Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

D'IN DA SARAH TA GANI HAR TA TSORATA DA GANINSA TA GUDU BA TARE DA TAYI ABUNDA YA KAITA ASIBITIN BA? MAI DOCTOR KHALIL YAKE NUFI DA YACE BA ZAI YUWU BA ACE SARAH NA D'AUKE DA CIKIN WATA BIYU? A INA YA SAN SARAH, KUMA MENENE ALAK'ARSU? WACECE LAMI? WANENE BABA NUHU? SHIN MAI MAI K'ANWAR MATATA YAKE NUFI? TUN FA DA AKA SOMA LABARIN BAMU GA MATAR BA, BAMU GA MIJIN BA, BARE KUMA K'ANWAR. HMM WALLAHI Y'AR UWA KAR KI BARI AYI WANNAN LABARIN BABU KE. DOMIN AKWAI CHAKWAKIYA MAI ZAFI A CIKINSA._


*_A NAN NA KAWO K'ARSHE. FREE PAGES, GA MAI BUK'ATAR KARANTA LITTAFIN K'ANWAR MATATA, SAI YA TURO D'ARINSA BIYAR ZUWA WANNAN ASUSUN BANKIN 0592412800, ZULFAU SAID GT BANK, SAI KI TURO DA SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER 08128755583_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜 *KANWAR MAZA* 🦜

*7*


Da sauri yabi Aina'u yana kwala kiran "Ke! Ke!! Dan Allah tsaya." Aina'u najin muryansa ta k'ara sauri don bata fata ko cikin mafarkinta wannan doctor d'in ya kasance mijin Sarah. Cikin sauri ta tari Napep ta fad'a ciki. Cak Khalil ya tsaya yana mai bin napep d'in da idanu har ya daina ganinsu. Ya jima tsaye a wajen yana jin wani abu na tasowa a k'asan zuciyarsa. Hannu ya kai ya yamutsa gashin kansa kamun yayi wani irin tsayuwa tare da tura hannunsa cikin aljihun wandonsa yana kallon sama. Can kuma ya juya da sauri tare da komawa office d'insa. Yana jin ana gaishesa amma ko juyawa bai yi ba balle ya amsa. Direct wajen computer ya nusa ba tare da ya zauna a kan kujera ya d'an rankwafo yayi danne-danne jikin computer tare da saurin d'aukar wayarsa ya kwashi numbers d'in Sarah dake rubuce a file d'inta sannan ya kashe computer d'in ya zira wayarsa cikin aljihu ya fita daga office d'in bayan ya rufo k'ofar ya saka key. Wayarsa ya fiddo ya danna ya lalubo numbern doctor Kamal tare da shaida masa ya bar asibiti yazo yayi replacing d'insa akwai wani abun gaggawa da zai je ya aiwatar. Yana gama waya da doctor Kamal ya fita ya nufi parking space. Wata arniyar mota *_Pagani Zonda HP Barchetta_* that worth 17 million ya shiga tare da yi mata key ya bar asibiti. Sai da ya hau titi kuma sai ya rasa inda zai je. Juya kan motor yayi ya nufi Sokoto road inda gidan su yake. A wani k'atoton mansion ya danna horn, cikin sauri mai gadi ya wangale gate shi kuma yayi shiga tare da yin parking anan harabar gidan ba tare da ya isa parking space ba. Fitowa yayi daga cikin motar ya shiga cikin gida da sassarfa, babu kowa a parlor do haka kai tsaye ya haura sama ya saka key ya bud'e d'akinsa tare da shiga ya maida key d'in ya rufe k'ofar sannan ya nufi wajen wani wawaken waje da aka rufe sa da tinted glass ya danna wani abu glass d'in ya zuge. Wata jaka ya fiddo y'ar karama mai hannun chain kalar pink. Sai da ya jujjuya jakar a hannunsa sannan ya k'arisa wajen gado ya zauna a bakin gadon tare da zuge zip d'in jakar ya zazzage a kan gado. Abunda ya fara cin karo dashi shine d'an kunne guda d'aya kalar bak'i hook d'insa ya b'alle. Murmushi yayi tare da maida d'an kunnan cikin jaka sannan ya d'auki kud'in dake kan gadon wanda a cikin jakar ya fad'o. Dubu d'aya ne da d'ari bakwai, Sai turaren soft da lipgloss. Sune kawai abunda yake cikin jakar. Mai da komai yayi a cikin jakar tare da kwantawa rigingine yana tuno wasu abubuwa da suka wuce a cikin idanunsa kamar yanzu komai ke faruwa. Cikin sauri kamar an tsikaresa ya tashi zaune tare da zaro wayarsa k'irar Samsung mai matuk'ar kyau da tsada yayi dialing number Sarah da ya d'auka. Sai dai tayi ringing har ta gaji ba'a d'auka ba. Ya kira yafi sau goma amma babu amsa. Tsaki yayi tare da jefar da wayar a kan gado. Yana bala'in bak'in cikin ya kira waya ba'a d'aga ba. Shi a k'a'ida sau d'aya yake kira bai k'ara na biyu. Mirginawa yayi tare da mik'a hannunsa ya jawo drawer ya tura hannu ya d'auko _Mastika Gum_ ya b'are ya watsa a baki ya hau tauna yana mai lumshe idanu. B'angaren Sarah kuwa tun da ta hau keke napep gabanta ke wani irin bugawa sai da ta saka hannunta ta dafe k'irjinta don ji take yi kamar zuciyarta zai faso k'irjin ya fito. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda ta dunga maimaita tun tana yi cikin zuciyarta har ya soma fitowa fili. Matar dake kusa da ita ta kalleta tare da fad'in, "Baiwar Allah lafiya?" Sarah bata bata amsa ba sai cewa mai napep d'in tayi, "Tsaya, tsaya zan sauka anan." Parking mai napep yayi ita kuma ta sauko gaba d'aya bata cikin hayyacinta. Mik'a masa d'ari biyar tayi tare da juyawa ta soma tafiya ko karb'an canji bata tsaya yi ba. Shi kuwa mai napep yaja napep d'insa yayi gaba. Sarah kuwa tafiya ta cigaba dayi a k'asa tana kalle-kalle. Tayi tafiya mai nisa kamun Allah ya had'a ta da wani asibiti a gabanta. Hamdala tayi tare da nufa cikin asibitin kai tsaye. Bud'e kati tayi sannan ta zauna domin jiran layi yazo kanta. Kamun layi yazo kanta har wani zabura take yi tana mik'ewa saboda tsabar k'aguwa. Sai da mutane takwas suka ga likita sannan aka kira sunanta. Cikin sauri har tana tuntub'e ta fad'a cikin office d'in a burkice. Doctor yayi saurin d'agowa ya kalleta, ganinta a hargitse sai yayi mata nuni da wajen zama tare da fad'in, "Have a sit." Zama tayi da sauri dama kuma abunda take jira kenan. K'ura mata idanu doctor Alpha yayi kamun yace, "Young lady, how can I help you?" Ai kamar Sarah jira take sai ta fashe da kuka, bai yi yunk'urin hanata ba, sai ma jingina da yayi da jikin kujera yana kallonta, sai da tayi mai isarta sannan ya mik'a mata tissue ta karb'a ta goge hawayen. A karo na biyu doctor da ya kasance bayarabe kuma bai jin hausa sannan kuma a haife ya haifi Sarah, yace, "My daughter what's the problem? Feel free to tell me exactly what's wrong with you. Let's have heart to heart conversation." Ajiyar zuciya Sarah ta sauke tare da fad'in, "Sir can I ask you a question?" Hannunsa biyu ya d'aura akan desk d'in dake gabansa ya bata full attention d'insa tare da fad'in, "You can ask any question. I'm here for you." Sai da ta sunkuyar da kai sannan tace, "Doctor can someone get pregnant without sexual penetration?" Sai da doctor yayi wani murmushi sannan ya kalli Sarah tare da fad'in, "What's your name young lady?" Ba tare da ta d'ago ba tace, "Sarah, Saratu Nuhu." Murmushin ya k'ara yi a karo na biyu tare da fad'in, " *_Pregnancy happens when a sperm fertilises an egg, which can happen even if you've not had sexual intercourse (penetration)._*
During vaginal penetrative sex (where the penis enters the vagina) semen can be ejaculated. Semen is the liquid produced during ejaculation and contains millions of sperm.
As soon as the penis is erect, (before ejaculation), a liquid called pre-ejaculate or "pre-cum" is produced. This liquid can contain thousands of sperm. The ovaries release 1 or more eggs (ovulation) 12-16 days before a period starts.
The sperm enters the body through the vagina, then travels through the cervix and womb to the fallopian tubes, where the egg is usually fertilised (conception). The egg can be fertilised by sperm contained in semen or pre-ejaculate." Kallon doctor Sarah kawai take yi alamar bata fahimce sa ba. Ganin hakan a fuskanta, sai ya sake yin murmushi tare da fad'in, "Here is the explanation, *_It is possible to get pregnant if sperm comes into contact with the vagina, if for example:_* *_your partner ejaculates very close to your vagina your partner's erect penis comes into contact with your genital area (vagina or vulva)_* *_The risk of getting pregnant in this way is very low because sperm can only live for a short time outside the body._*" A tsorace Sarah ta mik'e tsaye, shima doctor mik'ewa tsayen yayi tare da fad'in, "Hey calm down. Have a sit let talk." Da kyar ta iya zama tare kallon doctor babu kyaftawa. Shima doctor zama yayi tare da fad'in, "Sarah are you pregnant?" Ai fad'in haka da yayi Sarah bata san lokacin da ta mik'e da sauri ba ta fice daga office d'in har da had'awa da gudu. Shima doctor da mamaki yabi bayanta yana kiranta amma bata jo juyo ba ta bar asibitin. Tana fitowa ta nufi asibitin _ZAKARIYYA_ dake magajin gari. Cikin sa'a ita ce mutum na biyu da doctor ya gani, tana shiga tayi ta soma rab'e-rab'e har sai da doctor Usman ya d'ago yana kallonta har ta naimi waje ta zauna. Bai ce mata komai na tsawon mintuna biyu, ita kuma sai wasa da jelar hijjab d'in jikinta take yi. "Me ke damun ki?" Taji saukar muryansa a cikin kunnanta har sai da hantar cikinta ta kad'a. A hankali ta d'ago hawaye shab'e-shab'e a fuskanta. Doctor Usman bai yi mamaki ba don idan da sabo sun saba da ganin haka a wajen y'an mata sabon shigan fara iskanci idan sun yi ciki ko kuma masu fama da cutar HIV sabon shiga, ko kuma irin shagwab'ab'b'un yaran nan masu kuka idan basu da lafiya. "Me ke damun ki?" Ya sake tambaya karo na biyu. Bud'e baki Sarah tayi zata fara magana bakinta ya soma rawa sai ta kuma fashewa da kuka. Bai yi yunk'urin hanata kukan ba, ita da kanta tayi mai isarta sannan tace, "Doctor da gaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da namiji ya kasanceta ba?" Cikin zuciyar doctor Usman yace, "Anzo dai-dai wajen!" Amma a zahiri sai kallonta yayi tare da fad'in, "Ciki gare ki?" Gyad'a masa kai tayi tare da fad'in, "Duk asibitin da naje sai ace ina d'auke da juna biyu, kuma ni wani namiji bai tab'a kusantata ba." Mik'ewa doctor yayi tare da fad'in, "Tashi ki hau wancen gadon zanyi maki scanning." Babu musu Sarah ta hau kan gadon tare da d'age rigar jikinta sama tana mai lumshe idanu hawaye na zirarowa daga k'urmin idanunta. _AquaSonic_ (gel d'in da ake zubawa a ciki kamun scanning) ya zuba mata tare da soma yi mata scanning. Kallon fuskanta dake a rufe yayi tare da mayar dashi kan screen d'in computern dake nuna b'aro-b'aro tana d'auke da ciki. Bai fad'a mata ba sai mik'awa mata tissue yayi tare da fad'in, "Goge jikinki ki koma ki zauna ina zuwa." Gaban Sarah na fad'uwa ta goge cikin nata tare da sauka daga kan gadon sannan ta koma inda ta taso ta zauna tare da had'a kai da guiwa tana addu'a a zuciyarta Allah yasa wannan karon an gano babu ciki a jikinta. Dawowa Doctor yayi hannunsa d'auke da paper d'in da yayi printing ya zauna sannan ya kalleta na kusan second goma sannan yace, "Saratu Nuhu!" A firgice ta d'ago gabanta na bugawa. Kallon paper d'in hannunsa yayi sannan ya kalleta tare da fad'in, "Scanning machine ya nuna kina d'auke da ciki har na tsawon sati a jikinki. Fad'a min gaskiya tsakaninki da Allah ko na iya taimakonki, ta yaya kika yi ciki?" Kuka Sarah ta fashe dashi sosai tare da soma bubbuga k'afarta a k'asa tana jujjuya kanta. "Ba kuka za kiyi ba, fad'a min gaskiya za kiyi ko hakan zai iya sakawa na taimaka maki." Jin haka ya saka Sarah ta tsayar da kukanta cak tare da fad'in, "Wallahi tallahi doctor ni ba y'ar iska bace." Murmushin yayi don idan da sabo ya saba da jin haka a wajen wasu y'an matan. "Naji, fyad'e aka yi maki?" Girgiza kai tayi tare da fad'in, "Bai kai ga jikina ba wallahi. Bai kusanceni ba." Shuru yayi yana kallonta, sai can kuma yace, "Bari na amsa maki tambayar farko da kika min lokacin da kika shigo. Cewa kika yi, Doctor da gaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da namiji ya kasanceta ba? To amsarki ita ce, dagaske ne mace na iya d'aukar ciki ba tare da d'a namiji ya shiga cikin jikinta ba. Amna idan har mace zata bari namiji yayi wasa da al'aurarsa a jikin nata al'aurar har ya kawo, ma'ana ya fitar da maniyi a kan al'aurarta, to tabbas zata iya samun ciki sai dai kuma sai dai the risk is very low sabida kwayoyin halittar dake cikin maniyi zasu iya rayuwa ne na k'ank'anun lokacin a wajen jikin mace, amma a cikin jikin mace zai iya d'aukar kwanaki biyar zuwa shidda kamun su mutu. Idan har mace ta soma jinin al'ada (Menstruation) to a ranar idan ta fara k'irge, d'aya, biyu har zuwa kwana goma sha hud'u, to a ranar take samar da kwai, kuma a wannan lokacin she's not safe, namiji na kusantarta, zata samu ciki. Kuma sannan kar ki manta na fad'a maki sparm zai iya rayuwa a cikin jikin mace har na tsawon kwana biyar, hakan na nufin idan aka kusanceta 11, 12, 13, ko ba'a kusanceta 14 ko 15 ba zata iya samun ciki. Shiyasa yake da tsananin kyau mace ta rik'e kanta ko da wasan banza kada ta bari wani namiji yayi da ita idan ba mijinta ba. Amma ban san mai yake janku ku y'an mata ba kuke fad'awa tarkon *_Samarin Shaho_*! Su babu abunda suke so sai jikinku, kuma da sunyi amfani daku a k'arshe yar daku zasu yi sune su naimi ta kirki su aura." Kuka sosai Sarah keyi, bata san ta yanda za tayiwa doctor bayani ba, sai cewa kawai tayi, "Nagode doctor da bayanin da kai min." Sosai yaji tausayinta, amma har ga Allah babu wani abunda zai iya yi mata. Kuma ba zai iya bata shawara a kan ta zubar da cikin ba. Sarah kuwa mik'ewa tayi tana jin kanta kamar zai tsage tsabar yanda yake mata azabar ciwo, gashi irin bayanin da wancen doctor d'in yayi mata, shi wannan doctor d'in yayi mata. Sabida haka babu wani buk'atar sake zuwa wani asibiti domin tabbatarwa. Doctor Usman na kallonta har ta fice ta bar cikin office d'in. Ko da ta fito, a wajen asibitin ta samu wani d'an dandamali ta zauna saboda jirin dake d'ibanta sosai. Ga wani uban yunwa dake kwakwular cikinta. Had'a kai da guiwa tayi tana tariyo abunda ya faru kwanaki goma sha takwas da suka wuce................



*_DAN DARAJAR GIRMAN UBANGIJI KAR KI FITAR MIN DA BOOK. WALLAHI TYPING AKWAI MATUK'AR WAHALA DA CIN RAI. KI TAIMAKA MIN Y'AR UWA!_*

*_DUK MAI SONA TA HANYAR SAYAN BOOK D'INA KAWAI ZAI GWADA MIN, TURA D'ARIN KI BIYAR KI SHA KARATU CIKIN SALAMA BISA WANGA ACCOUNT 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK SAI KI TURA DA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA 08128755583_*


*_MATAR SAYYADEE_*
[9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*PAGE 8*


Kuka take yi sosai har da shashshek'a tana jin ina ma bata zo duniyar ba balle wannan abun ya same ta. Taso ta kasance ta daban a cikin y'an uwanta, sai gashi ita ma an rubuto a cikin k'addararta akwai samun ciki ba tare da aure ba. Sosai ta tsani rayuwar da y'an uwanta suke yi wanda mahaifiyarsu ita ce ta d'aura su a kan wannan turba saboda son abun duniya. Da ana canza mahaifiya da tabbas ta jima da canza nata mahaifiyar. Mahaifinta ne ya fad'o mata a rai, ta san tabbas shi zai fahimceta, to amma wanda zata aura fa? Tuno hakan ya saka ta kuma rushewa da kuka. "Shikenan ni ba'a rubutomin aure a nawa littafin ba. Na shiga uku! Ni wallahi da nayi ta zama a cikin gidan mu ina kwasar bak'in ciki, gwara na tafi *_Wamba_* wajen dangin mahaifina nayi zama na a can. Ban damu da ko k'auye bane ko birni! Buri na in ganni a d'akin mijina ina bautar ubangiji!" Sarah ta fad'i a bayyane tare da mik'ewa ta soma tafiya a k'afa kasancewar layuka shidda ne ya rabasu da inda take. Kan titi _Kasuwar gwari_ ta mik'e tayi ta tafiya har ta iso _Jos road_ sannan tayi k'asa kasancewar can k'asan Jos road d'in suke. Ga zafin rana, ga kuma zazzab'in dake damunta da matsanaici ciwon kai wanda ya ninku sakamakon kukan da tasha. Tana isa k'ofar gidansu gabanta ya yanke ya fad'i ganin motar y'an sanda da kuma y'an sandar a kwar gidansu ga kuma uban cincirundon samari da y'an mata har da wasu matan auren layin da suka fito suna baiwa idanunsu abincin. Tana isowa gaba d'aya idanun jama'a ya dawo kanta. "Yauwa, ga d'aya karuwar ta dawo. Da gani ba gida ta kwana ba. Ai mu dai Allah bai had'a mu da makwaftar kirki ba. Ni dama tashin su za ayi daga unguwar nan don muna da y'ay'a mata dake tasowa kada suga abunda suke yi suma su soma jin sha'awar yi." Fad'in wata mata tana hararar Sarah. Sarah kuwa kutsawa tayi cikin mutanan nan ta shige cikin gidan. Turus ta tsaya ganin Baba a tsakar gida dafe da goshi gaban rigarsa duk jini yana kuka, gefe kuma su aunties d'in Farouq ne da k'annansa maza da mata a gefe sai girgiza suke yi suna fad'in wallahi baza su yarda ba. Nuratu, Aina'u, Na'ima, da Hassana kuma a waje d'aya suna fad'in babu inda zasu je kuma babu uban da ya isa fitar dasu zuwa police station. Lami kuwa sai fad'i take, "Ko kotu za'a je, aje ban jin tsoron uban kowa, sune suka biyo mu har gida da fitina, mu kuma muka kare kanmu." Baba dake kuka ya kalli officer d'in da yake magana cikin lalama akan su Lami su biyosa zuwa station yace, "Bawan Allah d'an sanda, ni na baka umarnin ka tafi dasu da tsiya, idan sunk'i kuyi amfani da k'arfin ku na hukuma ku fitar dasu, amma kuma banda wancen da ta shigo yanzu, don babu hannunta a kan duk abunda ya faru." Ya k'arisa maganar yana nuna Sarah. Police d'in kuwa, bai saurari maganar Baba, sai bada baki yake yi, don babu yanda za ayi ya nuna power ya fitar dasu Nuratu zuwa police station domin Hassana budurwarsa ce, Marfu'a kuma yanzu haka ma tana d'akinsa a wajensa ta kwana jiya. Hassanar ya kira gefe, da kyar taje tana wani cin magani. Sun jima suna magana, a yanda yake lallaminta, zaka d'auka uwarsa ce ita. "To naji, amma wallahi baza mu wuce mintuna ashirin ba a can." Da sauri yace "Na maki alk'awarin haka." Sai da taja tsaki sannan ta koma tayiwa y'an uwanta magana sannan suka fita su duka banda Sarah da ta jingina da bango abun duniya duk ta ishe ta. Ta gaji da matsalar mahaifiyarta da y'an uwanta. K'arisawa tayi wajen Baba duk da jirin da take ji domin taimaka masa ya tashi. Rik'e mata hannu yayi tare da fad'in, "Bari zan iya tashi Saratu. Kema naji jikin naki da zafi sosai. Ya aka yi Aina'u ta rigaki dawowa daga asibitin, ko fad'a kuka yi?" Sai da ta taimaka masa ya mik'e tukun sannan tace, "A'a ba fad'a muka yi ba, nice na baro ta a can asibitin." Baba bai k'ara cewa komai ba sai nufa wajen pamfo da yayi ya wanke goshinsa sannan ya nufi kan baranda ya zauna a kan tabarma tare da fad'in, "Saratu, kiyi hak'uri duk laifi nane da na kasa zab'a maku uwa ta gari. Y'an uwana sun nuna basu son na auri Elizabeth (Lami) amma na nace ni ita nake so sabida yanda ta nuna min k'auna a wancen lokacin. Ban tab'a d'auka Elizabeth za tayi min butulci a rayuwata ba." Kallonsa Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ka bani labari, ta yaya ka had'u da Lami har kuka yi aure, kuma mai yasa danginka suke fushi da kai har yanzu? Bamu san kowa naka ba, haka suma basu san mu ba. Dangin Lami ma babu wanda ya san mu, muna bamu san kowa ba sai aunty Rose Merry wanda Lami tace mana y'ar uwarta ce." Sunkuyar da kai Baba yayi tare da fad'in, "Rose Merry ba y'ar uwar mahaifiyarku bace, asali ma itace mai d'aura mahaifiyarku akan turba mara kyau. Taso mahaifiyarku ta koma addininta da ta baro, amma kuma sai mahaifiyarku ta nuna ita tana son addinin musuluncin da ta karb'a." Sarah tace, "To amma Baba Lami bata sallah, bata azumi, duk wani abu na musulunci Lami bata yi. Kuma a hakan ne take cewa tana son musuluncin?" Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "Nima na jima ina wannan zargin Saratu. Anya kuwa mahaifiyarku bata koma addinin kiristancinta ba kuwa? Domin duk ranar lahadi da sassafe take barin gidan nan, kuma bata dawowa Sia wajajen d'aya ko biyu." Shuru Sarah tayi tana tuno wata rana da mahaifiyar tasu ta dawo daga inda take zuwa duk ranar lahadi, sai ta ganta d'aure da wani zani mai hoton k'atoton cross a jiki, zanin biyu ne, da ta d'aura d'aya a k'ugu, sai ta d'aura wani a sama kasancewar dama farar rigar less ce a jikinta. Ga wani k'aramin Bible a kan gado. "Lami! Wannan wani irin kaya ne haka a jikinki irin na y'an coci?" Saurin kallon jikinta Lami tayi tare da fad'in, "Kai, kin ganni nan d'azu da na fita, shine wata mota tayo kaina, garin na kauce mata sai na fad'a cikin kwata, kuma dama kusa nake da gidan auntynku Rose Merry, shine ta bani wad'annan kayan na saka. Yanzu ma Allah-Allah nake in cire su." Sarah ta kalli Bible d'in tare da fad'in, "Wannan kuma fa Lami!" A harzuk'e tace, "Ke dan ubanki uwata ce ke? Kin cika ni da tsinannun tambayarki. To Rose Merry d'in ce ta bani na ajiye mata a nan anjima idan zata wuce gida zata biyo tanan ta karb'a." Kallonta Baba yayi tare da fad'in, "Lafiya Saratu kike dogon tunani haka?" Sauke ajiyar zuciya Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ina tuna wani abu ne. Ina ji a jikina Lami ta koma addinin kiristanci." Daga nan ta kwashe duk labarin abunda ya faru wancen ranar ta fad'a masa. Da mugun mamaki Baba ke kallon Sarah, sai kuma ya girgiza kai tare da fad'in, "Babu abunda Lami ba zata iya aikatawa ba. Lami ta daina bani mamaki sai dai tsoro. "Baba mai ya same ka a goshin ka?" Fad'in Sarah ganin har goshin ya tasa. Sai da ya shafa wajen sannan yace, "Lami ce taje jifan y'an uwan saurayinki da suka yi cincirundo domin d'aukar fansar abunda suka yi shine ta same ni a goshi, kuma kin san budar ba ta roba bace. Don ma Allah ya tsare." Cike da tausayi Sarah yace, "Allah ya k'ara tsareka Baba." Da ameen ya amsa tare da kallonta yace, "To Sarah ya ake ciki? Mai likitocin suka ce wannan karon?" Fad'in Baba yana kallon Sarah data sunkuyar da kai tana hawaye. "Baba akwai cikin?" Sai da gaban Baba ya fad'i da jin haka, amma ya d'aure tare da fad'in, "Kuma Saratu har yanzu baki gano bakin zaren ba?" Shuru Sarah tayi don bata san ta inda zata fara yiwa Baba bayani ba. Hawaye ne kawai ke zubowa daga idanunta yana d'iga a kan tabarmar da suke kai. "Saratu ni mahaifinki ne. Kuma kin san duk fad'in gidan nan babu wanda na shak'u kuma nake jinsa har cikin raina cikin y'ay'ana idan ba ke ba. Kar ki damu, zan fahimceki. Zan kuma yi maki nasiha matsayina na mahaifinki kuma in karb'i k'addararki da hannu bibbiyu. Sai dai ba zan tab'a jin dad'i ba idan har ke da kanki kika kai kanki wajen wani namijin bayan kin yi mi alk'awarin baza ki tab'a yin irin rayuwar da y'an uwanki suke yi ba." Kuka Sarah ta fashe dashi tare da fad'in, "Na rantse da girman ubangijin halittu ban tab'a kaiwa wani namijin jikina ba domin yayi amfani dani. Wallahi, tallahi duk abunda ya faru tsausayi ne Baba. Ban san ta yanda zanyi maka bayani ba Baba. Amma wallahi ban tab'a karya maka alk'awarin da ba d'auka ba." Ko kamun Baba yayi wata maganar wani yaro ya kwad'o sallama tare

Please Login or Register in order to submit comment