Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin ka wanda aka haifesa da bak'in fentin talauci. Nuhu ka fita harkata da ta y'ay'ana tun kan in kai ka k'ara kotu a raba tsakanin mu." Wani dogon tsaki Nuratu taja tare da fad'in, "Ni wallahi Lami ban san mai kike yi har yanzu da wannan tsohon ba da baki rabu dashi ba. Ke kan ki da zaki d'au wanka ki fara shafa mayuka masu gyare jiki kina hawa leses masu tsada da atampofi, wallahi da wani mayen mai kud'i zai yi wuff dake kema kije kici arziki ki bar arziki inda yake. Don wallahi ba wani tsufa kika yi ba, kawai wahalar wannan tsohon ne ya mai da ki haka." Ta k'arisa maganar tana hararen mahaifin nata. Shi kuwa wani irin kukan bak'in ciki ya fashe dashi tare da dogara sandar shi ya juya ya koma d'akinsa wanda ba k'aramin abu yake fitowa dashi ba, ko alwala da sallah a ciki yake yi. Yana da bahon da yake alwala a ciki, sannan kuma akwai wani bokitin penti k'arami da yake yin fitsari ko ba haya a ciki wanda Sarah ce ke d'awainiyar fitar dasu tana zubar da abunda yake ciki tare da wankewa sannan ta dawo masa dashi ta ajiye. Da sauri Sarah tabi bayansa ita ma tana kukan tana kuma bashi hak'uri. Lami kuma harara ta bisu dashi tare da fad'in, "Munafukan banza da wofi! Kin ga yarinyar nan, wallahi za'a iya had'a baki da ita a kashe mu. Kuma zan yi maganin ta." Tana gama fad'in haka taji an banko gidan da k'arfi an shigo da gudu tare da afkawa d'akin ta. Da idanu duk suka bishi a tsorace, dai-dai lokacin da wani matashi shima ya fad'o gidan ya tsaya tsakar gida hannunsa rik'e da k'atuwar adda yana huci. Gaba d'aya su Na'ima suka koma bayan Lami a tsorace. Shi ko matashin ya k'ariso har inda suke fuska babu rahama tare da karta addan a k'asa yace, "Na rantse da ubangijin Yunusa da Musa, idan ba'a fiddo min da wayar k'anwata da d'an ki ya kwata yanzu ba, duk sai na sassare ku a cikin gidan nan. Ni dashi kar ta san kar billahil lazi. Dalla malama ware ki amso min waya a hannun kafurin d'an ki ko kuma yanzu lahira tayi bak'o." Ya k'arisa maganar yana zarowa Lami idanu. Jikin Lami da y'ay'anta gaba d'aya babu inda bai rawa saboda kaf cikin gari babu wanda bai san *Naliliyo* ba. D'an daba ne sosai wanda kisan mutum a wajensa kamar take kiyashi ne. Da sauri Lami ta juya zata shiga d'akinta domin karb'o wayar, sauran y'ay'an zasu rufa mata baya ya daka masu wata uwar tsawa tare da fad'in, "Duk wata kafurar da ta motsa a cikin ku sai na kashe a nan waje." Gaba d'aya suka k'ame k'am kamar an dasa bishiya. Mintuna kad'an sai ga Lami ta fito hannunta d'auke da iPhone 7plus a hannunta ta mik'awa *Naliliyo* har da d'an duk'awa. Fizge wayar yayi tare da nuna Lami da hannu sannan yace, "Ki hawa kafurin d'an ki kunne, wallahi ko da wasa na k'ara ganinsa ya gitta ta k'ofar gidan mu, to gawarsa ma sai tayi maki wuyar gani." Yana gama fad'in haka ya juya ya fice daga gidan. Na'ima ta saki dogon tsaki tare da fad'in, "Wannan d'an iskan wata rana sai ya jawo mana abunda zai saka a k'ona mu da ran mu a cikin gidan nan. Kullum fa sai kin bashi kud'i amma duk da haka sai ya fita ya jawo mana magana. To gashi nan dai yau ya d'auko mana maganar *Naliliyo* har yana ikirarin zai kashe shi. Wallahi kiyi masa magana Lami ya fita harkan gidan jarababben d'an DABAN nan. Tom!" Kamun Lami tayi magana Lukman (lucky boy) ya fito a fusace yana mai tsira mata hannu tare da fad'in, "Zan ci uwarki a gidan nan idan kika k'ara saka mun baki a cikin al'amura na. Ke uban wanene bai san cewa ke tantiriyar karuwa bace mai y'ay'a har biyu na shegu, dan ma d'ayan ya fad'i ta hannu hagu (Mutuwa) da yanzu y'ay'an ki uku duk shege. Wallahi kika k'ara saka min baki a cikin al'amura na, sai na maki mugun duka a cikin gidan nan. Y'ar iska taxi no garage!" Kallonsa Lami tayi a fusace tare da fad'in, "Kai! Kai Lukman!! Kayi min shuru a wajen nan. Kar in kuma jin bakin ka. Ba yarka bace ita? To ban so ka k'ara fad'in wannan maganar. Ka shiga d'aki ina zuwa akwai wasu kud'i da na ajiye maka." Juyawa Lucky boy yayi yana wani tafiya a b'ankare tare da fad'in, "Karfa ki dad'e kin san ban son jira." Lami kuma mai da dubanta tayi izuwa wajen Na'ima tare da fad'in, "Kin san dai ba hankali bane ya ishe sa, ki rik'a fita harkan sa." Turo baki Na'ima tayi tare da wucewa fuuuu tana fad'in, "Ai ke Lami sam baki son laifinsa, kullum sai dai ki rik'a d'iban kud'i kina bashi yana zuwa yana shaye-shaye dasu." Lami bata ce komai ba ta wuce d'aki domin bawa Lucky boy dubu biyar d'in da tayi masa alk'awari jiya. Sauran y'an matan ma duk suka shige d'aki. Sai da Sarah taji shuru a tsakar gidan sannan ta fito ta nufi pampo ta d'auro alwala saboda kwala kiran sallar isha'i da taji ana yi a masallacin dake gaban gidan su kad'an. Dawowa d'akin tayi ta taras da duka yayyinta a ciki ko wacce sai cab'a kwalliya take yi saboda lokacin fitar su yayi. Dama haka suke yi, wasu idan sun fitan ma, sai suyi kwana biyu, uku har sati basu dawo ba. Wata rana kuma a ranar suke dawo can cikin dare. Darduma Sarah ta shimfid'a ta tada sallar isha'i, don dama ita kad'ai ce a cikin su take yin sallar, to Lamin ma bayi take yi ba balle ta saka su a hanya. Sai bayan ta idar ta sallah ne ta saka doguwar riga irin mai kama jikin nan, sai ta d'aura k'atuwar suwaita a kai sabida sanyin da take ji. Tana cikin zuge zip d'in suwaitar aka kwad'a sallama a cikin gidan nasu tare da fad'in, "Wai ana sallama da Sarah inji Farouq." Ras gaban Sarah ya yanke ya fad'i, don gani take yi kamar tana fita suka hada idanu zai gane akwai ciki a jikinta. Da sauri ta lek'o tsakar gidan tare da fad'in, "Kace tana zuwa yanzu." Tana gama fad'in haka ta dawo d'akin domin d'aukar hijjab d'in da ta cire yanzu bayan ta idar da sallah. "Kanin ubanta yazo, jikinta sai rawa yake yi domin taje ta gaida shi." Fad'in Nuratu tana hararar ta. K'ala Sarah bata ce ba, sai ma hijjab d'inta da ta fara k'ok'arin sakawa. "Shegiya ko irin jan ajin nan baki iya ba. Daga ya turo jikin ki na rawa zaki fita." Fad'in Marfu'a. Sarah kuwa ko kallo basu ishe ta ba, ficewa ma tayi daga d'akin bayan ta gama sanya hijjab d'inta. A k'ofar gidan ta ganshi sanye da wando jeans da blue T-shirt, kansa sanye da facing cap ya jingina da wani k'arfe dake jikin gidan mak'otan su yana kallon d'aid'aikun mutanan da suke fitowa daga masallacin kasancewar ba'a jima sosai da idar da sallah ba. Juyowa yayi tare da zuba mata idanu har ta k'ariso inda yake tare da fad'in, "Sannu da zuwa. Ina wuni?" Kallonta yake yi for almost 2mins kamun ya bud'e baki yace, "Ina kika je d'azu na ganki kin ruwa ya maki duka?" Saurin d'agowa tayi ta zuba masa idanu, sai kuma ta sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa don gani tayi makar zai ga an rubuta _Ina d'auke da ciki_ a kan goshin ta. "Tambayar ki nake yi kin yi min shuru." Farouq ya sake magana a karo ba biyu. Sai a lokacin Sarah ta bud'e baki tare da fad'in, "Asibiti naje." Kallonta yayi tare da maimaita "Asibiti." K'ara d'agowa tayi ta kallesa a karo na biyu, sai kuma tayi saurin kau da kai tana kallon k'asa tare da wasa da zoben dake hannunta. "Are you sick Sarah?" Girgiza kai tayi tare da fad'in, "Dubiya naje yi. Lokacin da na fito kuma ban samu abun hawa ba saboda hadari. Shine ruwan ya duke ni, amma kuma ba fake. Da ruwan yayi sauk'i ne shine na fito shiyasa ka ganni a jik'e." Ajiyar zuciya Farouq ya sauke tare da fad'in, "Amma baki san hakan da kika yi zai iya jawo maki rashin lafiya ba. Mai yasa ma baki kira ni nazo na d'auko ki na dawo dake gida ba? And ina ta kiran wayar ki bakya d'aga wayar." Ya fad'i hakan yana mai folding hannunsa. Ko kamun Sarah tace wani abu an banko k'ofar gidan su, cikin sauri duka su biyun suka juya suka kalli k'ofar gidan. D'an duk'awa Farouq yayi tare da fad'in, "Mama ina wuni?" Harara Lami ta watsa masa tare da fad'in, "Uwar ka ba, ka baro ta can gida. Ni ba mamarka bace. Kaga wacce ta haifa nan." Ta k'arisa maganar tana mai nuna Sarah da hannu sannan ta cigaba da fad'in, "Ba gaisuwa ka na taho nan in amsa ba, zuwa nayi ka fad'a min shin kai ne uban cikin dake jikin Saratu ko kuwa. Don idan kai ne, wallahi na rantse list d'in ka daban ne. Kuma kar kayi tunanin zan yi maka ragi." Hannu Sarah ta d'aura a kai tare da fad'in..................



*_Chart me up 08128755583_*
[09/09, 10:03 A
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*🦜

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_


☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️

Page 3

Hannu Sarah ta d'aura a kanta tare da fad'in, "Haba Lami wannan wani irin magana kike yi haka? Mai yasa a kullum burin ki, ki zubar min da mutunci a idanun Farouq? So kike kiyi ta danka mu a cikin gidan babu aure?" Sarah ta fad'i tana kuka sosai. Shi kuwa Farouq da idanu kawai yake bin Sarah da mahaifiyarta kamar wawa. Don sam bai son gasgata abunda kunnuwansa suke ji. "Bak'ar munafuka! To sai nayi magana. Wato baki so nima na samu rabo na ko? To wallahi komai dani za ayi shi. Juyo nan ka bani amsar tambayata, shin kai ne uban cikin dake jikinta?" Wani irin b'acin rai ne yake tasowa tun daga can k'asan zuciyar Farouq, bai iya magana ba sai kallon fuskan Sarah yake yi yana son jin wani k'arin bayani ko kuma ta k'aryata zancen da mahaifiyar nata take yi. Amma maimakon haka, Sarah sai girgiza kanta kawai take yi hawaye na zubowa daga idanunta. "Wai ba da kai nake yi bane Umar da kayi min banza kamar wata sa'ar ka!" Lami ta fad'i a zafafe. Gyara tsayuwa Farouq d'in yayi tare da kallon Lami k'asa-k'asa sannan yace, "Ban san maganar da kike yi akai ba! Kwata-kwata ma ban fahimci mai kike cewa ba Mama." Dak'uwa Lami tayi masa tare da fad'in, "Uwarka nace kaji? Ai nasan ka fahimci wannan ko! To ni menene ma na tsayawa sai naji ko kai ne kayi cikin ko ba kai bane. Bayan na san kai d'in fak'iri ne ba wani abun kirki zan samu daga gare ka ba. Amma sai dai ka sani, daga yau ban k'ara bata ko loma d'aya daga cikin abincin gidana, don sai taci ne abun cikinta zai ci, kuma ni da in ciyar da jinin ka, gwara na ciyar da karuwai goma babu lada." K'asa-k'asa Farouq yace, "Ai yanzu ma karuwan kike ciyarwa a cikin gidan." Kallonsa Lami tayi tare da matso da kunnanta tace, "Kace me?" Kau da kai Farouq yayi tare da fad'in, "No babu abunda nace!" Dogon tsaki taja sannan ta juya ta shige cikin gidan har da bugo masu k'ofa. Kicib'is suka ci da Na'ima taci uban kwalliya ta tsuke cikin k'ananan kaya kamar d'iyar arna, "Y'ar albarka har zaki wuce?" Yamutsa fuska tayi tare da fad'in, "Eh! Idan kun ji shuru ku rufe gidan kawai, don ba lallai na dawo gida na kwana ba." "To Allah ya tsare." Fad'in Lami har da d'aga mata hannu. Duk abunda Na'ima da Lami suke cewa, tsaf a kunnan Sarah da Farouq. Fitowa Na'ima tayi daga cikin gida tare da gallawa Farouq harara ta saki tsaki tare da tsirtar da yawu. Har tayi gaba, sai kuma ta dawo dai-dai inda Farouq d'in yake a tsaye tare da sauke glasses d'in fuskanta k'asa kad'an sannan tace, "Ina fatan masoyiyar taka ta fad'a maka tana d'auke da ciki har na tsawon sati biyu." Ta k'arisa maganar tana daga yatsunta biyu a fuskan Farouq d'in. Wani banzan kallo Farouq ya bita dashi mai cike da tsana. Sarah kuwa ji tayi dama tana da layar b'ata ta danna kawai ta ganta a cikin gida saboda tsananin kunya mai had'e da tsoro da take ji. Farouq yana kallo Na'imar ta bud'e gaban motar wani mutum wanda a haife ta haife ta, yaja motar suka bar layin. Juyowa yayi tare da kallon Sarah wacce kanta ke k'asa, ya jima yana kallonta tare da had'iye wani miyau mai d'aci da ya tokare masa mak'oshinsa sannan yayi k'arfin halin fad'in, "Sarah mai nake ji haka daga bakin mahaifiyarki da y'ar uwarki?" Kuka kawai Sarah ta fashe dashi do ita kanta abun jinsa take yi kamar hauka ko rainin hankali ta bud'e baki tace bata san ta yanda aka yi ciki ya shiga jikinta ba. D'agowa tayi ta kallesa tare da fad'in, "Ni wallahi tallahi....." D'aga mata hannu yayi tare da fad'in, "Na fahimta, basa son alak'ata dake ne shiyasa suke son raba mu da wannan zancen na su. Ni kuma idan har ba canza hali za kiyi ba Sarah, babu mai raba mu idan ba mutuwa ba. Ni dai alfarma d'aya nake rok'o a wajen ki Saratu, dan girman Allah ko sau d'aya kada rayuwar da y'an uwanki suke yi ya burge ki. Idan kika mun haka, ni kuma zan cigaba da tsaya miki duk rintsi, kunnuwata zasu kasance a toshe, haka babu wani suka naki ko kuma laifin y'an uwanki da za ayi amfani dashi wajen nuna min bak'inki har yayi tasiri a waje na." Kuka Sarah take yi har da shasshek'a, ita kad'ai tasan mai take ji a cikin zuciyarta. "To wai kukan na miye ne haka? Idan har ba b'acin rai na kike son gani ba, ki share wad'annan hawayen naki." Bayan hannu Sarah ta saka ta share hawayen fuskanta tare da k'irk'iran murmushin babu babu inda ya tsaya sai iya lab'b'anta. "Yauwa ko ke fa! Sannan abu na gaba, ban ji dad'in yanda ba ganki d'azu ba, na d'auka tuntuni mun riga mun gaba magana akan irin shigar da kike yi. Kin san fa da shigar jikin mutum kad'ai akan iya gane wanene shi. Dan girman Allah ki daina saka wannan zaro-zaron gashin idanu nan da wannan k'umbar dake hannunki. Ni wallahi kyama yake bani. Wanda Allah yayi maki ma ya ishe ki Sarah." Hawaye na zuba a idanunta ta furta, "In sha Allah daga yau ba zan k'ara saka d'aya daga cikin abunda ka lissafo ba." Ajiyar zuciya Farouq yayi tare da fad'in, "Allah ya miki albarka amaryata ta sati hud'u masu zuwa. Ki shiga gida hadari ne sosai a gari. Sai mun yi waya." Bata iya cewa komai ba sai murmushin da tayi tare da yi masa bye-bye ta shige cikin gidan. Tana turo k'ofa ta jingina da k'ofar tare da dafe k'irjinta da hannu d'aya sannan ta toshe bakinta da d'ayan hannun tana kuka sosai. Juyawa tayi ta lek'a ta wani d'an rami a jikin k'ofar, ga mamakinta sai ganin Farouq tayi tsaye a wajen amma ba k'ofar gidan yake kallo ba, wani wajen yake kallo daban. Can kuma ya saki ajiyar zuciya tare da tsallake kwatar dake gaban gidan ya wuce. Sai a sannan Sarah ta zame k'asa ta fashe da wani irin kuka mai tafasa zuciya. Ta jima a wajen tana kuka kamun ta mik'e ta nufi cikin gidan. D'akin su ta shiga ta cire hijjab d'in jikinta ta ninke tare da rataye sa a hannun wardrobe sannan ta cire suwaitan jikinta ta mak'ale a abun rataye jaka sannan ta kashe wutar d'akin don babu kowa a ciki, sauran y'an uwanta suna d'akin Lami kamun masu zuwa fita dasu su k'araso. Hawa kan gadon tayi ta kwanta rigingine tana sak'awa da warwarewa akan cikin dake jikinta. Sosai tayi zurfi a tunanin ta yanda aka yi ta samu ciki, sai dai duk iya zurfin tunaninta, bata gano bakin zaren ba, don zata iya dafa Qur'ani tayi rantsuwa bata tab'a sanin wani d'a namiji ba a duk tsayin rayuwarta. Daren ranar bacci b'arawo ne ya kwasheta. Kiran sallar asubahi kuwa, a kunnanta ladani ya kwad'a shi. Saukowa tayi daga kan gadon tare da kunna wutan d'akin haske ya kawo, babu kowa a d'akin, hakan ne ya tabbatar mata da ita kad'ai ta kwana a d'akin. Don da ace y'an uwanta sun dawo daga yawon banzan su jiya, babu abunda zai saka su kyale ta ta kwanta a kan gado ba tare da sun turo ta k'asa ba. Kai tsaye d'akin mahaifinta ta nufa, kamar yanda tayi tsammani hakan ce ta faru. Zaune ta samu mahaifin nata ya fuskanci gabas yana sallah a zaune. Don ciwon k'afar nasa bai barin sa yayi sallah a tsaye. Tun kusan shekaru biyar baya sallah dare ta zame masa tamkar jinin jikinsa. K'arfe uku kamar a kunnansa take bugawa saboda sabo da tashi. Bai kuma komawa bacci sai gari yayi tarwai tukun. Sarah d'aukar roban pentin da yake yin bowali tayi ta fitar dashi tare da zubar dashi a makewayi sannan ta dawo dashi ta ajiye sannan ta fita ta koma bayin ta kamo ruwa sannan ta fito ta d'auro alwala. Kamar zata wuce, sai kuma wani zuciyar ta jata ta nufi d'akin Lami. Tun daga bakin k'ofar take jin wani wawan munshari mara dad'in sauraro kamar an danne rago. Hannu ta d'an d'aura akan k'ofar ta tura, sai taji k'ofar a bud'e. Tura kai tayi ta shiga d'akin tare da lalubar bango ta kunna globe d'in dake d'akin. Lami ta hango tayi wani irin washarere a kan gadon kamar gawa, babu riga a jikinta daga ita sai d'aurin k'irji, shi kansa zanin yayi gefe, mamukanta kuwa d'aya ya kalli arewa, d'aya ya kalli kudu. Gata Ma sha Allah irin jibga-jibgan matan nan ne. Hatta bakinta a bud'e yake. Kau da kai Sarah tayi ta kalli d'ayan gefen da autarsu y'ar shekaru goma sha bakwai da watanni take. Ita ma dai bacci take yi cike da rashin tsari domin bacci ne irin wanda ba'a son musulmi ya rik'a yi wato ruf da ciki. Hannu Sarah ta kai ta d'aka mata duka cinyarta ta baya da yake a kwaye. Da sauri Aina'u ta kai hannu wajen ta Sosa ba tare da ta yanke baccin da take yi ba. Wani dukan Sarah ta kuma kai mata, wannan karan a furgice ta mik'e tana mitsitsitsike idanu tare da sakin wani irin hamma kamar d'iyar arna. Sai da ta ware rass sannan ta k'arewa Sarah kallo wutar balbalin bala'i na taruwa a kwayar idanunta. Don Aina'u irin fitsararrun yaran nan ne wad'anda duk girman mutum ko da kuwa jikinsa kaf furfurace bata raga masa. Y'an unguwanmu sun ce ita ce tayo sak halin Lami, wasu sun ce tafi Lami d'in ma. Tun tana k'ank'anuwarta makirar yarinya ce ta bugawa a jarida. Ga salo kamar wata uwar mata. "Uwar me zan maki cikin daren nan da zaki zo ki katse min bacci na!" Fad'in Aina'u kamar harcenta zai zazzago, don ta kasance irin matan nan masu harshe. Duk yanda tayi magana a hankali, ji za kayi kamar a kwar gida take magana. Da dare da rana basu da bambamci a wajenta. Yanzu haka da tayi magana kasancewar dare mai d'aukar sauti, har sai da mahaifinsu dake d'akinsa ya jiyo sautin muryanta. Hatta Lami mai bacci kamar gawa sai da ta farka a firgice tana sambatu. "Sallah nazo tashin ki kiyi. Don gashi can shirin tada sallar ake yi a masallaci. Ace duk k'arar speaker d'in masallacin can ba zai iya tada ku kuyi sallah ba!" Fad'in Sarah tana mai k'ok'arin juyawa ta bar d'akin duk da kuwa ta san cewa ba sallar za suyi ba. "Dan ubanki baza muyi sallar ba. Idan mun d'aga k'afa zamu shiga aljanna sai ki dawo damu baya saboda ta ubanki ce! Fita ki bar d'akin nan tsohuwar annamimiya!" Fad'in Lami tana mai nuna mata hanyar k'ofa. Komai Sarah bata ce ba, sai ma ficewa da tayi daga d'akin ta koma nata d'akin ta shimfida darduma ta tada salla. Tana nan zaune ko da ta idar da sallar har sai da gari ya waye tass, lokacin k'arfe bakwai sannan ta soma jin bacci a idanunta, amma kuma bata son yin baccin. Burinta ta shirya ta kuma fita domin yawon bin asibitoci ko za tayi dace da asibitin da scanning machine d'insu zai k'aryata cikin da wasu asibitocin da suke cewa tana dashi. Ta yunk'ura zata tashi daga kan sallayar taji muryoyin mata na tashi a tsakar gidan su. Gabanta ne ya buga da k'arfi sai tayi saurin d'aga labule kad'an ta lek'a waje. Da sauri ta saki labulen tana mai dafe k'irjinta da zuciyarta ke barazanar fasowa ta fito saboda arba da tayi da yayyin Farouq mata uku da kuma aunties d'insa guda biyu, gaba d'aya fuskokinsu a turbud'e..............


_Ko mai zai faru a gaba?🤔_



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
[09/09, 10:03 AM] Matar Sayyadee: 🦜
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*🦜

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_


☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️

Page 4

"Ah'aaa! Yaya haka, menene haka kuma zuwa da sassafen na sai kace karb'an kud'in bashi? Ni fa bani son irin wannan naci tun ba'a je ko'ina ba." Fad'in Lami wacce fitowarta kenan daga d'aki baki duk miyan bacci. Bayanta kuma Aina'u ce ke mik'a tare da hamma babu addu'a sai wani "umm'iyyyyyyy!" Take fad'i kamar k'atuwar rago ko kuma bijimin sa. D'aya daga cikin matan wacce sai jijjiga take yi, ga dukkan alamu tafi kowa a cikin su hassala tace, "To dama uban me zai kawo mu wannan wulak'antaccen gidan wanda babu albarka cikinsa in ba tsautsayi ba. Banda fitina da jawowa kai jidali irinta Umar Farouq, menene abun so a cikin y'ay'an gidan nan wanda gaba d'aya kowa ya gama sanin karuwan gida ne su." D'ayar siririyar cikin sy tayi saurin cafe zancen wajen fad'in, "Aunty Bilkisu ai gansama-gansaman zaurawar gidan nan sun wuce karuwan gida, don ni kam ba zan Kira su da y'an mata tunda tun daga kan babbar har k'aramar babu wacce bata san dad'in d'a namiji ba." Saurin cafe zancen k'aramar cikin su tayi tare da fad'in, "Yo aunty Halima ai

Please Login or Register in order to submit comment