Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ[10/25, 11:38 AM] H InnaπŸ§•πŸΌ: [10/25, 11:18 AM] H InnaπŸ§•πŸΌ: (DA BAN SAN SHI BA) KASHI NA DAYA

(DAGA FAUZIYYA D. SULAIMAN)

(WANDA NI Zeinab Andiya Fox ZAN KAWO MUKU SHI)

(KAUYEN SANBAUNA)
(1)
Sararin samaniya yayi bak'ink'irin sai tsawa da ci da ake yi, garin ya murtike alamar daga lokacin zuwa ko yaushe za a iya tsinkewa da ruwa, kasancewar lokacin damina ne.
Sumaye tana tsugunne gaban murhun duwatsu guda uku tana hura wutar da bakin ta, kasancewar karan da take amfani da shi gurin girkin ya jike sharkaf da ruwa shi ya sanya yake bata wahala gurin hurar, idanuwan ta sun kada sunyi jajir ga yamma tayi rana na shirin fad'uwa, ga kuma hadari dake shirin zubar da ruwa bugu da k'ari kuma tsohon ciki da take d'auke da shi duk ta jigata tayi wuki-wuki da ita.
Lanto abokiyar zamanta da d'iyar ta mari da salame suna zuaune a gefe suna 6arar tumun dawa suna watsawa abakunan su da suka gasa, cikin hira da kallonta suna murmushi daga nesa inda suke zaune. Lanto tayi kwafa "a dai yi mu gani idan tusa zata hura wuta. "Sumaye ta dago ta kalleta kamar zatayi magana
[10/25, 11:37 AM] H InnaπŸ§•πŸΌ: Saikuma ta fasa taci gaba da abin da take yi, amman har lokacin idan karan ya huru sai kuma ya mutu. Alu ya shugo gidan cikin gaggawa yana dauke da daurin kara timili guda akan sa, yaro d'an kimanin shekaru takwas, mai kuzari da kazar-kazar, sallamar shi ce ta sanya lanto da 'ya'yanta waigawa da sauri suka kalle shi, mamaki da takaici ya bayyana akan fuskarsu domin basuyi tsammanin dawowar sa gidan ba yanzu, burin su bai wuce a tsuge da ruwa, samaye ta kasa yin tuwon dare maigidan yayi fad'a kamar zai rufeta da duka ba. Sumaye ta waiga ta kalli Alu farin ciki ya bayyana akan fuskarta, Alu yaisa gabanta ya ajiye damin karan yana murmushi. Sannu da aiki Inna? Sumaye tayi murmushi. Sannunka mai Sango, amman kayi sauri, banyi zaton zaka dawo haka da gaggawa ba. "Tana k'ok'arin zarar karan. Yayi murmushi ya k'arasa da murhun" ganin hadarin ya gangamo ya sanya nace bari na yi gaggawa, gashi sai dana kutsa can cikin jeji na samo busasashe, bari na hura miki koma zauna ki huta inna. Sumaye tayi baya cikin farin biki[8/1 01:13] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (3) maza je ka amso min. Alu ya d'aga idon sa ya kalli sararin samaniya inda hadari ke kara had'owa, sannan ya kalli murhun mahaifiyarsa, ya maida dubansa kanta, ta fahimci abinda yake kissimawa a zuciyarsa amman bata bari yayi k'okarin furtawa ba ta katseshi ta hanyar kara jajjada abin da ta fad'a tun farko. Alu ya d'aga kan shi alamar to, sannan yayi hanyar fita da gudu, lanto ta bishi da kallo gami da rike haba tana kada kai. "Tabbas idan kana wannan duniya zaka ga abubuwan mamaki da zaka gaza cewa komai, ban ta6a ganin irin wannan rayuwar ba bayan a gidan danke ciki ba, d'a namiji daya kasance haramun ayi mu'amala da shi shine abin ja a jiki tamkar d'iya mace? Tayi kwafa tana hararar sashin da sumaye take. Sumaye bata kula ta ba ta nufi gurin da garin tuwon ta ke ajiye ta dauko ta fara zubawa cikin k'warya, daman tana da ruwanta cikin kwatanniya don haka ta isa gurinta ta d'iba ta fara k'ok'arin talga tuwon, dukkan abin da lanto ke fad'i na habaici da k'azafi akan kunnenta har dariyar da yaranta keyi,
[8/1 01:13] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Can kasan zuciyar ta tana tausayin lanto domin tana ganin aibun koyawa yara musamman mata irin wad'an nan halaye da su daza su kasance gidan wasu, amman tasan rashin sauraran rediyo ke sanya lanto yin komai. Sumaye bata kasance mai ilimi ba, domin garin su babu wasu makaramtu na islamiyya dana addinin idan ka d'auke wata makaramta allo dake ba hayin garin su wacce sai an tsallaka ruwa ake zuwa, kasancewar su mata subasa zuwa wannan makaranta sai dai tsoffi masu karantun tsakar d'aki kan shiga gida-gida suna koyar dasu, da zarar an yiwa yarinya aure kuma shi kenan sai dai ta mai da hankalin ta ga bautar gidam ijin ta maganar karatu kau ta kare, sai ta fara girma ayyukan gida sun ragu, amman ita sumaye tana da kwakwar jin rediyo wacce ta tara kud'i da kyar ta siya, kusan itace mace ta biyu dake da rediyo a garin, sau da dama zakaga mata sun zagayeta suna jin rediyo, amman bata fiye samun damar kunnawa kasancewar babu hanyar siyan batiri sai an shiga babban gari ko binni wanda tsananin su da babban kauyen[8/1 01:15] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (4) da suke hauwa motar daza ta sada su da binni kusan tafiyar kilomita uku ce, don haka sai ranar kasuwa ake samun siyo mata batirin idan tana da kud'in a hannunta. Sumaye ta kammala talgen ta fara zubawa cikin ruwan dake tafasa tana juyawa da muciya aka fara yayyafi, lanto da yaranta suka tashi da gudu suka shige cikin dakin su wanda ya kasance na kasa suna dariya. Sumaye tayi tsaye cikin damuwa, ta daga kai tana kallon ruwan, wanda ya fara saukar mata akan fuskarta, ta maida dubanta ga karan data sanya cikin wuta, ruwa ya fara sauka akansa kad'an-kad'an, duk ida ruwa ya ta6a wutar gurin ta mutu, idamuwan ta suka kawo kwallo tausayin kanta da irin fad'an da malam Beld'o zai yi idan ya dawo bata kammala tuwon dare ba ya bijiro mata, ta durkusa ta fara kokarin maida kararan tana hurawa, yayyafin bai karu ba bai kuma ragu ba, amman wutar bata mutu gabad'aya ba, hakan ya bata kwarin gwiwar cigaba da yin abin da take yi. Kamar an wurgo shi sai ga Alu ya dawo da gudu cikin gaggawa, rigar dake jikinsa 'yar shara
[8/1 01:15] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Ta yadin dan madima ta jike da ruwa sharkaf, ta kalleshi da mamaki bakinta a bud'e. "Maisango har ka dawo? Ya daga kai yana haki "na dawo inna, acan baki ga ruwan da akeyi ba, amman nan ba'ayi da yawa. Ya mika mata sassaken dake hannunsa wanda babu ko leda a jikin sa. "Gashi tace tanagaisheki. Sumaye ta amsa tana murmushim jin dad'i" allah yayi maka albarka, maza wuce d'aki kada ruwan ya kara jika ka. Alu ya kad'a kai "Inna kije d'aki kizauna ki huta tuda bakya jin dad'i, bari na kular miki da wutar kada ruwa ya jika ki ciwon ki ya tashi. Sumaye tayi murmushi tanufi hanyar d'akin ta, domin bata son hana shi aikin ladan da yayi niyya, a cikin ranta tana godiya ga ubangiji daya bata alu. Har zuwa sanda ta kammala tuwan daran ruwan nan bai tsuge ba, sai dai kamar jira ake ta kwashe cikin kwanika ta mik'awa kowa nashi ruwa ya kece, lokacin tana kwance akan gadon ta na karfe, tayi murmushi da godiya ga allah ya sanya sai yanzu ruwan ya kece. Ta kai dubanta ga Alu wanda ya fara bacci yaci tuwansa ya k'oshi tayi[8/1 01:16] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (5) Tayi murmushi, haihuwar ta takwas amman dukkamsu basu zama, wani wata uku yake ya mutu wani shekara, waini wata biyar, Alu kad'ai allah ya bata wanda shine d'ana biyar cikin yaran data haifa, sai kuma kanne guda uku da suma suka rasu, shi kansa Alu bata ta6a sanya rai zai kai wannan lokacin ba, amman sai allah ya raya mata shi, domin an sha gaya mata tunda wabi takeyi baza ta samu d'an da zai rayu ba sai tayi haihuwa goma, amma ciki ikom allah alu ya rayu har tsohun shekaru takwas, hakan ya sanya suka shak'u, bata da abokin hira sai shi, kasancewar basu zaman jituwa tsakanin ta da kishiyar ta. Lanto tana daga cikin matan da ake labarin kishin su ciki garin san6auna, sannan shi kansa maigidan nata ya kasance mutum ma'abocin fad'a da saurin fashi ya sanya ta kasance cikin damuwa, domin babu wanda zata gayawa abin da yake damunta, Alu shine wanda take zama dashi tayi hira taji dad'i, wanda hakan ya sanya kishiyar ta da yaranta tsangwamarta. Yayan lanto bakwai, maza uku mata hudu, mazan sune manya, don haka
[8/1 01:16] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Basu gidan an kaisu almajiranci, domin kusan d'abi'ar garin ce dukkan yaran su akan fita dasu binni yin karatu wanda aka fisani da almajiranci, sai matan suka rage a gabanta, babar cikin matan salame, itace mai shekaru goma sha hud'u, sai mai bi mata da take shekaru shabiyu sai ta ukun mai shekara biyar karamar shekarar ta uku, daga kanta bata kara haihuwa ba, hakan kuma bakaramin k'onatamata rai yake yi ba, don haka kullum cikin hanyar da zata samu ciki take, bayyanar wannan cikin na jikin sumaye ya tsaya aranta kwarai da gaske, har ya zamo bai barin ta bacci, ita da take burin ace yau Alu ya fad'i ya mutu kamar yanda sauran 'yan'uwansa keyi amman sai hakan ya kauce sa6anin zaton ta kullum kara girma yake yi da kua k'aunar taimakawa mahaifiyar sa, wannan shine abin da keci mata tuwo a k'warya, sai kuma wannan cikin na jikin sumaye, wanda bata san me za'a haifa ba. Rayuwar gidan mai mutuwar wahalar ce, domin mai girki ita zata yi surfe ta daka garin tuwan ta d'ebo ruwa a rafi sannan tayi girkin, don ma girkin[8/1 01:16] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (6) sau d'aya ake yi tak, shine tuwan dare, shi za'a ci da daddare sannan a dumamashi da safe, sai kuma aci da rana idan yayi saura, idan kuma bai yi saura ba sai mutum ya nemarwa kansa abin da zaici da yaransa, kamar tafasa ko sauran kayan anfanin gona idan lokacin sune, idan kuma ba lokacin su bane ba, sai mace ta daka fura kamar ta sati guda suna damawa da ruwa suna sha, kusan wannan itace al'adar dukkan mutanan garin, domin babu wadatar arzik'i a garin bayan noma da kiwo. Rayuwar dukkan matan garin tana cikin wahala, domin tsakanin mace da miji shine yayi noma ya kawo mata danyan abinci, ita zata sissika abin da za'a dafa sannan ta daka kuka ko kubewar miya, ita zata samarwa kanta daddawa da gishiri da manja da barkono wanda sune kayan hadin miyar kawai, lanto bata da matsalar samun duka wad'an nan abubuwan kasancewar tana da 'ya'ya mata da takan dora musu talla musamman a bangaren sumaye abin ya kan zamo mata mai wuya , hakan ya sanya take amsar surf ko wani abin da tasan zata samu kudin dazata sai
[8/1 01:17] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Wad'an nan kayan, maganar sutara ma ba su santa ba, daga kayan lefe sai kuma idan mace ta haihu mijin yayi mata zanin goyo. Kamar kullum yau ma haka sumaye ta kwana juyi bata iya bacci domin nauyin cikin dake jikinta, tana kai kallonta ga malam. Beldo dake baccin shi a baban gadon k'arfe wanda ya zamto na shi shi d'aya, shi kuma Alu yana kwance akan k'aramin gadon, ita kuwa tana zaune bisa tabarmar karauni ta jingina jikinta da garun d'akin, haka nan rayuwar ke zuwar mata ko da yaushe musamman idan tana da ciki. Amman akwai wani abu dake damun ta cikin ranta, hakan ya sanya duk lokacin data kalli Alu sai idon ta ya cika da kwalla, kullum tayi sall tana addu'a akan wannan abin dake yawo cikin ranta game da d'anta, ta mike tsam daga inda take ta taka da kyar kasance kafarta akwai kumburi, takai dubanta ga maigidanta mal. Beldo, sai ta k'ara kai kallon ta ga Alu ta isa kusa da shi ta zauna ta kura masa ido, sai ta sanya hannunta bisa goshin sa ta fara addu'a tana tofawa a hannunta tana shafa masa, duk da bawani[8/1 01:17] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (7) ilimin kirki gare ta ba, amman taji a rediyo anacewa kayi addu'a da abin da ka iya, don haka fatiha da kulhuwallahu sune abin da tayi, sutake yiwa yaronta addu'a dasu kullum. Tajima tana yi masa addu'a, amman bata san mai ya sanya yau zuciyar ta ke rawa gabanta ke fad'uwa akan yaron ba, tana jin kamar zata iya mutuwa ta barshi, tana jin kamar yaune dare na karshe da zasu kara rayuwa tare, tabbas wannan cikin dake jikin ta yana daga cikin dake bata wahala kwarai da gaske a rayuwarta, sannan shine cikin da ya dad'e a jikin ta har ya wuce k'a'idar sa, idan ba taba bata lissfi ba kusan watanshi goma shadaya kenan yana jikin ta, haka ke sanya hankalin ta tashi a duk sanda ta tina halin da Alu zai iya shiga bayan bata duniyar ko kuma d'aya tinanin da yafi damunta cikin ranta, sai wajan gefen sallar asuba ta sami bacci ya d'auke ta, shima ba mai dad'i Ba, domin tanayi tana farkawa. SABO TIRKEN WAWA. Tun da gari ya waye Sumaye batajin dad'in jikin ta, dukkan abin da takeyi k'arfin hali takeyi amman bata jin dadin
[8/1 01:18] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Komai, Alu yana ta kai wa da komowa yana d'auko mata ruwa, tunda ya tashi da asuba bai hutaba, kasancewar akwai tazar tsakanin rafin da gidan su, sai da ya cika mata kwatanniyar ta sannan ya samu ya zauna yana hutawa, can ya k'ara hangota gaban murhun duwatsun tana hura wuta da zata d'umama tuwan safe, duk da shekarun sa ba yawa ne dasu ba amman ya fuskanci duk sanda ta zauna gaban murhun nan tana shan wahala saboda durk'uso, ya mike da sauri ya nufeta yana fad'in. "Inna bari na hura miki. Bata yi musu ba taja da baya tana murmushi, ya durk'usa ya fara hura wutar cikin sabo da yi. Mal. Beld'o ya shigo gidan cikin sauri kamar wanda aka koro yana sabe tsohuwar babbar rigarsa, babu ko sallama ya banko gidan, sumaye ta kalleshi da tsananin mamaki tana fad'in lafiya dai ko malam? Mal. Beld'o ya kalli Alu dake durk'ushe gaban murhu yace "kai maisango maza shiga cikin d'akin ka d'auko tsummokaranka, yanzu nake jin labarin mal... Dayazo ganin gida yana shirin komawa can binni." mamaki da tsora suka bayyana a fuskar[8/1 01:18] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (8) Sumaye ammam ta kasa magaNa sai kallon malam Beld'o da take yi cikin rud'ani, Alu bai ji abin da mahaifinsa ke cewa ba, domin hankalin sa gaba daya yana kan hura wutar, don haka yaci gaba da abin da yakeyi, Lanto ta zagayo daga kewaye rike da buta a hanNu yanayinta akwai tsananin farin ciki da murna aka fuskarta ta kalli mal. Beld'o. "Malam kamar magana naji kanayi ko? Mal. Beld'o ya k'ara kai kallon sa ga alu "kinga yaron dana keyi wa magana yayi kunne uwar shegu dani, kai Maisango baka jini bane? Alu ya waigo da sauri ya kai kallon sa inda mahaifinsa yake tsaye gami da fad'in "baba nazo ne? Lanto tayi dariyar jin dad'i gami da fad'in sarai fa yana fa jinka malam, amman ya nuna kamar bai ji abin da kace ba. Mal. Beld'o yace masa maza d'ebo tsummokaranka nace ka taho malamim dana ce zan had'aka dashi zai koma binni yanzu. Alu yayi narai-narai da ido kamar zai fasa kuka, ya kai kallosa ga mahaifiyarsa wacce ta Kauda kanta gefe sannan ya maida dubansa ga mahaifinsa yana fad'in Baffa sai na kara girma,
[8/1 01:18] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Sai inna ta haihu. Mamaki ya bayyana akam fuskar malam beld'o. Lanto kuwa tafa hannu ta kama yi tana sallallami allh buwayi, kaji fa mal, ai daman na gaya maka duk sanda matar nan ta sanya d'an nan a cikin d'aki hud'ubar banza take masa kala-kala, banda haka yaya wannan karamin yaron zai san girma da wata haihuwa, ko idan ta haihun uwar me zai iya yi? Hawaye ya fara kokarin zubowa daga idon sumaye, amman tayi kokarin sunkuyar da kanta k'asa tana kokarin had'iye damuwarta, mal. Beld'o ya maida dubansa ga sumaye. Sumaye kina jin abinda maisango ya fad'i ko? Yara nawa ya tashi ya tarar a gidan irinsa maza masu shekarunsa, dukkan yaran lanto maza suna can karatu ba kuma ta ta6a daga kai akan hakan ba, kosu ba 'ya'ya bane sai naki? Dama zata iya fad'i data gaya masa lanto tana da yaran dasuke taimaka mata suke maye mata gurbim sauran, amman itabata da kowa sai alu, shine abin da take kallo taji dad'i a rayuwarta, shine ya tabbatar mata da haihuwar rayayyan d'a ba, ya maida mata shi gaskiya, amman ba zata iya sanar[8/1 01:19] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (9) da shi hakan ba, don haka cikin rawar murya tace "ayi hak'uri malam. Lamto ta ta6e baki yayin da shi kuma yaji tausayin ta ya fara shiga ransa, sumaye ta kalli inda Alu yake tana k'ok'arin danne fishin ta cikin tsawa ta fara yi masa magana muryar ta narawa. "Maisaugo bakaji abin da Baffan ka ke fad'i bane, maza d'ebo kayanka, karatu shine abu mai muhimmanci a rayuwarka fiye da komai. Alu bai motsa daga inda yake ba sai hawaye da suka fara wanke idon sa, k'aramin yaro ne amman kwakwalwar sa tana aiki irin ma yaron da ya kai shekaru shabiyar, mal. Beld'o ya cika da tsananin mamaki, domin Alu bai ta6a yi masa musu ba balle har yace ga abin da yake so ayi yace a'a ba sai yau, hakan ya sanyaya jikin sa ya kasa ce masa komai. Lanto ta kula da yanayin da malam din ya shiga kishi ya bayyana akan fuskarta har ta kasa boyewa tace malam ko shi d'in barin sa zaka yi kasancewar dan mai ne? Mal. Beld'o ya dawo hayyacin sa cikin gaggawa yace shi d'in banza ai dolensa ya tafi neman ilimi, yan'uwansa duk suna ban,
[8/1 01:20] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Daga wanda yayi shekaru biyar sai wanda yayi shekaru bakwai, bazan fasa ko sauya ra'ayina akan sa ba sam. Ya maida dubansa ga sumaye da kanta ke durkushe cikin zafin rai yana cigaba da fad'in maza tashi had'o min tsummokar sa sumaye. Babu musu ko jayayya sumaye ta mik'e cikin tsananin sauri kamar babu komai jikinta, domin babu abin da take gudu bayan sa6a umarnin mijinta, tayi hanyar daki cikin gaggawa, mla. Beld'o yabi ta da kallo can k'asan ransa tausayin ta da sautin kukam Alu na so yin tasiri akansa, amman bai da halin janye k'udirinsa har abada, don haka ya kasa furta komai. Lanto ta dokawa Alu tsawa kai tafi can rufe mana baki, zaman gida bana maza bane sai mata, ka fita kaga duniya, duniya ta ganga yaro." Alu ya kuma fashewa da kuka cikin damuwa yana kad'a kai "ban son tafiya inna! Ban sn barin innata cikin halin da take! Babu wanda zai d'ebo mata ruwa a rafi, babu wanda zai mata itace inna. Lanto ta kara tafa hannu tana sallalami kaji fa malam, ai daga jin kalaman yaron nan d'ora shi akayi akan su,[8/1 01:20] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (10) duk yawan yaran gidan na a rasa wanda zai yi dukkan abin da yake fad'a sai shi? Wato hakan na nuna kai ne haife bata k'aunar kowa ya taimaka mata idan ba kai ba ko? Ta dinga surutai da soki burutsunta kala-kala, sai dai abin daya bata mamaki, dukkan fad'a da hargowar maigidan nasu yayi sanyi lakwas yau kamar bai son tafiyar alu din, hakan ke k'ara kona mata rai, dukkan abin da ya shafi lamarin sumaye sai ya nuna banbanci. Sumaye data shge cikin d'akin tayi tsaye cak domin k'afar ta rik'e ta kasa ko da motsawa, jikinta yana rawa hawaye ya cika idanuwanta, daga inda take tana jiyo shshekar kukan alu da kuma hargowar lanto da surutun ta. "Haba malam sai kace ba kai ba, ace kana bayar da umarni a gidan ka mace na k'ok'arin takewa, minti nawa ta kwashe cikin d'in babu labarin ta, da nice da tini ka fara kurarin na raina ka. Mal. Beld'o ya kalli lanto a fusace cikin taraddadin abin da yake shirin aikatawa, a k'asan ransa ya san abinda ta fad'i gaskiya ne amman yana k'ok'arin nuna mata ba haka bane ba,
[8/1 01:21] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: Cikin zafin rai yace haba lanto yaya kike abukamar na marasa tinani ne, nafi kowa sanin halin sumaye bata musu belle ja da abinda na fad'i, kina kallo ina bata umarni ta shige aikata abin na sanya ta, lokacin data d'auka bata fito ba bazai zama abinda za'a yanke mata hukunci da shi ba, matar nan juna biyu gareta dole sai tabi a sannu. Tamkar ya watsawa lanto ruwan zafi cikin ranta, har taji dama ta sani bata ambaci kalmar ba, domin babu abin da ta tsana bayan ganin wani abu ko misk'ala zarratin da zai nuna kulawa ko so da kaunar sumaye ga mijinta, ta kama haki cikin baci rai ta kasa furta komai. A 6angaren sumaye maganar mijinta ta bata kwarin gwiwar aiwatar da abin da ya sanya ta duk da idaniyar ta na zubda hawaye, zuciyar ta na k'una na rabuwa da tilon d'an ta, amman bata yadda shaid'an da makircin abokiyar zamanta yayi tasiri akanta ba, cikin sauri ta janyo wani tsohon buhu da take ajiye ganyen kukar miya ta zazzage ganyen kukar a k'asa ta fara tsunta kayan alu tama watsasu cikin buho, ta d'ebi abinda
[10/25, 1:41 PM] H InnaπŸ§•πŸΌ: [8/1 01:21] Zeinab Andiya Fox πŸ€—: (11)Ta d'ib kana tayi waje da azama, tana fitowa tayi ido hudu da Alu wanda ya fara ja da baya ganin ta fito rike da kayan sa cikin buhu, ya k'ara

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

5 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment