Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,

Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,

Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar 'din da idanuwansa yafi nakowa rufewa da 6acin Rai.

Mummunar fa'duwa gabanta yayi tai saurin sunkuyar da Kai cikin tsananin fargaba..

Kallonta ya abbakar yayi cikin 'daga murya yace,

Meyasa kikai yamma sosai yau?

A sanyaye tace,

Bansamu bus bane yau da wuri.

Shikenan maza wuce gida.

Wucewa tayi a hankali gabanta na tsananta fa'duwa,,
kaman daga sama saitaji ya Umar cikin zafi Yana cewa,,

Duk inda yake Yana guraren Nan sbd da idona nagansa Yana tambayar yara Kuma na tabbatarda akwai abinda yake qullawa.

Cak ta tsaya sbd qafuwanta dasuka 'dau rawa..

Taji ya sani yace,

Wlh Nima yau nayi ido hu'du da shegen kafirin Nan saina karairaya Masa qafafuwa Dan ya koyi tsaya matsayinsa.


Yawu ta ha'diye da qarfi jikinta na rawa sbd fahimtar datayi kenan Nik nacikin layin,,Kuma ta tabbatarda ita yake nema....

Juyowa tayi takalli mugayen gororin dake hannunsu taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan tasan duka 'daya za'ayiwa Nik da wannan bazai qara sanin inda kansa yakeba.

'daga kai tayi cikin bugawar zuciya Sai gasa ta hangosa kusada wata qaramar matsatsiyar kwana Yana tahowa..

Wani mumman yawun tashin hankali ta ha'diye tareda juyowa takalli su ya Umar taga ba 6angaren suke kallo ba Amma gaf sukeda juyowa..

Cikin wani irin zafin naman dabatasan tanadashiba tayi saurin Isa gabansa daidai ya Umar ya juyo kawai saita janyosa cikin kwanar da qarfi Saida ya fa'do jikinta.

Wani irin kallo yake Mata cikin Jin da'din ganinta qayataccen murmushi na fita a fuskarsa..

Ahankali takallesa qwayar idanuwansu ta ha'du tai qasa dakanta gabanta na fa'duwa cikin sanyi da laushin muryar tace,


Why are you doing this?

Yana kallon cikin idonta yace,

Because I love you..

Kalmar ta daketa matuqa ta rintse idanuwanta cikin sanyi tace,

It's impossible...so please stop following me...yo don't know wat trouble you're getting your self into..


Cikeda sonta daya rufe Masa ido yace,

I'm ready to face anything for your love..

Girgixa Masa Kai tayi idonta na gangaro da hawaye tace,

We can never be together can't you get it,,,,we are from a different rel....

Shihhhh yafa'da tareda matsota sosai Yana kallon idanuwanta da lazy eyes 'dinsa murya qasa yace,

I'm ready to be like you if that's will b the only way for me to get you..,to be with you...
I love you ayeeshah..


Stop please''''''tafada da 'dan qarfi kuka na qwace Mata..

Kaman zaiyi kuka shima murya na rawa yace,

I love you ayeeshah,,, even if I wanted to get it out of my head I can't...

Muryoyinsu ya abbakar taji suna kusanto gurin tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin kuka tace,

Please go from here,, leave please...

Gyara tsayuwa yayi Yana kallon hawayenta dake ta6a zuciyarsa yace,

I'm not leaving until you tell me why you are so worried like this...
and this tears???'''yafada Yana kallon yanda hawayen ke gangarowa..

Karkace Kai yayi cikin son tabbatarda abinda yake zargi murya na rawa yace,

Ayeeshah,,,do you have any feelings for me too???

Rintse ido tayi cikin qaguwa tace,,

No please go...

Jada baya yayi yace,

No I won't go anywhere...

Matsowa tayi cikin magiya da kuka tace,

They will beat you black and blue... please pls leave.

Kusantota yayi sosai har numfashinsu na ha'duwa Yana kallon cikin idanuwanta da lazy eyes 'dinsa dasuka cikada hawaye yace,

Idan har dukan dazasumin zaisa natabbatarda you love me too then so be it..

Zan jira suzo.

Kuka tasaki ahankali hartana ciccika Nan take jikinsa ya 'dau rawa cikin hawaye yace,

Am sorry my love,,,I know I'm being stubborn but I can't help it because *i love you*......

Kalmar data shiga kunnensu ya Umar kenan daidai lokacinda suka kawo gurin.




Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_



*19&20*



Zafin zuciya da bugawar zuciya ne suka mugun tasowa ya Umar ya rintse idanuwansa Dan Daman tuni ya fara zargin ayi hakan tun kallonda yaga Nik 'din yayi Mata a station lokacin....


Rufewa idanuwansa sukayi ya qarasa gurin zuciyarsa na tafasa bai tsaya komaiba ya 'daga qaqqarfan hannunsa ya shararawa Nik wani gigitaccen Mari saiga jini ya 6alle ta hancinsa...


Saukar wani mugun zafi taji a zuciyarta tayi saurin rintse ido ta bu'de hawaye suka gangaro Mata ta 'dago a cikin karaya ta kallesa saitaga ko motsi yaqi yi ita ya qurawa lazy eyes 'dinsa dasukai ja sbd azabar Mari ko qyaftawa bayayi...


Fixgota taji anyi da qarfi ta 'dago jajayen you takalli ya Umar 'din ta bu'de baki zatayi magana a zuciye ya mare bakin da qarfi...
Durqushewa tayi qasa cikin azaba Amma tabbas azabar da zuciyarta ke ciki taci wannan 'dan Marin..

'dagowa tayi idanuwan Nik suka sauka kan 'dan jinin daya fito gefen bakinta sbd Marin yayi saurin zubewa gabanta jikinsa na rawa hawaye na taruwa idonsa murya na rawa yace,

You're hurt ayeeshah....
Ya 'daga hannu ya nufi inda jinin yake.....

Cikin zafi ya Umar ya riqe hannun tareda mur'dewa su ya abbakar kuwa Nan suka rufesa da duka.


Rintse idanuwa tayi hawaye na tsiyaya akaro na farko dataji wata mummunar qiyayyar ya Umar tana shiga tareda Huda duk wasu jijiyoyin dake aiki acikin jinin ajikinta.


Miqewa tayi batareda tajuyoba takalli irin dukan dasuke Masa ta fara tafiya cikin damuwa tabar gurin.

'dakinsu ta nufa direct batareda ta leqa ko inaba ta gaida iyayensu kaman yanda tasaba.

Kodata shiga su husna basa 'dakin suna 6angaren mama sakina Dan can sukafi Zama a irin wannan time 'din..


Zubewa tayi bayan qofa tareda sakin wani irin kuka ahankali tana dafe zuciyarta datakejin kaman xata tarwatse...


Hayaniyace ta kaure cikin gidan Nan take tani kowa na fitowa sbd hayaniyarsu ya Umar hardai shi da muryarsa tafi tashi cikin 6acin Rai...

Tanajin an ambaci kafiri ta lumshe idanuwa hawayenta na tsananta zuciyarta na da'da karyewa sbd batasan mummunan halinda suka sako Nik acikiba...


Da daddare bayan tayi sallah Bata tashi kan sallayarba anan ta qudundune sbd damuwa da zazza6in datakeji mai tsanani...

Nuratu ce tashigo 'dakin jiki a sanyaye ta zauna kusada ita takalleta murya asanyaye tace,

Anty ayshah su baba malam na Kira..

'dagowa tayi takalli nuratu da jajayen idanuwanta a sanyaye tace,

Sun kashesa ko nuratu?

Girgixa Kai nuratu tayi cikin tausayin 'yar uwarta tace,

Aa,,,,amma dai abun yayi Muni...

Kuka tasaki ahankali zuciyarta naci gabada tsananin zafi..

Anty ayshah da gaske soyayya kuke?

Batareda ta 'dagoba cikin kukan ta girgixa Kai...
Kafin ta miqe cikin sanyin jiki ta fito 'dakin ta nufi babban palon baba malam Dan tasan yanxu kowa nacan ya halarta..


Kanta a qasa tashiga tareda rakubewa ta zauna qasa..

So 'daya ta 'dago taga yanda kowa ke Mata kallon 6acin rai,qyama da tuhuma..tayi saurin qasa da kanta Tana danne hawayenta.


Cikin 'daurwar fuska da zafi baba alhaji yace,

Ayshah meye ha'dinki da wannan arnen.

Cikin sanyi da nutsuwa tace,

Babu komai..

A hasale babanta yace,

To meyasa ya biyoki yau harkuka ke6e?

Lumshe ido tayi ta bu'de sbd akaro na farko kenan dazatayi qarya murya a tausashe tace,

Nazo wucewa ne Sai muka ha'du shine yakeson tambayana nace bazan tsayaba.

Sake zaburowa baba alhaji yayi yace,

To su Umar sunce sun gani sonki shi yaron yakeyi.

Girgixa Kai tayi tace,

Ni banta6a sanin wannan ba hasalima yaza'ayima ta yiyu tsakanin ni dashi ba yare 'daya ba,
Ba addini 'daya ba..


Sai lokacin baba malam yayi gyaran murya sbd anxo gurinda yakeso Kuma yayi na'am da abinda ta fa'dan ya kalleta yace,

Ayshah???

Na'am'''tace a sanyaye batareda ta 'dagoba yace,

Na yarda dake nasan bazaki iya ta6a sa6a Mana ba ko take doka da umarnin mu Dan haka ga garga'di da umarni Mai qarfi,,,,daga yau ko hanyar dayabi karki Kuma kallo bare har wata magana ta hadaku harma afara Kuma irin wannan zargin Dan ni ko maganar wani kafiri banaso acikin zuri'ata bare har irin wannan mummunar zancen ya tabbata..


'dago Kai tayi ta kallesa tareda cewa,

To baba insha allah.


Miqewa tayi ta bar palon ahankali ya Umar yabita da kallon tuhuma danshi yana ganin abubuwa da dama datake 6oyewa Amma saiyasa ta bayyanasu da kanta agaban kowa na gidan.


Koda wasa dama batai gangancin tunanin bacci zaizo Mata ba hakanan ta kwana cikin tunanin wane Hali Nik yake ciki.


Koda gari ya waye taje gaida umminta saitaji duk jikinta ya da'da sanyi sbd ganin ga dukkan alamu ma umminta na cikin tunani da fargabar Kar zancen jiya ya tabbata.

Gaida ummin tayi cikin sanyi tareda kallon nuratu dake Mata kallon tausayi tana gaisheta.

Amsawa tayi tareda kallon ummi tace,

Ummi zan tafi makaranta..

Cikin kulawa da sanyin jiki ummin tace,

Ayshah Dan Allah karki bari zuciya takaiki ga Dana sani da muguwar rayuwa.

Hawaye taji sun taho Mata Dan tasan saidai Kuma wani ceto daga Allah Dan Mai Sha tarigada Tasha.

Zama tayi tareda kar6ar cup 'din kunun tsamiyar da ummin ke miqo Mata ta kar6a badan zata iya sha ba saidan kadata kuma bawa ummin damar wata damuwar.

Abbanta ne yashigo tareda sallama ta sunkuyar dakai ta gaidasa cikin sanyin murya..

Amsawa yayi kadaran kadahan kafin ya zauna kan tabarmar kusada ummin Yana cewa,

Ki qara kiyayewa sbd gudun jawo fitina da tashin hankali tareda 6acin suna acikin zuriar gidan nan Dan yanxu ina amfanin irin hakan tunda shi yaron sun Masa mummunan duka sun barosa can kangon gidan bayan layi sbd......

Wata mummunar sarqewa tayi tafara tari Mai qarfi sbd gigitar da zancen baban yasata.

Saurin miqa Mata ruwa nuratu tayi tana Mata sannu..,
Baba da ummi kuwa kallo suka bita dashi fa'duwar gabansu na tsanantuwa .


Miqewa tayi ahankali tace,
Na tafi..

Allah tsare ummi tace a gajerance baba kuwa ko amsa Mata baisamu yiba sbd damuwa da fargaba.


Bakin titi ta tsaya cikin zurfin tunanin rashin sanin abin yi....

Kusan Rabin Rabin awa tashare bakin titin Dan Sam zuciyarta taqi barinta tafiya...

Juyawa tayi ta canza hanya zuwa bayan layin gidansu.

Bakin wani kangon gida ta tsaya da kusanma anmaidasa bola sbd dadewar da'akayi ba'a cigaba da gininsaba.

Jujjuyawa tayi taga Babu mutane sosai agurin saitayi saurin shigewa gabanta na tsananta fa'duwa Dan jikinta har rawa yake.

Cak ta tsaya tareda zubewa qasa ba shiri...

Kwance yake baisan inda kansa yakeba cikin jini duk gabaki 'daya kamannunsa sun canxa da sbd duka da wahala.

Da rarrafe ta qarasa gurinsa tareda tallafosa jikinta ta fashe da kuka Mai qarfi tana Kiran sunansa.

Kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan tabbas batasan sonsa yayiwa zuciyarta mugun kamuba Sai yanxu data gansa cikin wannan mummunan halin....

Jin tayi kamar ya motsa tayi saurin 'dagowa suka ha'da ido sabbin hawaye suka gangaro Mata ta fara girgixa Kai cikin kuka tace,

Why....why...why Nik,,,,why did you choose to make me suffer by seeing you like this????

Duk da a wahalce yake danko hannunsa bai iya motsawa Amma ganinta yakawo farin ciki sosai acikin ransa barema dayaga halinda tashiga ganinsa haka..

Wani mugun yunqurin amai yayi saiga jini na fitowa ta bakinsa..

Zaro manyan idanuwanta dasukai ja tayi takalli jinin takuma maida kallonta kansa taga Yana numfashi sama sama
Da gudu ta fito tareda mantawa da wani tsoron Kar aganta tasamo taxi itada mai taxi 'din suka sakasa mota..

Baya tazauna taredashi duk da numfashinsa zuwa time 'din yakusa 'daukewa...

Damqe hannunta yayi cikin nasa hawayen wahala na gangaro Masa murya qasan maqoshi yafada Mata sunan asibitin dazata kaisa.

Shihhhhhhhh don't talk pls""""''''''tace Masa qasa qasa cikin kunnensa tareda qara damqe hannunsa tanajin zafi da ra'dadin ciwonsa na shiga zuciyarta.


Asibitin daya fa'da can takaisa suna zuwa akai emergency dashi Dr naganinsa yayi saurin zare farin glass 'dinsa cikin tashin hankali da mamaki yace,

Oh my God,,Nik ne wanna ai...

Fitowa yayi tareda kallon nurse 'din data biyosa yace,,,

Waya kawo patient 'din dake ciki?

Ada sauri ta nuna Masa ayshah dake zaune ta sunkuyar dakai sbd kukanta dayaqi tsayawa Dan yanda taga hankalin nurses 'din dasuka kar6esa ya tashi tasan ba qaramin Hali Nik 'din yake ciki ba.

Qarasowa gabanta Dr yayi tareda kallonta dakyau kafin cikin mamaki yace,

Kece Kika kawo Nik?

Kai ta 'daga da sauri cikin tsoron Mai zaice yasamu Nik 'din.

Kallon tuhuma yakuma jifanta dashi kafin yace,

Ina muma 'dinsa da....

Bata Bari ya qarasaba cikin fargaba tace,

Please Dr kafadamin idan zaiji sauqi..

Yes zai zamu sauqi but....

Ok Dr ngd Amma Dan Allah idan kanada number mum 'dinsa kafa'da Mata.

Share hawayenta tayi tajuya batareda tabari yakuma wata magana ba.





Kwance take nurse 'din da'aka 'dauko Mata tun Daren jiya Dan kulada ita tana zare Mata drip 'din dake hannunta har lokacin idanuwanta dasukai mummunar kumbura Basu daina zubar da hawayeba..
Finn ne akusada ita ya kwantarda kanta kan kafa'darsa Yana shafa kanta alamar rarrashi.

Mr Aiden ma daya iso da safen zaune yake kusada ita Davina na zaune kusadashi tashige jikinsa...

Dukkaninsu kallo 'daya zakayi musu kasan mummunan alamarine yasamesu Mai kamada mutuwa.

Waya Mr Aiden ya Kuma 'dagawa akaro na ba adadi yakuma Kiran police yayi Koda akwai wani update Amma still Babu.


Wayar mum ce tafara ringing Amma ko qyafta idanuwanta batayiba bare ta motsa...

Finn ne yayi qarfin halin 'dauka tareda saka loudspeaker...

Gabaki 'dayansu atare suka zabura Jin abinda Dr yafada mum kuwa tuni takai qofa jiri na 'dan 'dibarta Amma batajin zata iya jira.

Da sauri Finn ya riqota suka 'dunguma mota gabaki 'daya Sai asibitin.


Tashin farko da mum taga halinda Nik 'dinta ke ciki Sai ganin sukayi ta yanke jiki Saida dadinsu yayi saurin riqota ta fashe da kuka tana kallon yanda Nik dinta ke numfashi cikin azaba da wahala duk da har lokacin tashiba.

Saidata shaqi kukanta kafin ta miqe Finn ya Kama hannunta suka nufi office 'din Dr suka bar dad da Davina a room 'din.

Dogon bayani Dr yayi musu akan Yana tunanin mummunan dukane akayiwa Nik 'din Wanda harya ja Masa internal bleeding Dan qila andaki kansa.

Share hawayenta tayi ta Kuma kallon Dr tace,

Where did you find him I mean who brought him here?

It was a lady,,, she was all covered by.....I think she's a Muslim.

Tafasa zuciyar mum tafara Nan take 6acin ranta da baqin cikinta suka danne damuwar dayake ciki...

Miqewa tayi tareda kallon Finn dashima yacika yayi fam dajin cewar ninja lady ce tayiwa Nik wannan mummunan aikin.


Kallon Finn tayi bayan sunbar office 'din cikin tuquqin da zuciyarta keyi tace,

I want them to pay double for wat they've done to my poor darling boy...make them cry and regret their lives.

Yes mum""""yafada Yana fiddo wayarsa aljihu Dan making call.

Da daddare ya farka Nan dukkanin familyn suka kewayesa suna basa kulawa cikin so da qauna musamman mum da kamar tayi ihu takeji duk ya motsa taga ya rintse Ido alamar azaba.

Da daddare bayan Finn da Dad 'dinsa sun taimaka Masa yayi wanka ya saka kayan bacci ya kwanta mum ta lullu6esa ya lumshe idanu alamar bacci duk suka fito Dan tafiya gida.

Lumshe idanuwansa yayi tareda sakin murmushin da iyakacinsa zuciya ya tuno baby face da fararen idanuwanta lokacinda take kuka tana Kiran sunansa.

Ahankali cikin maqoshinsa yace'
I love you my sweet ninja lady...





Washe gari ma data fito kasa wucewa makaranta tayi saita samu kanta dabin umarnin zuciyarta ta nufi asibiti gabanta na tsananta fa'duwa Amma ba yanda ta iya Dan batajin zata iya Kai yamma batareda taga halinda yake ciki ba..


Baba alhaji da baba shehu tareda Yaya Ahmad da Yaya abbakar ne suka dawo daga gurin wani taron fatawa...

Daf dazasu Kai anguwarsu wata baqar mota Tasha gaban taxi 'din dasuke ciki kafin suyi want motsi qartin maza majiya qarf suka fito da bindigogi suka tasa qeyoyinsu baba alhaji dayaso gardama aka 'dibesa wani mummunan Marin dayasashi ha'diye maganar dayaso yi sukabar gurin da mugun speed.




Kodata isa asibitin Kai tsaye emergency ta nufa cikin sauqi saiga 'daya daga nurses 'din dasuka kar6esa a jiyan ta tareta cikin sanyin murya ta tambayeta room 'din dayake.
Nuna Mata tayi ta nufi 'dakin gabanta na tsananin bugawa.

Nesa ka'dan da 'dakin ta tsaya tareda qurawa qofar 'dakin ido tana qoqarin controlling matsuwarta tason ganinsa.

nurses biyu taga sun fito 'dakin mace da namiji tayi saurin qarasawa ta tare macen cikin sanyi tace,

Please patient 'din dake ciki yaji sauqi kuwa?

Kallon up and down tayi Mata kafin tace,

Eh Amma dai yanxu mun Hana kowa shiga gurinsa har family 'din sbd munason yasamu isashen hutu.

Bin bayan nurse 'din tayi da kallo bayan ta wuce tana tunanin kenan ba kowa a 'dakin.

For the first time taji wani farin ciki bayan tsawon lokaci..

'dakin ta dosa gabanta nacigaba da fa'duwa.

Tsayawa tayi bakin qofa tareda rintse ido tasaki numfashi ahankali tareda tattaro Yar nutsuwa ta tura qofar ahankali.


Cak ta tsaya sbd idanuwanta dasuka sauka cikin nasa Yana kwance ya qurawa qofar Ido kamar Daman yasan itace zata shigo..

Tashi zaune yayi batareda ya 'dauke idanuwansa cikin nataba..

Har ya iso gabanta Bata motsaba sbd garkuwar jikinta da idanuwansa suka kaririya..

Hannunta ya riqo ya jawota ciki ya rufe qofar har time 'din batayi wani qwaqwaran motsiba.

Zaunar da ita yayi bakin gadonsa tareda durqusawa gabanta idonsa cikin nata yace,

Ayeeshah did you came to hia see?

'daga Masa Kai tayi sbd batada kuzarin magana..

Wani qayataccen Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka bayyana ka'dan..

Tasowa yayi ya zauna kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta da wata kasalalliyar murya yace,

Did you love me ayeeshah?

Shiru tayi tareda sunkuyar dakai qasa.

Murmushi yakuma saki yace,

Please talk to me ayeeshah..

Juyarda Kai tayi still batace qalaba.

Murmushi yayi tareda zubewa qasa ya riqe kansa Yana juye juye cikin tsananin azaba.

A ki'dime ta sauko gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali da tsoro Amma saitaga Yana qara mimmiqewa saikuma yayi dif ba alamar numfashi ataredashi.

Kansa ta rungumo batareda tasaniba tafara kuka tareda Kiran sunansa...
_*I love you Nik*_,,,pls wake up..
_*I love you so very much*_.....

Miqewa tayi da sauri Dan kirawo Dr taji anriqo hannunta tayi saurin juyowa sukai Ido biyu Yana sakar Mata wani hot smiling...

Kallon mamaki take Masa da sauran guntayen hawayenta Dan tagano da gangan yayi hakan Dan ta fa'di abinda yake son ji..
Wata fitinanniyar kunyace ta rufeta tayi saurin juya Masa baya tana sauke numfashi ahankali...

Zagayowa yayi tareda matsota sosai danshi Sam bai 'dauki hakan komai ba...

Matsota sosai yayi jikin bango tareda duqo da fuskarsa daf da Tata har numfashinsa na mugun ha'duwa ya 'daga hannu ahankali ya cire Mata niqaf tai saurin rintse ido... fuskarta na bayyana wani sahirtaccen murmushin daya Kuma tafiya dashi.

Bakinsa yakai daidai kunnenta cikin wata kasalalliyar murya yace,,

You finally said it my love...

Sake tamke idanuwanta tayi sbd Jin kalar muryar dayayi amfani da ita ba qaramin shigarta tayiba.

Kallon dogayen eye lashes 'dinta yayi yace,

Will you marry me ayeeshah...

'daga Masa Kai tayi ahankali sbd tuni ta manta da wani banbancin yare da addininsu.




Su baba alhaji kuwa wani qaton gida aka kaisu suna shiga aka 'daddauresu tareda jiqasu tsaf da ruwan qanqara kafin aka fara jibgarsu baji ba gani.





Mamuh💋
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_


*21*


Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido...

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma 'debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba...


Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya 'daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da'di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka 'daukosu a watsar..




Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us...

'dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik...I can't marry you without my family's approval.. besides that I'm Muslim you're Chris.....

Katseta yayi da cewa,

I'm ready to convert my love....I want to become Muslim too...

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu...Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah...

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa'duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths 'dinsa qasa qasa yace,

Wait hia...

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice 'dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.

Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.


Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa'duwa ta qarasa a darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..

Yawu ta ha'diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba'a fa'daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da'di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba'ai zancen komaiba kan al'amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..


Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..
Matuqar zafi gidan kusan kowa ya 'dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba malam ya 'dau zafi matuqa....
Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..

Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,

Ayshah Kinga abinda wa'innan mutanen sukayi Mana ko?

Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..

Cigaba yayi da cewa,

Duk bazanyi wani tashin zanceba ko dogon zance auren Umar da ayshah nasaka Nanda wata biyu kowa yaje yafara shiryawa Kuma nijar zasu koma bayan auren nagama magana kowa zai iya tafiya.

Takaici ne ya turniqe Yaya Umar Dan so yayi ace Nanda sati 'daya a 'daura auren..

Iyayensu da sauran 'yan gidan kaf sunyi na'am da hukuncin baba malam 'din Dan tsoron abinda zai iya biyowa baya.

Ayshah kuwa jitayi hankalinta yayi mummunan tashi hawaye yaciko idanuwanta jikinta har rawa yake ta miqe ko gani batayi sosai tabar palon.

Kuka take sosai cikin qaramin sauti zuciyarta na tsananta shiga qunci..
Kamar munafuka takoma cikin gidan ko fitowa Bata cikayiba..hakama zuciyarta a matse take dason ganinsa.

Zaune take akan carpet 'din sallah kaman kullum tayi shiru idanuwanta a lumshe..

Zama kusada ita taji anyi ta bu'de idanuwanta ahankali ta sauke kan nuratu...

Qasa qasa da murya nuratu tace,
Anty ayshah jiya Da ina dawowa daga makaranta nagansa acikin anguwar Nan..yauma Dana dawo nagansa.

Qurawa nuratu jajayen idanuwanta tayi gabanta na duka da qarfi....

Muryarta na rawa tace,

Kinfa'dawa wani kingansa?

Girgixa Kai tayi tana kallon ayshahn tace,

Anty ayshah kina sonsane?

Hawayen dasuka gangaro Mata ta goge da bayan hannu tace,

Ina sonsa nuratu..

Dafata nuratun tayi cikin danne mamakin da tausayawa tace,

Anty ayshah karki Bari zuciya da shai'dan suyi galaba akan tarbiyar da iyayenmu sukai shekaru suna bamu.

Cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta ta bawa hawayen datake dannewa Daman kwarara..


Washe gari shiryawa tayi a sanyaye Dan batada tabbacin za'a barta cigaba da karatun duk da tuni ya fara wargajewa.

Cikin ikon Allah ba'a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen titi nanta ha'diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar gida suna Shirin fitowa...

Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui Masa Mai kyauba.


Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron wani qaramin gida..

Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare dasuba.

Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi...

Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin 'dinsa ya saitashi ya jefa Masa Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya 'dago lazy eyes 'dinsa dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya batareda yau ya gano gidansuba.


Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.

Azafafe yace,

Uban me kakeyi anan?

Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa'daba..

Mari Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..
Yace,

He said wat are you doing hia you monkey fool.

Kallon Umar 'din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani 'dan Adam

Please Login or Register in order to submit comment