Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanadayyi dasaura.
H-Tani tace gata kyakykyawa barakallah,niko jummai danaga yarinyar nan ,harkinsa nayi sha'awar kibani ita,intafi da ita tanemo maki abinduniya.
Mama jummai tace anya!gaskiya bazan baki itaba,don itanake gani inajin dad'i,sauran 'yan uwannata duk ba zuciya.
H-Tani tace aiyara yanzun duk sai ahankali,saidai fatan Allah yashiryamana,to aike dama jummai irin wad'annan masu zuciyar su akesawa sunemi kudi.
Mama jummai tace to aikuma karatunfa?
H-Tani tace yome akedakaratu jummai?duk bagamasu takardunnan munaganiba,kaidai katashi kanemi nakanka kawai,aikine zannema mata kukanku kunhuta dawannan wahalar, kinsan Allah jummai don dubu ashirin dubu talatin saidai kiga anayomaki aike dasu.
Mama jummai tace Allah Hajiya Tani!!?
H-Tani tace to kedai zauna ainad'aka bayyi kallon nawajeba,dazaki shiryata kibani ita intafi da ita Kano,saikinyi mamakin yadda zata zama da abinda zata samo.
Mama jummai takara nanatawa da karfi, DUBU TALATIN fanajikince!
H-tani tace kwarai kuwa,barima kiga infara baki wani Abu,nandanan tazage Jakarta taciro rafar kudi 'yan hamsin-hamsin harna dubu goma,tamikama mama jummai.
Jiki narawa mama jummai takarba kudin taredafadin,Al'amarin nan nakifa Hajiya tani dagaske ne.
H-tani tace aah!yodafa,kedai kinji shawarar danabaki,don haka kishiryata inzan koma muwuce.
Mama jummai tace to yaushe zaki koma?
H-tani tace ieetoh!!nanda kwana biyu.
Mama jummai tace saidai matsala ta daya,wannan saurayinnata Hashimu ,idan yaji bazai bariba.
H-tani tace yo waye kuma hashimu?
Mama jummai tace saurayintane Wanda zata aura aiko anyi Alkawarin aure dashi tun mahaifinta nada rai ,bakiga irin dawainiyar dayakeyimanaba,lallai natabbatar bazai so tafiyar nan tataba.
H-tani tace yoshima idan yaga tacanza tayi kyau zaifi kara sonta,kuma 'yarki takara farashi.
Mama jummai tace hakane kumafa,Allah yataimaka nasan yadda zanyi dashi.
H-tani tace ahtoh!!kidayyi shawara.
Haka suka tsaida maganar cewa Mariya zatabi Hajiya Tani Kano acewarta zata nemammata aiki Wanda zata rika samun kudi sosai.
Mama jummai taja kunnan Mariya akan kadatasaki tasanar da Hashimu abinda kefaruwa,harsai bayan tatafi,itatasan yadda zata gayamasa.
Washe gari ana igobe zasu wuce Kano,Hashim yazo wurinta,duk da mama taja kunnanta akan kadatasanar dashi saida tafada mai, amma saice masa tayi unguwa kawai zata tayi sati biyu.
Hashimu yace har sati biyu Mariya?to Allah yadawo dake lafiya,kinsan Alkawarin DA nakeso kiyimani?
Tagirgiza kai.
Yace don Allah Mariya duk inda kikaje kitsare kanki,kitsare mutum cinki,karki yadda dasamarin bariki,nabaki amanar kanki harkije kidawo,nikuma inanan zantayimaki Addu'a kice kinyimin wannan Alkawarin.
Tace Hashim nayi maka Alkawari da duk rintsi duk wuya zankare kaina da mutumcina,bazan ta'ba bari wani mummunan Abu yasameniba,duk inda kuma natafi ,kana tareda ni acikin zuciyata,in sha Allahu yadda natafi haka zandawo maka,alkawarine nayi maka,hashimu INA SON KA,inasonka sosai,daidainan tasa tafukan hannayenta tarufe fuskarta......................

********* ********* ********** *******

Firgigitt!!!hashimu yafarka daga nannauyan tunanin daya tafi,nandanan hawaye suka 'kara kwararowa daga idanunsa,cikin sauri yatashi zaune,yaga dakin babu kowa.
Ashe abokannasa suntafi,atunaninsu barci yasamu,lokaci guda yakara kallon agogo,karfe goma sha d'aya da mintuna ashirin da shidda,ya mike dasauri yayi waje ko takalmi babu akafarsa.
Kaitsaye hanyar gidan su Mariya yanufa,yana tafiya kamar anzaremai lakka.
Mutane ne tunjum awurin,hakan shi yakara tabbatar mai dacewa lallai yau yarasa Mariya ,kanshi yaci gaba da juyawa,yana ganin sama nakomawa kasa,yana kallon kowa badaidaiba,hatta hayaniyar da akeyi awurin sama-sama yakejinta.
Daidai lokacin dayaji ance FATIHA!! Alamar andaura auren Mariya dawani bashi ba,saidai faduwa yayi awurin sumamme,akayo kansa,akadaukesa,wadanda basusan komai gamedashiba,saisuka dauka lalurace kawai,wadanda kuma suka Sani kowa nafadin albarkacin bakinsa.
Koda akagayama Mama jummai saicewa tayi,yama gaji yatashi,wahalalle kawai!!
Bikifa yayi biki,anyi shagali sosai,maroka-makad'a-mawaka sunzo sun baje kolinsu anan wurin, amarya kuwa tayi kyau harta gaji.
Misalin karfe biyar nayamma akakai amarya d'akinta,biki yasoma watsewa.
Bayan sallar isha'i,suna zaune cikin daki bisa gefen gado,bayan sungama sallolinsu.
Yace amarya yaudai burina yacika,duk wani Abu dakikeyimin ada yanzun yakare,yanzun sai inyi yadda nakeso.
Tace to kagodema Allah daya ganar dakai haka tunda wuri,domin tabbas zina mummunar hanyace,kuma kazanta.
Yace hakane,shiyasa nakejina cikin farin cikin daban ta'ba jina acikinsaba,abinda nadade INA nema yau gashi Allah ya mallakamin shi har d'kina.
Tayi dariya.
Azuciyarsa kuma yace yausaina kawar da sha'awarki danadade tana wahalar dani azuciyata,afili sayyace kici abincin mana,kici kikoshi sosai donnasan lallai kina jin yunwa,Sam!nasan hidima batabarki kin sake kinci abinci ba,Niko bazan yadda amaryata takwana dayunwaba.
Ya tsiyayi mafara mai kauri kofi yamikamata,yanata lallashinta sosai,saida takoshi sannan yakauda kayan.
Washe garima agida yawuni,suna d'ibar soyayyar su,itakam ganinsa take tamkar wani saurayine tasamu,don yadda yake kulata yake tarairayarta,ga uwa uba kuma ya iya soyayya.
Tana kwance kandoguwar kujerar falon ta,shikuma yanatsugunne yana matsamata kafa,suna fira jefi-jefi.
Yace Mariya lallai inakara godema Allah daya mallakaminke amatsayin Matar aurena,jinakeyi kamar intazama dake kada intafi Kano inbarki.
Saita wani yatsune fuskarta,cikin yanga tace:ashefa bani kadai bace matarka, hakane katunamanifa,yaushe zaka tafi kanodin?
Yace sati daya zanyi anan inkoma can.
Tace Allah yakaimu,
Yace kamar kar intafiko?
Tace Nina isa!kace lallai da madam tayi hukunci,to inkaje yaushe zakadawo?
Yace yadda kikeso aihakan za'ayi.
Tace kokuma yadda hajiyar ka taceba.
Yace kinganki,hajiyar nan tafita bakin ki.
Tace Abokiyar zaman tawa?
Yace a'a wadda kukahada muji daya da itadai,amma aibawuri daya kuke da itaba.
Tace to amma aikasan.....................
Yace don Allah dakata akauda zancen hajiyar nan,banaso kina tadoshi.
Saitaji farin ciki yamamaye zuciyarta,atunaninta bayaso anatada mashi zancen hajiyarne saboda yasameta,yafara sharewa da itane,azuciyarta tace naci gari!lallai nasan yanzun tamkar nikadaice azuciyar Alhaji, saita karajin takara wani isa.
Shiko abangarensa bahaka bane,duk sanda yatuna da hajiyarsane saiyaji kirjinsa nadukan uku-uku,saboda baysamma tayadda zaisanar da ita cewa ya kara aureba,yasan kuwa idantasani ba irin tashin hankalin DA bazai ganiba,shiyasa yaki sanar da ita,harsai duk abinda zaifaru yafaru, yanaso idanyakoma Kano yasan yadda zaiyi yasanar da ita Karin aurennasa,cikin hikima,sannan yayi hakuri,yadauki kowane irin hukunci zatazo masa dashi,don idan yasanar da ita kafin auren ,zata iya sanadin da za'afasa wannan auren,shiyasa yabarta harsai amarya tashigo d'aki tazama
Iyakaci tagama kurarin fadanta ta hakura.
Yana jin faduwar gabansane aduk lokacin daya tunata ko aka ambaceta,don baisan irin tashin hankalin dazasu fuskantaba,idan taji yayi aure,kuma yarasa wadda zai aura sai MARIYA!!! Kaih! Gaskiya akwai matsala!!! Domin idan harta Sani............................
Mariya ce takatsemai tunani dacewa,lafiya naga kayi shiru?kamatsamin kafafuna ciwo sukeyimani,zurga-zurgar bikinnan nayi wahala sosai. Tana wani kara shagwabemai,don ganitake bashida kamarta,shiyasa saiwani rawar jiki yake akanta,tace azuciyarta Ashe haka masu auren dattijan maza suke morema aure?suyita shagwabarsu suna watayawarsu shikuma yana tarairayarka,domin duk abinda zakayi yarinyace awurinsu,komai kayi aikin kuruciyane,yayta wani lallashin mace kamar yasamu baby ,idan kuwa har haka zanci gabadarayuwa da Alhaji mansur lallai bawadda tafini Saar aure amata.
Tad'ago fararan idanunta takara kallonsa taredafadin nagode,tajanye kafafunta tasaukesu kasa,shikuma yadawo kusa da ita yazauna,tareda yin saurin kama hannayenta dasu kaji kunshin amarci,yadan murzasu taredayimata kiss ahannayen,yace Mariya zanshiga wanka,yayi saurin mikewa saboda yaga lokacin Sallah yakusa,yafada kewaye yasanyama jikinsa ruwa.

Rayuwa mai dad'i da farin ciki suka kasance acikinta tsawon kwana biyar,gaba d'aya alokacin hankalinsa ya kad'a zuwa Kano,don yakosa yaje ayita takare,don kada watarana tasani dakanta,yakuma rasa amsar dazai bata awannan lokacin, don haka duk ys'kagara kwana bakwannan sucika yatafi.
Itakuwa Mariya tana zaune a dressing mirro tana tsala kwalliyar da ita kanta tasan tayimata kyau sosai, saiwani kara gyarawa take ,don atunanta hankalinsa NA kanta.
Shiko yana can yana tunanin tayadda zaifara sanar da matarsa wannan lamari,shin da wadanne kalamaima zayyi amfani ne yadda zata fahimceshi?
Daidai lokacin Mariya tamatso daf!dashi,tana fadin yakuma kaga kwalliyar yau?
Cikin karfin hali yace gaskiya kinyi kyau,irin wannan kwalliya haka,aibazanso inrikayin nisa dakeba,Allah yayi halitta kyakykyawa anan amaryata,wannan kwalliya yadda kikayi kyau haka kuwa,aidole inbiya.
Cikin murna tayi tsalle tareda fad'awa cikin jikinsa,shikuma yadageta sama yana juyawa da ita.
Daidai lokacin da kunnansa yajiyo wata murya daga waje tana cewa:
Tabbass!!!Hajiya nanne!donninan dakike ganina ganauce bajiyauba!lallai mujinki anan gidan yakawo Amaryar tasa!
Baisan alokacin dayayi saurin sauke Mariya kasaba,sobodajin muguwar faduwar gaba dayayi,cikin sanyi jiki yanufi kofar falon donya kara tabbatar ma kansa shin abinda kunnuwansa suka jiyo masa gaskiya ne?
Daidai kofar falon yala'be,saiyaji Matar nakara shaidamata,tana cewa:
Kaih!!lallai namiji maciyin amanane!wata kan yazo nan yakama gida yatareda yarinya har tsawon kwana biyar,kekuma kina can yabaroki!yananan yana holewarsa da yarinya!!!kaih!!!Namiji!Namiji!! Namiji beba!!!yatarwatsa maki farinkici wallahi!!!!
Alokacin kuwa H-Amina tagama cika,zuciyarnan tata kamar tafashe,cikin zafinnama kuma iya karfinta tahau dukan 'kyauran dakin,don tama kasa magana,sai huci kawai take,burinta kawai taga Alhaji mansur din,tanadukan kofar iya karfinta, irin dukannan da akecema koka bude ko inkarya kofar.
Tunda yaji haka cikin sauri yanufi wurin Mariya,jikinsa har 'bari yake,gaba daya yagama jikewa da zufa,cikin rawar murya yakecewa.
Mariya yimaza-maza kishiga bayi kirufe,karki kuskura kibude!wallahi Hajiya Aminace gatanan tashigo gidannan.
Mariya tabude baki zatayi magana.
Yace bana bukatar maganar ki yanzun,kiyi abinda nace kawai!!kishiga kirufe!kozata kwana acikin gidannan toki kwana akewaye,don idan tahadu dake,duk abinda yasameki kekijawo!
Tuni zufa tagama jikesa,cikin hanzari yake kara turata cikin bayin,tashiga yajawo yatufe.
Sannan yayi namijin 'ko'kari yace bari infita,ni inyaso tayagani.
A hankali yabude kofar,idonsa cikinnata,yakara shiga wani mummunan RUDANI dalilin wani irin kallo dayaga tayimasa.
Cikin tsawa tace INA yarinyar!!!
Ahankali yafito yajawo 'kyauran shima yasa mukulli cikin hikima yarufe,yamaida d'an mukullin cikin aljihunsa.
Yace Hajiya ce?
Taharareshi,tace lallai Alhaji mansur yayi kyau!!!wata kan ga 'yar iska kabaro Kano!!kazo nan kayi aure!!
Yace Hajiya kifahimceni wallahi..............
Takatseshi dacewa maganar infahimceka duk batasoba!don yanzun ni babu abinda zaka gayamin infahimceka!!donkariga kagama tarwatsani!!nace nanne Abujar?
Yace hajiya ki....................
Tace tambayar kafa nake nanne Abujar?? Oho!! Wata kan kacemin zaka aiki Abuja!! Shine kazo nan ka kara aure bada saninaba!!to daga kai har ita yau kunshiga uku kun lalace!!don duk Wanda yatsayamaku saina dauki matakin danayi niyyar indauka anan!!!
Kabude Mani 'kofa inshiga injawo yarinyar nan inkarairayata!!don yau koni ko kai ko ita sai anrasa d'aya!!!
Yace dakata Amina kiyi hakuri.
Tace kacucenine zakace inyi hakuri!!ni bamma sanshiba!!tad'aga murya da karfi tace,ka bud'emani 'kofar koko sai haukana yatashi!!!! Tajefar da jakar hannunta gefe guda, tacire gyalanta tayi d'amara dashi,tad'ora hannunta aka tafasa kururuwa,yayi saurin rufemata baki da hannunsa.
Yace lafiyarki Amina?
Tace banida ita!indai akan zancen kishiyane kakirani da komai, Donni yanzun badamuwata bane intara maka mutane!kowa yasan irin cin amanar dakayi Mani!!donba tsoro nakejiba!bakuma kunya nakejiba!!don mubar abin magana niduk dayane awurina!!
Kafin ka Ankara mutane sunfara shigowa gidan donjin ko lafiya, don kururuwar dasu kaji tayi.
Itakuma alokacin ta'kara farashin fad'anta,tana hargowa,don kowa yaji irin cin amanar da mujinta yayimata.
Inbanda cutama irintaka!harni zaka yaudara!!dacewa zaka tafi aiki!to Allah yatona asirinka!!kamarni zakaci amana!kayi kuskure babba daka rasa yarinyar da zaka aura sai Mariya!!kabudemin kofar nan inshiga injawota!inyimata rugu-rugu anan wurin!!don wallahi hankalina bazai ta'ba kwantawaba inba gawarta nagani ba!!Nina gayamaka kuma kasan zan iya!! SAINA KASHE MARIYA!!!!!
Duk gaba d'aya hankalin kowa yayo kanta,ana lafiya-lafiya.
Tace babu lafiya!yau sainayi maganin maciyan amanata!tarike kofar tana girgizawa iya karfinta.
Alhaji mansur yajanyeta yana fad'in kiyi hakuri kikoma Kano, inanan zuwa nima yanzun zanbiyoki,ni banason tashin hankali.
Tace ba kasan tashin hankali kuma ka nemosa?aikaida kwanciyar hankali aduniyarnan harsai yazamana babu d'aya daga cikinmu!amma muddin inada rai!kanada rai!!Mariya tanada rai toka dingi gamuwa da tashin hankali kenan har iyakar rayuwarka!!don Allah nikarabu dani inyi maganin la'ananniyar yarinyar nan!!!
Alhaji mansur yana riketa tana fizgewa,tuni kallabinta yarabu da jikinta,saboda tsabar masifa.
Wani bawan Allah yana wurin yace:haba Hajiya da girman ki,baikamata kina irin wannan abinba,saiki zuddama kanki mutumci,kisa kuma yarinyar nan tarainaki,tundadai aurene anriga andaura,hakuri yakamata kiyi,duk DA shima bai kyautaba,daya kara aure baisanar dakeba,lallai yayimaki laifi,amma tunda hakan tafaru,kiyayyafama zuciyarki ruwan hakuri,saikiga abin yawuce kamar ba'ayiba,kuma sainaga yarinyar nan dakike fad'a akanta 'yar cikinkice,don ahaifedai kin haifeta.
Alhaji mansur yace ah!toh!tareda langa'bar da kansa gefe guda.
Mutumin yacigaba dacewa,amma kizo kina tada hankalinki,kinatada jijiyoyin wuyanki akan wannan 'yarficiciyar yarinyar,ki zauna kina mugun kishi da ita,wadda bata wuce 'yar cikinkiba,duka yau kwana biyar da auren ko amarcimma basu gama Ciba kinzo kintada masu hankali.
Tace dakata da Allah hakanan!!nikarka 'kara 'bata Mani rai!shibaisan yarinyar bace ya aureta!sainice zanji kunyar yin kishi da ita!!
Har kake gayamin kwana biyar da aurensu!aiba saika gayamin cewar mujina yakwana biyar da wataba!! Kuma tunda yayimin wannan cin amanar saina dauki mummunan hukunci akansa!!sannan tajuyo ga Alhaji mansur.
Tace nizaka daudara!ni zaka ha inta!!nizakaci amana!!kayi babban kuskure,yau kuma INA cikin gidannan ba inda zani saidai afidda gawata!!
Wani can gefe yace:bawanda zai fidda gawarki da kafarki zaki fita!
Tawaigo tayo kansa kamar mahaukaciya,tana fadin inko aka kasa fidda gawata to za'afidda gawar Amaryar Alhaji!!don bazan yadda tana Raye INA rayeba!inayimata kallon wadda tata'ba kwana da mujina!!
Itace saboda tsabar masifa hartayi hanyar kofar gida tana zazzaga bala'i,shiko Wanda yafad'i wannan maganar tuni yayi waje baima bari ta iskoshiba,gaba d'aya idonta yarufe tsiya kawai takeyi.
Koda tadawo cikin gida babu Alhaji mansur, Ashe yayi wuf!yabar gidan shima dayaga hankalinta yayi wani wuri,yasan dai duk abinta bata iya 'balla 'kofar nan tashiga.
Tadawo tana huci tana kumfar baki,tana zage-zage,dadai taga babu abokinyin saita lafa.
Ahankali mutane kowa yafara kama gabansa,domin da gidan harya cika da mutane.
Wadda takawota gidan tadafa kafad'arta tace kibarshi kawai kishirya kikoma Kano,Nina tabbatar yau d'innan basai gobeba zai biyoki,idan yaje saiku can care, kiji kuma irin fad'in bakin dazayyinaki.
Wani dattijo dayake tsaye acikin gidan,Wanda shikadai yarage baifitaba,yace gaskiyarki kuwa takoma,tunfarkoma da batazoba tajirashi idan yaje saiya lallasheta,yayi mata dadin baki,hakanma dayafiye mata,dabata wahalar da kantaba kuma dayafi lada.
H-Amina takalleshi tagadai dattijone amma data gayamasa magana.
Kawar tata tace to shikenan baba mungode,dai dai lokacin datake daukoma H-Amina Jakarta da takalminta,tana fadin muje kawai!Allah yakiyaye!yadai gama dake kawai!!takamo hannunta sukayo waje,tasaka mata jakar acikin mota, tana cewa ki isa Kano din Nina tabbatar yau sayya biyoki,aikin tadamashi hankali.
H-Amina tace rabu dashi dani yake magana,sannan tace kishigo inmaidake gidanku sannan inwuce.
Tace to,tashiga tazauna kusa da ita,sannan H-Amina taja motar suka tafi,donta sauke ta gidanta itakuma tawuce Kano.
(Karka manta mai karatu kana tareda Littafin RUDANI 1 Wanda fateema Dahiru funtuwa Binta ta wallafa,dafatan yana nishad'antar dame karatu, 09162526909)

Bayan sun wuce wasu samari keta tattauna maganar,anan kofar gida,d'ayan yace Auwal gaskiya duk Wanda yasan me akecema adalci yasan ba'ayima matarnan adalciba,haba maza muji tsoron Allah mana,don Allah yabamu damar mu auri mace fiye da d'aya aikuma sai ayi masu adalci,tayaya za'ace zaka kara aure amma baka sanar data gidaba?saidai taji agari,wai harma katare da mata kwana biyar,dolene ranta ya'baci.
'Dayan yace kamal aikuma tunda abin yafaru dasaitayi hakuri,tundadai babu abinda zata iyayi,yanzun bagashiba tagama kurarin tatafi,kuma aurennan,to ribar metasamu aciki?inbanda 'batama kanta lokacima datayi.
Kamal yace ammadai duk dahaka wallahi maza saimun gyara,idan zaka 'kara aure,kasanar da matarka,tonifa inaso inkara aure,koda yafara fushin tagaji tabari kafin Amaryar tashigo tayi tahakura,kaga sai abin yazo mata da sauki,amma bawai kwatsamm!!taji kawai harma antare ,kaima kasan akwai matsala.
Itama yarinyar dazaka aura din saika sanar da ita,tonifa inada mata da 'ya'ya kaza to kunga duk sai adaidaita kafin lokacin auren,Allah dai yakiyaye yashigemana gaba.
Saida suka fara tafiya sai H-Amina tace wallahi Halima mujinnannawa yabani mamaki! Kamar ni zaici amanata!amma ba komai!!
Halima tace Namiji!Namiji!! Namiji macucine!!mayaudari!!kaih!!maza suna sheke ayarsu!bakuma abinda kemasu ciwo!humff!maza mutananmu.
H-Amina tace kirabu dashi sayya gane yata'boni,dani yake zancen!!zaizo yasameni har d'akina.
Halima tace kinunamasa kuskurensa!!!!
Wannan aicin amanane ta gaske!!kaih! aimu mata munada ha'kuri! Kiduba kigani H-Amina inkece komagana yaga kinayi dawani inhankalinsa yay dubu saiya 'baci!amma shi har ya iya auren wata yaje yakwana biyar da ita baisanar dakeba!!wannan cin amana aiyayi yawa!!!
Humf!!bari tunamin Halima, nan jinake kamar zuciyata tayi bunduga!koyazo wurinnawama mezaicemin?bacin aikin gama dai yagama.
Halima tace yo yalallashekimana.
H-Amina tace keyanzun kina ganin har akwai wata kalmar dazayyi amfani da ita wurin shawo kaina?ai duk duniyarnan bata!
Halima tace kisama ranki hakuri karkije wani ciwon yazo yahaye maki,kikwantar da hankalinki Hajiya.
Haba Halima donbake akayima abinda akayimanibane shiyasa kike fad'in haka.
Halima tace gaskiya nefa,kuma kinsan wani Abu Hajiya,yau inda ace matane keda ikon auren maza fiye da d'aya, nina tabbatar sai anyi ya'ki!kenifa idan naji ance anyima mace kishiya tausayi take bani,sai ince araina waiya takeji lokacin dataga anata biki anshigo dawata amatsayin Matar mujinta!!kaih!!lallai in ba'a tausayamanaba,nifa shiyasa tunda naji labarin aurennan ,naji ance a asirce zayyi aurennan,matarsa ta gida bata saniba nakasa sukuni,naga innice mujina zayyimin haka yazanyi?kawai saina shiga bincike,nagane mutumin kanone,nashirya naje da tambaya harnagano Inda kike,tunda nidai kinga bansankiba,inba dalilin hakaba,shiyasa nayi maki wannan 'ko'karin nazo nasanar dake,don kisan halin dakike ciki,to yanzun dai kinga dill!!.
H-Amina tace ainagode,Allah yasaka maki da Alkairi,naji dad'in wannan kokarin dakikayimani,koba komai nasan matsayina awurin mujina.
Halima tace karki yadda kisa damuwa azuciyarki,kizo hawanjini Yakama ki,don ba'kin cikin najimiji ba abinda bayasawa,DA kinga mace da ciwon zuciya,ko wani hawan jini,ba'kin cikin d'a Namiji ne kawai,aina tausaya maki sosai,

daidai nan tayi parking din motar ta 'kofar gidan su Halimar,tareda fadin aibaki tausayamin bama tukunna tunda bakisan
WACENIBA KUMA
WAYE ALHAJI MANSUR SANNAN
WACECE MARIYA???????

Halima takara gyara acikin motar datake shirin fita,tamaida hankalinta akan H-Amina, don taji amsar wadannan tambayoyi daga bakinta.

***** ******* ****** ******* ********

SUNANA AMINA YAKUBU,ni haifaffiyar garin kanoce,mahaifina shahararren d'an kasuwane,yanada arziki sosai,don intakaice maki labarin nikadaice 'ya awurinsa,tareda mahaifiyata Hajiya Asma'u,wanda muke kiranta da mommy,duk wani gata dajin dadin duniya nasameshi,iyayena basa hanani duk wani abinda nakeso, koda kuwa su abin bazaiyi masu dad'iba,saboda farin cikina kawai sukeso.
Inason sana'ar mahaifina ta kasuwanci,don haka nima danazama budurwa sainayi nufin in zama 'yar kasuwa kamar mahaifina,dukda mommy tana gayamin aure shine kawai darajar 'ya mace,amma Abbana yayadda da abinda nakeso,don haka idanna taso makaranta sai inbishi intayashi aiki.
Ahankali haryasakar min dayawa daga cikin ragamar kasuwancin nasa,koda baya kasar ni INA kula da abubuwa sosai,tare dasauran ma aikata.
Lokaci kad'an nazama BABBAR yarinya,maiji da naira!gani da hannun kyauta,shiyasa nakeda masoya sosai, inahawa mota irin wadda nakeso,haryazamana tamkar nice keda kammafoninsa,don yanzun hatta wata cinikayya dazata kaishi 'kasashen waje niyake turawa.
WATARANA dasafe nafito zani aiki,INA cikin tafiya a motata,sainaga wani mutumi yatsaida wani mai adaidaita sahu yanayimai fad'a,tareda an she mukullun 'kur'kurar,shikuma saurayin yanata bashi hakuri.
Tokasancewar ni macece mai taimako da tausayi,kawai saina tsaya don inji musabbabin rigimar,nayi parking din motata dai dai indasuke,nace:
Sannunku lafiya daiko?
Mutumin yace Hajiya yaronnanne naga bazamu shirya dashi ba,yau sati uku kenan bai kawomani balance ba,shine yazama dole in an she keketa,tunda naga ba sana'ar yakeson yiba!
Nace yokai bawan Allah meyasa ba kakaimasa kudinsa?in anahaka aibaza'aci gababa,todayake sauri nakeyi,kawai sainacema mai keke napep din nawane kudin ka?
Yace sati ukune,naira dubu A shirin da d'aya.
Naciro kudinnabashi,sannan nakalli saurayin nace kaikuma don Allah arika kiyayewa,naja motata natafi.
Bayan wucewar wannan Abu kamar da sati uku,wata rana nataso daga aiki,abin tsautsayi wani mai mashin yabugarmin amotata,yayi Mani 'barna,dalilin haka sainabiya da ita wurin gyara,gashi maraice yafarayi,don haka nanzanbarta insamu abin hawa inkoma gida.
Inanan tsaye saiga wannan mai keke napap din Wanda nabiyama bashi kwanaki,yatsaya yagaisheni,nalura dashi sosai ,kawai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment