Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

temakeni ya rikeni tamkar yarsa ko kanwarsa ya daukeni muna zaune a gidansa...ranar nan ya shigo yaga banida lfy ya daukeni ze kaini asibiti se yayi mantuwa ya koma ze dauko ni kuma ya barni cikin motar shine wata mace tazo itada wasu maza fuskarsu duk a rufe ita kadaice fuskarta a bude suka rufe min baki suka daukeni suka dinga tafiya dani bansan inda kaina yakeba seda kuka kawoni nan tukunna.....

Allah sarki inji nasir.....to ke daga wanne garin suka daukoki

Nima bansaniba....ta fada a takaice

Banda salati babu abinda kaka takeyi shiko nasir kanshi ne ya kulle tausayin suhana ya shigesu sosai sannan ya dubeta yace

To yanzu dai kina cikin garin yobe se kici gaba da addu'a se Allah ya bayyana daga inda suka daukoki....zamuci gaba da zama dake anan kamar yanda kika ganni nima maraya ne zaune nake gurin kakata anan......amma yaya sunan wanda kike zaune gurinsa din?

Gabantane yai mummunan faduwa don tinda takeda major bata taba sanin ko yaya sunanshiba.......jikinta a sanyaye tace shima bansaniba........tunowa tayi da ranar nan a gabanta ya ambaci sunan salman lokacin yana amsa waya wannan ya bata damar kallon nasir tace sunanshi salman a tunaninta koda ba hka sunan yakeba to itadai kawai ta fada don fitarda kanta kunya.....

Kaka ta dauki suhana tamkar yarda ta haifa da cikinta kulawa ta musamman an sanyata makarantar boko da islamiyya a jikin dukanin wata takarda tata tana amfani da sunan *suhana salman* yarinyace mai kokari sosai suhana ga ladabi da biyayya da nutsuwa.......a duk wani abu da takeyi hoton major salman ne a idonta ta kasa mancewa dashi cikin tarihin rayuwarta.....

*ABUJA STATE*
Babu binciken da salman beyiba akan suhana kamar wasa ba ita ba labarinta ba karamar damuwa ya shigaba amma da yake mutum ne me dauriya da juriya haka ya hakura ya manta da babinta sedai lokaci zuwa lokaci yana tunawa da suhana hotonta a idonsa baze taba gogewaba da tarin kaunarta acikin zuciyarsa


Su Emili an samu abinda akeso major ya samo mata Addmision a bayero university kano ta fara karatunta zama yakeyi da ita na hakuri taki yarda ta samu ciki wai ita sbd tana karatu se family planning takeyi tun abin na damunshi harya hakura ya zuba mata ido

Yanda suke da zee suna nan se abinda yayi gaba kullum tana taredashi suna holewarsu amma har yau yaki ya gaya mata yanada mata wato Emili......


*5 YEARS LATER*
Suhana an sake girma an zama babbar budurwa kyau kam akwaishi don zama fasalta muku kyawu irinna suhana ze iya daukata shekaru da yawa😂

Sanye take cikin uniform dinta na islamiyya da yayi mata kyau sosai abinka da doguwar mace tayi kyau kwarai kamar wata balarabiya ko yar pakistan a kyau.....tana cikin daura nikab din natane wata kawarta feedy ta shigo itama sanye cikin nata uniform din suka jero suka fito

Feedy ce ta kalli suhana tace

Waike suhana bakya gajiya kullum cikin nikab kamar wata matar aure

Kinsan yan unguwarnan da shegen kallo a nikab dinma basu barkaba sesun kalleka ni kuma na tsani kallo shiyasa bazan iya fitowa hakaba

Uhmm ai se kitayi in kika gaji kya dena ai toda kike ma gudun kallon cikin nikab waye ze ganki yace yanaso harya aureki

Idan shi be ganniba aini xan ganshi ni nan har yanzu banga mijin aurenaba.....ni bazanyi aureba har sena samu hadaddan soja sannan na aureshi

Tab waike meyasa kikeson soja ne kina kyakkyawarki mezaki da wani soja ya kulleki gida yaita faman yi miki axaba

Feedy kenan aini nawa sojan ba irin wanda kike tunani bane.....

Haka suka karasa makarantar a makare sbd hirar da sukasha a hanya don ma ba karatu akeyiba shirye shiryen saukar karatun alkur'ani akeyi tasu suhana da za,ayi sati me zuwa........


***
A office ya tarar da takardar da commander ya ajiye masa kafin ya karaso
Tsaki salman yayi sannan yace i can't make it wlhy a rasa inda zanje nayi aiki se yobe state gaskiya bazan iyaba.....mikewa yayi da sauri ya dauki takardar ya tafi gurin commander

Bayan commander yaji bayanin salman ne yace

Haba salman karka manta kayi rantsuwane akan duk inda aka turaka zakayi aiki....wannan karon saukar al-kur'anice za,ayi a yobe kuma makarantace ta state daga kan governor har sarki duk zasu halarci gurin don haka ya zama dole a basu tsaro me karfi sun turo mana da takadar neman tsaro ne shiyasa muka turaku......

I'm sorry to say ina da aikinyi dayawa a ranar don tuntuni na amsa gayyatar wasu......don haka ina ganin a cire sunana daga list din bazan samu damar zuwaba.......yana gama fadar haka yayi saluting commander sannan ya fice waje abinshi

Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 55-60

*Na*
*Maman hanan*

*Dedicated to my precious little angel hanan*

*Jummaah Mubarak May Allah Accept All Our Wishes Amin*

********

Direct gidanshi ya wuce na hutawa,zee ya tarar tana jiranshi kwance take a palour barci ma ya dauketa.....be kulataba ya wuce bathroom ya watsa ruwa sannan ya fito...yanayin sanyin garin da akeyine ya bashi damar debo coffee yanasha zuciyarshi cike da danasanin abun daya aikatawa commander gaskiya be kyautaba ace yayi musu da maganar commader be jira komaiba ya kirashi a waya ya sanar masa ya fada masa date din zuwa yobe din insha Allah zeje....

Bayan ya gama wayan ne zee ta taso ta zauna kusadashi ta fuskanceshi tace

My man tafiya zakayine

Yeah an turani aiki yobe state ne insha Allah i will be there

Gabantane yayi mummunan faduwa inda ta tuno da wani alamari daya faru shekara 5 da suka wuce....dariya tayi sannan a zuciyarta tace koma dai meye wannan yarinyar ai nasan ta dade da mutuwa ma....

Bata nuna wata damuwanta ba illa best wishes da tayi masa na cewar Allah ya kaishi lfy ya kuma dawo dashi lfy.....

Itama daya fadawa emili hakan tace mishi kawai ba tareda ta nuna wata damuwa ko kulawa a gareshiba.....

To waishi yaushe ze fara yin rayuwa irinta kowanne mutum me yancine?yaushe ze samu wacce take sonshi kuma take damuwa dashi tsakani da Allah....tambayoyin da yake tayiwa kansa kenan har bacci yayi gaba dashi


*YOBE STATE*
Kaka duba wannan kayan kiga da kyar na samu telan ya hada mata su duka ayau nasan zasu yi mata kyau

Allah sarki zako taji dadi wlhy bari a kirata tazo ta gwada

Suhana.....Suhana.....Suhana....kaka ce ke kiran suhana

Naam kaka...gani

Zo kiga kayan sauka yayanki ya kawo miki sunyi kyau sosai

Ta dubi nasir dake gefe yana ta faman baje baki tace yaya nagode Allah ya saka da alkhairi sunyi kyau sosai

Haba yar kanwata aiba godiya tsakanin kanwa da yayanta don haka indai sunyi miki burina kenan...


Anata faman shirye shirye don yau tunda suka tashi ita da feedy suke faman yawon gidan kitso zuwa gidan kunshi duk da ita suhana ba kitso zatayiba sbd gashinta baya yin kitso ya fiye santsi dayawa sedai gyara mata shi akayi sosai akayi mata kunshi se bayan magriba suka koma gida..

Da safen ma aiki suka danyi har suka kusan makara.....da yake feedy har tafi suhana sauri ta rigata shiryawa tazo gidan nasu tana jiranta

Feedy tace gaskiya suhana wlh kin fiye nawa ace har yanxu baki shiryaba ni har na gama shirina amma ke ko kaya baki sakaba yanzuma kika fito daga wanka

Kinjiki feedy kema kinsan kin rigani shiga wankan nan fa kuma niba kwalliya zanyi bama mai kawai zansa da powder se lipstick shikenan yanzunan zamu tafi naji ance har governor da sarkin garin nan duk zasuzo ni dama kinsan ban taba ganinsuba sedai a hoto

Tab aiko yau zaki gansu sosai kedai kiyi maza ki shirya don wlh mun makara sosai

Lace suhana ta saka red colour ba karamin kyau yayi mataba sannan ta dauko hijab dinta milk colour ta saka har kasa tayi kyau sosai da sosai sannan ta dauko nikab dinta ta saka ta dubi feedy tace taso mu tafi.....

Waike suhana yau dinma sekinsa nikab ranar saukar tamu guda

Hmmm ba dole nasaba kinsan banson jama,a sosai gashi banson kallo kinsani kema

Oho dai in kinje gaban me martaba da governor dai dole ki cire in zaki karbi allon zayyana din taki

Haka suka fita sunata hirarrakinsu



Guri ya cika sosai an fara gabatar da komai yanda ya kamata matakan tsarone cike a gurin kana kallon gurin kasan anyi komai cikin tsari inda tuni major salman ya halarci gurin cikin kakinsa na sojoji yayi mutukar kyau hannunsa rike da bindiga fuskarsa cikin hular kwano ta sojoji

Suna zuwa suka samu guri suka zauna don tuni an fara gabatar da karatun alkur'ani mai girma a gurin...


Hayaniyace aka fara jiyowa ta baya irin yan jagaliyar siyasannane waisu se sun jefi governor.....kafin kace wani abu tuni aka fara sakin harbi a gurin suma suka fara fitoda nasu bindigogi suna harbe harbe tuni guri ya rikice yara da manya aka fara gudu ana bada sanarwar kowa yayi ta kansa an daga yin saukar se wani satin..

Harbi yakeyi sosai wanda har yasashi cire hular kwanon dake kansa.....kamar a idon suhana yana cire hular idonta yakai gareshi......yayi mata kyau sosai ya dan kara kiba kadan amma komai nashi yana nan yanda yake.....kallonshi kawai take tana murmushi tamkar mahaukaciya shiko ko lura da gurin nata beyiba aikinsa kawai yakeyi

Wani babban mutum ne yazo ya janye suhana daga gurin yana cewa

Kaga mahaukaciyar yarinya kina ganin mutuwa kiri kiri amma kin tsaya kina dariya shashashar yarinya kawai maza ki wuce kiyi ta kanki

Bata saurareshiba illa kawai sake juyawa da tayi gurin kallon major amma cikin rashin sa'a tuni ya haye mota suka wuce don raka governor gida....

Faduwa kasa tayi timmmmm sakamakon bullet dinda ya taho daga kasa ya shiga kafar suhana tuni jini ya fara zuba mutane da yawa akayo kanta don kawo mata agaji....


Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 65-70

*Na*
*Maman hanan*

*sam bana wulakanci sedai idan na shiga busy ne dayawa shine zakuga kuna min magana ban amsaba amma ina kokari naga na farantawa kowa kamar yanda kuke farantamin nima,don haka kada a sake cewa ina yin wulakanci pls i hate it😡*


*Dedicated to zainab Abdullah yarima(fachala)*
*Ana mugun tare🤝🏻*
*Ana masifar tare🤝🏻*
*Ana bala'in tare🤝🏻*
*Ana jarabar tare🤝🏻*
*Ana fitinar tare🤝🏻*
*Ana shegen tare🤝🏻*
*I heart you😘*

*********
Jinsa yakeyi tamkar wani sabon ango,,,,,ya kagu garin Allah ya waye domin yaje gurin mahaifin nashi don yaji menene dalilin kiran nashi da yakeyi....zuciyarsa cike da damuwa ya kwanta

Tun bayan shekara 11 da mahaifinsa yayi masa korar kare be sake komawa koda unguwar tasuba balle har yayi kokarin zuwa gidan nasu......tabbas hausawa sunce duk wanda yabar gida gida ya barshi sannan zama da dan'uwa shine abu mafi dadi a dukanin wata rayuwa ta duniya......

An samu sanje sanje sosai a gidan nasu maimakon yaga gidan nasu yaci baya sakamakon kudaden da aka kwace gurin mahaifin nasa sema gani yai abubuwa dayawa sun sanja anyi modernizing dinshi.....zuciyarshi na harbin duka 3×2 haka ya shiga gidan sedai banan gizo yake saka ba tuni ranshi ya fara baci duk wani gate da yazo shiga na gidan se yasha checking da interview sakamakon chanjin ma,aikatan gidan da aka samu

Abinda ya bashi mamaki sallama yake tayi a gidan amma babu alamar kowa a cikin gidan tun daga kan matan gidan har yaran gida....abinda be saniba shine seda munir matawalle ya tura gaba daya iyalinnashi umara tukunna ya samu damar kiran dan nashi don su gana

Bayan kamar minti 10 sega Daddyn salman ya fito sanye cikin bakar jallabiya hannunshi rike da jarida dayan kuma rike da cup me dauke da coffee a ciki

Da sauri salman ya sulale kasa ya tsugunna don gaisheda mahaifin nashi amma tuni ya dakatar dashi da hannunsa tareda yi masa nuni da hannu yace

Dont ever try to bend for me again..... Ni ba kowanka bane yanada kyau matsayinka na babban soja ka mike tsaye muyi magana dakai a matsayina na babban me lefi ko hahahaha yaro kenan

Tunda ya fara magana salman ke kallonshi ganin irin zafin kai na mahaifin nashi .......cikin murya mara sukuni yace

Please daddy kayi hakuri ka yafemin wlh na tuba daddy bazan sake ba

Niba hakuri na kiraka ka baniba major salman na kirakane domin ja maka kunne akan ta,asar asarar da kakeson sake sani a ciki......dubi nan
Jaridar hannunsa ya mikawa salman me dauke da hotonshi a sakamakon karramawar da akayi masa don shine ya bada babban goyon baya akan kashe yan tada kayar bayan da akayi a gari yobe

Dago kansa yayi ya dubi daddyn nashi dake kallonsa cikin mugunta.......yace nagani daddy wannan ai harin da aka kaiwa governor din yobe ne kuma da yardar Allah duk mun kashesu mun kama wasu yanzu haka suna tsare

Munir matawalle neya doka wa salman tsawa yace shut up!ya isheka haka.....dama na kirawoka don sanar maka ka cire hannunka daga wannan case din domin kuwa nine nan na tura a kaiwa governor din yobe hari sakamakon wasu kudade daya hanani kuma ka gaggauta sakar min mutanena idan ba haka ba to wlhy zaka rasa rayuwarka kwananan.....na maimaita maka kayi gaggawar sakar min mutanena kuma hari bazamu fasa kaiwa governor ba harsai na cimma muradina.....

Hawayene suka wankewa salman fuska cikin tashin hankali yake magana haba daddy wannan wacce irin rayuwace haka,,,,,ashe har yanxu baka nutsuba baka dena wannan rayuwar banzar takaba


Hahahaaa yaro kenan besan wutaba seya taka.....ba shawara na kiraka ka baniba umarni nake baka akan ka cire idonka daga duk wani ayyuka da nake aikatawa idan ba hakaba ina tabbatar maka kaine wanda zaka zama matacce kwananan......get out from my house

Cikin muryar kuka salman ke magana zan tafi amma ina tabbatar maka ina nan kan aikina kuma dukkanin me lefi bazan fasa hukuntashiba....idan har satar kudin alumma da saida mugayen kwayoyi da sanya mana tashin hankali a cikin alumma shine sana'arka ni kuma bazan fasa mika ka gurin hukuma ba

Toh shikenan mu zuba mu gani......inji daddy be jira komaiba yayi shigewarsa ciki shima major waje yayo zuciyarsa na masa kunci da radadi



*Alhamdulillah anan na kawo karshen season 1 na MAJOR SALMAN se ku biyoni a season 2 me suna SOYAYYAR MAHAIFI(MAJOR SALMAN) don jin yanda zata kasance*


Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *MAJOR SALMAN*
Page 60-65

*Na*
*Maman hanan*

********
Tamkar gawa haka aka tafi da suhana asibiti.....kaka kuwa da Nasir kusan hauka sukayi da suka samu labarin da gudu suka garzaya asibitin kaka harda kukanta Nasir ne yake lallabata yana ce mata tayi hakuri ta dena kukan da ranta bawai ta mutu bane......

Haka aka dinga bawa suhana temako na gaggawa dama surgery akayi mata a kafar aka cire bullet din sannan akaci gaba da bata kulawar gaggawa....


Major Salman yaso komawa abuja amma aka hanashi saboda ba,a kammala investigation ba akan wayanda suka kawowa governor hari gashi kuma still next week za,a gabatar da saukar wadda aka dage ta.....


*After 7 Days*
Yauma gurin saukar a cike yake sedai tsarin gurin yasha banban dana wancan karan don duk wanda ze shiga se anyi checking dinsa sosai tsarone mai tsanani a gurin kowa yayi tsit anayin addu'ar bude taro

Shugaban makarantarsu suhana ne ya bude gurin da addu'a sannan yace ba tare da bata lokaciba za,a fara gabatar da abinda ya tarasu a gurin

Sunayen yan sauka aka fara kira daga kan mata har zuwa maza inda kowa da an kira sunanshi yake zuwa ya karbi allon saukar tashi tareda wasu yan kyaututuka daga hannun mai martaba....

Suhana salman shine sunan da aketa maimaitawa amma shiru bata fito ba.....

Jin sunan suhana da tun a rayuwarshi be taba jin sunan ba se akan suhana dinshi ya sashi baza idanuwanshi don ganin wannan wacece haka me irin sunan suhana....

Anata maimata sunan suhana salman amma shiru bata fitoba......tuni mamaki yakeyi wannan wacce yarinyace suhana salman me irin sunan dayafi so ya kasance cikin sauraronsa har abada....tabbas wannan ko wacece dole ne ya mallaketa don daga jin sunanta ya fada a tarkon sonta na har abada.....

Shiru dai babu suhana ba dalilinta a gurin da fari anyi tunanin kota fita daga gurin ne ko kuma bata karasoba amma har aka tashi daga gurin suhana batazoba domin kuwa tana chan kwance a gadon asibiti ko kafar tata bata iya dagawa...

Ranshi a bace ya bar gurin domin yaso yaga wannan wacce yarinyace wacce daga jin sunanta ta sace masa zuciya a lokaci daya
..



*ABUJA STATE*
Sanye yake cikin singlet da boxer bayan ya gama gyming ya shiga ciki ya dauki ruwa yanasha.....ringing wayanshi ya farayi yaso daga wayan amma ganin new number ya sashi ajiyeta kawai ya shiga wanka

Bayan ya fito wayan yaga yaci gaba dayin ringing tsaki yayi sannan ya daga wayan cikin muryarsa ta mazaje masu jini a jika yace "HELLO"

ina son ganinka gobe da karfe 5 a cikin gidana

What ya fada a cikin zuciyarsa don ko tantama babu wannan muryar daddy dinsane da baze taba mantawa dashiba a rayuwarshiba

Koba kaji abinda nace makaba ne....daddy ya fada daga daya bangaren

Okay daddy babu matsala zanzo

Karka sake cemin daddy domin na dade da cireka daga cikin yarana......yana gama fadan haka ya kashe wayar daga daya bangaren


Shima major jikinsa a sanyaye ya cire wayan daga kunnensa yana tunanin shin me kuma ya sake yiwa mahaifin nashi?


Muje zuwa
Mom hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*

*Na*
*Maman hanan*

Page 70-75

*********
Major salman sanye cikin uniform dinsa da kullum idan ya saka kamar kyau suke kara mishi...office dinsa ya wuce ya samu guri ya zauna don tun jiya rabonsa da wata walwala

Commander neya shigo kana ganinsa kasan ransa a bace yake....da sauri major salman ya tashi yayi saluting dinshi amma ko kai be daga mishiba ya fara masifa

Haba major salman wannan wanne irin shirmene zaku je ku aikata don an tura ku guri daga zuwanku se kuje ku fara bude wuta a guri ku fara harbi wannan ai haukane da shashanci

Mamakine ya kama salman don jiya commander har kusan dagashi sama yayi don murna amma ace lokaci daya ya chanja yana cewa abinda akai be daceba

Major salman ya kalleshi sannan yace i am sorry sir amma ina ganin komai an aiwatar dashi cikin tsari domin gurin nan da sukaje suka fara harbe harbe gurine na jamaa yara da manya wayanda basu san me yake faruwaba idan da an barsu ba karamar barna zasuyi a gurinba zasu kashe rayuka da dama shiyasa mukayi kokari muka kashe mutum 2 kawai a ciki tare da kama mutum 2 sauran sun tsere bamusan dalilin kawo harin nasuba dole mu rikesu harse sun fada mana wanda ya turo su

To bada sa hannunaba kuma ka gaggauta sakinsu babu abinda ya shafeni don an turo takarda dazun nan cewar a sakesu har nayi accepting nayi signing

What a sakesu fa kace wlh baze taba yiwuwaba idan kai baxaka iyaba ni na yarda xanyi handling case dun amma baza a sakesuba harse mun gano gaskiyar zancen....



Zaune take a beach bayan ta fito daga pool wayanta ya fara ringing ganin number ne yasata jan aji kadan kafin ta daga

Hello

Hello zee yammata adon gari

Dawa nake magana

Kina magana da Eng munir matawalle

What....your Excellency

Kada ki damu koki tsorata zee nasan kina tareda yarona salman shiyasa na kiraki don yimin wani aiki wanda kafin kiyi aikin ma da kanki zaki yankewa kanki kudin da kike bukata daga kan million 10 zuwa sama nakeso ki yankarwa kanki kudin

Tuni zee ta mike jin uban kudin da munir matawalle ke ambata cikin rawar murya tace ok your Excellency babu wata matsala a ina zan sameka

Dabo hotel room 448 VIP session....

Ok gani nan zuwa

Wani tsallen farin ciki tayi tareda da cewa major salman ina sonka amma nafison kudi fiye da komai don haka zan yiwa mahaifinka aiki koda kuwa kasheka yasani nayi indai akan kudina ni zee babu abinda bazan iya yiba.....



Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*
Page 75-80

*Na*
*Maman hanan*

*Pure love to you all👌🏻word can't express my love to you fans.....thanks for the love and support*


*********
Cikin mintina kadan zee ta karasa dabo hotel


Knocking daya tayi munir matawalle ya bude mata kofa....sanye take cikin riga kimono kanta wata hulace transparent ta saka babu alamar dankwali balle mayafi

Gaisheshi tayi ta sigar yaudara irinta yan bariki masu license.... Ba tare da bata lokaciba munir ya nisa yace

Zee bawai na kiraki bane don wani abuba illa inason kiyi min aiki akan salman.....sanin kankine ina mutukar son dana salman soyayyar da bazan iya hadata da komaiba a duniyarnan.....zee ina son salman kuma zan iya sadaukar da rayuwata akan salman kuma ina tare dashi aduk inda yake domin kare lafiyarshi....sedai salman ya tafka babban kuskure da har yayi kokarin ya ja dani a matsayina na mahaifinsa kuma babban minister ya zama dole in hukunta salman domin zuciyata ba irin tashi bace inaso ya fuskanci kudi shine babban muradina a gidan duniya

Jinjina kai kawai zee take sannan ta saki wata sassanyar murmushi tace babu wata matsala your excellency ka fadamin ko meye zan aikata makashi

Nasani zee domin kafin na sameki an tabbatar min da ingancin aikinki da kwarewarki a hatsabibanci......Am zee inaso duk wata kadara da muhimman takardu na gidaje zuwa filaye da salman ya mallaka...ki kawo minsu nan da sati daya zan baki dukanin address na abubuwan daya mallaka a rayuwarsa tuni na gama researching na samo locations dinsu shine first target dinmu sannan secondly inaso ki kawomin dukanin credentials na takardun karatun salman kafin nan da sati 2 zamu doka sunanshi a kotu a matsayin sojan da yake amfani da takardun bogi ba tareda originals ba kinga daganan za,a saukeshi daga sojan kuma ya tashi bashida ko sisi kinga dole ya dawo gareni a matsayinshi na talaka wanda bashida ko sisi kuma marar aikinyi idan beyi wasabama hukuma seta daureshi sakamakon raina musu hankalin da yayi

Ok Excellency babu matsala kasa a ranka angama komai domin nasan dukanin inda yake ajiye abubuwan da kake bukata

Kudi ya debo masu yawan gaske ya bata....ta juya ta fita cike da farin ciki


*YOBE STATE*
Kaka wallahi na ganshi na rantse da Allah shine

Waike suhana kina cikin hayyacinki kuwa nasir maza kira mana likita kaga tunda ta farka take faman ambatar ta ganshi to wai wata ganine

Duk wasu gwaje gwaje da likitoci suka gudanar anyi kuma an gane kwakwalwar suhana tana nan lafiya lau don haka alluran bacci kawai akayi mata donta samu nutsuwa....



Ayi hakuri da wanan
I'm little bit busy




Muje zuwa
Maman hanan
[1/27, 9:07 AM] ‪+234 701 472 7066‬: *SOYAYYAR MAHAIFI*
*(MAJOR SALMAN)*
*Season 2*
Page 80-85

*Na*
*Maman hanan*


*If i tell you say i love you oo my money my body na your own oo baby💃🏻💃🏻*

*Wannan shafin nakune*
*Jamila Abdullahi Aliyu(auntyn hanan)*
*Shaimah*
*Khaleesat shareef*
*Khadija waziri*
*Love you loads❤*

*Zainab Abdullah yarima fachala ikon Allah kenan ina yinki irin sosai dinnan 🙆🏼‍♀FEEDY irin an dade ba'a haduba dinnan🤣🤣😂😂😅😅labari kam yamun dadi masha Allah godiya nake*


********
Ba tare da wani bata lokaciba zee ta fara aiwatar da shirinta sedai abun da bata saniba shine tuni major ya sanjawa babbar akwatinsa ta ajiyar kundin mahimman abubuwansa

Tayi tayi ta sanya password din amma sam yaki karba don ya sanja pin din ranta a mugun bace ta fita daga gidan har tana mantawa da wayarta dama major baya nan lokacin data shiga

Abinda ya fara bashi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment