Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanuwanta ta kawai da Kai saikuma wata zuciyar ta ingizata ta kar6a Tasha batareda dogon tunaniba sbd kawai buqatarta ta dainajin ra'dadin da ciwon datakeji cikin zuciyarta..


Kanta taji yafara 'dan juyawa ta 'dago takalli shanty saitaga biyu biyu take ganinta Nan ta tashi tana bin 'dakin da kallo Yana juya Mata saitaji abin namata nisha'di Dan kamar a sama take jinta.....



_mugun mafari_,,,

Sannu ahankali saiga ayshah ta warware Ras kamar ba itaba tuni aka sallamesu suka dawo gida duk da anty fannah tayi mamakin ganin sauyin gaggawa daga ayshan Amma saita dangana hakan da adduar datake kwana tanayi Mata.


Ayshah kuwa sabuwar duniyar sha aka shiga Dan kuwa tuni takoma school duk wata mashaya yanxu tare suke zuwa da shanty Wanda Nan take idanuwanta suka qara bu'dewa ta qara zanzarewa Dan yanxu ko Zama gida Basu cika ba kullum suna club suyi nis su lalla6o gida su kwanta,,,,,

Lokuta da dama tana idan tana cikin hayyacinta zaunawa take tayi kuka kamar ranta zai fita sbd ganin mummunar rayuwar data tsinci kanta sanadiyar iyayenta da Deen,,,
Tanason dainawa Amma abin yayi matuqar shiga jikinta Bata iyawa Dan yanxu shiga kowace iri taga dama yitake ta fita sbd abin ba qaramin fara shiga cikin kanta yayiba Dan ita Shan hauka takeyi harsaida shanty tafara Dana sanin sata aharkar.


Anty fannah alamarin duniya ya taru yasata gaba tayi kukan harta gaji Amma ayshah ta zare ko maganarta ba wani jitakeyiba saidai idan abin yasaketa tazo tana kuka tana Bata hakuri.,,,

Tun anty fannah na 'daukar abin da sauqi harta gaji tafara tsanantawa ayshah Amma maimakon sauqi saima ayshah ta qara zarewa danko gida Bata dawowa wataran idan sukayi dare saidai takwana gidansu shanty.

Rama da ciwo yafarasaka anty fannah gaba danko fita office Bata iyayi tayi kuka tayi addua tayi fa'da Amma ba wani sauqi Sai kawai ta tattara kayanta tabar gidan bayan ta rubutawa ayshah wasiqa.



Yau da wuri tadawo Qarfe bakwai parking tayi taga ba motar anty fannah gabanta taji ya'dan fa'di sbd tasan anty fannah batada lpia Bata fita ko'ina tunda da'dewa,

Fitowa tayi riqeda handbag dinta cikin shigar doguwar straight gown ta English wear black Sai blue Vail 'daure akanta da blue designer takalmi masu tudu sosai.,,,

Tayi haske saidai Rama dake tattare da ita dakaga idanuwanta zakayi zargin tana kora qwayoyi sbd a wani lumshe suke.

Palon tashigo Kai tsaye cikin sanyin jiki Sai ganin Nana tayi rakube tanata darzar kuka...

Rass gabanta ya buga cikin tsawa tace,

Can you please keep quiet,,,ke kullum bakida aiki Sai kuka..

Sharce hawaye Nana tayi tareda miqewa ta miqa Mata doguwar letter.

Kallon Nana tayi ta kalli lettern ta kar6a tana yamutsa fuska ta bude tafara karantawa...



Jikintane yayi mugun saki ta zube gurin jikinta na rawa Sai kawai tasaki kuka cikin mummunan yanayi na tashin hankali...

I've lost another part of my life today,,,
Once again rayuwa ta nunamin I will never be happy in my life again..,,

Kuka takeyi cikin mummunan yanayi Dan har wani qanqamewa take..

Sunanta taji Nana takira ahankali ta 'dago da jajayen idanuwanta saitaganta tsaye da kayanta ta rintse ido cikin ra'dadi da quncin zuciya tace,

Kema tafiya zakiyi bazaki iya rayuwa daniba...

Dama wazai iya rayuwa Dani iyayen dasuka haifenima sun gujeni mijin danake tsananin so ya gujeni,
Mahmud ya tafi,,anty fannah ta tafi kema kitafi dama ni nasan bani ba farin ciki arayuwa sbd rayuwata tagama lalacewa bamai iya tolerating din mugayen halayen danake dasu yanxu,,,.

Tana gurin zaune tana kuka Nana ta wuceta tabar gidan cikin tsananin kuka da damuwar halinda tabar ayshah aciki Dan tasan ayshah ada Mai sanyin Hali da hkr tareda nutsuwa Amma yanxu takoma Banda tsiwa da masifa tareda rashin mutunci ba abinda ta iya.


Tunda Nana ta tafi takasa tashi agurin har tsakar dare da shanty tazo suje mashaya ta tararda ita cikin tashin hankali tayi kuka har kukan ya daina fita...

Acikin Daren shanty ta kwashe Mata kayanta suka koma gidansu shanty 'din sbd iyayenta basa qasar zaune ita kadaice Sai tsohuwar dake tayata Zama sbd karatunta.

Duk iya wani farin ciki tarigada tasan ya qare Mata damuwa da baqin cikin rayuwa sun rigada sun yiwa zuciyarta mummunan kamu sai rayuwa ta qara lalace Mata sbd rugujewar da rayuwar ta ida yi.




_Years back_.....
Lokacinda manyan doctors suka gama iya bincike da nuna qwarewarsu akan matsalarsa sun gano yasamu shafewar qwaqwalwa,,
Sunyiwasu mum bayanin komai maimakon nuna damuwa Sai mum ta nuna farin cikinta akan hakan Dan ko ba komai she'll get her son back yanda takesonsa...

Davina kuwa hakanan taji hankalinta yatashi zuciyarta taqi yarda da amincewa da karsu fa'dawa Nik komai akan abinda yasamesa dakuma auren dayayi,,,

Sam bazata iya 6oyewa 'dan uwanta yanada Mata da ciki ba Dan gwara yasani yaje ya ceci matarsa da 'dansa daga baqar wuya.


Tunda ya warke yakomawa normal life 'dinsa as a Christian Davina takasa zama saidata fa'da Masa komai da farko bai yardaba harsaida yaga nacinta da dagewarta yayi yawa qarshema wayarsa dake 'daukeda hotunan ayshah dashi ta nuna Masa Nan yaji jikinsa yayi sanyi amma ackin zuciyarsa bayajin tsananin sonta kaman yanda Davina tace yana tsananin yi..
Saidai tausayinta daya mugun shigarsa na yanda tayi sacrificing komai kan sonsa shiyasa yayi alqawarin nemota ya inganta soyayyarta garesa.

Cikin sirri suka shirya tafiya Nigeria shida Davina ta hanyar yiwa mum qaryar Mexico zasu auren wani friend 'dinsa.
Ba musu mum ta amince suka taho Nigeria tashin farko gidansu ayshah suka nufa Kai tsaye.

Su baba alhaji suka fara cin karo dasu a qofar gida.
Gaidasu yayi cikin mutuntawa Dan Koda yake cikin yanayi na shafewar qwaqwalwa wannan mutunci da tsarkin musulunci har lokacin suna taredashi.

Kallo 'daya sukayi masa jiki duk a sanyaye suka amsa Nan yaso fara yi musu bayanin abinda ke tafe dashi suka dakatar dashi tareda kallonsa dakyau sukace yabar gidan idan ayshah yazo nema batanan sun koreta basusan inda takeba.

Kallonsu yayi cikeda mamakin yanda suka iya rufe Ido suka Kori yarsu batareda Duba yanayinta na 'ya mace ba Kuma harda juna biyu ajikinta.


Gida suka koma cikin ikon Allah da zallar mamaki saisuka tararda Murphy a qofar gidan cikin shiga ta alfarma ta cikakken musulmi.

Davina ita tayiwa Nik bayanin waye Murphy agurinsa Nan dai suka tattauna ya sanardasu shi yanxu musulmi ne sunansa muh'd nandai suka ha'da Kai suka duqufa gurin bincike akanta Amma ba wani lbr.,

Mum kuwa tuni hankalinta yatashi sbd antabbatar Mata dasu Nik 'din basa Mexico.

Davina tun dawowar Murphy taji duk duniya ba abinda takeso kamarsa Dan nutsuwa da tuninta tuni suka qwace Mata Wanda Sai alokacin take qara jinjinawa ayshah Dan yanxune takejin abinda taji Kuma itama a shirye takeda ta kar6i musulunci akan soyayyar datakewa muh'd.

Tun mum na 'daukar abin wasa saigasu sun shafe kusan wata hudu a Nigeria wanda tuni sukayi Nisa tareda maida hankali gurin koyan karatu da sani gameda addinin musulunci Dan kuwa tuni Davina ta musulunta.

Ganin sunyi neman Amma ba lbari yasa suka koma Amma batareda muh'd ba daya koma Abuja bakin aikinsa.


Lokacinda suka fuskanci mum haukace kawai batayiba ganin 'yayanta datafi so cikin inuwa da arzikin musulunci..,,

Rufe idanuwanta tayi ta koresu fata fata a rayuwarta dadynsu kuwa bai tauyesuba yabasu damar bin addinin dasuke ra'ayin bi.

Ba 6ata lokaci Deen ya Nemo musu admission a makarantar Madina shida Davina cikin ikon Allah suka samu suka koma Madina suka maida hankali kan karatunsu batareda wata damuwa ba.

Lokacinda suka kammala karatun Davina takoma gida shikuwa zurfafa karatun nasa yayi Sai gashi allah yayi Masa baiwar sanin addini Nan take yayi fice yazamo matashi lamba 'daya daya haddace alqur'ani da littafai da dama akan addini Dan kuwa duk wani taron musulunci da da'awa Yana cikin manyan baqi da musulunci keji dasu ayanxu,,

Hutu, kwanciyar hankali da arziki Mai tarin yawa sun samu Zama sosai arayuwarsa shiyasa Mata da dama ke sha'awarsa musamman kyawunsa da class 'dinsa dake fuzgar duk wata mace Mai sauraron fatawarsa.

Siyama salees shine cikakken sunan yarinyar data maqale Masa tun ranar farko data fara ganinsa a wani taro dayazo Nigeria a Abuja tun Yana share Mata hardai ya amince akayi aurensu Wanda ranar 'daurin aurensu a ranar mahaifinsa ya musulunta Kuma a ranar mum tagano ayshah hartasa aka sato Mata Mahmud takaisa qofar gidan Deen ta aje tareda doguwar wasiqar cewa ayshah ce takawosa akan Bata buqatar sake ganinsa ga dansa Nan yariqe...

Sosai yaji zafin hakan datayi Sai kawai ya 'dauke yaron ya bar qasar dashi bayan yayi dna ya tabbatarda dansa ne,


Murmushi mum tayi cikin farin cikin ganin tasamu hanyar fara cusa tsanar ayshah cikin zuciyar Deen kamar yanda tasan ayshah ta tsanesa yanzu danso take ko kallon juna karsuyi da mutunci duk ranar dasuka ha'du


Muh'd kuwa duk wani tunaninsa ya karkatasa ga binciken inda zai gano ayshah Dan kuwa lokaci yayi da zai kar6i abarsa kamar yanda ya qudurta.







Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*




_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._



_Viawattpad@mamuhgee_




*30*



*_gskia I really appreciate_*😍
*_masoyan taura biyu_*💋




Zaune take gaban mum Banda tsayayar hawaye ba abinda take sbd duk duniya batajin zata iya abinda mum 'din tace na cewar ta cire muh'd cikin ranta sbd tasan ba abune Mai yiyuwa ba,

Cikin baqin ciki da damuwa mum 'din tace,

I will never forgive that horrible ninja lady for wat she has done to my family,,
The family I build with so much love,
She distroy everything for me,,,,

Cikin hawaye Khadija (Davina) tace,

Mum please stop blaming ayshah sbd mu muka dama muka za6i rayuwar datafi, rayuwa Mai 'dorewa ta gobe a qiyama,,

Tashi mum 'din tayi jiki a sanyaye sbd gabaki 'daya yanxu Bata iya zaman mintuna da 'yayanta sbd zancen addininsu dasuke yimata akoda yaushe.


Cikin sallama yashigo qayataccen palon Yana tashin qamshin turaren Arabian oud cikin farar tsadaddiyar jallabiya fara blue Sai Kyau da hasken fatarsa ya da'da bayyana.

Kallo 'daya mum tayi Masa ta 'dauke Kai ta nufi hanyar bedroom 'dinta yayi saurin Shan gabanta tareda riqo hannunta fuskarsa 'dauke da wani lallausan murmushi yace,

My sweet mum please don't stop ignoring me like this,,
I love you so very much mum so will you please stop ignoring me mum,,

Kallonsa tayi tayi son 'danta da kewarsa na 'dawainiya da ita ta rintse ido tareda juyawa zatabar gurin..

Granny,,,,

Cak ta tsaya tareda sakin tareda juyowa Nan take tasaki fuska kamar ba itaba da gudu ya qaraso gurinta ta 'daukesa sama duk da yaqara girma sosai tace,

I miss you so much my beautiful boy..

Kumatunta yaja cikin dariya kamar yanda taja nasa yace,

I miss you too granny but I won't stay with you today since you're angry with my daddy.

Bedroom 'dinta ta nufa dashi tana cewa,

Your daddy is a stubborn man he doesn't care for me now....


Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka 'dan bayyana sbd yasan mum ta sauko sosai sbd tsananin sonda takewa mahmud Amma yakasa gane meyasa ta tsani ko sunan uwar Mahmud 'din afada.


Juyowa yayi gefen Khadija dayar kolacin take zaune tana kuka ahankali ya zauna a sofa Yana kallonta yace,

Menene Kuma Khadija?

Ahankali tace,

Shaikh just pray for me sbd naji ajikina nice Zan biya dukkanin haqqin ayshah da aka zalunta Dan kuwa tun yanxu nafara ganin ishara Kuma na tabbatarda duk inda ayshah take Bata cikin kwanciyar hankali tunda Bata tareda iyayenta da 'danta duk sbd soyayya.,,,,

Katseta yayi cikin 'dan yamutse fuska yace,

Karki ha'da kanki da ita sbd ita itace ta za6i kawo 'danta dantayi rayuwar dataga dama afterall tasan inda nake tunda harta kawomin 'dana so inda tanada niyyar Zama Dani da tuni ta bayyana kanta Amma she chooses to stay away and wani gefen zuciyana is telling me we are better without each other.....

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta tana girgixa Kai cikin kuka tace,

Shaikh kaiba butulu bane karkayi butulci da raharamarda Allah yayi maka ta musulunci ta dalilinta,
Shaikh kome ayshah tazama arayuwa Kaine sanadi,
Koda yake basai nafada ba Zaku gani akaina duk da banjiba banganiba Amma haqqi zai sauka akaina.

Miqewa yayi batareda yakuma tanka zancentaba yace,

Maganar zuwana Nigeria ne yataso sbd gobe Zan wuce insha Allah if you're still interested in coming with us ki shirya.

Wucewa yayi yabarta farin ciki na ratsa zuciyarta najin maganar zuwansu Nigeria zataje taga muh'd dinta.


Washe gari shida matarsa siyama da 'dansu mahmud tareda Khadija suka diro Nigeria suka baro mum cikin 'dibbin damuwar ganin gabaki 'daya yayanta yanxu kamar ba nataba nantafara tunanin mezai Hana tabi nasu addinin matuqar familynsu zai qara Zama Happy family kamar da.


A qaton lafiyayyan gidansa dake asokoro suka sauka Wanda Nan aka qaro securities agidan
Siyama hankalinta ya qara kwantawa Dan dama tafison zamansu a Nigeria akan can Paris 'din,,

Babbar damuwa da tashin hankalinda take ciki shine rashin haihuwarta har yanxu,,
Tayita yimasa compain akan hakan Amma bai damu ba sbd ganin mahmud dayake jinsa cikin jinin jikinsa Dan ba qaramin so yakewa yaronba.
Hakan yasa gabaki 'daya hankalinta ya tashi dason haihuwa sbd batason Koda wasa yayi tunanin maido karuwarsa tada Dan ita Bata 'dauketa matarsaba saidai karuwa Dan bataga dalilin ha'da shimfida da kafiriba tunda alokacin yanada sauran dabiar kafirai ataredashi.







********
Wani qaton babban hotel daya amsa sunansa na manyan mutane,

Acikinsa akwai manyan halls na alfarma dan meetings ko taron manyan mutane.,

Hakama akwai club na 'yayan manya dake cikin gurin Wanda ya tsaru ya ha'du ba kadanba.,,

Zaune take cikin club 'din tayi crossing legs tana sanye da wata designer English gown red datayi masifar yimata kyau sbd kwantawar datayi ajikinta Sai wani siririn black scarf Mai adon red data 'daure gashinta gefe dashi Wanda duk Rabin gashinta a waje yake sbd tsawonsa Sai hakan ya qara Mata kyau,,

Abuge take banda lumshe idanu ba abinda take shanty dake zaune gefenta waya take tana kur6a ruwan qwayoyi ahankali tana lumshe ido,,,

Wani kyakkyawan saurayine ya qaraso gurinsu cikin qasaita na kasancewarsa 'dan senator ya kalli Ayshah dako kallo bai ishetaba yace,

Eshaah my love look at me please,,,,look wat your love has done to m..

Banza tayi dashi tareda 'daka cup 'din dake gabanta ta shanye zuciyarta na tafasa taji Bata dainajin qunar zuciyarba ta 'daga wani cup 'din takai bakinta yayi saurin Kai hannunsa zai riqe cup 'din ta miqe tsaye ta 'daga hannu ta sharara Masa wani lafiyayyan Mari Nan take 'yan koransa sukayo kanta kafin suyi wani yunqurin takuma yanka Masa wani Marin Nan take guri ya kaure da hayaniyar fa'da sbd wani 'dan governor dayake matuqar son ayshan ya shiga fadan dama yanajin haushin Abbas 'din sbd yanason ayshah Nan suka hau fa'da harda fasa kwalabe.

Shanty datafi ayshah qarfin jini Dan yanada wuya ta bugu duk abinda Tasha kuwa,
Kamo hannun ayshar tayi suka fito harabar hotel 'din inda Nan take gurin yacika sbd fadan Nan yadawo.


Fixge hannunta tayi cikin maye tace,

Let go of me shanty,,,I'm not done,,,let me teach the bastard a lesson...

Fitowarsa kenan daga meeting 'din dasukayi agurin yayi mamakin ganin mutane agurin tunda ko hayaniya ba'ayi sosai agurin.

Kamar a mafarki idanuwanta suka sauka akansa ta lumshesu tasake bu'dewa sai kawai tasaki dariya Mai qarfi cikin tsananin maye tareda nunasa tace,

There he is,,,,the one and only Niklaus Aiden,
The greatest cheat so far...

Kanta securities dinsa sukayo sbd tuni gurin yayi tsit kallo Yakoma kansu ganin tana qoqarin 6atawa shaikh suna cikin bainar jama'a Amma Abbas yayi saurin Shan gabansu cikin rashin mutunci yace,,,,.

Karku fara ta6amin babe okay...


Dariya takuma saki tareda nunasa cikin maye tareda kallon shanty da juyayun idanuwanta tace,

Look at him shanty my sweet friend,,,
He is the father of my poor son Mahmud...

He is nothing but a cheat,,,,he uses me and run away like a,,,,, like a,,,
Yesssss like a mosquito..hahhhhhhh

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa gashi tuni yafara ganin hasken cameras na tashi ana 'dauka koba'a fa'daba ya tabbatarda itace ayshah uwar 'dansa,,,


Kanta securities sukayo tayi saurin zillewa tana dariya ta isa gabansa takallesa from head cikin dariya ta ta6a Masa tana cewa,

Wow Mama's boy yatara muscles bayan yasha duka agunsu ummmmnnn Yama sunansa,,,,,yesss ya Umar the great heartless parson of the universe,,,,look shanty everyone look"""""tafada tana qoqarin Kai hannunta kan damutsansa cikin tsananin 6acin Rai da baqin ciki ya watsa Mata Marin dayasa Rabin mayen dake tareda ita sakinta ya fa'da mota da qarfi driver yaja sukabar gurin wasu na tir da halinsa na 6oye da yau tsohuwar karuwarsa ta tona..

Ita kuwa baqin ciki takaici da danasani ne suka shigeta na abinda tayi cikin mayen shanty tajata sukabar gurin..

Koda ya Isa gida Zama yayi a kujera zuciyarsa na tsananin tafasa he can't believe he once fall for that shameless crazy lady,,,no I can't love that thing'''yafada da qarfi Yana miqewa tareda fadawa toilet yasakarwa kansa ruwa Dan ji yake kaman zaiyi bindiga sbd baqin ciki da takaicin ganin Wadda ake cewa yaso abaya.



Qin fadawa Khadija yayi yaga ayshah sbd bayajin zai iya cigaba da Zama da mace kamarta,,,
Koda yafadawa muh'd kuwa ganin yayi hankalinsa yatashi Nan yaqara labarta Masa halayen ayshar nada shidai shiru yayi Dan baiga duk wasu gud qualities dake cewa tanadasu ba atareda ita.



Kwana biyu da faruwar hakan sukaje shopping a wata qatuwar sabuwar mall da'aka bu'de itada shanty duk da har lokacin ranta da zuciyarta kullum qara qonewa suke da baqin ciki da tsanarsa akan gagarumar qiyayyar daya nuna Mata ta hanyar marinta Dan abin ya daki zuciyarta matuqa Dan kwana tayi ta wuni tana kuka bayan mayen yasaketa ace mutumin dataso harta jefa kanta cikin wannan mummunan rayuwar shine ya 'daga hannu ya mareta.


Doguwar gown ce ajikinta Ash kamar ta maza Amma tanada shape da aljihu na gaba Dana gefe gefe tayi matuqar yimata kyau sbd kaskenta da kyawunta daya fito duk da tuni ta manta wata kwalliya,,,
Facing cap tasaka akanta red duk da gashinta ba duka yashigeba Amma ko ajikinta sbd yanxu ba komai take gane shine daidaiba.

Wayartace kawai ahannunta
Shanty ma dai goduwar rigarce Amma ita normal Arabian gown baqa Sai qaramin scarf yellow 'daure akanta.


Shanty ke 'daukar komai itadai Banda tunani ba abinda take duk da Tasha ka'dan kafin tafito abin dai yau da 'dan sauki bazakace Tasha komaiba matuqar ba magana tafara ba.


Daf da zasu fita taji gabanta yayi mummunan fa'duwa sbd muryar dataji har abada bazata mantataba...
Da sauri ta juyo tare jikinta har rawa yake tace,

Mahmud,,,,

Wat""""tafa'da da qarfi sbd ganin waye yake riqeda mahmud 'din...


Riqe yake hannun siyama tana tareda Khadija suna shopping cikin nisha'di hankali kwance...


Rantane yayi mummunan 6aci zuciyarta ta rufe ta qarasa gabansu batayi wata wata ba yankawa siyama wani gigitaccen mari,

Arazane suka kallota Khadija ta zaro Ido zatayi magana a qule ta 'daga Mata hannu tareda Kai hannu zata jawo 'danta taji anriqe Mata hannu tareda tureta baya cikin tsananin 6acin Rai ya kalli siyama dake dafe da kumatu ya maida kallonsa kanta yace,

Don't you dare touch him with these dirty hands dasuke aikata sa6on Allah,,,just leave here quitly sbd I won't tolerate your nonsense again so just leave..


Kallonsa tayi ido cikin Ido idanuwanta na cikowa da ruwa tace,

I hate you,,I hate you so very much,,I've never regretted anything the way I regret knowing you in my life,,
You take away my son from me you cheat....

Riqeta shanty tayi da sauri sbd tuni tafara jawo musu attention 'din mutane..

Kallon Khadija dake kukan ganin mummunar rayuwar da ayshah ta tsinci kanta aciki yayi cikin 6acin Rai da takaici ya nuna ayshah yace,

See,,, see the woman you've been praising and talking about.,,

Girgixa Kai tayi cikin kuka tace,

Shaikh ayshah is a decent and.....

Will you please keep quiet,
If this is the kind of girl I once loved then I must say mum is right she's not the kind of girl I should loved or married,,,,,


Kallonsa ayshah tayi da sauri idanuwanta na 6arewa da hawaye ta kalli Khadija tace,

I will never forgive your family for this,,,,

Juyawa yayi a fusace tareda riqo hannun siyama da Mahmud yabar gurin.

Duk yanda taso daurewa kasawa tayi ta durqushe a gurin tareda fashewa da kuka cikin qunar zuciya.

Tabbas ba itaba ko shanty yau zuciyarta ta ta6u da abinda yayiwa ayshah..

Koda suka koma gida gabaki 'daya kukanta sabo yadawo Dan kuwa saiyau ta qara gane kuskuran data tafka.




Kwana biyu duk yarasa gane kansa Dan duk yatuno abinda yafaru saiyaji ransa yayi mummunan 6aci sbd hakanan wani gefe na zuciyarsa ke cewa bai kyautaba koba komai bai kamata ace da aurensa akanta yabarta tacigaba da gantali agari Dole dai ya kawota gidansa ya killace ko kuwa ya sauwaqe mata.


Siyama Kam duk inda hankalinta yake ya tashi sbd ba qaramin ka'duwa tayi da ganin ayshah ba Dan kuwa Bata ta6a tsammanin tanada kyau ko ma'ana ba sbd Jin cewar kullum cikin hijab take,,,indai har tana cikin hijab Deen yakamu da mugun sonta to kuwa yanxu ma data zare hakan bazaiyi wuyaba itakuwa bazata ta6a yarda ko Bari ayshah tadawo rayuwar mijintaba Dan tasan itace da rabon barinsa.


Khadija kuwa rayuwa tayi Mata zafi sbd muh'd daya fito fili ya nuna rashin sha'awar sonta gareshi,
Nan komai ya dagule Mata ta rasa Ina zata saka kanta Dan har ciwo ta kwanta Amma qememe yaqi ko zuwa dubota sbd har cikin ransa yakejin zafin abinda mum tayiwa ayshansa.

Su shanty tafara bi batareda sanin shaikh ba tun suna wulaqantata har shanty ta 'dorata akan network ita kuwa ayshah cewa tayi ba ruwanta kowa tasa ta fishshesa....

Tun Abu na wasa saigashi zance ya bayyana har cikin jaridu cewar matar babban matashi shaikh nuraddeen da qanwarsa sun kar6i number 'daya a fannen shaye shaye..

Ranar da jaridar ta fito kasa bacci yayi tuni ciwo yafara qoqarin kamasa sbd baqin ciki da takaici,

Mum lokacinda taga abinda ke faruwa zubewa zaune tayi tana tsiyayar hawaye sbd inda qaddarar Khadijar tafi muni ita harda maza sha'aninta takeyi.


Tun ranarda jaridar ta fito Bata dawo gidaba sbd tasan mummunan hukuncinsa dazata tarar Sai kawai suka cigaba da sha'aninsu duk wannan sha'anin dasukeyi ayshah Bata ko kallon Khadija bare Bata cika ko amsa maganartaba Dan duk wani Wanda ya danganci Deen ta tsanesa.


Yau zaune suke a garden din gidan suna shaqatawa su duka ukun,,
Shanty da khadeee Sai annashuwarsu suke ita kuwa wayarta take daddanawa duk da kallo 'daya zakayiwa ayshah kasan Sam ta manta da ya farin ciki yake,

Dogon pencil jeans blue ne ajikinta da Pink armless top ta 'daure gashinta tsakiyar kanta Yana lilo...

Gate sukaga anbude hankinsu Yakoma can Banda ayshah dako 'dagowa batayiba taci gaba da kallon wayarta.

Motar Deen khadee tagani ta miqe da sauri tareda Kiran sunansa.

Itadai ayshah banxa tayi dasu duk da taji abinda Khadijar tafada tacigaba da abinda takeyi.


Cikin takun qasaita da burgewa yake takowa fuskarnan a 'daure Amma kyawun fuskar ya Hana aga mummunan 6acin Randa ke tattareda ita bayyana,


Tsayawa yayi gabansu tareda kallon Khadija Rai amatuqar 6ace ya nuna Mata mota.

Turo baki tayi cikin qunquni tayi cikin gida Dan dauko kayanta.


Har ya juya ya tsaya cak tareda juyowa ya kalli gefenta ahankali yaga Sam ko kallo duk Basu ishetaba saima game 'dinta datakeyi...


Kayan dake jikinta ya kalla yaji ransa ya 6aci a qule yace,

You're also coming so just stop that rubbish and get up....

Rintse idanuwa tayi tana qoqarin danne hawayenta zuciyarta na karyewa tace,,,, why is he doing this to me ya Allah,,i loved him more than anything is this the punishment for the mistake I've done,,,he is always the reason for my tears...

Hawayen datake dannewa ne suka gangaro Mata ta miqe zuciya karye zatabar gurin baisan sanda ya riqo hannunta ba sbd yaga hawayen dasuka gangaro Mata Kuma sunyi matuqar tasiri a zuciyarsa ta yanda bazai iya tafiya yabarta ba.

Juyowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasuka ka'da cikin karyewar zuciya tace,

I'm not coming Deen,
Nida Kai yanxu akwai matuqar banbanci duk da ko awancen lokacin akwai banbancin Amma so yarufemin Ido nakasa gani I don't want to repeat dsame mistake now,,

Kaci gaba naci baya so let's just end this now sbd bamai Sona yanxu bamai iya Zama Dani Dan nazama abin kunya,abin gudu abin kyama...

Fixge hannunta tayi ta juya da sauri tabar gurin sbd kukan daya qwace Mata Dan kuwa tabbas tana tausawa kanta duk ranar da shanty ta tattara takoma gurin iyayenta.

Harya shiga mota yaji bazai iya tafiyaba gwara ya 'dauketa ko gidan uwayenta yamayarda ita maimakon wannan mummunar rayuwar datakeyi.


Kuka take ahankali zuciyarta na qara karyewa taji anriqo hannunta a hasale ta 'dago tareda fixgewa Amma ba qaramin riqo yayi Mata ba yafara janta tana tirjewa harya saka mota ya rufe yashiga yabar gidan da shanty tsaye tana hawaye..

Koda ya Isa gidansa dama part biyu ne Sai

Please Login or Register in order to submit comment