Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiboyemin Aunty suhailat?waye zaki iyafadama damuwarki Wanda yake kusa dake bayanni?karki manta Aunty suhailat,iyayenmu sunrasu,sunbarmu,don hakabakida Wanda yake kusa dake Wanda yafini,bawanda ya cancanci kisanar dashi wata damuwa taki sama dani,inkuwa harni zaki iya boye Mani matsalar ki,to lallai zakita zama da ita acikin zuciyarki,domin kuwa bakida sama dani.
Cikin magiya takara cewa,don Allah Aunty suhailat,kifadamani meke damunki?
Suhailat takara kallon kubura,sannan tace:ba abinda zaki iya yimin akan matsala ta,don haka kawai kirabu dani.
Yakice haka?ko ban iyayimaki komai,aizan iyayimaki Addu'a ballantanama shawara bazata gagaraba.
To shikenan kubura tunda kinmatsa,zan fada maki,amma ki adanamin amatsayin sirrinane,karki fadama kowa.
Kubura takara gyara zaman ta,tare da maida hankalinta akan suhailat,Tace:inajinki menene?
Atsawon rayuwata,tun kafin intafi Engilar,Allah ya jarrabeni da son ya Ahmad,nayi duk iya kokarin dazanyi,inga nadaina sonshi,abin yagagara,sai dai kuma shirmen banza nakeyi,domin kuwa baisamma inayiba.
Kubura tace kawai saboda wannan zaki tadama kanki hankali,to kici gaba da SON shi!Nina tabbatar maki zaya soki,karki mantafa,Aunty suhailat yaya Ahmad fa Dan uwankine,wallahi bazai taba kinkiba,ai wannan abin farin cikine awurimmu!Allah ya tabbatar da Alkairi.
Suhailat ta girgiza kanta,sannan tace,aibakisan abinda kefaruwaba,a yanzun haka ya Ahmad yanada wadda zai aura,kuma harsun dai daita .
Kubura tace to shine me?namiji daya aimujin mace hudune,kadama wannan yadameki,indai kin tabbatar kina sonshi.
Suhailat tace kubura Ya Ahmad bazaisoni da aureba,yana dai sona amatsayina na 'yar uwarshi,amma ayanayin maganganunsa,babu alamar zai taba sona da aure,bashshidai ayi wasa ayi dariya kawai,amma yanada wahala yasoni da aure.
Kubura tace haka kike gani Aunty suhailat?
Aunty suhailat tace hakanema Tabbas!
Kubura tace to akwai yadda za'ayi,yau sauran kwana biyu mawuce Kaduna,don haka yanzun basai gobeba,kitashi kishirya,ni zannema maki mafita,wurin wani malami zankaiki,don bazai yuwu kibason Abu yagoce makiba,muje yatayiki da rokon Allah,kamar yadda kike son yaya Ahmad shima yasoki haka,koma fiye da haka,domin na tabbatar damunje kaduna ,Abba zancen Auren nan zaitada,kuma kinga aibazai yuwu ni inyi aure,yaya Ahmad yayi aure,kemubarkiba,don haka tundawuri munemi maganin abin.
Duk dadai abin baikwanta mataba,haka nan ta shirya suka tafi.
Suna cikin tafiya take cema kubura,wallahi nadade inason ya Ahmad,amma bazan iya sanardashiba,gashi har yananeman subucemani,INA yimasa wani irin so dani kaina narasa gane kaina,idan ban auri ya Ahmad ba bammasan yazanyiba.
Kubura tace kima daina wannan maganar,insha Allahu zaki Aure shi,ba abinda zai hana saidai inbamuje wurin malam musan nanba,domin ni inada tabbaci akan haka,nasha kawo kawayena wurinsa,akan matsaloli daban-daban,kuma anasamun nasara sosai,don gaskiya banga yayi aikin daba'asamu nasara ba,don haka kema kikwantar da hankalinki,kisa arankima kawai kin samu,awannan karamin aikine a wurinsa,in Allah ya yadda sai kin auri yaya Ahmad.
Sai Aunty suhailat takarajin karfin gwiwa akan wannan tafiyar tasu.
Cikin sa'a kuwa sunsameshi.
Malam musa Dattijone fari,Wanda furfura tagauraye gashin kansa Dana fuskarsa,mutumne mefara'a sosai,don haka cikin sakin fuskarsa da karramawa ya karbesu,domin dai dama kubura ba bakuwa bace a wurinsa,tasha kawo mai mutane yana taimaka masu da Addu'a.
Bayan sungaisa,kubura tayimai bayani kamar haka.
Malam yau kuma. 'Yar uwatace nakawo,akan wata matsala data shamata kai,wani Dan uwammune sunansa Ahmad,to Allah yajarrabeta da sonshi,saidai kuma shi zamma iya cewa baisan tanayiba,to shine mukeso malam yataimaka mata da Addu'a Allah yakarkato da zucuyarsa agareta,dontasamu natsuwa da kwanciyar hankali.
M-musa yakara kallon suhailat,yace to baiwar Allah,duk dadai nasan babu abinda yagagari Allah,Allah zai iya sauya Abu aduk lokacin dayaso,ammani nafiso ace abin nan dakikeso yazama na Alkairi agareki,domin idan babu Alkairi acikinsa to barinshi shi yafi,domin kuwa Allah yafimu sanin abinda zaifi zama Alkairi agaremu,idan bai baki abuba,kada kiyi fushi,watakila abin nan ba Alkairi abane agareki.
Amma tunda kince agayama Allah,shikenan,duk dadai yama fiki sanin abinda ke cikin zuciyarki.
Kafin nan zanyi maki istihara,zanbaki wasu Addu'oi DA zakiyi,nima zanyi anan,domin mutabbatar dacewa,shin abin nan alkairine koko akasin haka,zaki samu abin koko bazaki samuba.
Idan babu rabonki acikin wannan Dan uwanaki,to lallai kiyi hakuri,sai Allah yasauya maki da Wanda yafi shi,ni kuma intayaki Addu'ar Allah yacire maki abinda ya jarrabeki dashi,don haka zaku tafi ,nanda kwana biyu saiku dawo,domin muga abinda Allah zayyi.
Sukayi godiya ,sannan yadauko wasu Addu'oi yabata,nansukuma,suka ajemai kudi masu yawa.
Nan suka tafo.Ahanya kubura na kara tabbatar mata dacewa lallai zasu samu nasara,domin aikin malamin nan,kamar yankan wuka yake.
Tayi amfani da Addu'oin nan da M-musa yabata,saidai bawani canji game da yadda take jin son ya Ahmad.
Koda yaushe taganshi kara sonshi take,take kumaso ace itace tamallakeshi amatsayin mujin aure ba wataba.
Tana zaune itada kubura suna firar gobe zasu wuce Kaduna,kuma gobenne zasu koka wurin malamin su.
Suhailat tace kinsan wani Abu kubura? Haryanzun inason ya Ahmad,irin son danake jin bazan iya rayuwa ba tare dashiba,yanzun idan malam yace babu rabona ga ya Ahmad ya zanyi?
Kubura tace kimadaina wannan maganar,yaya Ahmad kamar kinsamesa,ai alamun nasarane kiji kina kara sonsa,kuma Nina tabbatar maki dahaka,nubanaso inji kina karyar da zuciyarki,kisa kawai aranki zaki samu,domin dai........
Sallamar Ahmad ce takatsemasu firar dasukeyi,suka amsamai tare da fadin barka dawo kenan?
Yace aiko kubura nadawo,nazone insanar daku kufa shirya,Donna gaji dazama garin nan,gobe dawuri zamu tafi,don haka kuyi shirinku tun yau.
Kubura tace yaya Ahmad wane irin dawuri,saikace dai ana korarmu,zadai mushirya yau,amma gobennan saikadanyi hakuri,muje mudawo.
Yace kinjiki dason yawo,INA kuma zaki?
Tace kayana zan amso wurin wata kawata.
Yace to don Allah karki bata mana lokaci,don banason mukai azahar anan.
Tace. Ahh!insha Allahu bazamukaiba.
Yajuyo yakalli suhailat,yace yaya dai kanwata,garinne koko jikin?
Tayi murmushi tare dafadin,duka babu Wanda babu.
Yace: sub hanallah!tare dakara matsowa kusa da ita,yace meke damunki?
Tace kaina naji yana yimin ciwo,amma nasha magani.
Dai dai nan kubura tatashi tabar masu falon,
Ahmad yace Allah yasauke,amma idan kinji ba dama anjima kishirya sai inkaiki Asibiti.

Talumshe idanunta cikin wani irin yanayi mai daukar hankali,tare dasa hannunta tadafe goshinta,tace wash!!Allah na!!cikin shagwaba.
Shikuma hankalinsa nakanta,yace suhailat yadai?
Tace bakomai.
Ya zauna kusa da ita yakafeta da idanu.hartaji tatakura,tace kallon menene wannan?
Yayi murmushi yace kyau naga kinyimin,sabanin yadda kikazo daga Engilar,kinga yadda kayan nan sukayi maki kyau kuwa?naji dadi dakika karbi magana ta dawuri haka,nadauka zansha wahala kafin inja hankalinki,wurin sanya tufafi irinnamu,amma sainaga cikin sauki.
Tace yaza'ayi kasha wahala,tunda nima banaso insamu matsala da yayana,domin na tabbatar dabandainasa kananan kayaba kullun sai nayi rigima dakai.
Yace Tabbas! Don kuwa zantakura maki harsai kibdaina.
Baki bani labarin Engiler ba.
Tace kaida kaki kawomin ziyara.
Yace tuba nake ayi hakuri.
Tamakale kafadarta cikin shagwaba tace nakiyi.
Yasa dariya tare da daukar filo yajefamata,sannan tamike tsaye tare DA fadin,natafi kira kubura kuci gaba dafirarku,sannan yafita.
Washe gari tunda wuri sujashirya suka koma wurin malam musa,domin aranarne sukeso suwuce Kaduna.
Cikin sakin fuskarta yayi masu maraba dazuwa,sannan suka gaisheshi,suka zauna kan tabarma.
Yafara dacewa. To Alhamdulillahi,ansamu yadda yakeso.
Nan danan fara'a tabayyana a fuskarta kubura da suhailat,cikin doki dajin dadi suma sukace,Alhamdulillah!!
Yaci gaba dacewa akwai Alkairi hadinki da wannan yaron,Tabbas!Nina gani,kuma zaisoki sosai,kikwantar da hankalinki,amma kikara hakuri,Ahmad shine mujinki insha Allah,zaki Aure shi kuma akwai Alkairi.
Kubura tace to malam ammafa nasan akwai wadda yakeso,kuma ita zai aura,yaza'ayi kenan?
Malam yace bazai Aure taba,wannan dindai itace matarsa,kuma zanci gaba dayi maki Addu'a.
Sannan yadauko wani jiko yabata,yace tashanyeshi anan,sannan yadauki wani rubutu kulli uku yamikamata,yace kwana uku zakiyi kinashan wannan ,sukayi godiya sannan suka tafi.
Aranar suka tafo Kaduna,Ahmad ke tukawa sai khadija NA kusa dashi,suhailat da kubura suna kujerun baya,
Sun isa Kaduna lafiya
Alhaji SULAIMAN mahaifin Ahmad yanada mata,sunan ta sa'adatu,'ya'yansu Hudu da ita,maza biyu mata biyu,Umar da Yusuf,Zainab da Shamsiyya .
Bayan tafiyar mahaifiyar Ahmad saudiyya ya aureta,shekararsu shidda kenan da auren,Ita kuwa H-Aisha da daya kawai suka Haifa da Alhaji sulaiman,wato Ahmad.
Sunakiranta da Aunty sa'adatu,gidan yakaure da murna,yaran sai tsalle suke,Ga Auncle!ga Auncle!!!yabisu yanadagasu daya bayan daya yana saukewa,don sunsaba dashi,dama yanayimasu wasa sosai ,yana kuma yimasu siye-siye.
Bangaren Aunty sa'adatu suka sauka,sukayi abinci sukayi sallah.
Shikuma Ahmad gaba daya yakosa yaganshi agaban sahubarsa Hafsat ,don haka yayi wanka yasha turare maikamshi sosai gamidasa bugaggar shaddarsa,yadauki mukullin motarsa sai gidan kawunsa Alhaji SALISU.
Hafsat tayi farin cikin ganinsa sosai,ta gaisheshi.
Shikuma yana tambayarta ya kewa?
Tayi dariya tace aidaga yau takare,tunda gaka INA gani,amma nasha wahala rashin ganinka daka tafi,idanuna sunrasa Amincin da sukafiso.
Yace to aigani nadawo,sai suzo suyita kallona harruwan cikinsu ya kafe,nasameki lafiyako?
Tace Iee toh!,lafiya lau,tunda nawarke daga jinyar daka Sani,yaya kabarosu?
Yace dasu mukatafo sunan gidammu.
Tace don Allah!hada khadija?yaushe zaka kawomin kawata?khadija sarkin surutu,kawatace sosai .
Yace saidai kekishirya inkaiki.
Tace aikasanni bana zuwa gudanku,kawai sai inje gidan surukaina?AA nidai nasan kunya.
Yace kuma kinsan wani Abu?inaji ajikina cewa nakusa malkakarki amatsayin matata,domin NA tabbata Abba yana shirin Aurar da 'ya'yansa bada jimawaba,yakika gani?kinshirya???
Yasa dariya tare darufe idanunta,nansukayi firarsu sosai,sannan daga bisani yashiga wurin iyayenta.
Alokacin kawunsa Alhaji salisu yananan .
Yace A Ah!Ahmad ne?sannudazuwa.
Ahmad ya amsa yana wani sunsunne kai waishi kunya yakeji,sannan ya zauna bisa kafet,kansa akasa.
Alhaji SALISU yace kasamu Hafsat dinko ?
Yace. e naganta yanzumma nafitone gida zanwuce,shine nabiyo tanan,
Yace to shikenan yakake ganin tsakaninka da yaribyar?kun dai daita kankune?domin inaso mushuga cikin maganar,saboda babu abinda zamu tsaya jira,kafin H-Ausha tadawo,yazama cewa saidai saidai tazo bikin ,don haka kasanar da mahaufinka idan kunshurya yazo inason ganinsa,domin. Atsaida maganarnan,aibawani juran da za'ayi.
Cikin farin cikin dabai taba kasancewa acikinsaba ya tsinci kansa.domin kuwa dama tuni yanajiran wannan ranar,gashi kuwa abin yazo akan gaba,donya tabbatar dama abinda Abbansa keshirinyi kenan,don haka ya amsa mai cikin kunya dakuma jin dadi,sannan yayi sallama yatafi gida .
Misalin karfe Tara nadare,lokacin Alhaji sulaiman yadawo gida,yana tare daduka 'ya'yansa,cikinnishadi da farin ciki,ga matarsa Aunty sa'adatu,gaba dayansu duk suna zaune a babban falon gidan.
DA sallama yafara magana,sannan yabude masu taron da Addu'a ,yaci gaba cewa
To kubura yanzundai Allah yanufemu da ganin dawowar yayarki suhailat,ancedai karshen tuka-tuka-kukk!gashi lokaci yayi,amatsayina na Wanda hakkin aurar daku yake akaina,to yazama lallai inyi kikari insauke wannan nauyin,kinga suhailat,har wasan buya mukarikayi da kanwarki,saboda inajemata da zancen aure,nima Dana ga haka saina zuwa,narabu da ita,inga iya gudunta,badai tace saikin dawo ba,to yau gashi Allah yayi dawowar ki.

Don hakani watannan basai yakareba,zan tsaida lokacin aurenku,in Allah yaso gaba dayanku,idanna aurar daku,khadija zata dawo wurina,saitaci gaba dayin jami 'arta anan Kaduna.
Yakuma cewa kubura.
Tace Na'am Abbah.
Kokinsan is'haka yasha zarya wurina,akan zancen Auren ki inakaramai lokaci?To don haka bada jimawaba zanbashi izinin yaturo atsaida lokacin auren.
Sannan yajuya da kallon shi zuwaga Ahmad,yace kaikuma ya ake ciki?
Gaba daya kubura da suhailat suka maida kallonsu agareshi,suhailat cikin wani irin tashin hankali take kallonsa.
Yace Abba dama dazunnaje gidan kawun munyi magana dashi,saiyace yanason ganinka.
Alhaji sulaiman yace kundai daita dayarinyarko?
Ahmad yace e Abbah.
Abba yace to shikenan,Allah yakaimu gobe zanje insamesa,kekuma kubura jibi is'haka zaituro asa rana,saboda..............
Kawai saidai ganin suhailat sukayi tamike tsaye,tanufi daki da sauri ,tana zuwa tafada kan gado,wani irin matsanancin kuka yakwace mata,bajimawa kubura tabiyota,tazauna kusa da ita,tare dasa hannayenta guda biyu tadagota zaune,tace
Haba Aunty suhailat miye haka?kibar tadama kanki hankali,har afahimci halin dakike ciki,don yaya Ahmad yace yana Neman auren wata,aiba shine yin aurenba,kima daina damuwa,Nina tabbatar wannan auren sayya lalace,kamar yadda malam yafada,kecedai matarsa,domme zaki rika damuwa tunda wuri haka?
Suhailat tashare hawayenta,tace kubura gani nakeyi kamar Ya Ahmad bazai aureniba,ko irin damuwa dani dinnan mafa bayayi,nikuma kullun soyayyarsa kara azabtar dani takeyi,wallahi kubura idannarasa ya Ahmad zan iya mutuwa!!
AAh!bari fadin haka Aunty suhailat,mezai hana bazaki aureshiba?zaki aureshi mana.
Suhailat tace tobagashi nanba,yana fadama Abba cewar sun daidaita da yarinyarba,kinga bama tani yakeba kenan!
Kubura tace to insun dai daita shine auren?aibashine aurenba,kuma kinsani so nawa akesa rana kuma daga baya afasa,nibanaso kikaraya Aunty suhailat,INA tabbatar maki dacewa aikin malamin nan,ba'atabayi ba'asamu nasara ba,kema kuma natabbatar za'samu.
Suhailat tasamu karfin gwiwa,gameda zancen da kanwarta kubura takeyimata,don haka tasaki fuskarta,tare DA fadin to shikenan.
Dai dai nan Alhaji sulaiman yashigo dakin,tare dayin sallama,yace lafiya?meya samu suhailat din?
Tace Abba kaina naji yana min ciwo.
Yace Ashsha!Allah yasauke,bari insa Ahmad yakaiki Asibiti,yanzun don kada ciwon kan yahanaki barci.
Sannan yafita yasanar da Ahmad yadauki mota yakai suhailat Asibiti,
Yace to Abbah
Suna cikin tafiya yake cewa,suhailat wannan wane irin ciwon Kaine ? Tunjiyafa kika fadamani,amma haryanzun bai saukaba?
Tace yasauka dawowa dai yayi.
Yace bakisha magani ba jiyako?
Tace nibanshaba.
Yakalleta sosai yace saboda me?baki son shan maganiko?to shima din bazamu shiya dakeba,indai bazaki rika kula da lafiyarkiba.
Harsuka kai Asibitin ysnayimata magana,Alokacin ita kuma takasa cewa komai,kuma takasa fahimtar shin awane hali take yanzun farin cikine koko akasin haka?
Anyimata aune aune sosai,sannan akabasu sakamakon,Ahmad yafara dubawa,lokaci guda kuma yadago kai yakalleta arazane,yace Hipotation?meya hadaki da hawan jini?
Tasadda kanta kasa,shikuma yatsareta da idanu,dayagadai takasa bashi amsa,sai ya tafi,ita kuma tabiyo bayansa,suka shiga mota bayan yabiya siyomata magungunan.
Bawanda yakara yima wani magana acikin su,kowa da abinda yake rayawa acikin zuciyarshi,har suka isa gida.
Suna isa falo ya ajiye magungunan sannan yazauna, yace dauko ruwa kizo kisha maganin.
Tabude firij tadauko robarruwa,ya karba yazuba mata acup,sannan yaci gaba da balle mata maganin,daya bayan daya,yana bata tanasha,saida tagama,yace nizan rike maganin,idan lokacin yayi,nizanzo inbaki dakaina,domin nalura basan shan magani kikeba,yatashi yawuce dakinsa .
Ita kuma dawani irin kallo,cike da kaunarsa,acikin zuciyarta,bayan yabace mata dagani,tace ya Allah kamallakamin ya Ahmad.
Is'haka yaturo da magabatansa,ansanya masu rana da kubura,haka shima Ahmad da Hafsat ansanya ranar Auren su.
Watanni shidda Alhaji sulaiman yasanya,yana kuma fatan Allah ya kawoma suhailat nata donya hada yayi baki daya.
Sannan yaci gaba da nemamma khadija makarantar dazataci gaba dayi,domin. Kuwa a yanzun soyakeyi tadawo hannunsa dazama.
Suhailat na kwance ,kubura nayi mata firfita,duk da sanyin A C dayake bugawa a dakin,amma wata zufa kekara yankomata,tana kara dafe kanta,dayake tsananin yimata ciwo.
Kubura tace:ni Al amarinnan Yakima Aunty suhailat har tsoro yake bani,gashi nan danan Dan tashin hankali bawani meyawaba,harciwo yazo yahaye maki.
Suhailat tayi saurin bude idanunta,tace yanzun kina nufin abinda yake damuna bawata matsala bace?kina ganifa yanzun ansa ranar auren ya Ahmad da wata,baniba,bakisan yadda nake jinsa bane acikin zuciyata shiyasa,saranar aurenshi da akayi da Hafsat yanunamin cewa bazan aureshiba,domin bawata alama dazatasa afasa wannan auren,shiyasa nayi muguwar karaya sosai kubura,Ya Ahmad barabona bane ,dai dainan kuka yakwace mata,hadi da zazzafan tari.,tace bazan iya auren waniba idan ba Ya Ahmad ba ,INA sonshi.
Kubura yace kada kikaraya Aunty suhailat,haryanzun munada sauran lokacin,badai wata shidda akasa ranar aurenba,tozaki iya ganin talalace kafin lokacin,yadawo kuma yace yana sonki,domin ni narigafa NA yadda da maganar malam.
Suhailat tace taya za'ayi bazan karayaba?kwata-kwata Ya Ahmad bai taba furtamin wata Kalmar dazan San yana sonaba,kubura juna Daff!,daku rasani,idan ban aureshiba mutuwa.................
Kubura tayi saurin rufemata baki da hannunta,cikin tashin hankali,tace bazaki mutuba Aunty suhailat,insha Allahu zaki aureshi ,bari gobe mushirya mukoma kano,saimu sanar da malam halin da ake ciki,in Allah ya yadda komai zai daidaita.
Haka kubura taita bata magana harta samu tashawo kanta.
Washe gari akaita rabon goron sa rana,ana kaiwa gidajen 'yan uwa da Abokan arziki, hakan yakara tada masuhailat hankali,
Don har sunyi shirin tafiya kano. Ciwon ta yatashi,cikin hanzari kuwa akakaita Asibiti ,taimakon gaugawa aka bata sosai,kuburace kejinyarta,Tasamu sauki.
Lokacin da Ahmad yazo dubata,yake tambayarta waidama tanada wannan lalurarne?
Kubura tace gaskiya bata dashi,daga bayane dai abin yasameta.
Yamaida kallonsa akan suhailat,yacewace damuwa kikesanyawa arankine hatta kaiki gahaka?
Kubura takalli suhailat suka hada ido.
Yamaimaita cikin magiya,yace waimeke damunki?waye yake bata maki rai?miye kika Nema kikarasa?
Gaba daya tambayoyin sunyi mata yawa,takasa bashi amsa,saidai kafesa da idanu kawai datayi.
Yakara matsowa kusa daita,yace fadamin menene?
Dai dai nan kubura ke kyafta mata ido sai tasanar dashi,ita kuma suhailat tagirgiza kai,alamar bazata iyaba,sai wasu zafafan hawaye suka gangaromata.
Cikin kika tace Ya Ahmad nima bansan abinda yake damunaba,.
Yace to kirika shan maganin ki akan lokaci,kuma kidaina yawan tunani kinji?
Ta daga mai kai alamar eh

Kwanansu biyu a Asibiti sannan akasallamesu,suna dawowa gida suka shaidama Abbah da Aunty sa'adatu,cewar suna so suje kano.
Abba yace toke suhailat jikinnaki yayi saukine?
Tace nasamu sauki.
Yace to kidaina yawan damuwa,ko Engiler kikeso kikomane?
Tace AA Abba
Yace tome kikeso?yaci gaba dacewa,kiyi hakuri suhailat,in Allah ya yadda,gaba daya zab aurar daku,bazasu tafi subarkiba,shiyasa nasan ya ranar da tsawo,kafin lokacin kema Allah tafito maki danaki,mujin,kinji,to kikwantar da hankalinki.
Gaba daya sunyi mamakin yadda Abba takusa gano miyene matsalar ta.
Sai cewa tayi aini Abba dacewa nayi aure nakesoba,.
Yace ainasani,ninedai naga dacewar hakan,amma kuje kudawo,za'asan yadda za'ayi,kwana nawa zakuyi?
Kubura tace kwana Hudu
Yace to Allah yakiyaye.


KANO
Misalin karfe Hudu darabi na yamma,suka ziyarci gidan m-musa,sun sameshi.
Cikin fara'arsa da sakin fuska,data zamemai dabi'arsa,yatarbesu.
Su kuma suka gaisheshi,sannan sukayi gaba dacewa.
Akan maganar nannedai mukadawo,Ahmad din datakeso dinne akasanyamaranar aure dawata,ita kuma gashi duk takasa kwantar da hankalinta,to shine mukeso malam Asama mana mafita.
M-musa yajinjina Kansas sannan yace:Toh!Al amarinne na Allah,lokacin dayawa dama yake badawa,amma Tabbas ni nasan wannan Abu zayayi jinjiri,shikuma jinjiri ga Al-amarin ubangiji alkairine,amma maganar ansanya mashi rana,aiba shine yin aureba,don haka zankumayin bakin kokarina,don ganin Auren nan tadawo gareki,Nina kara tabbatar maki dacewa kecedai matar Ahmad,saidai shi Dan Adam akwai shi da gaugawa,bayasonjinkiri,ammani inakarabaki hakuri,kikwantar da hankalinki,abin nan dakikeso zai samu,zankuma kara baki wani taimako yanzun.
Nan da nan yasa Allo yayi rubutu yawan ke,yahadasu DA wasu garin magani,sannan yabata yace ta shanye,bayan nan kuma yabata wasu,yace tafi wanka dasu tsawon kwana uku,sannan yaci gaba da karfafa masu gwiwa,akan lallai bukatar su zata biya,
Nan suka kara ajiyemai kudi masu yawa,sannan sukayi sallama dashi.
Bayan sunyi sallar isha'i,suna zaune,suhailat kecema kubura.
Nikau damukaje wurin malamin nan,saina karajin karfin gwiwa,koba komai dai naji sanyi acikin zuciyata,hankalina yakwanta,kuma nakara yadda da Al amarinnan.
Kubura tace aidama Aunty suhailat kekike tadama kanki hankali,ai saranar auren yaya Ahmad,bashine yake nufin kinrasa shiba,kobakomai kuma ai namiji daya mujin mace hudune,nifa nayadda da aikin malamin nan,domin kawayena dadama sun jaraba ,kuma ansamu nasara,shiyasa ni bantaba karaya akancewa bazaki auri yaya Ahmad ba,kawai dai dan jinkirine aka samu ,nikuma NA tabbatar kafin watanni shiddannan,sucika saimunga biyan bukata.
Suhailat tace to aini abinda yake dauremin kai shine,malamfa yasha fada Mani cewa nice matar ya Ahmad ta farko,to amma yaya hakan take faruwa?
Kubura tadanyi jimm!sannan tace,zai tabbata mubada watanni biyar mugani,idan baisauya ra'ayibsaba,Nina tabbatar kafin lokacimma komai ya daidaita.
Amma kuma Aunty suhailat inaso intambayeki.
Suhailat tace menene,?
Kubura tace nayi mamakin yadda akayi kika kamu da son yaya Ahmad lokaci guda,gashi haryana Neman yasa kirasa lafiyarki,idan baki samesaba,meyasa kike sonsa???
Humf! suhailat tayi ajiyar numfashi,tare dayin wani Dan guntun murmushi,tace:
Balokaci guda nakamu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On BABBAR HUJJA
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Yes

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment