Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaci gaba da magana. "Tabbas kana cikin damuwa, domin duk wanda akace bai san inda ahalin sa suke ba yana cikin matsala, amman kai na kula damuwar ka kad'an ce kasancewar kana da arzik'i, wllh wani ba zai ta6a yadda kai d'in wai amajiri bane a baya, domin yanayin ka da fatarka tafi kama data 'ya'yan manyan masu kud'i, don haka kaje ka shimfid'a rayuwar ka, a hankali danginka zasu bayyana kansu gare ka, kud'i sune 'yan'uwa a yanzu. Aliyu ya daga kai ya kalleshi, ba zai fahimci yanda yake jiba domin yana cikin iyalinsa, mutumin da ya kasance cikin irin halin da yake cikine kad'ai zai iya gane abin da yake ji, haka nan ya tshi jiki sanyi kalau
[8/1 01:47] Zeinab Andiya Fox : Ya baiwa malam kud'i yayi ta godiya, suka yi sallama ya shiga motar sa ya dawo gida. Cikin kwanakin abin yayi ta damumunsa, sai dai yawan addu'a ya sanya abin ya lafa a ransa, don haka sanda suka koma makaranta ya fuskanci karatunsa gada-gadan. SHEKARA KWANA. Ga wanda yake cikin k'oshin lafiya da wadata ba zai farga da tafiyar shekaru ba sai ya wayi gari ya ganshi cikin kabari ko tsufa ya baibai ye shi, hakan ke faruwa ga jama'a, domin idan aka ce shekaru hud'u sun ja daga tafiyar hannan abin zai baiwa mutum mamaki, tun da hannan ta tafi bata ta6a dawowa gida ba sai dai iyayan ta su kai mata ziyara, kasancewar ta yarinya mai tsananin hazak'a da k'ok'ari ya sanya bayan ta had'a digirin ta tad'ora da masters d'in ta abin daya sanya mahaifin ta cikin farin ciki, sannan hannan bata karance yarinya mai kule-kulen samari ba, saurayin ta guda d'aya ne shine d'an tsohon minista mansur assada gwarzo wanda suke matuk'ar son juna, sai dai shekara biyu kawai sukayi tare kasancewar shi ya riga ta shiga makarantar suka
1 · Like · React · Reply · Report · 15 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:47] Zeinab Andiya Fox : (45) rabu, amman basu rabu ta waya da kafafan sadarwa ma yanar gizu ba, kullum suna manne da juna, don haka ta k'agu ta kammala karatun ta dawo suyi auran su kamar yanda suka tsarawa kansu. Gidan da take zaune gida ne irin tsarin turawa domin Ammabasa Isa Babura da d'iyar ra d'aya tal Malika wacce take kusan sa'ar Hann dukda ta girme mata a karatu, hakan ya bata damar jin dad'in zaman gidan har ta kammala karatun ta tsab, sanda zata taho Najeriya taji kewar su kamar kar ta taho, musamman Malika, haj. Hasana mahaifiyar alhka ma taji babu dad'i amman ita da malika har kuka sai da suka yi, don ma Ambasada ya musu alk'awarin yana gab da komawa gida shima kar su damu, sannan Malika tana da ikon dazataje taga Hanan duk sanda ta buk'ata, wannan ne ya d'an rage masa radadi da zafin rabuwar. Yanayin da suka yi rayuwa ce mai tsada da daraja, domin duk tak'ama da tink'ahon Hanan data had'u da Malika sai data raina kanta, domin Malika tana ji da komai na rayuwa fiye da ita har da kyau ma, sai dai zaman nasu ya k'arar
[8/1 01:47] Zeinab Andiya Fox : Da ita abubuwa da dama, ta k'ara wayewa da gogewa, hakan ya sanya idan wanda ya san ta baya kafin ta tafi k'asar waje karatu ya ganta yanzu bazai iya gane taba. Randa zata dawo tun safe ake shiriye-shhyen tararta, gidan ya kaceme gabad'aya da girke-girke, masu aiki da kowa na gidan ya san lallai d'iyar da Haj. Bilki ke matuk'ar k'auna zata dawo, shi kansa alh. Musa yayi mata tanadi mai kyau, domin hatta motar da za'aje d'aukar ta daga filin jirgi subuwa be dal daga leda aka bareta, kowa ma gidan murna yake yi, Hamza da Umar suna suna cikin murnar tarar yayar su domin sun yi wayo, kuma lukuta da dama dasu ake zuwa ganin ta. Alh. Musa yaso zuwa ya d'auko Hanan kamar yadda ta buk'ata, sai dai wani taro da ya taso masa bagatatan da gwabma kasancewar shine shugabn 'yan kwangila na jahar ya sanya dole wakilta Aliyu yaje a madadin sa. Allah ya sani Aliyu bairo hakan ba, domin a yanzu ya k'ara hankali ya jenye harkokimsa da dama daga cikin gidan alh. Musa ya kanyi rayuwarsa shi kad'ai da k'annensa masu zuwar masa
2 · Like · React · Reply · Report · 15
[10/25, 9:23 PM] H Inna🧕🏼: 6angarensa, musamman dayake ya sami abin yi, domin sun bud'e shagon saida ice cream da kayan kwalam irin na matasan zamani, guri ne da suka yi masa gini irin na karya shi da wani abbukin sa Sunusi da suke karatu tare, kodayake Sunusi a yanzu ya uwuce abokinsa ya zamto amiminsa, domin sun hadakar sirrinsu ga juna. Sun kwata gurin sum dauki masu aiki, babu abim da basa yi a dangin snaks kamar kek fizza donnt da sauran su, ga ice cream da lemuka kala-kala, hakan ya sanya gurin yayi fice a wannan lokacin, sun sanya gurin suna A&S Join. Kusam kullum a can Aliyu yake wuni idan bashi da makaranta, ko kuma baxan ya tashi dag laca can yake wucewa, alh. Musa yasan da zancen gurin domin har da gudummawar sa biki sanda za'a bud'e, hakan ya sanya bai sanin duk abin dakd faruwa a gidan tun da sai dare yakd shiga, hatta kud'in mai yanzu baya tambayar alhaji komai yana k'ok'arin yiwa kansa. Ya kammala karatunsa cikin sa'a shima kasancewar bai sami yajin aiki kowata matsalaba, ya kuma yi sa'ar aka bar shi a kano bautar
[8/1 01:49] Zeinab Andiya Fox : K'asa, kodayake baffansa ya tsaya tsayin daka gurin ya zauna a kano, domin yana taimakon sa mutuka gaya, yayi matuk'ar sa'a kuma da aka tashi posting din sa sai aka tura shi ma'aikatar filaye da tsare birane wato (ministry of land and sur6ey). Yau da alhaji musa ya buk'aci ya d'auko Hanan daga aiport yana A&S Join, kasancewar jirgirn rana ta hayo, suna hira da kula da abubuwan dake gudana kiran wayar alh. Musa ya shugo ya sanar da shi abinda yake son yi, ya kuma d'oara dace masa sabuwar mota tana nan a cikin gida a ita za'a d'auko Hanan, don haka ya ajiye motarsa a gida, maganar bata yi masa d'ad'i ba har Sususi yafahimci hakan, amman sai ya amsawa alhaji da to kawai. Bayan ya kammala wayar Sunusi ya kalle shi gami da tambayar abin daya faru "Lafiya abokina naga lokaci d'aya yanayin ka yasauya, ba haka ka saba yin waya da alhajin kaba fa. Aliyu yayi doguwar ajiyar zuciya cikin bacin rai yace "yau Hanan yata dawo, shine yace naje na d'aukota a filin jirgi. Sunusi yayi tsaki "to menene abin damuwar kuma?"
1 · Like · React · Reply · Report · 17 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:49] Zeinab Andiya Fox : (47) Aliyu ya yarfe hannuwa cikin damuwa yana fadin "Bafa zaka gane ba, baza ta6a fahimta ba, kai dai saina dawo kawai." Ya fara k'ok'rin tafiya, Sunusi ya ya bishi da kallo har ya shige motarsa ya kad'a kai kawai. A yanda alhaji ya sanar dashi zai yi jiran jirgin nasu ya yak'arso na kusan awa guda, domin baison tazo tayi tajira gwara ita ajira ta, don haka yatafi ya zauna gurin da musu jiran mutane kezama ,amman yad'auko jaridarsa a mota yafara karantawa domin ragewa kansa damuwa , tsahon minti arba'in da takwas jirgin ya k'araaso, fasinja suka fara shigowa, shi ma ya fara raba ido ko zai ga Hanan cikhn dandazon mutane, amman iyakacin hangensa baiga kowa ba, yana tsaye yana ta waige-waige ya hango wata budurwa ta nufo shi tana sanye da riga kot mai zuwa iyakacin gwiwa da dogon wando, amman kayan sun kama jikin ta sosai, ta nade kanta da karamin gyale irin nad'in da larabawa keyi, tana sanye da dogon takalmi wanda yafi kama tsani, da bakin k'atotan glass a idon ta wanda ya kusa cika rabin fuskarta,
[8/1 01:49] Zeinab Andiya Fox : Farace tas irin farin dake d'auke hankalin duk wanda ya d'ora idon sa akanta, ta iso kusa da shi ta tsaya a gabansa, shima tsayawa yayi yana kallonta domin tabbatar da abin da take buk'ata a gurin shi, Hanan ta zare glass d'in dake idon ta a hankali ta kalleshi sama da kasa. "Ko kaine direban da yazo d'aukata? Mamaki ya kama Aliyu daya tabbatar Hanance, ko komai nata ya bace masa mryar ta da idon ta mai kama da zai ba zasu bace masa ba, yayi k'ok'arin kawo dakiya a ransa bisa dimbin firgicin da ya shiga, musamman sunan data kira shi, domin ya tabbatar ta gane shi sarai miskikanci da halin nata ne ya motsa cikin dauriya yace. "Eh nine, inata nemanki tun dazu ban gan kiba. Hanan ta maida glass d'inta tana tsaki "zamu iya tafiya, don bana son a 6ata mini lokaci." ta saki akwatin dake hannunta a gurin, Aliyu ya bita da kallon mamaki, kafin ya d'auki akwatin ya fara k'ok'in tafiya. Ita kanta Hanan cikin ranta tana mamakin ganin yanda Aliyu ya sauya, bayan tayi masa farin sani bazata gane shi ba,
1 · Like · React · Reply · Report · 17 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:49] Zeinab Andiya Fox : (48) tasan daman Aliyu farine dogo sosai, amman k'ibar da yayi wacce ta yauna a jikinsa ta sanya ya sauya daga ainihin Aliyu data san shi, sannan wayewar daya k'ara tafi ta yanda ta barshi, amman ta basar cijin ranta bata nuna masa komai ba kamar yanda shi ya nuna mamakin ganinta. Sun isa gaban motar yana tafe tana biye da shi a baya domin bzata iya sauri irin nasa ba, domin aliyu k'ak'k'arfan namijine dake tafiya kamar irin ta dawakai cijin k'arfim da kuzari. Ya dud'e bayan motar ya sanya akwatin nata, ta iso ta kama bayan motar zata bud'e, abubuwan da suka faru shekarun baya suka fad'o masa, wato dai idan karabu da mutum ko bayan shekaru dubu ne tambaye shi wani abin amman ba halin sa ba. Tana k'ok'arin shiga cikin motar wayar ta tafara k'ara daga cikin jakarta, ta zura hannu cikin jakar ta d'auko tana wani murmushi mai kashe zuciyar mai kallonta, ta kara wayar a kunnenta cikin zazzak'ar muryarta ta fara magana. "Hello man ya akai yine? Wow! Da gaske kake? Da fari dad ne zaizo d'auka ta amman sai suka
[8/1 01:50] Zeinab Andiya Fox : Shiga wani meeting shine ya turo yaron gidan mu yazo ya d'auke ni, wai da gaske kana cikin airport d'in nan, ok gani nan dai...ok na hango ka, naga inda kake zaka ganni jikin wata mota...yauwa...eh nice." ta kashe wayar cikin sauri, aliyu yana tsaye yana kallon ta cikin tsananin mamaki da k'ok'arin ganin abinda ke shirin faruwa, daga can nesa ya hango wani had'ad'd'an saurayi irin wanda kud'i da hutu ya jik'a ya nufo su yana murmushi, ya iso har kusa dasu hanan tana murmushi cikin tsananin farin ciki, ga mamakinsa sai yaga gayen ya rungomo hanan cikin sauri, Hanan tayi k'ok'arin zamewa tana fad'in. "Haba man meye haka ne? Mansur ya harareta a wasance yana fad'in "haba baby kamata yayi ace ki bani wani hot kiss, musamman yanda muka yi missing juna tsohon lokaci, amman ke kullvm jiya iyau. Jikin aliyu gaba d'aya yayi sanyi, idon shi ya jad'a yayi jajar, d'iyar baffan nasa aka runguma a bansa, chkin bainar mutane, tashin farko yaji tsanar mansur ta cika ransa, ya k'ura masa ido kamar ya kai masa duka daga inda
1 · Like · React · Reply · Report · 17 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:50] Zeinab Andiya Fox : (49) yake, amman ya kula suko a jikim su hirar su kawai suke yi, sautin mausur y ya k'ara janyo hankalinsa cikin wata irin murya yake magana da Hanan. "Wai baby baki yi tsammanin zanzo na d'auke ki ba, tun da muka yi waya dake jiya ban runtsa ba, fatana kawai ki iso, hakan ma yau ta kasance kasa zuwa ko ina nayi, ke hatta mom d'ina tasan zaki dawo garin nan yau, da ace dad d'in ki yazo d'aukar ki da kin kwafsa mini wallh. "Ya kamata mu tafi, domin ina buk'atar hutu please." ta k'arasa maganar cikin wata irin murya da shagwaba. Mansur xa bud'e hannuwa irin na 'yan gayu yana fad'in "why not, mu tafi. Sai a lokacin hannan ta juya ga aliyu "zaka iya wucewa da akwatin. Mansur ya kalli Aliyu da sauri sai ya d'an firgita ya fara kame-kame. "Hac hanan ashe tare da brother d'inki kuke baki gaya mini ba. Ya nufi Aliyu da sauri "sannu fa... Hanan ta rik'o rigarsa ciki sauri tana magana "waye ya gaya maka brotherna ne, yaron Gidan mu ne kawai. Mamaki ya kama mansur har yaji dad'i cikin ransa, Aliyu kam daman bai son
[8/1 01:50] Zeinab Andiya Fox : Gaisuwar tasa, don haka data taka masa burki dad'i yaji ma. "kawuce mu tafi don allah. Hanan ta k'ara bashi umarni, ya juya suka fara tafiya, amman yana waigen Aliyu yana kada kai cikin tsananin mamaki. "Amman abin nan akwai ban mamaki, kunyi kama da gayen can sosai Hanan, sannan kamaninsa da yanayin sa kwata-kwata basuyi kama dana yaron gida ba." Hanan ta ta6e baki "kasan dai ban ta6a gaya maka maganar k'arya bako? To ka yadda hakan ne kawai gaskiya. Suka wuce suka bar Aliyu tsaye yana bin su da kallo da tsananin mamakin faruwar abin daya faru, Hanan ce ta zamto haka, cikin ransa kawai yake addu'a, tabbas yau da ace Hanan kanwarsa ce uwa daya uba d'aya da sai ya fasawa Mansur baki akan abin daya aikata akanta, shin wai shi ma waye ne, yaya aka yi yasan Hanan, wacce irin shak'uwa ce a tsakanin su da har hanan zata iya barin umarinin mahaifinta ta isa ga wani wai ya kaita gida. Har suka shiga mota suka tayar yana tsaye yana kallon su, k'arar kiran wayar sane ya dawo da shi hayyacinsa, ya d'auko wayar da sauri
[10/25, 9:25 PM] H Inna🧕🏼: [8/1 01:50] Zeinab Andiya Fox : (50) ya kara a kunnensa, alh. Musa ne ya fara tambayar sa ya sun iso kuwa. Cikin sauri yace eh sun iso, maganar da yayi ta karshe ta sanya shi cikin damuwa, domin cewa yayi "kayi sauri ka kai ta gida ta huta. Kamar yace ai tabi wani, amman sai ya gaza fad'in hakan domin gudin abin da zai iya zuwa yazo, don haka yabe to kawai. Cikin sanyin gwiwa kamar an sassara masa gora ya shiga motar ya fara tafiya, sanda ya isa gida ya tadda gidan cike da murnar zuwan Hanan d'in, motar saurayin ta mansur tana fake a tsakiyar harabar gidan hakan ya tabbatar masa da lallai yaron yana ciki, kamar kada ya shiga cikin gidan, amman kuma dole zai je ya kawai haj. Bilki makullin motar kar azo nema, don haka ya shiga cikin falon bak'i kai tsaye. Abin da ya k'ara daure masa kai bai wuce ganin haj. Bilki zaune akan kujera Hanan a kusa da ita bub ko dankwali akanta, shi kuma mansur yana kujerar dake fuskantar tasu ana ta hira, ya shiga da sallama dakyar suka iya amsa masa, ya mik'a masu makullin motar, Hanan nayi masa kallon
[8/1 01:51] Zeinab Andiya Fox : Tara saura kwata, shi dai burinsa ya juya ya fice daga falon don haka cikin sauri ya fice kai tsaye. Hanan ta bishi da kallon mamakin datake ta 6oyewa tun d'azu cikin ranta, yanzu kam ta k'agu don haka ta fara tambayar mahaifiyar ta. "Momy wai yaushe wannan Aliyun yazama haka, kalleshi fa sai kace wani dan masu arzik'i bashi da babbanci da 'ya'yan gidan ma kwata-kwata. Haj. Bilkisu ta ta6e baki gami da fad'in "bawa kafi d'an masu gida kenan, ai Lamarin yaran nan kullum k'ara girama yake yi har ya wuce iya kacin tsayi na, komai da kika san d'an masugida yana yi haka Aliyu keyi, alhaji ya d'anka masa mota da komai na jin dad'in rayuwa kamar kowa, ya bashi ilimi mai kyau, yanzu haka bautar k'asa yake." Hanan tayi tsaki cikin 6acin rai "wato dad bai sauya ba kenan? Haj. Bilki ta mike "kinga kwantar da hankalin ki bar maganar sa haka kada ta 6ata miki rai, bari na barku na shiga ciki ni. "To momy sai anjima. Mansur ya fad'a yana kallon haj. Bilki wacce ta amsa da to ta shige ciki, kamar jira yake ta tashi ya mike
1 · Like · React ·
[10/25, 9:28 PM] H Inna🧕🏼: ox : (51) kamar jira yake ta tashi ya mike tsidik ya dawo kusa da Hanan kamar zai shige ta ya matseta k'am, Hanan tayi baya da sauri tana fad'in. "Wato baka sauya ba ko man, koka manta nan gidan mu ne, kuma kowa zai iya shi shugowa. Kema baki sauya ba yaya za'a yi nina sauya, ban san yaya keke ba Hanan, kin k'i yadda kiji d'ad'in rayuwar ki, haka muka yi tsahon shekaru biyu cikin damuwa. Bayan mun yadda muna son juna, don allah ki sauya kamar yanda zamani ya sauya. "Hanan ta k'ara matsawa baya "kaga tshi na raka ka katfi, kasan daddy bai san da maganar ka ba, kar yazo ya gammu anan rans ya 6aci, domin shi yana da tsari." munsur ya 6ata rai mutuk'a "au korata ma kike yi kenan ko Hanan? Ta kad'a kai cikin sauri tana fad'in "nina isa na kore ka, haba man d'i naka fahimta mana, ka gane karmu yi haka da kai. Da kyar ta samu ta lalla6ashi ya tashi zai tafin, a gurin motar ma sai da ya kamo hannuta ya rik'e k'am cikin nashi, duk da bata son hakan tana tsoran kar mahaifin ta ya tadda su amman dole ta hak'ura ta kyaleshi
[8/1 01:51] Zeinab Andiya Fox : Domin su rabu lafiya, Aliyu dake zaune acan gefen gidan kamar ance ya kalli gurin da suke ya hango hannun Hanan ciki na Mansur yana murzawa, wani irin takaici da bak'in ciki ya cika ransa, lallai Hanan ta lalace, allah ya sani yayi mata addau'a iyakacin iyawarsa, amman bai isa ya hana allah ikon sa ba. Sun jima a haka sannan Mansur ya juya ya shiga motar sa, sai da Hanan taga ficewar sa ta koma cikin gida cikin sauri, Aliyu yabi ta da kallo har ta k'ule, bai san dalilin da ya sanya yake jin ciwon abin da Mansur ke mataba, koda yake yana jin Hanan kamar 'yar uwarsa uwa d'aya uba d'aya ne, don haka duk abin da zai lalata rayuwar ta dole ya zamto abin da zai k'ona ransa. A cikin gida Hanan d'akin Haj. Bilkisu ta wuce kai tsaye, ta tadda Hajiyan tana kallo, ta shiga babu ko sallama, Haj. Bilki ta waiga da sauri tana fad'in. Yaya dai ya tafi ne? "ya tafi momy. Hanan ta bata amsa, Haj. Bilki tayi murmushi tana nuna mata kusa da ita. "Zo nan zauna Hanan taki bani labarin ina kika samo wannan yaron, gaskiya yayi
1 · Like · React · Reply · Report · 18 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:51] Zeinab Andiya Fox : (52) gasiya yayi d'ari bisa d'ari, shine irin mijin danake miki mafarkin aure cikin rayuwata. Hanan ta zauna kusa da mahaifiyar ta tana dariya da fad'in "momy d'an gidan tsohon minisitan kasa da safayo ne fa alh. Assada gwarzo. Haj. Bilki ta amshe cikin ji dad'i "haba babu mamaki, yaron yayi, kin sami mijin kerewa sa'a, ga kyau ga kud'i ga kuma wayewa, irin shi najima ina miki addu'ar samu, don allah hanan kirike shi da kyau, kar ki bari ya k'ubuce miki." cikin dariya da jin dad'i hanan ke magana "haba momy kin sanni bani da kwashe-kwashe, ban amincewa kula shi ba sai dana tabbatar ya mini. Haj. Bilki ta kad'a kai cikin gamsuwa naji dad'in hakan, bani labarin zaman ki acan hanan, domin kin sauya gabadaya, kamar banki watanni tara da suka wuce, kin k'ara girma da kyau, kamar ba Hanan d'ita ba. Hanan ta fashe da dariya jin dad'i "kai momy, kawai dai jin dad'i ne, kin san rayuwar gidan ambasada data nan gidan ba iri d'aya bace ba, zaka yi komai babu mai sanya maka gdo..." tayi d'an jim kamar ta tina wani abu
[8/1 01:52] Zeinab Andiya Fox : Sannan ta dafa cinyar mahaifiyar tata. Momy baki sanar dani komai akan rayuwar Aliyu ba yanda ya sauya fa ya bani mamaki, shi har yanzu bai shirya bar mana gidan mu ba, nifa nafara zargin gayen nan asiri yayiwa daddy wallah." abin dana fizato ke nan nima, amman duk asirin sa zai tashi a banza, lokaci kawai make bashi, komai yakusa zuwa karshe... Daga bakin k'ofa suka juyo gunjin kuka suka waiga da sauri cikin mamaki, anty Batula ce k'anwar haj. Bilkisu suka mik'e cikin tsananin mamaki suka nufe ta. Cikin rud'ewa haj. Bilki ke magana "batula meya faru? Hanan ma cikin tashin hankali ta fara yi mata magana "meya faru anty, kisanar damu don allah, menene? Batula taci gaba da kuka cikin tashin hankali tana kad'a kai, haj. Bilki ta fara magana cikin damuwar dake k'ara linkuwa. "Ki gaya mini Batula lafiya kodai wani ne ya mutu? Batulu ta girgiza kai cikin kuka tana fad'in "babu wanda ya mutu anty bilki aurena ne dai ya mutu, alhaji buba ya sake ni... Haj. Bilki ta waro ido cikin tsananin faragaba "ya sake ki,
1 · Like · React · Reply · Report · 18 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:52] Zeinab Andiya Fox : (53) shi alhajin ne ya sake ki, ina irin d'inbin son dayake miki batulu? "Ya k'are, bai sona bai ko k'aunar ganina ma, ya tsaneni a yanzu, duk wani abu dana saba yin don neman yaddar sa nayi amman a banza, bai hutaba sai da ya ambaci saki akai na. Haj. Bilki ta dafa kirji gami da kundama zagi "saki! Amman lallai alhaji buba bashi da mutunci, amman saki nawa yayi miki? "saki d'aya ne, sai dai yace bai k'aunar k'ara gani na har abada? Batula ta bata amsa. Na shiga uku, lallai matar nan bata da imani, bayan cika gida da tayi da 'ya'ya sai da tasan yadda ta raba ki da gidan mijinki, babu komai ki bar ta kawai, aman wllh kamar kin koma gidan nan kin gama, yanzu ina yaran suke? "suna gurin sa yace bazai bani yaro kod'a ba wai kada nabata musu tarbiyya."kiji d'an iska shi tarbiyyar ce da shi.? Ta inda ta shiga ba tanan take fitaba, hanan tana tsaye tana sauraran su, tabbas tasan antin ta bata da kirki mace ce mai gadara da izgili amman bai kamata ace mijin ta yayi mata sakin ba musamman da yake tana da yara hud'u
[8/1 01:52] Zeinab Andiya Fox : Da shi, da dai ta kula baza su daina jajanta maganar ba sai tabar musu d'akin domin ta huta. Abin da mahaifinta yayi mata yayi matuk'ar burgeta, domin hajiyar ta gaya mata subuwar motar daya sai mata, kuma tana shiga d'akin ta taga komin ya sauya, an maida mata komai sabo, d'adi ya cika ta, sai take ganin d'akin kamar d'akin ta na can, an k'ara gyara fasalin d'akin da komai , ta dinga zagaya d'akin cikin tsananin jin d'adi da farin ciki dadinta ya gama yi mata komai. Lokacin da alh. Musa ya dawo haj. Bikisu ta zayyane masa k'arya da gaskiya akan lamarin batulu ya amince har shima ya dinga fad'a, musamman daya hanata 'ya'an ta har da k'aramin ya bata bangare guda daga cikin gidan yace tayi zaman ta, kasancewar gidan babban gida ne. TUSHIYA MASOMAR DAWA. Mahafin su haj. bilkisu yana da rafin asiri, kasancewar sa tsohon ma'aikacin gwabmati, sanan yana samun taimako daga surukansa bayan da yayi rataya. zamtowar 'ya'yansa farare kyawawa saboda mahaifiyar su sadakar yalla, ya sanya masu kud'i ke auran yaran nasu.
1 · Like · React · Reply · Report · 18 January 2017
Zeinab Abdoul-karim
[8/1 01:52] Zeinab Andiya Fox : (54) Batulu itace k'arama cikin yaran nasa, don haka lokacin da alh. Buba ya ganta zai aure ta yayi musu barin kud'i saboda kyan ta, domin allah ya hore musu kyau wanda dashine suke amfani gurin samun mazaje musu arziki, lokacin neman auren matar alh. Bub tasha takaici domin ba dan takai zuciyar ta nesa ba da alokacin auran zai k'are,

1 Comments On DA BAN SANSHI BA Book 1
avatar
fatima-1-5-8

5 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment