Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saina tsaida shi nahau,nafadamasa inda zai sauke ni,har ina tambayarsa yanzun dai kana biyan kud'in bamatsalako?
Yace e amma saidai injin yatsufa dayawa.
Nace tokabar sana'ar mana,kayi karatun bokone?
Yace e nayi.
Nace to gobe kazo kasameni anan gida,nanyasaukeni na idasa shiga cikin gida,nabarsa yanata zabgamin godiya.
Washegari yazo,cikin sa'a kuwa NA bashi aiki a d'aya daga cikin ma'aikatun mahaifina.
KINJI YADDA NA HA'DU DA MANSUR.
Halima tace Ta'bd'ijan!!ya akayi kika aure shi??
H-Amina taci gaba dacewa,bayan yayi kamar wata shidda yana aiki dani,saiya goge kyawunshi yafito, nice nace inasonsa dakaina,duk danaso insamu matsala da rashin yadda daga wurin iyayena,amma daga baya kuma nice nayi nasara,sakamakon iyayena basa musantamin abinda nakeso,donhaka dasukaga nadage saisuka hakura suka barni da za'bina.
Kyawun halayyarsa da iya mu'amala da mutane shiyaja hankalina agaresa,bansamu wata matsala daga gareshiba alokacin dana kaimai zancen soyayyata,lokaci kad'an muka fahimci juna.
Wata rana,inagaban motata INA kokarin shiga don tafiya gida,mansur yanufoni dasauri,cikin fara'a yana fad'in.
Sarauniyar mata!d'awisu sha ado!!farar mace alkyabbar mata!! Ranki shidad'e harkin fito?
Cikin fara'ata nace nafito,tareda bude motata nacemai shigo muyi magana,yabude shima yashigo.
Sannan yace Amaryata nanda sati uku!mace d'aya tamkar da Hudu,kin tare gaba kin tare baya!kinmamaye dukkan ilahirin zuciyata!kinyimata kawanya da soyayyar ki,kinrufe ko ina daidai da kafar allura bakibariba,ballantana wata tasamu gurbin zama acikinta,ked'aya tilo uwar gida kuma amarya agidan Alhaji mansur manager! Babu sauran wuri dagake anrufe kofa,babu sauran d'aki agidan Alhaji mansur barewata tayi tunanin shigowa,sannan yakalleni sosai yace
Amina yaya dai?
Nayi murmushi cike dajin fad'in wad'annan kalamai nasa,nace Alhaji mansur idandasabo nasaba da irin wannan kod'awar taka,amma kodayaushe kake karantominsu sai injisu tamkar sabbi,in kasance cikin jindad'i da fara'a,sai intsinci kaina inamayyin murmushi idankanayimin irin wadannan kalaman,kuma koda acikin 'bacin rai nake dazarar kazo shikenan kawankesa.
Nagodema Allah dayayi had'uwata dakai,ya mallakamin kai amatsayin mujina,koba komai nasan zankasance acikin farin ciki na har abada,samun jajaurtaccen namiji mai sauya tunanin d'iya mace alokaci guda wannan BABBAR nasarace awurin kowace mace.
Sannan babban cikar burina gashi zangama rayuwata nikadai awurin namiji kamarkai,wannan wani abin alfaharine awurina,yadda natashi agidammu nikadai nasamu gata,haka zan rayu awurinka niadai batare da gatan yagoce maniba.
Yace tayaya za'ayi mace kamarke ahad'a soyayyar ta dawata?idan namiji ya aikata hakan tamkar yayima kansa gi'bine,kinga ne abinda nakenufi?
Idan mutum yahad'aki dawata duk ranar dayayenke wasu kwanaki donyakaima abokiyar zaman ki,tamkar yayankema kansa wani jindad'i,yatauye kansa sosai awannan rana.
Harcikin kaina naji maganar tayimin yawo,yawani kara tsunami,inajinkaina lallai ni watace tadaban.
Nace inasonka mansur!!
Yace nima inasonki Amina.
Fateema Dahiru funtuwa 09162526909
Mukagama firarmu
sannan yafito motar yashiga tashi yatafi.

Munyi aure da Alhaji mansur irin auren soyayyar dana saki jikina dashi akan lallai bawata saini din,kamar yadda kullun yake kara shaidamin.
Shekarata talatin da biyar dashi a yanzun haka,haihuwata bakwai tare dashi,INA cikin jindad'i da kwanciyar hankali sosai ,kuma arzikimmu kodayaushe kara gaba yake,,don yanzun mansur yafita daga karkashin aAbbana,yabude nasa,don haka gashin kansa yakeci yanzun.
Nimacece mai kishi!kamar yadda yakecewa,natare gaba natare baya,bana yadda kowace mace inganta da mujina,inba dawani kwakwkwaran daliliba.
NA kasance INA bibiyar wayarsa akowane lokaci,duk da inajin nayadda dashi, amma saboda tsaro,kuma koda yaushe yanakara gayamin inkwantar da hankalina,indai maganar aurece aishiyariga ya auru,bawata macen dazai kara gani taburgeshi.
Rannan naje shiga dakinsa,kawai sainayi kicibis!dashi yana waya da mace.
Nace Alhaji menakeji haka?
Cikin sauri yakauda wayar daga kunnansa,taredayin wata irin dariya,yace lafiya dai Hajiya?
Nace a'a nikainake tambaya,nakejin kamar muryar mace awayarka?
Yataso ahankali yakama hannayena,yace to inbanda abinki jin muryar mace awayata wani sabon abune?
Nayimai wani irin kallo nace banganeba,
Yace to amma atsayina name kasuwanci,mai harka da mutane kala-kala aidole kiji muryar koma wacece.
Nayi saurin fizge hannuna daga nasa,nace to anzo wurin!!dama inajiran haka!nagaji!Alhaji mansur nagaji!!harka kowace irice indai zata had'aka cud'anya da mata tonayafeta!!gara abarta kwata-,kwata!Donni bazan amince dawannan ba!!
Yace kintaba ganin inda kasuwanci yakasance ahaka?ace sai anware wasu junsi wadanda sukadaine za'ayi mu'amala dasu?haba Amina jimana" kikwantar da hankalinki, yanzun yawancin kasuwancimma matane,uwum!don Allah ki yadda dani mana.
Nace nifa indai harka da matane zan iya cewa kasuwancinma abarshi!!
Yace wannan ma datakirani awaya ba 'yar nan bace,daga Lagos take,zanyi order wasu kayane.
Nace wai Alhaji mansur suwa kake nemamma kudinnanne?
Yace kemana da 'ya'yanki.
Nace to zan iya cewa abar Neman kudin!kadawo kazauna cikin gida kullun intasaka gaba inakallonka,Donni gara muzauna ahaka zaifiyemin kwanciyar hankali!
Wannan maganar saida ta bashi dariya,yakara janyoni jikinsa,yana fadin,aiko watarana dakanki zaki koreni,inzodai intaremaki acikin gida,habawa aikemadai kinfadane.
Amma gabadaya narasa gane irin wannan kishinnaki,kuma azaman damukayi dake fiye da shekara talatin ayya kamata ace kin sanyaya zuciyarki,kin tabbatar dacewa nibazanyimaki kishiyaba,domin dazanyi datuni nayi,don Allah Amina kirage wannan zafin kishin naki.
Humf!nayi ajiyar numfashi,nace hakane,amma wani lokacin ne idan raina ya 'baci akan kishinka bansamma inayin wani abinba,don gaba d'aya idona rufewa yake.
Yace tokibudeshi kinjiko?uwar gidan Alhaji mansur!kuma amarya!babu wata bayanke,zinariya sarauniyar mata,haka yacikani da kirari kamar yadda yasaba,harsaida yaga nayi dariya, sannan yace:
Wohoho! Sarkin kishi,amma balaifinki bane,laifin soyayyatane datayimaki wawankamu,Nikuma nasan dole sai anason mutum akeyin kishinsa.
Nace aigaradai daka gane hakan,saida yakwantarmin da hankali sosai.
Shiyasa nakeson Alhaji mansur, domin shi mutumne Wanda ya iya lallashin mace,ya iya tarairaiya,ya iya kalamai,kuma kodayaushe jinsa yake tamkar wani saurayi,yasan kaina dayawa,Kowane irin bacin rai nashiga yasan yadda zayyi ya lallasheni,gashi da kissa kamar mace,shiyasa kullun nake karajin sonsa,nakekuma kishinsa,amma duk dahaka saida Yazagaye yaje ya auri wata !!
Halima Tabbas!! Danasan dawannan labarin kafin aurennan saina lalatashi!!bayadda za'ayi inbari ayishi,nasan shiyasa ya boyemani.
( mai karatu kana karanta littafin RUDANI 1 na fateema Dahiru funtuwa Binta 09162526909)

****** ******* ******* ******* ********

Hankalina yanatashi idannatuna irin kalamai masu dad'i dayake yawan fad'amani akunnena,sai intunacewa ya auri wata tsawon kwana biyar itama yana karantamata irinsu akunnuwanta,yatonamani asiri!!!
Daidai nan tari yasar'keta,tareda fitar wasu zafafan hawaye dasuka jika kuncinta.
Halima tahau lallashinta tana fad'in,kiyi hakuri karkitadama kanki hankali,donshi namiji babu ruwansa!sayya tarwatsaki!!yahaddasamaki ciwon zuciya,bakuma abinda yadamesa,kaih!Namiji dai!Namiji dai mayaudarine!!wallahi yacuceki!!kwana biyar kanata sharholiyarka da Amarya bakasanar da uwar gidaba!Hajiya idan kikaga mace da wani hawan jini ko ciwon zuciya sanadinsa Namiji ne!kidauki duk matakin daya kanata akansa!inagoyon bayanki!!natabbatar kuma yau dinnan saiyabiyoki har Kano.
H-Amina tace to mezayyimin?
Halima tace yomezayyimaki inbanda kalaman yaudara,dama can tunfarko yaudararki yake,ayya gama dake kawai!!saidai kisaurareshi kawai.
Daidainan taduba agogon motar ta,tace yamma tayi ,yakamata inwuce banason inyi dare sosai ahanya.
Halima tace AF!to aibakigayamin WACECE MARIYA BA.
H-Amina tace kibiyoni bashin wannan, duk ranar damukasake haduwa Zangaya maki,yanzun lokaci nakuremani.
Halima tace gaskiya kin bani labarin dazai dademani azuciyata ,Allah dai yakiyaye,sannan tafito daga cikin motar.
H-Amina kuma tadauki hanyar komawa Kano, daga manumfashi.

BAYAN AWANNI UKU

Mariya ce ketakai dakomowa acikin falon ta, hannunta rike dawaya,tana latsawa,zuwa can ta kangata akunnanta,harya yanke ba'ad'agaba,tacigaba da kewaye a falon, tana kwata tanatsaki,rannan nata abace,dagani cikin masifa take,tatsaya wuri daya tana karkada kafarta,tace wainid'in!!!humf!ba'asanniba wallahi!! Sannan takarakiran number datake nema,harta kusa yankewa sannan aka daga.
Tace mamammu tund'azun inata Neman ki awaya baki dagaba.
Mama jummai tace mariya bani gidan yanzun nashigo,wayar kuma nabarta tana charge, lafiya daiko?
Mariya tace bata!mamammu ba lafiya! Gaba daya nakosa inganki!ingayamaki damuwa ta!don Allah mamakitafo yanzun!
Mama jummai tace wani Abu yafarune mariya?
Mariya tace aa nidai mama kawai saikinzo,maganar bata wayabace.
Mama jummai tace incedai bayaronnan bane Hashimu?
Mariya tace mama kedai kizo kawai,bawanda nakeso ingayama damuwata saike,kiyi maza-maza don Allah kizo kada inhuce!
Mama jummai tace to shikenan Mariya kibani mintina talatin ,don inbiya tawani wuri tukunna,sannan inzo.
Mariya tace mama dadai kinfara zuwa nandin.
Aa Mariya kibari inda zanfara biyawadin yanada muhimmanci sosai ,sannan takatse kiran,tana karayin kwata,tace lallai kam!!dani ake magana!!
Itakuwa mama jummai cewatayi,heee!lallai kam dama nasan ba abinda zaihana yaronnan bai dauki matakiba!amma dani yake magana,in yasan wata aibaisan wataba,wata kan yarikitamin yarinya adakin mujinta!yahanata zaman lafiya,wata'kila ture yayimata,akebata tsoro agidan,baridai inje ingani,don gara inyi maganin abin tunda wuri,shiyasa yanzunma kafin in isawurinta saina biya wurin bokana nakaimashi bayani,donyadaukar Mani mataki akan yaronnan (Hashimu) donbashakka bakowa bane shine,tadaga matashin kanta tadauko kudi,ta 'kirgi naira dubu goma tafita da ita.
Batazame ko inaba saiwurin mai maganinta.
Tace boka akwai matsala!yanzun yarinyar nan mariya takekirani,tace inyi maza-,maza inje gidan ta akwai gagarumar matsala!Nina tabbatar yaronnan bazai barta hakananba,shiyasa nazo kataimakamin,asamu yarinyar nan tazauna d'akinta lafiya, inba hakaba kuwa zamuga samu muga rashi.
Boka yace kikwantar da hankalinki, tunda kikaxo nan komai yabiya,maganar zaman lafiyar 'yarki ad'akin mujinta an gama!! Bawanda ya isa yatadata!indai nikina tareda ni.
Tace kuma boka sonake amantar da hashimu cewa yatabason yarinyarnan.
Yamanta da ita kwata-kwata!don inbahakaba nima bazaibarni inzauna lafiya ba,don ranar bikintafa har somewayayi.
Boka yace indon wannan ne ba matsala,yadauki 'yansaddabarun dazai bata yamika mata,itakuma ta karba tana farin ciki,tafito dasamu adaidata sahu tahau batazame ko inaba sai gidan 'yarta mariya.
Tashiga tanata sallama bataji an kar'baba,tayi tsaye kofar falon tana sallama taji shiru,don haka saita shiga azatonta ko mariyar tashiga kewayene,tasamu kujera tazauna,shiru bataji motsin mutum ba.
Saitadau waya takira number mariya,harta gama ringing ba'ad'agaba ,tace aah!towai lafiya?yanzunfa takirani inakuma tajene?takara hakuri kamar na mintuna goma don jiran mariyar waiko wani wuri tashiga amma shiru takeji, don cikin gidamma babu alamar mitsin kowa,saita mike tsaye tana kwala Kira, Mariya! Mariya!!mariya!! Taji shiru,kawai saita shige dakin.

Kwance taganta abisa gado male-male cikin jini,gakuma wukanan ajiye agefenta.

Mama jummai tafasa wata gigitacciyar kara,tareda fadin mariyaah!!!! Lailahaillallahu Muhammadurrasulullahi sallallahu alaihi wasallam!!!mariya!!!tasa hannu tajuyo da ita,sai tatafi yaraf! Almar babu rai ajikinta.
Nashiga uku mariya waye yakasheki?? Tafasa kuka sosai tana Neman dauki,tayo waje aguje donta shaidama mutane,tana ataimaka mata.
To dayake unguwar babu mutane sosai,gidaje ko INA arurrufe,inbanda hayaniyar da H-Amina taxo tayi dazun,tatara mutane,to yanzun kuma kowa Yakama gabansa,bakowa alayin.
Donhaka tanufi kofar wani gida,tana bubbuga get din gidan .
Cikin sauri mai gadin gidan yafito,takara fashewa da kuka,tanayimai nuni da gidan da mariya take tana cewa:
Don Allah kataimakamin ankashemin 'yata a can gidan!!
Ganin tanunamai gidan kuma tafad'i kisa,yayi saurin dafe kansa yana salati,yace yanzunnan matarnan saida ta aikata wannan danyen aikin?mumin zacima tatafi!!yanzunnan saida tatsaya takashetadin?

Cikin kuka mama jummai tace wacece?
Yace kishiyarta mana ,Matar mujinta,dazun tazonan taita hayaniya,tatara mutane,tana cewa saita kasheta, nandai aka lallasheta mumund'aukama tahakura tatafi,Ashe saida tadawo takasheta.

Mama jummai tace kishiyartatace tazo gidannan?
Yace kwarai kuwa,don akwai wad'anda sukaganta dayawa,hartana ikirarin saita kasheta,kibari inshiga insanar danasu gidannan don suji abinda hayaniyar dazun ta haifar,yawuce cikin gidan da gudu-gudu yana salati.

Nandanan saigashi yafito tareda masu gidan,cikin sauri.
Koda sukazo mama jummai tazame kasa tanata kuka iya karfinta.
Hajiya (Matar gidan) tace kece mahaifiyar amaryarko? Sannan tayi salati,tareda fadin sukau wasu matan inazasukai rayuwarsu da irin wannan kazamin kishin? Takasheta kikaceko?

Mama jummai tace wallahi takasheta!!bamu dade dagamayin waya da itaba,tacemin inzo akwai matsala! Ashe bazamu hadu da itaba!
Hajiyar tace gaskiya tsakani da Allah wasu matandai suna bada Kansu,inazamukai rayuwarmunewai?mezamu samu aduniyarnanne wai?
Sannan takoma ga kallon maigidanta tace Alhaji asanar da jami'an tsaro,don sushigo suga abinda yafaru.
Shiko dama yananan yarasa wurin tsayuwa,duk yadaburce,yadauko wayarsa donya Samar da 'yan sanda.

Hajiyar taci gaba dacewa:
Nikinganninan mu ukune awurin mujimmu,amma ba'atabajin wata hayaniya tafito damu wajeba,muna zamanmu lafiya, da mujinmu,amma ita daga anyimata kishiya daya kawai,duk tazo ta hargitsamana unguwa!tatada hankalin kowa, muna zamanmu lafiya, kaih!!wannan ba'kin kishi nata Allah wadaransa!gashinan zata jama kanta muguwar nadama! Kisan kai!!kisankai saboda kishi? Kaih!wannan mata wallahi tabada mata! Zatayi danasani! Mujin datake takama dashi karshenta tarasashi har abada! Zaman gidan yari yasameta!!
Kinga mujinnata da take kishi akansa saima ya auri mata Hudu inyaso,oohni!!Nafisa yaunaga tashin hankali!!
FatimaDahirufuntuwa 09162526909
Kafin kace miye wannan unguwa takuma cika fiye da dazun, kowa NA fadin albarkacin bakinsa,wadanda basuga hayaniyar da H-Amina tayiba dazun sunata tambaya,wadanda ko suka Sani sunata kara bada labarin abinda H-Amina tazo tayi dazun, jama'a nata Allah wadai da irin wannan bakin kishinnata.

Cikin mintuna A shirin da faruwar wannan Abu saiga motar 'yansanda,kaitsaye suka shiga ciki,don suga gawar,daga busani kuma sumikama likitoci ita suwuce da ita Asibiti.

Haka akayi wannan yammaci acikin tashin hankali a wannan gari na manumfashi,musamman ayankin da abin yashafa.

Jama'a nata fad'in kishiyace tazo har gida takashe kishiyarta!

Ankira number Alhaji mansur yadaga wayar:
Hello.
Yace inajin ka.
Shikuma yace Alhaji kana inane?
Alhaji mansur yace inamota,don yanzumma nakusa kaiwa Kano.
Tokayi maza-maza kadawo don kabar tashin hankali agidanka.
Cikin kaduwa Alhaji mansur yace meyafaru?
Mutumin yace uwargidanka tazo takashe Amaryar ka, gashinan yanzun unguwa tacika!har jami'an tsaroma gasunan sun halarci wurin,don haka kome kake kayi maza-maza kadawo.
Alhaji mansur yaja wani mahaukacin birki,cikin kaduwa,taredasakin wayar dake hannunsa tafad'i,cikin gigita yace:

Hajiya Amina takashe Mariya?? Nandanan yaji zufa tayankomai,tareda fad'in subuhanallahi!!wannan wane irin tashin hankaline? TAYAYA ZA'ACE HAJIYA-AMINA CE TAKASHETA??? Wannan kuma wane irin balaine?nida nasan yanzun H-Aminama takai Kano .
TAYAYA ZA'AYIMATA WANNAN SHARRIN???

Sayya juyo da motarsa yadawo dabaya,yanufo gida,zuciyarsa cike da sake-sake,lokaci zuwa lokaci yana ambatar.
Hajiya Amina! Hajiya Amina!!wannan wane irin bala'ine?

Saibayan magariba sannan yaiso,koda yazo unguwar nanan cike,cikin sauri yaketa kutsakai cikin gidan da aka hana kowa shiga,inbanda lokitoci da jami'an tsaro da suke aikinsu acikin gidan.
Duk da ana kokarin taresa saida yayi kokarin shiga cikin gidan, har yasamu yashiga dakin da gawar take.
Wasu mutane daga waje nafadin meyasa ake kokarin hanashi shiga gidan? AISHINE MUJIN!wadanda basu sanshiba suna fadin dama shine?aiko shine!!akansa ne akayi wannan rigimar,anata nunashi anacewa aishine!aishine!!harya shiga cikin gidan.

Yanashiga yatarar da gawar Mariya kwance bisa gado, lokacin da likitoci ke 'ko'karin daukar ta.
Yanazuwa yafada jikinta yarungumeta yana fad'in Mariya don Allah kitashi kada kimutu!idan kuma kin mutu Mariya maza kitaimaka kutashi kisanar dasu WAYE YAKASHEKI!!! Cikin kad'uwa da kuka yake fad'in wadannan maganganun.
Kitashi kifad'amasu Wanda yakasheki!
Kamar daga sama yaji wani yace ba ance kishiyarta tazoba?to ai ita takasheta, Alhaji mansur yayi saurin sakin mariya tareda kallon mai maganar,yace tayaya za'ace Aminace takasheta, Alhalin nasan Amina ma tuni takai Kano, gaba daya duk ya gigice.
Cikin 'yansandar wani yace kofir usman!
Cikin sauri ya amsa da yes sir!
Atafi anemomin H-Amina acikin awanni A shirin da Hudu akawota.
Yace angama tare da Sara mai.
Sannan yadafa kafad'ar Alhaji mansur, yace kakwantar da hankalinka,kafad'amana inane zamu samu H-Amina matarka?
Cikin kaduwa yace bazata iya aikata kisankaiba.
Dan sandan yace bamunce lallaine ita ta kashetaba,bincike zamuyi.
Alhaji mansur yabasu Address din gidansa dake Kano.
Sannan Spector 'yan sanda yace ma Usman kutafi tareda sergeant hasana atafo da ita.
Alhaji mansur najin anfad'i haka,kawai sai yafad'i kasa sumamme ,nanfa shima aka had'a dashi anufi Asibiti, ita kuma gawar mariya akanufi da ita inda ake Adana matattu,zuwa kwana biyu kafin agama bincike.

Nandanan wannan labarin yakarade garin manumfashi,don haryaje kunnan kawar Hajiya Amina, (wato halima)lokacin da halima taji wannan labarin hankalinta yayi mummunan tashi,,don haka cikin sauri ta dauki waya takira Hajiya Amina.
Alokacin isarta gida kenan,rannan nata 'bace ,tanata fad'anta itakadai,da 'yanzage-zagenta akan muguwar cin amanar da maigidanta yayimata,sannan harma yake sanar da ita cewa yana hanya a yanzun,tomema zaizo ya gayamin?banda yariga ya aikata abinda yayi niyya,amma gara yazo ayita takare,don lallai yau sayya fuskanci hukuncina! Yazodin dani yake magana!!
Daidainan wayar dake cikin jakarta tahau ringing, atunaninta Alhajintane,sai taki d'agawa.
Ind'aga to ince mashime?mayaudari kawai!aizakazo kasameni har gida!
Har wayar tayanke batama dauko tadubaba.
Itakuwa halima nacan takasa zaune takasa tsaye,tanaso H-Amina tadauki kiran,dontasanar da ita abinda kefaruwa.
Takirata yakai sau biyar har tayanke ba'ad'agaba,sai kawai tayanke shawarar tatura mata Text message, tarubuta tatura mata.
Itakuma can sai cewa tayi kaih!wannan fitina taka tayi yawa,watakan yaga bazan d'aga kiranba,shine yaturo sako,baridai induba,aidai baisannaduba ko bandubaba,iyakaci koyazo yatambayeni ince nidai banganiba,sannan tadauki wayar taduba,an rubuta kamar haka:
H-Amina munfa 'ballo ruwa!
Muna cikin tashin hankali!
Yanzun aka shaidamin cewar anje
har gida anyima kishiyarki kisan gilla
Kinga kuwa dole ayi zargin mune........

Batama idasa karantawa ba tayanke cikin sauri,takira number Halimar, bugu d'aya tad'auka,tace:

Halima bangane abinda kikenufiba!
Halima tace gaskiya nake gayamaki!
Don yanzunma 'yansanda suntafo ne
Manki,kingakau akwai matsala.
H-Amina tayarfar da wata zufa data
Yanko mata,tace to yanzun yazamuyi
Halima tace kigudu kinemi wani wuri
Ki'buya,in an kwana biyu ki haure
Kibar kasar,inko bahakaba lallai a
Kwai matsala.
H-Amina tace ba inda zani,don duk in
da naje dole zandawo,kuma guduwar
me zanyi?TUNDA BANINA KASHETA
BA,idannagudu aisai ayi zargin lallai
Nina kasheta din,tunda kuma nibani
nakashetaba!ba inda zani suzodin.
Halima tace to nidai guduwa zanyi
don gaskiya natsorata sosai.
H-Amina tace karki gudu halima don
Zaki jamana,za'ace mune muka aika
ta,badai iyakaci bincike bane?koba
Da'de kobajima gaskiya zatayi halin
ta,don haka karki gudu,sannan ta
Yanke kiran.

Awannan Daren H-Amina agigice takwana,atsorace dataji motsi saitaji kamar 'yan sandanne zasushigi,haka takwana zarya acikin d'akinta ,tana kullawa tana kwancewa,batada mafuta.
Acikin Daren tasanar da iyayenta abinda kefaruwa,dazuwan datayi manumfashi tayi rashin mutumci,sannan cikin kuka tace:
Abba wallahi banina kasheta ba"
Inda nasan kwanan yarinyarnan sunku
Sa karewa dabamma wahalar dakaina
najeba!ammanina tabbatar yanzun ba
Wanda zai iya fitar dani daga wannan
Zargin sai Allah, kuma gashi nataka
Shari'arsa,naje har gida naci mata mu
tunci,daga ita har mujinnawa,ta'kara
fashewa da kuka,tace Allah kaga ha
lin dana shiga,Allah kafitar dani,ba
Wanda zai iyayimin haka saikai Allah
Allah nasan na aikata laifi,kuma nakar
'bi laifina,Allah kayafe Mani,Allah ka
nunamani ban isaba,dakayi Mani wan
nan hukuncin cikin gaugawa,kuka yaka
ra kwace mata tareda fad'in Allah kafi
tar dani!!

Mahaifin ta Alhaji yakubu yayi salati, yace wannan wace irin jarrabawabace?dukdakema kinada laifi,babu abinda bamu fadamaki abaya akankirage wannan zafin kishin na ki, toyau ga abinda yajawo maki.
Awannan dare har gidan iyayenta ba'asamu runtsawaba,don kuwa ita mahaifiyar tama tafowa tayi gidan 'yartata,nan suka zauna tare,duk yaran basusan abinda kefaruwa ba.
Sai Al amenn babban dan H-Amina Wanda ayanxun yakeda shekara TALATIN da biyu, farine dogo dashi,kamanninsa daya da mahaifin sa,yarone mai hankali tuntasowarsa,yanada natsuwa sosai.
Inda yakammala degree dinsa,yafara aiki a Asibitin malam Aminu Kano,shiyarone mai hazaka sosai ga nutsuwa.


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment