Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai wani zunubi dakika taba dauka,Wanda Allah yakeyimaki hukunci da hanaki mujin aure,azaman takewardakikayi da mujinki.
Faiza tabude baki tace.
SUNANSA GARZALI. Munyi zaman aurene dashi,irin aurennan da akecema ,
BAZA FITA HAKKINABA NI KUMA BAZANYIMAKA BIYAYYABA!!!!!
Ahaka mukayi rayuwar zaman auremmu.
Hakika zanfada maka irin zaman da mukayi da GARZALI,zama NA rashin fahimtar juna.
Farkon Al-amarin dai shine,munyi.....................
Is'haka neyashigo gidan da kuka,Dan dan fauzane,yayan khadija,yana kuka yana fadin,mama kizo ga khadija can antafi da ita Asibiti,batada lafiya!!mamammu mutuwa zatayi!!
Faiza najiyo muryarsa tayo waje dasauri,tatarbi ishaka,tace meke faruwa??
Yace kgadijace ankaita Asibiti asume,batasan inda kanta yakeba,sai jini yake zuba ajikinta.
Faiza tace hatsari tayi?
Yace a'a kizo muje.
Cikin sauri kuwa faiza tabiyo bayansa don ganin meyasamu 'yartata.
Kwance tatarar da khadija,batasan Wanda kekantaba,sai jini daya bata mata kafafuwa.
Afirgice faiza tace meyasameta!!?akace kuntafi Asibiti?
Mama tace tana kuka,daukota kawai akayi daga waje a some,wanine yayimata fyade.
Faiza tafasa wata gigitacciyar kara,tareda fadin,mama waye shi!!?
Mama tace bamu saniba kawai dai dauko mana ita akayi ahaka,bamusan Wanda yayimataba,yanzun dai jira muke asamu tafarfado,sai asanyamata ruwan dumi,inya kama sai atafi Asibiti,daharmun dauketama zamu tafi,saikuma muka tuna bamuda kudi.
Faiza kanta juyawa kawai yake,cikin sambatu tana fadin.
Waye wannan?waye shikuma ya aikata mata haka?khadija ta! Inna lillahi wainnailaihirrajiun,takara fashewa dakuka,tareda girgiza khadija,datake kwance akan tabarma.
Tana fadin zadai tatashiko?bakasheta akayiba?
Mama tace kiyi hakuri faiza zata tashi,debo ruwa akara yayyafa mata.
Cikin rawar jiki tadauko ruwan sanyi tamikama mama,aka kara yayyafa mata,amma shiru.
Wani irin tashin hankaline yakara ziyartar faiza,shindamema zatajine?
Datalaucin daya ishesu zasuji koko dawannan mugun Abu dayasamu diyarta?koko da matsalar datake tareda ita tarashin aure?
Batasan lokacinda takara fashewa dawani matsanancin kukaba,gashi basuda kudin dazasu kinkimeta sukai Asibiti,inma sunje ana iyacewa saisunzo da dansanda,to duk inasukaga kudin dazasuyi wannan cuku-cukun?
Don haka kawai duka hakura dukaita iya bakin kokarinsu,sai zuwa dare sannan tafarfado.

Bayan tasamu kanta sosai,ake tambayarta waye yayimata haka?
Tafada masu....
Tafada masu,wanine nan anguwarsu,aiko adarennan,faiza tayi nufin taje tasameshi,hardakin dasuke kwana,amma akafada mata bayanan.
Nan take tambayar samarin dakin,sukace mata bazo kwanaba yau.
Tace:towa yasan inda yake yanzun?
Wani yanakwance cikin barci yace: wai surajo ake nema?
Faiza tace e kokasan inda yake?
Yace dazundai kafin magariba munhadu dashi yake cemin idan inada kudi inrantamai zai tafi legos,nacemai banidasu,sayyace zaitafi yanema awani wuri.
Sai daya daga cikin samarin dakin yace aiko yasamu kudin nan bazai samu tafiya yauba,saidai dasafe yayi sammako,karshenta dai yana shagon baya,dakinsu kamisu.
Faiza tace inane dakin?
Yace meyafarune,dai dai lokacin dayake tasowa daniyyar zairakata.
Tace nemansa nake ruwa ajallu!!
Yace lafiya daiko?
Tace 'yata zankarbarma hakkinta nalalata mata rayuwa dayayi,tafada masa abinda yafaru.
Yace kaih!kaih!!kaih!! To Allah koyasa bai guduba,don Tabbas naji yana cewa Lagos zashi.
Suna zuwa kofar dakin yayi sallama,sannan yace subudemai shigowa zayyi.
Bagaddama suka budemai,yanashiga yace mata gayacan!!!
Tace Alhamdulillahi! Fito!!
Yawani tokare yana fadin lafiya!
Wanda yarakotadin yace a'a bazaifitoba,gashinandai munrike makishi,donyana iya fitowama yaruga,nan zamu tsaremaki shi harkije kinemo 'yansanda.
Nanfa samarin dakin sukaita lafiya-lafiya!!yabasu labarin abinda yasa take nemansa,duk kuwa suka bada hadinkai akahanashi fita,don inyafita baza'akara ganinsaba,aiko suka sakashi atsakiya,don kada yagudu.
Duk dahaka hankalinta baikwantaba saida takarasa kannanta maza sukazo donsu kara tsarematashi kafin safe.
Tunda sassafe kuwa tafara Neman mafita,inda zata samu rancen kudi,domin tamikama 'yansandashi.
Tarasa yadda zatayi,saita dauko wasu Turmin zani dataketa ajiyarsa,daniyyar in Sallah tayi zata dinkama yara,to bayadda zatayi,wannan zani tadauka tatafi bin gidajen dillalai.
Bayan tatafi mama nazaune da yarinya agabanta,sukajiyo sallama,cikin hanzari dakuma mamakin muryar dataji tana sallama agidan,tamike tsaye,tare da tunanin shin meyazoyi?waya sanar dashi?
Yana shigowa abinda yafara fadi:
Khadijar ce anan kwance?meyasa ba'akaita Asibitiba?
Mama kuwa mamaki ma gaba daya yahanata bashi amsa,sai cewa tayi waya fada maka?
Sannan yace Inakwana mama?
Tace lafiya lau inakaji wannan labarin?
Yace fadamin akayi,shiyasa nayi sammako nazo,amma dai yanzun afara kaita Asibitin,sannan indawo inyi binciken wane DAN ISKANNE YAYIMA 'YATA HAKA!!!!!wallahi sai inda karfina yakare!!saina kwatar nata hakkinta!!!
Dai dainan maman Hafsat tashigo gidan,tana salati,tace kai jama'a!wannan wane irin abune?Ashe haka tafaru?sai yanzun nakeji!
GARZALI yace aiba yadda zanyiba!!karamar yarinya kamar wannan!!aisai inda kargina yakare!!adai kaita Asibitin adawo,sainayi kararsa,sai anyankemai hukuncin dayahau kansa!!!

Maman Hafsat tace Tabbas!!haka yakamata,aidolenema adauki mataki!saboda gudun kara faruwar haka anan gaba,Faiza tagane yaron kuma tasa antsare matashi,lallai wallahi kadage sai ankwato mata hakkinta!
GARZALI yadauki khadija yafita da ita
Maman Hafsat tace waye wannan???
Maman faiza tace humf!Babansune,kinganshi,nigaba dayama mamaki yarufeni,koya akayi yasan dawannan abin?kinganni nayi tsaye inakallon ikon Allah,mutum kamar daga sama.
Maman Hafsat tace labarin duniya aibaya boyuwa,yanzun haka wani yaje yafada masa.
Maman faiza tace ikon Allah bari nabishi muje Asibitin,mama tafita suka wuce.
Maman Hafsat tana zaune tana jiran dawowar faiza.
Kimanin mintina goma shabiyar saiga faiza tashigo,tana fadin maman Hafsat nasamo kudin!!aiyyau wannan mutumin sayya gane kuskurenshi!!!karamar yarinya kamar khadija zaka lalata!!
Karamar yarinya kamar khadija zaka lalata!zaici ubanshi kuwa wurin police!!
Maman Hafsat tace aininamaga kokarinki,dabaki fara tsinkamai mariba!komin girmansa,tunda bayada gaskiya,aiyau zaigane kuskurensa.
Faiza tace humf! Kedai bari,INA maman take?
Maman Hafsat tace sunwuce Asibiti.
Faiza tace ya'akayi?jikinnatane yarude?INA suka sami kudin?
Maman Hafsat tace kedai bari,abin mamaki,Babansune yazo,Ashe har mota gareshi?amma baya kulaku,Ninagama ajikinsa bawata alamar wahala,nifa nadauka talaucine yasa baya kulaku,aiko yazo ranshi abace,yadauki 'ya yatafi kaita Asibiti.
Faiza tace kenifa banganeba,wane Baban kikenufi?
Maman Hafsat tace GARZALI mana.
Faiza tace GARZALI?meyakawosa?waye yafadamasa???
Maman Hafsat tace oohoo!!nimadai zuwa nayi nataddashi.
Ran Faiza yayi mugun baci,tace maman Hafsat bari naje Asibitin,Fuuuu!tafita gidan cikin sauri.

Tana isa Asibitin kuwa tatarar dashi,yanata kumfar baki,akan sayya dauki mataki akan Wanda yalalata rayuwar 'yarsa.
Yana ganinta kuwa yace:yauwa Faiza!INA Wanda yayima yarinyarnan fyade?ance kinsa anrikeshiko?fadamin INA yake,kokuma muje kinuna manishi,in makashi a Coute bada wani bata lakaciba!!don yau................
Tace Dakata da Allah!kai harkanada bakin dazaka iya fadin wannan maganar?kai Asuwa?wane karambanima yasa kadaukomin 'ya kakawota Asibiti?sanyaka nayi??
Wallahi Garzali akan wannan maganar ta fyade,baikamata kana saka bakinkaba!duk waye yajawomana hakan?dukkaine,nayi nadamar kasancewarka amatsayin uban 'ya'yana.
Annabi (S A W ) yayi gaskiya,dayace kazabama 'ya'yanka uwa tagari,ta ishi hannayenka,to kamar hakanema idan uwa tazabama 'ya'yanta uba nagari ,wallahi Garzali indakai mutumin kirkine,da wannan matsalar bata samemuba,Kaine musabbabin haddasamana ita!kai yanzu atunaninka har wani mataki zaka iya dauka?bakaji kunyar fadin wannan maganarba!nikadai yakamata inbugi kirji ince zandaukarma 'yata mataki bakaiba!kuma kaikaje kayi tunani da kanka,kaga abinda kake fadima yadace yafito daga bakinka!!
Garzali!kafita harkar 'ya'yana!!dama bakomai kakeyimasuba!!sai wannan zaka kwaso jiki kace kazo karbarma 'yarka hakkinta!dalilinmeto??asunan kanawa?
Mama tataso tace ya isa hakanan Faiza,kibarshi ya karbarma 'yarshi hakkinta,Wanda dama kema kudurinki kenan,abinda yawuce yawuce kawai.
Garzali yace:aiduk duniyarnan bawanda ya isa yahana insa ahukunta wannan la'anannen daya lalatama 'yata rayuwa,mama kibarta kawai,nibazan fasa abinda nayi niyyaba,kuma natabbata itama tanaso akwatoma khadija hakkinta,ninedai data tsana,shine zatazo tayi wata burgar banza da wofi,kuma natabbatar abinda keraina itama shine yake aranta.
Tace karya kake garzali!bazamu taba hada kuduri daya nidakaiba!!hanyar jirgi dabam ta mota daban!!kuma nice da nasara akanka,bazaka taba cimma kudirinkaba!! Ada nayi niyyar inkwatarma 'yata hakkinta nikadai,amma tunda kasa baki kudurinka bazai taba cikaba!!
Tana gama fadin haka tabar Asibitin dasauri.
Dakin samarinnan kawai tanufa,tana zuwa tace:
Surajo kasamu kudin motar jiya dakayi niyyar guduwa?
Yace bansamuba.
Tace kukwanceshi.
Samarin sukace yaza'ayi mukwanceshi?muna kwanceshi guduwa zayyi.
Tace Ku kwanceshi kawai bashi ya aikataba,sannan tamikamai kudin dasuke hannunta,tace gashi kayi maza-maza kagudu,kada kabari akamaka,duka kudin data saida Atamfar nan tamikamasa.
Sannan tawuto gida cikin wani irin yanayi,data kasa gane meke damunta,tana zuwa tafada daki taci gaba da kuka mai tsuma zuciya.
Maman Hafsat ce tashigo gidan,tasameta tafara bata hakuri.
Itadai kuka kawai take,takuma kasa cemata komai,suka dade ahaka maman Hafsat nata bata magana,ita kuwa kukanta kawai takeyi.
Zuwacan Garzali tashigo gidan yana fadin:
Amma gaskiya faiza kinbani....
Amma gaskiya Faiza kinbani mamaki!ya akayi kikasa akasakesa?
Maman Hafsat tayi saurin kallon faiza tace wakikasa akasaki?
Garzali yace yaron dayayma khadija fyade,waishine tasa akasakeshi!bayan tayi kokari tasa anrikematashi.
Maman Hafsat tace garin yaya hakan tafaru faiza?Guduwafa zayyi yanzun shikenan yaci bilis!kinkausan abinda kikayi? 'Yarkicefa za'akwatarma hakkinta.
Garzali yace baici bilisba! Wallahi saina dauki tsatstsauran mataki akansa!
Maman Hafsat tace bayan yagududin? Gashi bata fadamana kodan inabane.
Garzali yakalli faiza faiza yace gaskiya baki kyautaba!kifada mana kowayeshi,kokuma inazamu sameshi?kokuma harke saina dauki mataki akanki!!
Tace bazan fadaba!!yaci bulus din!!saboda baka isa muyi tarayyadakai wurin kwatoma 'yata hakkiba!bazan taba yadda ra'ayinmu yazo daya nida kaiba!!kai harkanada bakin dazakace kazo karbarma 'yarka hakkinta?kai hakkokinnata nawane katake?
Maman Hafsat tace faiza yanzun balokacin wannan maganarbane, 'yarkuce 'yarshice,wannan iftila'i yafaru akanta,tunda har Allah yasa yazo kamata yayi kuhada karfi kukwatarma yarinyarnan hakkinta,duk wani fushi dakikeyidashi,kamata yayi ki ajiyeshi gefe,Ku tunkari wannan matsalar gaba daya kedashi.
Faiza tace maman Hafsat bazaki fahimci komaiba,bakisan miye tsakanina dawannan Azzalumin mutuminba!!iyakar abinda kikagani kawai kikasani.
Barin danayi akasakeshi shine daidai hukuncin daya kamata inyima garzali,domin yakara tabbatarma dakansa cewa narabu dashi har abada,kuma bazamu taba hada ra'ayi daya nidashiba!
Sannan takalleshi sosai tace: kai baka dace daka zama uban 'ya'yanaba! Mace mai kyawawan halaye da kyawawan dabi'u da ilimin Addini da aiki dashi,bai kamata ace ta auri muji mai mugun hali da jahilci da mummunar dabi'a irinka!!
Kai yanzun don har anyima 'yarka fyade kanada bakin dazakazo kace zaka karbar mata hakkinta?kai harka manta dacewa munanan halayankane suka jefa 'yarka ahalin datake yanzun ,Garzali kaje kayi tunani da kwakwalwarka kaga matakin dakakeshirin dauka akan Wanda yayima 'yarka fyade yadace daka daukeshi?
Dai dainan wasu hawaye suka zubomata,tace: lallai Annabi ( S A W ) yayi gaskiya dayace kazama yayaka uwa tagari,to kamar hakanema idan uwa tazabama 'ya'yanta uba nagari.
Nayi nadamar kasancewarka amatsayin uban 'ya'yana! Kada kamanta Garzali abinda kayine..............
Dai dainan kuka ya kwacemata,takasa idasa fadin abinda yake bakinta,tashige cikin daki dasauri tana rizgar kuka.
Nan tabar Garzali tsaye cike dajin haushin daya kasa fahimtar inama maganar Faiza ta dosa?har a lokacin ranshi abace yake,kuma cike da alwashin sayya dauki matakin dayayi niyyar dauka akan Wanda yalalata rayuwar khadija,lokaci daya kuma haushin faiza yakara turnukeshi,domin kuwa talalatamai wannan shirinnasa,yanzun inazaiga wannan yaron?bayan tasa yagudu.
Cikin fushi yace: baki isaba Faiza!kamar yadda kikasa yagudu haka zaki nemosa,kokuma duk hukuncin danayi niyyar dauka akansa insaukeshi akanki!!!don wannan varazanar banzace kikeyimani!!!
Sannan cikin. Fushi yafita yabar gidan.
Maman Hafsat natsaye tana kallon ikon Allah,cike da mamakin wannan Al amari dayake faruwa,shinma wai duk menene musabbabinsa?
Ahakadai tashiga dakin da Faiza take,zaune tasameta tana aikin kuka,zuciyarta cike da kunci da bakin ciki.
Zaunawa tayi Daf!da ita,tace Faiza gaba daya wannan Al amarinnaku nakasa gane kansa,duk daban taba ganin mujinkiba,sai wannan karon,amma hakan kawai yanunamani cewa lallai bakuyi zaman dadi da fahimtar juna atsakaninkuba,kuma hakan yatabbatarmin dacewa,koda Garzali yanada laifi a zamantakewar da kikayi dashi abaya to lallai kema kina dashi.
Faiza tadago kai takalketa tace: bazaki taba fahimtar halin wannan Azzalumin mutuminba!gani daya kadai dakikayimasa,bai isa yasa kice kin tantance halayensa da dabi'unsaba!
Maman Hafsat natsani Garzali!! Bana sonsa! Banason duk wani Wanda yake sonsa,tun lokacin Dana aureshi natsanesa!
Maman Hafsat takara kallonta cike damamaki,tace: tun lokacin dakika auresa kikatsaneshi? Meyasa hakato? Kintaba zama da kishiyane?
Humf! Faiza tayi ajiyar numfashi,tareda share hawayen dasuka jikemata fuska,sannan ta sassauta muryarta tace:
Banzauna da kishiyaba,Asalima saubayan barabu dashi sannan yakara aure,nasanki da zargi,don kada kiyi tunanin ko kishiyace tarabani dashi,Toni banzauna da kishiyaba,dagani saushi mukazauna,har Auren yamutu,sannan kuma yayi watsi damu,yasakarmin dawainiyar 'ya'yansa, khadija bata sanshiba,don miye yanzun don wani iftila'i yafadomata zaizo yabugi kirji yace yazo karbar mata hakkinta!shi hakkokin nata nawa yatake?
Maman Hafsat tace kuma da alama yanason 'ya'yansa,tunda dibifa yadda ya hakikice akan wannan al'amarin,anya kuwa faiza bawani sihirin akayimasa akarabashi da 'ya'yansaba?
Faiza tace bantaba zargin hakanba,kawaidai mugun haline irinnasa,don bakiji labarin yadda nazauna dashibane.
Maman Hafsat tace fadamin yaya kikazauna dashi?
Faiza tace hakika nayi zama da Garzali irin zamannan barashin fahimtar juna,zamane Wanda bazaka fita hakiinaba nikuma bazanyimaka biyayyaba,hakika yanzun nan zanbaki labarin irin zaman damukayi da Garzali.
WATA RANA................
Sallamar maman Faizace takatsemasu firar dasukeyi,don haka sukayi saurin amsawa gabaki dayansu.
Cikin fushi maman Faiza tashigo,taredayima faizar fada,dacewa:
Wannan wane irin haukan banzane! Yaya zakisa asaki mai laifi,al halin laifinnan keyayimawa!wannan wace irin zuciyar babzace gareki! Kina ganin hakan dakikayi shine zaisa ran Garzali ya baci! To wallahi koda ranshi yabaci naki sayyafi nashi baci? Tayaya kikeso dole laifin da ubansu yayi maki kuma kihuce akan 'yarsa?to kisani wannan bawata mafita bace kikafito da ita maibullewa! Kullun Addu'a muke Allah yakarkato da zuciyarsa akan 'ya'yansa,kikasani ko dalilin hakan Allah yajuyo da hankalinsa akan 'ya'yan.
Nan dai tarufeta da fada,ita dai faiza banda kuka da kuncin da takeji acikin zuciyarta,ba abinda takeji,don kuwa harlikacin batayi nadamar wannan mataki data daukaba,domin gani take wannan shine dai dai abinda zatayima Garzali,donya dandani bakin ciki da takaicin dashi yafara jefa rayuwarsu aciki,kuma yakara tabbatarma dakansa cewa ta tsaneshi,kamar yadda tatsaneshi tun afarko,don haka koda wasa bazata taba yadda suhada ra'ayi daya ita dashiba.
Nan dai maman Fauzar taitayimata fada,ta inda takeshiga batanan take fitaba,dinta nunamata irin kuskuren data tafka akansawa datayi akasaki yaron dayayima khadija fyade.
Maman Hafsat kuwa kasa cewa komai tayi,don gaba daya ita kantama yakulle,wani lokacin taga laifin Faizar,wani lokacin kuma tace ayyakama ayimata uzuri,domin kuwa ita tazauna da Garzali,ita tasan ukubar daya ganamata,wadda takasa mantawa da ita,tasa harta dauki wannan matakin.
HAKIKA ZANSO INJI WANNAN LABARI NA RAYUWAR AUREN FAIZA DA GARZALI
Haka dai taita tunani,daga karshe takomaba maman Faiza hakuri.
Awunin Ranar haka Faiza tawuni cikin kunci da bakin ciki,Wanda azuciyarta har takecewa inama mutuwa tayi da irin wannan tashin hankalin,kuka dai tayi shi harba iyaka,gabakin cikin ketama 'yarta budurci da akayi,ga Garzali kuma yazo yakara bata mata rai,don Tabbas! Dabaizoba saita karbarma 'yarta hakkinta amma zuwansa yalalata mata wannan kudurin,yanzun shikenan Wanda ya aikata wannan laifin yasha? Yatafi abanza kenan?
Amma dukda haka idan tatuna yadda Garzali yake hakikicewa akan sayyabima khadija hakkinta,tatuna yadda ranshi yabaci,yadau zafi,haryana rantsuwar sayyasa anhukunta yaronnan.
Idan tatuna cewa tawargazamai wannan shirin,saitaji farinciki yamamaye zuciyarta,hartadanyi dariya,takara godema Allah dabaisa Garzali yayi nasarar kama yaronnanba.......
Tasandai ko banza shima ta Dan danamai wani bakin cikin dabazai manta dashiba.
Domin kuwa tatsanesa!tatsani farin cikinsa! Haushinsa takeji!!
Garzali yazo yagama fadansa da kurarinsa yabar garin,domin cewa yayi baiga amfanin zamansaba.
Azuciyar Faiza tace:Allah yasa kayi hatsari ahanya kamutu kowama yahuta! Insan cewa 'ya'yana marayune kotallafi Marika samu.
Abangaren maman Hafsat kuwa,azuciyarta tana kara rayamata cewa lallai akwai abinda kefaruwa gameda Faiza,amma tafi danganta abin dacewa sihirine akayimata,domin inba sihiriba waye zaiki 'ya'yansa? Koda sunyi fada tsakaninsu baikamata ace yawatsar da 'ya'yansa ba,kamar yamanta dasu,anya kuwa wannan Al-amarin babu sammu acikinsa??
Gashi kuma Faiza tacika taurin kan tsiya! In ance tanemi magani saitace shirkane,duk inda akace game magani ta amsa sai tace Bokane,ninama rasa yadda zanyi da ita,tunda NA malan shehu dinnan abin yakici basaimuje wani wurin ba,amma taki yadda.
Amma dai nasanyadda zanyi.
Saitadan jima tana tunani,sannan tace yawwa!! Kauyensu Faiza zani! Ainasan garin muntaba zuwa tareda ita,yaronnan mai magani daya taba ganinta yace tanada lalura shizanje innemo duk inda yake, tun lokacimma data amshi maganin dayanzun anwuce wurin! Tatsaya kinibibin cewa ai Bokane.
TONI NAYI ALKAWARIN DUK INDA YARONNAN YAKE ZANNEMESA IN'ANSAMMATA MAGANI AWURINSA.
KODA KUWA YARON ZAI KASANCE BA MUTUM BANE!!!!!!!
Misalin karfe Hudu nayamma,Faiza nazaune,akayi sallama,akace ana sallama da Faiza.
Tasanya hijabinta tafita. Malam shehu tagani,tasandai yazone yayi masu Allah kyauta,bayan sungaisa,tace bari nadaukoma abinzama.
Yace a'a kibarshi kawai.
Sautashiga gida takira maman ta,m-shehu yayi masu Allah yakyauta,tareda jajantamasu.
Maman Faiza ymtayimai godiya sosai gameda kokarin dayakeyi akan Faiza NA Adduoi,sannan tashiga gida.
Har lokacin idanun faiza juwur suke,tana digar da hawaye lokaci zuwa lokaci.
M- shehu yace jarrabawace,komai dakike gani yasamu bawa kaddarace,kuma musulmi kedauka.
Tabbas indai kace kayi imani da Allah tokadingi gamuwa da jarrabawa kenan arayuwarka,saidai muyi fata da Addu'a Allah ya jarrabemu da Kaddarar da imaninmu zai iya dauka.
Yaci gaba dacewa rannan dakikaje wurina,kinso kifara bani labarin yadda kijazauna da tsofon mujinki,sai kuma wannan kaddara tafaru,Wanda yayi sanadiyyar tafowarki gida baki fadaminba, to aibafasawa za'ayi ba,idan komai yalafa hankali yakwanta kisamu lokaci kizo kifadamani don musan ta yadda zamu bulloma Al amarin.
Tace to shikenan malam insha Allahu zanzo,dai dai lokacin datake kara share wasu hawaye dasuka gangaro a idanunta.
( mai karatu kada kamanta kana karanta littafin WATA SAKAYYAR.....1
Wanda Fateema Dahiru Funtuwa Binta ta wallafa, gamai Neman marubuciyar kai tsaye domin bada shawarwari ko wani karin bayani zai iyasamuna tawannan Number. 09162526909 )
Malam shehu yace sai hakuri,Allah yakiyaye gaba,amma dai duk dahaka Faiza kinyi kuskure babba da kikasa akasaki yaronnan,kowannan kadai yayta sanyaki bacin rai domin baki bima 'yarki hakkinta ba,kuma bakiyima kanki adalciba,idan har anasakin masu laifi aikinga baza'adaina aikata laifinba,kowama sayyayi abinda yaga dama kenan.
Faiza tace gaskiya nayi niyyar inbima 'yata hakkinta amma tunda babanta yashiga cikin maganar nan dolene inhakura da ra'ayina,kodan ganin nashi kudurin baicikaba.
M-shehu yace tome yasa hakan??
Faiza tace Saboda natsanesa!banason farin cikinsa kamar yadda bayasonnamu! Saina wargaza tsarinsa kamar yadda yawargaza tsarin rayuwarmu! Saina sanya Mashi kunci da bakin ciki azuciyarsa kamar yadda yakeso ya dawwamar damu acikin kunci da bakin ciki arayuwarmu!!!!
Yabarmin 'ya'yansa baisan cinsuba,baisan shansuba,baisan suturarsuba,baisan ciwonsuba,duk wata dawainiya da uba yakamata yayima 'ya'yansa bayayi.....
Yasakarmin dukkan wahalarsu,nikuma bakarfi gareniba.Hakika WATA SAKAYYAR SAI A WURIN ALLAH!!! Allah ya isa tsakanina da Garzali!!
Dai dainan takara fashewa da kuka,sannan tana fadin,hakika malam idanna fada maka yadda bayi zaman aure dashi, dawahalar danasha nida 'ya'yana awurinsa,saika tabbatar dacewa matakin Dana dauka akansa yayi dai dai dashi,saika yadda dace duk wata hanya dazanbi domin in muzgunamashi itace tafi cancanta dashi daga gareni.

ALHAMDULILLAH!
Anan nakawo karshen littafi nadaya,mai karatu biyoni acikin littafi NA biyu donjin yadda zata kasance.
Shin maman Hafsat zata samu nasarar haduwa da wannan yaronnan mai magani???
Wadanne irin kalu abale zata fuskanta awurinnemansa???? Tunda dai munsan cewa Gwagwgwo Hauwa ta fadama Faiza cewa masu magani shigowa kawai kauyen suke sutafi,ba lallaima kakarajin duriyarsuba.


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment