Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacin rai riya ta bata masa rai mutum ne meson addininsa da kishin kasarsa da kuma son yaga ya kwatarwa mutum yancinsa amma tabbas indai har se yayi wasa da addininsa sannan ze temaki riya to baze taba iyawaba...

Kwananshi 2 a mumbai ya dawo gida nigeria wanda tun a wannan lokacin ya rufe babin riya sharma daga cikin rayuwanshi


Kuka takeyi sosai ta matse jikinta a jikin kujera sam rayuwar gidan major salman bata yiwa suhana dadi duk data kasance yarinya karama amma tunani dayawa yana neman yi mata illa a rayuwarta da farko tayi tunanin ta samu me temaka matane se daga baya ta gane kawai ta samu wanda zeci gaba da wahalar da rayuwartane ya kuma ci gaba da bata tsoro a rayuwarta...banda abinci da sutura da salman yake bawa suhana sam baya kulata ko kallon arziki bayayi mata hakane yasata zabarwa kanta rayuwar kuka..seta wuni tana kuka babu abinda ya dameta

Ya dawo daga office duk ya gaji ya wuceta tana kukan nata data saba har yayi wanka yaci abinci suhana batada niyyar dena kukan yasashi zuciyarsa mugun jin haushi tayi mummunan baci....kansa tsaye yaje jikin kujerar ya fincikota ta fadi kasa abinka da siririyar yarinya tuni duk ta firgice ya dubeta cikin tsawa....

What are you crying for?kukan mene kikeyi tell me fadamin mana ina sauraronki.....kin rasa cine ko kin rasa sha ne ko sutura kika rasa amma zakizo ki sani gaba kina kuka yau sekin gaya min abinda yasa kike kuka ko na yankaki a gidannan

Habawa nan fa suhana aka sake rikicewa ganin ran soja ya baci tuni ta tsuguna tana yi masa magiya yayi hakuri zata fada masa

Okay ina jinki maza ki fadamin ko ke wacece

*SUHANA ZARBAN*
Suhana yarinyace karama yar shekara goma sha 13 sedai suhana tana da karfin basira da kuma tsawon kafa don inka ganta se kace mata takai shekara 15.....yarinyace mai tausayi da jin kai duk wani na kasa da ita....suna zaune da iyayenta a garin nasu me suna addis zuru chan gaba da agadez mahaifin suhana zarban sadakar yalla ne itako mahaifiyarta buzuwace sun taso cikin halin kuncin rayuwa don kaf danginsu sun gujesu sbd rashin wadata da suke fama dashi....kawun suhana ne guda 1 yake iya zuwa gurinsu shima sbd yanzu mahaifin suhana ya samu aiki a wani company dake chan garin maradi tuni ya fara dawo da arziki don yana da shanu da rakuma kamar guda 6 dalilin hakane yasa kaninshi tasi ya dawo garesu babu yanda beyi dasuba don rabasu da wannan kayan da yake mahaifin suhana ya gane aiko baya sakar masa fuska shine ya hada baki da wasu yan tada kayar baya na garin akazo aka kashe mata iyayenta da dan uwanta tilo zakwan wanda datafiso a rayuwarta suhana batada kowa se Allah batasan kowaba se kawunta wanda tuni ta dauki alwashin idan ta ganshi seta kasheshi.....

Kuka takeyi sosai abinka da farar fata fuskar nan tayi jawur........cikin sauri major ya riko hannun suhana wanda tuni shima fuskrsa ta jike da hawayen da bemasan suna zuba ba

I'm very sorry suhana....kiyi hakuri daga yau na dena saki kuka zan dinga saki dariya kullum nayi miki alkawari zan dinga kula dake kullum safe da dare zan dinga baki lokacina suhana nayi alkawari kinji......

Toh naji amma yauche zaka fara min dariya in gani...

Silent smile ya kakaro wanda bekai zuciba donshi tunda ya taso dariya ko murmushi be dameshiba sbd takaicin tsanar da mahaifinsa yayi masa kuma ya koreshi daga cikin family dinsa.....

Da kanshi ya tashi ya shiga kitchen ya zubo mata abinci ya dauko ruwa da lemo me sanyi ya ajiye mata a gabanta....

Maza sa kici abinci kinji banso ki dinga zama da yunwa kinga duk kin rame ko

Na koshi tace sannan ta kawar da kanta daga kallon abincin

Nasan kin koshi amma ki daure kici ko kadan ne kinga ke bakison cin abinci fa ko

Ni fa na she maka na kochi indai ni daya zanshi abinshin toh na kochi nina saba shin abinshi da yayana zakwan bana iya shi ni kadai

Maganar suhana tana mutukar birgeshi murmushi yayi yace okay to naji daga yau tare zamu dinga shin abinshin nima tare dake

Itama murmushi tayi jin ua fara iya yaren nata......abincin da major yafiso ya dafa white rice da soup din kayan ciki don haka ya bude ciki yai ta ci a dole yasa suhana itama taci dayawa.....

Karfe 8 na dare ya tuna da yau be he gun Emili ba don haka cikin tashin hankali ya mike ya dauki mukullin sa ya fita......


Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
page 25-30

*Na*
*Maman hanan*

*Thank you guys for the love and care...Thank you once again and a big hug to you all...*

Baifi 30 minutes da fita ba suhana taji motsin mutum a cikin gidan ba karamin tsoro taji ba don ita tunda ta shigo gidan bata taba ganin major yayi wani bako ba da har ze shigo masa gida kai tsaye asalima dukanan kofofin gidan suna tare da password ne ita kanta kofar dakin tane kawai ya fada mata password din amma sauran dakuna baxata iya kai kantaba....hakan ne yasata firgita

Budurwa ta gani wacce bata wuce shekara 24 ba kyakkyawar gaske sedai shigar da tayine kawai zeyi saurin baka cewa arniya ce amma sam babu alamun haka a fuskarta......Zee kenan tsohuwar budurwar major da suka dade suna holewarsu sunyi mutukar shakuwa don gidan major ya zame mata tamkar wani gidane wanda ko idonta a rufe yake zata iya shigarsa kai tsaye....

Ta window suhana ke lekenta...dakin major ta wuce straight kanta tsaye hakan ya tabbatarwa suhana lallai wannan yar gidance ko kuma matarshicema oho tunda ance a nigeria baka gane matan aure da yammata da haka taci gaba da tunane tunanenta har bacci ya kwasheta....

Rashin ganin major ne ya batawa zee rai ta dauko wayarta ta fara laluben number sa A kiran karshene major ya dauki wayar

Hello haba major inata kiranka no picking

Wow special suprise kar kicemin kin dawo dai

Yeah na dawo saukana kenan a airport yanzu haka ina bedroom dinka ina jiranka

Gaban major ne yayi mummunar faduwa wanda yasashi harda kwarewa....cikin sauri yace bedroom dinafa kikace zee kina nufin kina cikin gidana

Yes mana ya naji ka wani rikice ne nidai kayi ka dawo ina jiranka you know how much badly i miss you fa

Ok yeah i know zee gani nan zuwa just bani some minutes....

Addu'a yakeyi Allah yasa zee bataga suhana ba don idan har taga suhana zata iya kasheta anan take zee mugun kishi gareta sam batason taga major tareda kowacce mace itadai tafison ta ganta daga ita seshi shiyaasa ma major sam baya kula mata zee kadai itace budurwarshi....sunyi tsawon 4 years suna tareda zee suna matukar son junansu zee itace mace ta farko da major ya taba disvirgin a rayuwanshi kuma itace mace kadai da take biya mishi kowacce irin bukata shiyasa ko aure babu a budget din major zee kawai ta isheshi rayuwanshi....taje Scotland ta dan samu hutu na 2 months yanzu haka ta dawo....

Gudu yakeyi kamar ze tashi sama da yake darene titin ko jama,a babu sosai cikin 7 minute's ya karaso gidan...jin be fara jiyo hayaniyar zee ba ya tabbatar mishi da bataga suhana ba duk yanda akayi

Yana shigowa dakin ya tararda ita a kishingide kan gadon tana charts a wayanta.. Forehead kiss yayi mata tareda shafa mata ciki yace you are welcome babe

Cikin murya kamar me shirin kuka tace thank you sweetheart.... Gani tayi ya sake yi mata kyau ya kara haske kamar balarabe ya danyi yar kiba kadan tace you looks hot my man.....bata jira me zeceba ta saka bakinta a nashi suka fara deep kiss

Seda ya tabbatar da zee ta samu nutsuwa kamar yanda take bukata sannan ya tashi ya fito ya janyo mata kofa yasa lock....dakin suhana ya nufa

Baiwar Allah!Baccinta takeyi sosai ta kudundune cikin blanket da alama sanyi takeji jikinta se rawar sanyi takeyi....tabbas garin ana sanyi sosai gashi Ac din dakin shima a kunne yake....

Tausayin suhana ne ya kamashi yasan bata iya kashe Ac dinba shiyasa ta barta haka har sanyi yana neman illatata...kashe Ac din yayi sannan ya dawo ya zauna kusa da ita ya dan fara bubbuga ta alamar ta tashi a hankali

Firgigit ta tashi ta fara laluben waye yake tashinta da daren nan tasan dai major baze taba zuwa ya tashetaba

Shhhhh!!nine nan karki tsorata kinji

Daga mishi kai tayi tace toh

Sannan yace kinga mamana tayi tafiyane dama kuma yanzu ta dawo don haka ki dinga boye kanki a daki karki kuskura ki bari ta ganki zan dinga ajiye miki komai sannan zan chanja miki pin din bude daki da rufewa kinji kar kiji tsoro bazata dadeba zata tafi kinji

Toh kawai take ce masa aduk abinda ya fada...seda ya tabbatar da ta tsorata sosai kuma babu abinda ze fito da suhana sannan yayi mata addu'a ya koma dakin nashi

Zee har tayi bacci kafin ya koma don haka shima kwanciyar yayi ya janyota jiknsa ya rufesu da blanket...


Muje zuwa
Maman hanan da unborn😜
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 30-35

*Na*
*Maman hanan*

*Before i proceed let me use this opportunity to wish this cute sister of mine Zainab Abdoullah yarima a very happy belated birthday to you age with grace wish you long life and prosperity.... Enjoy your day kiyi komai ba komai bane ki mari uban kowama in sukai magana just tell them it's your day....Allah ya kara nisan kwana da yawan rai me albarka kita haifo mana yara dozen....i love you🤼‍♀🤼‍♀❤*


*********
Kwance suke cikin blanket zee ta sake manne major tamkar wani wanda ze gudu tana mutukar sonshi sosai don tasha wahala kwarai kafin ta samu shiga gurin major salman....kallonshi tayi sannan tace

My man ina ganin lokacin da zamuyi aurefa yayi kaga tun last year mukayi shirin aurefa kace mu bari se this year so ina ganin mu fara shirin auren nan kawai

Gabanshi ne ya fadi amma da yake major gwarzon namijine se ya nuna sam be damuba yace mata....haba zee ki duba yanayin da nake cikifa kike kirawomin sunan aure yanzu banida kowa gaba daya daddy yayi wa duk wani dan'uwana katanga dani yace duk wanda ya nemeni se ya tsine mishi to tayaya kike tunanin har inada wani waliyi daze yimin aure yanzu ina ganin mu sake kara lokaci kadan mu gani...

Alright amma my man meyasa baza kaje ka bawa Daddy dinka hakuri ba ina ganin ya kamata ka bashi hakuri abinda ya faru shekara shida daya wuce amma ace har yanzu baka nemi gafararsaba

Karki damu zee On 1st October akwai celebration da za,ayi a villa na independence day na samu labarin Daddy yana daya daga cikin guest na Mr president i will try to make it zanje na samu daddy achan

Perfect! Hakan yana da kyau naji dadin tunaninka my man ...sannan don't forget remain 5 days to my birthday zanyi celebration a cilantro club dafatan baza kayi disappointing dinaba kamar yanda ka sabayi...ta karasa maganar ranta a bace

Dafo ta yayi ta baya yace never mind barbie zee zanyi kokari inga naje gurin insha Allah amma zee meze hana kiyi celebration alone kinsan banson kina zuwa clubs dinnan i hate it....ni gaskiya bazan iya zuwa cilantro club ba karki manta cilantro ba wajene na yara ba duk wani babban mutum a kasar nan cilantro club shine gurin zuwansa don holewa don hka a gurin zan iya haduwa da abokanan daddy na don haka gaskiya i don't think zan iya zuwa.....

Da kyar dai zee ta samu ta shawo kanshi ya yarda zeyi attending birthday party dinta sannan ta tafi.....

Tana fita kamar jira yake ya shiga dakin suhana da sauri.....zaune ya tarar da ita akan gado tana ta kallon wani series film a zeeworld da alama film din yanayi mata dadi....

Da sauri ta tsugunna ta gaisheshi cikin ladabi ya amsa mata sannan janyo stool din kusada ita ya zauna.....


Ayi hakuri da wannan


Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 35-40

*Na*
*Maman hanan*

********
Emili abin duniya ya fara damunta don tunda salman ya fuskanci bawai sonshi takeyiba sbd Allah kawai tana sonshine saboda kudinshi tun daga wannan lokaci tausayinta ya fita a zuciyanshi yanzu salman se yayi morethan 2 days be je ya duba lafiyartaba tunda kudin takeso to gashinan ya ajiye mata komai don yaje mata matane a zuwan a barrack yake kwana...

Suhana ko yanzu ko palour bata fitowa kamar matar kulle kullum tana cikin daki tsoronta daya kada maman salman ta ganta kamar yanda yai mata karyar fada mata haka tun daga lokacin rayuwarta a boye takeyi a gidan don ita zee idan tazo seta kwana 2 gidan major batare da taje ko'inaba don haka takura tayiwa suhana yawa


*1st October 2017*
Shine yai dai-dai da ranar independence day na nigeria dukanin wani dan kasar nigeria yana cikin halin farin ciki banda major salman da yake cikin tashin hankali wanda tun shekara 6 da suka wuce yake cikinsa...yauce rana ta farko da ze tinkari mahaifinsa don neman yafiya da sulhu

Sanye yake cikin suit da ko makaho idan ya shafa jikin major a cikin suit dinnan yasan ta zauna masa....ya taje gashinsa ya kwanta luf luf ya sanya black shoe da yayi matukar karbar wankan nasa tareda golden watch a hannunsa me hade da zobe tamkar a hannun nashi aka haliccesu......

A hankali yake tafiya a presidential street babu karar komai se karar motan sojoji da yan sanda ke tashi...be wani sha wahalan shiga villa ba domin duk inda yaje ID card dinsa yake nunawa domin shi kansa ya isa ya bawa gidan cikakkiyar kulawa...

Yana zuwa yayi parking ya tsaya yana kallon mutane na shige da fice cikin farin ciki da annushuwa....Daddy dinsa ya hango ya fito daga motanshi sanye cikin light blue din shadda tayi masa kyau matuka sedai yafuskanci rama a tareda mahaifin nashi amma haskensa yana nan da kyansa me shiga rai dako yarinya yar shekara goma sha biyar se tayi sha'awar auren munir matawalle koda na kwana 1 ne,,,,,,,,,wasu zafafan hawaye ne ya zubowa major salman a fuskarshi adai-dai lokacin da yaga Mr president yana gaisawa da Daddyn nashi sannan suka shiga tare..

Tsahon 2 hours major na zaune yana jiran fitowar Daddyn nashi.....

Cikin fara,a Munir matawalle ya fito yana tsananin fadada murmushi a fuskarshi ya nufi inda yai parking motanshi don tafiya
Wannan ya bawa major kwarin gwiwar saurin fitowa don haduwa da mahaifin nashi

Har kasa ya tsugunna ya gaisheshi amma ko kallonshi daddy din nashi beyiba se cigaba da tafiya da yakeyi da alamun bacin rai a fuskarshi hakan be hana major ci gaba da binshiba yana kiran Daddy,Daddy please ka saurareniba Daddy

Wani wawan mari ya sakarwa dan nashi tareda pointing dinsa da hannu yace mishi

Karka sake cemin daddy tuni na cire fuskarka da sunanka daga jerin ya'yana kuma idan kaci gaba da bibiyar inda nake to ina tabbatar maka da tsinuwata a tareda kai kwanann ka fita a idona karka sake nemana ko wani daga cikin ahalina idan ba hakaba seka raina kanka shashashan banza da wofi...

Ganin yana kokarin tara masa mutane yasa salman saurin shiga motarsa ya wuce shima munir matawalle motar tashi ya shige ya muzurai ya wuce.....

Tafe yake a hanya soyayyar mahaifinsa na sake dawo masa sabuwa....hawaye masu zafi sukaci gaba da zuba daga idonsa....

Shima Munir matawalle addu'a yakeyi tunda ya rabu da salman to kada Allah ya sake hadasu amma yau Allah ya nuna masa dan nasa ya taso masa da ciwon da ya dade yana damunshi a zuciya tuni zufa taci gaba da zubo mishi



Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 40-45

*Na*
*Maman hanan*

*I dedicated this page to everyone that read this page from now till tonight....Major salman fans👌🏻ana mugun tare irin sosai dinnan*


*My cute pie hanan i love you too babe...May Allah continued shower you his blessings to your entire life😘My beloved daughter muah*


********
Jikinsa babu kwari ya shiga katafaren gidan nashi be saurari kowa ba ya wuce sama fuuuu kamshin turaren babbar rigarsace kawai yake tashi ko babu tambaya kasan cewar ran munir matawalle a mugun bace yake.....

Haj zuwaira ce ta hada ido da haj rakiya bata kanta mata ba ta mike tsam ta hau upstairs din don zuwa jin meya faru ran megidan nata yake a bace....a tsaye ta tarar dashi yana kaiwa da kawowa a dakin nashi zufa duk ya bata masa kaya......cikin tashin hankali ta karasa gurin nashi ganin yanda yake kaiwa da kawowa ba tareda yasan ta shigo dakin ba

Haba Alhaji me yayi zafi haka kake faman gumi ka kasa zama meyake faruwa ne

Bece mata komaiba se tsayawa yai yana kallonta jikinsa a sanyaye

Tace tambayarka nakeyi Alhaji ka fadamin me yake faruwa ne wai

Rufe kofar hajiya rakiya ce ta sasu duka juyowa don itama basu san ta shigoba....ganinsu tsaye kamar wasu zakaru ne yasata itama karasowa jiki a sanyaye ta taba haj zuwaira tace lafiya na ganku haka

Cikin zafin rai Munir matawalle ya dubi matan nashi a zafafe yace ku ficemin ku bani guri bana bukatar ganinku dukanku ku ficemin a daki

Haj zuwaira tayi murmushi me boye dukanin wata damuwa sannan tace tabbas nasan akwai abinda kake boye mana kuma duk yanda akai babban alamarine kuma ka sake tunani nasan salman ka hadu dashi yau tunda naga yanayinka ya sauya akwai mummunan abinda ka hadu dashi yau kayiwa kanka fada alhaji ka rabani da yarona guda 1 dana mallaka na hakura wanda yanzu bansan wacce duniyar yakeba shekara 6 kenan ka taimaka ka yafewa salman muma kuma ka bamu izini mu nemeshi dan Allah alhaji

Bazan hakura dinba nace bazan hakura dinba in haifi yarona kuma jinina amma ace shine ze kaini gurin hukuma kuma ya zamo shine sanadiyyar karyewar arzikina da lalacewar tattalin arzikina taya zan yafe masa ni ko zancen yaron banaso kuma har yanzu ina kan bakana bazan taba yarda wani nawa ya kusanci inda salman yakeba har abada bazan taba yafe masaba....yana gama fada yayi waje matan nashi suka bishi da kallo cikin tashin hankali tuni hawaye ya fara zubowa haj zuwaira...



Salman na shiga gidan nashi hannunsa rike da suit dinshi ya shiga dakinsa ya fada kan gadon nashi kamar me shirin kuka...sedai cikin rashin sa,a yaga zee ta shigo dakin kamar wacce take jiran shigowarsa....

Ayi hakuri da wannan......

Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 45-50

*Na*
*Maman hanan*

*Always love,love,love Omg thank you for the love and support guys masha Allah😜haters i will be back to you soon i'm just here busy with my lovers joor.....team major salman❤👌🏻*

********
Zama tayi a gefenshi sannan ta dafashi tace my man yanaga ka dawo ranka a bace instead na ganka kana murmushi kana murna

Cikin damuwa ya fitarda wata zazzafar iska daga cikin bakinsa sannan yace barbie zee daddy yayi rejecting apology dina...yayi insulting dina morethan the way you think ya nunawa jama'a cewa niba danshi bane...gaba daya kaina ya kulle i have no idea

Tausayinsane ya kama zee ta sake rike mishi hannu a karo na 2 tace kayi hakuri my man take it easy komai ze zo da sauki ka hakura ka bari daddy ya sake hucewa seka sake tunkarar zuwa gurinsa....

Hawaye ne tuni suka fara zuba daga idon major salman sannan yace haba zee look deeper to my eyes.... U can read alot of worries from my eyes....i need to stay with my family karki manta 6 years yau bana tareda kowa a cikin yan'uwana da dangina hatta friends dina duka na gujesu sbd kowa yana ganin banyi dai-daiba taya zanyita zama haka ba tareda kowaba ina cikin damuwa sosai...zee i love my dad morethan everything i cant live without him...i am missing my mom taya zan kwantar da hankalina

Nasani my man amma ka kara hakuri zamuyi wani abu akai...da yake zee muguwar shu'umace tuni ta mantar da salman komai suka shagala..........

Se karfe 6 na yamma sannan zee ta tafi hakan ya tunawa major yau be saurari ma duniyar da suhana take cikiba....bayan ya iddar da sallah ne ya karasa dakin nata

Kwance ya tarar da ita tana ta rawar sanyi jikinta yayi zafi sosai kamar wuta da alama bata cikin hayyacinta.....ba karamar firgita major yayi ba ganin halin da suhana take duk ya rikice yama rasa taya ze dauketa don gani yakeyi koya ya dauketa zafi zataji....a hankali ya dauketa ya fita da ita ya sakata a mota don kaita asibiti

Har yayi warming din motar seya lura da babu wadataccen mai a cikinta.....da sauri ya juya ya koma ciki don daukan wani key din motar...

Har seda ya kunna motar sannan ya fito don dawo da suhana cikin daya motar sedai abinda ya firgita major shine ya sashi bude baki kamar wani wawa😳babu suhana babu dalilinta a cikin motar babu inda be duba ba a parking space din gidan amma bega suhana ba.....da gudu ya koma gidan yayi iya bincikenshi amma bega suhana ba....

Kamar wani dan karamin yaro haka salman ya dinga bincika kaya daga gidan yana kiran suhana hatta cikin wardrobe seda yai kacha kacha dashi babu alamar ganin suhana....

Waje ya fito cikin bacin rai tareda tashin hankali a tare dashi idanunshi sunyi ja kana ganinsa kasan allurar soja ceta motsa😜....

Gaba daya ma'aika da securities din gidan ya tara amma sam sunce basuga alamar shigowar kowaba sedai idan suhana dince ta gudu da kanta itama kuma basuga fitar taba....

No never.....suhana bazata taba guduwa daganan ba batada kowa da zata gudu gurinsa....suhana bazata gudu ta barniba tasan inasonta.....inajin suhana a cikin jikina bazata taba guduwa ta barniba

Daya daga cikin yaran nasane yace cikin jikinka kuma sir....

Se lokacin ya lura ashe zancen da yakeyi a cikin zuciyanshi bemasan ya fitoba anajinsa

Cikin tsawa ya dubeshi yace yes cikin jikina nace.....so what shashashan banza da wofi kuna cikin gida ace an rasa yarinya.....to wlh kuje ku nemomin yarinyar nan kafin nan da safiya idan ba hakaba a bakin aikinku.....sakarkarun banza da wofi wayanda basusan amfanin uniform dun da yake jikinsuba maza kuje ku samomin ita kafin safiya

Tuni suka sunkuyar da kansu kasa tareda cewa okay sir......a guje sukayi waje don neman suhana duk da su kansu basu taba ganin taba balle susan hotonta....

Se a lokacin ya lura da takalmin suhana guda 1 a bakin motan nashi sunkuyawa yayi ya dauka tareda shiga cikin gidan nashi jiki a sanyaye......



Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 50-55

*Na*
*Maman hanan*

*Wannan page din nakine my fachala zainab Abdoullah yarima keda feedy gora,members of agir🗣🗣 yarfillo,yar balamalle,ladifa and others😜😜😜😂😂😂😂Allah ya kara shiryani kuma amin ya Allah*

*********
*YOBE STATE*
Haba baiwar Allah kin zauna tun dazu kin kasa cin komai ya kamata ace kinci wani abun kinga zazzafi me zafine a jikinki se kisha magani

Wata tsohuwace wacce takai shekara 80 take wannan maganar gefenta jikantane tsugune yake yi mata bayani

Wlh kaka babu yanda banyi da itaba bakiga a yanayin dana tsintotaba kwance kamar gawa don nayi tunanin wlh bata motsi ma kaka ashe tanada rai gaskiya yanzu kasar nan azzaluman mutane sunyi yawa kome wannan yarinyar tai musu da zasu kawota irin wannan daji su yarda ita cikin wannan yanayin da take ciki

Hmmm ai kai dai bari kawai duniya yanzu yarda tayi karanci se addu'a kawai

Haka aka lallaba suhana taci abinci tasha magani cikin yardar Allah da gari ya waye ta tashi jikinta garau ba wani zazzabi

Bayan sunyi breakfast ne da safe nasir ya dubi suhana yace baiwar Allah yana da kyau ki fada mana wacece ke domin muyi shirin maidake gaban iyayenki kinsan batan ya mace ba karamin dagawa iyayenta rai yakeyi ba

Hawayene suka fara zubowa daga idon suhana don yau karyarta ta kare batasan ma ta inda zata fara basu labariba har su yarda da ita.....haka ta daure ta fara gaya musu

Ni bani da kowa se Allah iyayena sun mutu wani mutum guda 1 shine ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment