Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za suyi mata aiki su ciro abinda ke cikinta domin ba zata iya haihuwa da kanta ba”.
Shuru ya yi yana ƙoƙarin maida kukan da ya ci ƙarfinsa, amma hakan ya faskara domin gaba ɗaya ya saki kukan mai ƙarfin gaske.
Nan da nan tausayinsa ya kama Haj Hudah, zata iya cewa ba ta taɓa ganin soyayya irin wacce Musaddiƙ ke ma Afrah ba, shin Afrah da me ta fi sauran mata?, tambayar da kullum take yi ma kanta kenan.
Da sauri tace “ ka kwantar da hankalinka gani nan zuwa asibitin” ya jinjina kai yace “ Toh”, ta tashi da sauri tana faɗin “ wane asibitin ne ku ke?”, musaddiƙ yace “ Asibitin dai da muka saba zuwa”. Daga nan ta kashe wayar ta jefata a cikin jaka, tana gyara zaman gelen da ke kanta.
A yayin da Haj shafa’atu ke binta da tambayar meke faruwa.
Tana tafiya tana sanar da ita matar musaddiƙ ke kwance a asibiti yana buƙatar taimakonta ne.
Harta fita Haj shafa’atu na bin ta da kallo, zuciyarta na nuna mamakin yadda Haj Hudah ke damuwa da lamarin musaddiƙ, domin ko a ɗan zuwan da suke yi tare tana ganin yadda take damuwa da duk wani motsinsa. Sai dai babu abinda ta kawo a zuciyarta face ta su ce kawai ta zo ɗaya.

Tun a mota Haj Hudah ke saƙawa da warwarewa,lokaci ɗaya ta shiga tunanin wannan hanyar itace hanya mafi sauƙi da zata sami cikar burinta akan musaddiƙ, tunda ta fahimci Afrah itace gazawarsa to zata yi amfani da ciwon Afrah domin tabbatar da cikar burinta.
Isarta asibitin ta tadda Afrah cikin mawuyacin hali, har yanzu oxcigine ne a hancinta, idanunta na rufe, tsananin tashin hankalin da ke tattare a fuskar mallam Mahmud da Inna Halima kuwa ba’a magana, amma data dubi musaddiƙ sai ta ga duk na su damuwar shafar mai ne, bayan ta dubata, tare da musaddiƙ su ka jera har ofishin likita, inda ta sami yin magana da shi, ya kuma tabbatar mata da hatsarin da Afrah take ciki na rasa rayuwarta, domin suna tunanin kamar ƙodojinta suna neman su daina aiki, amma ba zasu tabbatar da hakan ba sai bayan an cire abinda ke cikinta.
Sai dai da ya yi lissafin kuɗin da jinyar ta ke buƙata tsawon kwanakin da zata yi a asibitin kafin a ciro abinda ke cikinta, ya gigita musaddiƙ domin ba ƙananan ƙuɗi ba ne, tunda asibitin kuɗi ne, Haj Hudah ta dubi musaddiƙ a lokacin da suka fito daga ofishin likitan, cikin sanyin jiki yake duk ya ƙara sukurkucewa.
Dai dai wasu kujerun ƙarfe da ke girke a harabar asibitin inda yake da ƙarancin jama’a suka tsaya, suna fuskantar juna, sannu a hankali Haj Hudah ta ɗan matso kusa da shi tana jin tamkar ta rungume shi ta kuma lallashe shi, domin duk da tana da ɓoyayyiyar manufa to fa har cikin ranta tana jin tausayin musaddiƙ ba kuma ta ƙaunar duk wani abu da zai zamo masa damuwa.
Murya shaƙe musaddiƙ yace “ Haj waɗannan kuɗaɗen sunyi yawa ƙwarai da gaske, ko kina ganin mu ɗauketa mu maidata asibitin gomnati”.
Ta girgiza kai tace “Asibitin gomnati ina suka ga kayan aikin da zasu taimaki Afrah, ina suka ga ƙwararrun ma’aikatan da zasu kula da ita, ciwon Afrah babban ciwo ne da yake buƙatar kayan aiki da ƙwarewar likitoci wanda ba asibitin kuɗi ba, Afrah ƙasar waje take da buƙatar akaita”, musaddiƙ ya gyaɗa kai yasan duk abinda ta faɗa gaskiya ne, to amma ina yaga kuɗin da zaiyi wannan hidimar, ita kuma da yake tunanin zata taimaka masa yasan ba zata iya taimaka masa da wannan kuɗin gaba ɗaya ba, don kuwa yasan ko rabi ta bashi to ta yi matuƙar bajinta.
A sanyaye yace “ Nasan hakan, to amma ina naga kuɗin da zanyi hakan?” Haj Hudah ta gyara tsaiwarta tace “Kada ka damu ni zanyi ma Afrah komai idan ta kama har ƙasar wajen zan iya fita da ita, nerarka ba’a buƙata zan ɗauki nauyin komai”, cikin matuƙar zumuɗi da murna musaddiƙ ya shiga fara’a yana godiya a gareta, amma sai ta dakatar da shi da cewa “ sai dai da sharaɗi ɗaya, wanda sai ka yarda ka amince sannan duk abinda na lissafa zai tabbata”, ya haɗiye yawun bakinsa domin jiƙa maƙogwaransa, sannan ya nemi nutsuwarsa, ya dubeta sosai yace “ wane irin sharaɗi ne……………..



Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(mrs Aliyu Mayere)

Page 14


Ya ƙarasa tambayar cikin rashin ƙarfin guiwa, Haj Hudah ta ɗan juya bayanta tace cikin wani irin yanayi, “sharaɗina babba ne, don haka babu buƙatar muce zamu tattauna anan, don haka idan ka sami lokaci ka zo gida ka same ni, sai mu yi magana ta fahimta”, Musaddiƙ ya zame ya zauna sosai akan ɗaya daga cikin kujerun dake wajen, fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa yace “ Wannan wane irin sharaɗi ne, Ranki ya daɗe kinsan dai Afrah ba ta da wani isasshen lokacin da za mu ɗiba a cikin nata, yaushe na ke da lokacin da zan zo muyi magana, me yasa ba zaki taimaka muyi maganar yanzu ba”.
Ta juyo ta dube shi sosai tace “ magabar Afrah ake don haka bana tunanin akwai abinda zai hana maka zuwa muyi magana, don haka idan ka shirya ceton rayuwar matarka ka same ni a gida”, tana gama faɗin haka ba ta jira komai ba ta juya ta yi tafiyarta, mamakinta yasa ya bi ta da kallo har ta ɓacema ganinsa, ya runtse idonsa ya buɗe mai yasa yake ganin canjin halayya a cikin idanun Haj Hudah, me yasa a da duk taimakon da take masa ba ta taɓa kafa masa sharaɗi ba sai wannan karon da ya fi buƙatar taimakonta akan kullum.
Ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya yi abinda Haj Hudah ta buƙata, domin ceto ran Afrah.
Hakan yasa ya na idar da sallar issha’i ya sanar da Inna Halima zai je ya dawo, Inna Halima ta dube shi sosai cike da tausayawa tace “ Da zaka ji abinda zan faɗa maka da nace don Allah ka wuce gida ne ka je ka sami ko ruwan lipton ne ka sha, tunda ka ƙi ka ci komai, idan ka sha ka samu kayi wanka ka kwanta ka ba ƙwaƙwalwarka hutu, don Allah ka samu kayi bacci”, ya juya ya ƙurama Afrah ido da take kwance tana motsi, amma idonta na rufe sannan har yanzu ba’a cire mata oxcigine ba, ya yi dubarar share hawayen da ya fara fita masa, sannan ya dawo da kallonsa ga Inna Halima yace “Inna babu hutu a gare ni bayan Afrah tana cikin wannan mawuyacin halin, duk inda ki ka ga na matsa daga gareta to ki sani don ba ni da yadda zanyi ne ya zama min dole ne”
Inna Halima ta gyaɗa kai tana jinjina ƙarfin ƙaunar da musaddiƙ ya ke ma Afrah, babu abinda ta ƙara iya furtawa har Musaddiƙ ya fice da ga ɗakin a gaggauce, ta aje ajiyar zuciya ta na cigaba da addu’ar Allah ya ba Afrah lafiya, ya kuma sanya nutsuwa ga Musaddiƙ.

Ya na fita kai tsaye gidan Haj Hudah ya nufa, zuciyarsa cike da saƙe saƙe, lokaci ɗaya kuma ya na jin wata irin fargaba a tattare da shi.
Tun daga harabar gidan ya gane Alh yusuf sanda ba ya gidan, amma duk da haka sai da ya ɗakko wayarsa ya kira Haj Hudah ya sanar da ita ya zo yana waje, ta ba shi izinin ya shigo.
A ɗarare Musaddiƙ ya wuce zuwa cikin gidan, domin zai iya cewa bai taɓa zuwa gidanta da daddare ba. Kai tsaye falon da ya saba zama idan ya je gidan ya shiga, ya zaɓi ɗaya daga cikin kujerun da suka mamaye falon ya zauna, sanyin gari ya haɗe da sanyin AC ɗin da ke falon, hakan yasa falon ya ɗauki wani irin sanyi wamda har ya yi ma Musaddiƙ yawa. Nan da nan Hadiman gidan suka shiga sauke masa abinci da abin sha, duk da yana gaya musu cewa su bar shi haka baida buƙata, amma haka suka cigaba da aje masa komai, wanda hakan ya dasa masa mamakin yadda ya ga kamar yau a wani muhimmin baƙo ya fito a gidan, bayan shi yasan dai ba baƙo ba ne a gidan, kallon komai na gabansa yake amma sam baida sha’awar cin komai don haka ya cigaba da addu’ar Allah ya fito da Haj Hudah da gaggawa ko sa yi su gama maganar da za suyi ya koma asibiti.Amma ya yi zama me tsawo ba tare da Haj Hudah ta fito ba, a lokacin da agogon hannunsa ya nuna ƙarfe tara ne, haƙurinsa ya fara gazawa, duk zaman ma yabi ya gundure shi. Zuwa can ɗaya daga cikin hadiman ta dawo ta iso gabansa tana sanar da shi Haj Hudah tace ya sameta a ƙaramin falonta na ciki.
Mamaki ya ƙara rufe shi ƙaramin falo nanne take ganawa da baƙinta na jikinta maau matuƙar muhimmanci, duk wanda kaga ta shigar da shi wannan falon to matsayinsa ya kai a wajenta, ya miƙe da sauri yana tafiya yana tunanin yaushe ya sami wannan matsayin?. A can falon ma ya tadda tataccen lemo kusan kala huɗu a aje da kofunq masu matuƙar kyau, nan ya zauna yana addu’ar Allah ya taƙaita masa zaman jira, ya fito da wayarsa ya kira Inna Halima domin jin yadda Afrah ta ke, Tana nan dai yadda ya barta, a hankali ya kashe wayar ya jefa a cikin aljihu.

Ita kam Haj Hudah tana can ɗaki tana tsara kwalliya tamkar mai shirin zuwa gidan biki, ta yi kyau ƙwarai cikin riga da zani na exculusive super wax me ruwan ganye, wanda ɗinkin yabi ya lafe ajikinta ya fito mata da komai na surar jikinta kasancewar ɗinkin mai matsewa ne. A haka ta iso falon ta na wani irin tashin ƙamshi, kallo ɗaya Musaddiƙ ya yi mata ya yi saurin ɗauke kansa, saboda yadda gabansa ya faɗi sosai. Ta zauna akujera mai zaman mutum biyu, tana dubansa lokaci ɗaya tana cewa, “ ya me jikin?”, a hankali yace “ Alhamdulillah”. Ta janyo lemo ta zuba a kofi ta fara sha, “ Na daɗe ina zaman jiranki, yakamata ki yi maganar da kika kirani dominta, saboda ina son na koma asibiti”
Ta yi ɗan murmushi gami da gyara zamanta, tana yi masa wani irin rikitaccen kallo, wanda Musaddiƙ bai gane masa ba. Sannan ta fara magana a hankali a kuma tausashe.

“Musaddiƙ maganar da zan yi da kai mai matuƙar nauyi ce da kuma muhimmanci a gare ni, ina kuma son ka ɗauki wannan maganar da zamu yi a matsayin wani babban sirri wanda babu wanda zai ji ina son ya kasance tsakanina da kai har abada”. Nan da nan Musaddiƙ ya tattaro duka natsuwarsa, ya kuma tsaida hankalinsa waje ɗaya, ya dubeta yace “ Ina sauraronki Ranki ya daɗe”.
Ta ɗan saki numfashi tamkar itama tana jin nauyin abinda take son ta faɗa, a hankali kamar me raɗa tace “ Musaddiƙ sharaɗin da zan kafa maka, bana son ka zarge ni ko kayi zaton haka nake illa jarafta da Allah ya ɗora min a kan ka”, a gaggauce ya ƙara kallonta ransa da zuciyarsa na son su tura masa tunanin da ba ya so, amma duk da haka cewa ya yi “Cigaba da maganarki, ina sauraronki”. Ta ɗan ɗago gami da aje kofin lemon akan tebur ɗin da ke gabanta, sannan ta miƙe tsaye ta shiga shawagi a tsakiyar falon, shi kuwa kallo ya cigaba da bin ta da shi.

Sannu a hankali ta fara warware masa abinda ke ƙunshe a cikin zuciyarta, na tsawon lokaci, sannan ta ƙara da cewa
“Allah shi ne shaida, tun daga ranar da idanuna suka fara yin tozali da kai na tsinci kaina cikin wani irin bakon yanayi wanda sai daga baya na fahimci tsantsar so da ƙaunarka na ke, sai dai dole ta sa na dinga ƙoƙarin yin yaƙi da zuciyata domin cire abin acikin zuciyata, musamman da nafi kowa sanin ni matar aure ce, abinda kuma zuciyata take kitsa min haramunne a gare ni, to amma ya zanyi? Ni fa ba icce bace , jikina kuma da jini sannan ina da sha’awa kamar yadda ko wace mace take da shi”, ta numfasa ta koma a hankali ta zauna, a yayinda tsoro da mamaki ya narkar da Musaddiƙ a zaune, yana jin maganganunta tamkar cikin mafarki.ko ƙwaƙƙwaran motsi ya kasa yi.
Ta cigaba da cewa “ Ka da ka ga laifina ko laifin zuciyata da ta faɗa tarkon ƙaunarka, domin kamar yadda na gaya maka ni fa ba icce bace, kai shaida ne akan irin zaluncin da maigida yake yi min, na yadda yake tafiya ya barni tsawon lokaci ba tare da ya damu da hakkina da ke kansa ba, kuma duk buƙatun rayuwa babu abu ɗaya da yake yi min ni nake yi ma kaina komai, amma duk da hakq ina ƙoƙarin tsare mutuncina, duk da kallon da ake ma na na yan siyasa basu da kamun kai, amma bansan yadda akayi akanka komai ya canja ba”.
Ta tarwatsa idanunta akan nasa, wanda tuni jikinsa ya ɗauki rawa, bata damu da ganin yanayin da musaddiƙ ya faɗa ba, domin dai a yau tasha alwashin warware masa komai.
Ta ɗauke kallonta a kansa ta cigaba da cewa “ Musaddiƙ kai cikakken namiji ne, wanda kwarjininsa yake murƙushe duk wani kwarjinin wanda ya tsaya kusa da kai, kana da wata baiwa da ba kowa ya sani ba, kana da haƙuri kana da kyawun zuciya kana da daɗin zama, kai ɗin na dabanne”,
Tayi wuf ta dawo kusa da shi cikin wani irin shauƙi ta zauna a hannun kujerar da yake zaune, cikin matsanancin fita hayyaci tace “Musaddiƙ sharaɗina shi ne zanyi ma Afrah komai idan ta kama har ƙasar waje zan iya kaita, idan kuma ananne zan kaita asibiti mafi kyau a nigeria inda za’a kula da ita matuƙar kulawa ba tare da ƙwandalarka ba, amma ina son ka taimake ni ka zama mai share min hawaye na, ka dinga ɗebe min kewa ba tare da wani ko wata sun san wannan sirrin ba, kaima kuma duk abinda ka ke so zanyi maka Musaddiƙ”.
Ido kawai ya cigabq da ɗora mata ba tare da ya iya buɗe baki ya yi wata magana ba saboda gani yake kamar ba Haj Hudar da ya sani bace.
Ta ƙara kallonsa tace “ kayi magana don Allah kace wani abu , ko na sami kwanciyar hankali”.
Ananne cikin mutuwa da sanyin jiki cike kuma da ɗimbin mamaki mara misaltuwa, Musaddiƙ ya tashi ya kasa haɗa ido da ita bayansa ya juya idanunsa duk sunyi jajir ya fara magana cikin dishewar murya.
“Lalle duniya abar tsoro ce, haka zalika duniya cike take da abubuwan mamaki, kamar yadda a yau na haɗu da abu mafi ban mamaki a rayuwata, tun da nake da ke ban taɓa tsammanin zan ji irin waɗannan furucin daga bakinki ba, haba Haj idan kince sirri tsakanina da ke babu mai ji, to mahaliccin mu fa? Wanda gyangyaɗi ko bacci basa kama shi, masanin gaibu, wanda shi ne ya halicce ni ya kuma halicce ki, yake kuma tsakanin mu, sannan masani ne akan duk wani abu da bayinsa suke aikatawa a doron ƙasa, sannan mai zamu ce? Me kuma muka tanada a ranar tonuwar dukkan asirai domin kare kanmu?”.
Ya juyo gaba ɗaya ya na kallon ta, ya ja numfashi ya fesar ya cigaba da cewa “kina matsayin matar aure, ina matsayin mijin aure, ta ya ya ki ke tsammanin zan baki goyon baya wajen aikata wannan mummunan aikin da zai taɓa mana mutuncin mu, mu’amalar mu da kuma addinin mu”, a gaggauce Haj Hudah tace “ Don Allah kada ka watsa min ƙasa a ido, na riga na yi nisan da bana jin kira, muryarka kawai jefa ni cikin masifa take”, ya girgiza kansa yana mamakin yadda nasiharsa ba tayi tasiri a wajen Haj Hudah ba.
Yace “ ki ji tsoron Allah, wannan shaiɗanne kawai ya ke buga miki gangarsa ke kuma ki ke taka rawa, nasani don cuta mijinki yana cutar da ke amma wannan bai baki lasisin aikata wannan aikin ba, don hakq abu mafi sauƙi a shawarce ki zauna da mijinki ku tattauna akan haƙƙinki , kuma mq ni banga dalilin da lokaci ɗaya zaki bijiro da wannan maganar ba, bayan da sonki da kuma ra’ayinki akan abinda mijinki yake yi, asalima akan raya dukiyarki yake tafiya ya barki, tunda duk kun yarda da cewa dukiya tafi rayuwar aurenku muhimmanci, to me kuma zai kawo wannan canjin na farat ɗaya?”.

Haj Hudah ta miƙe da sauri ta dawo ta tsaya a gabansa tana faɗin “ ka fahimce ni a bai bai Musaddiƙ domin kuwa ban taɓa goya masa baya akan danne hakkina ba, ban taɓa fifita dukiya akan aurena ba illa dai ra’ayinsa ne shi kaɗai na yaje ya yi kasuwanci a ƙasashen waje”, ta nisa gami da juya bayanta tace “ me ka sani akan maigidana, kawai kana kallonsa ne cikin riga amma ni nasan waye shi, mijina mutum ne mai matuƙar son kuɗi, duk abinda zaiyi don kuɗi su zo gare shi zai iya yi,Allah ya riga ya hore min tarin dukiya tun kafin na shiga siyasa, a dalilin tsohon mijina na farko marigayi Alh Bashir mai dala, wanda ya rasu ya barni da ɗimbin maƙudan ƙuɗaɗe da kadarori, aurena da Alh yusuf sanda ya wayar min da kai akan yadda zan faɗaɗa na kuma kawo ma dukiyata hanyar da zata ƙara haɓaka, a dalilin hakan bayan auren mu saina sakar masa duka dukiyar tawa domin ya cigaba da juyawa min tun daga lokacin kuma ya maida hankalinsa kan dukiyar fiye da komai”, ta ƙara juyowa tana kallonsa ta cigaba da cewa,
“ Tun abin yana burgeni, har ya koma yana tayar min da hankali, domin ya fara taɓa yancina, haƙƙina da kuma mutuncina, to ya zanyi musaddiƙ ba ni da wata hanya domin komai na faɗa ya kan ce ai ni yake taimakawa”.
Musaddiƙ ya juyo yana kallonta wannan karon ido cikin ido sannan yace, “Duk wannan ba kafaffiyar hujja bace da zaki ƙaunaci haram har kiyi mata ado ki kuma ƙawata ta a cikin zuciyarki ba, ni haramunne a gare ki, mijin kuma shine halal ɗinki, gyaran rayuwarki yana hannunki, ki zauna da mijinki, ku canja tsarin rayuwarku, domin baki da wani dalili da zaki bani wanda zan yarda da ke har na taimaka miki wajen ƙaddamar da saƙon shaiɗan a gare ni, ina son ki sani ko a lokacin da nake kan tafarkin shaiɗan, duk irin abinda na aikata to ban taɓa zina ba, ban kuma taɓa sata ba, balle yanzu da nake kan turbar shiriya, na kuma yi tir da wannan buƙatar taki ina kuma shawartarki da ki tuba zuwa ga Allah, ki kuma kori shaiɗanin da yake kanki, domin ba zaki taɓa samun goyon bayana ba”.
Yana gama faɗin haka ya juya a fusace zai tafi ta yi saurin shan gabansa ta tsaya tana maida numfashi a gaggauce.
“ Baka isa ka tafi ka barni ba tare da ka yarda da buƙatata ba, bayan ka gama jin ɓoyayyen sirrina sannan ka juya bayanka a gare ni, saboda rashin imani da kafiya irin ta ka, har wane tsoron Allah kake tutiya da shi, bayan haka wane namiji ne zai iya rantsewa da Allah akan baya bin mata”, ya dubeta sosai cike da fushi yace “ Idan ko tunaninki kenan to kinyi kuskure babba, domin duk lalacewar rayuwa akwai nagari, zan iya rantse miki da cewa kamilallun maza sunfi fanɗararrun maza yawa, sannan ni na rantse miki ban taɓa zina ba tun daga samartaka ta har kawo aurena”, ya ratseta zai fice nan ma ta ƙara shan gabansa duk ta gigice tace “ Ka taimaka min don Allah, ina sonka sha’awarka ta riga ta zamar min fitina” a hankali yace “ zan taya ki addu’ar Allah ya yaye miki fitinar, domin har abada ba zaki taɓa samun abinda ki ke so ba daga gare ni”, itama ta fara fusata tace “kada ka min haka , duk mutuncina da na zubar na gaya maka buƙatata sannan ka ƙi yarda da ni”, ya numfasa yace “ matsa don Allah na tafi”, ta watsa masa harara tace “ Afrah fa ya zakayi da ita”, ya yi mata wani bushasshen kallo yace “ Allah zai duba min ita”, zai wuce ta ƙara babbake hanya alamar fa ba zata yarda ya fita ba, amma ina cikin ƙosawa da tashin hankali musaddiƙ baisan lokacin da ya sa hannu ya ture Haj Hudah gefe ba, ya fice daga falon a gaggauce. Cikin tsananin tashin hankali da damuwa gami da tsantsar mamaki, yana fatan idan mafarki yake yi ya farka, yana ficewa daga get ɗin gidan, saminu ɗaya daga cikin jami’an tsaron Haj Hudah dake kwana a gidan ya ɗaga waya ya danna nambar Alh yusuf sanda, bugu ɗaya ya rarimo wayar ya ɗauka alamar daman kiran nasa yake jira……………….


Yar gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(mrs Aliyu Mayare)

Page 15

“ Saminu ya ya ake ciki?”, ya tambaya a gaggauce, saminu ya yi ƙasa da murya sosai yace “ Ranka ya daɗe, na bi ta ƙofar baya kamar yadda ka gaya min, na kuma yi nasarar naɗo maka komai, ka duba whatsapp ɗinka na tura maka komai”, Alh yusuf sanda ya yi wani murmushi gami da ajiye wata gwauruwar ajiyar zuciya yace “ Da kyau saminu, zan duba yanzunnan, zan kuma turo kuɗin data”, cike da murna saminu yace “Godiya nake Ranka ya daɗe”, yace “ yauwa ka cigaba da aje sirrin mu a zuciyarka ko da wasa ka da ka bari wani ya yi zargin wani abu”, ya gyaɗa kai yace “ In sha Allah”, lokaci ɗaya duk su ka aje wayar.
Da sauri Alh yusuf sanda ya shiga whatsapp ɗinsa, kasancewar baya kashe data kullum a buɗe take, yasa ya na shiga ya tadda har vedio da aka tura masa har ya gama buɗewa, ƙara luntsumewa ya yi kan doguwar kujera yana kallon vedion, duk abinda ya faru tsakanin musaddiƙ da Haj Hudah ya gani tamkar a gabansa aka yi, abin tamkar yana bashi nishaɗi domin yadda yake murmushi yake shafar tumbinsa. Sai dai ƙarshen vedion baiyi masa daɗi ba, ya miƙe ya shiga sinturi a tsakar ɗakin lokaci ɗaya yana magana a fili.
“ Kar dai ace nayi zaɓen tumun dare ne, banyi tsammanin Musaddiƙ yana da tsoron Allah da zai iya tsallake

Please Login or Register in order to submit comment