Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haryanzun batayi aureba.
Faiza tace gwagwgwo nima inaso inyi aure,abinne yagagara,nikaina narasa gane meke damuna,tunda aurena yamutu nafara zawarci,BA'A TABA CEWA ANASONABA,to taya za'ayi nayi aure???
Gwagwgwo tace dagaske faiza?tsawon Shekara gomafa?
Faiza tace gwagwgwo koda wasa wani baitaba zuwa yace yanasonaba,nikaina INA cikin tashin hankali amma dai inata Addu'a,Allah yakawomani iyakar abin.
Gwagwgwo Hauwa tajinjina kai,tace aiko zama baigankiba faiza,tashi zakiyi kiyi dagaske,ai wannan yazama lalura,sai dai duk satin duniya kaji ana daurama 'yammata da zawarawa aure,kai banda naka?kuma bama rana,tunda bakisa rai,to bakisa rai mana,ai in anazuwa ace anasonkama shine zakasa rai,amma shiru!!aiko faiza zama baigankiba,tashi zakiyi duk inda ake Neman magani kinemeshi,inba hakaba rayuwarki takare azawarci,kwanakifa bajiranki sukeyiba,shekara goma bako kare shege!!!yazoma yace yana sonki,wannan wane irin bala'ine?a'ah!tashi zakiyi kinemi magani,wallahi bakiga tazamaba.
Nan take faiza takarajin hankalinta yatashi,tace inatayin Addu'a sosai.
Gwagwgwo tace aiduk dahaka saikin hada da magani,shima magani airokon Allahne,yanzun zazzabi ko ciwonkai Yakama ki kikishan magani,kice aikina Addu'a?dole kokina Addu'a saikin hada da magani,ki dauka kawai wannan halin dakike ciki ciwone kinemi magani.
Faiza tace gwagwgwo harkinsa naji tsoro,nakuma tuna da maganar yaronnan na dazun,mai tallar magani,dayacemin inada lalura mai wuyaragani,banasofa zancensa yazama gaskiya.
Gwagwgwo tace ai gaskiyar yafadamaki,domin kuwa rashin aure ko rashin masoyi ciwone,kazauna kai arayuwarka bawanda zaice yana donka,Ayyazama ciwo.
Faiza tace wurinwa zan anshiagani?banason fadawa ga halaka ko shirka.
Gwagwgwo tace yaronnan daya kawo magani dazun........
Gwagwgwo tace yaronnan daya kawo magani dazun dakin amsa.
Faiza tace haba dai maganin wannan yaron ba'abinda zayyimani,ganinake kawai duk shirmene.
Gwagwgwo tace:a'a faiza ba'araina magani,komin kankantarsa,dakin amsa,ba'asan inda za'adaceba,nikaina nan Ayace akan hakan,domin kuwa natabayin wani ciwo.

SHAKARA TALATIN BAYA.
Ciwo mai tada hankali,duk Wanda yaganni yasan yaddanake lokacin da inada lafiya sai yayimin kuka,sai an kwantar dani sai antayar dani,komai sai anyimani,alokacin hatta hankalinama soyayi yagushe.
Ace hawan jinine.
Ace sammune.
Duk wani babban Asibiti dakikasani a kasarnan munkwantashi,kudi kuwa sunsha kashi,hatta gonakimmu da kiwukammu daga nawa harna mujina Dana iyayena saida suka kare,sakamakon wannan lalura.
Ayi na hausa,ayi nagargajiya kisauki ciwon bayayi,duk inda akaji mai bada magani tabullu sai ankaini kominnisan garin,Amma inahh!sai Dana shekara goma sha biyar dawannan lalura,gaba dayama har angaji ansama sarautar Allah ido,wasuma suce lokaci kawai akejira.

Wata rana lokacin zafi,akayimin shimfida tsakar gida,duk muduka muna nanwaje ana kwanciyar zafi.
Saimukayi bakon mai bada magani,a can gindin itaciya yadaura lasifikarsa,yanata tallar maganinsa,bayan anyi sallar isha'ine kuwa bana mantawa,ayadda yake tallar maganin yana lissafo lalurori kala-kala,sai naji harda irin tawa,kinsan mai ciwo duk inda yaji magani gani yake za'dace,nace ma mujina a anso Mani wancan maganin da ake tallah.
Saude kuwa NA zaune tace:kajiki Hauwa yanzun wancan maganin kike tunanin zayyimaki?duk kudin da aka kasa na Asibiti bayyiba,da wurin manyan masu magani,sai wannan Dan balo-balo dinne zaki tunanin zayyi maki?asara dai kawai kikeso akara.
Saikuwa akaki bada kudin a ansomani wannan magani,har yakusan tashi,saiga musa mahaifinki,alokacin bayyi aureba.
Nace musa idan kanada kudi ka anso Mani wancan maganin da ake tallah.
Yace to.
NAIRA GOMA GOMA MAGANIN YAKE,UKU ASHIRIN
Haka aka ansomanishi,kullun maganin kananane,kulli uku tsawon kwana uku zanyi amfani dashi,NAYI.
Yau shekara Ashirin da biyar kenan rabon dako makamancin ciwomma yakara tasomin,narabu dashi,Allah yarabani da wannan ciwon sanadiyyar wannan magani,anyi mamaki sosai,don kuwa fara amfani da wannan maganin cikin sati saida nafara yima kaina wanka da kaina.
Don haka faiza duk inda kikaji magani ki amsa kawai,Allah shine mai warkarwa.
Kuma haryau danake baki wannan labarin baikara dawowa garinnanba,bankuma karajin labarin inda wannan mai maganin yabulloba,dama yawon tallarshi yakeyi,mai rabo kuma ya amsa
Faiza tace Tabb!dijan!!Allah mai iko,Allah yasa mudace,toshi yaron dazun daya kawo tallar magani dannan garinne?
Gwagwgwo tace a'a shimadai kawai yazone,kuma ba lallaima yakara dawowaba,haka masu magunguna suke shigowa sutafi,wani har abada baki kara kojin labarinsa.
Faiza tace to Allah yasa mudace
Satinta biyu awannan kauyen,tadawo gida.
(Karka manta mai karatu kana tare da littafin WATA SAKAYYAR......1 na fateema Dahiru Funtuwa Binta whats app number 09162526909)

Ranar wata juma'a da yamma,faiza taje gidansu maman Hafsat,suna kofar daki zaune sunata fira.
Maman Hafsat tace wai yaushe zaki shirya muje wurin malam Shehu dinnanne?yakamatafa,gara kifara sanin halin dakike ciki.
Faiza tace zanje,amma kibari musa rana.
Maman Hafsat tace to shikenan saikin shirya.
Faiza tace aibakisamma abin dariya Abin haushiba,tafiyarnan danayi kauye,kawai INA zaman zamana lafiya,wani mai bada magani yakalleni,yace wai inada lalura,kwata-kwata yaronnan bai wuce Dan shekara gomaba,wai inba shi sadaka zai bani magani,kekinji daukar magana!!
Maman Hafsat tace irin yarannanne wadanda iskoki ke budemasu ido suke bayar da magani ,Aida kin amsa..............
Aida kin ansa.
Faiza tace yakike haka maman Hafsat?wannan aikauce hanyane,duk Wanda zai fada maka lalurar ka batare daka sanardashiba,to aiko yake da Aljanu ,kuma Bokane,saikace banida ilimin islama,sabida wannan matsalar bazan yadda inkauce hanyaba,Allah shiya jarrabeni da wannan lalurar, kuma shine kawai Wanda zai iya rabani da ita,bawani mai aiki da Ajanuba.
Maman Hafsat tace:Aida kintsaya kinji wace lalura zaice tana damunki,shin sihirine koko iskoki?da saiki kara samun haske.
Faiza tace Allah yasauke!aibamma tsaya sauraronshiba,kadama insaurareshi yabatamin tunani,yacemin sihirine akayimani,yasa inzo inta hasashen ko wanene ko wanene,yagurbatamin tunaniba,yasanyamin zargin mutanen dabasuyimin komaiba,Akarshe kuma bazai iya yimin maganin ba.Tunda daikince muje wurin M-Shehu mai Almajirai saimu jaraba aishi malamine.
Maman Hafsat tace to Allah yasa mudace.
Bayan kwana uku kuwa suka shirya sukaje wurin m-shehu,bayan anyi sallar isha'i,suka sameshi adakinsa,yayi masu izinin sushigo.
Bayan sun zauna suka gaisheshi.
Yace:bayin Allah meke tafe daku?
Maman Hafsat tace malam wurinka mukazo,domin ataimaka atayamu Addu'a ,tunda ga Almajirai atare dakai,bamusan inda za'adaceba.
Yace hakane meke faruwato?
Faiza tace natabayin Aure haihuwata hudu da mujina sannan mukarabu,to tunda muka rabu nadawo gida inata zawarci ,shiru haryau shekara goma kenan koda wasa wani Namiji bai taba cewa yana sonaba,tun abin baya damuna harya fara dagamin hankali,duk da inayin Addu'a ammadai haryanzun shiru.
M-shehu yace ikon Allah,shin ba'ataba zuwa ance ana sonki bane koko dai anazuwa dawowane ba'ayi?
Tace ba'ataba zuwa bane.
Yajinjina kai yace to shikenan,wannan duk mesaukine,muji daiko?insha Allahu za'anemosa,ki kwantar da hankalinki,babu abinda yaga gari Allah,kici gaba dayin Addu'a ba'asarewa,nima zansa ayi ayi saukar Alkur'ani agani,saikuma za'ayi sadaka,insha Allahu komai zaizo dasauki,wannan ai abune mai sauki awurin Allah,bakomai Allah yanasane da halin dabawansa yake ciki.
Faiza tace to nawane za'a bada,?
Yace a'a ai abin sadakane kawai zaki bayar,duk abinda Allah yahore,da safe za'sayi wani Abu,ko kuli-kuli ko fanke ayi sadaka dashi,saikuma saukar Alkur'ani danace maki,saikuma wasu magunguna da za'arubuta wasu daga cikin ayoyin Alkur'ani awanke sai ajika maganin da wannan rubutun idan yabushe zansa adaka idan kikadawo zanbakishi,sannan infadamaki yadda zakiyi amfani dashi,Allah yasa mudace,amma muji kamm!za'anemosa.
Faiza tadauki 5k tabashi tace gashinan ayi sadakar dakuma abinda za'anema bahadin magungunan.
Yasa hannu yakarba tare dafadin Allah yakarba,Allah kuma yabiya bukata.
Suka amsa da Ameen,sannan suka tafo gida,tareda fatan Allah yasa anyi asa'a.
Nan sukazo sunaba mamansu faiza din labari.
Tace toyaza'ayi?ainema yazama dole,Allah yakawo maki iyakar abin,aibazan hanaba,dolene mutum yatashi yanema,wannan zama ayya isa hakanan,Allah yasa adace,amma ace kaita rayuwa ahaka,tunda aurenta yamutu bawani aidolene kanemanma kanka mafita.
Ranar wata juma'a,ranar zasu koma wurin m-shehu,faiza tayi wanka tashirya,tafara biyama maman Hafsat.
Tana shiga gidan tace kee!maman Hafsat yau naga abin mamaki!!
Maman Hafsat tace meyafaru??
Faiza tace majalisarnan ta 'yan sa'ido!kofar gidanku!kinga yadda suke kallona kuwa?hada wani cemin saikin dawo!nida har in bar wurin babu Wanda yake daga ido yakalleni,amma shine yau harda yimin magana.
Maman Hafsat tace to aiko inaga wata lalura gareki tasa maza ko kallon ki basayi,ballantanama suce suna sonki,keee!!!wannan Abu dame yayi kama?amma insha Allahu komai yazo karshe!kice har magana sukayimaki??!!
Faiza tace hummf kedai bari,nihar abinma mamaki yabani,tunda nakewucewa tagabansu ko dago ido basuyi......
Faiza tace humf!kedai bari,nihar abin mamaki yabani,tunda nake wucewa tagabansu,ko dago kai basayi sukalleni amma waiyau harda yimin magana,kedai shirya muwuce wurin malamin nan.
Maman Hafsat tadauko hijabinta,basu biya koinaba sai wurin malam shehu mai Almajirai.
Bayan sun zauna suka gaisheshi,yayi masu sannu dazuwa,sannan yacigaba dacewa:
NASA anyi rokon Allah sosai,an sauke Alkur'ani,anyi sadaka,da izinin Allah kuma zamuga hasken abin.
Sannan yacema Faiza kina mafarkin ruwa ko iska?
Tace a'a amma lokacin da inabudurwa nayi fama da irin wadannan mafarkan,da kuma lokacin da inada aure,amma gaskiya yanzun ba nayi,tundayake INA amfani da Addu'oi sosai.
Yace toh!shikenan,ba matsala,kinsan abinda kefaruwa dake?
Faiza tayi saurin dagokai takalleshi,don taji abinda zaice.
Yace gaskiya DUHU ne yagitta maki,kinada tsananin duhu sosai,tayadda babu yadda za'ayi wani yace yanasonki,amma insha Allahu za'aita Addu'a ,arabaki da wannan duhun.
Tace DUHU malam?
Yace e duhune yaguttamaki,amma karki samu damuwa,wannan bawata matsala bace babba,za'ayi maganinta,za'arabaki da ita.
Sannan yadauko magunguna dakuma ruwan Addu'a yamika mata,sannan yayimata bayani akansu,dayadda zatayi amfani dasu,cikin kwanaki hudu,saiki dawo kifadamin yadda kikaji.
Takarba tace toshikenan,sannan sukayi godiya suka tafo.
Ahanya Faiza kecema maman Hafsat,kinji kuma wata matsala,wai duhune yagittamin,shin wane irin DUHU kenan?
Maman Hafsat tace Sihiri ko iskoki yana iyazame maki DUHU arayuwarki,kingadai magana ta tafara fitowako?bayadda za'ayi ace mace kanarki San kowa kin Wanda yarasa ace batada mai sonta,sai dai in lalura ,yanzun inda kin zauna kinata cewa aure lokacine sai dai kita zama ahaka,domin kuwa babu ranar dazakiyi aure,sai ranar da wannan duhun yabarki,shikuma duhun bazaitaba rabuwa dakeba,inba magani kikayiba,ayya zanemaki tamkar ciwone shi wannan duhun,dole saikin nemi maganinsa, Allah yasa munfara a sa'a.
Faiza tace Ameen.
Haka dai rayuwa taita tafiya,tayi amfani da maganin tanajin dadi ajikinta,sai kuma sa rai datake yi naganin ko za'adace wani yace yana sonta,don haka takedan kasancewa cikin farin ciki.
Amma lokacin da batayin maganimma kosarai batayi,hidimar gabanta kawai take.
Amma abin mamaki harya zuwa wannan lokacin saidai saran kawai,ammafa bawani canji,canjinta daya datake lura dashi,shine lallai yanzun idan tana tafiya maza na iya dagon ido sukalleta,amma da bata samun koda hakan,komin kwalliyar data dauka kuwa.
To ganin anakallonta shine ma take karasaran wata rana za'ayi mata magana,amma dai haryanzun babu Wanda yataya.
Duk ranar dasu kaje wurin m-shehu kuwa abinda yake fara tambayar ta,( WANI YAZO KUWA???)
Tana bashi amsa dacewa babu Wanda yazo,amma inasaran in Allah yayadda za'a samu.
Yace Tabbas!aikin yanayin haske sosai,amma nayi mamakin da haryanzun babu Wanda yazo,amma babu komai,za'azo din,ai Allah aka roka,kuma bazai taba bari muji kunyaba.
Haka dai rayuwa taci gaba DA tafiya saidai saran kawai, amma haryanzun babu Wanda yazo,
WATA RANA suna zaune tare da maman Hafsat da kuma mahaifuyar Faiza din,sunata kara tattauna wannan lamari dayake ta faruwa.
Alokacin kuwa wata makabciyarsu tashigo kitso wurin faiza din,tana dai jinsu sunata firarsu.
Har maman faiza nacewa:to aini dama bin malamannan sai ahankali,saidai aitayimaka gafara sa bakaga kahoba,saidai kaita sarai amma bawani canji,kawai Faiza kihakura,kibari, 'yankudinnan dakike samu ya isheki kiyi wata bukatar dasu,amma kita kaima malam yana cinyewa,dakin samu 'yankudi bakida wani buri sayyazakiyi ki kaima malam.
Maman Hafsat tace to mama ausadaka akeyidasu bacinyewa yakeba.
Maman faiza tace yo itama aubukatar sadakar take,yanzun dai ga wankin yaranta can yataru,ko omo batashi,sai yawo suke...
Sayyawo suke cikin dauda,amma yanzun haka batunanin siyen omon takeyiba,tana nan tana tunanin yatayi tahada dubu daya ko Dari biyar takaima malam,dama kinsanyama rayuwarki hakuri kizauna kawai kirike 'ya'yanki,kibasu tarbiyya kihakura kawai duk ranar da Allah yakawo lokacin Aurenki zakiyi,amma wannan bin malaman tadama kanki hankaline kawai,kuma abinda kikeso haryanzun baisamuba.
Jamila wadda faiza keyima kitso tasaka baki cikin maganar,tace mama kuma aibazai yuwu dakuruciyarka ace kaita zama ahakaba,kowace mace dai tana bukatar ace takama dakinta,dukkowace mace data taba zama dakin kanta,bataso tadawo gidansu tatsugunna,dai dai dasati daya indai bada bakunta tazoba.
Inko zawarcine duk wadda tagama idda sotake tasamu tayi aure,amma wannan zama NA faiza aidolenema tatashi tanemi magani,amma kunje wurin malam shehu kuwa?
Maman Hafsat tace aican mukezuwa.
Jamila tace yawwa! Ainasan yanabada wannan taimakon,kuma anadacewa sosai,gashi babu shirka ahidimarsa,shifa in Allah yataimakeka,ka anshi magani wurinsa,CIKIN KWANA HUDU BUKATA TABIYA!! Da izinin Allah bantaba ganin Wanda yaje wurinsa baidaceba,kuma karkarima andade asamu sati daya saikaga bukata tabiya.
Faiza tace sati daya kuma?aini akalla munkai wata biyar kenan muna zuwa wurinsa,amma haryanzun babu wani canji,shiyasa kullun innacemai bawanda yazo wurina har mamaki yakeyi.
Maman faiza tace humf!kudai kukasani!wani ya isa yasauyamaka kaddararkane?komin rokon Allahn da za'ayidai sai lokaci yayi.
Maman Hafsat tace:Allah maman su faiza ana iyayimaka sammu don ahanaka aure,ninamafi zargin tsofon mujinta.
Maman faiza tace bawanda yaisa yacutar dawani saida izinin Allah,kada kuzama kamar bakuda ilimi mana,kuna zuwa islamiyya kuma kunkaranta Hadisin.
(Daga Baban Abbas,Abdullahi Dan Abbas,Allah yakaramasu yadda yace:watarana nakasance abayan Annabi tsira da amincin Allah sutabbata agareshi.
Sayyace yakai yaro lallaini zansanar dakai wadansu kalmomi,kakiyaye dokokin Allah zai kiyayeka,kakiyaye dokokin Allah zaka sameshi agabanka.
Idan zakayi roko karoki Allah,idan zaka nemi taimako kanemi taimako awurin Allah.
Kasani daduk mutane zasu taru akan su amfanar dakai dawani Abu ,bazasu iya amfanar dakai dakomaiba,saida abinda Allah yarubuta agareka.
Kuma dazasu taru akansucutar dakai dawani Abu ,bazasu iya cutar dakai dakomaiba saida abinda Allah yarubuta akanka.
Andauke Alkalumma takardu sunbushe,Tirmuzi yaruwaito,kuma yace Hadisine maikyau ingabtacce.
Acikin wata ruwaya yawanin tirmizi,kakiyaye dokokin Allah,zaka saneshi agabanka,katuna da Allah lokacin dakake cikin yalwa,zaituna dakai alokacin tsanani,kasani duk abinda baisamekaba,dama baikasance zai sanekaba,kuma duk abinda yasameka dama baikasance zai kubucemakaba,kasani lallai nasara tana tare dahakuri,kuma lallai farin ciki yana tareda bakin ciki,kuma lallai tsanani yana tareda sauki.
ARBA INANNAWAWI (ARBA INA HADITH,hadisi nagoma sha Tara.)
Donhaka faiza kiyi hakuri,ko sihirine akayimaki,Aida sanin Allah,saida yaddar Allah sannan sihirin yakamaki,toki dauka kawai wannan yanadaga cikin kaddararki wadda kuma bazata taba sauyuwaba,tunda haka Allah yarubutamaki ita.
Kufa iyakacimmu aikatawane kawai,domin kuwa komai Allah yariga yarubutashi,kuma bazamu iya sauyashiba,Aure-mutuwa-haihuwa idan lokacinsu yayi bamai iya dakatar dasu,idankuma lokacinsu bayyiba duk yadda kakosa dole kayi hakuri kajira lokacinsu,gaugawa bataki baceba faiza,kamata yayi ki tattara zancen aure ki ajiyeshi gefe,duk abinda kikanema kikula da 'ya'yanki kawai kici gaba dabasu tarbiyya.
Jamila tadanyi dariya tace kaji maman faiza,itakuma saitayi zaune ahaka?bata bukatar aure,haba aibazai yuwuba.
WATA SAKAYYAR........1
Sai dare yayi kowanacan tareda mujinta,ita saita kwanta itakadai,aida tausayi,duk kannanta nakwana daazajensu ita sai ita,kuma bama rana,aineman magani yazama dole
Maman Faiza tamike taredafadin,Bari inje induba girkina.
Tana wucewa su Jamila suka fashe dadariya itada maman Hafsat,wato mama taji firar zatafi karfinta tatashi tatafi.
Itakuwa faiza jinsu kawai take,gawani kullutu yazo yatokare mata makogwaro,Wanda tarasa dalilinsa,hawayene kawai kekokarin fitowa daga idanunta tana kokarin maidasu.
Haka takai hardare tarasa abinda keyimata dadi.
Misalin karfe uku nadare tatashi,tayi sallar Nafila,tafara Addu'a.
YA Allah kayayemani wannan kuncin danake ciki.
Allah kasabyamin farin jini.
Allah kabani masoya.
YA Allah kazaba Mani muji NA kwarai.
Allah ka iyakancemin wannan zawarcin.
YA Allah wannan DUHU danake taredashi Allah kayayemanishi.
YA Allah kahaskakani.
YA Allah ta gabas,data yamma.
Ta kudu data Arewa,Allah kafitomin da muji mai Albarka.
Allah kayafe Mani zunubaina, ka yafemani kura kuraina.
Tadauki lokaci tana karanto Addu'oi kala-kala abakinta,daga karshe taita karanta salatin Annabi (S A W ) har bacci yadauketa.
Saida akakira sallar Asuba,tatashi tayi RAKA'A TANUL FAJIR sannan tayi sallar asuba.
Nan taci gaba dazama harrana tafito,dama bata komawa baccin safe,Al-Kur'ani take dauka taita karantawa harrana tafito.
Misalin karfe Takwas nasafe, 'yarta khadija tashigo,bayan tagaisheta tace mama, malam fayayi maganar kudin wata,tun wancan satin bakibaniba.
Faiza tayi shiru,fonta manta da maganar kudin watan yarannan,tace:
To yanzun dai banida kudi,kuje kuzauna nanda kwana biyu idannasamu zanbaku kukai.
Khadija tace to mamammu aikoromu za'ayi.
Tadaka mata tsawa,bacewa nayi kuje kucire kayan kuzaunaba!!kocewa nayi kuje makarantar?kubar zuwan innasamu nabaku kunje,tunda kokunjedai koroku za'ayi.
Kuma kinatsu agida,saura kitafi yawo,iyacidai aikene aita aikenku,kowane yaro yatafi makaranta saiku,wannan ya aika-wannan ya aika,Allah dai yarufamana Asiri.
Khadija tawuce,sukaje sukacire kayan makarantar gaba dayansu.
Faiza tafara tunanin inakuma zata samu kudin dazataba yarannan sukoma makaranta,haka wancan watan saida yayi sati biyu basujeba,Toh!Allah yakawo hanya.
Misalin karfe Hudu NA yamma,maman Hafsat tazo wurin faiza,bayan sun gaisa take cewa:
Dazun INA tafiya baje siyo kayammiya,dayake duk yara suntafi makaranta,saina hadu da malam shehu,zashi gona,yake tambayata kina INA?yaga kinrabu da zuwa.
Nace kinanan lafiya lau,shine yace idannazo wurinki infada maki yanason ganinki.
Faiza tace wallahi maman Hafsat nida nama hakura kawai,wannan dai Abu Allah yayi Mani maganinsa,kumani yanzun konacema zanje wurinsa banida kudi,kumani banaso inta zuwa banda kudi.
Maman Hafsat tace hakane,amma kuma ai ansan halin da ake ciki,taimakamaki kawai zayyi,kidai shirya kije kiji Neman dayake Maki.
Faiza tace toshikenan,nidai banda kudi,hakanan zani.
Maman Hafsat tace kije hakanan din,aidai kinji abinda zaice maki.
Karfe biyar nayi,faiza tashirya tatafi wurin malam shehu mai Almajirai,bayan sun gaisa yace:
Faiza kwana biyu?
Tace malam kuma lafiya lau,nadai rabu dazuwane.
Yace tome yasa?
Tace hakanan malam,abinne naga sai ahsnkali,haryanzun daishiru,nida harma nahakura.
Yace inayimaki bakin kokarina,al-amarinne yayi Nauyi dayawa,gaskiya bantabayin aiki irinnaki Wanda yadauki jinkiri hakaba,idnnayi Rokon Allah to acikin ikonsa ba'awuce sati daya bukata batabiyaba,amma naki gashi haryanzun,meke faruwa dakene?
Shinko zaki iya tunawa,kokin tabayin wani laifi Babba Wanda yasa haryanzun bukatarki bata biyaba?
Faiza tadanyi jimm! Tana nazari,sannan tace gaskiya a iyasanina bazance gawani laifi babba Wanda bazan iya mantawa dashiba,tsakanina da Allah saidai kananun kura-kurai kawai, wadan da baza'arasa kowane bawa dasuba,sannan bana wasa da ibada,koda yaushe kumani onacikin yin istigfari,gaskiya malam babu.
Bayan malam yagamajin maganganunta sosai,sannan yace toshikenan,amma yaya mu'amalarki da mutane?baki taba cutar wani ko wataba?
Kinsan kana iyayin wani laifi,ko kayima Allah kokuma bawansa,sai Allah yahukuntaka tun aduniya.
Misali:keko kintabayima Allah wani laifi ko kin cuci wani bawansa,sai yakeyimaki hukunci da abinda kikafi so,yahanaki mujin aure sakamakon wannan laifin?
Faiza tace gaskiya babu,INA zaune dakowa lafiya.
Malam yace: TOYAYA KIKA ZAUNA DA TSOFON MUJINKI?????????
Nan da nan daji gabanta yafadi,domin koda wasa bataso taji anyimata maganarsa,domin kuwa bazan dadi tayi dashiba,kaddaracema tasa harta iya Tara 'ya'ya Hudu dashi,wadanda gasunan kuma yasakarmata dawainiyarsu,nan danan taji idanunta sunciko da hawaye.
M-shehu yalura da hakan,yace kifadamin yaya kikayi zamantakewa tsakaninki damujinki????kifada Mani kada kiboyemani komai,domin asan ta yadda za'abulloma al amarinnaki.
Karshenta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment