Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/21, 6:10 AM] Bareemah Rabiat Ibrahim✍️: https://chat.whatsapp.com/IODG6CVfyVb9m3vQrw0vq6



💋YANBIYUN MACIZAI💋

The twins snake🐍🐍
BY
MIHZ. BAREEMAH
Daga alkalamin ✍️✍️mihz bareemah



Dedicated to essential group members thank you for the support you people give to me 👏
Free page1️⃣

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
_______________________________
_______________
BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me
via: 07083134831
GARGADI
KAR A KUSKURA A CANZAMUN WANI ABU NA LITAFFIN NAN, TA KOWACE SIGA BAN AMINCE AYI AMFANI DASHIBA, KUHUTA LAFIYA

DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

GEMBU MAMBILA TARABA STATE
Wani irin hadarine mai masifar karfi, dakuma duhune yamamaye illahirin yankin gembu membila. yayi masa kewanya tako wani sashi gabas da yama, kudu, da kuma arewa, gangami yaketayi a yayinda ya hade da duhun dare mai gauraye da duhun damina’ hakan yasa babu abunda yake tashi a wanan yankin sai wasu irin tsawa dakuma rugugin da aketayi babu gaggautawa,
wata iriyar iska mai dan Karen karfine dayake tatareda sanyine ke cigabada kadawa da karfin tsiya, a dai dai irin wanan lkc ne kuma gaba dayan bani adama mazauna cikin gidaje. sunyi nisa a bacci kasancewar karfe biyun darene,!

A cikin babbar masarautar membila katuwar masarautace da bazan iya misaltashi ba. wanda inka shiga cikinta garine guda dan kowa
tako ina kaikawo aketayi dukda kasancewarsa darene. shiyasa ama kasancewansa gidan sarautane wanan ne yasa haryanzu aketa kaikawo, kama daga bayi dakuyangun wanan masarautar kuwa da posion din aikinsa.
Masarauta ce babba wanda kedauke da bangarori daban daban. hakama kuma ta kunshi kofofi kala kala, masarauta ce maikyau dan tundaga wajenta zaka gane an zuba kudi gurin tsarashi,.

Gudu takeyi da iya karfinta a yayinda gashin kanta yake abaje tamkar mahaukaciya. ga kuma turtsetsen cikin dake gabanta, wanda sam sam hakan bai sata ta saurarawa kanta ba, wajen tseratar da rayuwarta ba
Gudun takeyi sosai tanayi tana waiwayan bayanta, kara karfin kudun tayi ganin alaman sunkusa cinmata, daidai tayanko wata kofar dazata sadaka da kofar karshe wanda daga shi kabar masarautan kenan,
cak ta tsaya, ganin hanyar takasu kashi biyu?
juyawa tayi takali hagu da damanta ko ina shuru babu alaman motsi dasauri tadoshi hanyar dajin mambila. daidai wata baiwa tafito danyi fitsari, yunkurawa tayi tareda daga rigarta sama.

fara fitsarinta keda wuya, kamar walkiya taga giftawar abu dasauri tamike tareda jan rigarta kasa. juyawa tayi danbin bayan abun, taku daya ana biyu taji ance ke? da mugun tsoro tajuyo, wani irin mumuna faduwan gabane ya ziyarceta,! ganin wasu garda gardan mazane guda biyar. a tsaye a gabanta ai batasan lokacin da tasake fisarinba. da wani irin murya mai amo taji daya daga cikinsu ya ce kifito da ita yanzun nan kokuma yanzun nan ki bakunci lahira. cikin tashin hankali baki na rawa ta ce
wa wa’ wace a tsawace yace tana ina nace cikin rawar baki tace wlh wlh bangantaba ama dai naga? ke yasake fada a tsawace bazaki fito da itaba kenan saina sa miki wuka,? alama yayi wa daya daga cikinsu dasauri wanda akayima alama yazaga tabayanta tareda saka mata wuka a wuya.
Ya ce zakiyi Magana kona datse miki numfashi, jiki narawa tace danallah karka kasheni wlh niban san komaiba?


Banma san wakuke Magana akaiba a tsawace yace to meyakawo ki nan gurin a daren nan, dasauri tace fitsari nazoyi ama kuyi hkr bazan karaf bata kaiga karasa maganar dake bakintaba. daidai tsakiyan bayanta yacaka mata wukan tareda yin cilli da ita juyawa sukayi suka cigaba da, bin bayanta


DAJIN MAMBILA
Sosai take gudun danko kallon gabanta ma bata iyayi, ga maranta dayake kokarin kulewa. numfashinma dakyar take saukewa. tana kaiwa daidai wani katoton dutse wani irin jirine ya.?
[1/21, 6:10 AM] Bareemah Rabiat Ibrahim✍️: https://chat.whatsapp.com/E4N9Uc4IW6GFA1ESf2AxmA

💋YANBIYUN MACIZAI💋

The twins snake🐍🐍
BY
MIHZ. BAREEMAH
Daga alkalamin✍️✍️ mihz bareemah



Dedicated to essential group members thank you for the support you people give to me 👏
FREE PAGE 2️⃣

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
_______________________________
_______________
BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me
via: 09167472935
GARGADI
KAR A KUSKURA A CANZAMUN WANI ABU NA LITAFFIN NAN, TA KOWACE SIGA BAN AMINCE AYI AMFANI DASHIBA, KUHUTA LAFIYA
DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

*Naceba duk inda kukagan typing error to kawai kubasar wlh dakyar nayi editing🤧🤣🤧🤣

*
tana kaiwa daidai wani katoton dutse wani irin jirine ya kwasheta. tim takife cikinta saman wanan duten’’ wani rirn razanan kara tasaki. Dakyar tamike tareda jan jikinta jin alamar tafiya tayi dakyar dasauri ta rarafa zuwa bayan wani bishiya.
rukubewa tayi a bayan bishiyan ciro dankwalinta tayi tacusashi cikin bakinta. ga azababen ciwon marandake adabarta, alamar naguda ce take shirin zuwan mata? kara tura zanin tayi abakinta ganin harsun karaso cikin dajin. daga inda take tana iya hango yanda suka dage sai nemanta sukeyi
waigewaige suka shigayi ama ko digon alama mosti basujiba!,
daya daga cikinsune ya ce oga ina ganinfa bata a wanan dajin babu inda bamu dubaba ama babu ita babu alamarta, gaskiya ni nafara gajjiya mukoma kawai dasuri dayan ya ce ni wlh nama fara tsorata wanan dajin fa, mai hatsarine? gwara tunda wuri mubar wanan dajin tunka.

Shuru yayi saboda mugun kallonda ogan yabisu dashi. a nitse wani daga cikinsu ya ce taya kake tunanin mutafi idan muka koma me zamuje muje mufadawa! gimbiya zaliha?
dasauri matsoracin cikinsu ya ce aha kawai muce mata munriga mun aiwatar da aikinmu. Dayan yankuma cewa eh wanan shawarar tayi mufada mata kawai munkashate, Munkuma zubar da gawanta. Dasauri ogan yajiyo yakaleshi yace kanada hankali kuwa a ina kuka kasheta din.
yace oga kayarda wlh dan wanan shawaran dakake ganin shawarace mai kyau. Shuru ogan yayi yana nazarin maganganun su , can dai yace ina zuwa kujirani,

juyawa yayi yafara tafiya, a daidai gurin bishiyan yaja yatsaya jin alamar kamar motsi mutum a wajen, wanan yasan, ta kara kankame jikinta, a waje daya tareda danna abunda ta toshe bakinta dashi sosai. ga azaban naguda daya taso mata gadan gadan ama babu yanda ta iya dole tasamu tasteratar da rayuwanta ko dan cikin dake jikinta, tsayawa yayi ya kasa kunne yaji dakyau? jin kamar saukar numfashi, Cak ta tsayar da numfashinta kudun karya yaji, ganin alaman hankalinsa yana neman karkatowa izuwa gare ta, yana kuma son yagane akwai mutum a wajen? Sai da yazo gab da bishiyar yaja yatsaya kuma motsi kadan zatayi yagane tabas akwai mutum a nan gurin. Sosai tayi namijin kokari dan gannin ta rike numfashinta dakyau!. kusan mint 10 yayi a gurin a tsaye aman shuru babu alaman komai , can dai yagaji da tsayiwa. Ya fara tafiya dan barin gurin. yana zuwa yace da guys dinsa sutafi kawai juyawa sukayi suka fara tafiya dan barin dajin;
a galabaice tasauke hanunta kasa tareda yin zaman dirshan tawani sake wani irin marayan kuka, sosai take kuka cikin kuka ne tashiga fadin inalillahi wa inna ilaihi rajiuna wanan wace iri rayuwace, dasauri takai hanun ta dafe cikinta jin maranta yasake kulewa. mutsu mustu tashiga yi, tana karanta kowani irin adu’an da yazo bakinta, wani irin kara tasaki jin
Afuwan inshallah gobe Zaku gan long page👏

COMMENT & SHARE PLS
[1/21, 6:10 AM] Bareemah Rabiat Ibrahim✍️: https://chat.whatsapp.com/IODG6CVfyVb9m3vQrw0vq6


💋YANBIYUN MACIZAI💋


The Twins Snake
BY
MIHZ. BAREEMAH
Daga alkalamin ✍️✍️mihz bareemah


Dedicated to essential group members thank you for the support you people give to me
FREE PAGE 3️⃣

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than
the sword🗡️*

_______________________________
_______________
BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me
via: 09167472935 or 07083134831
GARGADI
KAR A KUSKURA A CANZAMUN WANI ABU NA LITAFFIN NAN, TA KOWACE SIGA BAN AMINCE AYI AMFANI DASHIBA, KUHUTA LAFIYA
DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

kowace aduan da yazo bakinta tashiga karanto wa wani irin kara tasaki, jin alamar kamar wani abu kulolo a karkashinta,
dasauri tamikar da kafafuwanta tareda daga katuwan rigarta sama, a hankali tadaga gugunta sama nan da nan saiga kan jaririyar ta tafito. kasa kasa ta dinga karanto adua tana mai runtse idanunta ta wani sake dogon nishi, a take jaririyan tafado sosai takeyin adua, tareda kara sakin nishi nan take wata jaririyar tabiyo baya,
babu bata lokaci, a hankali tashiga sauke nufashin wahala kafin kuma tafara jada baya sanan taja rigarta tarufe; Idanunta ne yashiga juya mata tashiga ganin ko ina biyu biyu, Sakamakon jinninda yabile mata, gyara kwanciyarta tayi dakyar a hankali tashiga lumshe idanunta.
kasa kasa tashiga ambaton sunan Allah lokaci daya tasake bude idanunta. kwayar idanunta da yiyi fari sol yashiga kafewa a hankali a hankali. lub yarufe daga nan rai yayi halinsa, allahu aqbar
WANAN KENAN

zaune take a kan kujera irinta sarauta tadan kishingide a jikin kujeran, a yayinda bayi sunkai su goma wadanda suke zagayeda ita suna maiyimata hidima, uku na zaune a gabanta. Biyu na gyara mata fruits a yayinda daya nadaga gefe tana mika mata fruits din’ ita kuma tana karba tanaci a hankali cikin izzah, kallo daya zakayi musu ka fahimci ko wannensu a tsorace suke? basa son suyi wani abu waishi kuskure bale har ace zaayi musu hukunci. dan haka suke taka tsantsan da itadaga gefenta bayi uku ne a tsaye masu yi mata fifita. Ana cikin haka ne saiga wata tashigo cikin dakin dasaurinta tareda zubewa a gaban matar tana mai cewa takawarki lafiya magajiya kuma gimbiya a gurin sarki mai adallci allah yaja datsawon kwananki gaba!. gaba dayan bayin suka amsa da Amen jakadiya tacigaba da Magana tace ranki shi dade labari mai dadi dakuma gardi nazo miki dashi, daga mata hannun tayi alamar ta dakata?

juyawa tayi bangaren bayin dake yimata hidima da hanun tayi musu nuni da zusu iya tafiya dasauri duk suka mimike tareda barin gurin a hankali tadawo da hankalinta gurin jakadiya. cikin izzah tace aha inajinki?
sasauta murya jakadiya tayi a hankali tace ranki shi dade komai yatafi yanda muka tsara, yanzu nan muka gama maganar da sule yakuma fadamun komai yakankama, yanzun haka, gimbiya Aleesha dasauri Gimbiya Zalliha tace dakata. kirata da sunananta Aleesha, banason nakarajin Gimbiya daga bakin kowace baiwa tafada tare da yin kwafa, dasauri jakadiya tace allah ya huce zuciyar sarauniyar sarki , a hankali tace a akiyaye jakadiya tac inshallah sanan tacigaba da yanzun haka Gimb saikuma tace Aleesha tana lahira.

Sanan koda ace sarki zai zagaya illahirin garin Gembun Mambila bazai taba samun gawanta ba, wani irin dariyane Gimbiya Zaliha ta fashe dashi, a lokaci daya kuma tasake komawa ta hade rai;
Tace ina fatan babu wanda yaji wanan maganar kuma babu wanda yaga lokacinda suka biyo bayanta a daren jiyanko, Dasauri jakadiya tace babu ranki shi dade kafinma sushiga bangarenta saida na tabatarda sariki yabaro bangaren nata tukun.
na nakuma tabatarda babu mahalukin da yake numfashi a duniyan nan kowa yayi nisa acikin barcinsa, sanan nayi musu jagora izuwa dakin nata, bayan hakanma, akan idona naga tafito dagudu tayi hanyar yama. Kinkuma san wannan hanya mai hatsarine, bare kuma uwa uba dajin Mambila.

Gimbiya Zaliya tawani sake murmushin jindadi, a hankali tace jakadiya aikinki nakyau dan haka kyautarki ta dabance, kije zan aiko miki da tukwaicin ki akawo miki. washe baki jakadiya tashigayi tareda murnan yau ta faranta ran uwar gijiyarta wato Gimbiya Zaliha.
Tashiga fadin Allah yabar mana ke Gimbiya sarautar mata farar mace alkamban mata uwa a gurin magajin sarki,
Daga mata hannun tayi sanan tayi mata nuni da hanun alamar zaki iya tafiya, Dasauri jakadiya tamike dan barin waje . gimbiya zaliha tasake cewa dakata? tacigaba dacewa idan kinje kikirawo min sarkin gida kice ,masa ina son ganinsa yanzu yanzu nan! Cikin rawan jiki jakadiya tace.

Angama ranki shi dade. Allah yaja daranki tajuya tatafi jiki na bari,
niko mihz bareemah nace ajuri zuwa rafi wata rana tulu zaifashe allah dai yasa mudace idan muka dace mudafe kar yayan shugu su kwace

FADAR SARKI
Manya manya mallaman fadane suke a zazaune kusa da kujerar alfarma wace sarki yake a zaune, a yayinda gaba dayansu basu a cikin nutsuwarsu saboda batar Amarya kuma matar sarki wato Gimbiya Aleesha wace aka nemeta aka rasa tundaga daren jiya zuwa safiyar yau. sosai suke cikin tashin hankali gaba daya mutanen garin Gembun Mambila, abun yadaure musu kai. yana kuma basu mamaki? kowa sai fadan albarkacin bakinsa yakeyi.
dogaraine kuda hudu biyu a gefen sarki daya kuma yana rike da bullalar dorina irinta dukan rakumi nan murdadiya mai taurin gaske, a hankali sarki ya dan daga kansa da idanunsa wanda suka rine sukayi ja, saboda tashin hankalinda yake ciki yakali gawan baiwan da aka kasha a daren jiya, a yashe a gabansa, an lulubeta da farar kyale’ wanda jinni duk yabata wanan kyalen gakuma sauran bayin wadanda suke daki daya da ita, kowace hankalinta a tashe,
dukaninsu a durdurkushe. cikin razanar dasu dansuji tsoro sufadin gaskiya daya daga jikin dogari guda daya yace dasu kuntabata bakusan lokacinda tafita daga dakinba? dasauri dukansu suka hada bakin wajen cewa a a, a a wlh bamu saniba? saboda lkc dukaninmu munyi nesa acikin bacci. A hankali sarki yace akaisu a rufesu tukuna har sai an gano gaskiyar lamarin, ama banda horo a kuma tabatar da ana basu abincci akai akai. Angama ranka shi dade. nan aka kwashesu sai gidan kulle. niko nace allah sarki bayin allah basujiba basu ganiba.

DAJIN MAMBILA
[1/21, 6:10 AM] Bareemah Rabiat Ibrahim✍️: https://chat.whatsapp.com/IODG6CVfyVb9m3vQrw0vq6



💋YANBIYUN MACIZAI💋


The Twins Snake
By
MIHZ. BAREEMAH
Daga alkalamin ✍️✍️mihz bareemah


Dedicated to essential group members thank you for the support you people give to me 👏

FREE PAGE 4️⃣
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
_______________________________
_______________
BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me
via: 09167472935
GARGADI
KAR A KUSKURA A CANZAMUN WANI ABU NA LITAFFIN NAN, TA KOWACE SIGA BAN AMINCE AYI AMFANI DASHIBA, KUHUTA LAFIYA
DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.

4:58 daidai sanyine da iskar asuba, mai tatareda niama kana kuma yake sanyaya jiki shine yaketa faman tashi a cikin wanan dajin, ayayinda bishiyoyi dakuma shukoki suketa faman kadawa, adaidai wanan lokacine kuma nahangota, tsaye take da wata katuwar riga wanda tsawonta ya zarta ta sau goma, rigar irin na sarautane wanda ake daura mata kambu akanta mai balain daukar ido sai kyalli yakeyi kana ganinshi kasan na zalar zinarine.
kallo daya zakayi mata ka fahimci cewan aljanace ba mutum bace. idanunta sunyi jajir dashi. ayayinda gashin kanta suke abaje iskar damuna tana kadata. Hannunta daya yana rike da sandan irina sarautarnan?
dayan hannun kuma tana rike da wata katuwar kwariya wande aka zuba wani abu mai kama da jinni, sosai takurawa wadanan majizanda suke a nanade da jariran nan ido, Kusan mint 10 tayi tana kalonsu. da wani irin kara ta ambaci wani suna, ZULFAAN kusan sau uku, adaidai lokacine kuma akayi wani irin tsawa mai matsukar razana tareda walkiya nunasu tayi da sandarta atake wani abu mai hasken balayi yafito daga sandan yashiga jikin yanbiyun nan guda biyu’ a hankali a hankali macizan suka shiga warwarewa tareda barin wajen gaba daya takawa tayi zuwa kusa dasu tareda durkusawa kasa, Sandar hanunta ta ajiye tasaka Hannun ta dago da kan Gimbiya Aleesha. wanan abundake cikin wanan kwariyan tadauko tareda dibawa ta watsa mata a fuska, tasake debowa ta watsa mata kusan sau uku, atake jikin gimbiya aleesha yashiga karkarwa wani abune yafara fitowa daga cikin hancinta da bakinta kusan mint 6 kafin komai ya lafa.

Kwantar da ita tayi tajuyo bangaren yanbiyu suma tayi musu irin abunda tayima Gimbiya, ama su ko gizau basuyiba sai blue eye dinsu dayaketa kyali wasu abubuwa suna fitowa daga idanunsu yana shiga idon wanan aljanar. shafasu tayi hankali ta furta,
Jazla.nazla daga kanta tayi sama tareda fashewa da wani irin razananiyar dariya mai tsoratarwa. A cikin dariyan ne tashiga fadin?. Jazooooo jazooooo jazooooooo! lokaci yayi dazan kawo karshenka.? Kafin a hankali tasauke kanta kasa,,
zut wani abu yafito daga idonta yashiga idon yanbiyun nan. mikewa tayi tareda saka hannun ta daukesu a tare taje daidai inda Gimbiya take a kwance, takwantar dasu a kijinta. Takoma tadauko sandarta da kwaryanta, daura sandar tayi a jikinsu itama tarike bangare daya, tareda rutse idanunta nan take wata iska tataso mai matukar karfi tazo takwashesu tayi sama dasu gaba dayansu.

Basu sauka a ko inaba sai a garin(JAMAARE). a cikin wata ruga maisuna RUGA FAIKO. a nan tsakar gidan suka zube dukansu A hankali ta mike ta taka har zuwa wata kofar dake a bude Daidai bakin kofar taja tatsaya da wata irin murya mai amo da sauti tashiga sunan sa (ARDO) Ardo wanda yariga yagane muryan ko wacece? mikewa haja matar Ardo zatayi, dasauri Ardo yace dakata hajara inazakije? kizauna bari naje naduba, ya mike da sauri yafito, a hankai yadaga Labulan dakin ganinta yayi a tsaye kamar gunki dasauri yakarasa fitowa daga dakin jiki narawa yace (BOODIMAZA) ganin wata mata da jaririya a yashe a kuma tsakar gidansa dasauri yajuyo? Yace Boodimaza wadan nan bayin allah’n fa daga ina kika samosu,? dago da jajayen idanunta tayi takaleshi tajuya takali gimbiya, tasake juyowa bangaren Ardo.

Ta bude bakinta da muryanta mai tsoratarwa. tana mika masa kwaryan hannunta tace gashi karbi wanan katabatarda kayi musu aikin yanda yakamata inason daga yanzu zuwa wayewar gari katabatarda tatashi.
hannu yasa yakarba kwaryan tareda kyada mata kai, juyawa tayi taje ta dauko yaran Tamika masa. dasauri Ardo yaja da baya saboda firgitan dayayi yadago yakaleta yace Boodimaza ina kika samo yayan jinsinku? a gaskiya bazan iyaba dama ace jinsin mune na yan adam to shine zan iya karbansu ama,?
daga masa hannu tayi a kausashe tace dakata, zuwa yanzu ranta idan yayi dubu yabace idanunta sunsake rinewa, harwanin wuta wuta yakeyi. da wani irin razananiyar murya tace su din jinsu bani adam ne ba aljanu bane, sai dai, ina mai gargadinka daka kakiyaye, daga haka tabace, bat.
Hango tahowan matar Ardo zata fito daga daki gudun karta ganta, mallam lafiya? kaida waye kak? kasa karasawa tayi ganin ardo rike da yara yaranma yanbiyu Dasauri cike da murna tace mallam a ina kasamo mana yanbiyu? Tana karasowa tawani ja dasauri tashiga fadin inalillahi mallam aljanu llahilaa illahu tashiga tafa hannu tana daura hannu akai cike da tsoro tace mallam?

Kasa kasa mallam yace ya isa hajara karki taramun jamaa, ba aljanu bane kingama mahaifiyarsu can dasauri haja tajuya takali bayanta. ardo yaci gaba dacewa sudin bayin Allah ne kuma suna neman temako nikuma nadau alkawarin zan taimaka musu ki kwantar da hankalinki, sosai tafahimta takuma yarda da mijinta dari bisa dari.

Hannu tasa takarba yanbiyu daga hannun Ardo tashigar dasu daki tareda kwantardasu, tadawo ita da Ardo suka cicibi Gimbiya suka kaita cikin wata daki daban. kwantarda ita sukayi asaman katsifar dakin, dasauri Ardo yace jirani ina zuwa yana

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment