Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki ganin number mahaifin nashi a jikin wayar zee baro baro babu kunya ba tsoron Allah ta rubuta sunansa complete munir matawalle

Gabanshine ya fadi domin tabbas yasan zee akwai wata munafinci da takeson isarwa

Murmushi yayi me dauke da daukan fansa sannan ya nisa yace zee kenan "don't ever try to enter my garden coz the fruits are not yet been there"

Seda tayi nisa sannan ta duba wayarta bata ganiba don haka cikin gaggawa tayi reverse ta koma gidan salman gabanta na faduwa a tunaninta ze duba mata waya

Zaune ta tarar dashi yana aiwatar da wasu ayyukansa a laptop dunsa ko daga kai beyiba ya kalleta ta shiga dakin ta fito bata tanka mishiba itama illa kiss dinda tayi mishi sannan ta fita

Kansu zee da munir matawalle gaba daya ya dauki zafi sun kasa gane inda salman ya ajiye wayannan takardu ......



Emili zaune cikin kawayenta wanda ko babu tambaya kasan cewa basa tareda mutunci ballantana imani
Karamar cikinsuce ta nisa tace waiko ke emili yanzu haka zakita zama duniya tana nunaki kece matar wanda suke gaba da mahaifinsa wlh kedai kinji kunya

Emili tadan tabe baki alamar she don't care tace ke nifa na fiki damuwa wlhy kawai dai babu yanda zanyine kuma saboda abin duniya nake zaune dashi da babu kudi a hannunsa ai kema kinsan da tuni na gudu kauye

Gaba daya suka kwashe da dariya....lokaci daya kuma suka mike kowacce ta nufi class dinta

******
Jikin suhana kam ya fara sauki sedai kafafuwanta da har yanzu bata iya takawa dasu seda sanda take amfani shima din kadan kadan take takawa har an sallamesu daga asibiti






*Dan Allah ayi hakuri da wannan bacci nakeji😴😴😴😴*

Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*

Page 85-90

*Na*
*Maman hanan*

******
Ina ganin zee baki yiwa gidan salman kyakkyawar fahimtaba shiyasa kika kasa gano inda yasa wannan takardun nashi a tunanina zamanki da salman ya isa ace kin gane dukanin wani sirrikansa amma kin gagara a fadar munir matawalle ranshi a mugun bace

Zee ce ta kalli munir matawallen itama da alamar bacin rai a tareda ita tace wallahi your Excellency nayiwa salman kyakkawar fahimta kuma na fuskanci komai dake cikin gidanshi amma wannan karan na kasa gane wanne irin shiri salman yakeyi da har ze boye wani abu a cikin gidanshi tunda ko yasan babu wanda yake shigar masa gida seni that means yana zargina kenan?No salman baze zargeniba domin be taba kamani da wani akasin abuba maimakon wanda yake tunani

Toh indai hakane na sake kara miki sati 2 kije ki sake shiri sosai sannan ki kawo min dukanin abinda na umarceki.....kudi ya sake bata mai yawa sannan sukayi sallama

A cikin sati 2 da aka bawa zee ta maida hankali sosai wajen gano inda major ke ajiye muhimman takardunsa kuma ta ganosu sedai abu guda 1 ne ta kasa ganewa shine password dinda zatayi amfani dashi wajen bude akwatin nashi....



Kamar yanda ya saba idan ya tashi daga office seya biya gurin emili sannan ya karasa gidanshi....yau ma hakan yayi zaune ya tarar da ita tasa fruits a gaba tanaci tamkar wata sabuwar sarauniya

Guri ya samu ya zauna gefenta ya dan fitar da iska a bakinshi alamun ya gaji

Hararanshi tayi tayi tsaki tace sannu sarkin aiki dama jiranka nakeyi ka dawo don wlhy na gaji niba wahalalliya bace irinka da kullum kana cikin aiki to wlh nina gaji ina matsayin matarka baze yiwu ace bana samunka complete kaman yanda kowacce mace take zama da mijinta to nima ya zama dole ka dinga zuwa gidannan kana kwana aiki aiba hauka bane nina gaji gaskiya

Ohhh keni sa,ankine da zaki dingamin shouting akaina inajin tausayinkine shiyasa har yanzu na kasa nuna miki true colour dina na major salman amma idan kika takuramin da tambaya zanyi kokarin nuna miki kalata ta gaskiya....

Mtsss inka fasa aini kawai kallonka nakeyi har kana da wani abin da zaka fadaminne ainafi kowa sanin true colour dinka....wanene kai banda mara hankali wanda basa zaman lafiya tareda mahaifinsa

Ganin emili na kokarin sanyashi abinda beyi niyyaba ya sashi fita daga gidan ranshi a bace..


Yana shiga gidan dakin barcinsa ya wuce don babu abinda ze iya aikatawa koda ruwa baze iya shiga cikinsaba sedai abin mamaki zee ya gani tareda mahaifin nashi a tsaye suna jiranshi

Kasa magana yai illa pointing din daddy dinshi da hannu da yayi cikin mamaki yace daddy

Shiko munir matawalle murmushi yayi yace major salman nazone har inda kake don yi maka last warning akan ka sakar min mutanena domin kama mutanen da kayi ba karamar asara zaka sani nayiba ina sake gargadinka kuma ina umartarka daka sakar minsu ka cire hannunka daga ciki domin na samu labarin kaine kayi handling case din,shashasha mara hankali kai ko kunya bakaji ace kai kake tonawa mahaifinka a baya asiri da kanka don yanzu sam babu kai a cikin list din yarana

Cikin ladabi yace haba daddy ai kaine ya kamata ace kaji kunya baniba domin irin ayyukan da kake aikawata sam basa dacewa koda kuwa a duniya kawai zamu kare ballantana akwai lahira....daddy karka manta irin ta,asar da kukeyi a kasarnan tamu kune masu karya mana tattalin arziki kisan kai,shigoda miyagun kwayoyi da sanya mana kasa cikin tashin hankali duk kana daya daga cikin masu yin hakan ko kana tunanin don sawa kakeyi ayi kisa shine yake nufin bakada alhakin yin hakan to daddy ka sani kaine me babban lefi kuwa don zata iya yiwuwa shi wnda kasa yayi lefin tilasta mishi kayi.....to ni dankane wanda ka haifa kuma bazan taba bari inganka cikin tashin hankaliba a lahira ya zama dole na temaki rayuwarka kuma na kare kasata a bisa sharudan rantsuwa da nayi lokacin dana farasa kakin sojoji cewar zan rike kasata kuma zan kare kasata dan Allah daddy ka fahimceni ina mutukar kaunarka daddy

Karka sake kirana a matsayin mahaifinka sannan zaka fuskanci hukunci domin nan da lokaci kadan zaka gane yaro yarone koda kuwa ya hau dogon dutse a matsayin yaronshi yake lets play the game.....

Dan Allah daddy try to understand me mana

U have nothing to tell me salman....yana gama fadan haka yayi waje

Salman ko ji yayi kamar ya kashe kanshi ya huta ji yakeyi taya daddyn shi ze fahimceshi se a lokacin ya tuna da zee wacce tai pretending a zuwan itama datazone ta tarar da daddy a cikin gidan

Murmushi yayi na mugunta sannan ya dubeta yace it's ok zee karki wani damu kanki dama zan gaya miki gobe zan wuce yobe an turomin da invitation governor zeyi promoting dinmu sakamakon mutanen da muka kama suna kokarin hallakashi

Amma my man ina ganin kawai ka cire hannunka daga cikin wannan sha,anin nasu inba hakaba fa zaka shiga matsala

Shhhhhh!!!! best wishes kawai nakeso i will never give up



Tun da major ya iddar da sallar asuba be koma bacciba ya fara shirye shiryen tafiya yobe.....kafin ya tafi seda ya fadawa dukanin masu aikin gidan cewar karsu yarda wani bako ya shigar musu gida koda kuwa zee ce karsu kuskura su barta ta shiga

12pm ya shiga garin yobe,yayi lodging a wani hotel kafin 4pm din da za,a basu promotion letter



Albishirinki suhana cewar feedy data shigo a guje

Goro ya akayine

Ashe yau za,ayi wasan sojoji a lonber stadium da karfe 4 nima yanzunan ake gaya min kinji harda governor zezo kinga dama ke meson ganin governor se muje ki ganshi ko

Wani tsalle suhana tayi se a lokacin ta tuna sauran ciwonta na kafarta dabe karasa warkewaba tadanji zafi kadan tareda yin siririyar kara tace assh kinga kinsa na fama ciwona ko kice in tashi tun yanzu in fara shiri don yau kam inason sake ganin governor sosai

Nasir dake tsaye a bakin kofar dakin yace ke suhana karki kuskura inga kin dara koda nan da nan in banda ke sakarai ce kin manta harbin da aka miki a gurin ganin governor din har yayi sanadin rashin zuwa gurin saukar alkuranin ku sannan kizo kina cewa zaki sake zuwa to wlh karki kuskura tunda bakida hankali

ta tuna da kyakkyawan farin cikin da taci karo dashi a cikin rayuwarta ta yarda idan har zata sake ganin salman a gurin koda kuwa shine ajalinta indai yauma zata sake ganinshi to ta amince ta mutu a gurin

Cikin shagwaba tace yaya nasir don Allah ka barni naje kasan inason ganin wasan sojoji kaga wancaan karan ma tsautsayine

Nidai na gaya miki wlhy babu inda zaki karki kuskura naga kafarki a waje balle har kije lonber stadium......yana gama fadar haka ya fice waje

Suhana ko hawayene ya fara zuba daga idonta ta dubi feedy tace kinga yaya nasir ya hanani zuwa ko ki tashi ki tafi ki shirya kuma karki manta kiyo min video da pictures don inason gani

Karki damu kinga ko wayata inada full charge zanyi kokari na dauko miki



Anyi taro a lonber stadium an tashi lafiya ba tareda komai ya faruba......su major salman ansha kyau tamkar balarabe kowaa gurin yabon kyau irin na major salman yakeyi daga ciki ko harda nasir da tuni yaketa faman yi masa video musamman lokacin da major yake karbar award yayi matukar kyau....

Se bayan isha'i nasir ya dawo gidan dakin suhana ya fara shiga domin yasanta da fushi.....cikin murmushi ya shiga dakin amma suhana na ganinsa ta hade rai alamar shagwaba

Nasir yace haba yar kanwata me nayi mikine da ake fushi dani haka

Yaya nasir ba kaine ka hanani zuwa kallon sojojin ba da governor kuma bacin kasan yanda nakeson ganinsu

To yi hakuri ni naje ai saboda na sanyaki farin ciki nayo miki pictures da videos masu kyau a gurin

Haba wow yaya nasir kamomin na gani



Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*

Page 90-95

*Na*
*Maman hanan*


Lah wlhi yaya nasir shine....dan Allah ka kaini gurinsa Allah shine bakaji sunan da yake fadaba sunanshi major salman yaya nasir shine wlh

Cikeda mamaki nasir ke kallon suhana

Shi wa to aini ban fahimcekiba suhana waye kika ganine

Yaya nasir shine wanda aka saceni daga gidansa shekara 5 da suka wuce dan Allah ka temaka ka kaini gurinsa

Allahu Akbar shine abinda nasir keta nanatawa sannan ya dubeta yace to suhana nidai kinsan bansan taya zan sake ganin shiba amma zanyi iyakar kokarina don ganin na sanya ki a cikin farin ciki insha Allahu zanje na samu abokina gobe semu tattauna maganar
Itama kaka banda farin ciki babu abinda takeyi

Da sassafe ko nasir ya samu abokinsa cikin sa,a ya sanar dashi major salman zasu kwana 2 a yobe kafin su wuce zeyi kokarin samo masa adress din gurin da sukayi lodging....

Ranar ko da aka samowa suhana inda major salman yake kar kaso kaga farin ciki a gurinta ji take tamkar an samo mata iyayentane wayanda suka rasu

Bayan anyiwa major salman dukanin bayani akan suhana shima ji yayi kamar ranar sallah don farin ciki ya karbi address din gidansu nasir yayi sallama a zuwan da yamma zezo ya samesu.....

Karfe 5 major ya sauka a kofar gidansu suhana nasir ko ya shigar dashi gidan kowa se farin ciki yakeyi....major kuwa tuni aka rude saboda yaga ruwan kyau dama yasan suhanar tashi kyakkyawace amma yanxu data sake girma kyawun nata ya sake fitowa sosai

Suhana kunya ce duk ta cikata ji take kamar ta nutse kasa don kunyar major takeyi sosai

Ba tareda bata lokaciba major ya fadawa su nasir da kaka muradinsa na auren suhana nan bada dadewaba kuma ze barta anan har ayi daurin aure se ya tafi da matarshi.....haka ko suka amince

Soyayya me karfi tsakanin major da suhana kafin ya tafi seda ya siya mata waya da zasu dinga yin communicating da ita banda uban kudin daya cikasu dashi kowa se albarka yake sa masa.....

Zuciyarshi ta fara samun sukuni tunda ya samo suhana don haka with his confidence ya koma abuja

Gidan Emili ya wuce duk da darene amma yana da kyau yaje ya ganta tunda ya kwana 2 baya garin

Master key dinsa yasa ya bude gidan kai tsaye bedroom dinta ya wuce sedai abinda ya gani shine yayi mutukar tsoratashi....emili ce kwance tareda wani katon mutum bakikirin kamar kingkong Lol aiko suna ganinshi suka rikice kowa ya fara kokarin daukan kayanshi yasa aiko major ya zare belt dinda ke jikinshi ya fara tafka musu kamar Allah ya aikoshi da gudu katon mutumin ya fita major yayiwa emili pointing kofar da hannunsa alamar itama ta bishi aiko tuni itama ta zura da gudu tabi bayanshi hahahahahaa mara gaskiya kenan ubangiji Allah ya tsaremu da aikata zina...


Achan gida zee tuni kanta ya dauki zafi don ta hango wata hanya da zata saci kudin munir matawalle cikin sa,a kuma ta kwashe masa gaba daya kudin dake cikin account dinsa ta kara mai ta gudu tabar kasar ma gaba daya

Munir matawalle tamkar zeyi hauka gaba daya duniya tayi masa zafi babu abinda ya tsira dashi se gidaje guda 3 kawai donshi dama ba ma,abocin siyan muhimman abubuwa bane yafi ganewa ya cika account dinsa da kudi kawai

Waya ya dauka ya kira major salman ya sanar masa cewar yanason ganinshi da gaggawa a main house dinsa


Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*




Page 95-100

*Na*
*Maman hanan*

*This page was dedicated to my bestie zainab Abdallah yarima(fachala)ubangiji Allah ya saka miki da alkhairi bisa tsantsar soyayya da kaunar da kike nunamin bani da wani bakin godiya a gurinki Kuma Allah ya kara basira nima ina sonki sosai Allah raya mana deeja da haidar kuma ubangiji ya kara muku dankon soyayya keda angonki......ana mugun tare🤝🏻*

4pm major yaje gidansu ya samu daddy dinshi sedai abin mamaki shine dukanin family dinsa suna zaune tareda dad din nashi don haka cikin sallama kuma jikinsa a sanyaye ya samu guri ya zauna.....

Daddyn salman ne yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa....Salman nasan zakayi mamakin kiran nan nawa domin sanin kanka kasan bakar zuciya irin tawa to kada kayi mamaki domin kasan shi Allah shine yakeyin komai kuma a lokacin da yaso
Ada ban yarda da abubuwan da kake gayaminba akan cin kudin jama'a da aikata munanan dabi'u se yanzu na gane gaskiya kake fadamin domin shedar ya rigada ya shiga zuciyata
Salman duk wani abu daka sani na mallaka ta hanyar haram yanzu babushi domin ko yarinyarka zee ta damfareni ta kwashemin komai yanzu hka banida komai se wannan gidan da nake ciki da wasu guda 2...tabbas duniya ta juyamin baya gashi yanzu ba dani ake garawaba a majalissa tuni na tuba na koma ga Allah domin an haliccenine bawai don nayi sunaba ko na tara kudi No an haliccemune domin mu gina wani abun alkhairi a duniya kafin mu barta salman na yafe maka duniya da lahira nima ka yafemin don Allah salman.....zubewa yayi kasa kamar wani karamin yaro a gaban salman

Da sauri dad ya tashi yayi hugging din daddy din nashi shima yana kuka yana godewa Allah....

Karkaso farin ciki gurin hajiyan salman itama ta taso ta rungume dan nata tana kwallar farin ciki

Ranar dai a gidansu salman ya kwana tamkar wani kwai haka aka dinga lallabashi duk inda yayi se kulawa kawai ake bashi.....

Da safe bayan sunyi breakfast daddy din salman ya kalleshi cike da kunya yace salman kenan anki ayi aure dai ko

Cikin sosa keya yace daddy nayi aure kwanaki amma yanzu mun rabu da matar yanxu wata yarinyace nakeso xamuje yobe achan take daganan ya bawa mahaifin nashi duk labarin suhana

Cikin kwana 3 akaje yobe da kudin aure da kayan lefe da komai su kaka sune sukayi wakilci aka fara shirye shiryen bikin suhana.....sati 2 kawai akayi aka daura auren suhana da salman daganan tana kukan rabuwa dasu kaka da nasir haka aka tafi da ita kano

Gidansu salman aka fara wucewa da ita seda ta kwana 4 sannan aka gyara amarya aka kaita gidan angonta masoyinta na hakika wato *Major salman*

Bayan yan kai amarya an watse ya rage suhana kadai gabanta se faduwa yakeyi Amma idan ta tuna ita mallakin salman ce se taji dukanin wani tsoro ya kauce

Cikin light blue din shadda salman ya shigo dakin da suhana ta takure akan gado tsayawa yayi a kanta don ya tabbata bata san ya shigoba...mintsilinta yayi a hankali aiko suhana ta firgice ta fara ihu

Da sauri yayi hugging dinta sosai don besan zata firgita hakaba cikin kunnenta ya rada mata cutie wanene?

Cikin shagwabar fushi tace ba kai baneba ka bani tsoro

Am sorry amaryar soja bazan kumaba

Murmushi tayi ta mintsileshi a kumatu tace ok sir

Da kyar ya samu ta danci abinci kadan bayan sun gabatar da sallarsu ta nafila don taga major duk ya rikice mata

Towel ya mika mata ba musu ta karba ta daura ta shiga wanka ta fito shima ya shiga yayi wankan ya fito mai kawai ya shafa tareda romantics perfumes dinsa don major ma,abocinsune

Jikin wardrobe ya tararda suhana na kokarin daukan kayan da zatasa be jira ta kai hannu ga dauko kayanba ya dauketa cak ya ajiyeta akan gado...tana kici kicin tashi ya sanya bakinsa cikin nata french kiss yakeyi mata deeply baki daya ya birkice....gaba daya jikin suhana ya sauko ya dinga lashewa....suhana ko banda kuka babu abinda takeyi tausayintane ya kamashi sosai da sauri ya dagota idonta rufe ta kasa ko hada ido dashi cikin sanyin murya irinna major yace
Cutie banason kukanki ko kadan stop it please... U know how much long nake bukatarki suhana baki saniba ko...i really love you cutie.... i love your everything... Keep calm my boo i promise to make you the most luckiest princess just give me a chance please i will prove it baby..... Tamkar me kuka hka major ke faman radawa suhana kalamai barkatai
Suhana batasan sanda ta sake janyoshi jikintaba....tuni abubuwa suka ci gaba da faruwa ihu kam suhana yi takeyi tamkar ranta ze fita......banda albarka babu abinda major yake shiwa suhana itama tana sake tabbatarwa da kanta lallai major salman yayi deserving a kirashi da hero......


Soyayya me karfi da ma'ana ake gabatarwa a gidan major salman suhana tayi kyau sosai shima major yayi kyau sosai.....

Zaman lafiya me dorewa da kuma tsaftataciyar rayuwa ita akeyi a gidan Alhaji munir matawalle don tuni ya fita daga harkar siyasa ya dawo full time business man.....

Su zee ko ana chan babu wanda yasan duniyar da take amma zamu iya cewa duk inda take bata cikin kwanciyar hankali domin ko duk wani wanda yake a cikin rayuwa irinta zee to lallai karshensa bazeyi kyau ba mutukar ba tuba yayi ya koma ga ubangijiba domin shi Allah me yafiya ne.......

*Alhamdulillah nan ne karshen wannan littafin ubangiji Allah yasa a amfana da koda kalma dayace daga cikin littafin kuma ya yafe mana kuskurenmu amin ya Allah*


*Maman hanan*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment