Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fada tana kokarin kara taba jinkin nasa taji saidai tana kai hannu taji kamar kara zafi jikin nasa yayi a lokacin kuma.
Hankali tashe tayo waje zuwa dakinta tana jawo gyalenta na sallah ta dora saman kanta ta nufi waje gidan makwabtansu ta nufa saidai ba taimako don maigidan bayanan don haka ta fito daga gidan.
Malam Tanimu ta hango kofan gidansa wurin sana,anshi ya dan rarafo yasha iska don bai gama farfadowa daga tausan da gina yayimas bako a lokacin.
Ganin ta a hargitse yake tambaya Dije mai kamu ince ko lafiya ina fa lafiya malam Tanimu jikana ya dawo min a cikin wani yanayi na rashin lafiya yana kwance a dakinshi rai a hannun Allah.
Subbahanallahi ya fada yaba yunkura saidai gefen kafadab shi da gina ya taushe yayi tsami a lokacin yasa ya koma da sauri yana yamotse fuskanshi kafin yace meke damun shine ?
Dama tun kan ya fita yake fadin sanyi yakeji da kuma nauyin jiki na jiya kuma yace kai ke dan sara mai haka dai ya fita yau din zuwa daukan karatun shi na boko sa yakeyi.
Yanzu shine nace bari nazo ko za a taimaka min ko wani shawara na samu ga mutane indai da kai barin bashi wani magani ya shaka in,sha Allahu zai samu lafiya indai ya shaka wanan din.
Kinsa sana,ar tamu dole saida tambaye tambaye don haka na aje wanan danaji ba daidai sai nadan yi amfani dashi naji wasai.
Mikewa yayi da kyat ya shiga gida ya dan dauki lokaci kafin ya fito sai gashi ya fito da kullin dan bakin leda a hannunshi yana fadin ina ai Amadi yaron kirkine bada kamar shi a unguwar nan baki daya .
Ki kai mashi wanan insha Allahu yana amfani dashi kome ke damunshi da yarda Allah zai sake indai yayi amfani da wanan dai ya aje sauran a wurinshi.
Godiya sosai Dije ta fara yi mashi kafin ta dingisa kafantal taja zuwa gida yana kwance yadda ta barshi ta zaunava kusa dashi tana bude ledan kafin ta debo ta turmuza bashi a hanci ta koma gefe ta zauna ta kafa mai idanu tana tunane a zuciyar na jikan nata.
Kafin dan wani lokaci taji ya saki wani irin atishawa da karfi lokaci guda tana zaune saida ta zabura daga inda take zaunen tana ambatan sunnan shi take fadin Amadi sannu sannu kaji Amadi.
Wani atishawan ya kara sakewa har yana dan dagowa daga kwancen da yake dije sai fadi take Alhamdullilahi barka Amadi sannu kaji Allah ya yaye sai kuma tasa kuka lokaci guda.
A hankali ya fara bude idonshi yana ganin dishi dishi a dakin kafin ya sauke kallonshi kan Dijen yana fadin Dije lafiya dakyat yake wanan maganan lokacin.
Sannu Amadi ta fada a cikin muryan kuka tana share hawaye da gefen gyalen ta tace yaya jikin hankalina ya daga sosai banda dabara shine na tafi wajen malam Tanimu yabani wanan na shaka ma tana nuna mai kullin dake hannunta din.
Kallon maganin yayi a hannunta kafin ya yunkura da niyar tashi jiri ya mai dashi ya kwanta yana lumshe idanunshi a hankali tare da jin wani iri a idonshi ya mayar ya rufe.
Kaci wani abin kuwa yau ta tambayeshi ya dan girgiza mata kai yana gyara kwanciya ta mike ta fice daga dakin kwano ta dauka ta fice daga gidan .
Wurin masu sayar da abinci layin ta nufa ta sayo shinkafa da taliya da ganye a sama ta kawo mashi dakyat ya tashi ya fita ya wanko bakin shi ya dawo ya ya zauna ta kara tura mai abincin gaban shi .
Saida ya dan samu natsuwa ya bude kwanon shinkafan ya kalla yasan saye tayi don basu da halin dafa wanan a gidansu tausayin kakan yaji ya kara shigan shi lokaci guda yana tausayawa tsohowan kan irin rayuwan da suke fuskanta din.
Mikewa tayi ta fice daga dakin ruwan zafi ta hada mai ta kai mai bandaki ta dawo tana ka gama tashi ka watsa ruwa a jikin ka ko zakaji karfin jikim naka ko ?
Sai kuma takai kallo ga kwanon dake rufe har kaci abincin ke nan ta tambaya tana kallon fuskanshi ba zan iya cin wanan din ba dije ya fada ya kokarin mikewa ta sakw fadin me zakaci to ?
Banjin cin komai a yanzu ya fada tare da mikewa da karfi ya barta dakin tsaye tana mamakin shi dama ita din da yunwa tare da marmarin shinkafan take saidai babu halin hakan a gareta.
Yasa ta daukan kwanan zuwa waje ta zauna ta faraci tana lumshe idanu wani gefe kuma tana jin zafin kudin data fitar ta sayo wanan abincin gashi yanzu baici ba ta bata kudin a banza.
Shiko yaki cine don yasan itama tana so ko kan ya fito har ta kusa gamawa da abincin ya fito daga bandakin wankan maza yayi na watsawa aji iska a jiki kawai a lokacin.
Alwala ya zauna yayi don ya rama sallolin dake kanshi yana kallon dijen a fakaice tare da girgiza kanshi ya mike zuwa daki ya gabatar da sallah bai sake fitowa ba sai washegari.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[25/12/2022 3:34 PM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣
AL MU'MIN,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA A KANKI BA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO
KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN ,,,,,,,,

Washegari ummah na tana kitchen tana hada breakfast na sameta a tana tsaye tana fere arish daga bayanta nake fadin ina kwana ummah ?
Da sauri ta dan juyo zuwa inda nake a kofan tana fadin fuska ba walwala a cikinsa maamah kin tashi yaya kan da sauki ta fada tana kallon yanayi na a lokacin.
Nace eh ummah ina kwana yau kece ke girkin da kanki kafin Tani tazo tace nice kinsan Alh na gari dan anjima nan kadan jama,a basu barin ya zauna karshe ma ya fita.
Abba ya dawone na tambaya a cikin mamaki jin haka yasa ta juyo dakyau tana fuskantana tare da fadin yadawo mana jiya ai har nan yake wurin ki shida malam bawa ai.
Cikin mamaki na dago kai na kalleta nace malam bawa waye haka ummah tace wanan malamin dake kasan layin nan shi ya dauko a cikin dare yazo ya ganki.
Jikinane yayi sanyi na karasa inda take ina karban yunkan data dauka a hannunta tana shirin fere dankali don ta nufi inda dankali yake na tako ina mika hannu zan karba.
Baki da lafiya ki koma ki zauna ta fada ummah naji sauki zan iya na fada ki barshi ai ba wani abin mai yawa zanyi ba dankalin nan ne kawai da kwai zan soya sai ruwa tea gaya na dora a kattile.
Hakan baisa na fasa amsan yukan a hannunta ba ta miko min kafin ta juya ta duka tana debo min adadin dankalin da zan fere din a lokacin.
Tsaye nake ina fira naji muryan ummah tana fadin waini Maamah ina kika hadu da iskane haka har suka shafeki ?
Wani irin juyowa nayi wanda ya fitgita ummah har ta kalli yukan dake hannuna danayi setin inda take dashi da sauri na sauke hannuna kasa tare da fadin iska kuma ummah ?
Aiba shiganki sukayi ba shafanki kawai sukayi malam yace ki kula da addu,a maamah ko banza kinsan yadda muke a cikin mutanen nan bawai sun daukemu da daraja bane.
Don gani suke har gobe mu bamu cancanci rabar Alh ba matsayin mu baikai ace muna cikin ahalin Alh ba a yanzu don kasancewar iyayyena tallakawa ko don na zama bare a cikin su yasa har ku suke kallon ku a matsayin da bankai ga tantanceshi a zuciyana ba.
Kallon Ummah nake cikin mamakin zancenta gareni wanda ban gama na iskan data fada sun shefeni ba ga wani zance ta dauko min a yanzun kuma wanda na kasa tantance inda zancen nata ya dosa a lokacin.
Taci gaba da fadin sai jiya na kara fahintan cewa har yanzu maman ku bata dauke mu da muhinmanci ba a gidan nan don irin maganganun data fada min a jiya kan kawai wai Alh ya dawo gidan nan a ranan girkina ta rufe ido ta fada min magana na kaskanci lokaci guda.
Nayi duk kokarin da zanyi wajen tausan zuciyana a zauna lafiya amma a kwanakin nan tun dawowan mu garin nan yanzu ina ganin wasu halaiyan da hjy maimuna take tsiro min dasu na daban dake nuna ni banda daraja ko kima a wurin Alh da kowa.
Ummah meta fada maki haka haka har kika kasa hakuri dashi ranki ya baci haka don nasan a zaman ku kece mai hakkuri da kawar da ido akan komai da akeyi a cikin gidan nan.
Nishin ciki ummah tayi lokaci guda tana fadin yi sauri muyi aikin nan kada mu makara rana ya fito bamu gama ba naci gaba da fere dankalin gabana a hankali zuciyana tab da tunane.
Allah ya taimaka anyi angama har ankai falo an jera duk lokacin ba wannda ya fito ummah ta koma tayi wanka ta shirya cikin wasu simple lace masu taushi dinkin zani da riga sai turare mai taushe data goga a jikinta.
Part din Abba ta nufa sai ta samu mama a cikjn zaune tare dashi suna magana da ace can bayane fita zatayi daga dakin da sauri amma wanan karon ga mamakin mama sai taga tayi sallama ta shigo.
Abbah tafara gaidawa tayi mai ya gajiyan hanya kafin ta juyo inda mama take tana fadin hjy antashi lafiya ya kwanan su Aisha dacewa yan matan dakin mama din a yanzu su biyu.
Ciki ciki mama ta amsata ba yabo ba fallasa ta mike daga inda take zaune zuwa bandakin Abba din ta hada mai ruwan zafi ta kara gyara wurin ta fito.
Lokacin ne Abba ke fadin mamana ta tashi kuwa ko har yanzu bai sake ta ba tace tashi tare ma mukai aikin breakfast da ita ai.
Ya jikin nata yanzu ummah tace Alhamdullahi don ta dan watsake masha Allah ya fada barin yi wanka na lekota sai wayanshi dake gefe ya dauki kara lokaci guda ya kalli wayan kafin yace jiya saidai muka dauko malam bawa wa mamana lokacin kin rufe part dinki.
Umm, ummmm ta fada kawai tana mikewa tsaye tare da fadin yanzu ni ai uwarta ta nuna bani na haifeta ba don ta nuna min hakan kaima gashi kuma ka fada yanzu da bakinka ai.
Da inada muhinmanci ko iko da ita aikona rufe kofa zaku tayar dani mudai zuba daku inga iya gudunku inda zaku da wanan sallon da kuka dauko min a yanzu.
Dukkan su kallon mamaki sukai mata lokaci guda ta juya ta fice daga dakin ta gaban ummah tayi saurin jada baya da sauri kada su kai ga hada jiki abinda ba a so ke nan kishiya da kishiya su hada jikin su yana jawo tsiya a gida koga mijinsu inji manya.
Na rasa meye matsalan maimuna a kwanakin nan murmushi ummah tayi ba tare datace mashi komai ba tabarmashi dakin itama ya bita da kallo yana gyada kai.
Mikewa yayi ya shiga wanka ya fito ya ya shirya bai zauna cin abinci ba ya nufi part din ummah tana zaune da kannena a falo su uku ya shigo part din.
Gaidashi suka farayi ta hanyar tasowa daga inda suke zaune suna mashi sannu da zuwa tana amsa masu tare da tambayan su karatunsu a lokacin naji muryan shi a falon mu yasa na nufo falo da sauri.
Daga kofa da zaka fito daga dakunan kwanan mu nace Abba you are welcome ya dago inda yake yana kallona fuskanshi cike da murmushi yake fadin mama kece nan haka yau ya fada a cikin kulawa.
Karasowa nayi zuwa tsakiyan falon namu na sameshi kasa nakai yadda muka saba gaidashi ina fadin ina kwana Abba ka dawo lafiya yace Alhamdullahi mama yaya jikin naki da sauki dai yanzu ko ?
Kan ya daina ciwo ko jiya nazo mun dade dake baki san lokacin da haka ya faru ba dake hankalina ya tashi jiyan sosai yadda na ganki din sai nake tunanen ina kika hadu da iska haka.
Da sauri na dago kai na kalleshi kafin nayi kasa da kaina da sauri ba tare dana bashi amsa ba ganin hakan yasa yace to ki kula don Allah mama don malam ya fada muna gamo dasu kikayi a wani wajen.
Nan ma na sake dago kai a cikin mamaki sosai ina ksllon su Abba din nace dasu Abba ban hadu da kowa ba hakani bansan zancen kaba Abba.
Kallon ummah yayi kafin ya juyo inda nake gurfane yana fadin ki kula da kanki watarana inyi lfahari dake uwata yawan jin kida da kallace kallace a cikin dare ko shiga bandaki kai tsaye ba tare da yadda musulunci ya koyar damu ba duk ki daina uwara don tsaron lafiyan ki.
Na amsa da toh Abba nagode ina mikewa hannu yasa ga aljihun riganshi ya ciro kudi masu ya miko min lokacin har na juya zan tafi tafi kanena daya ke fadin anty maamahb Abba yana mika maki ya nuna min Abban da hannu.
Juwowa nayi inda Abban ya ya zaune ya rike kanin mu karami a jikinshi wanan sallon na Abban namu mun dade rabon mu da muga irinsa a garemu tun dowowan mu garin zamfara Abban ya daina bamu irin kulawan da muka taso yana bamu.
Lokacin da muke zaune Abuja kula muke samu wanda duk wani uba zaibawa iyalanshi irin wanda ke kawo shakuwa ga iyali amma muna dawowa sai sallon rayuwan ya canza a wurin mu gaba daya har Abban namu din a yanzu.
Don ko bu za a bamu saidai mama ce zata sayo ita Abba zaibawa kudi ko kuma ta saya idan yazo ta karbi kudinta a hannunshi.
Irin abubuwan da dai ke tauyewa dan adam hakkinsa da rashin
yanci a gida shi muke gani a zamam mu nan zamfaradin daga mu har mahaifiyar mu muna a tauyene muna zama na rashin gata a cikin mama da yaranta wanda muke ganin su suna komai nasu a cikin gata da walwala na jin dadin nuna halin akwashi a gidan mu din.
Don ko motan da nake hawa yanzu wanda anty Aisha tayi amfani dashine mama tace ta barmin shi a ka sayo mata wani na mata mai kyau na yayi ni kuma don zuwa school aka ban wanan din don shima baiji jiki ba.
Gyara akai ta kara komawa sabuwa nake hawa har mutane na ganin aimu a cikin gata da jin dadi muke koda yaushe don basu gane gaskiya idan ba wa yanda suka zamo na jikin mu ba sunsan komai.
Kaina girgizawa Abba din alaman ya barshi murmushi naga ya sake a fuskanshi yana fadin uwata idan ban bakiba wa zai baki ki karba karbi ki aje a wuri ki.
Hannu bibiyu na mika na karba ina godiya kafin na tashi na mike na bar falon saida ya dan jima da yaran kafin ya fito yal nufi part din mama data riga ta samu labarin cewa Abbn yana part din mu kusan minti ashirin a ciki tare da mu.
Don haka yana shigo tana zaune ta hakince saman kujera sai commad da take bayarwa daga inda take zaune din don ita mama tana da yan aiki har uku part dinta.
Bayan diyan yan uwa maza da mata dake zaune tare da ita don har yan aikinta biyu a nan suke kwana a gidan namu don aikin mama.
Abba ya shigo da sallaman shi fuska mama ta hade mai nan wanda suke falon suka shiga gaida Abba din yana amsawa ya kai zaune a gefen mama din ta dan jaye tana gyara zama.
Lafiya naga kin hade rai haka ta kallo shi tana fadin duniya na hada haka kawai za a ce wai na hade rai a kan me kan wa yancan banzan iyalin naka kome zan hade raina.
Murmushi yayi yana fadin sune kuma banza yau da bakin ki ke fadawa iyalina haka maimuna wai meke damun kine haka wai ?
Lokacin su Aymana da Aisha suka fito daga dakunan su jin muryan Abba din a part din nasu suka fara gaidashi kafin su fara zuba mai shagwaba yana biye masu.
Daddy sai ka ban kudin gaskiya don in katafi saidai muji cewa ka bar gari kila Aisha ta fada tana wani shagwaba kamar karamar yarinya.
Dole Abban yasa hannunshi a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa suma ya mika masu har lokacin mama na zaune sai busan iska takeyi tana jan kamshi ita a dole an mata ba daidai ba.
Yayin da shikuma Abban yake kokarin ganin cewa ya daidaita tsakanin shi da mama din ita kuma tana bultsewa.
Ranan ya kamata ya juya don wayan daya samu amma dole ya daure ya kara kwana don mama suka daidaita kansu suka koma daidai.
Shi kanshi Abba din a lokacin ba zaice ga dalilin dayasa yaji lokaci guda ummah ta tsaya mai a rai haka ba har yake dan jin tausayinta ita da iyalanta a wanan zuwan.
Don baibar gari ba saida yayi dabaran ganin ya kyautatawa kowa don ya cikawa ummah account dinta da kudi har saida tayi mamakin ganin hakan wanda da dane saidai mama ta bata idan yatafi tace Alh ya basu su rike.
Lokaci guda itama ummah din tana jin wani son mijinta yana taso mata dan lokaci lokaci a ranta wanda yasa Abba yana isa Abuja ummah ta kirashi tana mashi godiya tare da addua mai inganci a gareshi wanda hakan yasa shi lumshe ido a cikin wani yanayi.
Yau kwana biyu ke nan yana zuwa school yana dawowa hannu sake ba kamar yadda ya saba rikowa Dije dan ledan abinda ya samo a wurin aikin shi ba.
Saidai Dije din ta amsa gaisuwan shi sannan tayi mai sannu kafin tace da alaman dai kunyi fada da shugaban aikin kuce kwana biyun nan ko ?
A cikin mamaki ya juyo yace tun wancan ranan ban koma wurinta ba don na samu labarin cewa tace idan nazo korata zatayi yasa nayiwa kaina kiyamalleni da ita.
Ka kyauta gara da baka tafi ba ina amfanin wullakacin Allah daya bata bai manta damuna muma idan da rabo namu yana tafe a wurin Allah.
In sha Allahu ya fada tare da jingina jikinshi da bangon ginansu ya shiga tunane don yasan abinda tsohuwar keyiwa dan abincin daya saba shigowa dashi gidan da yanzu ya daina yasa ta kai ga magana har ta fahinci akwai magana.
Itama dijen shiru tayi na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin sana,a nake son in nema in fara yi saidai jari shine matsalata a yanzu don sana,a saida jari mai dan tsoka a hannun ka.
Tau Amadi kace kayi sana,a babu wani kudi ko abin sayar a hannun ka indai ba wa yan nan dabbobin da su kawai muka mallaka a yanzu ba.
Saidai idan su din zaka kama ka sayar saika rike dan kudi a hannunka kai ya girgiza mata tare da fadin mu daiyi addua Allah zai kawo muna mafita ga komai.
Allah ya nufa ta fada a sanyaye sai kuma ta dora da fadin dadai kabi shawarana sai ka dauki ita uwar garken kakai kasuwa kudin sai kayi amfani dashi Allah yasa akbarka kaga saura kwara hudun in Allah ya raya muna su sai a more masu kuma gaba.
Dije ki bari na kara addua a kai insha Allahu Allah ba zai barmu haka ba da yardan ubangiji da fadin haka yai shiru yana tunane ba komai yake tunane ba sai halin rayuwan daya tsunci kanshi a ciki .
Yau ace mahaifinshi da mahaifiyar shi suna raye amma yana zaman kunci irin na marayu don dan wani dalili mara tushe da mahaifin nasa ke takama dashi a zuciyar shi.
Har yakai dije na magana dashi lokacin bai jiba yayi imani da abinda zuciyar shi ta yanke mashi akan mahaifin nasa.
Dago kai yayi da idanuwan shi da suka kade sukai ja kallonshi tayi lokaci daya sai taji jikinta yayi sanyi ta fasa fadin abinda tayi niyar fada mashi din a lokacin .
Shirun dayayi yawa yasa ta dauko mai zance makwacinsu da maciji ya sara a daji jin hakan yasashi dago kai da sauri yana fadin subbahanallahi shi malam Abashe din ?
Tace kwarai taci gaba da fadin dazun nan aka dawo dashi daga gona inda abi
n ya sameshi suje noma gonan su a can ya tabashi aka daukoshi zuwa gida.
Yanzun dai suna asibiti dashi ance magani dubu sittin da biyar na shiga masu tanzango abin ba dadi gaskiya saisai Allah ya gyara kawai.
Bari inyi sallah sai in leka gidan in yakama har asibitin sai in tafi jn gaidashi can tunda yau naga babu hadari a garin ya mike ya nufi inda suke aje buta.
Washegari na tashi da sauki sosai don haka na shirya zuwa school lafiya lau na shiga mukayi darasin farko bamu fito ba sai sha biyu da rabi.
Wurin motana na nufa na bude shiga na zauna nafito da goran ruwa tulawa cikina saida nayi rabin ruwan na daga goran na cire a bakina.
Kainane ya sara lokaci guda hakan yasa na dora kaina saman sitiyarjn motana na dukar da kaina lokaci guda motar ta fara horn hakan ya jawo hankalin mutanen dake dan sintiri a wajen.
Wai yarinyar can tana da hankali kuwa tun dazun take duke mota na horn haka wasu gugun matasa dake zaune suke fadi daga bayan su Amadine zaune yana karatu saye yake a cikin wani dogon wandon jeans
Pdayo kode sai wata shirt fara mai zanen kanana kana tsaye jikin rigan duk da farine shima rigan ya kode saboda tsufan da yayi shima.
Dan juyowa yayi inda yake jin horn din yanatashi ya hango mace ta kifa kai saman sitiyari mikewa yayi da sauri ya nufi wajen kamar wanda ake ingizawa zuwa wajen.
Ganin ya nufi wajen ya kara jawo hankalin sauran matasan dake zirga zirga a wajen da sauri ya karaso yana dan magana daga inda yake boyar Allah lafiya kike kuwa ?
Shiru yaji ga goran ruwan da nasha ya zube a jikina rabi

Please Login or Register in order to submit comment