Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kumani a iya sanina Hauwau mai biyayyace,tana batagirmanta suna kuma zaune lafiya,Toni meyasa takeyimin haka?saboda nakara aure kawai??meyasa suwaiba take dafani da ruwan Dana kasa tantance na sanyine kona zafi?metakeso inyimatane tagane inasonta?tagane haryanzun yadda take acikin zuciyata bata canzaba,tasancewa.......................
Kamshin turarentane yafara katsemai tunani,yadago dasauri yana kara kallonta,tayi shirin kwanciya bacci,jikinta sanye da kana nan kayan bacci,Wanda duk sukafito da ainihin halittata afili,sai kamshin turare dayake tashi ajikinta,.
Takaraso inda yake anatse,shikau idanunsa NA kanta,
Hannayensa tafara kamawa,tace love baka saba kaiwa wannan lokacinba,meke faruwa?miyene yakeso yahanamin mujina bacci?
Yajanyota yazaunar da ita kankafafunsa.
Yace:Afuwan babyna,bawani Abu daya isa yadaga Mani hankali idan inatare dake,domin kuwa keme share hawayenace acikin kowane irin hali,inayina sauran maza Addu'ar samun mace mai kyawawan hali irinnaki,domin kuwa duk Wanda yayi dace dasamun mace irinki yagamayin kuka,I LOVE YOU Hauwa'u,yayimata kiss a kumatunta.
Tayi dariya tare dakara narkewa ajikinsa,tace to muje kayi wanka kakwanta hakanan,kaga dare yayi.
Yayimata wani irin kallo cike da tsantsar sonta acikin idanunsa,yace to zakiyimin wankanko?
Tace to wannan kuma aiba sabon abubane.
Sukayi dariya baki daya,tare dashigewa uwar daka,yana sabe da ita akafadarsa.
Haka yakasance cikin samun kulawa,a kwanaki biyunnan dayayi adakinta,tana nunamasa tsantsar soyayyar dasai kayi tunanin ma yadda take sonsa shibayama sonta haka,nankau tsabar iyakula da mujine kawai.
Misalin karfe biyar nayamma yashiga dakin suwaiba,yanayin sallama saiyafara kwalamata kira,dacewa
Sweety!Sweety!!kina inane kifita mana,yakara tura kansa cikin dakin,tare dakara nabatawa haba Sweetyna saikace bakowa?
Kafeshi da idanu tayi cike da mamaki,tayi sororo tana kallonsa.
Yace AAh!waidama kinajina kikayi shiru?
Tace yo aibansan dani kakeba,yau kuma wata sabuwar yaudararce kabullomin da ita.
Yace yaudara kuma?
Tace yoto aini bantaba jiba,yau kasanyamin wannan sunan kuma?
Ya kyalkyace da dariya,yace to aikinji matsalar taki,ko sunanma baki iya amsawa,to bari inkuraki da sunan dakikasaba,Suwaiba!shikenanko?,koshima yaudararce?
Tace umfh!!kaidai kasani!niduk wata dubara nan dazaka bullomin da ita kallonka nake karrr!humf waini zaka dauka Mara wayau!yanzunne kasan kakirani da Sweety?
Yakama hannunta tare dafadin ajiye kayannan zauna,muyi magana.
Tace ammadai aikunne kejiko?
Yace nasani amma dai zokizauna kiji.
Sannan tazauna,tare dafadin inajinka.
Yace yawwa tokokefa,mezaki bani inci?
Tace AAh!wannan wace irin tambayace?yawuce abinda kakawo,kaga Nasser dakata!duk wani kwane-,kwane nan dazakayimin na yaudarace kokuma munafunci!bazasu taba wanke laifinka awurinaba!!
Yamaimaita,yace laifi?laifi kuma?
SHARE!!
Suwaiba laifin menayimaki?don Allah sanardani.
Tace Nasser aibazaka ganeba.
Yamatsa hannunta da karfi,yadda yatabbatar taji zafi,yace kobazan ganeba saikin sanar dani,yakuma daure fuskarsa alamar babu wasa,yace gara ayita ta kare yau!suwaiba yau saikin fadamani laifina koda bazan fahimtaba!!
Idanunta sukayi rau! rau!!suka ciko dahawaye,tace Nasser dani kadaice awurinka,yanzun munzama mubiyu,dabiarka da halayyarka tacanza ,koban fadamakaba,kai kanka kasan dabahaka kakeba,Nasser kacanza Mani!dai dai nan hawayen dake kwance cikin idanunta suka ziraro.
Hakanan saiyaji tausayinta yakamasa,yasassauta rikon dayayimata,sannan yace:
Haryanzun bangane abinda nacanzamakidashiba,akwai abinda nakeyimaki da yanzun nadaina?kokuma akwai abinda nakeyimaki yanzun Wanda bakyaso?
Yace a'a amma inaso kafahimta Nasser kowace mace tanada kishi,yin aurennan dakayi naga kabullo dawasu abubuwa dayawa,wadandani bansankadasuba,gaba daya Nasser rawar jikinka akan Amaryar nan taka yaki karewa,kullun dokin ta kake kamarranar akakawomaka ita,ko amgayamaka cewa ni zuciyata tadutsece?banajin zafinkomai idan'anyimani badaidaiba?
Bawai inanufin ince banason aurenka daitabane,niban isaba,tunda ya halastamaka,amma nalura soyayyar dakakeyimata nibakayimin irinta,baburina inrabu dakaiba,a'a sonakeyi ka kwatanta adalci atsakaninmu.
Yace akwai abinda kikaga nabata kebanbakiba?
Tace:a'a.
Yace:akwai abinda nayimata kebanyimakiba?
Tace:a'a
Yace:towane adalci kikeso ayi yanzun?
Tadago idanunta jajur takara kallonsa,tausayinta yakara kamashi,duk dayakasa gane laifinsa awurinta.
Tace :akwai!duk ranar dazaka koma dakinta akwai banbanci daranar dazakazo dakina Yakara kallonta arazane yace wane irinbanbanci kuma?
Tace:doki,zumudi,dakuma kosawa.
Yace waye yafadamaki haka?
Tafashe dakuka tare dafadin angayamaka nibanida hankaline dabazan ganeba!!itace babynka itace love dinka,itace sweetynka,har agaban kowa kana fada mata haka.
Yace toke yanzun bagashi nakiraki da Sweety dinkinki amsawaba,Suwaiba bawani abune yake damunki ba ,KISHINE,kuma duk abinda kika lissafomin amatsayin laifina balaifi bane,bazance Allah yarabaki da kishinnan nawaba,domin hakan yatabbatarmin da cewa kinasona sosai,sai daiince Allah yarage maki zafin kishin,Suwaiba inasonki,Daga kanharshena harcikin zuciyata,abinda nakefadamaki gaskiyane,kada kidauka cewa aurennan danayi yarage wani Abu Daga cikin sondanakeyimaki,haryanzun kina nan kamaryadda kike acikin zuciyata.
Kikawar da idanunki Daga kan Hauwa'u,kidauka tamkar babu ita acikin gidanki,kimanta da ita kishareta acikin zuciyarki,saikiga kinzauna lafiya.
Amma idan hankalinki NA kanta duk wanimotsinta kina sanya mata ido,to bayadda za'ayi kizauna lafiya ,domin kuwa abinda ba'ayibama sai zuciyarki taraya maki cewa anyi,tokinga daganan sai shedan yasamu wurin zama acikin zuciyarki,yana saka maki sawu abubuwa daban acikin tunanin ki,abindama baifaruba sayya kawatamakishi dacewa yafaru,todaganan shikenan bazaki karasamun kwanciyar hankaliba.
Tace to yanzun kananufin duk abinda nace kanayi baizama laifiba?
Yace:toh!inkin daukeshi amatsayin laifin shikenan,idan har laifi nayimaki,
Yasauko kasa yatsugunna da gwiwoyinsa,yace nadauki laifina dakuma kuskurena,don Allah suwaiba kiyi hakuri,bazansakeyiba,amma inarokonki daki kawar da hankalinki akanmu nida Hauwau,idan kikayi haka zaki zauna lafiya,bakiga ita harkarta kawai takeyi batadamu damuba.
Ya miketsaye tareda kamo hannayenta yatadata tsaye suka fuskanci juna,yakafeta da idanunsa,yana kara nazarin fuskarta,haryanzun batasauko Daga irin zafin kishin datake kaiba yayi mata murmushi yace Suwaiba kinasona dayawa.
Tace aishiyasa kake wahalar dani.
Yace to Daga yau nadaina,jeki shirya kiyi wanka kisanya turare mekamashi,barci zanyi dawuri yau.
Tayi dariya tareda an she hannayenta Daga nashi,tajuya tashige daki,don tayi wanka.
Shikuma nanyaauna bisa kujera yana tunanin irinwannan kishi na suwaiba,sai dai yanakara godema Allah da abin yatsaya akansa kawai,duk iyafadanta da fitinarta,batayima Hauwau,tsakaninta dashine kawai.
Yayi dariya,tare dagirgiza kai yace watankan tunda ninayimata laifin baritahuce akaina nikadai,humf!Suwaiba rigima! Lokaci guda kuma yatuna ranar da Hauwa'un tasamu kwana bakwai agidan,a wannan ranar itace ranar da za'araba kwana,yakuma tuna iyakar abinda yafaru a wannan ranar.
**** **** **** **** **** ***** *****
Bayan yataso masallacin sallar isha'ine,yanufi dakin Hauwa'u,yace:baby kizo kisamemu afalo,zamuyi magana.
Tace to shikenan gani nan zuwa.
Sayyajuya yakoma falo inda suwaiba take zaune tana jiransu,wuri yasamu yazauna tareda saurarawa, domin sunajiran fitowar Amaryarsa Hauwa'u.
Lokaci kadan tafito,cikin hijabinta taredazaunawa kan daya Daga cikin kujerun falon,sannan takuma gaishesu.
Nasser ne yafara magana dacewa .
Alhamdulillah!sallu alannanabiyyul Kareem.yabude masu taron da Addu'a,kana yacigaba dacewa.
Kamaryadda Addinin musulunci yatadarma ko wadanne maaurata,yakuma Gina rayuwa akantsari,musamman rayuwar aure,yau Hauwa'u tacika kwana bakwai agidan Aurenta,kamar kuma yadda yake a hadith .
Idan ka auri budurwa akan bazawara,zaka kwana da ita tsawon kwana bakwai,sannan ayi rabon kwana.
Idan ka auri bazawara akan budurwa zaka kwana da ita tsawon kwana uku,sannan ayi rabon kwana.
Amatsayina na auri Hauwa'u budurwa,kwanakin ta suncika,ayaune za'araba kwana,to amma kuma ra'ayinnakune,yadda kukatsara iya adadin kwanakin da kukeso to sai atsaya ahakan.
Wannan shine dalilin taraku,dominjinnaku ra'ayin,kwana nawa-nawa kukeganin za'araba?
Suwaiba tace toh!yadda dai mafi yawan mutane suka dauka,muma haka zamubi,kwana biyu-biyi kokuma uku-uku.
Nasser yace hakane,sannan yamaida kallonsa ga Hauwa'u,yace my love bakice komaiba.
Tadago idanunta taredayimai wani irin fari,maidaukar hankali,tace:
Yo ai Aunty suwaiba tagama magana duk yadda tayanke dayane.
Tunda take maganar nan hankalinsa NA kanta,irin yadda take sarrafa harshenta cikin wata irin yanga fa kissa maidaukar hankali,shikansa yarasa abinda yasa komai nata birgeshi yakeyi,lokaci daya tatafi da ziciyarsa,yadade yana kallon fuskarta,sannan Daga baya yanumfasa,yace
Hakane babyna,Suwaiba kinji abinda ta fada,tace duk yadda kikayanke yayi,to amma abinda nakeso infahimta,kwana biyu biyun ko uku ukun?
Suwaiba tace biyu biyun sunyi,amma saidai inada magana,amatsayina na mace daya wadda tashekara Hudu awurin mujinta,koda yaushe muna tare,sainaga yakamata inkarama kan wata wadansu kwanaki Daga cikin kwanakina,domin itama tasake da mujinta sosai,kuma amatsayinka nawanda yayi sabon aure,gaskiya kwana bakwai sinyima kadan,ace akagama cin angoncinka,gara inbarku kukara sakewa dajuna sosai.
Don haka bayan kwanaki bakwai dinnan da kukayi,na yarjema ka kara WATA GUDA A DAKIN AMARYARKA,wadannan kwanaki TALATIN din kyautarsu nabaka,aci amarci lafiya.
Falon yayi shiru nawani lokaci.
Sannan Nasser yace to shikenan Suwaiba nagode,Allah yahadamin kanku yazaunar daku lafiya.
Baby kinji abinda Auntynki tafadako?to don Allah azauna lafiya,kibata girmanta da matsayinta,da take dashi na UWAR GIDA,sannan idan kin...............
**** **** **** **** **** **** *****
Suwaiba tatabashi tareda shafamai ruwan dayake hannunta,cikin dariya tace tunanin mekake?
Yace tunanin ki tunda kikashiga nakosa inga fitowarki,INA nan inata tunaninki mai masifar dadi,daya daukemin hankalina,kinyi kyau sosai,sai kamshi kike,yamike tsaye tareda fadin muje,inaso inyi bacci dawuri yau,inada aikin dazan fita tunda safe.
Yashiga gaba tana biyedashi abaya,suka wuce dakin.
Can cikin dare yafarka,yasa hannu yalaluba,baiji suwaiba ba,yayi saurin murje idanunsa,yatashi zaune.
Canya hangeta zaune tasauka Daga kan gadon,tanata sharbar kuka,tayi gaje-,gaje.ya saiko yazo inda take,yace
Suwaiba lafiya mekedamunki?
Tayi saurin share fuskarta tareda cewa bakomai.
Ya tsugunna gabanta sosai,yace yazakicemin bakomai?hakanan zakita kukane?ko wani abukeyimaki ciwo?
Tace don Allah kaje kayi barcinka kawai,niba abinda keyimin ciwo!
Yakamo hannunta yace to taso muje kizauna kan gadon tanbayarki zanyi.
Tace koka tambayeni babu amsar dazanbaka.
Yace naji taso dai muje kiji.
Dakyar ya lallasheta tataso suka zauna gefen gadon,sannan yakalleta tare da kara tsaida hankalinsa akanta,yace:
Kishiko?waimeyasa kike wahalar da kankine akan abinda bakida maganinsa?suwaiba inda ace idanna mayar maki da kwanakin ki TALATIN zamu samu zaman lafiya dake to inaga da inmayar maki dasudin kawai shiyafi alkairi.
Tace to aikaji inda matsalar take,zaka mayarmin da kwanakinane kawai domin asamu zaman lafiya,badon soyayya da dokiba,bakuma don son rankaba,a'a saidon kawai asamu zaman lafiya,kaga kenan yasha ban ban da irin kwanakin dakayi adakinta.
Nasser duk lokacin Dana tuna sanda nabaka kwanakin nan,ka amshesu cikin doki dajin dadi,harkanayimin godiya hankalina tashi yake,koba komai nasan yadda kakesonta nibaka sona haka,kaga kenan mayarmin da kwanakimma basuda amfani,
Nasser ya za'ayi indaina kuka?alhalin ninatabbatar sonda kakeyimata nibakayomin irinsa.
Yayi saurin cewa suwaiba waye yagayamaki haka?INA sonki harbansan dawane yare kikeso insanar dake cewa inasonkiba ki yadda.Suwaiba don Allah kibani izinin inmayar maki da adadin kwanakin ki,Nidai kidainayimin wannan kukan.
Tace banaso domin kuwa badon kanaso zakayisuba,saidon yazamemaka dole,ninasan cewa nayi asarar wadannan kwanakin har Abada!don haka babu yadda za'ayi karabani da kuka.
Yace to kinsan abinda za'ayi?Tashi kiyi Alwallah kiyi Sallah zaifiyemaki wannan yin kukan,da zaman da kikayi kina kuka dama Sallah kikayi kika samarma da kanki kwanciyar hankali,kiroki Allah yayemaki wannan matsalar datake tare dake,tashi muje inrakaki kiyo Alwallah kinji?
Tatashi suka shiga,gaba dayansu suka dauro Alwallah,sannan sukayi sallar Nafila raka'a Hudu,sukayi adduoin su.
Harzata kwanta yatambayeta,wace Addu'a kikayi?kuma mekika roka,?
Tace naroki Allah yakara sanyamaka soyayyata acikin zuciyarka,
Yayi dariya tare dafadin kai!kai!!,kaih!!!Suwaiba duk tarin soyayyar ki datake cikin zuciyata sokike akara wata?idan soyayyar ki tafi yadda take acikin zuciyata zata iya fasata,domin kuwa soyayyarki tariga tagama mamaye dukkan ilahirin zuciyata,INA sonki suwaiba,kuma irinnaki son dabanne Dana kowa,kece mace tafarko Dana fara gani kika dauki hankalina, tun alokacin kika dauki mafiyawa Daga cikin bangaren zuciyata kika mamaye,don haka kikwantar da hankalinki,duk wata mace tadaina baki tsoro,domin dai mujinki kafin yaganta keyafara gani,kafin yafara sonta keyafara so.
Don haka ba soyayyarkice zaki roki Allah ya sanyaminiba,wannan yariga yasanyata,takuma zauna cikin ikonsa.
Abu dayane yake wahalar dake KISHI to shine yakata kuroki Allah ya sassauta maki shi,yarage maki zafin kishinnan,yasanya maki dangana,kinji Suwaiba ta,yafada cikin sigar lallashi.
Tadaga kanta alamar e.
Yace tashi mukwanta,kidaina damuwa kinji.
Aiko duk yadda yaso yafita wurin aiki dawuri,saida yamakara,don haka safe cikin sauri yayi break,yana shiyawa kosallama baije yayima Hauwau ba yafita.
Bayan kwana biyu,misalin karfe biyar nayamma,yadawo gida,kai tsaye dakin Hauwau yawuce,bayan yazauna,takawomai abincinsa tare dafadin.
Sannu da dawowa,yau dai nagakadade.
Yace hakane nadade,wani aikine yatsayar dani,mekika dafamin?
Tace abinda nasan kafiso,inaso yau kaci abinci sosai,sannan tafara zubamai,yana kallonta sosai,bayan tagama yace sannu da aiki.
Tayi dariya,tace nagode mujina,inajin dadin yadda kake yabamin akan komai.
Shidai yakafeta da idanu,sannan yace zauna inason muyi magana.
Tazauna tare dafadin,ammadakabari kagama cin abincin.
Yace a'a bakomai,maganar tanada muhimmanci sosai.
Hauwa'u inasonki,INA kuma kaunar dorewar zaman lafiya tsakanina dake,da kuma abokiyar zaman ki,to don Allah kiduba darajar soyayyar dake tsakanina dake,kiyimin wata alfarma guda daya,Hauwau bakisan halindanake cikiba,INA boyemakine saboda banason tashin hankalinki.
Tabbas!!nalura kemacece wadda take farin ciki alokacin data samu mujinta cikin farin ciki,kuma kike bacinrai alokacin dakikaga wata damuwa a idon mujinki,dayawan maza irin matar dasukeso susamu kenan,nikuma Allah ya azurtani da ita.
Hauwau kokinsan cewa INA cikin tashin hankali daya hanani walwala?sai dai inaga da taimakonki za'asamu saukinsa,koma maganceshi baki daya,Hauwa'u , Suwaiba tatadamani hankali ,idannashiga adakinta,babu abinda takeyimin sai aikin kuka,nikuma banason inga tana kuka,tatada hankalinta duk iya yadda baki zato,nima kuma tatadamin nawa hankalin,kuma duk hakan bayarasa nasaba da KWANAKINNAN TALATIN FATABAMU NA AMARCI,shine Daga baya take danasani,takuma kasa hakura tadangana.
Dai dai nan yasauko Daga kan kujerar,yadurkusa gabanta,yace:
Hauwa'u kitaimaka kabani KWANAKINKI TALATIN inmayar mata,kona samu zaman lafiya ,don Allah Hauwau.
Humff!! Tayi ajiyar numfashi ,tace:babu abinda zaka nema awurina karasa,babu wani taimako dazaka nema awurina banyimaka shiba,zan iya baka duk wani Abu danamallaka arayuwata,indai baifi karginaba,AMMA BANDA KWANAN AURENA!!
Bari inkara jaddada maka Nasser!wadannan kwanaki TALATIN tayi asararsu har Abada!bazan iyabatasuba!kuka kuma taitayi!duk ranar data gaji kokuma ruwan jikinta yakare saita bari!kada kakarayin tunanin cewar donkamayarmata da wadannan kwanakin za'asamu zaman lafiya,kadauka tamkar kakara bankado wani tashin hankaline acikin gidanka!kuma kodawasa kada kakara kawomani wannan zancen!dai dai dakwanana daya bazan iyabataba!
Kukaratacan!!kai daita,inkunga dama kukwana kuna kuka tare,ni inanan inabaccina.
Yace amma kuma................
Tace:kaga dakata Nasser!innasamma wannan maganarce tasakatsaidani,wallahi daban saurarekaba!kuma wannan maganar nakasheta Daga yau!duk ranar daka kara kawomin ita zanyi fito na fito da suwaiba,domin ita bata isa tahargitsamin rayuwar Aurenaba!shikenan ta tadamaka hankalin da zaka kasa sakewa daniko?to kabarni da ita zamyimaka maganinta!!
Yayi saurin cewa a'a banason irinwannan Hauwa'u!tunda muke rigimarmu da ita kintabajin tasakoki aciki?tsakanina daitane kawai,ban tabajin tace ga abinda kikayimataba,don haka banaso rigimar takoma tsakanin keda ita,maganar Mani abarta.
Tace Ah toh!aigara inyi maganinsa abin tunda wuri,don karka dauka cewama kowata rana zanyadda.
Yasa hannu yature abincin data kawomai,cikin fushi yatashi yabar dakin.
Tace haka kawai,mata tatadamaka hankali,don inkadawo dakina kakasa sakewa!donneman tahadani dakai!nasan maganinta!!kila nima sainafito nanuna mata inada 'yanci!kuma gidan mujinane!!!
Hakataita fadanta itakadai,tana tattara kayan abincin data ajiye
Wannanma aimugun abune!gashi ko abincimma tasa yakasaci!to dani take maga.
Baidawo gidan ba sai misalin karfe goma NA dare,tana zaune tanajiranshi,sannan saigashi yashigo,babu dai wata fara'a ataredashi,wuri yasamu yazauna taredacemata.
Hadomin ruwan zafi zansha.
Tatashi tahadamai,takawomai,sannan tazauna daf!dashi,tace yau shine abincinkako?naga kodarana bakaci abincibafa,yanzun kuma kadawo banga alamar zakaciba.
Yace shikadai zaniyasha yanzun.
Tatabe bakinta tare dafadin to aishikenan,tasa hannu zata hadamai,yatareta yace bashshi kawai zan hada.
Tacire hannunta tarabu dashi,don taga iyakar fushin dayake daita,bata karayimasa magana ba haryagama sha,sannan bataredayace komaiba yatashi yashigewarsa dakin.
Tabishi dakallo,yau naga ikon Allah,wannan fushin kuma namenene?tadai tashi takawar dakayan tea din daya sha,sannan tashiga dakin.
Kwance tasameshi yanashirin yin bacci,tadafa wuyansa tareda cewa,love bakada lafiyane?
Yayi banza daita,yajuya mata baya,tazauna gefen gadon,tace mekake nufi?
Yace Hauwau kirabu dani,tunda har inada wata alfarma dazannema awurinki kikasayimin,to gaba dayanku zan tattaraku in kyaleku,randa kuka daidaita kanku aci gaba da zaman auren.
Wai Nasser kana nufin indauki kwanakina inbaka?hardon nace bazan bayarba kake fushi,to shikenan nayadda,amma saidai inka amince intafi gidanmu inyi wata guda,sanda kagama kwanakin adakinta saika dawo dani.
Yatashi zaune ,tareda cewa,ita gidan su tatafi lokacin data baki nata kwanakin?wata hanyacedai kawai zaki bullomin daita donkibani wahala,kuma kinsan abinda bazai yuwuba kenan,domin. Kuwa hakan wata hanyace kika biyo donki tonamin Asiri,mezaisa bazamuyi hakan dagani saikuba?babu Wanda yasani,amma yanzun inkintafi gidanku,aidole asan dalilin,nima kuma bazan yadda kitafi gidaba itama sanda tabaki kwanakin ta aiba Wanda yasani,don haka nibanyadda kitafi gidankuba.
Tace to kasani nima bazan iya bada kwanakinaba,Kikasauko Daga fushin dakakeyi,kokada kasauko duk dayane!taja bargo takwanta tareda juyamai baya.
Yatashi danufin zaibarmata dakin,itama yatashi tsaye,tace meyayi zafi shiba wutaba?koma kayi kwanciyarka nisai inbarmaka dakin,gadai falo basai inkomaba,yi kwanciyarka nikagama fitata.
Tabarmai dakin takoma falo,bisa kujera tana tunanin wannan kuma wane irin abune?WATA kan shiyayadda inbata kwanakina yakaimata,saboda bayason fushinta,Tab dijan!!!aiko zasu kare afushi,to wannan wane irin sone yakeyima suwaibane?tun farkoma inyasan haka aida baikara aurenba,gaba dayamani nalura sondayakeyima suwaiba yayi yawa.
Harya kwanta yakasa runtsawa,shikansa yana ganin abinda yayima Hauwa'u bai kyautaba,komadai metafadamasa,aidon tana sonshine,yakuma tuna irin kula dashidin datakeyi,sayyaga baikamata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment