Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dason Ya Ahmad ba,kinsan ita DABI'AR ZUCIYA tanason mai kyau tata mata,tuntuni ya Ahmad yakejidani,idan yazo gidan nan kafin ya ambaci sunan kowa,niyake fara kira,yana Jana ajikinsa sosai,alokacin har daddyn mu NA fadin ba wadda jininsa yahadu Dana Ahmad agidannan irin suhailat kowani wuri zashi sayyace suhailat zoki rakani,kafin yace wani yamikomai wani Abu yace suhailat tamikomai,harya zamana idan Ahmad yazo gidan nan bayacin abinci da kowa saida suhailat,na shaku dashi sosai.
To irin wannan kulawar dayake bani,saina dauka soyayyace ta aure bawai ta tsaya ga 'yan'uwantakaba kawai,saina sakankance akan cewa nan gaba Ya Ahmad zai zama mujina.
Nayi kewarsa a Engilar sosai,sai dai dayake munayin FIFA dashi ta waya.
Kubura idan kikaji yadda muke fira da ya Ahmad zaki dauka wani saurayinane Wanda mikeda Alkawarin aure dajuna,so dayawa inmuna fira dashi kawayena sukan dauka soyayya mukeyi,duk danidama ahaka nadauki abin,amma kuma kawai daga dawowa ta sai ace ansanyamai ranar aure dawata?tayaya za'ayi hankalina bazai tashiba??
Idan kuma hakane miyene ma'anar firar damukeyi dashi awaya,?miyene ma'anar kalamai dakuma soyayyar da yake nuna Mani azahiri,Wanda azuciyarsa Ashe bahaka bane,meyake nufi kenan ??yau darata yake ?idan haryasan ba aurena zayyi ba meyasa ya yadda nasaba dashi?meyasa tun farko bai rika janye jikinsa daga gareni ba?harya bari nayi sabo dashi.
Wallahi kubura inason ya Ahmad,idan bai aureniba yacuceni!!!
Kubura tace tabdijan!!yanzun samunshi zakiyi ,kiyi mai gwari-gwari,kiji dalilin dayasa yasakar maki jikinsa da kalamansa har kikayi sabo dashi,kiji dalilin dayasa yake fada maki kalaman da wadda kakeso da aurene kawai yakamata tajisu daga agareshi,wannan aiyaudarace!!lallai kisanar dashi abinda alakarki dashi tahaddasa maki acikin zuciyarki.
Suhailat tace AA bazan iyaba,amatsayina namace,bazan iyasamunsa infadamai damuwataba,kuma kema koda wasa bance kufada wani sirrinaba,kuyi hakuri kawai,Tabbas idanbarasa Ya Ahmad kuma zaku rasani,donko soyayyar shi bata kasheniba,NIZAN KASHE KAINA!!!!
Cikin tsorata kubura tace bazai yuwuba Aunty suhailat!!dolenema saikin aureshi!!bazamu rasakiba,duk tahanyar dazamubi zamubi,wannan ai yaudarace!!!
Suhailat tace bakomai ,mudai kara hakuri mugani zuwa wasu watannin,muga abinda Allah zayyi.
Kwanansu Hudu a kano,cikin kwana hudunnan suhailat duk ta gama amfani da magungunan da m-musa yabata,sannan sukayi shirin dawowa Kaduna .
Bayan sunyi kwana biyu a Kaduna ranar wata juma'a. Dayamma,sunyi wankansu,sunyi kwalliya,Ahmad yashigo falon,ya Tarar da suhailat,cikin fara'arsa,yace kanwata kuzo inji Abba.
Tamike tare da fadin gani nan zuwa,tabi bayansa,tana fadin INA Abban yake?
Yace mata yana dakinsa,biyoni inrakaki.
Tace to yana gaba tanabinsa a baya,tana kara kallonsa,sonsa nakara yaduwa acikin zuci
da sassan jikinta.
Yana kaiwa kofar dakin sayya tsaya,yace to shiga,nakawoki ko tsoro kikeji?
Tayimai wata irin harara dabatasan lokacimma datayitaba,acikin. Idanunta cike datsantsar son sa,
Yadun kule hannu zai kaimata duka cikin wasa.
Tayi baya dasauri,tana dariya,
Yace aidama nace matsoraciyace ke,inba hakaba aikinsan bazan iya bugunkiba.
Tace ya za'ayi insani,tunda gashi naga Alama.
Yadan bubbugar mata kumatu ahankali yace:kishiga Abban yana nan ciki,sannan yajuya cikin sauri yawuce.
Ita kuma tabishi da kallo harya bace mata,sannan tayi sallama tashiga cikin dakin.
Yana zaune bisa kujera yace,
Suhailat magana dama nakeso inyi dake .
Tace inaji Abbah,duk dajin datayi kirjinta na dukan uku uku,don batasan irin maganar dazayyumataba.
Yace:suhailat kinada Wanda kikesone?kuma kyka shirya dashi koko?
Tace AA tahanyar girgiza maikai datayi.
Yace to shikenan,anjima bayan anyi sallar magariba zakiyi bako.
Cikin wani matsanancin firgita tadago kai takalleshi,amma saidai bata iya gaddama abinda tazo mata dashi ayanzun,nan da nan taji zufa naneman rufeta,azuciyart tace
To wai INA zancen ya Ahmad,kodai bazai soni bane??
Alhja sulaiman yaci gaba dacewa,don haka saiki shirya,Dan Dan wani abokinane,Alhaji Hassan,tummuna yara muke tare dashi,to shima dannashi guda dayane,mahaifin ki Alhaji kabiru yasanshi,duk tare mukataso,to shine mukeso muhada wani zumunci a tsakanin 'ya'yanmu.
Gaskiya suhailat idan kika aureshi kin more ma aure,yarone mai natsuwa,ga kwakwkwaran aiki,don Allah kada kibani kunya,ki amince da wannan zabin danayimaki.
Nan dai yaita bata magana,Wanda daga bayama daina fahimtar abinda yake cewa tayi,saidai daga karshe taji yace:
Jeki cikin gida kishirya,bayan magariba zaituro kiranki.
Cikin rashin karfin jiki tatashi tawuce,daki,tana zuwa ta fada kan gado tafashe da kuka.
Kubura tamatso kusa da ita,tare da fadin mekuma yabata maki rai yanzun?
Suhailat takamo hannunta tareda fadin zauna kiji,sai Abbane yakeso yahadani aure dawani,wai Dan Dan Abokinsa Alhaji Hassan.

Kubura tace aishine Wanda Abbah yaturo wurina,to Aunty suhailat ki yadda dashi mana,bayada wata makusa kyakykyawan gaskene,gashi aikin costom yakeyi,Allah kau dakin hakura da wahalar da kanki,indai shidin yace yana sonki,kuma bakiga.........
Suhailat ta daga mata hannu taredafadin dakata kubura!ke meyasa bakice kina sonshi ba,lokacin dayazo wurinki,koda banganshiba bazabsoshiba!
Kisani kubura anayin Aurene da soyayya ,sannantayi karko,bazan biyema irin. 'Yammatannan da auren kawai sukeso,bawai damuwarsu wazasu auraba,duk Wanda akace yafito kawai saita yadda ta aureshi,ba tare dajin sonshi acikin zuciyarta ba,face dai kawai auren takeso.
(Musamman idan mace taso aure,kawai bazata tsaya taduba Wanda yayi dai dai darayuwartaba,kuma take sonsa,AA ita kawai bukatar ta ace tayi aure,saikiga idan akayi auren baya zuwa koina,dasundan Dade da auren shikenan sairashin zaman lafiya,todama bashi takesoba,auren kawai takeso,toyanzun kuma tayi,sai alokacin zata fahimci bamashine yadace ta auraba,saikiga auren baije ko inaba,anrabu)
Nikuma sonakeyi inyi aure Wanda bazan fitoba,kuma hankalina yakwanta ga Wanda zan auradin.
Don haka daga ba. YA AHMAD ba zan iya hakuri da aure!!!
Zandaibi umarninAbbah in saurareshi,amma balallaima in tsaya inkalli fuskarsa dakuma tsarin jikinsa ba,domin kuwa banason abinda zai zamema Ya Ahmad kishirya acikin zucuyata .
Bayan sunyi sallar magariba,Bakon yazo.
Babu laifi tayaba datsarinsa,da kuma yanayinsa,kobata tambaya ba tasan yarone Wanda Hutu dajin fadin rayuwa suka sanyashi atsakiya,kyakykyawan gaskene,
(Bacimmadai SO sone,koni danace tazabeshi tabar Ahmad dinnan,domin kuwa babu abinda yafi shi.
Yafara dacewa,suhailat ai inazaton kin samu labarina saurin kuburako?
Tace e tafara fadamani.
Yace Alhamdulillah.sunana Abdullahi,kuma nazone da kokon barata agareki,domin samun siyayyarki.
Budar bakinta sai cewa tayi bazaka samuba,domin kuwa inada Wanda nakeso.
Yakalleta sosai tare da fadin niko meyasa Abbah zayyimin hakane?kawai baikara wata magana ba yafita.
Dakin Ahmad yanufa,sannan yabashi labarin yadda sukayi da suhailat,yakara dacewa,amma Abba yasan cewa yarinyarnan tanada Wanda takeso yasa Nazi Neman ta?
Ahmad suhailat tabani mamaki,banyi zaton haka daga garetaba,nibarasama meyasa Daddyna yakeson dole sayya hada auren da diyar Abokin nan nasaba.
Ahmad yace don Allah kada kakaraya,nizan shawo maka kanta,domin kuwa tana jin magana ta sosai.
Abdullahi yace to aitace tanada Wanda takeso.
Ahmad yajinjina kansa,sannan yace to kaje kasanar da Abbah yadda kikayi da ita,kafin katafi.
Yatashi yatafi wurin da Abban yake,tasanar dashi.
Shikuma Ahmada nan take yakira suhailat a waya.
Tazo,DA sallama tashigo dakin,taredafadin gani Ya Ahmad.
Yace meyasa bakison Abdullahi?
Tayi shiru.
Yace tambayarki nake,waye kikeso?
Tadago kai dasauri takalleshi,kamar zatayi magana,sai kuma takasa,tamaida kanta kasa.
Yakuma cewa kafadamin waye kikeso?
Koko sokikeyi shikenan asanyamaki ido kita zama!to shikenan tunda haka kikazaba,ni inyi aure kubura tayi aure ,kekuma saikita zama agida!tunda haka kikeso.
Dai dai nan tafashe dawani matsanancin kuka.
Yayi saurin cewa tashi kifita kibani wuri! Sai kiyi shirin abinda zaki fadama Abbah idan yatanbayeki.
Tatashi takoma dakinta,cikin wani irin rikicewar tunani.
To yaya, Ya Ahmad din da malam yace zaisoni,amma yake fadamin irin wadannan maganganu,na tabbata Ya Ahmad haryanzun baifara sonaba.
Alhaji sulaiman yayi mata fada sosai akan abinda tayi masa,kuma ya turketa saita fada mashi Wanda takeso.
Sai cewatayi yabata lokaci zata kawo mai Wanda takeso kafin lokacin auren su kubura.
Cikin bacin rai Alhaji sulaiman yayi fada iyayinsa,akan yarannan sunwatsamai kada a ido,kawai yana cikin fada saiya tuna aiyanada khadija, 'yar autar su suhailat,nan danan yadai daita zancen auren Abdullahi da ita.
Aka kumayi sa'a yaran suka amince.
Yayi farin ciki sosai yaji kuma hankalinsa ya kwanta,anan yakara tabbatar da cewa,lallai
MATAR MUTUM KABARINSA!!!!
Don baitaba tunanin zai aurar da khadija ,awannan shekararba.
Aunty sa'adatu taso tanuna bataso ya aurar da khadija ba,tace mai.
Alhaji nikuwa kayi saurin yanke hukuncinban,duka khadija shekararta nawa?dazaka aurar da ita?saurin girmane kawaifa datayi.
Yace kina nufin khadija bata isa aureba?toya kikeso inyi?kinadai gani naturashi ga kubura,bata aminceba,yanzun kuma ga suhailat itama takiya,to sokikeyi itama khadijar inbari tayi girman da zan kasa bata umarni tabi?tunda tana sonshi yana sonta aiba matsala,badai karatu bane?kotana dakintama zatayi.
Mahifinsane yakeso ayi wannan hadin,yaturoshi,nikuma banaso ace ansamu matsala daga garemu,tunda dai harsuka roki wannan arzikin aibaikamata ace mumunkasa bayarwaba,kadai Allah yasa Alkairi acikin wannan Al amarin.
Kuma kike wannan maganar,ita kanta hafsat wadda Ahmad zai aura,aiba wani fin khadija tayiba,itama duka basha takwas garetaba?kuma aiba auren dole zanyi mataba,aurene Wanda ya yadda itama ta yadda,fatanmudai kawai Allah ya daidaita zamantakewarsu.
Aunty sa'adatu tabishi da Ameen.
Acikin satin nan kuwa,Alhaji Hassan yakawo kayan sa ranar dansa Abdullahi,haba daya yahado da sadakin da kuma kayannagani inaso.
Anandin kawaima ya kashi kudi,domin. Kufito dasu akeyi daga mota kamar bazasu kareba,harda akwatinanta guda uku,shake da kaya,duk cikin kayan gaisuwa suke,gaba daya mutanan gidan yabasu mamaki,don kodaya basuyi zaton hakaba.
Sannan kuma ango yakara ba Amaryarsa khadija kudi naira dubu dari biyu da hamsin,250,000 yace tayi siyayya .
Farin ciki awurin Alhaji sulaiman ba'a magana,nan danan itama aka tsaida lokacin Auren ta,dai dai danasu kubura da Ahmad.
Kowa yashigo yaga irin kayan da aka shigo dasu sayya rike baki.
(Lallai kam!nace wai Arziki nabin wasu suna gocewa!!)
Ahmad NA zaune adakinsa misalin karfe Tara nadare,yakira Number mamansa dake saudiyya,yake sanar da ita sa ranar khadija .
Yayi mamaki sosai hartana cewa
Khadija? Kodai suhailat??
Yace AA momi khadija dai.
Tace yo yarinyar hatayi girmane?
Yace tayi momi,sannan yabata labarin yadda akayi har Neman auren yadawo akan khadija .
Tace Allah mai iko!shiyasan abinda yasa yayi haka,Allah yasa hakan shi yafi zama Alkairi.
Sunsha fira da mominsa sosai,hartake fada mai,tafara shirye-shiryen tafowa,amma dai saibikin yarage sauran kwanaki kadan sannan zata dawo.
Ahmad yayi-yayi hafsat tazo gidansu wai ita kunya takeji,saidai shine yadauki khadija dakansa yakaimata ita.
Taji dadin ganinta sosai,don dama kawance sukeyi duk sanda suka hadu,taje mata da kayan sa ranar ta ,itama hafsat din tatayata murna,nan gidan suka wuni harda Ahmad,sukasha firarsu sosai.
Kwanaki nata shudewa,watanni nata tafiya,tun ana lissafin auren su kubura saura wata kaza,yanzun har anzo saura wata guda.
Babu wani Abu daya canza tsakanin soyayyar Ahmad da hafsat,kullun kara sonjunansu sukeyi,kuma babu wata Alama korashin dai daito da zaisa afasa wannan auren.
Hatta yanzun ita kanta kubura da take karfafama suhailat din,jikinta yayi sanyi,tafara karaya dacewa Ahmad zai auri suhailat.
Acikin 'yan watannin nan,kwanciyar suhailat Asibiti uku,domin abimma yana Neman yazame mata jiki,domin. A awon da akayimata na karshe,zuciyartama taharbu,hakan bakaramin tadama kubura hankali yayiba.
Kuma acikin watannin nan,zuwansu kano wurin m-musa yafi akirga,kullun kuma magana daya yake fada masu.cewar ITACE DAI ZATA AURI AHMAD!!!
To ayanzun sunfara daukar maganar tashima ba gaskiya bace,kawai dai yanayine don yaci kudin su.
Ranar da akasallamo suhailat daga Asibiti,suna zaune kubura tace:
Nigaba dayama nakasa gane irin wannan rayuwar taki,yanzun gashi kinnace kinason Wanda baimasan kinayiba,sai wahalar da kanki kikayi ,duk Wanda yaxo kice bakiso

Wallahi danasani da bamma fara kaiki wurin malamin nanba,domin duk shine yake kara kashe maki jiki da dadin bakinsa,har kike ganin lallai Ahmad zai dawo gareki,to amma tayaya zaidawo gareki baimasan kinayiba?kullun malam shike kara gaya maki lallai zaki auri yaya Ahmad,amma kuma haryanzun gashi shiru,basaiki hakuraba.
Allah akaroka kuma shi Allah ba'ayimasa dole,wata kila babu Alkairi a Auren ki da yaya Ahmad,shiyasa Allah yaki bashi damar dazaima furta yana sonki,ballantanama kuma shiga yarinyar dayake so.
Sannan takara tausasa muryarta tace
Don Allah Aunty suhailat kada kibari DOCTOR AUWAL dinnan shima yagoce,ki tsaidashi ayi Auren nan baki daya,indai basokike Abba yayi fushi dakeba.
Suhailat takara kallonta,tace wai kubura wane irin. Aure kikeso inyine?sokikeyi inyi aure da mutumin dabai kwanta maniba?wane irin zama zanje inyi dashi?Toni gaskiya ba irin matannan bane,wadanda su auren kawai sukeso,bawai damuwarsu waye zasu aureba.
Kiyi hakuri kubura lallai soyayyar Ya Ahmad tana Daf!!da tafiyar da rayuwata ,bazan iya tsayawa inga auren Ya Ahmad dawata,baniba,don haka ni yanzun inasauraron lokacin mutuwatane kawai,kokuma................
Kubura ta katseta da cewa,don Allah kada kikashe kanki"
Suhailat tace to zanyi nisa daku,zantafi inda bazan kara ganin ya Ahmad ba,kuma kudimma bazaku kara ganinaba,domin idan har...................
Tari ,tareda daukewar numfashi yasarketa,nan danan tafita haiyacinta,da kyar kubura tashawo kanta,nan danan tadauko mata magungunan ta Tasha ,sannan bacci mai Nauyi ya dauketa.
Bayan wasu kwana ki suhailat tana zaune acikin barandar gidan,bisa kujera.
Ahmad yazo wucewa,sayya hangota,dasauri yatafo inda take,yayi mata sallama,sannan yasamu wuri yazauna,
Yace dama inason inyi maki magana.
Tadago manta dasauri takalleshi,tare da fadin inajinka.
Yace maganar Dr Auwal CE,naga yadaina zuwa wurinki lafiya daiko?
Saita bata ranta,don batayi zaton wannan maganar yazo mata da itaba,
Tace lafiya lau,nadai sallameshine.
Yakalleta a razane yace kinsallameshi kamaryaya?kina nufin kice shima baki aurensa?lafiyarki lau kuwa?
Tace lafiya ta lau,kawai dai Wanda nakeso dinne haryanzun baizoba.
Ahmad yayi saurin cewa dama akwai Wanda kikeso?A INA yake?don Allah sanar dani,ko INA yake zanje inneminaki shi,suhailat banaso ayi bikinnan batare danakiba.
Ganin datayi mai duk yarude yanason jin amsarta,sai cewa tayi
Aiwanda nakesodin basai kaje wani wuri nemansaba akusa yake.
Yace akusa yake?don Allah fadamin. Waye,?
Tadago kai takalleshi kamar zatayi magana,saikuma tayi shiru,wata zuciyar tace mata kisanar dashi kawai,kome zai faru yafaru.
Saitayi tunanin,aikuma Kim makara,domin kuwa ayau saura kwana goma sha Hudu aurensa,zaki bata bakinkine kawai,ki tada hankalinsa,kikuma tada hankalin kowa NA gidan,Alhalin abin nan dakikeso basamuwa zayyi ba,yakamata kawai in.................
Ahmad yakatsemata tunani dacewa kanwata ya kikayi shiru,baki sanar daniba,please suhailat menene kikeso?banason tashin hankalinki,yanzunfa kin zama sai lallabawa,kodon lalurar dakike tare da ita,shiyasa nake ganemaki auren Dr Auwal zai zamemaki wata garkuwa tsakaninki da wannan ciwon,domin daganinsa wayayyene,zaikula dake sosai,zaki samu tarairaya a wurinsa,kinga daga nan hankalinki zai kwanta,ciwon dakike tare dashi kuma za'a samu saukinsa,wuddin kika samu kwanciyar hankali.
Tace aiwanda yasan hakan kawai yakamata yazama mujina,bawanda ake tunanin zai iyaba.
Bai fahimci inda maganart tadosaba.
Don haka sai cewa yayi,aishima yasani,tunda kobakomai aishine likitanki,don haka shiyafi kowama Sanin matsalarki, da maganin ta,da matakan da za'abi domin. Kawar maki da ita.
Tace badhida atakin dazai kawar Mani da damuwata ahannunsa,maganinsa saidai ya jwantarmin da ciwon,amma ainihin maganin ba'ahannunsa yakeba.
Ahmad yayi saurin cewa ainayake?
Taluradai haryanzun bai fahimcetaba,koko yagane abinda nake nufi,wulakancine kawai?
Sai cewa tayi mubar wannan maganar,acikin sati biyunnan zankoma Engilar,shikenan sai kowa yahuta da damuwata!!!!
Cikin sauri da razana yamike tsaye,tare da fadin What!!!mekike nufi suhailat?kina nufin kicema bazaki tsaya ayi bikinnan dakeba ??
Itama tamike tsaye kamar zata tafi ,yasha gabanta,tare da fadin baki bani amsaba.
Tace e bazan tsaya ayidaniba,dai dai nan wasu zafafan hawaye suka jike mata fuska,
Yace:Innalillahi wainna ilaihirrajiun!!Suhailat bansan damuwarkiba,kifadamin menene???
Tayimai wani irin kallo sannan tawuce,tabarshi nan tsaye yanata nazari.
Abin yadamesa sosai,Yakima kasa iya tuna miyene matsalar ta .
Hardare yakirata a waya yana lallashinta,amma ita takasa bude baki tace mai shine takeso,ba yadda bayyi da itaba,akan tagayamai damuwarta,amma takasa.
Daga karshe saicemai tayi Engiler kawai takeso takoma,shine damuwarta
Yace kodai kema auren kikeso kiyi?
Tace AA aikaima kasan in aure nakeso inyi inada manema,kawai dai tafiya nakeso inyi,kila zai iya nesantani daga damuwata.
Yace to miye damuwartaki.
Tayi shiru
Yakuma tambayarta miyene damuwartaki???
Sai cewa tayi sirrine
Yayi saurin cewa suhailat kobakida lafiyane?kike boyewa,idan bazaki iya fada maniba kifadama wani mana,sai anemamaki magani,
Tace ni lafiya ta lau.
Yace to shikenan saida safe tunda bazaki fadamaniba.
Haka yakwana tunane-tunane,waiko zai iya gano damuwar suhailat,amma takasa.

Mai karatu ayi hakuri nan zantsaya,saimun hadu awani page din.



Daga maison farin cikinku Fatima Dahiru Funtuwa

Haka washe gari yanemi kubura tasanar dashi,kotasan matsalar dakedamun 'yar uwarta suhailat ?
Amma sai cemai tayi itama batasaniba,domin yanzun kuwa,ko itama tasha jinin jikinta gameda wannan al amarin,domin kuwa kota sanar dashi babu amfanin yin hakan,abinda dai sukeso basamuwa zayyiba,dole takaraya da zancen malam musa,tunda yanzun gashi saura kwanaki kadan ayi bikinsa da Hafsat,kuma bawani alamu dazai nuna cewa za'aiya fasawa acikin wannan 'yan kwanakin,don haka taki sanar dashi komai gameda sirrin suhailat,don haka yahakura.
Tun ana saura kwana biyu H-Aisha tadawo,aketa shirye -shiryen tarbarta,kowa yakosa yaganta,musamman Ahmad,Dan ta guda daya aduniya.
Dohaka Ahmad din yasanar da Amaryarsa Hafsat cewa lallai tazo gidan ranar da ummansa zata dawo,domin atarbeta tare da ita.
Bayadda ta iya,don haka itama tayi shiri,ranarda H-Aisha zatazo itama tanufo gidan,domin sutarbeta.
Ranar Alhamis kuwa misalin karfe Hudu nayamma H-Aisha tana gida,karkuso kuga murna,hard a wadandama basu santaba,('ya'yan Aunty sa'adatu) domin kuwa bayan tafiyarta saudiyya aka auri Aunty sa'adatun.
Akahada lafiyayyar Dinner,da dama anriga angama shirya komai kafin ta iso,akaci akasha,sannan aka nutsu.
Acikin babban falon gidan suka taru gaba dayansu,anata fira acikin jin dadi,tanata farin cikin ganin 'ya'yanta,
Gasu kubura gasu Hafsat,tazo itama da kannanta,bayan sunhuta sosai,tafitoma dasu Hafsat tsarabarsu,tunda tafiya gida zasuyi,taraba sosai tayimasu,saibayan ishsha'i sannan Ahmad yamaidasu gida.
Airanar gaba daya suhailat batada sakewa,rannan nata abace,tunda taga Hafsat sai cika take tana kumbura,ballantana idan taga yadda Ahmad ke nan nan daita,kamar zata fashe don cika,karma lokacin dataga Ahmad yadaukesu zai maidasu gida,yadda suketa wasa da dariya da ita,hankalin suhailat yatashi sosai.
Sodayawan firar da akeyima acikin falon wani abun bata fahimtarsa,don hankalinta ba'anan wurin yakeba,gaba daya kanta juyawa yakeyi.
Har Ahmad yadawo batayi wani kyakykyawan motsi anan wurinba
Yana shigowa idonsa akanta,yalura dahalindatake ciki,don haka yaje daf!da ita ya tafa hannayensa dai dai fuskarta,tayi firgigit!!ta tsorata.
Yace yayadai sarkin tsoro??
Ta kirkiro wani Dan murmushi tayi mai.
Yasamu wuri yazauna,tare da fadin,Ummah na!!nakaisu,su kawu sunce sunayimaki sannu da zuwa,suma sunanan shigowa gobe.
Tace Allah yakaimu,sannan taci gaba dacewa.
Tsarabarku sai abari sa gobe sannan araba.
Ahmad yace toni umma tsarabar mekikayimani?
Tace tamefa?niyanzun kayan surukata nasiyo,irin tawa gudummuwar,amma sai gobe zanbaka.


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BABBAR HUJJA
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Yes

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment