarumi Salmanu,"
Koda gama fadin hakan sai Sarki Taryan
ya dubi Jarumi Salmanu cikin murmushi.
Cikin biyayya Jarumi Salmanu ya risina ya
yi gaisuwa ga Sarki Taryan sannan ya taho
gareshi suka koma gefe daya suka tsaya.
Tsayuwarsu ke da wuya sai Sarki Taryan
ya dubeshi cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai wannan
babban Jarumi mai ban al'ajabi, ka yi sani cewa
Jarumi Imhal ne babban abin dogarona a cikin
wannan gasa ta kambun jarumtaka na duniya,
amma a yanzu na sauya shawara, kaine gwanina
domin na tabbatar da cewar kaine za ka lashe
wannan gasa."
ya
Koda jin wannan batu sai mamaki ya
turnuke Jarumi Salmanu, ye dubi Sarki Taryan
cikin alamun rashin yarda ya ce, "Ya kai wannan
Sarki, kai kuwa mene ne dalilin da ya sa ka
zabeni a matsayin gwaninka alhalin akwai
alarnun cewa tsakanin Sarki Gurzalu da Jarurni
Imhal ne za a sami zakaran wannan gasa?
Ta ya ya ni da ba ka tafa ganina ba sai
yau, kuma ba ka ga iyakar juriyata ba da iyakar
jarumtakata ba za ka ce ka zabeni a matsayin
gwaninka?
Ina mai baka shawara akan cewa ka sauya
gwani, idan ma hasashe ka yi a kaina ko kuma
tsafi ne ya sanar da kai hakan to ka saki Reshe ne
ka kama Ganyc"
Koda jin wannan batu sai Sarki Taryan ya
bushe da dariya sannan ya ce, "Ya kai Jarumin
jarumai, ka yi sani cewa, Makaho ba ya cewa ayi
Wasan jila face ya taka hoge!" Ni na san wani
al'amari boyayye a tare da kai wanda ka ke zaton
ban sani ba.
Kada ka damu, lokaci ne zai bambance ma
na komai. Yanzu dai ina so ka sani cewa ba zai
yiyu a ci gaba da gasa tsakanin Sarki Gurzalu da
Jarumi Imhal ba sakamakon raunin da ke jikinsu,
dole ne su yi jinya ta yan kwanaki don haka
kaine za ka ci gaba da debewa 'yan kallo kewa ta
hanyar cigaba da wasa har izuwa lokacin da za su
sami lafiyar jikinsu su yi wasan karshe a
tsakaninsu in ya so wanda ya yi nasara kaine
abokin gwaminsa.
Ya ke Gimbiya Lamrita, ki yi sani cewa
kin kamnu da tsananon son yarimna Imhala yanzu
kamar yadda shima ya kamu da tsananin sonki, to
ki sani cewa 'yata Gimbiya Shumaira a yan
haka tana kwance cikin mugun yanayi sabo da
tunanin cewa Jarumi Imihal ya rasa rayuwarsa,
sabo da itama ta kamu da tsananin sonsa fiye da
ke.
Ina mai rokonku alfarma ku bani Jarumi
Imhal na tafi da shi domin 'yata ta ganshi don
kada rayuwarta ko lafiyarta ta salwanta".
Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa
sai jikin Gimbiya Lamrita da Jarumi Salmanu ya
AA Misau ke Magana
yi sanyi, suka dubi junansu suka yi shiru aka rasa
wanda zai ce kala.
Daga can sai Jarumi Salmanu ya dubeta
ce, "Bamu da wani zabi a yanzu wanda ya fi mu
Mika Imhal ga Sarki domin mu ceci rayuwar
"yarsa".
Da jin haka sai Gimbiya Lamrita ta
murtuke fuskarta ta dubi Salmanua fusace ta ce.
"Ta ya ya ka ke zaton cewa zan iya hakura da
Jarumi Imhal a yanzu alhalin na san cewa. shi ne
kadai dan uwana da ya rage a duniya a wnnan
duniya? Idan har akwai abin da zai iya rabani da
Imhal a yanzu ba zai wuce takobi ba".
Tana gama fadin hakan sai ta zare
takobinta ta fuskanci Jarumi Salmanu da Sarki
Taryan ta ce, "Ku kasheni idan kuna so ku rabani
da dan uwana kamar vadda Ubana ya ha'inceni ya
rabani da shi tsawon shekaru, kuma ya Sa na
zama babban abokiyar gabarsa."
Nan take hawaye ya zubowa Gimbiya
Lambrita, kuma hannunta mai rike da takobin ya
kama karkarwa. Al'amarin da ya karya zuciyar
Jarumi Salmanu da ta Sarki Taryan ke nan, suka
kamu da tsananin tausayinta.
Kawai sai Jaruni Salmanu ya mika
hannunsa ya karbe takobin Lamrita sannan ya
dubeta a nutse cikin alamun tausayawa ya ce, "Ya
ke Gimbiya, kin sani cewa in da so na ke na cutar
da ke ba zan ceci rayuwarki ba daga sharrin
wannan Macijiya da take son hallaka ki a cikin
Kogi.
Ki kwantar da hankalinki, na yi miki
alkawari cewa ko Mahaifinki ya gane cewa yanzu
kin san Jarumi Imhal a matsayin dan uwanki ba
zan bari ya sake rabaku ba,"
Sa'adda Gimbiya Lamrita ta ji wannan
batu sai hankalinta ya kwanta.
Nan take Jarumi Salmanu ya dauki Jarumi
Imhal ya dorashi akan dokin Sarki Taryan gaba
daya tamkar ya dora gawa domin ko alamar rai
babu a tare da shi.
Nan dai duk su ukun suka hau dawakansu
suka juya da baya suka durfafi hanyar da za ta
mayar da su cikin Birnin.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su
Gimbiya Lamrita bayan an yi gasar kambum
jarumta tsakanin Sarki Gurzalu da Jarumi Imbal
L'AMARIN Sarki Gurzalu kuwa
shima bai farfado daga dogon
suman da ya yi ba sakamakon sukar
da takobin Jarumi Imhal ta yi masa ba sai bayan
Likitansa ya gama yi masa aiki da nisan sa'a uku.
Koda ya bude idanunsa ya tsinci kansa a
kwance cikin masankinsa na gidan Sarki Taryn
sai kawai ya ji 'yarsa Gimbiya Lamrita ta fado
masa a rai, ai kuwa sai ji ya yi zuciyarsa ta buga
da karfi, al'amarin da yai matukar dugunzuma
hankalinsa ke nan, ya rasa abin dake mesa daci,
kuma ya ji ban da son ganin Lamrita babu abin da
yake so.
Nan take ya yunkura da nufin ya mike
tsaye daga kan gadon da yake kwance, amma sai
yaji ya kasa sakamakon wani irin zafi da zogin da
yaji a gefen cikinsa.
Bisa dole ya koma ya kwanta cikin
tsananin takaici da bakinciki, sabo da nan take ya
tuno da duk abin da ya faru a fiin gasar kambun
jarumtaka tsakaninsa da Jarumi Imhal.
Bayan haka kuma sai tunanin yarsa
Gimbiya Lamrita ya sake fado masa zuciya.
Cikin tsananin kaduwa da firgici Sarki
Gurzalu ya kwalawa Likitansa kira ya shigo cikin
turakar.
Da shigowarsa ya zube
guiwoyinsa yana mai amsa kira.
kasa bisa
Cikin karfin hali Sarki Gurzalu ya dubi
Likitan ya ce, "Ina labarin Sarkin yakina? Shin ya
dawo ne daga Birnin Kisra?"
Likitan ya sake risinawa ga Sarki Gurzalu
cikin biyayya ya ce, "Ya shugabana ai tun da
Sarkin Yaki ya tafi har yau bai dawo ba.
Yau fa kwananka uku a kwance cikin
mugun hali, bamu taba zaton cewa za ka tsira da
rayuwarka ba".
Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki
Gurzalu ya sake dugunzuma fiye da koyaushe, ya
juyo da kansa da kyar ya dubi Likitan ya ce,
AA Misau ke Magana
"Yanzu tsawon wanne lokaci ka ke ganin
cewa zan iya dauka kafin na warke har na ci
gaba da wannan gasa?"
Sa'adda Likitan yaji wannan tambaya
sai ya sunkui da kansa kasa cikin alamun
damuwa da fargaba ya ce a cikin murya mai
sanyi, "Ya shugabana tun da na fara aikin
Likitanci ban taba ganin mutumin da ya sami
irin wannan rauni naka ba har ya tsira da
rayuwarsa face kai kadai.
Takobin da Jarumi Imhal ya soka maka
a gefen cikinka sai da ta 6ullo ta gadon
bayanka, kuma kaima haka ka sokeshi, amma
na sami labarin cewa shima ya tsira da
rayuwarsa.
ina mai tabbatar maka da cewa a kalla
sai ka yi kwana sittin a kwance kana jinya
sannan za ka iya mikewa tsaye har ka iya
tafiya".
Koda Likitan yazo nan a jawabinsa sai
zuciyar Sarki Gurzatu ta kama tafarfasa kamar
za ta kone sabo da tananin bakinciki, bai san
sa'adɖa hawayen takaici ya zubo masa ba, ya
dubi Likitan ya ce, "Yanzu shi ke nan kana
nufin ba zan iya ci gaba da wannan gasa ba ke
nan har a kammalata?"
Koda Likitan ya ga hankalin Sarki
Gurzalu ya tashi ainun sai ya ce, "Ka kwantar
da hankalinka ya shugabana, domin kuwa
shima abokin gabar taka Imhal bai isa ya ci
gaba da yin wannan gasa ba tunda shima yana
dauke da irin raunin da ke jikinka, kuma
komai saurin warkcwarsa da rashin kan jikin
nasa sai ya kwana a kalla talatin a kwance
yana jinya".
Koda jin wannan batu sai zuciyar Sarki
Gurzalu ta yi dan sanyi kadan har ya yi dan
guntun murmushi na mugunta ya ce, "Ni kam
gwara ace na mutu da dai wannan yaro lmhal
ya lashe wannan gasa alhalin ina raye, kuma
ina ji ina gani.
Ya kai babban Likita abin da na ke so
da kai shi ne, duk yadda za ka yi ka hada baki
da Likitocin Sarki Taryan domin a sawa
Jarumi Imhal Guba a jikinsa wacce Za ta zamo
sanacin ajalinsa.
Kudi ko nawa ka ke bukata zan bayar.
kuma idan aka yi nasara kaf! A Birnin Kisra
ba za a taba samun Attajiri kamar ka ba".
Koda jin wannan batu sai jikin Likitan
ya kama karkarwa sabo da tsananin murna.
Muryarsa
rawa ya ce, Ya
shugabana ai kuwa duk yadda zan yi na ga
wannan bukata taka ta biya zan yi ta kowanne
hali"
Sarki Gurzalu ya dan yi mumushi na
farinciki sannan ya kira sunan wani babban
Hadimi nasa kuma amintaccensa wanda ake
kira SALUHU
Salahu na tsaye a kofar Turakar da
Sarki Gurzalu ke kwance sai ya ji kira. Nan da
AA Misau ke Magana
nan ya fada cikin Turakar da sauri ya zube
kasa a gaban sa yana mai amsa kira.
Sarki Gurzalu ya dubi Sahalu ya ce,
"Aiki biyu na ke son ka yi mini yanzu.
Da farko ina son ka tashi Dakarı
arba'in daga cikin Dakarunmu da suka rage
anan Birnin su garzaya izuwa can Birnina
domin su jiyo mini labarin Sarkin Yaki, kuma
su gano mini halin da 'yata Gimbiya Lamrita
ke ciki, domin na tabba tar da cewar tana nan a
tsare a cikin gidan Sarautata kamar yadda na
bayar da umarni.
Lallai wadannan Dakaru su hanzarta
dawowa kafin a kammala gasar nan ta
kambun jaruntaka.
Aiki na biyu da za ka yi shi ne yanzu
ka baiwa Likita dinare dubu dari bakwai
domin yaje ya fara gudanar da babban aikin
da na ba shi".
Koda jin wannan umarni sai Hadimi
Sahalu ya risina ya ce, "An gama ya
shugabana".
Nan take Sahalu ya mike tsaye ya fice
daga cikin Turakar Likita na biye da shi.
Fitarsu ke da wuya sai Kuyangin Sarki
Gurzalu guda uku suka shigo cikin Turakar
suka shiga aikinsu na yỉ masa hidima.
Koda Sarki Gurzalu ya ga yadda ake
shriya masa abincinsa, shimfidarsa da kuma
kawar da ke cikin dakin duk da cewa yana
cikin wannan hali na jinya sai ya bushe da
dariyar murna a cikin yana mai cowa,
"Hakika duk wanda bai danđani Mulki ba a
cikin wannan duniya to bai san dadin duniyar
ba. Kawai dai rakiyar wasu ya zo a cikinta.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin
Sarki Gurzalu da Likitansa da suka yi
tattaunawar siri.

AL'amarin su Sarki Taryan kuwa,
lokacin da suka iso cikin gari sai
ya dubi Jarumi Salmanuda
Gimbiya Amrita ya ce,"'Ku tafi izuwa
Masaukinka, kuma ke Gimbiya ki ci gaba da
6oye fuskarki kada ki kuskura wani ya
shaidaki har izuwa ranar, da za a kamnmala
wannan gasa".
ob Koda jin wannan batu sai mamakiya
kama Gimbiya Lamrita, yå dubi Sarki Taryan
ta ce, "Wai shin akan wanne dalilizan ci gaba
da boye kaina alhalin ma yanzu shi Mahaifin
nawa ta kansa ya ke, babu tabbacin ma zai iya
tsira da rayuwarsa?
Ai ni burina a yanzu shi ne, na je
mu yi gaba da gaba ni da shi na gaya masa
duk irin mugayen abubuwan da ya shuka a
rayuwarsa da kuma irin tsananin kiyayyar da
na ke yi masa a yanzu, in ya so mu yaki juna
ni da shi"
Koda Sarki Taryan yaji wannan batu ne
Gimbiya Lamrita sai ya tuntsure da dariya,
al'amarin da yai matukar baiwa Jarumi
Salmanu da Gimbiya Lamrita mamaki ke nan
suka tsaya suna duban Sarki Taryan.
Lokaci guda Sarki Taryan ya murtuke
fuskarsa kamar wanda aka aiko masa da
sakon mutuwa ya ce, "Ya ke Lamrita, ina so
ki sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dole
ne ya rigaka tashi, kuma koda Zaki yaje kasa
to fa gawarsa ma abar tsoroce, kuma abar
shakka ga dukkan dabobin daji! Mahaifinki
tsohon makiri ne, masanin tuggu da makirci!
Kuma wanda bashi da imani da tausayi ko
kadan.
A yanzu hakan da yake kwance zai iya
haddasa masifar da za ta sa gaba daya duniyar
nan ta hautsine, don haka ni kaina ina
shakkarsa.
Ni dai yanzu burina da kwanciyar
hankalina kawai shi né ya amince cewar
janye batun cigaba da wannan takara ta
kambun jarumta ya tafi Birninsa domin karasa
jinyar da yake yi".
Koda jin wannan batu sai Hawaye ya
zubowa Gimbiya Lamrita ta ce, "Ni kuwa
burina shi ne Mahaifina ya rasa rayuwarsa a
cikin wannan gasa da ake yi, domnin ban ga
amfanin rayuwar tasa ba a doron kasa a
matsayinsa na azzalumi, kuma maci amanar
da ya kashe dan uwansa na jini sabo da kawai
ya hau karagar mulki."
Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan batu
daga bakin Gimbiya Lamrita sai ya yi dan
guntun murmushi ya ce, "Haba Gimbiya ai
naka, naka ne har bada!
Komai irin mugun halin Mahaifinki ai
ba ki isa ki cire jininsa daga cikin naki ba.
Mahai finki ba zai mutu a filin daga ko a
cikin gwagwarmaya ba, don haka ma ki daina
tunanin cewar zai mutu a cikin wanran gasa.
Ina mai tabbatar miki da cewa in ba don
baya tare da Gurunsa na tsafi ba a yanzu da
tuni ma ya dade da zama Zakaran wannan
gasa.
Ba wani ne ya sace masa wannan Gurin
tsafi nasa ba face Muzaina kanwar Mahaifiyar
Jarumi Imhal, wacce ita ce kadai ta rage daga
cikin zuri'ar tasu.
Koda jin wannan batu sai mamaki da
muma suka sake turnuke Gimbiya Lamrita ta
dubi Sarki Taryan cikin zakuwa da damuwa
ta ce, "Yanzu a ina zan ga Muzainat kuwa?"
Sarki Taryan ya yi ajiyar zuciya ya ce,
"Ai kin tambayeni abin da ban sani ba, sabo
da a halin yanzu babu wanda zai iya sanin
inda take sabo da karfin sihirin Gurun tsafin
da ke jikinta.
Mutum đaya ne kacal zai iya gano
hakan, kuma ba wani bane wannan mutumi
face shi Mahaifin naki...
TopA nikaina AA Misau a nan zan tsaya

Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah

Admin
AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part B. 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing By AA Misau
✍️⭐⭐⭐

(Hallau Yau Ma Dai Ina Dauke Muku Da cigaban Wannan Littafi Ku Bamu Aron Kunnuwanku
Kucigaba da antaya manaa likes and comments domin Samun cigabansu akan lokaci)
(Sannan ina dauke muku da group din da zamu cigaba da kawo litattafan da kuke nema ko kuka karanta kuke son sake karantawa
Wato https://facebook.com/groups/1511287118906332/
SAIKUNZO

Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa...
MUTUM ĐAYA NE KACAL ZAI IYA GANO
HAKAN, KUMA BA WANI BANE WANNAN MUTUMI
FACE SHI MAHAIFIN NAKI.
Kuma shi din ma sai idan ya shiga
đakinsa na sihiri da ke can Birninku ya yi
bincike.
Abin da na sani kawai shi ne, Muzainat
tana tare da mu a koyaushe, domin ba za ta
yarda ta yi nisa da mu ba, tunda ta san halin
da Jarumni Imhal ke ciki".
Sarki Taryan ya dubi Jarumi Salmanu
cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai wannan bakon
Jarumi mai abin al'ajabi, yanzu kuwa tsawon
wane lokaci Imhal zai shafe yana yin wannan
barci?
Ka sani cewa bani da wani buri wanda
ya fi na ga ya dawo cikin hayyacinsa domin
na kaishi wajen 'yata ta ganshi a raye, sabo da
hakan ne kadai abin da zai ceto rayuwarta".
Koda jin wannan batu sai zuciyar
Gimbiya Lamrita ta buga da Karfi sosai, taji ta
kamu da tsananin kishi.
Jarumi Salmanu ya numfasa ya ce, "Ai
da izinin Ubangijina nan da kamar tsawon sa'a
uku kacal! Imhal zai farka daga barcin da
yake yi, kuma insha Ailahu zai sami lafiyar da
zai iya mikewa har ya taka afafunsa".
Koda jin wannan batu sai farinciki ya
lullube Sarki Taryan da Gimbiya Lamrita.
Ba tare da 6ata wani lokaci ba Salmanu
da Gimbiya Lamrita suka yiwa Sarki Taryan
sallama suka tafi izuwa nasu Masaukin, shi
kuma sai ya nufi hanyar da za ta kaishi
Fadarsa dauke da Jarumi Imhal a gaban
dokinsa.
GimbiyA SHUMAIRA na kwance
akan gado a cikin Turakarta tana
ta faman shara barci mai nauyi
sakamakon Maganin barcin da Likita ya ba ta
ta sha, Kuyanginta sun kewayeta a zazzaune
dulkkaninsu fuskokinsu na nuna alamun
damuwa da fargaba, sai kawai suka ga ta
mike zaune zumbur! A firgice kamar wacce ta
farka daga yin mugun malarki mai ban tsoro.
Abin da ta fara ambata a bakinta shi ne
sunan Jarumi IMHAL.
Koda ta duba ko ina da ina a cikin
Turakar ta ta ta fahimci a inda take sai ta
sauka daga kan Gadon na ta da sauri kuma a.
dimauce da nufin ta ruga waje.
Kawai sai ta ga an turo kofar dakin na
ta an shigo.
Ba wani bane ya shigo ba face
Mahai finta Sarki Taryan fuskarsa cike da
annuri.
Shumaira ta karasa gareshi da gudu ta
rungumeshi tana mai fashewa da kuka ta ce,
"Ina masoyina Imhal?
Shin ya mutu ne ko kuwa tuni ma an
binnc gawarsa?"
Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan
lambaya sai ya janye jikinsa daga cikin na
Shumaira ya sa hannu ya share hawayen
sannan ya ce, "Kwantar da bankalinki ya ke
'yata, ina mai yi miki albishir da cewar
Masoyinki Jarumi Imhal na nan a raye kuma
nan da cikar tsawon sa'a biyu da rabi ma zai
farka daga barcin da yake yi har ya iya
mikclewa tsaye ya yi tafiya da kafafunsa".
Koda jin wannan batu sai farinciki ya
mamaye Gimbiya Shumaira, ta dubi Sarki ta
ce, "Ma za ka kaini inda yake na ganshi da
idanuna domin na samu kwanciyar hankali".
Sarki Taryan ya cc, "Haba ya ke 'yata,
me ki ke ci na baka na zuba? Ai kamata ya yi
dai ki yi hakuri har ya farka daga barcin
tukunna, in son samu nc tunda yana dauke da
babban rauni a jikinsa".
Gimbiya Shumaira ta ce, "A gaskiya
zuciyata da jikina ba za su iya daukar wannan
hakuri ba har na tsawon sa'a biyu da rabi.
Ya kai Abbana, ina rokonka da ka
hanzarta kaini wajcn abin begena domin idan
AA Misau ke Magana
ban ganshi ba yanzu zan iya shiga cikin wani
halin mara dadi".
Koda jin haka sai Sarki Taryan ya
gyada kai cikin alamun damuwa ya ce, "Shi
ke nan zo mu je na kai ki inda yake".
Nan take Sarki Taryan ya kama hannun
Gimbiya Shumaira ya ja ta suka fice suka nufi
wata hanyar dabarm a cikin gidan sarautar.
Sai da suka yi tafiya mai nisa sannan
suka iso wani babban daki na musamman
inda aka saba saukar manyan Baki.
Shi dai wannan daki an kebeshi ne a
wuri dabam inda ba kowane ya san da shi ba,
hatta kuwa da yawan Hadiman gidan.
Kusan shi ne đaki na karshe a cikin
gidan sarautar, kuma sai an kure wani dogon
lungu mai duhu sannan za a iso wani babban
fili inda dakin yake.
Da isowarsu kofar đakin sai suka iske
Dakaru sama da guda dari ukun sun kewaye
đakin don tabbatar da tsaro.
Koda Dakarun suka ga Sarki Taryan
tarc da 'yarsa Gimbiya Shumaira sai suka
risina suka kwashi gaisuwa, kuma suka dare
da sauri suka basu hanya.Kai tsaye Sarki Taryan da Shumaira
suka kunna kai cikin dakin.
Sai da suka ratsa ta cikin wani katon
falo sannan suka shiga cikin dakin da Jarumi
Imhal ke kwance.
nan Shumaira na sa kafarta guda cikin
đakin sai ta hango Jaruni Imhal kwanceua
akangado yana ta faman shara barci, gai
alamar numfashi akan kirjinsa.
Nan take ta ji wani irin dumbin
farinciki ya lullu6eta, har ta yunkura za ta
juya da baya tunda hankalinta ya kwanta sai ta
ji Jarumi Imhal ya fara sambatun Mafarki.
Cikin hanzari ta juyo da baya ta nufi
kan gadon da yake kwance, sai da ta iso kansa
sannan ta zauna akan gefen gadon daf da shi
sannan ta kara kunnenta daf da bakinsa domin
taji abin da yake fadi sakamakon cewar yana
magana ne a hankali.
Koda ta ji kalmar da yake ambata sai
zuciyarta ta buga da Karfin gaske, hankalinta
ya dugunzuma ainun, kuma ta kamu da
Tsananin bakinciki, ba ta san sa'adda hawayen
takaici suka zubo ma ta ba.
Sarki Taryan da ke tsaye sai shima
hankalinsa ya tashi sakamakon ganin halin da
'yarsa ta shiga.
Bisa wannan dalili ne shima ya karaso
daf da Jaruni Imhal ya sunkuyo dai-dai kansa
ya kara kunnensa.
Kawai sai yaji Imhal baya ambaton
komai face sunan Gibiya Lamrita.
Yana hada idanu da Shumaira sai ta
fashe da kuka sannan a mike tsaye ta
rungumeshi tana mai cewa, "Ya kai Abbana
yanzu ina zan sa raina na ji dadi tunda ba ni
da gurbi a cikin zuciyar wanda na ke bege
dare da rana?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki
Taryan ya kamu da tsananin tausayin 'yarsa
Gimbiya Shumaira ya kara kankameta a
kirjinsa kuma yai shiru ya ma kasa cewa
komai, kawai sai ya janyeta suka juya da baya
suka fice daga dakin.

LOKACIN DA Jarumi Salmanu da
Gimbiya Lamrita suka isa
Masaukinsu wato gidan da suka
karba Haya tun daga ranar da suka iso Birnin
sai kowanncnsu ya tsaya a kofar dakinsa ya
kasa shiga.
Al'amarin da ya bai wa Kowannensu
mamaki ke nan. Ba tare da Salmanu ya dubi
fuskar Lamrita ba ya cc, "Kina da wata
magana ne da ki ke son ki yi min?"
Koda jin wannan tambaya sai Lamrita
ta yi murmushi ta ce "Ai kaima ka sani cewa
ina da maganganu da yawa, to amma tun da
yanzu Magariba ta yi me zai hana mu
huta tukunna har ma ka yi Ibadarka in ya so
sai na zo dakinka mu zauna mu tattauna?"
Koda jin haka sai Salmanu ya girgiza
kai ya ce, "A'a ba za a yi haka ba, duk abin da
zai sa mu kadaita ba zan yarda da shi ba,
domin karya dokar Addinina ne.
Sai dai ki bari bayan na kammala 'yan
ayyukana na fito harabar gidan nan".
Larnrita ta yi murmushi ta ce, "Shi ke
pan ba nstsala"
Tana gama fadin hakan sai ta shige
cikin dakin na ta, shina bai tsaya bata wani
lokaci ba sai ya kunna kai izuwa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment