Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kar kuce ban faɗa muku ba ku tashi kuban waje " tashi sukai kowacce ta yi ɗakinta tana saƙe-saƙenta, suna shiga ya kalli Mommy ya ce " Maryam karki sake faɗin irin wannan abun ga ƴarki bai daceba " ok yallaɓai ta ce sannan ya ce " Allah ya kyauta " ta ce " Ameen "......





Tunda ta shiga ɗaki take kuka meyasa su Daddy baza su gane mai take nufiba?, meyasa suke tunanin zata yiwa Saima baƙin ciki?, meyasa suka gaza saurararta ?, wannan sune tambayoyin da takewa kanta amma babu mai bata amsa hakan yasa ta tashi ta shiga banɗaki tayi wanka ta shirya ta kwanta...





Ɓangaren Saima ma haka ta kasance tunani take meyasa Samha take haka?, me nai mata takemin baƙin ciki bayan da ba halinta bane, duk ta ruɗe tana cikin wannan tunanin Yazeed ya kirata ta ɗaga suka hau hirar soyyaya sai taji ta manta da wata Samha ma....





Tun wannan ranar Samha bata sake yiwa kowa magana ba hasalima ko parlour bata fitowa kullum tana cikin ɗaki ita kaɗai, yau ma kamar kullum tana zaune akai sallama ta ɗaga ido taga Saima ta jingina da ƙofa ta sauke idonta ƙarasowa ta yi ta zaune gefen gadon ta ce " Twinny meyasa kika canza lokaci ɗaya?, meyasa bakison na auri Yazeed?, meyasa kika guji mu'amula da kowa a cikin gidan nan?, why twinny?, why?" kallonta ta yi amma ba tace komai ba hakan yasa ta ce " meyasa kike ignoring magana dani tun waccan ranar, wallahi banjin daɗi " murmushin takaici Samha ta yi sannan ta ce " babu komai kawai naga ya kamata nabaki dama kiyi rayuwarki karna takura miki nai miki baƙin ciki, idan na ɓata miki rai kiyi haƙuri dan Allah Saima Allah ya zaunar dake lafiya a gidan mijinki " kallonta kawai tayi sai kuma ta ce " Daddy ya ce ki shirya anjima zamu tafi " ok ta ce sannan ta tashi ta shiga banɗaki, girgiza kai Saima ta yi sannan ta yi waje.....






Fitowa ta yi cikin wata abaya peach colour tayi rolling round face ɗinta ta fito tayi kyau kamar ka ɗauka ka gudu, kallonta Daddy ya yi ya ce " Samha komai za'ayi sai kinsa anmakara ko ?" cikin ladabi ta ce " i'm sorry Dad " murmushi ya yi ya ce " Allah ya shiryeki " sannan ya yi gaba, kowacce tafiyarta take daban saɓaninda da zasu riƙe hannun juna su tafi suna nishaɗi....






Kusan ƙarfe takwas na dare suka sauka a garin Ethopia wasu motocine na alharma sukazo kusan goma murmushi Daddy ya yi sannan ya ƙarasa kusada wata ash ɗin mota, wani kyakyawan matashi ne ya fito daga cikin motar kana ganinsa kaga asalin ajebo irin takeaway ɗin nan cikin ladabi ya sunkuya ya faɗa " welcome uncle ya hanya " murmushi Daddy ya yi ya ce " lafiya lao Haidar ya kuke ?" murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce " muna nan klao Alhamdulillah, sweet Mommy ina wuni ya hanya " dariya ta yi sannan ta ce " wato sai yanzu ka tuna dani babu komai nasan Ayaan shine mutumina " shafa kansa ya yi ya ce " i'm sorry sweet mommy ban ƙarawa " ok na yafema" thank you ya faɗa.Kallonsu Daddy ya yi ya ce " baku iya gaisuwa ba ?" Saima ce ta ce " ina wuni " cikin sakin fuska ya ce " lafiya lao Saima ya Nigeria da karatu " ganin ya yi mata magana friendly saɓanin yanda yakewa kowa magana yasa ta washe baki ta ce " wallahi lafiya lao Alhamdulillah, ya Azaad da Mommy'n sa ?" suna nan lao ya amsa mata, kallon Samha Daddy ya yi ganin batada niyyar gaidashi yasa ya ce " Samha banji kin gaida yayanki ba?" kwaɓe fuska ta yi ganin irin kallon da Daddy yake mata yasa ta ce " ina kwana " batareda ya kalleta ba ya ce " lafiya "sannan ya ce " Daddy mu tafi muna ɓata lokaci " ok Daddy ya ce sannan sukai gaba. Da Daddy da Mommy suka shiga mota ɗaya da Haidar da Saima suka shiga wata motar, Samha kuwa wata motar ta shiga daban dukda akwai ragowar waje acikin tasu motar Saima ce ta kalleta shikuwa yanda kasan baisan da ita awajenba haka ya nuna, ahaka suka tafi gidansu......





Duk wasu Family na kusa dana nesa sunzo dan tarbarsu, banda murna babu abinda family ɗin keyi, kakarsu wato Fatima wacce suke kirada Mama ta ce " kuje kuyi wanka ku huta sai kuzo ayi dinner ku kwanta tunda dare ya yi " ok sukace sannan aka kai kowa ɗakinsa, bayan sun shirya kowa da kowa yazauna a babban dinning area ɗin gidan sai hira ake banda Samha wacce tun zamanta batace komai ba abincinma da kyar take ci, lura da hakan yasa Yaseer wato mahaifin Haidar wanda ya kasance wane ga Daddy uwa ɗaya uba ɗaya ya kalli Samha ya ce " ƴar biyu meyasa kikai shiru ko har yanzu baki daina miskilanci ba? " kallonsa ta yi ta sunkuyar da kanta, girgiza kai Mama ta yi ta ce " Ke kam kina fama da wannan jarabar taki yarinya kamar wacce aljanu ke shafa kwata-kwata batason mutane anya kana mata addu'a kuwa Ahmad?" murmushi ya yi ya ce " wallahi Mama munayi saidai gyaran Allah lamarinta " to Allah ya sawwaƙe miki kuwa " turo baki ta yi ta tashi tabar wajen tanason zuwa wajensu amma wannan maganar ta tsana..





Wata kyakyawar macace ta shigo wacce aƙalla bazata wuce shekara 23-24 ɗinnan hannunta riƙeda wani kyakyawan yaro wanda baifi three years ba, da murmushi a fuskanta ta gaisheda su Daddy Saima ta ce " Aunty Zaheera yaushe rabo? Ina Azaad ɗin namu ?" murmushi Zaheera ta yi ta ce " wallahi kam kwana da yawa, kin ganshi" ta faɗa tana miƙa mata shi kallonsa Saima ta yi ta ce " wow kasan yaya wallahi kamarku ɗaya dashi " murmushi Haidar ya yi ya ce " ay har nagaji da wannan maganar to ba dole ɗa ya yi kamada ubansa ba " dariya kowa na ɗakin ya yi sannan suka cigaba da cin abincinsu..





Wajejen ƙarfe biyu na dare jikinta ya fara yimata ciwo tun tana daurewa harta fashe da kuka saboda tsananin azabar da takeji gashi babu kowa a kusada ita haka ta ƙaraci ciwonta har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba sannan abun ya lafa mata hakan yasa da kyar ta samu tayi sallah sannan ta kwanta saboda matsanancin baccin da takeji..






Kowa da kowa na gidan ya hallara donyin breakfast Haidar ne ya fito hannunsa riƙe da Azaad za'a kaishi makara nta kallonsa Mama ta yi ta ce " yau naga jaraba kabar yaro ya huta acikin ƴan'uwansa kace sai ya tafi makaranta " murmushi ya yi ya ce " Mama kenan wallahi kin fiye rikici banda abinki ba yanzu zai dawo daga school ɗin nagadai ba yau su uncle ɗin zasu tafi ba " banza tai masa ta cigaba da cin abincinta ya ƙaraso cikin ladabi ya ce " Mami , uncle's, Mommy good morning " murmushi ɗauke a fuskarsu suka amsa masa Saima ta kalleshi ta ce " good morning yaya " murmushi ya yi mata ya ce " how was your night ?" fine ta faɗa, Daddy ne ya kalli Azaad ya ce " babanmu sai makaranta " dariya ɗan ƙaramin yaron ya yi ya ce " granny kacema Abu ya barni anan banason school ɗin please " murmushi Daddy ya yi kana ya ɗorashi akan cinyarshi ya ce " karka damu babu inda zaka muna nan tare anjima muje yawo " dariya ya yi yayiwa Daddy kiss a kumatu sannan ya ce " yawwa granny shiyasa nake sonka please idan zaka koma Naija zan biku " ok Daddy ya ce sannan ya fara bashi abinci, Zaheera ce ta fito tasha wata black ɗin abaya ta gaishesu sannan ta zauna dan yin breakfast. Uncle Yaseer ne ya ce " wai ina Samha ne bata fitoba?" cikin ɓacin rai Mommy ta ce " wallahi lamarin Samha ya isheni i don't know what wrong wiz her kullum cikin ignoring mutane take " Mama ce ta ce " gaskiya yarinyar nan ba lafiya ba " Saima ce ta tashi ta ce " bari naje na dubata " ok suka cemata sannan tai gaba ...






Tana shiga ɗakin ta sameta zaune gefen gado ta yi tagumi dan batasan ma tashigo ba, dafata ta yi ta ce " Samha what are you thinking ?" kallonta ta yi ta ce " mefa ?" kizo Daddy na kiranki, ok ta ce sannan ta tashi suka fito...




Sanye takeda riga da wando amma ba matstsuba ta tufke gashinta ya sakko har gadon bayanta sukayi sallama suka shigo, kallo kowa ya bita dashi banda Haidar wanda tun tana shigowa ya yi mata kallo ɗaya ƙarasowa ta yi ta ce " good morning everyone " "morning " suma suka amsa mata, wajen Daddy ta ƙarasa ta ce " Daddy gani " kallonta ya yi ganin yanda ta rame ya ce " Samha what wrong with you ?, meyasa bakya zama cikin ƴan'uwanki ?" ƙasa tayi da kanta bata bashi amsaba ganin haka yasa ya ce " zauna " zama ta yi tana kallonsa ya ɗebo abincin ya miƙa mata, babu musu ta buɗe bakinta ya fara feeding ɗinta domin Allah ya sani yana jin Samha sosai acikin zuciyarsa bayaso wani abun ya sameta kokaɗan saida kawai ya basar. Bayan sungama breakfast ɗinne uncle Yaseer ya ce kowa ya shirya zasu fita, kowa yagama fitowa banda ƴan mazan gidan wanda Haidar ne daman kawai yake ƙasar yakuma fita kallon kowa uncle ya yi sannan ya ce "ina Mamana ?" Mami ce ta ce " let me check her " sannan ta koma cikin gidan dan jin meya hanata fitowa. Kwance ta sameta ta ƙarasa ta yaye duvet ɗin jikinta ta ce " daughter meyasa baki shirya ba ?" da kyar ta ce " Mami i'm not feeling fine " taɓa jikinta ta yi ta ce " subhanal-lahi meyasa baki faɗaba har yayanki ya fita ? " bakinta na rawa ta ce " sai yanzu ya kamani " taimaka mata tayi ta tashi sannan ta ce " bari nakira Son ya kaiki asibiti " tafita takirashi bayan ta faɗa masa ya ce asa driver yakawota asibitin. Fitowa tayi da ita da mamaki uncle ya ce " lafiya ?" jawota tayi saboda yanda jikinta ke shivering ta ce " wallahi batajin daɗi amma nakira Aliyu yanzu driver zai kaita asibiti yana can " kallonta ya yi ya ce " sannu Mamana " kasa amsawa ta yi sai kanta data ɗaga masa Daddy ne ya ce " bari muje nakaita asibitin " murmushi Mami ta yi ta ce " no basai kajeba ai Aliyu na gurinta kawai mu mutafi " ok ya ce Saima ta ce da damuwa " Daddy muje na rakata asibitin " girgiza kai ya yi ya ce " no need mutafi kawai " badan ranta yasoba ta haƙura aka sakata amota suka tafi sannan suma suka kama hanya.....






A harabar asibitin wanda ya kasance mallakinsa ne sukayi parking ya tura nurses suka kawo masa ita kallonta yayi ganin yanda jikinta ya yi weak yasa ya ce rai ahaɗe kamar bai taɓa dariya ba " meyasa tun ɗazu bakice bakida lafiya ba ?" shuru ta yi masa kusan two yasa ya ce " keee! Badake nake magana ba" fashewa ta yi da kuka lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa hakan yasa ya ƙaraso inda ta ke ya ce " rufemin baki kona kwaɗa miki mari waza kiyiwa shagwaɓa " turo baki tayi ta ce " ni wallahi babu ruwana dakai ka maidani gida kuma saina faɗawa Mami Allah " ta ƙasara maganar tana sakin wani sabon kukan " kallonta ya yi ganin yanda take kuka kamar wata Baby ya ce " who stop you kije ki faɗa mana kuma dama ni nakawo ki asibitin nan?" shuru tayi masa yatashi ya fita daga ɗakin not too long ya dawo hannunsa riƙeda injection ya ce " tashi tsaye " kallon abinda yake hannunsa ta yi ta fashe da kuka ta ce " dan Allah Abu Azaad kada kayimin allura wallahi bana so " tamke fuska ya yi dukda dariyar data bashi ya ce " ni sa'an wasanki ne ?, i'm play with you ?" girgiza masa kai tayi ya ce " ohyaa ɗauke hannunki ko ki daku " ganin da gaske bazata tsaya ta daɗin raiba yasa ya ce " shikenan na fasai miki tafi ki kwanta " gogen hawayenta ta yi ta ce " thank you " sannan ta huce gefensa har yanajin hucin jikinta saboda yadda temperature ɗinta tayi high. Bayan ta kwanta kusan two minutes sannan yazo gefenta ya zauna a hankali ya yi ƙasa da trouser ɗin jikinta batareda ta sani ba, cikin dabara ya saita allurar ajikinta batayi auneba taji ya tsira mata wata azabbabiyar ƙara ta saki tana kuka murmushi ya yi ganin ta tashi yasa ya rungumeta ya ce " sorry kinji ban ƙarawa kiyi bacci " kuka ta hauyi cikin two minutes kuma allurar ta fara aiki ajikinta nan da nan bacci ya ɗauketa, saida ya tabbatar baccin ya yi nisa ya ɗagata dan kwantar da ita yaji ta riƙeshi cikin magagin bacci ta ce " Abu kabarni anan " murmushi ya yi sannan ya komar da ita ƙirjinsa yana shafa kanta yana kallon cute face ɗinta shikaɗai ya saki wani smile har saida beauty point ɗinsa suka loma ya ce " rigimammiyata "










Comments, like nd share.








Written by:
*Nanameera*








Meera Love's you 💋💋💋💋💋[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj

💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.




Page Four.



Wajejen bayan sallar isha'i suka shigo gidan bayan ya yi parking ya kalleta rai ahaɗe ya ce " sauka " babu musu ta sauka ya ce " keee !!" juyowa ta yi ya kalleta ya ce " wane zai ɗaukar miki maganin ?" turo baki ta yi sannan ta ɗauki ledar maganin ta yi gaba..




Tana shiga shima ya yi sallama ya shigo kallonsu Mama ta yi ta ce " sai yanzu " zama ya yi ya ce " wallahi kuma nagaji " sannunku Mama ta faɗa, da gudu yazo ya rungumeshi ya ce " welcome Abbu " kiss ya mishi a kumatu ya ce " thank you Son " Mami ce tafito ta ce " au daughter zonan kici abinci " tashi ta yi ta ƙasara wajen Mamin ta zaune aƙasan kujera shafa kanta ta yi ta ce " ya jikin naki?" da sauki ta amsa mata daidai nan Saima ta fito daga kitchen da sauri tazo ta dafata ta ce " twinny ya jikin naki?" kallonta ta yi ta ce " dasauki Alhamdulillah " murmushi ta yi ta ce " wai Mama bakiga takwararki bane ?" cikin masifa Mama ta ce " to sallamammiya ita data shigo ta kulani ne?, ko saboda ni nafi kowa barbaɗa saina hau kulata " dariya kowa yake yi hakan ya ƙara tunzurata ta ce " A'a nifa ba mahaukaciya bace da zaku dinga yimin dariya " little Azaad ne ya kalleta ya ce " ke granny kin iya comedy wallahi " mitsi-mitsi ta yi da ido ta ce " kai karkaga ina cemaka mijina wallahi ranka ne zai ɓaci dan ko ubanka bai isaba bare kuma kai " ɗagowa Haidar ya yi ya ce "gaskiya Mama babu ruwana a wannan zance karki sako dani kije can ki ƙaraci rikicin tsufanki " ta buɗe baki zatayi magana kenan Daddy da uncle suka shigo sai wasu maza biyu a bayansu waɗanda bazasu huce shekaru 30 ba tana ganinsu ta fashe da kuka da mamaki Daddy ya ce " Mama lafiya kedawa ?" cikin shasheƙa ta ce " yanzu ace kamar ni Aliyu ya zauna yana zagi shida wannan ɗan nasa " da mamaki Daddy ya ce " Aliyu kuma shi Aliyun?" baki buɗe kowa na parlour'n yake kallonta sanin halinta yasa uncle ya ce " Aliyu koda wasa karka sake shiga har karta ka riga kasan halinta yanzu sai addu'a " girgiza kai ya yi ya ce " ni bansan meyasa takeson yimin sharri ba wallahi agaban kowanefa ko yaushe na zageta bansani ba " murmushi Saima ta yi ta ce " sai haƙuri yaya " tsaki yayi ya ce "shiyasa fa bana shiga harkarta kwata-kwata " wata uwar dariya aka sheƙe da ita kallo ɗaya ya yi masa ya ce " wai dan Allah Ayaan yaushe zakayi hankali?" shigowa ya yi ya ce " gobe, mutanen Naija saukar yaushe ?" ya faɗa yana kallon Samha, murmushi ta yi ta ce " wallahi tun rannan akace kana india " eh wallahi aiki ya riƙeni bansan kun zoba, ɗaga masa kai kawai tayi dan har sannan batajin daɗin jikinta kallon Saima ya yi ya ce " A'a kace harda baƙalli akazo, wai dan Allah uncle awane asibiti aka caka maka ?" haɗe rai tayi ta ce " Allah yaya Ayaan banaso kadai naimin " dariya ya yi ya ce " Allah Daddy akoma asibitin wannan ba ƴar familyn mu bace ƴarinya baƙaƙirin " yanda ta haɗe rai kamar zatayi kuka zaka kane batason yanda yake tsokanarta, daga baya Asaad ya ce " sorry rabu dashi kinji Saima ai kowa yaganki yasan ke familynmu ce kuma ai baiwace da Allah ya yoki chocolatey kinji stop worring kinji "murmushi ta yi ta ce " yawwa yaya Asaad kuma In sha Allah sai ya auri baƙar masa wacce tafini baƙi kuma ƴar talakawa " dariya ya tuntsire ya ce " lallaima yarinya ni bakisan ƴar shugaban ƙasar America zan auraba " Uncle ne ya ce " kai kutashi kubawa mutane guri sai surutu kamar kunci aku " kallonsa Mama ta yi ta ce " A'a karka matsawa jikokina kabarsu idan basuyi hiraba mai zasuyi kaji ɗa " murmushi Daddy ya yi ya ce " hajiya Mama Allah ya baki haƙuri " tashi tayi ta ce " ai gaskiyace da son samune ai su auri junansu " dariya Ayaan ya yi ya ce " tab ai kuwa wannan baƙallin zata daɗe bata sami mijiba " kallonsa Mama tayi ta ce " kaji sallamammen ɗa to in bansa ka aureta ba " tab wallahi bazai yiwu ba kawai ni tasawa agaban mota zan aura " tsaki Mama tayi ta shige ɗakinta dan ita lokacin kwanciyarta yayi.....






Daddy ne ya kalli uncle Yaseer ya ce " wai kuwa har yau yaya bai dawoba ?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce " wallahi bai dawoba yace nanda two weeks zai dawo amma ai zaku jirashi " gyara zama Daddy ya yi ya ce " ba lallai ba saboda su Samha zasu koma makaranta next week to kaga akwai buƙatar mutafi kafin sannan " Zaheera ce tashigo ta tsuguna ta gaidasu sannan ta ce " Saima inasu Mami " miƙewa ta yi ta ce " yanzu suka shiga ciki da Samha " ok tace sannan ta koma part ɗinta.....






Zaune yake yana operating laptop Zaheera ta miƙa masa kofin coffee ɗin amsa yayi ya ce " thanks " zama tayi gefensa ganin kusan ten minutes amma bai bar abinda yake ba yasa ta ce " Abu Azaad " batareda ya kalletaba ya ce "uhmm " cikin damuwa ta ce " meyasa bakason kulani ?, kwata-kwata tunda mukai aure baka shiga harkata yaushe rabonda wani abu ya haɗani dakai ?" kallonta yake tunda ta fara maganar Allah ya sani yana son kyautata mata amma kwata-kwata bashida feelings ko kaɗan ƴa mace bata gabanshi ganin yayi shuru yasa ta ce " kayi shuru " daidaita nutsuwarsa yayi sannan ya ce " Zaheera i'm sorry amma tun bayan munyi aure nima nakejin haka bansan meyasaba kiyi haƙuri idan da rabon watarana nadawo kamar da sai kiga Allah ya yayemin " goge hawayen idonta ta yi ta ce " Abu Azaad na yarda dakai domin son da nake maka yasa nayarda na aureka dukda nasan baka sona alharma kayi min " da damuwa ya ce " Zaheera banason kina irin wannan maganar amma narasa meyasa kika saka haka aranki fiyeda komai " cikin shasheƙar kuka ta ce " Abu Azaad kana sona ?" kasancewar bai iya ƙaryaba yasa ya ce " bazan miki ƙaryaba Zaheera ina ƙaunarki amma bantaɓai miki so irinna aure ba " goge hawayenta tayi ta ce " shikenan hakanma nagode sosai Abu Azaad amma dai kanason Azaad ko ?" murmushi yayi ya shafa kan yaron wanda yake bacci hankalinsa kwance ya ce " kin taɓa ganin ubanda baya son ɗansa?, inason Azaad, ina jinsa araina " murmushi ta yi ta ce " nagode sosai Abu Azaad " rufe system ɗin yayi ya jawota jikinsa ya ce " faɗamin yanzu me kike so?, kwanciya tayi aƙirjinsa ta ce " nadinga jin ɗuminka akoda yaushe shine muradina " dariya ya yi yana ƙoƙarin zame ƴar rigar baccin dake jikinta hakan yasa nayi musu saida safe najawo musu ƙofar....






Kamar jiya haka yauma jikinta ya dinga ciwo sai zufa take haɗawa lokaci ɗaya taji tanajin wata irin ƙishirwa hakan yasa ta lallaɓa ta fito dan ɗaukan ruwan batareda ta luraba ta shiga wani ɗakin wanda aka ƙawatashi da kayan more rayuwa bata kalli kowaye akwance ba taje takwanta jikinta sai rawa yake jin mutum ya danneshi yasa ya buɗe ido yana ƙarewa kyakyawar fuskanta kallo tashi yayi zaune yana kallonta dakyau mamakin abinda ya shigo da ita ɗakinsa yake , shima ji yayi ya takura awancan yasa yadawo ɗakinsa tun kan yayi aure, yanda jikinta ke rawa yasa yakai hannunsa jikinta sosai yaji temperature ɗinta tahau sosai kuma kamar tafara fita hankalinta tashi yayi ya dudduba amma bai sami magani ko injection ba hakan yasa ya ɗauketa ya direta a toilet, without second though ya fara ciremata kayan jikinta itakuwa batamasan abinda yakeyiba saida ya rage daga ita sai pant da bra sannan ya kunna musu shower wata irin zabura tayi ta shige jikinsa tanajin kamar zata waɗi sosai shima ya rungumeta tsam ajikinsa, kusan ten minutes sannan ya ɗauketa kamar ɗazu ya fito da ita towel yasa ya goge mata jikinta sai a sannan ta fara gane ina take, bayan ya gama gyarata ya rasa mezai bata tasa kasancewar babu kayan mata aɗakin, hakan yasa ya ɗauko mata armless ɗin riga da boxer ya samata sannan ya jata bakin gado shikuma ya koma banɗakin...





Some few minutes ya fito cikin sabuwar shiga zama yayi gefenta ya kalleta ya ce" me kika fito yi da daddare ?" turo baki tayi ta ce " ni ruwa zansha " tashi yayi ya fita ya kawo mata ruwan bayan ta gama sha ya ce " to tashi ki tafi " kwaɓe fuska ta yi ta ce " ni tsoro nakeji saidai ka rakani " kallonta ya yi sai kuma ya yi kwanciyarsa ya ce " saidai ki kwana anan indai ni zan rakaki " yana gama faɗa ya juya mata baya. Kallonsa ta yi ganin bashida niyyar rakata yasa ta fashe da kuka tana cewa " Abu Azaad please kazo ka rakani wallahi tsoro nakeji " yana jinta yayi mata banza har tagaji ta fara gyangyaɗi azaune can kuma saita kwanta gefen gadon yanaji ta kwanta dama yasan asalin matsoraciyace yayi wani murmushi sai kuma ya ce "mmmyywww " ai da gudu tazo ta ƙanƙameshi tana cewa " Abu Azaad mage please ka fita da ita " juyowa ya yi ya kalleta ya ce " to ina ruwana ta kama mai tsoronta " kwaɓe fuska tayi ya ce " kina yin kuka ni kuma zan kirata " turo baki tayi ta ce "ai ni ba kuka nace zanyiba " ɗauke kansa ya yi yana wani cute smile, kusan five minutes yaji saukar numfashinta alamun ta yi bacci blanket ya ja musu kana yayi musu addu'a bacci ya ɗaukeshi.......





Bugun ƙofar da akeyi yasashi ya farka sosai yayi mamakin lokaci dan tun bayan sallar

Please Login or Register in order to submit comment