Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana magana yana tafuya ya fice, ta bishi da jallon takaici domin bata da abin da zsta iya yi, idan ya sanya kansa yin abu babu wanda ya isa ya hana shi, wannan hali na mijinta yakan k'ona mata rai kwarai da gaske, tayi tsaki ta zauna a bakin gado ta manta da abinda zata yi niyyar yi wato sallah.

Acan Asibiti Alh. Musa ya isa cikin motarsa Marsandi 190 ya sunkuci Alu ya shiga da shi cikin asibitin, kasancewar Asibitin na kud'i ne shi ya sanya yana shiga ma'aikatan lafiyar suka yi kansa da tambaya, cikin sauri ya tambayesu Likita suka sanar da shi yana cikin domin yayi cikin dare yanzu kuma yake shirin fita, d'aya daga cikin ma'aikatan ya amshi Alu daga hannunsa da gaggawa ya amsheshi kai tsaye ya nufi d'akin da ake duba marasa lafiya dashi wanda aka rubuta counselting room a samansa yashige da shi,[8/1 01:36] Zeinab Andiya Fox 馃: (31)
Alh. Musa ya bishi cikin gaggawa suka fad'a d'akin.
Likita yana zaune akan kujere yana rubutu akan wasu fayal ma'aikcin lafiyar da Alh. Musa suka shigo, likita ya mik'e cikin mamaki kafin su kai gayi masa bayani yayi kan Alu wanda aka kwantar da shi akan gadon da ake duba marasa lafiya, likitan ya fara dubdduba Alu cikin gwaninta da kwarewa, nan da nan yayi rubatu akan wata takadda ya baiwa ma'aikacin lafiyar gami da ba shi umurnin ya amso masa wad'an nan magungunan cikin gaggawa a d'alin siyar da magani, sannan yayi umarni da a d'auki Alu a kai shi d'akin kwanciya.
Cikin awanni da basu gaza uku ba aka samo rayuwar Alu wanda yunwa da wahala suka kusa halakawa, sai a sannan Alh. Musa yaji sanyi sanyi cikin ransa da ya tabbatar Alu bai mutu ba, sai dai irin cutar da akace tana damun yaran ta tsoratashi, wato nimoniya da ulcer abin da yake sak'awa da kwancewa a ransa shine wannan d'an waye daga ina yaron ya fito, su waye iyayansa, mai ya sanya ya sami wad'an nan ciwukan? Wad'annan sune tambayoyin da suka cika ransa amman bubu amsar su, sai da ya tabbatar ko da yabar asibitin babu matsala sannan ya fara k'ok'arin tafiya, amman yabar kula da Alu a hannun wata nurse kafin ya dawo.

Haj. Bilki ta cika tayi faf kamar zats fashe tana kallon yarinyar ta Hanan yar shekru Biyar dake wasa a tsakar gida cikin jin dad'in yau bataje makaranta ba, Alh. Musa ya shigo da sallama fuskarsa d'suke da farin ciki sa6anin fitar shi da asubar.
[8/1 01:37] Zeinab Andiya Fox 馃: Haj. Bilki ta mik'e cikin masifa tana kallon Alh. Musa cikin tsiwa tamkar zs ta kai masa duka.
"Yanzu Alhaji ka kyauta kenan? Ka tafi ka barmu akan wani d'a baka san waye shii ba? Kalli yarinyar nan bata sami tafiya makaranta ba domin babu mai kai ta, koda yake daman ai ka fad'a kafin ka tafi ba zataje makaranta ba, bai kamata na dami kaina ba, duk abin da sakacin kaita majaranta ya haifar, da kan ka ya kamata kayi kuka bani ba, yarinyar nan dai ita kad'i Allah ya baka, bai kamata ka dinga wasa dalamarin ta ba."
Alh. Musa yayi murmushi yana kallon Haj. Bilkisu yace Bilkisu kenan tsiya ta dake rashin tinani, abin da ya kamata ki farayi dana shigo gidan nan tambayar halin da yaron nan ke ciki ba ki kama fad'a ba."
Ta kalleshi takaici ya k'ara bayyana akan fuskarta "Tambayar halin da yake ciki, menene had'ina da shj?
Alh. Musa ya kula bazata fahimci abin da yake nufin ta fahimta ba sai ya kalli Hanan dake wasa ya fara yi mata Magana.
"Yarinya ta baki ganni bane? Hanan ta d'aga kai ta kalleshi tana murmushi.
" Dady ina yiwa Baby na kitso ne, ka bari nagama sai nazo muyi hira, yau ba zanje School ba ko?
Ya d'aga kai yana murmushi sannan ya matsa kusa da ita ya durk'usa yana fad'in "Shike nan tun da ke bazaki zoba ni gani nazo, bari nabaki wani labari mai dad'i." Yayi d'an shuru yana kallonta, Haj. Bilkisu tana kallon sa cikie da takaici da jiram jin abin da zsi fad'a.
"Yau naga wani yaro mai kama da yayan ki Abdul danake baki labari kullum...
Haj. Bilki ta k'ara kumbura tabbas data san abinda zai fad'a kenan da babu abin da zai sanya ta tsayiwa taji, taja dogon tsaki wanda yaja dai-dai lokacin datake k'ok'arin barin gurin cikin fishi ta shige d'aki.
Muryar Hanan ta dawo dashi cikin hayyacinsa ya maida dubansa gurin ta yana sauraran ta.[8/1 01:37] Zeinab Andiya Fox 馃: (32)
"Daddy ko dai shine ya dawo gidan mu? Yayi murmushi "Ba shi bane ba, idan mutum ya mutu bai k'ara dawowa har abada Hanan, yayyanki sun mutu baza su k'ara dawowa ba har abada, sai da a haifi masu kama dasu".

Haj. Bilkisu tana d'aki tana jin dukkan abin da ke faruwa, a rayuwarta babu abin da ta tsana illa taji mijin ta yana maganar tsohuwar matarsa da 'ya'yansa wanda sun bar duniyar tsahon shekaru, amman ya kasa mantawa dasu. Duk da tana ganin ta maye masa gurbin su ita da d'iyar ta amman hakan ya faskara."

CIWO BA MUTUWA BA
Kwana biyu Alu ya dawo cikin hayyacinsa har yana fahimtar komai, sai dai abin da yake baiwa Alh. Musa mamaki bai wuce ganin yanda yaron ke cin abinci kamar maye ba, dukkan abinda aka bashi hannu baka hannu kwarya yake cin sa nan da nan zai kammala, wannan ya sanya Alh. Musa ya matsa ya kammala warwarewa yaji labarin sa, yayi k'ok'arin bashi kwanaki biyu yanda zai kammala dawowa cikin hayyacin gabad'aya.
Tun ranar da aka kwantar da Alu a asibiti ya nemi Haj. Bilkisu taje duba shi amman saj ta buga k'asa tace Allah ya sauwak'e haka kawai bata san yaro ba zataje ta duba shi, shi dai daya d'orawa kansa sai yaje yayj tayi, har cikin ransa yaji ciwon abin domin saida fuskarsa ta nuna, hakan ya kuma k'ular da ita, sai take jin jamar da gaske d'sn nasa da ya jima da mutuwar ne ya dawo, amman dai tasan mutuwa d'aya ce, idan kuma aka yita ba'a dawowa har abada.
Saboda wannan dalilin ya sanya tun daga ranar bai k'ara neman ta dataje ba, da kan shi yake zuwa ya duba shi yayi masa siyayya mai yawa.
Yau kam da Hanan ya tafi yarinyar taci kwalliyar ta, hajiya Bilki bata so hakan ba amman kuma babu yanda ta iya, domin tasan bata isa ta hanashi ba, don mutum ne da ba'a sanya shi ba'a hanashi.
[8/1 01:37] Zeinab Andiya Fox 馃: Alu yana zaune akan gadon yana shan lemo da ayaba wanda Nurse d'in dake kula dashi ta yanka masa, domin dukkan Nusrse d'in suna bashi kular daya kamata saboda irin k'udin da Alh. Musa yake basu, Alh. Musa da Hanan suka shigo da Ssllama, Alu ya fad'ad'a fara'arsa da ganin Alhaji, domin ya san shine ya ceto rayuwarsa kamar yanda Nurse d'in ta bashi labari, cikin ladabi ya fara Magana tun kafin su k'arasa.
"Ina wuni Baffa? Sunan daya kira Alh. Dashi ya sanya zuciyar Alh. Musa jin dad'i Hanan ta kalli mahaifin nata cikin mamaki sannan ta kalli Alu dake zaune a tsakiyar gadon tana fad'in "Kai b sunan shi haka ba Daddy zaka ce." Alh. Musa yayi dariya yana kallon Hanan yace "Hanan da Daddy da Baffa duk d'aya ne, d'aya da turanci ne d'ayan kuma da Fulatanci ne."
Hanan ta daga kai alamar gamsuwa, Alh. Musa ya k'arada ya zauna a gefen gadon, ya d'aga Hanan ya zaunar da ita kusa da shi yana kallon Alu wanda ya tsaya da cin abin da yake yi ya sunkuyar da kansa k'asa.
Alh. Ya k'ura masa Ido kafin ya fara Magana yana son karantar komai na yaron, domin kullum zuciyarsa k'ara sanar dashi take yi wannan d'an sane Abdul.
"Yaya sunan ka? Ya tambayi Alu kai tsaye. Alu sunana." Yaron ya bashi amsa shima kai tsaye.

Alh. Musa ya girgiza kai cikin gamsuwa yana fadin "Aliyu Haidar kenan zakin Allah, anan garin kuke ne?
Alu yayi shuru domin bai fahimci abin da Alh. Musan yake son fad'i ba, kamar Alh. Musa ya fahimci haka ya sauya tambayar da wata.
"Ina ne gidan ku , ina baban ka yake aiki?
Alu yayi ajiyar zuciya domin ya fahimci dalilin tambayar, nan da nan idon sa ya cika da kwalla, ya kauda kai gefe abin da ya d'an taba zuciyar Alh. Musa, amman bai ce masa komai ba domin kada ya katse shi daga jin abin da yake shirin fad'a.

[8/1 01:37] Zeinab Andiya Fox 馃: (33)

"Gidan mu ba anan yake ba, yana cin garin mu, Baffana kuma noma yake yi, an kawo ni nan karatun almajiranci ne...
Hanan tayi tsalle gami da dira daga gurin cikin sauri, abin da yaja hankalin su duka suka dubeta da mamaki, cikin fishi tana yiwa Alu kallon banza ta fara Magana.
"Daddy daman almajurine muka zauna a kusa dashi, bayan akwai datti da kazanta a jikin shi." Alu yabita dakallo yana jin wani abu a cikin ransa, shi kuwa Alh. Musa kunya da takaici ne suka cika shi, duk da Alu yaro ne amman yasan zai fahimci abinda Hanan ke nufi akan sa, wato kyama da wulakanci, sai yayi k'ok'arin kwantar da kansa yana fad'in.
"Waye ya gaya miki, duba Aliyu babu datti a jikin shi kwata-kwata, dawo kizauna kinji baby na.
Hanan ta nok'e kafad'a tana tsaye a inda take taci gaba da Magana "A'a Daddy ni bazan zo kusa dashi ya shafamin datti ba, ni zan fita waje naje gurin mota, bana son almajiri kwata-kwata, momy tace kazamai ne basu wanka kuma suna d'aukar mana kayan mu."
Mamaki da takaici ya k'ara cika Alh. Musa har ya kasa Magana, kafin ya kai ga k'ok'arin yin wani abu Hanan ta bud'e k'ofa ta fita d gaggaw, ya mik'e a fusace ya fara kwala mata kira.
"Hanan! Hanan! Bata tsaya ta saurareshi ba, ya juya ga Alu wanda yake zaune zuru da damuwa ya k'urawa yaron ido, suna had'a ido jikin Alu ya kama rawa ya fara Magana cikin rawar jiki.
"Wallahi ni bana sata Baffa, ban ta6a daukar abin kowa ba, Rabe ne ke d'aukar abin mutane, shine idan yaje gida yaga babu kowa yake d'auko abin su, amman ni Inna ta gaya min sata babu kyau, allah zai k'ona mutum ranar lahira a wuta." Tausayin sa ya shigi Alh. Musa ganin yanda duk ya gigice ya k'ara zama a kusa dashi ya saki fuskarsa cikin alamun lallashi yana magana.
Kwantar da hankalin ka Aliyu na yadda baka sata kai, kowa daman da irin halin sa, idan ka warke zan mai dakai gurin Malamin ku....
[8/1 01:38] Zeinab Andiya Fox 馃: "Don Allah kada ka mai dani can, ka barni a gidan ku na dinga yi maka aiki kana bani abinci, a makaranta bana samun abinci." Tausayin yaron ya k'ara shigar Alhaji Musa wato shi abinci ne kawai matsalar rayuwarsa, bayan wannan bai damu da komai ba, bai san dalilin da tasanya iyayan yara ke raba 'ya'yan su dasu ba, shi iyaye basu san duniya ta sauya kowa kansa ya sani ba, tabbas a zsmanin da ya gabata anyj karatun Allo yanda ya kamata, amman yanzu kam komai ya sauya, mutanan ma sun saya basu taimakon almajiran yanda ya kamata, hakan ya sanya zuciyoyin almajiran kekashewa tunda sun fuskanci ba'a kaunar su.
Ya samu ya lallaba Alu akan zai dinga bashi abinci ko da ya koma makaranta kullum, sannan ya nuffi gurin Hanan bayan ya bashi abincin da ya taho masa dashi, yaron ya amsa cikin farin ciki yana godiya, wannan godiyar itace ke k'ara sanyaya masa ransa yake k'ara sakankancewa da lamarin Alu d'in, yake ganinsa kamar d'an sa Abdul.
A can jikin motar sa ya tadda Hanan tacika ta batse kamar zata fasa kuka, da ace bata yi masa laifin komai ba da rarrashin ta zai fara yi sabuda yana mutuk'ar k'aunar ta, amman kasancewar tayi masa laifi yanzu ya sanya bai kula taba ya bud'e mota kawai ya shiga, sannan ya bud'e mata 6angaren mai zaman banza ta shiga tana kumbura.
"Allah kuwa Daddy kar ka k'ara zuwa gurinsa, ko kanaso ya shafa maka datti ne?
Alh. Musa ya kalleta, a ransa abin da yake sak'awa shine ya kwad'a mata mari, amman a fili yaga rashin dacewar hakan, domin ita bata san komai ba, abin da aka d'orata akai shine abin da ta tashi da shi, yana d'aya daga cikin sbin da ya sanya bai son halin matar sa, sannan yake kasa tina tsohuwar matarsa da ta rasu domin Bilkisu macace mai izgili da wulk'anta dan adam, wannan halin nata kuma take k'ok'arin koyawa yarinyarsa, duk da yana iyakacin k'ok'arin ganin hakan bai yuwa ba, amman abin ya faskara, domin ta fishi zama da yarinyar, yayk k'ok'arin kwantar da muryarsa domin yayi mata bayani.
"Kina jina ko Hanan, dukkan mutumin da ki kagani akwai baiwar da Allah ya bashi, ba'a son ka dinga wulak'anta mutane, shima daya zamto almajirin ba dan yaso bane ba, kuma Baban sa ba don baya son shi ya kawo shi nan ba, ya kawo shine domin ya sami ilimi mai nagarta...[8/1 01:38] Zeinab Andiya Fox 馃: (34)
"Amman mai ya sanya suke yi mana sata Daddy, idan maigadi ya barsu suka shigo su d'auke mana abun mu ko idan muka yi shanya sai su d'auke...
"Hakane amman b lallai ne su suke d'aukar muku ba, shi wannan da kike ganin sa baya sata kwata-kwata, sannan sauran ma basa yin sata, duk wanda kika ga yana sata halinsa ne ko da ba almajiri ba ne zai yi, koba ki ga yaron nan Halliiru na kusa da gidan mu yana yin sata bayan yana da Baba da Mama ba?
Yarinyar tayi kasak'e alamun maganganun da yake fad'a sun fara shiga jikinta, domin yarinya ce mai mutuk'ar wayo, domin wayon ta ya girmi shekarunta, ganin ta fara fahintar abin da yake son nuna mata ya sanya yaci gaba dayi mata bayani cikin hikima da dabara, fatan sa ta fahimci darajar mutum har sai da ya tabbatar ta fahimci abin da yake nufi sannan ya tayar da motar suka wuce giida.
Sanda suka isa gidan Haj. Bilki bata ko kalli inda suke ba taci gaba da sabgar gabanta, babu sannu da zuwa balle yaya kuka dawo, shima bai kula ta ba ya shige d'aki kai tsaye.
Hannan ce ta nufi mahaifiyar ta da gaggawa tana nuna mata abin da babbanta ya siyo mata a hanya, Haj. Bilki ta amshi ledar kayan tana kalla ta fara ta6e baki domin da wuya ta yabi dukkan abinda ba itace ta siya da kanta ba, a rayuwarta bata k'aunar siyayyar mijinta tafi son ya bata ta siya da hannun ta, abin da shi kuma bai yi, domin bai k'aunar shgar ta kasuwa.
Hannan ta katse mata kallon nata ta hanyar kiran sunanta, Haj. Bilki ta daga kai ta kalleta da ssuri jin yanda ta ambaci sunanta tasan akwai labari.
"Momy kinsan waye ne Daddy ya kai Asibiti?
Gabanta Haj. Balki ya fad'i don tana zaton kamar d'iyar tata zata ce mata da gaske Abdul d'in ne ya dawo duniyar amman sai taji Magana sa6anin abinda tayi zato. Yarinyar ta k'ara rage murya tana fad'in.
"Momy wanda Daddy ya kai Asbiti fa almajiri ne."
[8/1 01:38] Zeinab Andiya Fox 馃: Wani rin takaici ya mamaye zuciyar Haj. Bilkisu har yayi naso akan fuskarta, amman ta kasa furta komai sai wani dugon tsaki da taja, yarinyar bata kula da halin da mahaifiyarta ta shiga ba ta fara k'ok'arin amsar jakarta tana fad'in.
"Bani kayan na kaisu d'aki na boye." Ta amshe kayan, ta fara k'ok'arin tafiya, Haj. Bilkisu ta kwala mata kira sanda taga tana k'ok'arin isa ga d'aki.
"Hanan! Yarinyar ta waigo batare data k'ara sa kusa da ita ba. "Kin taba jikin sane?
Ta wurga mata tambaya, Hanan ta girgiza kai alamar a'a gami da k'arin bayani.
"Ban taba shi ba Momy da Daddy ma ya fad'a ban zauna a cikin d'akin ba na gudu gurin mota."
Haj. Bilki ta kad'a kai cikin jin dad'i gami da fad'in "Yauwa haka nake son ji yarinya ta." Hanan tayi murmushi cikin jin dad'i tayi hanyar d'akin cikin sauri.

K'AK'A K'ARA K'AK'A

Wata rigima data so fin karfin Alh. Musa ta kunnu kai cikin rayuwarsa, sai dai kasancewar sa jajirtacce akan komai ya sanya yayi yak'i da lamarin har ya shawo kansa.
Zaman da Alu yayi cikin Asibitin ya sanya ya fahimci halayyar yaron da abubuwa dake yawo da rayuwarsa da kuma halayyar yaron, sai yaji ya kwad'aitu da zama tare da yaron, tun kafin a ssllami Alu ya fara k'ok'arin ganin hakan ta kasance a cikin ransa, don haka ranar da aka sallme shi ya d'auki Alu a motarsa ya nufi makarantar su dashi.
Tunda abokan karatunsa suka hangoshi dsga cikin motar suka fara gudu suna sanar da malamin su wanda yake cikin tsananin tashin hankali, domin an wayi gari an nemi Alu an rasa, kwana biyar ana abu d'aya, shi malamin bai fahimci yaron baya nan ba saboda yawan almajiran sai da aka kwana aka hantse Rabe ya kula da rashin ganin Alu ya fara magantuwa har Magana ta isa kunnen malamin nasu aka fara bincikar inda Alu ya shiga amman har tsahon kwanaki uku babu wanda yaji ko labarin inda yake, wannan ya k'ara d'aga hankalin malamin nasu domin bai san me zai sanar da wanda ya kawo masa Alu ba,
[10/25, 8:24 PM] H Inna馃馃徏: [8/1 01:39] Zeinab Andiya Fox : (35)
Kuma shi hakan bata taba faruwa akansa ba, dukkan wani abu daya kamata yayi amman shuru babu labarin yaron, tashin hankalin daya shiga kowa ya sani a makaranta, shi ya sanya yaran suna hango Alu cikin motar suka garzaya da gudu suka fara sanarwa da malamin nasa
Malam Sadau ya mik'e cike da tsananin mamakin jin wai anga Alu cikin motar wani mutum, abin da zuciyar shi ta fara sak'a masa shine mutumin d'an yankan kai ne kawai, don haka yayi tsayuwar jiran zuwan mutumin.
Alu. Musa yayi parking ya fito daga cikin motar sa bayan ya bud'ewa Alu 6angaren mai zaman banza, mamaki da zargi suka k'ara cika zuciyar malam Sadau ganin Alu cikin sabbin kaya ya ci kwalliya kamar ba Alu din daya sani ba, kafin su iso ya nufesu da hanzari cikin 6acin rai.
Bawan Allah menene had'in ka da wannan yaron? Abinda ya fara tambaya kenan, ya manta da sallama ko wata gaisuwa ma
Alh. Musa yayi murmushi gami da mik'a masa hannu yana fad'in. "Haba bawan Allah ya kamanta mu fara gaisuwa kafin ka fara tambayar komai." Ya mik'a masa hannu "Salamu'alaikum!
Kunya ta kama Malam Saudau yaba shi hannu suka gaisa jikinsa ya fara yin sanyi, Alu yana tsaye yana kallon su cikin fargaba domin yanayin dayaga malamin su ya shiga zai iya zane shi idan Alhajin ya tafi, don haka duk ya rud'e.
Kafin Mal. Sadau ya fara yin Magana Alu
Musa ya riga shi.
"Da farko zan fara baka hak'uri akan rashin zuwa na sanar da kai halin da yaron nan yake ciki, abu na farko da ya jawo hakan shine yaron bai farka da wuri ba har sai da yayi kwanaki biyar, sauran kwanaki uku kuma wasu ayyuka ne suka sha kaina."
Mal. Sadau yana kallon Alhaji da rashin fahimtar dukkan bayanan da yake masa, ya kasa 6oye mamakin nasa sai da ya furta.
"Alhaji nifa ban fahimci komai daga abinda kake fad'a ba, nadai san yaron nan tsahon kwanaki biyar kenan muna nemansa, amman bamu san inda yake ba, har mun fara zargin sace shi aka yi sai kuma gaka tare dashi, ya kamata ka mini bayanin abin da ya faru."
[8/1 01:39] Zeinab Andiya Fox : Alh. Musa ya gyara tsayuwa "Haka ne, ni kaina bansan abin da ya faru ga wannan yaron ba, na dai san na wayi gari na ganshi kwance a k'ofar gida na kamar matacce, na d'aukeshi na kai shi Asibiti, bayan tsahon lokaci da binkice da akayi aka samo lafiyarsa da rayuwarsa, sai bayan ya farfad'o yake mini bayanin wani mutum ne yaje gurin sa ya bashi abinci sai mutumin yace sai ya cere wandon sa shi kuma ya gudo shine ya kama yin amai a hanya."
Hankalin Mal. Sadau yayi mutuk'ar tashi ya kama salati gami da kallon Alu dake raba idanu cikin tsoro.
"Kai Alu garin yaya hakan ta kasance, a kuma ina mutumin yake?
Cikin rawar baki Alu ya fara Magana "Nima ban sani ba, ban san a ina bane ba, naje gurinsa bara ne kawai yace mini haka.?
Malam yaci gaba da sallalami cikin tsananin tashin hankali "Kaji rashin imani irin na mutanan wannan zamanin Alhaji, yaro kamar wannan ka umarceshi da yin wannan aikin, wannan masifa ce babba wallahi, shi ya sanya d'aliban mu na yanzu sai mun yi da gaske muke samun nagari, domin muna tarbiyar su wasu na 6atawa, kai dai Alhaji nagode Allah ya saka maka da alkhari, ko zamu k'arasa can kan tabarma mu zauna ne." Ya 6uk'ata.
Alh. Musa ya kad'a kai yana fad'in "Ai nan d'inma duk d'aya ne, ina sauri ma zan tafi, amman daga yau Alh ba zai k'ara zuwa baraba, na sanar dashi a gidana na zai dinga amsar dukkan abin da yake 6uk'ata, idan da hali ma ina son ka barshi a hannuna ni zan yi masa dukkan abin da ya kamata na d'a da uba."
Cikkn sauri malam Sadau ya kada kai yana fad'in Ina hakan ba zai kasance ba, yaron nan amana ce a gurinna, idan na aikata hakan ban kyau taba, na amince daai da ya dinga zuwa yana amsar abinci, amman maganar zama gurin ka bata taso ba, musamman da yake ban san kaba...
"Ni na sanshi Malam, gidan sa yana can wajan sabuwar unguwa, shine me wannan gidan mai katuwar k'ofar nan" Daya daga cikin almajiran ya fad'i, Malam ya kalleshi gami da kai masa bugu a fusace yana fad'in.
"Uban waye ya tambaye ka, fad'i ba'a tambaya ba? Yaron ya zabura ya fice a guje,
1 路 Like 路 React 路 Reply 路 Report 路 14 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:39] Zeinab Andiya Fox : (34)
Amman duk da haka sai da malam ya sameshi a bayan shi.
Duk yanda Alh. Musa yaso lank'asa malam Sadau abin ya faskara haka ya hak'ura ya kyaleshi, amman Allah ya sani Alu ya shiga ransa kwarai da gaske, yana jin kamar ya kwace shi, amman dai ya hak'ara ya tafi, da yarjejenir zai dinga zuwa gidan sa yana amsar abincin.
Bayan tafiyar Alh. Musa Malam ya sanya Alu a gaba da tambayar shi abubuwan da suka faru, Alu yak'i yadda ya ambaci sunan Bala a ciki domin yana tsoroan irin abin da zai biyo baya, har dai malam ya gaji ya kyaleshi ya shiga cikin d'aliban ya zauna suka fara tambayar sa abubuwan daya faru, Bala baya gurin shi da manyan gardana kasancewar ranar babu makaranta sun tafi yawon dako da sauran sana'oi.
Acan gidan Alhaji Musa kuwa rigima ce taca6e tsakanin sa da Haj. Bilkisu domin tace bata ga dalilin da zai sanya kawai ace kullum safe dare da rana dai ta baiwa wani almajirin banza abinci ba a cewarta, yayin da shi kuma yace gidan sane dole ayi dukkan abin da yake so a gidan sa idan kuma ba haka ba duk abinda ya aikata kada tayi kuka da kowa tayi kuka da kanta, domin akan taimakon rayuwar Aliyu zai iya yin komai, wannan maganar ta tsaya a zuciyar Haj. Bilkisu musamman ganin yanda mijin nata ya hak'ik'ance akan lamarin yaron nan, tun kafin taga yaron taji ta tsane shi a rayuwarta bata k'aunar ganinsa, sai dai irin barazanar da mijin ta yayi mata akan sa ya sanya ta yadda bata da zabi bayan aikata abin da mijin nata yace akan yaron, domin ta san ko baice mata komai ba tana tsoron faruwar wani abu, musamman a wannan lokacin da dangin mijinta saka sanyata a gaba akan neman mijin nata ya k'ara aure yak'i yadda, domin shi ba mutum ne mai ra'ayin k'ara aure ba, tun bayan mutuwar matar shi ta farko bai kuma sha'awar k'ara aure ba, ko ita kanta Haj. Bilki rabo da kuma girman mahaifinta wanda ya kasance sun taba aiki a ofishi d'aya ya zama a k'ark'ashin sa a matsayin ma'aikaci lokacin mahaifin na yana.matsayin darakta kafin ya kai ga yin ritaya, ya aure tane ba wai don

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

5 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment