Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalilin wannan yagejetaba yau.
Mikewa yayi jiki asanyaye yanufo falon,dai dai inda take yatsaya,yace Hauwau taso kikoma daki.
Tace a'a nanma ya'isa,lafiya lau ba abinda zaisameni.
Yace tokiyi hakuri kitaso.
Tace to'aini ba'abinda kayimin kakebani hakuri,nibakayimin laifin komaiba,nayi maka uzuri akan duk abinda kafadamin,nasan bayin kanka bane,masifar SON suwaibane yarinjayeka,harkake fadamin duk abinda yafito Daga bakinka,wannan kuma bamatsala,nima zanroki Allah yasanyamaka Soyayyata acikin zuciyarka kamar yadda yasanya maka ta Suwaiba,don haka kaje kawai bakomai.
Yace me kikeso kice?kina nufin nan zaki kwana?don Allah yihakuri kitaso muje.
Tace muje inah?kaida kace zaka iya tattaramu kakyalemu sai sanda mukashirya ayi auren,tome zaisa kazo wurina yanzun?kadan rabu damu zuwa sati biyu kagani koma shiga hankalinmu,
Yayi tsamm!!yana nazarin maganar ta,sannan Daga baya yace gaskiya bazan iyaba,don Allah kiyi hakuri Hauwau.
Tace au! Ashedama barazanace?muje badon halinkaba.
Washe gari dasafe yana tsaye cikin falo yayi wanka yanakara gyara jikinsa,suwaiba tashigo ,tayishirinta tsaf!NA tafiya anguwa,tagaisheshi ya amsamata lokacin dayake gyara maballin rigarsa.
Tace nashirya dama inaso inje gidammune,inga iyayena konaji dadi,kuma hankalina yakwanta.
Sayyayi tsaye yana kara kallonta,saidaga baya yace wannan wace irin tambayece?wai suwaiba meyasa kikeyimin hakane?yanzun don zaki unguwa saida kikagama shiryawa tsaf!sannan zaki tambayeni?salon ince ban aminceba kuma rai yabaci!to banyadda da tafiyarba!sai kije kicire kayan!
Dai dai nan Hauwau tafito,dauke da hula ahannunta,tanufo inda yake tasanyamai,tace:
Kai my love kayi kyau sosai,kamar kada kafita.
Wani kululun bakin ciki yatsayama suwaiba awuya,battasan sanda tace:
Inje incire kayanfa kace?
Yace e banyadda tafiyar takiba kizauna gida!!
Hauwau tawaigo tayi mata wani irin kallo kamar dabatasan da ita adakinba,sannan takara kallon Nasser tace my love muje ka kara kallonkanka a mudubi,saikaga abinda nake fadamaka gaskiyane,cikin wasa tare kama hannunsa,tace kilama Daga nan inhanaka fita.
Ran suwaiba yakara baci,cikin kuluwa tace gaji muguwa!Azzaluma!inda baya fitama kinganshi ki makalemai!to immake mayyace saikin sakeshi!!mayaudariya kawai!!
Hauwau tace kitambayeshi kiji nikadaice namakale Mashi?koko dai muka makalema juna.
Suwaiba tace kekika makalemaiba,domme zakice sayya shigadaki yaduba madubi?dalla sakashshi!!!
Tasa hannu tabige hannun Hauwau dayake jikin Nasser din,takumace baya shiga dakin,ahakan zai fita komin kyandayayi,inbai fita dakyanbama kekin Ganshi?muguwa kawai!!!
Hauwau zatayi magana,yasa hannu yarufe mata baki,karki kara magana,dama Neman fitina yakawo ta wurina,inkika biyemata kuma abin zai dawo kanki.
Yawaigo yakalli suwaiba,wadda idanunta sungama cikowa da kwalla,yace:
Wuce kitafi dakinki!don banga dalilin zuwanki nanba!
Hawayen dasuke cikin idanunta suka ziraro,cikin kuka kuma tace:saina tafi gidannamu!don bazan tsaya bakin cikinku yakadheniba!!tafita dasauri.
Shikuma yabi Hauwa'u dakinta,yaduba madubi,shima yayabama kansa sosai,yace gaskiyarki Hauwau,nayi kyau sosai,kamar bawanda matansa sukeso su hargitsamai tunani ba,
Kamar bawanda kullun yake fama da matansa akan suzauna lafiya ba.
Kamar bawanda idanyanemi uzuri wurin matansa suke kasayimasaba,kamar bawanda idan yana............
Tasa hannunta tarufemai baki tareda cewa,ya isa hakanan,naji korafinnaka zayyi yawa.
Yace kuma sauri nake.
Tace bye bye adawo lafiya.
Yana fitowa saida yaleka dakin Suwaiba,don yaga dagaske wai tafiyar zatayi koko?amma sayyaganta kwance tayi Ruf!daciki tana kuka.
Yace Suwaiba taso muje inkaiki.
Tatashi tana share hawayen fuskarta,tafito sukawuce.
Suna cikin tafiya yace ikon Allah!Suwaiba saikace wata karamar yarinya,yanzun danna hanaki tafiya unguwa shine kike kuka?
Takallai da gefen idonta tace ni bashi yasanya ni kukaba.
Yace to menene?
Tace dakai da Hauwau kunayimin abinda kukaga dama,ni wani abimma sai inga dankungannine kukeyi.
Yace Allah sarki shidai kishi halittane,Allah yaragemaki wannan zafin kishin,gaskiya kinashan wahala,ai duk macen da kishi yake wahalar da ita tanashan wuya.ninaga wannan Abu tunda yariga yafaru,bakida maganinsa,to mezaisa kikasayin hakuri,ki rungumi kowace irin kaddarace tazo maki.
Tace nice maka nayi banyi imani da kaddararba?dakai da Hauwau be kullun sokuke saikun sanyani bacin rai,aikasan inada kishi,amma kukeyin wani abin agabana,kawai don raina yabaci.
Yace don muna nuna soyayyar junanmu afili shikenan yazama tashin hankali?
Kina nufin yanzun donmunajin tsoronki saimu kasa nunama junanmu irin sondamukeyima juna?saboda munagudun ranki yabaci?
Tace basaika gayamaniba Nasser,Nina Sani dukkan ma aurata akwai soyayyar juna atsakaninsu,amma idanyazamana akwai idon mutane akansu saisurika kiyayewa,wani abin sai abarshi kodan kunya.
Yace to suwaye mutanan?
Tayimai wani irin kallo tace:niba mutum bace?Tasakani da Allah Nasser kana wulakantani!!yanzun kai da Hauwau kuzauna kunayin irin wannan wulakancin agabana,ta daukeni me?
Yace Abarmaganar,nasan yanzun ranki yabaci.
Tace to aini dama kariga kagama batamani rai!ko daya bason farin cikina kakeba!kai indai wannan Sweety din taka tasamu farin ciki,toko rankowama zai baci babu abinda yadameka!
Kuma malamai sunata fadin ayi Adalci-ayi Adalci,ammani bawani Adalcin dakakeyimani!!tunda kullun sokakeyi kaganni cikin fushi!!soyayyace nibazan hanakuba!amma saika rika bari saikunshiga daki can!inda idona bai ganiba!!bansan kuma anyiba!amma wani abimma saikun ganni kukeyi!!saboda kai kullun sokakeyi kaganni INA kuka,
Nibanga Amfaninma hada mata biyunkaba!!tunda haryanzun kakasa shawo kammu!!kuma rashin adalcine kawai!!!
Ko angayamaka don kana iya ciyar da mata biyu!kabasu wurin kwana kawai shine adalcin?amma kuma gashi baka iya kiyaye bacin ran matanka!!Idan kasan idan kayi Abu kaza,zai iya bata ran matarka,saika barshi,amma kiii kiii kieee!!!!katashi kakaro aure,alhalin kuma ba iya sai saita su zakayiba!!!
Yace to sauko ankawo,don Allah Suwaiba kada kikai dare,in anyi sallar magariba kidawo gida.
Tace to aini naga kamarma baka damu damaganar danakeyiba.
Yace aidama basauraronki nakeyiba,Adalcidai in inayi Allah yasani,badonke nakeyiba,yimaza kifita.
Tace to bani kudin dazan hau mashin.
Yace bazan bayarba,aigidanku kikazo.
Tana fita yaja motar dakarfi yatafi.
Misalin karfe shidda nayamma,yadawo yana zaune afalo,yasadda kansa kasa,ranshi abace,donko Hauwau ma batasan yashigo gidanba,sai juya kansa yake kamar yanayimai ciwo,maganganun da Suwaiba tafadamai dazun sune kawai sukeyimai yawo acikin kwakwalwarsa,saboda maganar tatadamai hankali sosai.
* kuma malamai sunata fadin ayi adalci-ayi adalci ammani bawani adalcin dakakeyimani!!!!
* tunda kullun sokakeyi kaganni cikin hushi!!!
* tunda kullun sokakayi kaga INA kuka!!!!
* ni banga amfaninma hada mata biyunkaba!!!
* tunda haryanzun kakasa shawo kammu!!!!
* kuma rashin Adalcine kawai!!!!!!
* don kana iya ciyar damata biyu kabasu wurin kwana kawai shine Adalcin!!!!
* amma kiiii kiiii keee!!!katashi kakaro aure!!!!!!!!!!
Wasu zafafan hawayene suka gangaro fuskarsa,cikin tashin hankali yahau bugun kansa da hannayensa yana fadin.
Suwaiba me nayi maki?wane rashin adalcine nakeyimaki?nidai iyakar sanina INA bakin kokarina,wurin kwatanta Adalci agareku,suwaiba menayimakine?????
Hauwauce tayi saurin girgizashi,tare dafadin lafiyarka lau kuwa?yakaketa magana kaikadai?
Humf!yayi ajiyar numfashi tareda rarraba idanu kamar yayi karya,domin kuwa baisan abinda yake fada yafito filiba,
Tazauna tare dacewa mekuma suwaibar tayi maka?
Yace a'a bakomai,kawai dai abinda tayimin dazunne yake damuna,amma komaima yawuce,
Tace to shikenan. Amma don Allah kadaina tada hankalinka,inka biyema sha'anin mace saita zautaka,saika dauka azuciyarka cewa duk abinda mace tayi kuruciyane da rashin hankali,idan kace zaka biyema mace,to saika aikata badaidaiba,
Ita mace kometayi aganinta daidaine,indai akan abinda yashafi mujintane,koda kuwa bata Mashi rai tayi,ita aganinta hakan shine dai dai dashi,kuma mace bata cikayinnadamaba saitaga wuri yakuremata.
Don Allah mujina kamaida komai ba komaiba,bana son tashin hankalinka.
Ya kirkiro wata dariya hakanan yayi,domin yafaranta mata,amma saiwasu hawaye masu masifar zafi suka ziraro a idanunsa.
Tayi saurin kara matsowa jikinsa,tasa tafin hannunta tana share mai.
Dai dainan suwaiba tabankado kofar falon tashigo,saikuma tayi tsaye turus!tana kallonsu,saikace takama marasa gaskiya.
Kodamuwa da ita Hauwau batayiba,taci gaba da abinda takeyi,taredakara lallashinsa.
Suwaiba tashige dakinta taredajan wani dogon tsaki.
Nasser da yagigirza kai,taredacewa ni bamuyima haka da itaba,cewa nayi sai anyi magariba,zata dawo.
Dama INA nufin innataso masallaci inwuce indaukota,kinga tama hutar dani,amma kuma wannan tsakin datayi namenene?
Hauwau tayi saurin cewa haba don Allah meyasa kake kula irin wannan?kadama kadamu da ita,kasan tunsafe take Neman rigima,yanzun Wanda zaibiyemata takeso,to kaji gayacan ma anfara kiran Sallah.
Suka tashi suka dauro Alwallar sallar magariba,yawuce masallaci.
Saida yatsaya yayi sallar isha'i a can sannan yadawo gida.
Aranar kuwa dama suwaiba kekarbar aiki,don haka yana dawowa dakinta yawuce.
Kamar yadda yazatadin hakayasameta,rannan mata abace,donshidai ko sallamarshi baiji ta amsaba,imma ta amsa to aciki tayita.
Yaji dai shurun tayi yawa,yasa hannu Aljihunsa yaciro naira dubu daya yamika mata.
Tayi banza dashi,kamar bata ganshiba.
Yace ki amsa mana.
Tace tamecece?
Yace kudin motar dakikahawo daga gidanku zuwa nan,dama nayi niyyar innafito masallaci zanje indaukoki,saikuma gaki kin dawo.
Tace Nasser bahaka kake nufiba,nice zaka dauka Mara wayau!aikai kanka kasan bakayi dai daiba!!inace yau kwananane?amma dana shigo gidan menatarar?shine zakayimin dubara da kudi?to aigidannamu ba matsiyata bane!!anbani kudin motar a can.
Ran shi yayimasifar baci,amma saiyadanne bacin ran,yace to amma aini yakamata in baki,kuma baki taba zuwa gidanku nabarki kikayi kudin mota dakankiba.ballan tana kice inaso inwanke wani laifine awurinki.
Tace to banaso!!dai dai alokacin datake daukar filo da bargo zatabar dakin.
Yariko hannunta tare dafadin,Suwaiba kiji tsoron Allah,Kisani cewa abinda kikeyimin,yafara fita hankali,wallahi abinnaki Suwaiba yafara wuce kishi yafara zama wulakanci da rainin hankali!!to kibi duniya asannu,domin banga amfanin yin fushi akan abinda bakida yadda zakiyi dashiba.
Yasa hannu yagizge filon dake hannunta cikin fushi,kuma yace:idan kika fita falo kika kwana bada izininaba!ya ajiyemata kudin yayi shigewarsa wanka,nanya barta tsaye kuka ya kwace mata dakarfi.
Yau kimanin watanni uku kenan dayin auren Hauwau,harmadawasu kwanaki.
Mahaifiyar Naseerce takirawoshi awaya Daga Funtuwa,take shaidamai tanason ganin sa,dakuma damaga bikin Abokin sa Ibarahim yamatso.
Nan yake shaidama mahaifiyar tasa yana nan zuwa cikin satinnan,in Allah yaso.
Bayangama wayarne yake shaidama suwaiba cewa,da ita zaifi,domin kuwa Hauwau tace itama zataje Lagos wurin kawunta,kuma duk tafiyar zatazo lokaci dayane,don haka keki shirya sai intafi dake.
Tadai amsamai da to.
Saidayarage saura kwana biyu tafiyar,take cemai.
Kasan wani Abu Nasser?
Yace menene?
Tace bazani Funtuwa ba.
Yace saboda me?
Tace kawai dai nidai naji natsani tafiyar,kotunawa nayi cewa zamu funtuwa sai inji raina yabaci,har takaigama yanzun gabana faduwa yake,kai dai Allah yakiyaye hanya adawo lafiya,nidai bazaniba.
Yace amma dai banji dadi ba dakikace kinfasa,ko bakijin dadin zama da 'yan uwanane?
Tace a'a lafiya lau,ni da innajema sukesona,aita nunani,ana nan nandani,kawai dai nibansan daliliba.
Kawai dai naji tafiyar tasiremin,inda ace Hauwau ba inda zata saiku tafi tare.
Yace kai aigaskiya bazan hanata zuwa legos dinnan ba,saboda kawuntane yadawo Daga America toshine takeson taje,kuma INA tunanin komawa zayyi idan batajeba kinga kafin takara ganin sa za'adade.
Suwaiba tace tokumafa hakane gaskiya,nidai kayi hakuri bazani.
Yace a'a bakomai sai intafi nikadai.
FUNTUWA
Agida FUNTUWA yayi sallar Azahar,sannan yadawo dakin mahaifiyar sa,sunata fira tareda kannansa maza da mata.
Kanwarsa Aisha tace yaya Nasir nasha zakazomana da Amaryarka bantaba ganintaba.
Yace ai itama unguwa zata,shiyasa bamu tafo tareba.
Tace to INA Aunty suwaiba?ita meyasa bakazo daitaba?
Yace itama nabarta tayi tsaron gida.
Dai dai nan H-Asamau tashigo tareda mai aikinta tanadauke da tiren daakajefo kayan Abinci asamansa.
Tace kana nan kuna fira kenan?
Yace e inna inajirane inbaci Abinci zan fita,inzagaya inga Abokaina,yasa hannu yabude kular Abincin,kamshi yabugai,yace laaa!inna Dambu?dama saboda kinsan inasonshi kikayiko?
Tayi dariya tare dafadin Nasiru kenan,aidama nasan kanasonshi,shiyasa mace bari atarbeka dashi,duk yakabaro gidan?
Yace lafiya lau inna suna gaisheku.
Saida yaci yakoshi su kadan taba fira sannan yafita,gidan su Ibrahim dinyawuce kai tsaye,nan yahadu da Abokansa,firace takaure tsakaninsu,ballantana dama anrabu da haduwa.
Hassan yace kazo bikin tuzuru kenan?
Sukasa dariya baki daya,Nasser yace Babban tuzuruma kuwa,kasan saida yagama jama 'yammata aji sannan,gamunan wasummu harda mata bibiyu,shisai yanzun zayyi tafarko.
Ibrahim yace kusha kuruminku,badi iyanzumma zakudawo auren ta biyun,ainabarkune dukjugama,ni innatashi akai-akai zanyi su.
Nasser yayi dariya cikin girgiza kai yace Allah yatayaka riko,aikasan rike mata biyunnan sai jajurtaccen namiji,mai kokari!kaga shi Hassan tunda yayi tafarko shekara biyar kenan yakasa karawa,kazo Abuja inyi maka budurawa.
Hassan yace kasan wani Abu?mata dayannan dai daidahudu nake ganin ta,don hakan ita isheni.
Nasser yace inah!!wasa kake bazaka zama jaruminba,kenan?
Ibrahim yace to kaga kunfara karaya ko?kuda kukafara auren,nikusa ido kuyi kallo,duk bayan shekara biyu sainayi aure,harsai nahada mata Hudu cuf!
Nasser yakara tuntsurewa da dariya,tareda bubbuga kafadar Ibrahim,yace kasankau nanne zaka gane anasonka,ingayamaka kota inatarairayarka za'arikayi,mata hudu!lallai kam!aiko zakaga soyayya!
Hakasukasha firarsu cikin wasa tareda zolayar juna,harsaida akayi sallar la'asar sannan sukawuce masallaci baki dayansu.
Bayan suntaso Nasser yace yanaso yaje gida,anjima zai dawo,sai afara shirye-shiryen yadda za'ayi hidimar bikin,don atsara komai yadda yakamata,sukayi sallama yahawo motarsa zaitafo gida.
Akan hanyarsa ya hangi HABIBA sanyeda kayan makarantar islamiyya,saida yazo dai dai indatake sannan yatsaya,tareda sauke gilas din motarsa,yaleko da kansa yace:
Malama Habiba INA zuwa?
Cikin mamakin ganinsa yasa hannayenta biyu dake cikin hijabinta tarufe bakin ta tare dafadin.
Yaya Nasser yaushe kazo?
Yace aibaki bani amsaba.
Tace makaranta zani.
Yace toshigo inkaiki,kinga Hudu tawuce sosai,yabude motar tashiga,tareda fadin yau kazo?
Yace dazunnazo,yaya karatunki?
Tace gashi nan muna tayi,Alhamdu lillah,nayi mamakin ganin ka!
Yace aiko yaunazo,kina zuwa makarantar boko ko?
Tace ainagama,
Tace kingamafa kikace?
Tace e secondary ba.
Yasa dariya tareda fadin tokuma shikenan kin gama karatun?
Tace nidai indai ra'ayina za'abi inaso inci gaba.
Yace tome zaihana ba'abi ra'ayinnakiba?
Saitayi saurin canza firar dacewa,yaya Nasser banfa ganekaba da farko,saida nalura.

Yace saboda me?
Tace kaga yadda kazama?daba haka kakeba,
Yace:AAh!toda yaya nake?
Takara kallonsa tace yaya Nasser kayi girma kakara kyau sosai.
Yasa dariya yace ashedai haryanzun kina nan yaddanasanki da surutuko?nasha tunda kinyi girma yanzun kinrage surutu.
Saikuma taji yabata kunya,tarufe idanunta,tace to saukeni nan ankawo makarantar.
Yasauketa tare dafadin ayi karatu lafiya,bye bye,
Itama tadagamai hannu sannan tawuce tashiga aji.

Misalin karfe Takwas darabi nadare,Nasser nazaune shida mahaifiyar sa,H-Asama'u,suna fira ,takecemai.
Nigaba daya Al-amarinka mamaki yakebani,domin ni yanzun bansamma manufarkaba,koko matannakane kasamu 'yan bariki suka sauyamaka tunani oho,to yanzun dakake wannan kauce-kaucen mekake nufi?
Nasser yace Inna bawai umarninkine banaso nabiba,a'a yadda za'ayi inrike mata uku shine nake tunani.
Tayi saurin cewa hanyar dakabi karike biyun ita zakabi karike ukkun!abinda ba 'ya'ya kuka taraba,
Shintomawai dakake wannan maganar ya kakeso ince da iyayen yarinyarnan?kasandai tun mahaifanku nadarai wannan maganar take,kuma Al-kawarine!koko sokakeyi arusashi?
Yace bahaka bane ba inna,bazaki fahimceniba,domin niyanzun bamma shirya kara aureba,kuma yarinyarnan kinga karatuma take.
Tace to yaya za'ayi infahimceka Nasiru?aini fahimtata dakai dayace!inji kawai ka amsamin ka amince da wannan auren,kuma dakake maganar karatu waya gayamaka bata gama ba?tagama secondary kuma kwanan nan sukayi saukar Al-kur'ani,tome kuma ake bukata?aiyin auren shine kawai darajar 'yamace.
Yace Inna secondary fa kikace?ni inna immazasu yadda sai inbiya mata taci gaba da karatun,Wallahi Inna dayafiye mata wannan Auren.
H-Asamau tace tunda kai kannan naka gaba sukaciba?kaini duk wannan hanyar dazaka biyomin bafa yadda zanyiba! AH!toh!!karatune kakeso kafakemin dashi,kuma tana iyayinsa adakinka,tunda kaima 'yan bokonnan kake aure,kaga baikamata ita ace batayiba,duk dadai aizaman Aure tajeyi!
Nasiru banyi zaton zakayi aure har biyu babu HABIBA aciki ba,amma bakomai haka Allah yahukunta,Allah kuma yatayaka riko.
Yace to inna kijira inmunyi magana da Habibar idan tace karatun takesonyi,sai inbiya mata kudin karatun taci gaba,inyaso Daga baya sai ayi zancen auren,sabidani gaskiya banshirya rike mata ukuba.
Tace niyanzun bashirinka bakesoba!yaddarka kawai nake nema,domin niyanzun inkayaddama bazaka koma Abuja ba saida Habiba.
Arikice yayi saurin dago ido yakalleta muyarsa narawa yace:inna wane irin Aure kuma yanzun?duka yanzunfa banrufe watanni Hudu da auren Hauwa'uba,don Allah inna kidaina wannan maganar,domin ni nanatabbatar yarinyarnan tafiso tayi karatun.
Dataga tsabar tashin hankalin dake cikin idanunsa,tagane e lallai dagaske yake,bazai karbi umarnin taba ,sai itama tadaure Fuskarta cikin fada tace:
Nasiru bafa shawara nake bakaba!!wannan abun dolene kayi shi!!ai Allah bai hanaka abinda zaka rike koda mata huduneba kuwa!!saboda haka ni wannan yarinyar tayimin!kuma bakama barin garinnan saida ita!!!domin idan katafi bamusan ranar dazaka kara dawowaba,don haka yanzun kaje kayi shawara,ranar da za'adaura auren Abokin ka Ibrahim sai ahada danaka,
Yatashi tsaye zufa nawani irin ketomai,dakin sa kawai yawuce yakwanta kan gado,cikin wani irin tashin hankali.
INKARA AURE????
Yaketa tambayar kansa,to yaya zanyi dasu kenan?gaskiya da ancuci Habiba in dauki wannan yarinyar insakata cikin wadannan matan,gaskiya akwai matsala,nan take yafara hanho irin tashin hankalin da suwaiba zatayimai,intaji wannan auren,me zabcemasu idannakoma?wace hujjace kuma zankafa masu dalilin kara auren?
Haka yakwana juye-juye yana hango irin hargitsewar da gidabsa zayyi,idan yakai Habiba amatsayin matarsa ta uku,asu biyunma ana'irin wannan kishin?inaga kuma yakai wata.
Bai samu mafitaba sai misalin karfe uku nadare,sannan dubara tafadomai,nacewa,yaje ya lallashi Habibar,yace zaibiyamata kudin makaranta tacigaba,inyaso Daga baya tasamu wani mujin tayi aure.
Sannan yasamu hankalinsa yakwanta,yayi barci.
WACECE

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment