Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LDX80EfO3RZE9fukjFzcTL

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCAIATION 🖊️
(J.W.A)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i ✏️

Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga ubangiji wanda yayi sammai da kassai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (S.A.W)

wannan littafin mai suna

RAYUWA DA MACIJIYA, PAID BOOK 📚
MALLAKIN AISHA M.B

banyi wannan littafin , don naci zarafin wata, koh wani bah, Nayi shi ne don mu dau darusan dake tattare acikinta. idan wannan littafin yayi Daidai da rayuwarka toh Arashine.

Ban yarda a chanza min wani Bangare koh sashi a cikin littafi nan bah, idan kuma mutum ya kuskure ya sauya min littafi na, toh na barshi da Allah,

BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM 🌺

🌸RAYUWA DA MACIJIYA🐍
FREE PAGE 1⃣▶2⃣

WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISHA M.B🌺 (BABY ISHA)


----------------------

KAUYEN GEMBIZA🌳

Gabadaya kasar kauyen ta bushe.
bishiyoyin sun kafe, gonan naki sun bushe, ruwan garin ya kafe, babu wata ciyawa dake tsirowa, saboda rashin ruwa, yayi musu tsanani.

Daga dayan bangaren, jama'a garin suna a zazzaune Duk tulun su babu Ruwa koda na alwala, Duk lebu k'ansu ya bushe, yayin da kowanne su yayi tagumi, suna jiran ranar da zasu cinye wannan jaraba wa da suka tsinci kansu aciki.


Daya daga cikin matan dake Zaune tace, idan tsanani yakai makurar tsanan ta, toh mafuta daya gare tah".

Mai gari yace, wace mafuta kenen? Menene ba'ayi bah don kawai, musamu mu ceci rayukan mu da Kuma na y'ay'an mu, Wanda zasu taso nan gaba.
Sadaukar wa, azumi, sallah, babu wacce babu yi bah, amma abun saika ra tsamari yake, shekara da shekaru kenen, rabon da ayi mana ruwan sama a wannan kauyen.mutane sai mutuwa suke, ya yinda ruwan kogin mu ta kafe, babu ruwa koh kad'an acikin ta,yara gasunan wasu sun zama marayu dalilin wannan rashin ruwan, iyayen su, sukaje suka rataye kansu,

shin wane laifi koh zunubi muka aikata? Da muka cancan ci irin wannan, azabtar war!. wannan azabar ta isa, aka. Inna wuro ki taimaka kine man mana mafuta

Wacce aka kira Inna wuro tace, komai yayi farko, toh zaiyi karshe, ni bansan menene mafuta bah, amma tabbas inada tabbacin cewar, Allah zai Kawo mana agaji nan bada dadewa bah,

Malam liman yace, yanzu wajan shekara da shekaru kenen, kina cewa, Allah zai kawo mana agaji, sai yaushe kenen, sai yaushe ne, zamu daina zubda hawaye, akan wannan kuncin rayuwar da muke,

Yanzu muna tsakanin mutuwa da rayuwa ne, saboda bayan rashin samun ruwa mah, kayan gona sun Kare, bamuda wani amfanin gona, saboda babu ruwa ko mun Shuka bata tsirowa,

Gaskiya nidai inada wata Shawara, jama'an garin suka ce, Tom munaji, Allah yasa mai amfanu wa ce.

Malam liman yace, mezai hana mu nemar wa kan mu mafuta , mu koma, kauyen makota, har sai komai ya lafa, an yafe mana zunuban mu, Danni dai a ganina, zunubai ne, suka mana yawa, da har za'a dunga yiwa sauran kauyuka ruwa amma banda tamu, wannan itace Shawara ta inba aka bah, mutanen mu zasu cigaba da mutuwa ne daya bayan daya, koh muje mu nemi ruwa har sai inda karfin mu ya Kare.

Ard'o yace, wannan wace iriyar gurguwar Shawara ce! ta yaya, zamu bar Asalin garin kakannin mu, sannan mu koma wani kauyen daban, gaskiya wannan Shawarar tsam, bata yi bah.


Malam liman yace, tabbas maganar ka gaskiya ce, amma ya muka iya, dole ne mu nemar wa kan mu mafuta koh munaso, koh Bamua so, kafun lokaci ya d'ad'a kure mana , Kuma na bada wannan Shawarar ne badan komai bah, sai don don mu ceci rayukan mu,

Jama'an garin suka ce , tabbas wannan Shawara ce mai kyau, Kuma a yau bah gobe bah zamu tafi nemo wa kan mu mafuta,

Tashi jama'an garin su kayi, saka Fara har'ada kayyayakin su, saida suka dau lokaci kafun su gama, sannan daya bayan daya suka Fara tafiya.

"Inna wuro" cikin ranta tace, shin yaushe ne zaki bayyana domin kawo wa wannan dauk'i. Ki taimaka, ki hanzarta, muna cikin halin tsaka mai wuya, bayyanar ki itace, mafuta a garemu,



::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Cikin fargaba da tsoro, take bin jikin bishiyoyin dajin, gabadaya ta ranta da Kuma jaririyar dake hannunta take,.

raunuka da tab'o gabadaya sun b'ata mata jiki, Daidai wani katoton bishiya wanda yafi kowane bishiya fad'i da Kuma girma acikin wannan dajin.

Zama tayi, Tana saukar da ajiyan zuciya, ajiye jaririyar da bazata wuce watanni biyar zuwa shidda a haihuwa bah, wuyanta sanye yake da tsarkar lu'u lu'u (Diamond 💎) wadda tambarin masarauta ke Ajiki, da Kuma sunan yarinyar.

Ajiye jaririyar matar tayi,
Ta shafa bayan ta, Wanda wuka ke soke Ajiki, rintse idanuwanta tayi, hawaye nabin kan kuncin ta, ta Fara zaro wukan a hankali, har tayi nasaran zare shi baki daya, wani ihuu ta kwallah wanda ya Firgita jaririyar ta fashe da kuka.

Hatake hadari bakin kirin ya taso, inda aka fara iska mai hade da guguwa,

Kukan jaririyar ne ya gauraye dajin, baki daya.

tsawa da walkiya ne ya wanzu, inda dabbo bin dajin suka fara guduwa suna koma wa guraren su.


Inda gefe guda kuma, Macizai, kala-kala, iri -iri, daban -daban, suka Fara futowa daga cikin ramu kansu, suna nufan inda jaririya take,

Daidai wajan, da jaririyar take, suka je, inda suka Fara zagaye tah, suna shafar jikin ta,

Cikin fargaba da tsoro matar ta tashi, da niyyar koransu, cikin rashin sa'a daya daga cikin macizan ya sare ta,

Faduwa matar tayi, kunfa yafara futa a bakinta , cikin dak'ewa tace, ya Allah, ka Kare min y'ata, kashiga lamarin ta, ya Allah ina rokan ka, da kasa ta fada hannun mutanen kirki, kada ka Bari makiya su ci galaba akanta, Duk abunda zatayi a rayuwarta ya, kasance tayi shi da kyakyawan niya. Inason ta kasance mai taimako, tausayi, da Kuma juriya. Ta kasance abun Misali ga wasu, Wanda za'a dunga Alfa'ari da itah.

Tabbas nasan y'ata zata kasance Tana Tareda sa'a a rayuwar tah. Ya Allah kada ka Bari y'ata ta fada a mugun hannu,

Wa enda kuma suka zalunce ta, sukayi sanadiyar kasan cewar ta Hanan, tabbas wata rana zaizo da zasu ne mi gafarar ta, sannan Kuma su dafa kafafunta. Daga hannun ta, tayi sama tace, Allah ya yi miki albarka y'ata, Tana kaiwa nan tayi Tsit,


Kuka jaririyar ta kuma fashewa dashi,



Dafa Malam liman" Mai gari yayi yace, shin Bakua jin kamar kukan karamin jinjiri.

Inna wuro tace tabbas nima naji, Kuma Gashi yau naga, anyi hadari, gabadaya garin yayi duhu, al'alin yanzu bah lokacin Damuna bane.

Ard'o yace, muje mu duba wane yaro ne,

Chan cikin dajin suka nufa, suka Fara bin, inda suke jiyo kukan, jinjira.

Aska dajin suka farayi da wutan iccen dake hannunsa, Chan idanuwan su ya sauka, akan jaririyar, dake yashe a k'asa, Koran macizan suka farayi, da wutan hannun su,

Hajiye wutan hannun ta Inna wuro tayi, ta nufi wajan matar dake yashe a kasa. Kallon matar tayi, ta shafa kanta, Tareda rintse idanuwan ta , bude idanuwan ta tayi tace, kuzo , ku cincibi, wannan matar, ta Fada a doguwar suma, Kuma tanada bukatar taimakon gaggawa saboda, dafin macijin da ya sare ta Mai matukar, karfine.


Tashi tayi ta nufi inda jaririyar take, Tareda daukan yarinyar, ta dora idanuwanta akan na jaririyar, abunda ta ganine ya matukar tsorata ta, tabbas yarinyar ruwa biyu ce, a gigice Inna wuro tace, jama'a, itace, ta bayyana, Mai cetan mu, ta karaso.

Gabadaya jama'an garin suka nufi inda Inna wuro take, suka zubawa yarinyar ido,

Kuka yarinyar ta fashe dashi.

Hatake aka fara ruwan sama, Wanda yake hade da iska Mai ni'ima,

Farin ciki ne ya lullube fuskokin su, cikin jin dadin Ganin wannan ranar, Mai gari yace, Dama zan sake Ganin anyi wa wannan kauyen ruwa, tabbas yarinyar nan yar sa'a ce,

Kallon idanuwan yarinyar wanda suke Ars, Inna wuro tayi , ko kadan babu tsoro a fuskan yarinyar,

Murmushi inna wuro tayi, sa'anan tace, tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Kai ya ubangiji, wannan yarinyar, itace zata kawo karshen zalinci a wannan karnin.







COMMENT & SHARE PLS

ALKALAMIN 🖊️
AISHA M.B🌺






BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
RAYUWA DA MACIJIYA FREE PAGE 2⃣➡3⃣
WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA

-------------------------------------
Kallon sarkar dake wuyan jaririyar Inna wuro tayi, taga an rubuta (JODA,)murmushi tayi sa'anan tace tabbas kinci sunan ki Joda, amma daga yau, sunan ki zai kasance DU'A, domin kece wacce Allah ya turo domin kawo mana agaji cikin wannan kauyen Gembiza, daga yarinyar Inna wuro tayi wacce sai kuka take ta faman yi, Inna wuro tayi tace , wannan yarinyar daga yau sunan ta zai kasance DU'A ne,
Farin ciki ne ya baibaye fuskokin su, jama'an garin suka hada baki wajan fadin, barkanki da shigowa kauyen Gembiza Du'a, muna farin cikin bayyanar ki a garemu, Allah ya baki abunda kike son cimma na alkhairy nan gaba, Allah ya Kare mana ke, kuma Duk rintsi Duk wuya, bazamu taba barki bah, har sai numfashin mu na karshe.

sosai jama'a kauyen, ke farin cikin sake haduwa da irin wannan ranar da ruwan sama zata zubo a yankin su.
Mai gari yace tabbas wannan babbar kyauta ce daga ubangiji, shekara da shekaru kenen muna fafu tuka wajan neman ruwa, amma Zuwan wannan jaririyar Allah ya sauko mana da ruwan sama, tabbas wannan yarinyar yar sa'a ce Kuma yar baiwa, Zuwan ta wannan garin bah karamin kawo cigaba zai yi bah .
Bamusan Wacece wannan jaririyar bah, kuma bamusan daga ina ta futo bah amma tabbas wanda ta haife ta, ta haifo mana da kwarin gwiwa, sa'a da Kuma kwanciyar hankali.
Hamdalah gabadayansu sukayi, babu bata lokaci, suka koma cikin garin, suna shewa, Tareda fara tsalle tsalle, farin ciki lullube a fuskan kowanne su,
Tara tulun su kowa yayi, suka ajiye a inda ruwa ke zubowa,
Wanka sukayi wa jaririyar, sa'anan suka saka mata kayan Fulani, Wanda suka karbi jaririyar ciff kamar an auna ta.
Washe garin ranar, Ard'o da Kuma makarabban sa suka futa domin yin farauta kamar yadda suka saba,
Daya daga cikin su ne ya hangi, ciyawa tafara tsirowa daga cikin kasan, ihuu ya kwalla, wanda yasa mutanen yankin suka Fara futowa daga cikin mu'alinsu.
Ard'o yace sani meyafaru? Sani yace ciyawa ta Fara tsirowa a gonar mu, shekara nawa kenen, rabonda muga kasar mu a jik'e ,amma yau Kalli ciyawa mah ta tsiro, acikin kasar.
Hamdalah gabadayansu sukayi, suna mai godiya wa Allah,
Ard'o yace, yanzu kenen zamu iya Shiga gona muyi shuka, Allah mun gode maka, shekaru kenen, da gonan nakin suke a bushe, yau Kuma ga gonar mu a jike sharkaff.

Malam liman yace, inda Allah ke ikon sa kenen, babu abunda ya Kama ta muyi sai godiya ga ubangiji, Wanda yasa muka sake yin ido hudu da wannan ranar wanda ya sanya kowannen mu acikin kauyen nan farin ciki.
Inna wuro yaushe wannan matar zata farfado, Kallon matar Inna wuro tayi tace, dije, sanin Yaushe zata farfado wannan bah a hannu na ya rataya bah, ki Bari Allah yayi ikon sa, wannan matar bah Lallai ta farfado nan kusa bah, saboda ta fada doguwar suma
Sai dai aci gaba da kula da ita, acikin wannan bukkar, har sai lokacin da Allah yayi zata farfado.

Dije tace, Tom shikenen Inna wuro, barana tafi, zanje na dora girki, Kallon yarinyar dije tayi tace, Tom Dan Allah Inna wuro a tayamu kula da Du'a. Murmushi Inna wuro tayi tace,

Idan ban kula da ita bah wa kike son ya kula da ita, karki damu dije itama kamar yarmu take, kulawa da tarbiyar da zamu iya bawa y'ay'an mu, aka itama zamu bata, insha Allah bazan taba bamban ta, ta bah da sauran yaran garin nan, ba iya ni kadai bah, har mutanen kauyen nan.

Tom shikenen barana jee, tashi dije tayi ta fuce daga bukkar , bayan fucewar dije, Inna wuro Ta dauki Dua, tareda dora idanuwanta akan yarinyar tace, Dua, na miki alkawarin cewar zaki ga gata iya gata, zaki samu kulawa wacce koda wacce tayi sanadin kawo ki duniya bazata iya baki bah, zan kula da rayuwarki gabadaya. Ina matukar sonki y'ata. Tana kaiwanan ta rungume yarinyar.



BAYAN SHEKARU BIYAR.
Mai gari wannan yarinyar tabbas tana da kokari a boko harda islamiyya, amma abunda yake yawan ziyartar ta , ya fara yawa, ana cikin karatu kawai saidai muga, tana magana ita kadai kuma idanuwanta su sauya lauli su koma Ruwa toka,

Dan jimm Mai gari yayi, yana mai fadin, y'ata Dua zonan, Hatake naga yarinyar da bazata wuce shekaru biyar da haikuwa bah, ta nufa inda Mai gari yake a Zaune, kyakyawa ce makurar kyaun gaske, kana ganinta Kaga cikakkiyar Shuwa. fuskanta a hade, babu walwala a tattare da ita.
Ta karasa inda Mai gari yake a Zaune.

Mai gari yace, y'ata Dua menene ya faru,? Meyasa kike magana ke kadai?
Motsa Dan karamin lebenta tayi cikin muryar, yara tace, Baba zuciyata yana fadamin cewar wani mummunan abu na shirin faruwa a wannan kauyen. Kuma ina iya ganin abunda Bakua gani ,

Inna wuro tace, mee, kike gani? Kallon ta Dua tayi tace, ina ganin Macizai.

Manage page pls
Comment & share
ALAKALAMIN
AISHA M.B (BABY ISHA)


BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍🐍
PAGE 3⃣➡4⃣

WRITTEN & DIRECTED 🔏
AISHA M.B (BABY ISHA)

PEN🔏 IS MIGHTER THAN SWORD🗡

-----------------------------------------
Binta Inna wuro tayi da kallo, Cikeda jin mamakin kalaman ta tace, Joda me kika ce? Macizai fah kika ce, a ina kenen?

Shiru sukaji tayi, cikin kankanin lokaci, jiri ya d'ibeta ta, Hatake ta fadi a wajan sumammiya.
Cikin tashin hankali mutanen kauyen baki daya, su kayo kanta!, daukar ta inna wuro tayi, ta nufi dakin magani da ita

Kwantar da Joda Inna wuro tayi, sa'anan ta yayyafa mata ruwa, babu bata lokaci, Joda ta tashi. Hamdalah Inna wuro tayi,
Babu bata lokaci bacci yayi hawan gaba da ita.

Tashi Inna wuro" tayi, Tareda fucewa daga dakin, bata nufi koh ina bah, sai fadar Mai gari, da sallama ta Shiga, yayinda yan kauyen suka bita da kallo, Damuwa bayyane a fuskokin su ganin ta yasa Mai garin hanzarin fadin ya jikin Joda"? Inna wuro ta bashi amsa da fadin, da sauk'i.

Hamdala gabadayan su, sukayi. Gyaran murya Inna wuro tayi, sannan tace, Mai gari, ina da wata k'ok'an to, Mai gari yace, menene? Inna wuro ta cigaba da fadin, ina tunanin kamar yarinyar nan akwai shafar aljanu a tattare da ita, saboda ba yau aka fara dawo mana da ita bah, yau ace ta suma, gobe Kuma ace ta na sauya kammani .

Wannan abunda yake faruwa da ita, ya kamata munemi mafuta, saboda kar abun nata yayi tsamari, dan naga abun nata kara harzuka yake. Dan jimmm Mai gari yayi, yana mai fadin, toh me kike so ayi Inna wuro, ke da ni da Kuma wadanan mutanen kauyen, munsan da cewar yarinyar nan, bah yar kauyen nan bane, bamusan daga wace ahali ta futo bah, bamusan sanadin dayasa ta fada a wannan mummunan halin bah. Ga mahaifiyar ta mah rai a hannun Allah, tabbas na yarda da maganar ki, amma kuma wajan wa zamuje mune mi taimako.

Malam liman yace, me zai Hana muje Dajin Jarmuna, domin neman taimako. Zaro idanu gabadayan su sukayi, cikin kidima! da tsoro, Malam liman yace, me kika ce, dajin Jarmuna, wanda babu wani bil Adam dazai Shiga dajin nan ya futo, idan ya Shiga, ya Shiga kenen, saidai buzun shi, bashi bah, dajin Aljanu da mayu, dajin Macizai, wannan bazai yuhuba gsk, nidai ban shirya mutuwa bah

Ard'o yace akane Malam liman Nima ban shirya bah, dajin da babu Wanda yake Shiga saboda hatsarin ta, tabbas akwai magunguna acikin dajin nan, da Kuma magani warke kowane cuta, amma babu Wanda yake da zuciyar dazai tunkari wannan dajin.

Khadija wato matar Ard'o tace, wannan gaskiya ne, amma me zai hana muje wajan, Malam Ali, shine kawai zai iya Sanin abunda ke damun Joda,

Mai gari yace, aba khadija, kin manta gabar dake tsakanin mu da Malam Ali, na nasan cewar bah Lallai ya taimake mu bah,
Inna wuro tace, zai taimaka mana, tabbas ina da tabbacin cewar Malam Ali bazai k'i taimakon mu bah.

Kallon dakaransa Mai gari yayi, sannan yace musu, suje su kira Malam Ali, Mai gari na nemansa, yanzu nan. Babu bata lokaci, dakaran nasa suka nufi gidan Malam Ali.

Cikin kankanin lokaci, Malam Ali ya bayyana a wajan, Kallon Mai gari Malam Ali yayi, sa'anan yace, me Kuma ya faru, koh yau din mah, an kara makala min sharri kamar yadda aka saba.

Kallon sa Mai gari yayi, sannan yace dashi, Aa Ali bah aka bane, na sa a kira ka ne don sulhu, inason wannan gabar dake tsakanin mu yazo karshe, Dan Allah, akawo karshen komai a yau

.Murmushi Malam Ali yayi, yana mai fadin, aini komai ya ruga daya wuce a wajena, saidai Kuma Allah ya kiyaye gaba. Inna wuro tace, Malam Ali, abunda yasa Kaga mun taru Hanan, ba komai bane yasa akan, sai Joda, munason mu ceci rayuwar ta, muna tunanin kamar tanada Aljanu .


Murmushi Malam Ali yayi, yace sun kansu Aljanu basu isa sun tunkare ta bah, shin bakusan Wacece wannan yarinyar bah, itadin daya ce tamkar dubu, yanzu yarinya ce bah Lallai kusan wane irin baiwa Allah ya bata bah, amma kijira nan da shekaru, zaku sha mamaki.

Ard'o yace yanzu me zamuyi tadaina
sume -sumen da takeyi, kuma wani sa'in idan tana kuka, saimu ga za aitayin ruwan sama ruwan bazai tsaya bah, harsai tadaina kuka. Menene zamuyi domin ta daina

Malam Ali yace babu wani abunda zamu iya yi akai, kukan da takeyi Hana ruwan sama wannan baiwar tace daga ubangiji, babu wanda ya isa ya karbe wannan.

Kuma ina gani cewar tabbas wani abun al'ajabi zai faru da yarinyar nan bayan shekaru masu zuwa. Amma kuma a halin yanzu naga rayuwar ta yana cikin hatsari, kuma dole Tana bukatar kariya, saboda Joda bah kowace mutum bace, ta bambanta da sauran mutane.

Mai gari yace, Ali menene mafuta yanzu? Me zamuyi Dan kar rayuwarta yashiga hatsari?

Malam Ali ya bashi amsa da fadin, mafuta daya ce, wannan yarinyar za'a ajiye tane a d'aki, wato ina nufin daga yau, ba za'a Kara barin ta, ta futa koda tsakar gida bah, karatu, ci da sha, futsari, komai, zai kasance Tana yinshi ne a d'aki, yayinda za'a yi mata ba aya a dak'in da za'a saka ta., za'a barta ne a dakin na wajan shekaru sha biyar masu zuwa,

saboda ranar da zata cika shekaru ashirin a duniya, ranar abun al'ajabi zai faru wanda koda wasa, baku taba tsanmmani bah, a ranar ne asalin Wacece ita zai bayyana, ikonta, da baiwar ta, zasu habbaka a lokacin ne zata fara yin aikin da ya dawo da ita duniya,

Bazata sarara wa azzalumai bah, sufarta, halittar ta, yanayin ta, zai sauya saboda lokacin zata kasance asalin DU'A dinta.
Cikin rashin fahimtar magannanun shi, Inna wuro tace, bamu fahimci abunda kake nufi bah, Malam Ali, murmushi Malam Ali yayi sannan yajuya ya Kare wa kauyen kallo, yace, na tausaya muku, bazaku fahimta bah sainan gaba.

Zira hannun sa yayi cikin jakar sakar sa, ya ciro kullin magani, sa'anan ya mikawa Inna wuro, karba Inna wuro tayi, Tareda jujjuya shi a hannun ta tace, wannan fah?

Malam Ali yace, wannan maganin kariya ne, a Duk lokacin da kika ga tana wani irin abu, koh Kuma, ta suma, toh ki dunga bata wannan maganin insha Allahu za'a samu sauk'i.

Ard'o yace, amma Malam, matan kauyen mu shekaru sha daya, sha biyu, wasu mah basua Kai wa aka, muke aurar da su, taya Kuma zamu bar Joda acikin daki na wajan tsawon shekaru sha biyar, ai kawayenta mah a lokacin suna da yara, ina ganin kamar a barta basai an rufe ta bah.

Murmushin takaici Malam Ali yayi, yana mai fadin, idan babu lafiya Hana yin aure ne? Idan babu rai zaka yi aure ne? Wannan abunda za'a yi badan aceci rayuwarta daga, mugun abunda zai tunkare ta bane, ku kuka sani, Kuyi yadda kuka gadama, nidai na ruga danayi iya bakin kokarina, an wuce gurin.

Yana kaiwanan ya juya da niyan tafiya, kamar ya tuna da wani abu, sai Kuma ya juyo. Yace na manta, ban fada muku abu daya bah, Duk wani da namijin da ya fara ambatar mata Kalman soyayya, koh akasin aka, toh shine zai kasance mijin ta, na har abada. Amma sai wanda da gaskiya yake sonta bada yaudara bah, shine kawai zai aureta, kuma shi zai yi sanadin yadda zatasan Wacece ita daga wane ahalin ta futo, yana kaiwanan ya bar wajan.

Barin shi keda wuya, Mai gari yasa aka rufe taro kowa ya watse.

Inna wuro bata nufi ko ina bah sai cikin gidan ta,
Kallon Joda Inna wuro tayi, tace Joda, mene yake faruwa dake aka, meyasa kike suma a makaranta, bayan kece dogaran wannan kauyen, ke zamu tura makaranta domin ki gyara mana kauyen mu, meyasa Kuma akan zata dunga faruwa dake.
Daidai lokacin Joda ta bude idanuwan ta a hankali,
Cikin rashin fahimtar maganar Inna wuro, Joda" ta

9 Comments On RAYUWA DA MACIJIYA
avatar
falmata-3

8 months ago

Reply

Please ineed the next page

avatar
hausa

8 months ago

Reply

Replying to falmata-3

Contact this number for complete09130398321

avatar
aishatu-sabiu

8 months ago

Reply

Next page Wanda ba free b pls

avatar
hausa

8 months ago

Reply

Replying to aishatu-sabiu

Contact this number for complete09130398321

avatar
rukayya-6-3

8 months ago

Reply

Please next

avatar
hausa

8 months ago

Reply

Replying to rukayya-6-3

Contact this number for complete09130398321

avatar
arwanatu-jafar

6 months ago

Reply

Nice novel Please complete 09169118280

avatar
arwanatu-jafar

6 months ago

Reply

Nice novel Please complete 09169118280

avatar
arwanatu-jafar

6 months ago

Reply

Nice novel Please complete 09169118280

Please Login or Register in order to submit comment