Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya ta kusa, zan kiraki anjima " ok ta ce sannan ta kashe wayar ta hau shiryawa...






Zaune suke a restaurant amma kwata-kwata takasa cin abincin ganin yanayinta yasa Aleeya ta ce " wai Saima me akai miki naga ranki a ɓace?" tsaki ta yi ta ce " wallahi sai naiwa Samha rashin mutunci dan wallahi abinda takemin ya isheni akan Yazeed saidai mu yanke zumuncin dake *TSAKANINMU* dan saboda ita bazan rabuda Yazeed ba idanma baƙin ciki takemin saidai ta mutu amma wallahi saina aureshi " dariya Aleeya ta yi ta ce " Ai sanda nake faɗa miki baki saurareniba kina ganin kamar inaso ne na haɗaki da ƴar uwarki wallahi ko kaffara bazan miki Samha baƙin ciki take miki bataso taga kin auri wanda zaki huta shine kawai damuwarta " shuru ta yi nawasu mintuna sannan ta ce " ai kuwa taci ƙarya ta kwana da yunwa kuma bari nakoma gidan wallahi yau saidai ayita ta ƙare dan nagaji akan Yazeed babu abinda bazan aikata ba" wai ke har saikin bari ankoma gida?, ay yanzu ya kamata kije kisameta kiyi mata tijara agaban kowa wallahi bazata ƙaraba " Allah ko? Saima ta tambaya, tsaki ta yi ta ce " to zauna ni nafi zarginma so take ita ta auri Yazeed ɗin shiyasa take waɗannan abubuwan gwanda kije yanzu ki taka mata birki " tashi ta yi ta ce " zo mutafi wallahi yau saidai na yanke alaƙar dake *TSAKANINMU* dan saina sauke mata buhun rashin mutunci idan har tana tunanin zata auri Yazeed ne " kama hannunta ta yi sukai waje......








Comments, like and share.






Written by
*Nanameera*










```Meera Love's yhu```🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj

💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.




🅿️......0️⃣8️⃣...





____________Ahanya suka haɗu da Yazeed wanda daman wajenta zashi ganin yanayinta yasa ya ce " baby what's wrong?" kallonsa ta yi ta ce " please muje ka rakani " ok ya ce sannan sukayi gaba.....






Tsaye take itada Sir Sapwan suna taɓa hira Saima ta ƙaraso da tawagarta da murmushi Sapwan ya ce " A'a ƴar biyu ce anan ko kinzo sada zumunci ne?" wani kallo ta yi masa ta ce " A'a nazo yanke zumunci ne" bai fahimci inda ta dosaba ta kalli Samha ta ce " inason magana dake idan da hali" da mamaki ta ce " idan maganar sirrice kibari sai mun koma gida mana" zatayi magana Aleeya ta jata gefe ta raɗa mata wani abu sai kuma suka dawo tana huci ta ce " daman warning nakeso nayi miki saboda na fuskanci baƙin ciki kike yimin da kuma hassada saboda na sami mijin aure wanda yafi naki komai da komai, to wallahi tun muna mu biyu dake ki fita harkar saurayina bance dole sai kin kulashiba, kuma bance karki yimin hassada ba amma inason ki ɓoye abinki dan wallahi ni Saima zan iya yimiki kowanne irin rashin mutunci akan wanda zan aura, zan iya raba alaƙar dake *TSAKANINMU* rabawa ta har abada saboda haka behave your self " sosai mutane aka taru ganin yanda take zazzaga mata bala'i kamar wata uwarta, Samha kuwa hawaye ne ke zuba daga idanunta tana ganin abun kamar a mafarki wai yau ita Saima ke faɗawa irin waɗannan maganganun a cikin mutane kuma a makaranta, cikin rashin jin daɗi abinda tayi Aysha ta ce " haba Saima wannan wane irin wasane a cikin mutane ai bai kamata ba wani ay saiya ɗauka gaske ne" cikin masifa ta ce " dallah malama rufemin baki banza kawai duk kece kika ɓatata da wannan muguwar ɗabi'ar ace wai ɗan uwanka na jini zakayiwa hassada wallahi kiji tsoron Allah kuma....... Cikin daka tsawa ta ce " ya'isa Saima enough!!enough Saima babu ruwan Aysha a cikin wannan maganar ba tada laifi ko kaɗan amma dan Allah idan wasa kikemin stop it twinny wallahi zuciyata bazata iya ɗauka ba kinji stop it please" wani tsaki Saima tayi ta ce " nasani Samha kin iya pretending you are so good at it amma ni nafi ƙarfin kiyimin wallahi idanma zaki goge munafukan hawayenki ki goge dan ni baza su ƙaramin komai ba " goge idanunta tayi ta ce " shikenan Saima babu komai tunda har kinga kin zaɓi saurayi akan ƴar uwarki to babu komai amman kisani watarana sai kinyi danasani a rayuwarki alokacin da danasanin bazai amfana miki komai ba, tunda har kin yarda saurayi da ƙawa su shiga *TSAKANINMU* shikenan babu damuwa ina yimiki fatan alkhairi kuma ina yimiki addu'ar Allah ya baki ikon cinye jarrabawarki dan nasan ƙarshe baza'a wanye da kyau ba" ta kalli Yazeed ta ce " kai kuma kaji tsoron Allah ka sani idan ka cutarda ƴar uwata wallahi kaima sai anwa taka saboda alhaki kuikuwone " tsaki Saima ta yi sannan ta nunata da yatsa ta ce " babu ruwanki dashi kinji, kiyi harkarki nayi tawa please idan kuma baki jiba to wallahi nadinga tozartaki agaban mutane kenan " tana gama faɗin haka tayi gaba suna binta abaya......





Girgiza kai Sapwan ya yi ya juyo da niyyar ya yiwa Samha magana yaga ta tafi luuuu zata faɗi yayi sauri ya riƙeta ganin har ta sume saboda tashin hankali.....





Zaune yake gefen gadon sai Aysha akan kujera suna kallonta bayan ansamata drip da allurai ta samu tayi bacci, ganin har kusan 5pm yasa ya ce " Aysha ko zaki tafi gida kar dare yayi miki " girgiza kai tayi ta ce " bazan iya tafiya nabarta acikin wannan halinba sai ta farfaɗo tukunna " ok ya ce sannan ya cigaba da danna wayarsa....





Tun dawowarsa daga makaranta yake zaune agidan babu kowa makarantarma school bos ce ta kawoshi buɗe ƙofar da akayi yasa ya tashi da gudu cikin murna yake cewa "oyoyo Aunty Samha " shigowa tayi ganin ba ita bace yasa ya ce " Aunty Saima ina Auntyna?" wata uwar harara ta zabgamai ta ce " tana gidan uwarka" tana faɗin hakan ta tureshi tayi ɗakinta, fashewa ya yi da kuka ya koma kan kujera ya zauna yanata rera kukansa har bacci yayi gaba dashi.......





Sai gab da magriba sannan aka sallameta bayan an bata magunguna, saida suka fara ajiye Aysha a gida sannan ya wuce kaita, ana kiraye-kirayen sallar magriba suka shigo Nassarawa bayan ya yi parking ya kalleta ya ce " Samha please karki saka damuwa aranki, ki maida komai ba komai ba na tabbata Saima zugata akayi to ke kiyi ƙoƙari ki danne zuciyarki kodan lafiyarki, ita kuma Allah ya ganar da ita gaskiya kinji " murmushi ta yi ta ce " nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi insha Allah zanyi yanda kace sai anjima" ok yace sannan ta sauka saida yaga ta shiga gidansu sannan ya bar layin...



Tana shiga gidansu taga alamun babu kowa agidan saboda babu motar Daddy ko Mommy,tana shiga parlour'n ta tadda little Azaad kwance akan kujera ya takure jikinsa ƙarasawa tayi kusada shi, sosai tayi mamakin ganin ko uniform ba'a cire masaba ɗaukansa tayi ta wuce ɗakinta dashi ta kwantar dashi kan gado sannan ta fara cire masa kayan.Buɗe ido ya yi ya kalleta sai kuma ya tashi zaune ya ce " Aunty Samha ki maidani wajen Abbuna please " da mamaki ta ce " meyasa Love?, ka gaji da zama damune?" murza idonsa ya yi ya ce " toba Aunty Saima bace ta yimin tsawa kuma ta tureni na waɗi saboda na tambayeta kina ina" sosai ranta ya yi matuƙar ɓaci ta tashi ta ɗaukesa suka fito parlour....




Zaune ta sameta tana danna waya tana cin cake tana zuwa ta kalleta ta ce " Saima abun ya isheni haka kada kiga ina yi miki shuru ki ɗauka ina tsoronki ne, wallahi zan ɓata miki rai fiyeda yadda kike tunani, zan iya rabuwa dake kiyi mini duk irin abunda kikaga dama amma wallahi akan Azaad sai nayi miki abunda baki taɓa zato ba, akan Azaad zan iya yanke alaƙar dake *TSAKANINMU* yankewa ta har abada, tun wuri ki shiga taitayinki malama dani kike faɗanki kaga ki sake including ɗinsa a ciki " ajiye plate ɗin hannunta ta yi ta miƙe cikin faɗa dakuma tsiwa take cewa " idan kin fasa baki ƙaunar Allah da Annabi ko anfada miki ina tsoronki ne?, ki yanke alaƙar dake *tsakaninmu* kiga idan bazan rayu ba ni daman tun asali ba hanyar mu ɗayaba saboda ni ba yar iska bace mai kwana ɗakin mijin wata bana yaudara da saɓan Allah naga......wani wawan mari ta ɗauketa dashi ji kake tasss daidai lokacin su Daddy suka shigo atareda cikin tsantsar baƙin ciki idanunta har ruwa yake ta ce " ke kin isa wallahi kinyi kaɗan kice zaki haɗamin irin wannan maganar, kuma kinsan ko goma ta zube tafi biyar albarka har gobe nice asaman ki kinsan da wannan wallahi idan bakiyi wasaba saina hanaki kwanciyar hankali acikin gidannan" da mamaki iyayen suka kallonsu Mommy tayi ƙarfin halin cewa " wai mene ya faru dakune?" cikin ladabi Samha ta basu labarin komai amma ko kaɗan batayi tunanin faɗa musu abinda tayi mata amakaranta cikin ɓacin rai Daddy ya ce " Saima kwata-kwata baki kyautaba ko kaɗan mene laifin Azaad?, yarone ƙarami bai kamata ace kina treating nashi hakaba ke idan akayiwa ɗanki zakiji daɗi, to wallahi duk randa na sake jin kinyi irin wannan abun idan ranki ya yi duba sai ya baci, ku tashi kuban waje" tashi sukayi kowa tayi hanyar ɗakinta...




Tana shiga ta zauna gefen gado Azaad na gefenta lokaci ɗaya ta fashe da kuka ita kaɗai tasan baƙin cikin datake ciki ganin yanda take kuka yasa ya dawo kan cinyarta ya zauna yana share mata hawayen fuskanta ya ce " Auntyna please ki daina kuka banso kinji dan Allah kiyi shuru idan ba haka ba nima zanyi kukan" ganin da gaske kukan zaiyi yasa tayi masa murmushi ta ce " shikenan nayi shuru Love, tashi muje nayi maka wanka" tashi ya yi tashiga dashi banɗakin dan yi masa wanka.........






Bayan ta shiryashi ta kunna masa game a wayarta ta ce " ka zauna kayi game karkayi bacci kaji " ɗaga mata kai ya yi sannan ta shiga kitchen dan dafamasa abinci....





Bayan sun gama ci suna zaune sun lulluɓa cikin bargo ya ce " Aunty Samha please kiramin Abbuna mu gaisa kinji " murmushi ta yi ta ce " ayyah kabari idan Allah ya kaimu gobe saina kira makashi please " kwaɓe fuska ya yi yana taɓe baki hakan yasa ta ce " A'a Allah ya baka haƙuri bari na kirawo maka shi " murmushi ya yi ya ce " thank you so much " girgiza kai ta yi sannan ta yi dialing number sa kusan two ringing sannan ya ɗauka yana ɗagawa ta saka masa a kunnensa cikin jindaɗi haɗi da murna ya ce "Abbunaaaaa" dariya Abu Azaad ya yi ya ce "






Comments, like and share..







```Written by```
*Nanameera*






Meera Love's yhu 🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[1/31, 19:58] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj

🌹*TSAKANINMU*🌹

*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



_Hadaka palace_


Page.9&10...




__________Murmushi ya yi yana kwanciya jikin kujerar office ɗinsa ya ce " na'am Love ya kake, yasu Daddy da mommy?" yana wangale baki ya ce "Abbu suna lafiya yaushe zaka zo?" murmushi ya yi ya ce " daga tafiyarka har zaka fara cewa yaushe zanzo, ko ka gaji da Nigeria ne?, nazo na tafi dakai Umminka kullum cikin zancenka take " girgiza kai ya yi ya ce " A'a nafison nan, nafison wajen Aunty Samha, Abbu kasan me Aunty Samha take min? " ya ce "A'a " yana kallon fuskanta ya ce " tana yimin wanka ta bani kayan daɗi harda ice-cream sannan ta bani wayarta nayi game kuma bata kwacewa wallahi Abbu ina sonta" dariya Aliyu ya yi ya ce "yaro ɗan gidan Auntynshi kace kafisonta damu?, tunda abun hakane next month zanzo na tafi dakai naga yanda zakai " turo baki ya yi ya ce " ni dai A'a ko kazo bazan bikaba Allah " murmushi ya yi ya ce"kwantar da hankalinka Love bazanma zoba Allah ya ƙara soyayya" Ameen ya ce sannan sukai sallama....




Washe gari bayan sungama shiryawa sunfito ta tsaya tana jiran Saima har kusan 10mins bata fitoba hakan yasa ta shiga ɗakinta amma ga mamakinta sai taga bata ciki bayan ta fitowa ta kira maid ɗinsu ta ce " dan Allah bakiga Saima ba?" cikin girmamawa ta ce " ai hajiya tun ɗazu naga anzo an ɗauketa na zatama yau bazaki bane " da mamaki ta ce " anzo anɗauke kuma?" ɗaga mata kai ta yi ta ce "anyway sai mundawo" Allah ya tsare ta faɗa ta kama hannun Azaad sukai waje......





Bayan ta saukeshi a makaranta ta huce ta ta makaranta tana shiga ta tararda Sapwan wanda zuwansa kenan, yana murmushinsa mai kyau ya ƙaraso kusada ita ya ce " morning sweetheart " ta ce " morning" ganin yanayinta yasa ya ce " what's wrong ko Saiman ce?" murmushin yaƙe tayi ta ce " babu komai kawai dai banajin daɗine " ya ce " Ayyah sannu ko jikin naki ne?, ay da kinsani baki fitoba kinyi zamanki" suna tafiya ta ce " no banason zama agida ni kaɗai kowa bayanan gwanda nazo makarantar " yana murmushi ya ce " tooh yanzu idan mukayi aure na fita ya zakiyi?" turo baki ta yi ta ce " tab ai kuwa saidai duk inda zaka je mudinga tafiya tare dan bazan zauna ba" dariya ya yi ya ce " to keda ba yiwa mutane magana kike ba meyasa kike son zama a cikinsu " tana murmushi ta ce " kawai nafison haka ko bazan kulasu ba nagansu zanji daɗi kasan Annabi ma ya ce Al-jama'atu rahmatun wal furqatu Azabatun kaga kuwa mutane rahama ne dole mu sosu kawai dai nafison na zauna ni kaɗaine saboda banson hayaniya amma inason mutane " dariya ya yi ya ce " Allah yasa nine mijinki Fateematu " murmushi ta yi batace komai ba ya ce " shikenan kije aji anjima mun haɗu " ok ta ce sannan ta yi hanyar ajin shikuma ya yi gaba......




Bayan sun fito daga lecture itada Aysha ta ce " please Aysha muje ki rakani wajen Saima " ok ta ce sannan suka tafi.....




Zaune suke a kan kujeru sunata hira sukai sallama suka shigo kallo ɗaya tayi masu ta ɗauke kai, ƙarasawa Samha ta yi ta ce " Saima zo mana" kallonta ta yi tana nuna kanta da yatsa ta ce " niii " ɗaga mata kai ta yi ta taso ta ce " gani to " cikin sanyin murya ta ce " meyasa kika tafi kika barni yau?, kuma wane wanda yazo ya ɗaukeki har gidanku ?" tana mata wani kallo ta ce " abunda yasa na tafi na barki saboda banga amfanin tafiyar dakebane, kuma banyi ra'ayin hakaba sannan kuma wanda yazo ya tafi dani bakowa bane face masoyina, mai ƙaunata mai son abunda nakeso koda kuwa shi wannan abin bai yi masaba wato Yazeed shine yazo ya tafi dani yau " tana girgiza kai ta ce " wannan bai kamata ba Saima, wannan ba tarbiyyarmu bace ba Saima, ina jiye miki shiga kogin danasani amma baki jina kin biyewa ƙawaye da kuma saurayi wanda nasan duk yanda suke sonki bai kama ƙafar yanda nake sonki ba amma kwata-kwata baki yarda da maganata kin mai dani abokiyar gabarki, kimsani Saima wallahi koda zan cutar da wani a rayuwa banda ke har abada bazan taɓa cutar dakeba amma.....kuka ne yaci ƙarfinta yasa tayi shuru sai shasheƙar kuka take, kusan 5mins sannan ta ce " karki damu zan rabuda rayuwarki kamar yanda kika buƙata amman kisani duk randa wani abu ya sameki wllh bazan taɓa yimiki duban rahama ba Saima wllh Allah ya baki sa'a ya kuma tsare rayuwarki "tana gama faɗin hakan ta kama hannun Aysha sukai gaba....




Har aka tashi ba tada walwala ko kaɗan bayan sun fito ne suka haɗu da Sapwan ganin yanayinta yasa ya ce " muje na kaiki gida kinji " girgiza masa kai ta yi ta ce " no kabari zani da kaina " dakyar ya lallaɓata ta yarda sannan suka huce dan ɗauko Azaad daga tasa makarantar....



Koda suka shigo gida ta tadda Mommy zaune tana cin abinci, da gudu Azaad ya tafi ya rungumeta tana murmushi ta ce " balarabe an dawo daga makarantar?" ɗaga mata kai ya yi ta ce " ok yanzu kaje ka cire kayan ka sannan kazo zan baka abun daɗi " ok ya ce sannan ya yi ciki da gudu, tana kallon Samha ta ce " what's wrong with you Samha?" girgiza kai ta yi ta ce "nothing Mommy kawai na gajine " murmushi Mommy ta yi ta ce " Samha kenan, tun kafin kisan kan ki na sanki nasan irin zurfin cikinki saboda haka faɗamin mene ne matsalar?" fashewa tayi da kuka Mommy ta rungumeta tana shafa bayanta saida tayi mai isarta sannan ta ɗagota ta ce " sorry yanzu faɗamin mene ne?" tana goge idanunta ta ce "Mommy dan Allah dan Annabi kiyiwa Saima magana ta daina kula Yazeed wllh ba mutumin kirki bane cutarta zaiyi "murmushi Mommy ta yi ta ce " karki damu kinji sweetheart kiyi mata addu'a nima zan tayata idan bashine alkhairinta ba Allah ya canza mata da wanda yafi Alkhairi " tashi ta yi ta ce "to Mommy In sha Allah zanyi kamar yanda kikace" murmushi ta yi ta ce " Allah yay maki albarka " ta ce " Ameen"........




Da daddare bayan Azaad ya yi bacci tana kwance ita kaɗai tana tunanin rayuwarsu ta baya da kuma yanzu ahaka har bacci ɓarawo ya saceta....



Kusan one week kenan basa wata magana da Saima, suna zaune ranar asabar suna kallo Daddy ya ce " Samha, Saima " cikin ladabi suka ce " na'am" yana kallonsu ya ce "banson wannan dabi'ar da kuka tsira ta ƙin yiwa juna magana, kanku a haɗe yake sabida haka bazan zuba ido wani saurayi ya shiga tsakaninku ba wallahi kunji na rantse duk randa nasake ganin ɗaya acikinku bata kula ɗayaba kuma baku dawo yanda kuke daba wallahi sai ranku yayi mugun ɓaci " kan su a ƙasa suka ce " sorry Daddy " cikin faɗa ya ce " sorry For your self my dears " shuru kowa na parlour n ya yi saboda sunsan halinsa idan aka ɓata masa rai yana musu wani kallo ya ce" get out of my side " babu shiri kowacce ta tashi sukai ɗakinsu, shikuwa Azaad rungume Mommy ya yi yana kwalalo idanuwa.....




Tunda daga sannan suke yiwa juna magana amma banda maganar saurayi dan da anfara za'ayi faɗa, yauma kamar kullum suna kitchen suna girki Saima ta ce " wai yaushe Azaad zai koma Ethopia ne?" tana ɗauraye hannunta ta ce " babu rana saboda nasan ko nayi aure to Daddy zai cigaba da riƙeshi indai ba shi yace zai koma ba to babu wanda zai ce masa ya tafi " murmushi Saima ta yi ta ce " to idan kikayi auren sai ki tafi dashi gidanki ko kuma ki auri babansa tunda naga soyayya kuke " wani kallo ta yi mata ta ce " bangane na auri babansa ba wace irin soyayya muke?" murmushi ta yi ta ce " idan tayi tsami zamu ji" harararta ta yi ta ce " na rantse ranki zai ɓaci, banda rainin hankali ni zaki kalla ki cewa wai inason Abu Azaad ubanme zanyi da mijin wata ragowa" dariya Saima ta hauyi saida ta yi mai isarta sannan ta ce " ay naga alama bakison ragowa harda satar kwanan Zaheera " tsaki tayi tana ɗaukan tray ɗin abincin tayi waje. Murmushi Saima ta yi ta girgiza kai sannan itama ta kashe gas ɗin ta fito"...........





Fitowarsu kenan daga lecture Samha ta ce " nikam zani unguwa Aysha sai gobe" ok Aysha ta ce sannan sukai sallama.......




Abakin wani katafaren gida tayi parking sannan ta fito, sosai ta gama ƙarewa gidan kallo sannan tashiga ciki. Kai tsaye entrance ɗin gidan tayi , bayan tashiga ta yi sallama da murmushi a fuskarsa ya ce " wa'alaiki Assalam Fateema Ahmad Azaad kina lpy?" wani kallo ta yi masa sannan ta ce " ina lpy Yazeed Abubakar" yana nuna mata kujera ya ce " have a sit" harararsa ta yi ta ce " banzo gidanka da niyyar zama ba nazone saboda nayi warning ɗinka Yazeed" murmushi ya yi ya ce " warning kuma ex?" tana masa wani matsiyacin kallo ta ce"





*Written by*
*Nanameera*





_Tauraruwar royal star ce_
💖💖💖💖[2/1, 21:37] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj

[1/31, 15:43] Nanameera writer: 🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*
[1/31, 15:48] Nanameera writer: 🌹*TSAKANINMU*🌹

*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


_Hadaka palace_


Page.11&12....


__________tana masa wani matsiyacin kallo ta ce " wacece ex ɗin taka?" wani killer smile ya yi ya ce " kemana Samha ai nasan har abada baki taɓa mance *TSAKANINMU* ba kamar yanda nima bazan mantaba, nasan har yau har gobe kina sona kamar yanda nake sonki dan dalilin son da nake miki yasa naji inason biyuninki Saima" sosai gabanta yake faɗuwa amma ta dake cikin faɗa da kuma nuna zallar ɓacin rai ta ce " lier!, ƙarya kake domin ni na daɗe da mance alaƙar dake *Tsakaninmu*, bana fatan sake tuna irin wannan alaƙar sannan ina gargaɗinka Yazeed ka fita a harkar Saima idan ba haka ba wllh saina fasa kwan idan yaso kowama yaji, naƙi faɗane saboda na rigada nayi maka alƙawarin zan riƙe maka sirri amma wllh da tuni kowa ya ji kuma yanzuma idan baka fita harkan ƴar uwataba wllh zaka sha mamakina i will show you the other side of me" ta ƙarashe maganar tana nunashi da yatsa.


Zama ya yi akan kujera alokacin mood ɗinsa ya fara canzawa ya ce " who stop you Samha?, kije ki faɗawa duk wanda kike tunanin zaki faɗawa amman karki manta ƴar uwarki ma na hannu idan kuma ciwon zuciyar naki kikeson ya dawo sabo bismillah " tsugunawa ta yi ta haɗe hannayenta biyu ta ce cikin rauni " please Yazeed kada ka cutarda Saima she can't take it nasan halin twinny, kasan na sanka farin sani kuma da zarar naiwa Saima bayani wllh kona sakan ɗaya bazata sake kulaka ba saboda haka please and please ka fita a rayuwarmu ka rabu damu " wata irin dariya ya hau yi saida ya yi mai isarsa sannan ya ce " Samha kenan, kin san nasan duk abinda zaki iya wllh haka kawai bazaki zo ki tsuguna a gabana ba, kinsan ina sonki sabida haka zan rabu da Saima idan har zaki dawo gareni " a firgice ta tashi daga tsugunon tana masa wani kallo ta ce " macuci, mayaudari, azzalumi kawai, wllh har abada ni dake banso na sake ganinka acikin rayuwata ba Yazeed naso munyi rabuwa irinta har abada saboda kwata-kwata bakada imani a cikin zuciyarka, kuma idan kana mafarkin ina sonka to ka sani kaci ƙarya kodada na sakan ɗaya banasonka kuma bazan taɓa sonkaba" tashi ya yi yana mata tafi yana zagayeta sannan ya ce " maƙaryaciya kawai, idan baki sona meyasa kika faɗi hardasu ciwon zuciya Samha?, nasani har yanzu kina sona so kawai muzo mu rufawa juna asiri kinji" goge hawayen fuskanta ta yi ta ce " har abada wlh zan tafi amma ka sani wata rana zakayi danasani alokacin da bazata amfaneka ba" dariya ya yi yana gaba yace " muje na saukeki" tsaki tamasa sannan tayi waje......





Bayan ta dawo gida ta zauna ita kaɗai sai tunani take irin abubuwan da suka faru a wancan lokacin Azaad ya yi sallama ya shigo, haurowa ya yi ya zauna gefenta ya ce " Aunty Samha

Please Login or Register in order to submit comment