Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi a k'asan nan ba kika bari nazo wajen nan zan baki mamaki!" A fusace Sarah tace, "Wani mamaki? Nace wani mamaki ne kuma ya rage baka bani ba." Ba tare da yace komai ya mik'e a fusace. Ko kamun yayi taku d'aya ta mik'e da sauri ta zauna a kan kujeran dake fuskantarsa. Wani dariya ne ya taho masa amma yayi saurin mayar dashi tare da kau da kai yana murmushi don dama ba zuwa wajenta zai yi ba, kawai barazana ce domin ta bar tiles d'in saboda sanyi. Zama yayi tare da cigaba da abunda yake yi. Ita kuma Sarah sai harare-harare take yi. Sun kwashi kusan awa guda sannan ya mik'e tare da fita ya kullo k'ofar. Sarah na ganin ya fice kuma ya kullo k'ofar ta kifa kanta akan desk d'in ta fashe da kukan bak'in ciki. Shi kuwa _Khalil_ yana fita suka ci karo da doctor Kamal dama kuma wajen _Khalil_ d'in zai zo. "Wajenka dama zan zo." Gyara tsayuwa yayi tare da yin bake-bake a k'ofar office d'in ya wani ci d'aci tare da fad'in, "To gani!" Sai da doctor Kamal ya kalli k'ofar office d'in sannan yace, "Ka kira ni emergency akan inzo nan kai zaka je yin wani abu, sai kuma gaka na ganka tare da wannan yarinyar. _Khalil_ ba halinka bane. Dan Allah kar kace zaka zubar mata da cikin dake jikinta. Y'an iskar yara sai sun gama yawon banzan su a tit....." A mugun tsawace _Khalil_ yace, "Enough! Enough doctor Kamal Isah Bashir! Kar ka k'ara jifan Sarah da wad'annan kalmomin. Sarah ba irin matan da kake tunani bane." Baki bud'e doctor Kamal ke kallon _Khalil_ don bai tab'a ganinsa a irin wannan yanayin sabida mace ba. Macen ma mai d'auke da cikin shege. A iya sanin da yayi wa _Khalil_ ya tsani y'an iskan mata. " _Khalil_ this lady that you're protecting haka, she's prostitude! Duk abunda zata fad'a mak......" Bai kai k'arshen zancen ba yaji wani gigitaccen mari ya sauka akan kuncinsa sai da yayi saurin saka hannu ya dafe kuncin yana mai kallon gefe-gefe. Ganin babu kowa kuma babu wanda yaga komai sai ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Ibrahim ni ka mara? Ni ka mara saboda ina fad'a maka gaskiya." Wani kallon banza yayi masa tare da fad'in, "To hell with the fucking stupid gaskiya gaskiyarka. Idan bakinka ya kuma kuskuran kiran matar da zan aura da karuwa, na rantse maka da ubangijin rana da wata sai na d'aureka kuma babu uban da ya isa ya fito da kai. Kuma cikin jikinta it's mine. Na fad'a da babban murya, cikin dake jikin Sarah, nawa ne! Kuma duk uban da ya isa ya kira ta da karuwa yaga abunda *_Ibrahim Khalilullah Nurudden_* zai aikata." Yana gama fad'in haka ya wuce fuuuuuu ya nufi pharmacy domin d'auko mata magunguna don tun d'azu yake lura da ita jiri take gani kuma babu k'arfi a jikinta. Shi kuwa doctor Kamal da mugun tsananin mad'aukakin mamaki yabi _Khalil_ d'in da idanu. Don ya mugun sanin hakinsa. In fact tare suka yi karatu a _London_ har kammalawan su. Yasan yanda ya tsani Zina da kuma mazinatan. Sannan yaga mata kyawawa iri-iri, turawa, indiyawa, larabawa duk bai fad'a halaka ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinyar duk da ita ma kyakykyawar ce. Shafa kumatunsa da suka ji mari yayi tare wucewa ya bar wajen. _Khalil_ kuwa sai da ya d'auko duk magungunar da yasan Sarah zata buk'acesu sannan ya dawo office d'in hannunsa d'auke da leda mai tambari da sunan asibitin still kuma fuskansa a mugun d'aure. "Ki tashi in mayar dake gida." Ya fad'i sounding command. Cikin sauri ta mik'e shi kuma ya fita tabi bayansa. Kulle k'ofar yayi tare da fad'i, "Kiyi tafiya a hankali kar ki fad'i. Ko in rik'e ki?" Da jin haka tayi saurin yin gaba don taga alama sam bai da kunya. Har wajen motarsa suka isa, shi ya bud'e mata gidan gaba ta shiga sannan ya zaga ya shiga driver sit sannan ya tada motar yayi reverse ya bar cikin asibitin. A hankali ya dunga tafiya ba tare da ya k'ara ce mata ko uffan ba har suka isa k'ofar gidansu Sarah. Parking yayi tare da kashe motar ya juyo ya tsura mata idanu. Tana jin idanunsa na yawo a jikinta amma tak'i kallon wajen. Ledan maganin ya d'auko tare da fiddo da magungunan ciki sannan yace, "Hey, kalle ni nan." Kamar baza ta juyo ba, sai kuma ta juyo ta kallesa tana mai turo baki gaba. Tsurawa kyakkwar bakinta kallo yayi yana tuno ranar da tsautsayin ya afka. "Kin san wani abu? Tsiwarki ita ke ja mutun yayi maki abunda bai yi niyya ba. Ko wancen ranar ke kika ingiza ni har mai afkuwa ta afku. Idan kika b'ata rai ko kuma kika turo baki, wani irin kyawu kike k'ara yi sosai. Sai ki rik'a looking very sexy!" Wani irin kuka Sarah ta fashe dashi jin abunda yace. Bak'in ciki take ji idan yana maganar cikin dake jikinta. "Kin san Allah idan kina kukan nan, wancen ranar ba'ayi na gaske ba, amma ina ganin soon an kuwa zuwa wajen." Hannu ta kai zata bud'e k'ofar taji sa a gark'ame. Kallonsa tayi tare da shagwab'e fuska tace, "Dan girman Allah ka bud'e min, kaji ma kiran sallah ake yi!" Kallon maganin da ta fito dashi yayi tare da fad'in, "Kalli nan, wad'annan guda ukun kullum sau d'aya zaki rik'a sha, wannan kuma safe da dare. Allah ya k'ara maki lafiya Matata. Kiyi min magana da Mama idan kin shiga ciki. And lastly, wallahi kar in k'ara kiranki a waya kik'i d'agawa. Don wallahi komai dare sai nazo, kuma ni kai na ban san mai zai faru ba idan nazo d'in." Yana gama fad'in haka ya cire lock d'in yana kallon fuskanta. Bud'e motar tayi ta fita a hankali ba tare da ta d'auki ledar ba, sai da ta rufe k'ofar sannan ta lek'o ta window kasancewar ya zuge glass d'in tare da fad'in, "Ba zan d'auka ba, dan girman Allah kar ka fasa abunda kace za kayi. Kuma bazan sha maganin ba. Ka tafi da tsiyarka. Kuma cikinka dake jikina, a leda zan juye na watso maka shi a fuska na huta da jaraba." Da wani irin hanzari ya cafki hijjab d'inta ya cukuikuyota da hannu d'aya tare da fad'in, "Maimaita mai kika ce?" A gigice tace, "Na rantse cewa nay na manta ga ledan maganin nan baka mik'o min ba. Kuma wancen farin ma ya ma kace ayi amfani dashi." Dariya ce ta taho masa sosai amma bai yi sai murmushi ya saki tare sa d'aukar maganin da d'aya hannunsa ya mik'a mata. Da sauri ta amsa har da fad'in, "Nagode" shi kuma ya saki hijjab d'in nata tayi saurin barin wajen ta nufi k'ofar gidansu ba tare da ta waiga ba. Tana bud'e k'ofar suka ci karo da Baba ya fito karo na bakwai ko Allah zai sa ya ganta. Don lokacin dasu Na'ima suka baje a tsakar gida babu labarin da suke yi sai na _Khalil_ da irin motar da yazo da ita. Jin hakan sai ya tada hankalin Baba ya soma tunanin ko Sarah ta soma hawa layin y'an uwanta ne. Ya jira kusan mintuna ashirin ko Sarah zata dawo amma yaji shuru, ya daure ya k'ara goma akai, ganin har lokacin shuru sai ya mik'e ya d'auki sandarsa ya fito waje amma wayam. Yana jin sanda su Na'ima suke dariyar ya fita nemo y'ar gwal. "Baba dama dawowa kayi kar ka wahalar da kanka. Don saurayinta yazo sun fita tare." Fad'in Hassana. Bini-bini Baba ke fitowa ya duba ko Sarah ta dawo amma wayam. Sai a karo na bakwai sannan ta turo k'ofar suka yi ido hud'u. Wani ajiyar zuciya Baba ya sauke tare da fad'in, "Saratuuu!" Sai kuma ya fashe da kuka. Da sauri Sarah ta waiga taga motar _Khalil_ na nan, sai taji hankalinta ya tashi don bata son yardar da Baba yayi mata ya rushe. A gigice ta soma magana, "Wallahi Baba ba abunda kake tunani bane. Dan Allah ka daina kuka." Ta fad'i tana mai fashewa da kukan. Da sauri _Khalil_ ya bud'e mota ya fito tare da k'arisowa wajen ya duk'a tare da fad'in, "Ina wuni Baba?" Baba dake matsar hawaye ya d'ago ido ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Bawan Allah na rok'e ka da girman ubangijin idan ba alkhairi bane ya kawo ka wajen Saratu kayi tafiyarka Allah ya had'a ka da dai-dai da kai. Ka dubi Allah da annabi kar ka lalata min tarbiyan y'ata guda d'aya da ta fita zakka!" Shuru _Khalil_ yayi na y'an dak'ik'u tare da fad'in, "Baba wallahi alkhairi ne ya kawo ni wajen 'yarka ba sharri ba. Ni da niyyar aure nazo k'ofar gidan nan ba da niyyar yaudara ba." Da sauri Sarah ta kalli Baba tare da fad'in, "Baba kar ka yarda da maganarsa, fatar bakinsa ne fad'i amma cikin zuciyarsa ba haka bane. Shine sanadiyar duk abunda ke faruwa dani yanzu. Shine dalilin rugujewar farin cikina. Shine dalilin fasuwar aure na. Baba wannan dake durk'ushe a gabanka shine uban cikin dake jikina." Ta k'arisa maganar tare da fashewa da kuka. Baba kuwa ji yayi kamar an d'iga masa dalma a kunne. Rintse idanu yayi cike da k'una a zuciya yace, "Bawan Allah mai muka maka? Mai d'iyata tayi maka ka tarwatsa mata rayuwa? Kana ganin kayi min adalci kenan? Ban tab'a b'ata d'iyar wani ba, wannan jarabawace kawai daga mahalicci!" Idanun _Khalil_ gaba d'aya sun kad'a kun yi jazur ya d'ago tare da kallon Baba yace, "Baba, dan alfarmar ubangiji halittu ka saurare ni ko da na mintuna biyar kacal. Wallahi, tallahi rantsuwar musulmi ban zo nan da niyyar cutar kowa ba, zuwa na nan k'ofar gidan nazo ne domin in auri 'yarka." Hakanan baba ya d'an ji _Khalil_ ya kwanta masa. Kallon Khalil d'in yayi tare da fad'in, "Shiga masallaci kayi sallah, idan an idar kayi sallama zan aiko Saratu ta shigo da kai har ciki. Bari na shiga nima nayi sallar." Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar _Khalil_, cike da ladabi yace, "Nagode Baba!" Ya fad'i hakane tare da mik'ewa ya nufi masallacin gaban gidansu Sarah wanda yake daga hannun hagu, yayin da nasu gidan yake daga dama. Baba ma shigewa yayi Sarah na biye dashi kanta a k'asa hannunta rik'e da ledar magungunan da _Khalil_ ya bata. Gaba d'aya suna tsakar gida har da y'ay'ansu. Rabo d'an wajen Na'ima ya kalli Sarah tare da fad'in, "Lami ga Saratun ta dawo daga wajen saurayin nata." A fusace Sarah tace, "Daga wajen ubanka na dawo." Na'ima mahaifiyarsa ta taso a fusace tare da fad'in, "Zan ci ubanki a cikin gidan nan wallahi idan kika ce zaki rik'a takurawa d'ana. Babu ruwana da cikine a jikinki duka zan maki." Harararta Sarah tayi tare da fad'in, "To ai sai ki kashe ni kawai. Banza kawai." Yunk'urawa Na'ima tayi zata taho wajen Sarah karaf Lami ta rik'e ta tare da fad'in, "Barta! Yanzu haka duk salon kar ta bamu abunda ta samo ne daga hannun saurayin nata." Juyowa Baba yayi tare da kallon Sarah yace, "Saratu wuce ciki kinj." Babu musu Sarah ta shige ciki. "Ban gane abunda kake nufi ba Nuhu anyi yamma da kare!" Ko kallonta Baba bai yi ba ya shige d'aki. "Ahafff! Ba na fad'a maki ba Lami. Baba fa ya san duk tsiyar da Sarah take shukawa. Raba kud'in suke yi a tsakanin su shiyasa kike ganin yafi sonta akan mu gaba d'aya." Fad'in Aina'u. "Na ko tabbatar da maganarki yanzu Aina'u. Aikuwa dani suke zancen." Fad'in Lami tana kwafa. Dai-dai nan Sarah ta kuma fitowa ta nufi fanfo Lami na harararta. Alwala da d'auro sannan ta kuma komawa d'aki. Tana idar da sallah ta jiyo muryan Baba yana kwad'a kiran sunanta. Da sauri ta fito ta nufi baranda inda ta ganshi tsaye a bakin k'ofar d'akinsa, "Yi maza gashi can yana kwad'a sallama, je shigo dashi." Da "To Baba" Sarah ta masa tare da juyawa. Na'ima kuwa kallon Hassana tayi wacce itama kallon nata take yi sannan gaba d'aya suka mai da dubansu ga Lami wacce tayi suman tsaye tana kallon Baba cike da mamaki. Mintuna biyu sai ga Sarah tafe, _Khalil_ biye da ita a baya. Bai kalli kowa a cikinsu ba, don har yanzu bai gama tabbatar da cewar Lami ita ce cikakkiyar mahaifiyarsu Sarah ba. Dama kuma tuni baba ya shige cikin d'aki. Sallama _Khalil_ yayi tare da shiga don tuni baba ya amsa tare da bashi damar shiga. Yana shiga Sarah ta bar wajen zata wuce d'aki Lami ta shak'o ta tare da fad'in, "Dan ubanki shine zaki kai sa wajen mahaifinku! Wato kin fi k'aunarsa dani ko? To wallahi baku isa ba komai dani za'a ci." Tana gama fad'in haka ta fad'a d'akin babu sallama lokacin _Khalil_ suna k'ara gaisawa da Baba. "Na rantse da, girman Allah Nuhu baka isa Kaci kud'in nan kai d'aya ba. Ai nice na d'auki cikin Sarah wata har tara na kuma sha wuya nayi nak'uda na haife ta. Fito da duk wani abu da yaron nan ya baka ayi kaso." Sai kuma ta mayar da dubanta ga _Khalil_ wanda kansa ke a k'asa tare da fad'in, "Kai kuma Munafuki................



*_Na rok'e ke ki da girman ubangiji kar ki fitar min da littafi. Kud'in karatu kawai kika biya ba kud'in mallakar littafi ba. Kiji tausayin marainiyar Allah don wallahi Sana'a na d'aukesa ba nishad'i ba. 🙏_*


*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*



*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment