Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makamancinsa, babu kuma abinda zai girgiza shi domin shi ya shirya wasan a taƙaice ma ba don ka da ya cika baki ba da yace yasan yadda faɗan ƙarshe zai kasance.yace “ ka da ka damu ka sanar da ni komai, ka da ka rage min komai”.

Sannu a hankali saminu ya gama sanar da shi komai , cike da takaici ya ƙara da cewa “ A gaskiya, idan har kana bibiyar Haj ne saboda ka tabbatar da ta na cin amanarka to gaskiya ka yi gaggawar ta ka mata burki, domin maganar gaskiya babu maganar zato ko zargi tabbas Haj tana aikata alfasha da auranka akanta”, ga mamakin saminu sai ya ji yace “Babu komai saminu, Allah dai ya shiryeta bana nufin komai a gareta face shiriya, duk kuma abinda take yi baisa na tsaneta ba ina sonta ina kuma ƙaunarta har yanzu, zan kuna cigaba da yi mata addu’ar fatan shiriya”, sosai saminu ya ji tausayin Alh Yusuf, har ƙwalla ya ji tana ƙoƙarin sakko masa, haƙiƙa ya na ganin samun mutum irin Alh Yusuf Sanda sai an tona, tausayinsa ya kama shi yana ganin mutum irin sa bai kamata da mata irin Haj Hudah ba, ƙarfin halinsa da kuma haƙurinsa sunyi yawa, domin dai ya na ganin ko shi ne matarsa take cin amanarsa haka a gaskiya ko da gold aka halicceta sai ya rabu da ita bayan ya yi mata abinda ba zata taɓa mantawa da shi ba. Amma shi har wami fatan shiriya yake mata.

“Kaima kuma kamar kullum ina ƙara roƙonka ka da ka sanar da kowa wamnan sirrin , ina son ka cigaba da aje min sirrin nan ba tare da ko da wasa wani ya ji ba, saboda maganar mutunci da kimar iyalina ake magana, zan kuma iya yin komai domin ganin na kare wannan mutuncin”, furucin Alh Yusuf sanda ya daki dodon kunnan saminu, lalle Alh Yusuf sanda na dabanne, a wannan dare Saminu ya ƙara ganin kima da darajar sa kamar yadda ya ji ya tsani Haj Hudah da halayenta.

“In sha Allah zan riƙe amana”

Saminu ya faɗa cikin sauti me cike da tausayinsa.

Daga ɗaya ɓangaren Alh Yusuf sanda ya gyara zamansa yana murmushi kafin daga bisani suyi sallama ya kashe wayar, yana buga ƙafarsa a ƙasa, ya fahimci duka kalamansa babu wanda bai yi tasiri a zuciyar saminu ba, kamar yadda ya fahimci ya jefa tsanarta a cikin zuciyarsa shi kuma ya sanya tausayinsa a cikin ziciyarsa, ya yi dariya sosai yace “wannan katin ma da na ke bugawa zaiyi amfani”. Lokaci ɗaya ya miƙe yana shawagi a tsakiyar ɗakin kamar yadda ya saba. Ko ta halin ƙaƙa yana buƙatar wannan vedion da Haj Hudah ke ma Musaddiƙ barazana da shi, domin zaiyi masa amfani mai yawa.

Ya saki wani ɗan matashin murmushi yace a fili, “ Hudah kin gama ɗanɗanar daɗin Musaddiƙ domin bazan taɓa bari ya ƙara kusantarki ba, domin abinda nake nema na samu, ina ta lale katina nasan kuma ni zan cinye wasan tare da riba me tsanani”.
Ya koma ya zauna yana faɗin

“Allah ya kaimu goben”, dai dai lokacin wayar da aka haɗa masa kira da layin Haj Hudah ya shiga ruri, itace take kiran musaddiƙ, ya saki numfashi.

Yaushe rabon da Haj Hudah ta yi waya da Musaddiƙ,da sauri ya cigaba da kallon wayar gami da wannam mugun murmushin nasa yana addu’ar Allah yasa musaddiƙ ɗin ya ɗauka. Sai dai addu’arsa bata ci ba domin har wayar ta ƙaraci kukabta ta katse bai ɗauka ba ita ma kuma bata ƙara kira ba. Ya buga tsaki cike da takaici yace “ Allah ya nuna mana goben”. Ko dai babu komai ya ji daɗin yadda suka koma yin waya domin hakan zai sa ya dinga samun jin halinda su ke ciki.

Babu wani sukuni ga Musaddiƙ a wannan daren, haka ya dinga mirgine mirgine, daga bisani huɗubar da kullum Afrah take yi masa na duk halin da ya shiga ka da ya manta da kai kukansa ga ubangiji, ya yi sake a baya ya yi ragon azanci tare da gangancin kama wanin Allah wajen biyan buƙatarsa, wanda hakan shi ne yake wahalar da shi ayanzu tare da naƙasa dukkan wani ƙwarin guiwarsa, ya na jin tamkar Allah bazai yafe masa kuskuren da ya tafka ba, sai dai kuma Allahu gafururrahim ne yana yin gafara ga wanda ya ga dama , yana kuma gafara ga wanda ya yi nadama ya kuma nemi gafararsa, don haka a gaggauce Musaddiƙ ya tashi ya ɗauro alwala ya shiga gabatar da sallar nafila domin kai kukansa ga Allah baya son komawa saɓon Allah da Haj Hudah ya na addu’ar Allah ya kawo wani sanadin da burinta bazai cika ba.
Saɓanin Haj Hudah da ta yi kwanan farincikin dawo da Musaddiƙ hannunta, ta ƙosa ƙwarai gari ya waye, domin ta na buƙarar ƙara ganin Musaddiƙ jikinta har wani irin sanyi yake yi idan ta tuna zata samu keɓewa da shi.

Har gari ya waye Musaddiƙ baida wani karsashi. Ya amsa kiran Murtala a ofis ɗinsa Murtala ya tabbatar masa da cewa takardunsa sun sami shiga wani babban kamfanin gine gine da yin hanya da suka buɗe branch anan Minnan, kamfanin da tunda daɗewa ake ta raɗe raɗin cewa za’a buɗe branch a Minna, ko bayan barinsa aiki a kamfanin Musaddiƙ ya na ta addu’ar Allah yasa a kawo branch ɗin, sai gashi ba’a buɗe ba har sai bayan da ya sami aiki, don haka ya yi sha’awar ya nema ma Musaddiƙ aikin . Don haka ya sanar da shi sai a cigaba da addu’ar Allah ya tabbatar. Wannan albishir shi ne ya faranta ran Musaddiƙ har ya so ya manta damuwar da yake ciki, ya yi ma Murtala godiya sosai, daga nan kai tsaye gidan Inna Halima ya wuce.
Haka ya isa gidan Inna Halima babu yabo ba fallasa, wanda daga Afrah har Inna Halima sun gane a kwai matsala, dama ita Afrah tasan akwai damuwar kawai ta ƙyale shi tunda ya ƙi gaya mata, hakan yasa yauma ta tsuke bakinta ta ƙi tambayarsa abinda ke damunsa tunda tasan ko ta tambaya zai ce mata bakomai ne, bayan kuma tasan akwai komai. Yana riƙe da Hanan ya na aikin yi mata wasa, yaƙen dole kawai yake yi. Inna Halima ta aje masa tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya sai tashin ƙamshin man shanu take, abinci su na rana kenan. Ta ɗan dube shi tace “kawota ka ci abinci, don daga ganinka nasan ko karyawa ba kayi ba”. Idanunsa ya ɗago ya ɗora akan Afrah wacce tuni ta rage walwala. Ya yi saurin ɗauke kansa ya dubi Inna Halima ba tare da yace komai ba ya miƙa mata Hanan. Domin idanun Afrah da ke kansa sun hana masa yin musun ba zai ci abincin ba. A hankali ya buɗe kwanan tuwon, Afrah ta taso ta iso gabansa, faranti ta ɗauka ta janyo kwanon ta ɓare ledar tuwon guda ɗaya ta zuba a farantin tasa miya ta ɗora cokali akai sannan ta miƙa masa, jiki a sanyaye ya amsa, ba tare da tace uffan ba ta tashi ta koma wajen zamanta.

Inna Halima ta ɗan saki numfashi tana kallon yadda yake juya cokalin a cikin miya, tace “Nayi zaton daga lokacin da Afrah ta sami lafiya kayi bankwana da damuwa, amma ga mamakina sai naga ko kaɗan baka fita a cikin damuwa ba, maimakon hakama sai rama da ka ke ƙara yi, ga rashin walwala da natsuwa, wai menene kuma damuwar yanzu?”. Kafin ya yi magana Afrah ta yi wuf ta amshe maganar tamkar tana jira, “Ai Inna dama kin daina ɓata bakinki tunda bai shirya gayama kowa damuwarsa ba ce miki zaiyi babu komai, tunda kuma ya na ganin bai dace mu musan damuwarsa ba ai shikenan, kullum addu’ata tana kansa Allah ya yi masa maganin abinda ke damunsa”, Inna Halima ta gyara zamanta tace “To Afrah barin kashi a ciki ai baya maganin yunwa, idan har Musaddiƙ yana da damuwar ai gara ya fito da ita mu sani mu kuma taimaka ko da da shawara ne”, Afrah ta kauda kanta tace “To bazai faɗa ba Inna ai gara a ƙyale shi”.
Duk wannan maganganun da suke yi idon Musaddiƙ nakan Afrah yana hango tsantsar fushin da tayi, na rashin gaya mata damuwarsa, tabbas idan bai ɓoye damuwarsa ba to da kansa zai tonawa kansa asiri, Allah yasa ma a yanzu yana da abinda zai iya gaya musu domin kau da tunaninsu akansa.
Don haka ya muskuta lokaci ɗaya ya kai lomar tuwon bakinsa ya tauna ya haɗiye, Afrah ta saki ajiyar zuciya abincin da ya fara ci ji tayi kamar an sauke mata wani babban kaya asaman kanta, ta maida idanunta ta lumshe.
Maganar da ta ji ya fara ne yasa ta buɗe idonta ta na kallonsa.


“Inna ina cikin damuwa ne, naso kuma sai bayan na sami gidan da zamu zauna sannan zan gaya muku, amma tunda naga kun damu zan sanar da ku komai”.

Nan da nan Afrah ta sami natsuwa

“Ka gaya mana yaya menene?”

Ta faɗa cike da ƙaguwa, tana kallon Inna Halima, da itama ta ke faɗin

“Ko menene ka sanar da mu”.

Ya ɗan saki numfashi yace “Hassana ce ta zo min da maganar da ta tayar min da hankali, akan cewa zasu sayar da gidan da muke ciki, saboda a halin yanzu ba su da halin ɗaukar ɗawainiyar Haj kuma gidan mahaukatan suna bin maƙudan kudaɗe, sannan babu abinda ya rage ma Haj a duniya sai wannan gidan shi yasa zasu sayar a cigaba da nema mata lafiya”.

Jikin Afrah ya yi sanyi tausayin Musaddiƙ ya ratsa zuciyarta ta yi ƙuri d ido tana kallonsa, Inna Halima ma shuru ta yi, kafin ya cigsba da cewa.

“Wannan gidan shi ne alfaharin mahaifina, duk ɗimbin arziƙin da Allah ya bashi da tarin gidaje da kadarori bai taɓa tunanin tashi daga gidan ba don wai ya canja muhalli duk da wasu gidajen nasa ma sunfi shi kyau, yana son gidan ƙwarai da gaske, sai gashi kuma yau gidan zai salwanta, zai faɗa hannun wani”, ya waiwaya cike da raunin zuciya yana kallon Inna Halima yace “karo da dama kenan da na ji takaicin suɓucewar damata, a dalilin Haj kilishi da Hannatu, don yau da ina da dama ni zan sayi gidan nan”.
Inna Halima ta numfasa tace “ ka da ka shiga damuwa akan wannan, shi duk abinda ka ga ya sami bawa to daga Allah ne, yanzu ita kilishin da tayi maka zamba cikin aminci, me ya tsinana mata sannan me ta aje?, ina ce komai ya kakkaɓe gashi har ana shirin saida gidan da ya rage mata a duniya, yau ina kuɗi da kadarorin da ta rabaka da su, babu naka babu nata, ƙarshe ma gata can gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya, ko ko ita Hannatun da tun ba yanzu ba itama suka rasa komai ita da magaufiyarta, ga ciwo da ya sami mahaifiyarta babu mai kula da ita, ga rashin kuɗin da zata kula da ita, uwa uba har yanzu na ji labarin ba ta da wani manemi tsayayye, banyi niyyar gaya maka ba ne, amma zamanmu a asibiti a Abuja da Afrah na haɗu da ita wajen sayen magani”.

Da sauri Musaddiƙ ya dubeta yace “Hannatun Inna?”.

Ta gyaɗa kai tace “Ita fa Musaddiƙ, mun haɗu tana cikin mawuyacin hali ta gaya min mahaifiyarta ta kawo asibiti amma sun ƙi karbarta saboda babu kuɗin gado shi ne suka rubuta mata magani kawai, to shi ma maganin ta zo ta ji tsada ba zata iya saya ba, zasu koma gida ne kawai, har ƙasa ta duƙa tana roƙona na baka haƙuri ka yafe mata abubuwan da ta aikata maka itama ba’a son ranta ta aikata ba, tuntuni take neman yadda zata nemeka ka yafe mata amma tana jin nauyi da kunya da kuma tsoron rashin sanin abinda zaka yi mata, to ni ma dai banyi mata alƙawarin zan gaya maka ba tun a wajen kuma na sanar mata da hakan, yanzu ma ɗaurowa ta yi na gaya maka”.
Afrah ta ƙara zubama mijinta ido tana jin Musaddiƙ ya cancanci ya sami farunciki ko ya ya ne a rayuwarsa, domin dai bai san daɗin rayuwa ba. Inna Halima ta katse mata tunaninta da cewa “Shi yanzu sha’anin duniya tun a duniya Allah ke yin sakayyarsa ga duk wanda ya zalunci wani, saboda haka ka daina damuwa da komai, in sha Allah Musaddiƙ zaka ɗaukaka ko don wannan siraɗin na rayuwa da ka ke tsallakewa kullum”. Afrah tace “Abinda Inna ta faɗa gaskiya ne, don Allah yaya ka aje duk wata damuwa ka manta da komai, ka fuskanci rayuwarka ta gaba, batun sayar da gida kuma su je su sayar shi ma wanda ya gina ya tafi ya bar shi, ka sami natsuwa, ba zamu rasa inda za mu zauna ba ko da gidan haya ne, ka da ka damu”.
Musaddiƙ ya numfasa yace “Nagode da ƙarfafa guiwarku a gare ni”.

Ya juya ya dubi Inna Halima yace “Inna kinga batun komawar Afrah gidan dole mu dakata sai zuwa lokacin da na sami gidan haya tunda da gaggawa suke son sayar da gidan, yanzu zan tuntuɓi Murtala tunda ya na da hanyar gidajen haya ta ɓangaren yayansa, idan na samu ta hanyarsu shikenan”, Inna Halima ta cigaba da dubansa cike da ƙauna tace “kada ka damu, ayi komai a natse a sami gidan mai kyau, akwai kuɗi a hannun yaya Mahmud na kadarorin mu da muka sayar don a biyama Afrah kuɗin aiki, kaga sai muyi amfani da su wajen kama muku gidan, kafin Allah ya hore maka gidan kanka da muke fata”.
Musaddiƙ ya yi saurin kallon Inna Halima idanunsa na son cika da ƙwalla yace “Na rantse Inna ko kaɗan ba na jin damuwar rashin mahaifana domin taɓangarenki duk abinda uwa ta kema ɗa shi ki ke min babu wani bambanci, shi ma kawu Mahmud taɓangaren mahaifi babu abinda ya gaza akaina, ya Allah ya ba ku ladan zumunci, Allah ya saka muku da alheri ya yi muku sakayya da gidan aljanna”.
Inna Halima ta yi murmushi tac “ kai ɗana ne halak malak, don haka duk abinda na yi maka babu godiya, domin duk abinda na yi maka kaina na yi ma”.
Afrah ta aje numfashi ahankali tace “inna mun gode Allah ya saka da alheri”

Ta ɗan sakar mata harara cikin sigar wasa tace “Bana ce babu godiya ba”. Gaba ɗaya suka yi dariya, Inna Halima ta yunƙura da Hanan ta fice domin ta cire mata Pampers da ta ji alamar kamar ta ɓata shi.
Kamar yana jira ta fita ya yi saurin tsallake kayan abincin ya dawo kusa da Afrah, ya lalubo hannunta ya riƙe, yana kallonta, ta yi murmushi tace “yaya dai?” Ya ƙara matsanantar ta yace a hankali “ Marmarin abin jiya nake”, ta saki dariya tana ture shi tace “Aiko duk kwaɗayinka sai dai ka haɗiye shi domin kaima kasan yau babu abinda zaka samu tunda Inna na nan”, ya tura hannunsa cikin rigarta yana ƙoƙarin shafawa tana zillewa “ ki barni mana tunda bazan sami na jiya ba.na yi abinda zai lafar min da sha'awata”. Ta yi tsalle gefe tana faɗin"Ba da ni ba.kawai Inna ta shigo ta gan mu.bari ka gani" ta nufi kayan abincin ta ƙwashe ta fice tana dariya.

Ya jingina sosai a jikin bangon gami da lumshe ido, baya jin zai iya fassara irin son da yake ma Afrah, ya na sonta so na haƙiƙa.
Lokaci ɗaya gabansa ya faɗi da Haj Hudah ta faɗo masa arai. Ya yi saurin kallon wayarsa har yanzu bata kira shi ba, sosai yake addu’ar Allah kada ya bata ikon kiransa.

Dai dai lokacin kuwa Haj tana kwance lamau a saman gadonta ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi, zuciyarta ta yi baƙi, damuwa ta addabeta ji take kamar ta ɗora hannu aka ta fasa ihu, tun bayan samun wayar Alh Yusuf sanda na bazata ta rasa sukuni.
Ta ɗan saki tsaki tace “ Don me bazai gaya min zai dawo ba tun jiya?, waye yace masa ina son bazata Sam bata burge ni, sannan har yace bai buƙatar kowa ya je ya ɗakko shi a airport sai ni”. Ta ƙara sakin tsaki, ya riga ya rushe mata duk wani tanadi da tayi ma Musaddiƙ, yanzu shikenan ba zata haɗu da musaddiƙ ba duk mafarkin da ta kwana ta na yi bazai tabbata ba. Bata taɓa Allah wadai da jin haushin dawowar Alh Yuauf irin wannan karon ba, me yasa baiyi zamansa ba?.
Ta ɗaga ido ta dubi tangameman agogon da ke maƙale a jikin bangon ɗakin, zuwa yanzu ya ci ace ta shiga Abuja daga sanda ya kirata cewar ya sauka amma ta rasa ƙarfin guiwar tashi ta tafi. Wayarta ta ɗauki ƙara sunan mijinta ya fito, ido kawai ta zubama wayar harta katse bata iya ɗauka ba, second biyar tsakani saƙonsa ya shigo cikin wayar.

“Ina cikin airport har yanzu, ina zaman jiranki”. Abinda ya turo kenan. Ta ja wani dogon tsaki lokaci ɗaya ta duro daga kan gadon, sai da ta tsaya a gaban madubi ta gama kallon ƙasaitacciyar ƙwalliyar da ta yi ma Musaddiƙ wacce dole zata zama rabon Alh Yusuf sanda. A haka ta fita bayan ta ɗau jakarta da gyale, direba dake zaman jiranta tana fitowa ya buɗe mata ƙofar motar ta shiga tana shiga ya ja motar da sauri suka bar gidan fuskar ta a dagule. Suna fita, saminu ya ciro wayarsa ya kira Alh Yusuf kamar yadda ya bashi umarnin ta na fitowa ya sanar da shi, bayan ya ɗauka ne ya sanar da shi yanzun nan ta fito amma cikin ɓacin rai ta ke.
Godiya kawai ya yi masa ya kashe wayar yana dariya sosai, ya na faɗin ai dole ta fito cikin ɓacin rai tunda na watsa mata shirin haɗuwa da Musaddiƙ………………..

Yar Gidan Imam✍️
MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Mayere)

Page 22

Alh Yusuf sanda ya janyo kwalin sigarinsa ya zari ɗaya ya kunna ya zuƙi hayaƙin ya fesar da hayaƙin ta baki da hanci, sannan ya ɗauki kofin tataccen lemonsa ya kurɓa, ya na murmushin nan nasa da ya zama tamkar ɗabi’ar rayuwarsa, ya ƙara mimmiƙe ƙafa ya na jin tamkar ya riga ya gama cinye wasan.
Ita kam Haj Hudah ko a cikin motar hankalinta baya jikinta, ita kanta tasan ya zama dole ta mallaki natsuwarta ta kuma kori damuwarta, kamar yadda ya zama dole ta canja salonta a gaban mijinta, domin ko kaɗan bata son ya gane akwai wani baƙon al’amari a tsakaninsu wanda har zai sa shi zargin wani abu a tattare da ita.
Gaf da shigarsu Abuja ne, wayar Alh Yusuf sanda ya shigo wayarta, cikin ƙarfin hali ta ɗauka gami da daidaita muryarta tace “Ranka ya daɗe”, ya ɗan shafi gemunsa ya na murmushi yace “Tare da naki uwargida kuma amarya daga kan ki an rufe ƙofa makullin ma an jefa shi a tekun maliya”, ya na maganar ne cike da ƙwarzanta ta, hakanan ta ji ranta ya ɗanyi mata sanyi, ta ɗan saki murmushi tace “Allah yasa har cikin zuciya ne”, duk da yasan ta sigar wasa ta faɗa masa naganar to fa sai da ya ji wani yarrrr a cikin jikinsa domin ji ya yi tamkar ta buɗe zuciyarsa ne ta hango tsantsar ƙarya ya danƙara mata.
Da sauri yace “Har cikin zuciyata nake wannan maganar Hudah, zan kuma tabbatar miki da haka idan muka haɗu”, ta ƙara murmusawa tace “To godiya nake”, ya ɗan yi jim na wasu daƙiƙai sannan yace “Na yi ta jiranki a airport har na gaji, ga gajiyar tafiya dama ta riga ta gama nuƙurƙusata, amma ba ki iso ba, na kira ki na sanar da ke cewar na gaji da zama na yi hayar taxi zuwa sheraton hotel, amma ba ki ɗaga wayar ba, yanzu haka ina can ina jiranki a ɗaki mai namba hamsin da biyu”, ta saki ajiyar zuciya tace “Banga kiranka ba sai yanzu da ka kira ni, ayi haƙuri na kusa isowa sai da na tsaya ƙarasa wani meating ne kasan ka gaya min dawowarka a ƙurarren lokaci da kuma sharaɗin da ba ka taɓa gindaya min ba na cewa dole sai ni zan zo na ɗauke ka, kaga da na san haka da wuri da tuni na soke komai tun farko”.
Nan ma murmushi ya yi, kar yake kallonta don dai ya riga yasan dalilinta na rashin tahowa da wuri, ya so da ta hutasshe da kanta wajen dole sai ta yi bayanin kanta a wajensa domin ya fi kowa sanin ko ita wacece, ƙasa ya yi da wayar ya kashe ya maida idonsa ya runtse hakanan ya ji ya na jin takaicin ƙaryar da take masa. Katsewar wayar baisa ta kira ba kamar kuma yadda bai sa mata wani tunani a ranta ba.
Kafin isarta hotel ɗin ya riga ya gama gyara komai yadda babu wanda zai ɗauka ya daɗe a hotel ɗin, komai ya na nuna yau ya shigo hotel ɗin.
Haka zalika Haj Hudah ta yi mamakin yadda Alh Yusuf sanda ya furfure cewa ba zasu koma Minna ranar ba, yace ya na da buƙatar ƙara yin hutun sabon amarci, direban da ya kawota ma da kansa ya sallame shi ya koma da motar a cewarsa zasu kira ranar da zasu dawo
Zahiri har cikin zuciyar Haj Huda bata ji daɗin wannan bazatar da mijinta ya ke yi mata ba, duk yadda ta so ta nuna masa tana da ayyukan da ta tsallake ta bari ta taho gunsa ya kasa fahimtarta,
Gashi bata son ya gane komai, bata son ya fahimci ita ɗin fa a yanzu babu shi a ranta ko a zuciyarta.
Ƙila hakanne yasa ko kaɗan duk wamnan bajintar da yake yi don ya burgeta ya kasa burgeta ko kaɗan.
Hatta kaya da bata zo da shi ba, tace ya bari taje gidanta na abujan ta ɗakko ƙi ya yi, da kansa ya yi shatar taxi ya fita da daddare domin ya sayo mata ƙananan kaya, kamar ta na jira ya fita ta ɗakko waya ta kira Musaddiƙ, Alh Yusuf na bayan mota ya ɗauki tasa wayar, sai da ta kira har sau uku a cikin na huɗun ne ya ɗauka, cikin wata nannauyar murya tace “Haba Musaddiƙ ko ya ya ne ai ya kamata ace kana nuna damuwarka a kaina”, cikin rashin walwala yace “Don me zan nuna damuwa ta a gareki? A matsayinki na wa? Me na haɗa da ke?”.
Ji ta yi furucinsa ya daki zuciyarta ta yi zumbur ta miƙe tsaye tace “Ni kake gaya ma waɗannan maganganun Musaddiƙ, to babu amfanin na baka amsa domin ka riga ka san amsar”.
Bai tanka ba ta cigaba da cewa “Yanzu da ka jini shuru ba zaka iya kirana ka ji halinda nake ciki ba, bayan kasan abinsa zai hana mu haɗuwa ba ƙaramin al’amari ba ne”.

“Don me zan kira ki, idan nayi

Please Login or Register in order to submit comment