Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taki yarda da hakan har saida hjy ta kulafuci tani din taso ta tasa a kori tani din daga gidan saida ummah ta fahinci me mama ke nufi ta nuna jajircewan ta kan hakan.
Tun lokacin sai gaisuwane da sannu ke hadasu da hjy ddin tana taka tsatsan da lamarin mama din a gidan harta shigo ta fita da yamma tana part din ummah zaune.
Wanan gaskiyan da amana na Tani din yasa ummah kara yarda da lamarinta da har yanzun din ma hankalin ummah din ya kwanta da maganin data kawo wanda ita tsakani da Allah ta amsawa ummah din shi.
Dauka tayi ta kara dubawa kafin ta mike ta fito zuwa kitchen dashi a hannun ta Tani din tana tsame shikafan data wanke a ruwa taji shigowan ummah din yasata juyowa lokaci guda.
Ummah ce kofa rike da ledan maganin data kawo mata a hannun ta idon tani ya sauka kan ledan gabantane ya fadi take fadin hjy lafiya dai ko ?
Lafiya Tani ummah ta dan sake murmushi tana takowa cikin kitchen din tana fadin kinga Tani ba zan boye maki ba da farko ban dauki wana maganin da kika kawo min dazun ba.
Amma yanzun nayi tunane na aminta dake Tani duba da yadda mukai sabo da amana kuma a tsakanin mu dake nasan kinyi wanan ne da niyar taimakona nida diyana.
Don sanin halin rayuwan da muke ciki a gidan nan daba kowa yasan da hakan ba sai yan tsiraru suka sanda hakan a garemu.
Allah sarki hjy yadda kika rikeni nida diyana da yan uwana meye ba zan iya maki ba a rayuwa wallahi Allah jiya na kwana da tunanen uwar dakina a raina don kiri kiri ake son a illanta maki zurian ki nan a gidan nan.
Wanan yasa nayi asubancin zuwa gidan yaron nan na jiya da yai min kwatance shine nayi asubancin zuwa unguwar na kuma gane gidan nasu.
Saidai a lokacin nayi rashin sa, a don shi ya fito zai tafi makaranta a lokacin shine ya hadani da kakarshi ta kaini wurin wani dattiju a nan unguwar tasu.
Ni kuma sai ban boye mai komai na irin matsalan da kuke fuskanta a gidan nan shine yaba da wanan yace a kawo maku kuyi amfani dashi mugu na fili dana boye saidai aniyar shi ta koma mai .
Watau aniya makomiya ke nan yadaice kuyi amfani dashi kamar yadda yace ayi in sha Allah ya wadatar daku saida hjy naga kamar baki yarda dani ba kan hakan ?
Saidai banga laifin hakan ba tunda ba da sanin ki najeni ba amma idan kina wani shakku ga hakan kina iya sa uwar dakina ta binciko maki wanan wurin yaron jiya din tunda suna ganin juna wata kila dashi din a makarantar su.
Haba Tani ba zancen rashin yarda bane ko wani abu yanzu tsakanin mu don mun zama daya daku yanzu ai bake ba ko wani naki bazai cuta min ba a yanzu.
Zuwa nayi ki kara min bayanin yadda zamuyi amfani dasu don dazun sam ban fahinceki ba koda kike min bayanin su a lolacin.
Karban ledan tayi ta warwale ta fara yiwa ummah bayanin yadda akace kafinta dago tana fadin kaidai kada kaiwa wani sheri kadai tsare jikinka yadda ko yayi saidai ya koma kan maishi don ansan asiri gaskiyace tunda yaci Annabawan Allah.
Ina shigowa gidan namu mamace naci karo da ita a waje da alama fita zatayi lokacin mota na fito na rufe na nufi inda suke suna magana da driver gidan mu koshi zai kaita unguwar ban sani ba lokacin.
Fuskana dauke da fara na nufi inda suke din saidai nayi mamakin ganin yadda mama din ta daure min fuska tam babu ko yar fara,a a fuskanta gareni.
Ganin hakan yasa na rage nawa fara,an dake fuskana na karasa ina fadim mama lafiya dai ko ko fita zakiyi ne na tambayeta lokacin ta juyo gareni tana fadin.
Eh zan fitane har kun dawo tana kokatin shiga mota na bita da kallon mamaki daga hakan bata kara juyowa inda nake tsaye ba din sukaja mota suka tafi.
Ajiyan zuciya na sauke tare da juyawa zuwa cikin gidan namu zuciyana da tunanen wanan sauyin da nake gani a gun mama din yanzu.
Da sallama a bakina na shiga part din mu saidai babu kowa a falon mu lokacin haka yasa na wuce zuwa bedroom dina na fara kwabe kayan jikina.
Sauyawa nayi zuwa wani dogon riga kafin na sake fitowa zuwa dakin ummah don na gaida ita kuma tasan na dawo a lokacin ban son ta shigo ta same ni a dakina.
Zan shiga dakin ke nan naji motsinta a falo na juya zuwa falon na sameta a nan ummah na kira sunan ta tajuyo tana fadin ashe kin dawo ke nan to yaya kan naki bai tashi ba acan yau ko ?
A, a ummah saidai nan gefe daya danaji ya daure min kamar zai fara min ciwo din lokacin saina shaka wanan maganin na jiya a masalaci naji ya bari .
Kikuma dinga yin addua kina tofawa ai haka wanan yace min yau da muka hadu dashi a school yau din ma kun hadu ke nan dashi ummah ta tambayeni ?
Eh yazo wurin motana yana duba da mamakin har naji sauki nafito yau makaranta shine yake fadin na kula da jikina da kuma addua don ni mace ce daba don Allah ya kawoshi jiya ba baisan yadda zamuyi ba a wurin.
Gaskiya ya fada addua ya dace bawa ya tsare a kullun don ita kariyace ga mumuni don haka ki kara tsare addua sosai ya fada maki gaskiyan da nima iya nan zan iya fada maki ai.
Ummah wai meya samu mamane naga zata fita ranta a bace ina gaida ita bata tsaya ta amsa min ba tana dauke kai gareni kamar nayi mata wani laifi.
Yanzun nan zata fita da yamman nan haka ban jin nisa zata tafi don bata faye fita haka da yamma ba saidai in wani wuri mai muhinmancin zata tafi hakan yanzu a wanan lokacin.
Amma ai mama bata daure min fuska haka irin yadda tamin yau din nan idan ta dawo anjima zan sameta a part din ta ai na gani..
Kice mata me idan kinje ki barta kawai idan wanan zaikaiki wurinta saidai idan wani abin zai kaiki gunta ban hana ba amma kada ki mata zancen hakan koda wasa.
Kaina gyada mata alaman amsawa kafin na gyara zama ina tunanen abinda ummah ta fada daga haka mikewa tayi zuwa dakin ta a lokacin kannena suka shigo sun dawo daga islamiya.
Nan nake tar dasu har akai kiran magariba muka watse zuwa sallah ban fito ba sai bayan salllah isha,i da muka fito na samu ummah na waya da Abban mu lokacin naji tana fadin da sauki sosai don yau din ma har taje schoon din ai kuma ba abinda ya faru.
Banji meyace ba tadai miko min wayan na karba a hannunta muryan Abbane ke kiran sunana na karba mashi yake tambayana ya jiki ya karatu na amsa da naji sauki.
Muka dan taba hira yace in ba ummah din waya a lokacin na mike zuwa part din mama da naji dawowanta ana bude mata get ina sallah isha,i a lokacin.
Dukkan su basuyi zaton shigowa na part din ba a wanan lokacin sai ganina kwatsam da sukayi na shigo hakan yasa da sauri naga Aisha tana kokarin boye wani jarka karami dake dauke da wani ruwan rubutu a bayan .
Nayi kamar banga haka ba lokacin wurin mama na nufa a sake ina fadjn mama ashe kin dawa andawo lafiya ya gajiya ta amsa a cikin dan darare da fadin lafiya tana kawar da kai gareni.
Nan ta barni zaune tankar ba mama ba a ranan yadda ta nuna min din tankar bata san dani ba zaune a wurin ta kama harkan gabanta ta fita batuna ga baki daya.
Saida na gaji da zama na mike nake fadin mama zan tafi dama na shigo na gaida kene don dazun bamu gaisa sosai ba zaki fita.
Ta dan juyo gareni tana fadin OK zaki tafi zarah saida safe ke nan wani irin ba dadi naji a rain haka naja kafana na fice daga part din mama ba tare da kowa ya kulani ba lokacin.
Ina shiga part din duk suna falon a lokacin ummah tana basu wani abu da bansan ko meye ba na daiga yaran na bata fuskansu alama abin da ake basu baida dadi ke nan a baki.
Kokarin shiga dakina nakeyi a lokacin naji muryan ummah tana fadin maamah oya zo nan ki karbi naki kisha .
Fuska na bata daga inda nake tsaye din ina fadin ummah bana sha a koshe nake na juya zanci gaba da tafiya wanan din ba wani abu bane maganine na ciwon zazzabi kawai.
Ummah oya zoki karba ban son korafi Anty zarah sai kinsha dole ummah tace don maganin ba dadi kuma kanina ya fadi daga gefen ummah inda yake zaune.
Dole nazo na zauna a gaban ummah ta debo maganin a wani silver ta miko min tare da fadin oya yi bissimillah kisha.
Karba nayi ina bissimillah nakai bakina ba dadi abin amma haka na daure nasha maganin kafin ummah ta umurce ni da naci abinci.
Na tsakwara na tashi zuwa lokacin duk jikina ya mutu tashi nayi zuwa dakina ummah ta dubeni tana fadin saida kika je gun maman taku din ke nan ko ?
Kallon ummah nayi a dan shagwabe kafin na gyada kai alaman naje amma ban yi zancen komai da ita ba ai itama din kuma ko kulani batayi har yaranta


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[29/12/2022 9:52 PM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣
AL JABBAR,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Zan iya cewa wanan lokacin na gane sauyin da gidan mu ke ciki a yadda ni na daukeshi ashe ba haka abin yake ba a dunkule a baiyanene nake ganin komai normal a gidan namu.
Wata kila kuma watan hankalinane ya kama a lokacin har yakai ga na fahinci hakan a yanzu sabanin da da dauka daya nakewa iyayyen namu a zuciyana.
Yanzu na gane kowa danshi ya sani kuma yake kokarin ganin ya zama wani abu a duniya ya kareshi daga duk wani sherin kada ya cin mai.
Saidai wani abu da bai sauya ba shine yaran mama maza manya da suke daukan ummah da matsayi mai mutunci a idanun su basu fasa hakan ba don suna bugowa ummah waya kamar yadda suka saba a baya.
Idan sunzo garin kuma zasu shigo su zauna a nan suyi hira duk da mama zatayi ta aikowa suzo tana neman su a wurin ta bai hana insun tafi su kara bullowa kafin dare kuma.
Hakama alheri bai katsewa a tsakanin su da ummah din saidai nasan a boye sukeyin shi don yanzu sun fara aiki suna kuma kula da harkokin Abba haka yasa kudi ke shigo masu ta ko ina a yanzu.
Saidai a garemu yanzu babu daman kwatanta hakan ga mama don bamuga fuskan yin hakan ba gareta a yanzu babu wani sakin fuska ko kara na jan mu jikinta kamar yadda ummah kewa nata diyan.
Sai gaisuwa kawai koshi saida kyat take karba muna a tsatsaye dole mukaja jikin mu da ita ya kannena idan sun ganta jikinsu har rawa yakeyi.
Wanan satin ma kamar kullun sunzo gida don suna garin na fito da shirina zan tafi school a waje na samu ya musa wanda yaci sunan kakan mu shine da nabiyu ga mama.
Yana tsaye a farfajiyan gidan mu da kayan motsa jikin a jikin shi wurin shi na nufa ina gaidashi ya juyo fuska a sake yana fadin .
Sai ina haka yan matan mama da safen nan haka school na bashi amsa kafin na karaso inda yake tsaye murmushi nayi tare da fadin ya musa ai yanzun mama ta daina sona kamar da.
Ido ya kwalo waje yana fadin garin yaya haka ya faru keda maman ki dan shagwabewa nayi ina fadin nima ban sani ba ya musa na daiga ta daina sona ta daina kulani a yanzu na fada kamar zanyi kuka.
Kai haba dai baki dai jida kyauba zarah har yaushe keda mamanki zata daina sonki kuma nace Allah ko ya musa nima bansan abinda nayi mata ba yanzu har haka ya faru.
Wa zai kaiki school din ya tambaya ta hanyar kawar da zancen da mukeyi nace nike zuwa da kaina yaya da wani mota kuma yana raba ido ga motocin dake parke a haraban gidan.
Nace cikin dan sakin fuska ga motata can ita nake ja yanzu ina nuna mai motan dayasani na Aisha da tayi accident da ita kamar ma ba zata gyaru ba lokacin.
What ya fada yana kwalo ido waje tare da fadin wanan tsohowar motar dai yanzu har an saura shiganta gidan nan ashe ?
Kai haba yaya garau take fa da ita nake fita kuwani duk inda zan tafi na bashi amsa ido ya kura min a zahiri zaki iya cewa ni yake kallo a lokacin.
Kafin na katse mai tunane da fadin zan tafi yaya kada in makara amma dai aiba yau zaka tafi ba ko kada in dawo in samu ka wuce.
Yau kuwa yan mata don Abba na jirana akwai inda zai turani kilama yau din nan nabar kasan nan insha Allahu.
Allah sarki ashe da banganka yanzu ba saidai na dawo na samu ka wuce ke nan yace gaskiya kan zan bar maki sako hannun ummah idan kin dawo sai ki karba .
Nagode yaya Allah ya saka da Alherin sa kai tun bakiga sako ba har kike min godiya haka aiko baka bayarba kayi niya kuma na gode Allah tsare hanya yace amin .
Na juya zuwa wurin motar ya bini d kallo har lokacin dana bude na shiga na fice daga gidan ina masa horn ya daga min hannu mukai sallama dashi.
Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya tura hannu cikin aljihunshi ya ciro wayanshi lamban ya jafar ya kira suna gaisa ya fara fadin wallahi akwai matsala fa idan bamu fadawa mama gaskiya ba ka wanan abinda takeyi a gida nan.
Meya faru ya jafar din ya tambayeshi yace yaya za,ace kowa zai shiga jami,a gidan nan ana sai mashi mota amma yanzu yazo kan zarah ace sai tsohuwar motar Aisha za a bawa zarah motan da har accident tayi da ita amma ita zarah ke shiga yanzu.
Au kai sai yanzun kasan da wanan zancen ashe nina dade da sanin hakan da akayi na nuna bacin raina ga hakan da akayi nayi magana mama tace ina ruwana koni aka ba.
Nayi shiru badon raina yaso hakan ba at,list ya kama tunda wanan shine karo na farko da za aiwa ummah haka ya kamata ace an kyautata mata itama tunda anyi muna tana gidan bata nuna hassadanta ba ita.
I don't no why mama take haka na rasa dalilin sauyawan mama a wanan lokacin haka gaba daya ita da yaran nan yanzu sun tsani mutanen nan yanzu a gidan mu.
Kaidai bari kawai wanan zuwan da nayi last bakaji irin fadan da mama tayi min bane kan naje wurin ummah na zauna saida na tattara na bar garin cikin bacin rai.
Gaskiya nikan ba za yarda da hakan ba zan mata nasiha kada son kai yasa mama ta halaka kanta Allah ya tambayeta hakan gobe kiyama.
Wanan matar ta barsu ga Allah kan duk abinda suke mata kuma hakan bai isa ba sai an hanasu harda walwala a cikin gida haba don Allah abin yayi yawa mana.
Ya kashe wayan tare da daga kai ya kalli kayon gidan namu yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda ya fara takawa zuwa cikin gidan kai tsaye.
Yanzu Amadi haka zaka zauna ba wani sana,an da kakeyi da zai taimakaqa rayuwanmu mu samu muci a ciki har mu tufatar da kanmu ga hakan.
Da ka dauki wanan uwar garken ka kaita kasuwa ka sayar sai ka nemi sa,an da dan kudi zai dinga shigo ma yau wajen kwana biyar fa munacin ganye a gidan nan.
Dije nima hakan yana damuna ina nan ina ta neman aikin da zanyi inda zamu rika samun abinci yana shigo muna hakan yana damuna sosai a raina.
Nasani Amadi nasan da hakan kadai ki shawaranane daka jaraba hakan an gani zaifi ya nisa yana fadin Dije banaki bane akuyan nan ita kenan muna a rayuwa ina gudun akaita kasuwa azo a tayata wullakance.
Kinga kuma hakan ba dadi ai gara dai a bari har Allah ya kaimu sallah saina fitar da ita a hurhura da wata karama a sake saura kudin saina fara juyawa.
Ikon Allah yanzu dan nan sallah da sai nan da wata shidda ga mai yawancin rai ka dauka ka kai kawai Allah na nan tare damu in sha Allah kafin sallahn yazo aika tara na tarawa har ka mayar da kudinta kuma.
Zan gwada hakan Dije ya yunkura yana fadi ya nufi hanyar dakin shi yaja ya tsaya ya kafawa uwar garke dake kwance tana gyangyadi a inda turken su yake.
Ya dan jima tsaye kamar yana nazarin akuyan kafin ya shige dakin shi bai jima a ciki ba ya fito ya sauya kayan jikin nasa lokacin Dije ya ambata daga kofan dakinta daya tsaya din.
Ta amsa mai daga ciki yake fadin ni zan dan fita naga ko zan samu mai sayen akuyan cikin unguwa tunda sun santa ai daga haka bai jira ta fito ba yasa kai ya fice daga gidan koda ta fito yariga ya tafi.
Yana fita ya tsaya a kofan gidan yana bin gidajen dake wurin da kallo kafin ya nufi gidan makwabcin su mai irin wanan sana,an na dabbobi ya sallama mashi.
Babban danshine yafito ya sanar maida mahaifinsu bayana nan ai ya tafi cin kasuwan kauye hakan yasa ya juya zuwa gidan wani can kasan layinsu.
Shima haka yana kasuwa bai dawoba ya dawo kofan gidan malam Tanimu da ba kowa sai tarin gumaguman icce dake zube a kofa gidan da wanda aka faskara ya zauna shi kadai kamar yana jiran wani a wurin sai bin masu wucewa da kallo yakeyi.
Yayi nisa a tunane yaji ana mashi sallama ya amsa yana dago kai ga maishi wani dattijone a tsaye ya rataya buhu a kafadan shi da ganin shi kamar mata fiyi bayan sun gaisane yake tambayanshi malam tanimu yace.
Cikin ladabi nima ban san inda ya nufa ba baba zamana ke nan wurin nan yanzun nima ban wani dade ba sai mutumin yace kai gashi ko ina son ganin shi wallahi wai dama dabba nashigo saye yai min jagora.
Yana fadi yana kaiwa zaune Amadi yace gashi ko da alama kamar yaje daji daukan icce ne don in yana gari bai faye zuwa wani wuri ba dai.
Shiru dattijon tayi kamar yana nazari kafin Amadi ya mike tsaye yana fadin bari na shiga ciki a amsa maka ruwa da dan farafarau ka kora don alama ya nuna yanzu ka shigo.
Yana fadin hakan ya mike bai jira jin tsohon ba ya shige cikin gidan malam Tanimu din bai dade ba ya fito da ruwan randa mai sanyi an surka da kunu anyi farau farau dashi a kofi mai marfi.
Dattijon ya karba yana saka mashi albarka tare da mai fatan alheri yana fadin nagode nagode yadda ka tareni kaga tarbon arziki kaima a rayuwan ka har duniya ta nade.
Shima godiya yayi yana fadin amin baba nagode nagode kwarai baba ya fada yana kaiwa kasa muryan dattijun ne ke fadin.
Yaro kasan inda zan samu yar akuya ita nazo nema da yamman nan na dauka zan samu malam tanimu mu hada kafa muje tare.
Kallon mamaki yaiwa dattijo saidai fuskan dattijon na kallon wani wuri a lokacin yayi karfin halin fadi a cikin mamaki aiko baba akwai akuya da akai niyar sayarwa dama barin shiga inwa maishi magana sai a fito dashi ka gani in zai maka.
Ya mike zuwa gidan su bai jima ba sai gashi jaye da uwar garke a hannun shi yana ja zuwa wurin dattijon dake zaune saman kututuren da malam tanimu ya heke ya hada ice da ice a kofan gidan yana zama a sama.
Yazo gab dashi ya mike tsaye yana fadin kai wanan ai zatayi kudi da yawa da daidai yar madaidaiciya ce sai insaya ai
Zaka iya saya idan zatayima baba lalura yasa maishi fitar da ita aiko lalura yakai lalura wanda zaisa a fitar da guzuma haka iri mai kyau da ita yanzu zata kai nawa wanan ?
Tau baba maishi tace jakka arba,in amma sai ka taya a, a yaro ba zan taya ba idan har ta bari ga kudin Allah yasa ta amfana dasu har abada.
Kallon tsohon yayi cikin mamaki jin ko gardama baiyi ba daga sa suna har ya yarda da hakan shi ya banye wani kulli ya fito da kudin ya bashi ya karba cikin mamaki.
Dubu biyar ya kirga ya mayarwa tsohon dashi sai lokacin suka hada ido dashi gabanshine ya fadi ras lokaci guda duk da tsohon yayi saurin kawar da kanshi gefe daya.
Kai ya girgiza mashi tare da fadin jeka dasu yaro Allah yasa masu albarka abinda ka dafa yazama alheri a rayuwanka ya sake amsawa da amin baba yaja akuya ya tafi shi kuma ya koma gida cike da mamaki da al,ajabin wanan bawan Allah.
Mama ya akayi Zahar take amfani da wanan tsohon motan bayan kowa saya mai sabuwa akeyi idan zai shiga jami,a amma ita sai naga tsohuwar mota take amfani dashi na Aisha ?
Uwartace tace kazo ka tambayeni ko wa ?
Haba mama ya ummah zatayi min wanan maganan kuma nidai na ganta yanzu ta shiga wanan mota yasa zo na tambayeki meyasa haka mama ?
Haka naga daman yi don haka ka barta dashi amma mama baki ganin hakan ba da, , , , , , hannu ta daga mai tare da fadin kaga na fada ma ra,ayina don haka kada ka dameni.
Koda aka bata tsohuwar tafi katfin shiganshine ita din uwarta yar waye da yarta ba zata shiga motan da Aisha ta ajeba ?


Please Login or Register in order to submit comment