Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yace kaih!!amma umma kinaji da matarnan tawa,mekika siyomata??
Tace set din akwatinane cike da kayansu,zan bayar akaima surukata tsarba,kafin lefenta yazo.
Yace kaih!!amma umma naji dadi,gata dason kwalliya!!umma baki ganiba!!!
Tace toya za'ayi nagani Tunda BANSANTABA,A'INA KASAMO YARINYAR?????
Kafin yabata amsa sai ganin suhailat sukayi tamimmike akasa,numfashinta yana fita da kyar dakyar,sannan tasamu tafasa wata gigitacciyar kara,data gigita duk Wanda yake cikin dakin.
Gaba daya hankalin Iowa yadawo kanta,tuni kubura tafashe dawani matsanancin kuka,don atunaninta suhailat tamutu kawai,gaba daya duk akadaburce,akadebo ruwa akayayyafa mata,amma inah!!tariga tayi doguwar suma.
Nan danan akafara kici kicin kaita Asibiti,Ahmad yafita yadauko mota.
Sukuma nan sunata kokarin yadda zasuyi sudauketa,sunkasa,har Ahmad din yadawo.
H-Aisha tace zoka kama mana ita afita da ita.
Shima cikin rudewa,yana zuwa yasungumeta Cak!!yasabata awuyansa,yafita da it's yasanya cikin mota.
Kubura da Aunty sa'adatune suka shiga motar,sukabishi,hankalin kowa atashe,haka akashigar da ita dakin Asibitin,taimakon gaugawa akaci gaba da bats.
Jinintane yahau sosai,sannan kuma zuciyartama tana Neman tabuga,lallai anaso tasamu bacci ishashshe,kuma banda hayaniya a inda take,domin asamu tadawo cikin hayyacinta.
Cewar Dr -Auwal.
Donhaka sukabi wadannan dokoki.
Sannan yakira Ahmad zuwa opice dinsa,bayan sun zauna,yace:
Waime kukeyima suhailatne?hakan take faruwa gareta??
Ahmad yace kamar yadda kake tambayata nima haka nake tambayarta,amma bantaba samun wata amsa daga garetaba,ni kaina inatunanin,akwai wani Abu dayake damunta,amma zurfin ciki yahana tasanar da kowashi.
Dr-Auwal yace,to lallai kusan menene matsalarta,sannan kufara magancemata ita,idan ba'akawar mata da abinda kedamuntaba,to lallai hakan zataita faruwa,tanashan wahala,don haka koba kaiba,Wanda yafi kusanci da ita tadaure tasanar dashi matsalarta,domin. Asan yadda za'ayi magance mata ita,idan bahakaba,zataita shan wahalane,umma kwananta bai kareba,amma da angane matsalarta akayimata maganinta shikenan.
Ahmad yace to shikenan,mungode,in Allah yaso za'ayi bakin kokari don ganin ansanmiye yake damunta.
Washe gari haka akaita zuwa dubata,alokacin tafarfado, 'yan uwa duksunzo dubata,har Ahmad ma dakansa yaje yadauko Hafsat tadubata.
Ahmad duk yakwashe yadda sukayi da Dr-Auwal ya fadama mahaifiyarsa H-Aisha,dakuma kokarin dayakeso tayi Mashi wurin gano meke damunta.
H-Aisha ta jinjina kanta,sannan tace to lallai yarinyarnan tana acikin matsala,toko aure takesone?
Ahmad yace mumada munyi zaton hakan,amma daga baya mukagane bashibane,domin kuwa tanada masu sonta,acikinsu kau harda Dr Auwal,to kinga kuwa matsalarta tadabance.
H-Aisha tace to shikenan, in Allah ya yadda za'ayi kokari,zan tuntubeta injimiye kedamunta,sannan tawuce tashiga dakin da aka kwantar da suhailat din.
Zaune tasameta bids gado,idanun nan NATA jawur,alamar tayi kuka tagaji.
H-Aisha takalleta sosai,sannan tajawo kujera tamatso da ita gefen gadon.
Tace suhailat kuka kikayi?meyasanki kuka?
Tadago takalli umma,acikin muryar kuka,tace:niba kuka nakeyiba.
Yace. Yazikice bakuka kikeyiba,alhalin gashi kuma kinayi,taurin kai ko suhailat?kinaso ki murine?
Tagirgiza kai alamar Aa
Tomeyasa kinsan lalurar datake damunki,zaki rika kuka,kinaso kullun jininki yayta hawane?kiso koke zuciyarki tabuga kimutu gaba data?
Toki kwantar da hankalinki,kicire duk wani Abu dayake damunki na kunci,nan Asibitine Inda akenemammaki lafiya,kinjiko??
Tadaga kai taredafadin eh.
Haka sukaita jinyarta kimanin kwana uku sannan aka sallameta
Rukayya tashigo,da sallama,tare dafadin,Aunty kizo umma nakira.
Tace to jekice ganinan zuwa.
Bayan tagama,sannan tatashi tanufi wurin kiran da akayimata.
Afalonta tasameta,tazauna tare da fadin gani ummah.
H-Aisha tamike tare dafadin taso muje.
Tayi gaba suhailat nabinta abaya,harcikin uwar dakanta,sannan tanunamata bakin gado,tace zaunanan.
Suhailat tazauna jikinta asanyaye,sannan itama H-Aishar tazauna kusada ita,tadan karkato tana kallonta,sannan tace.
Tambayarki nakeso inyi,kitsayar da hankalinki wuri guda,kibani amsa,kidauka cewa ni mahaifiyarkice wadda ta haifeki,zaki iya boye mata wani sirri naki?
Suhailat tagirgiza kai tare da fadin AA.
H-Aisha tace to kifadamin mekedamunki?meyake yawansawa ciwonki yake tashi?
Suhailat duk tadaburce,taji wata zufa naneman ketowa dukkan ilahirin jikinta,tayi imani bazata iya sanar dakowa wannan sirri nataba,koda kuwa zaizama ajalinta,ballantana kuma umma,to ince matame?ince danta nakeso?ai abunema Wanda bazai taba yuwuwaba,to amma yazanyi da ita yanzun data turkeni?dole ko karyace infada mata,don bazai yuwu intafi banbata amsaba,komain.........
Suhailat! H-Aisha takatsemata tunani,tace meke damunki???
Suhailat tace iyayena nake tunawa,shine kodayaushe hankalina yake tashi,wataranma ko bacci bana iyawa,shine kawai matsalata.
Aiko saita yadda,nan danan taji jikinta yayi sanyi,tace Allah sarki,lallai kinada tausayi,amma kuma kada kimanta,duk fa mairai mamacine,kiyi hakuri,nima nan kinga babu iyayena amma inayin rayuwata yadda takamata,kidaina yimasu kuka,Addu'a zaki rika yimasu,yanzun basa bukatar komai sai Addu'arki,kinji"kar inkarajin kintada hankalinki akan wannan,dakintunasu kiyimasu Addu'a kawai,kinjiko?
Tace to ummah.
Nan dai H-Aisha taita kwantar mata da hankali,akan hakan,domin ta yadda da abinda suhailat din tafadamata.
Sannan dai washe gari tafitoma da kowa tsarabara,tabashi.
Koda sukayi fira da maigidanta Alhaji sulaiman ,tasanar dashi damuwar suhailat kamar yadda itama ta sanar da ita
Nacewa iyayenta take tunawa,shine yake sanyata damuwa.
Saicewa yayi to wannan dalilinne yasa takiyadda da kowane saurayi inyazo wurinta?airashin iyaye bashi zaisa kakiyin aureba,idan harta bullo dahaka tana jayayya da hukuncin Allah ne?donyarabata da iyayenta,saitakibin umarninsa takiyin aure?haba Maman Ahmad,adai kara duba maganarnan.
Sannan yasa hannu yadauki wayarsa donyakira number suhailat.
Itakuma alokacin suna tare da kubura,suna karatattauna wannan lamari.
Suhailat tace kidubafa kigani ,har kayan lefen auran ya Ahmad angama hadawa,amma bawani canji,badole kullun ciwona yadinga hawaba!kwata-kwata ninasan bazan auri ya Ahmadba,ni rokon Allah nake yadauki rayuwata kafin bikin,Donni ranar bammasan irin tashin hankalin dazanshigaba,wuyar dazansha a wannan ranar Allah yayi tawa daita,shiyasa nake fatan ni inmutu kawai!!
Kubura tace :koni Aunty suhailat nakaraya da wannan abin,domin tunda mukafara bawani alama,yadda akedai haka ake,immada munaganin wata. 'Yar tangarda gameda aurennasu saimusa rai,to lafiya lau suke,gashi kwata-kwata bikinnan yau saura kwana gomasha daya,.
Don inajimma gobe za'akai kayan lefennan.
Dai dai nan wayar dake hannun suhailat tayi kara,Number Abbansu tagani,saida suka hada ido da kubura sannan ta daga kiran.
Kizo falon Maman Ahmad inason ganinki.
Tace to Abbah.
Shikuma yakashe kiran,
Takalli kubura tace kinjiwai Abba keson ganina,sannan tawuce.
Bayan tazauna yace:kikace iyayenki kiketunawa kikeyin kuka??

Ta kuma daure dukda taji tsoron tambayar,tace mai e Abbah.
Yace to abinda za'ayi gobe zansa Dr Auwal yaturo akanzancen aurenki,kila inkikayi aure kisamu nutsuwa,kinga zaizame maki uwa yazame maki uba,tunda mubamu ishekiba.
Aibatansan sanda wani tashin hankali yaziyarcetaba,cikin rudewa tace:Abbah Wallahi bashinakesoba!!
Yace wakikeso??
Tayi shiru,sai kuka yakwace mata.
Sukayi maganar duniyarnan,takasa yimasu magana,har dai sukagaji sukarabu da ita.
Alhaji sulaiman yace to shikenan,tashi kutafi radda kikaso auren kinfiddo mijin dakanki.
Cikin sauriko tatashi tabar dakin.
Aranar dayamma,bayan anyi sallar la'asar,H-Aisha nazaune tare da danta Ahmad,takecewa gobene za'akai lefennan,tunda Abbankama yasayo nasa kayan,Nina sayi guda shidda,Abbanka yasayi guda uku,to kaima kaje kahado guda uku,sunzama goma sha biyu kenan.
Yace ummah basuyi yawaba?
Tace surukata duk tafi karfin wannan,saidai kuma har yanzunfa baka sanar dani wacece zaka auraba.
Yace ummah nayi zaton Abba yafadamaki ai.
Tace AA bamuyi maganar dashiba WACECE?????
Yace ummah Hafsat ce diyar kawu ALHAJI SALISU.
Cikin wani irin yanayi,hartana sarkewar yawu amakoshinta,tace WAKACE?????
Shikanshi saida yadanji tsoro dairin yadda yaga umman tashi tacanza lokaci guda,
Tace diyar Alhaji salisu kacefa???yayana!!
Yace shimana umma wani Abu????
Kawai saita mike tsaye,tarika kewaye acikin falon,tana wani huci,
Sannan tadawo ga Ahmad takallai tace:
DIYAR YAYANA ALHAJI SALISU ZAKA AURA????
Tashi kabarmi daki!!acikin tsawa tayi masa maganar,sannan tazauna visa kujera,tare da dafe kanta da hannayenta gida biyu.
Shikuma jiki bakwari yatashi yafita .

ALHAMDULILLAHI
Mai karatu kabiyoni acikin littafin nagaba donjin yadda zata kasance. SHIN MECECE BABBAR HUJJAR?????
Shinko maikaratu yasan cewa yanzumma akafara labari? Kadauka cewa duk abinda akayi abaya tamkar shimfidane. Ynzunfa za'ashiga labarin,
Ayanzun darasin yake!!
Maikaratu zakasha mamaki,kuma zaisanyaka cikin tunani mai zurfi,
Harkallar da take acikin wannan labarin....humwummm!!kaidai biyoni kawai,zan warware maka zare da abawa,saikayi mamakin yadda wannan labarin zaikasance,
Akwai harkallah!!
Akwai rikita rikita,kaidai kawai saka tugwicin naira Dari uku kacal acikin Account number Dana baka afarko,sannan katuro da shaidar biya ta wannan number

09162526909

Idan ansamu matsalarta rashin account na bank ,toka turo katin naira Dari uku kacal akan wannan number
09162526909
Kadakabari abaka labarin


Daga maison farin cikinku Fatima Dahuru funtuwa Binta
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BABBAR HUJJA
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Yes

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment