Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qyamatar wani yaren.


Washe gari ga murna ga baqin ciki Dan kuwa Banda iyayensu maza da sauran manyan mazajen gidan Babu Mai farin ciki musamman saudat data kwana tana kuka.
Koda zasu tafi bayan 'daurin auren daqyar aka 6an6areta daga jikin umma sakina.

Ayshah kasa tsayawa tayi takoma 'daki ta lafe tana tsiyayar hawayen tausayin saudat Dan jitake idan itace bazata iya rayuwa ba iyayenta da 'yan uwantaba ko qin ji daga garesu.



Yau Monday kusan kowa nada lectures shiyasa makarantar take cike kowa Sai kaida kawo yake.

Lecture 'daya tayi 8 to 10 Kuma bazatai wataba Sai 2 shiyasa Kai tsaye ta fito ta nufi masallacin Mata na cikin school din ko karatun alqur'ani tayi kafin time 'din.


Tun safe mum 'dinsa ke rigima dashi akan yaje makaranta ya dage akan bazashiba sbd tsoron ninja lady.

Zama tayi bakin lafiyayyan gadonsa dayake dunqule cikin lallausan bargo ta kamo hannunsa
Ya zame hannunsa tareda 6ata fuska yace,

Mum please don't force me,I don't wanna go.

Never Nik,,I will never force you but please Christ sake don't leave your studies for some stupid crazy mask lady,, you're a man Nik so please act like one..

Kwantowa jikinta cikin sanyin murya yace,

I'm scared mum.

Murmushi Murphy dake tsaye tuni yayi yace,

Nik she's a normal human being just like you....

Hararsa mum tayi tareda 'daure fuska tace,

Not like him,
And I'm giving you 7days if she tries even coming closer to him talk to the pc make sure she leaves the school for good,
And you Nik get up and get ready I'm giving you 15 minutes to leave.


Tana gama fa'da ta Fice 'dakin Dan itama akwai zafi tana lalla6asa ne sbd tsananin sonda take Masa Amma Bata wasa da harkar karatun 'yayanta hardaishi Nik 'din daba karatun yakesoba sbd son jikinsa da rashin son wahala.

Wurgi yayi da pillow kamar wani qaramin yaro yanajin kamar yayi kuka sbd har cikin ransa tsoranta yake.


Wanka yayi ya shirya yafito tsaf Sai qamshi yake ga wani shining da fatarsa take.
Saukowa yayi Yana 'daura wani tsadadden Rolex watch 'dins na diamond.

Davina ce kawai zaune a dining tana breakfast taci ado cikin wata tsinananniyar gown iya cinya black saita da'da fiddo hasken fatarta gata dama kyakkyawa kamar Nik din.

Ko kallo dining 'din bai ishesaba ya fice sbd haushin ansashi tafiya makaranta dole
Da hanzari Murphy ya aje tea 'din dayake Sha yabi bayansa.

Tunda suka shiga makarantar yake dube dube gabansa na fa'duwa.

Murmushi Murphy yayi Yana mamakin halayya irinta Nik sbd komai nasa kamar mace yake yinsa Dan qila ko Davina dake mace Kuma qanwarsa tafisa juriya da qarfin zuciya.


Daqyar yaga sun fito first lecture dinsu suka nufi restaurant sbd yunwa yakeji.

Harsun kusa isa ya dakata Yana tuno abinda yafaru last time dasuka zo.

Kallon Murphy yayi tareda nuna restaurant din da ido yace,

Buy everything and Meet me in the car.

Daria Murphy yasaki kafin ya wuce sbd ganin duk Nik din a firgice yake.


Cikin nutsuwarta take tafiya kamar ko yaushe kanta a qasa gurin lectures zata koma Dan Time yayi.

Saurin ja da baya tayi sbd karo datayi da mutum.

Ajiyar zuciya tasaki ahankali sbd ganin macece tayi karo da ita ba namiji ba.

Da sanyin muryarta tace,

Sorry..

'Dif gurin sukayi sbd yau shine karo na farko da wani yaji muryarta a makarantar.,
Zaqi da sanyi tareda laushin muryar yasa kowa qara kwa'daituwa dason ganin fuskarta musamman ma zeey(zeey is back)😜 Wadda tafi kowa takura da tsangwama Mata ko a wancen karon itace sanadin fadowarta stairs harta fadawa 'dan hutu.

Kallonta zeey tayi tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,

Yaudai Kam dole muga abinda ke lullu6e cikin niqaf 'din Nan Dan jikina nabani kilama aljana ce muke tareda ita.

Danne niqaf dinta tayi ta ra6ata zata wuce taji ta riqo hannunta tareda dawo da ita baya da qarfi.

Wani qaramin flask taga ta bu'de ba zata ta watso Mata ruwan ciki da qarfi saitin fuskarta tayi saurin juyarda fuskarta gefe daidai da kawowarsa gurin ba zato yaji saukar ruwan zafi a qirjinsa..

Da gudu suka bar gurin shukuma want azababben ihu yasaki tareda sakin wayoyinsa

Da sauri ta juya Dan ganin wanda aka qona shima 'dagowa yayi Dan ganin wanda ya qonasa sunayin four eyes kawai saiya yanke jiki ya Fadi a sume.







Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*5&6*



Mummunar fa'duwa gabanta yayi ganin wanda abin ya sama juyawa tayi da sauri tabar gurin sbd Murphy dayayi mata alamar ta ta tafi,

Cikin tashin hankali da fargabar masifar mum ya kinkimesa Sai asibiti.


Koda su mum suka iso asibiti Banda tashin hankali babu abinda take ciki sbd Murphy cemata yayi coffee mai zafi Nik 'din yaje Sha ya zube Masa.

Koda Dr yafito yayi musu bayanin ba wata qonewa bace dan da alama ruwan basuda wani mugun zafi kawaidai yaji tsorone dakuma qila rashin sabo.

Fita mum tayi Dan Kiran waya hakama Finn bayanta yabi Davina kuwa kujerar 'dakin ta zauna tana chatting tana taunar chewing gum 'dinta.

Kallonta Murphy yayi lokacinda Nik 'din ya farka yaga hankalinta nakan wayarta ya maido kallonsa kan Nik murya qasa qasa yace,

Ninja lady....

Manyan fararen idanuwansa ya ware cikin tsoro,,
Murphy yayi saurin dafesa yace,

Easy Mama's boy,she's not hia but she'll soon be if you tell your mum that she is responsible for this.

Kallon wat do you mean yayi Masa,

Yace,
Yes bcox your mum won't let it go in vain so she's probably coming to take her revange and who knows h....

A tsorace ya katseshi da cewa,
No no no no i won't tell my mum and you too won't tell her anything...

Murmushi Murphy yasaki ganin ya ku6utarda ninja lady cikin sauqi sbd yasan duk mum taji the poor girl will lose everything.


Koda mum takuma tambayarsa akan qonewar yawu ya ha'diye tareda tuno abinda Murphy yafada saiya shagwa6e Mata batareda yabata amsa ba.


Aiki ja yasamesu Dan kuwa jinya ake ba sauki 'dan lele ya qone qiri qiri akasa Dr treatment 'din dole sbd dai shi baiga wata qonuwa ba Amma tunda Mama's boy ya lafe yace yanajin zafi agurin hakanan ake jinyar harkusan sati biyu a asibitin kafin suka dawo gida nanma wata sabuwar kulawar ta tashi masu aikin gidan basuda hutu Sai hidima suke.


Koda yaji sauqi qara lafewa yayi Dan karyaje makaranta mum ta takurasa saiyaje sbd duk son 'yayanta bata wasa da karatunsu.





Shika'dai yau yazo makarantar sbd Murphy na gurin wani program.

Zaune yake kan motarsa bayan ya fito lectures
sanye yakeda black dress da black speck Sai kyau da hasken fatarsa suka qara fitowa sbd duhun kayansa.

Waya yakeda dad 'dinsu saiga wasu friends 'dinsu dake shige Masa Amma shi Sam bai cika son mu'amala dasuba sbd sun cika neman Mata Dan ko acikin mota suna iya having sex da Mata Sam basuda class ko agurin za6ar matan shikuma mutum ne Mai son Abu Mai kyau tsaftatacce danshi qyamarma wasu matan yake shiyasa bai cika wani shiri dasuba.

Datse Kiran yayi Yana kallon 'daya daga cikinsu Mai suna Josh.

Murmushi Josh 'din yayi tareda Hawa tasa motar ya zauna yace,

Unbelievable Niklaus Aiden...
How could you let yourself get embarrassed by letting people know you're scared of some stupid mask lady afterall you're a man..


Kallonsa yayi da fararen idanuwansa ya lumshesu batareda yace komai ba sbd shima Sam bada son ransaba yake tsoronta gashi yanxu zancen yafara ya'duwa acikin makarantar.

Matsowa Josh yayi daf fuskarsa yace,

Let's do one,, let's get rid of this problem..

How?
Yace Yana Danna wayarsa.

Let's scare her....

Meaning?'''''yakuma fa'da Yana kallon fuskar Josh 'din.

Kashe Masa ido 'daya yayi Yana murmushi.

Shiru yayi Yana nazarin shawarar Josh 'din sbd zuciyarsa tayi na'am da zancen.
Murmushi yasaki tareda dirowa motarsa yashige Yana cewa,

I will see you guys tomorrow.



Washe da hadari sosai aka tashi shiyasa jiki ba qwari ta shirya ta wuce makarantar.

Tana Isa makaranta ruwan ya 6arke masu qarfi Nan kowa yafara gudu Dan fakewa.

Fixgota taji anyi tareda jefata cikin mota akabar makarantar a guje da ita batareda kowa ya luraba sbd qarfin ruwan.


Babban filin qwallo ne daya ha'du,
Tsakiyar filin yake zaune kan kujera sauran abokanansu biyu na tsaye riqeda umbrella sun Kare Masa ruwa.

Three quarter jins ne a jikinsa da boot Sai wata jibgegiyar rigar sanyi Mai laushi da hula.


Tsakiyar gurin motarsu ta tsaya suka bu'de tareda jefota inda yake zaune gabansa.

Qanqame jikinta tayi tareda sakin kukan tausayi da fargabar masifar dake gabanta ga ruwan saima tsananta qarfi suke.


Fa'duwa gabansa yayi ya miqe tsaye tareda juya musu baya Dan har lokacin akwai sauran tsoranta a ransa.


Zagayeta su Josh sukayi suna qyakyata dariya.

Rintse idanuwanta tayi tareda qanqame jikinta tana sake sakin Wani sabon kukan.

Niqaf 'dinta Josh ya fixgo tareda wurgi dashi tayi saurin duqar da kanta tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskar.


Hijab 'dinta yakuma fixgowa da qarfi Saida ya 6arke tundaga sama har qasa.

Doguwar rigar wani red shaking material ne ajikinta ruwan dake dukanta yasa tuni ya lafe ya kwanta ko ina a jikinta.

Wani yawu dukkaninsu suka ha'de sbd wata irin kyakkyawar surar fuxgar hankali dasuka gani.


Hannu Josh yakai zai janye hannuwanta don ganin fuskarta sbd shi tuni yagama kwa'daituwa Dan idanuwansa harsun fara wani Jan kwa'dayinta.

Caraf yaji anriqe hannunsa da qarfa.

Dagowa yayi sukai ido hu'du da Murphy.

Murmushi yasaki yace,

What is the rush Murphy?
We're all gonna enjoy so let me go first.

Turesa Murphy yayi da qarfi
Jin sunan Murphy yasa Nik juyowa ahankali idanuwansa Basu sauka ko inaba Sai kanta
Gabansa yayi mummunar fa'duwa...,

Fuskarta soke take tsakinin qafafuwanta babu Wanda yaga fuskarta Sai kyakkyawar farar fatarta da surarta data bayyana.

Kuka take sosai Amma ba'anjin qarar kukan sbd qarar ruwan saman dake sauka Dan dukkaninsu akansu ruwan ke sauka idan kacire shi shida baya shiga ruwan sama Dan yanxun ne zai kwanta ciwo.


Qura Mata ido yayi Yana kallon yanda jikinta ke girgixawa sbd sheshekar kukan datakeyi,,

Duk qarar ruwan saman masu qarfi dasuka hana kowa Jin kukanta shi tsaf yake Jin sautin kukan na shiga kunnuwansa suna amsa amo.
Cak ya qame agurin dukan zuciyarsa na tsananta.

Hijab 'dinta Murphy ya 'dauka ya yafa Mata
'dagowa tayi akaro na farko ta takallesa da manyan idanuwanta dasukai jajir.

Bugawa gabansa yayi da qarfi yaja Baya da qarfi Yana kallon fuskarta.

Dukkaninsu ja da baya sukayi cikin tsoro sbd ganin Murphy ya tsorata da ganin fuskarta sbd dukkaninsu babu Wanda yagani Dan baya ta Basu.


Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro takuma kallonsa.

Niqaf 'dinta ya wawuro ya miqa Mata sbd shi kansa bayason yacigaba da kallon wannan kyakkyawar fuskar da baita6a ganin irinta ba Dan zai iya zaucewa.

Kar6a tayi tasaka tareda gyara zaman 6arkaken hijab 'dinta tabar gurin tana tsiyayar hawayen baqin ciki.

A tsorace suke kallon Murphy Dan son yafada musu abinda yagani a fuskarta daya tsoratashi.

Dahar zai fa'da musu saiya fasa ya kalli Nik da ke tsaye kamar andasashi sbd har lokacin kukanta na amsa kuwa a kunnuwansa zuwa zuciyarsa.





Mamuh💋





_Dont forget to follow, vote and comments_.
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*7&8*



Harta Isa iga ruwa ake sosai shiya Hana aga 6arkewar hijabinta da jajayen idanuwanta.

Shigewa 'daki tayi ta dunqule da jiqaqun kayan tasaki wani sabon kukan.

Wasa wasa saigata da zazza6i ciwo kwance rigis sbd kukan datake yawan yi batareda anluraba.
Jinya tayi tsawon kwanaki kotaji alamar sauqi saita lafe sbd Sam batako qaunar taji ankira sunan makaranta bare hartayi sha'awar zuwa
Babu abinda tafi buqata yanxu kamar ace antsaida ranar aurenta da ya Umar anyi ta huta.





*********
Kwance yake cikin lallausan bargon gadonsa idanuwansa a lumshe Yana sauraron Murphy dake Masa fa'da akan abinda ya yarda su Josh suyiwa ninja lady.


Sautin kukan tane yadawo Masa ya cikin kunnuwa ya lumshe idanu tareda qara shigewa cikin bargo.


Kwana biyu mum 'dinsa tarasa gane kansa sbd son jikinsa ya da'du dan kullum daga makaranta Sai gida yazo ya kwanta ya lumshe idanu.


Kwana 'daya kwana biyu har sati batazo makaranta son ganinta yake sbd kullum Murphy bayada zance Sai nata shiyasa yanxu yakeson yaganta yayi Mata kallon mintuna sbd kawai ya cire tsoronsa akanta.



Yau kwana goma rabonta da makaranta dole tashirya zuwa sbd yawan tambayarta da ya Umar keyi akan rashin son zuwanta makaranta yanxu.


Tsaf tashirya cikin dogon hijab 'dinta maroon da niqaf dinta harma da safarta ta hannu da qafa kamar kullum.

Tunda tafito gida take addua harta Isa makarantar.

Sosai takuma Kama kanta sbd fahimta datayi komai zai iya faruwa matuqar batayiwa kanta babbar katanga da duk wata hanyarda Nik yabi ba.



Cikin ikon Allah hankalinta ya 'dan kwanta sbd kusan sati biyu kenan Basu ha'duba acikin makarantar Nan tasawa ranta Allah ne ya kar6i adduarta yayi Mata tsari dashi.



Sun fara exam shiyasa Bata cika Zama cikin mutane ba saidai taje can baya inda Babu mutane ta zauna tayi karatu kokuma ta zauna tana nazarin rayuwarta a makarantar.


Yau zaune take baya gurin wasu ciyayi dasuka kwanta luf iskar ni'ima na ka'dowa ahankali tana ratsata.

Ba karatu takeba kawai zaune take tareda lumshe idanu tayi zurfi cikin tunanin rigimar dasukayi jiya da ya Umar akan shima nijar yakeson komawa bayan aurensu itakuma Sam bazata iya rabuwa da iyaye da sauran 'yan uwantab dukda Sam Bata iya ko 'dagowa tayi Masa dogon kallo bare harta iya musa masa saidai tashige 'daki tayita hawayenta.



Zaune yake shima agurin ammashi Saida aka kafa Masa 'yar rumfa sbd iskar tayi Masa yawa sbd Sam ko ka'dan jikinsa bayason sanyi sosai Dan Nan take ne zai fara mura ko zazza6i.


Tare sukeda Murphy Amma yaje ya dubo Davina data kirasu yanxu wai gatanan tareda police cikin school 'din sbd glass 'din motarta da'aka fasa aka 'dauke Mata purse da laptop aciki.


Shika'dai ya rage zaune agurin fuskarsa sanye da black goggles daya qara fiddo haske,kyau,hutu tareda wayewarsa a fili.

Wayarsa yake ta6abawa kamar daga sama yaji Abu na tafiya a kafa'darsa ya zabura da sauri ya Duba...

Zaro idanuwa yayi cikin wani masifaffen tsoro da tashin hankali yayi wurgi da wayoyinsa duka tareda qwalla qara Yana cewa,


Mu..mu..mummmm scorpion,, scorpion,,help help help me,,mummmm


Dummm gabanta yabuga ta bu'de idanuwanta da sauri tareda miqewa sbd itama ba laifi akwaita da shegen tsoro...

Juyowa tayi da sauri zata bar gurin Ashe inda yake ta nufa saigata gabansa turus.

Tsayawa tayi tareda juyawa da sauri cikin tsoro sbd ganin kyakkyawar farar halittar qirjinsa a bayyane Dan tuni ya cire rigarsa yayi wurgi Sai ihu yake Yana qoqarin zare wan.....

Cikinta yayi tareda cukuikuyeta Yana ihu bakin Rai Yana Kiran scorpion..

Tsoro da tashin hankali yasa tafara qoqarin qwacewa Amma ba qaramar cukuikuyewa yayi mataba ba zato Sai gasu a qasa gaba 'daya Kuma har lokacin ihu yake sosai Dan duk ya yage kyakkyawar farar fatarsa sbd tsoro gashi yaqi sakinta.

Turesa tahauyi tana kuka ahankali Dan ita tsoron biyu ya kasar Mata gana scorpion 'din dayake Kira ga nasa.


Idonta ne ya sauka kan wuyansa taga gizo gizo irin Mai kaurin Nan Yana tafiya saman fatarsa...

Hannunta ta 'daga ahankali takai kan wuyansa ta 'dauko gizogizon tareda kai hannunta saitin fuskarsa ahankali cikin sanyin murya tace,

Look it is not a scorpion,,it's a spider...

Cikin wani irin yanayi ya 'dago sbd mummunan dukan da muryarta tayiwa zuciyarsa da gangar jikinsa taredayin rugu rugu da tsoron dayakeji Nan take.

Fuskarta ya kalla har lokacin a rufe take ya maida kallonsa kan tafin hannunta data ware tana nuna Masa spidern dake cikin hannun nata.,,

Kyakkyawar farar fatar hannunta fara tas ya qurawa ido gabansa nacigaba da fa'duwa sbd wannan shine karo na farko data cire Safar hannunta acikin makarantar,, Zara zaran fararen yatsun hannun nata dasukaji Jan lalle Mai matuqar tsari ya qurawa ido zuciyoyinsu na bugawa kusan atare....

Ahankali yafara 'daga hannunsa yakai fuskarta zai yaye niqaf dinta batareda ta hanasaba ta rintse ido hawaye suka gangaro tana jiran taji ya yaye niqaf 'din......


Wat da heck Nik''''''sukaji Davina tafa'da da qarfi sbd yanayin dasuka samesu Shiba Riga ajikinsa hakama kwance a qasa Yana maqale da ita.


A zabure ta turesa tareda miqewa tsaye shima miqewa yayi jiki a sake Yana kallon wainda ke tsaye akansu.,,

Davina, Murphy tareda police 'din case 'din motar Davina da wasu friends 'dinsu kusan su shida.

Dukkaninsu kallon Nik 'din suke cikeda mamaki da tuhuma musamman ma Murphy da tuni yaji zuciyarsa tafara quna.


Juyawa tayi jiki a mace kamar munafuka zatabar gurin cikin takaici Davina Tasha gabanta tareda kallonta a wulaqance tace,

Arrest her officers for trying to take advantage of my brother's inno.....

Stop Davina'''''' murphy yafada cikin Jin zafin abinda take fa'da.


Ayshah kuwa cikin tashin hankali takalli Davina da police din Jin tozarci da qazafin daza'ai Mata Dan kawai a lalata Mata suna.

Ido cike taf da hawaye ta juyo gefen Nik takallesa
Ya juyar da Kai tareda juyawa yabasu baya Dan har lokacin bai gama dawowa nutsuwarsaba ta yanayin dasuka kasance tareda ita.


Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suka gangaro Mata ganin yanda yajuya baya maimakon ya fa'di gskiar abinda yafaru.


Cikin tsawa Davina takalli officers 'din tace,

I said take her away.


Hannu police 'daya yakai zai kamo hijabinta yaja yaji anriqe hannunsa.

Dukkaninsu kallon mamaki sukabi Nik dashi ganin shine yariqe hannun police din ransa amatuqar 6ace.






Mamuh💋





_dont forget to follow, vote and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*9&10*



Cikin tsiwa ta matso gabansa tace,

Wat do you think you're doing Nik?

Kallon police 'din yayi da alamar kubar gurin da sauri suka bar gurin ya juyo ya kalleta yace,

Yes I mean she's not going anywhere and......

A hasale tace,

Wat?
are you crazy?
You must be out of your mind right?
I mean wat......

Shut up Davina''''''' yafa'da cikin qosawa da zancenta sbd zuwa time 'din zazza6i da ciwon jiki yakeji sosai na 'yar wahalarda yayi akan spider 'din.

Juyawa yayi zai bar gurin Amma wani irin jiri da azabar ra'dadin da fatarsa ke Masa yasashi yanke jiki ya fa'di a sume.


A ki'dime sukayo kansa Davina tuni ta 'daga waya takira mum ta sanarda ita Aiko a gigice tabar office tayo asibiti.


Kinkimarsa sukayi sukabar gurin dashi Davina na jifanta da wani mugun qyamataccen kallo Dan tayi alqawarin na'da Mata mugun tarkon dabazata iya fitaba.


Zubewa gurin jiki a mace hawaye na tsiyayo Mata zuciyarta na wani irin nauyi,
Daqyar ta miqe tabar gurin jikinta a sake.


Kodata koma gida saita kasa samun sukuni ta zare hijab 'dinta zata ninke taji wani Abu Mai 'dan nauyi a hijab 'dinta.

'dagawa tayi taduba gabanta yayi mummunar sarawa sbd ganin agogo maqale a hijab 'din
Tabbas koba'a fa'da mataba tasan na Nik ne..

Zarosa tayi jikin hijabin takalla saiga hawaye sun gangaro Mata ta zauna bakin gado tareda rintse idanu tana Jin zafi cikin zuciyarta.



Asibiti kuwa sunga tashin hankali Dan kuwa qaramar haukace kawai mum batayiba ganin jikin Nik duk a yakushe abinka da farin mutum da fatarda Bata Saba da wahala ba tuni yayi jajir har wata fa'dawa yayi cikin qanqanin lokaci.

Cikin sati 'daya ya warke sbd kyakkyawar kulawa da tattalin dayake samu hakama dad 'dinsu tuni yazo sbd yanda suka zuzuta ciwon.



Sauri take ta qarasa gida sbd yamma datayi ga yunwa da gajiyar data kwaso a makaranta.,


Ya salam'' tafa'da ahankali tareda saurin Jada baya sakamakon wata ha'daddiyar jeeb tareda motar police datasha gabanta.


Yawu ta ha'diye da qyar idonta na kawo ruwa ganin Davina ce janye da jeeb din tareda 'yan sanda.

Glass ta sauke takalli officer mace cikin police 'din tace,

Arrest her she's the one.

Girgixa Kai tayi tareda ja baya Amma haka matar tajawota da qarfi ta tura motarsu sukai station da ita.


Suna Isa Kai tsaye aka bu'de file 'din qarar wai ta fasa motar Davina tayi Mata sata hakama tayi amfani da akaifa duk da yayyake jikin Nik.

Ba kunya ba tsoron Allah police suka filen case 'din ahaka
Banda kuka babu abinda takeyi hartana shaqewa.

Address 'din gidansu tabayar sukaje suka sanar dasu cikin qanqanin lokaci saigasu ya Umar da baba alhaji.


Tana ganinsu tasaki wani sabon kuka tana qara tausawa kanta da zuriarta sbd wannan shine zuwansu police station na farko atarihin rayuwar gidan Sai gashi akanta anfara.

Kai tsaye sukace basu yarda da wannan zancenba Dan kuwa sunsan halin ayshah babu yanda zaai su yarda da wannan qazafin.


Money and power Mss queen tayi amfani dasu ta Hana a tsaya a saurari su baba alhaji qarshema turata cell akayi aka rufe
Kuka Babu kalar Wanda batayiba
Gidansu ma gabaki 'daya suna cikin tashin hankali Dan iya zafi sun 'dauka matuqa akan wannan zalinci da toxarci da akai musu.


Kwananta 'daya a cell 'din ciwo ya rufeta ala dole aka saka Umar maimakonta itakuma akai asibiti da ita.

Kwananta biyu taji sauqi suka zo suka Kuma tafiya da ita.

Tunda suka iso police 'din take kuka wannan karon gaba 'daya su harda baba malam da abbanta da baba alhaji sukazo taredasu Yaya abbakar.


Isowar mss queen tareda Finn da Davina yasa dukkaninsu miqewa suna kallonta cikin qyanqyami musamman ma iyayensu dasukafi Jin zafi ganinma Ashe kafiraine wainda suka yiwa ayshah wannan mugun wulaqancin.


Wani kallo tabisu baba Mal dashi kafin tashige office 'din officer incharge tabarsu tsaye kafin shima baba Mal yashiga daga baya.

Alamari dai baiyi kyauba sbd kaca kaca akayi a office 'din hardasu fa'da dansu Yaya abbakar taruwa sukayi sukaiwa Finn duka Suma Nan police suka hau dukansu kan kace me gurin ya ida hargitsewa Saida akaida gaske aka shiga tsakani.



Kwance yake a Palo Yana hutawa Dan har lokacin qarfinsa bai gama dawowaba duk da dai tunanine wannan karon yafi hanasa qarfafa jikinsa.

Three-quarter blue jeans ne a jikinsa da farar designer shirts qal,

Fatarsa tayi kyau hutu ya da'da bayyana ajikinsa sbd tun ranarda aka sallamosa ko gate 'din gidan bai ta6a fitaba Yana lafe kullum ana lilinsa.



Shigowa Murphy yayi cikin yanayi na damuwa ya kalli Nik yafara Koro masa bayanin halinda ake ciki.


Cikin wani irin yanayi zancen ke shiyarsa ya aje cup 'din milkshake dake hannunsa ya miqe tareda kallon Murphy yace,

Take me to the station...

Gudu Murphy yayi cikin mintuna qalilian suka iso station 'din daidai lokacinda Davina ta 'daga handbag 'dinta Mai qarfe ajiki zata qwalawa ayshah cikin zafin nama ya janyeta ta fa'do jikinsa cikin rashin sa'a niqaf dinta ya zame ya fa'di qasa.


Wani wahallalen numfashi yasaki kunnuwansa da idanuwansa sukai 'dif numfashinta dake fita da sauri kawai yakeji.


Fixgosa ya Umar yayi da qarfi tareda sakar Masa wani wahallalen Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini tayi saurin rintse idanuwanta wani nauyi na na sauka zuciyarta.

Ihu mum tasaki tareda shararawa Umar wani gigitaccen Marin itama.

Zaburowa su abbakar sukai aka damqesu tareda turasu cell shikuma mum da Murphy sukaja hannunsa zuwa mota Dan kaisa asibiti Dan hancinsa dake jini
Shikuwa duk baimasan sunayiba idanuwansa na kanta ko qiftawa bayayi

Itakuwa kanta na qasa takasa 'dagowa Dan jikinta yabata idonsa har lokacin na kanta.


A asibiti bayan anyi treating 'dinsa sun dawo gida kwantawa yayi kamar Mai bacci tareda dunqulewa cikin bargo bugun zuciyarsa na tsananta.


Daqyar da biyan ku'din suka samu aka sakosu abbakar suka dawo gida zuciyoyinsu duk a qone da tsananin 6acin Rai da baqin ciki ace wai su rasa abin arxikin dazasuyi fa'da dashi Sai kafirai.


Fa'da da nasiha Kam ayshah tashasu harta gaji.,

Sati 'daya kenan da faruwar alamarin kullum tana 'daki kwance lamo ko doguwar magana batason yi Dan ita tuni tacire Rai da batun komawa makaranta Dan tasan yanada wuya abarta takoma.


Zaune take da safe tana a 'dakinsu tana karanta wani hadisi su husnah nata Shirin tafiya makaranta.

Nuratu ce tashigo cikin uniform 'din makarantarsu takalleta tace,

Anty ayshah ya Umar nakira.

Lumshe idanu tayi tareda rufe hadisin ta miqe tsaye tasaka dogon hijabinta ta nufi 'dakin mama sakina Dan tasan yanacan.


Kallo 'daya yayi Mata ya 'dauke Kai sbd duk ya kalleta yanxu tunowa yakeda fixgowarda wannan shegen Christian yayi Mata ta fa'da jikinsa saiyaji zuciyarsa na tafasa Dan duk ranar dayakuma ganin wannan gayen ko a hanyane saiya cire Masa hannun daya ta6a Masa aysharsa dashi.


Gaishesa tayi a ladafce taredayin qasa dakai tana sauraron abinda zai fa'da.


Cikin danne baqin cikinsa yace,

Ki shirya kici gabada zuwa makaranta munyi mgn dasu baba sbd bazakibar karatunki kan wasu kafiran banxaba.

Lumshe ido tayi sbd yanda hakanan zancensa ya daki zuciyarta ahankali tace,. To tareda ficewa tabar 'dakin.





Mamuh💋

*_MAMUH GEEE_*



_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida_....



_viawattpad@mamuhgee_


*11&12*


A sanyaye ta shirya tanajin fargaba da tsoron sake ha'duwarta da Nik a makaranta.

Kodata fito nasiha da da'da su baba Mal da babanta suka sake yimata akan kwata kwata ko hanyar da wainnan kafiran sukabi karta kalla bare tayi sha'awar bi.


Tunda suka iso ta fito bus taji hankalinta ya

Please Login or Register in order to submit comment