Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai a hankali ya ce" toh daman ba wani abu bane friend ɗina ne ya ganki ya ce yanaso shine nasaka a kiraki saboda na sanar dake halin da ake ciki, idan yaso sai kije kiyi shawara zan nemeki" tunda ya fara maganar take kallonsa with mouth agape har ya idar sannan ta masa wani kallo ta ce" yanzu Sir dakai za'a haɗa baki wai wani ya kula ɗalibar makarantarka, wanda kamata ya yi ace kaine zaka hana faruwar hakan?". murmushi ya yi ya ce" Samha kenan ai wannan da kika sani amma yanzu zamani ya sauya kuma ni nasan halin abokina bazai miki wasaba sabida haka kamar yanda na faɗa kije kiyi shawara in sha Allah zuwa gobe zan nemeki" zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce" tashi kije" babu musu ta miƙe ta yi hanyar waje tana tafe tana waiwayen su cikeda mamaki.......




Tana fitowa ta koma aji amma har suka tashi bata daina tunanin irin maganganun da ya faɗa mata ba kuma ta rasa wazata faɗawa dan tasan duk ba hankali suka cika ba. Da daddare bayan sun gama night prep sun kwanta kasancewar gadonta na kallon na Zahra yasa suke taɓa hira kafin suyi bacci, ganin tayi shuru yasa Zahra ta ce" balarabiya lafiya?" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" wlh wani abune yake damuna tun ɗazu" waro idanu ta yi ta ce" meya faru?" a nutse ta fara bata labarin duk abunda ya faru tun daga farko har ƙarshe............



Shuru Zahra ta yi na wasu mintuna sai kuma ta ce" shikenan kice masa kin amince saboda ina ganin hakane kawai mafita saboda idan baki faɗaba bazai rabu dakeba amma idan kince kin yarda zaki iya dinga ƙin kulashi a haka har ya haƙura, a shawarata" murmushi Samha ta yi ta ce" wlh hakama za'a yi kinga a hankali saina janye jikina na rabu dashi batareda sunga nayi musu rashin mutunci ba" da haka sukayi addu'a kowa ya kwanta.......nima naje nayi kwanciyata sabida naga dare ya yi, kuma lover's kuje ku kwanta......




Attention!! Attention!! Attention!!
*Na kusa gama book one na TSAKANINMU kuma book two ɗinsa isn't free it's 400# amma mutum ashirin ɗin farko zasuyi paying 300#only via 9086030007 Hauwa lawan Opay digital, you can start making your payment send evidence via 09086030007 whatsapp only*




_Written by_
*Nanameera*



_Tauraruwar royal star ce✍️_[2/12, 22:52] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


🌹*TSAKANINMU*🌹

*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*



_Haɗaka palace_


_Page 23&24_


__________Da safe bayan sun gama shiryawa suka fito dan tafiya aji a hanya suka haɗu da Yazeed saboda daman kullum ne sai yazo makarantar kamar ibada, gaisheshi sukai kamar kullum sannan ya yi gaba yana kallon Samha, suna shiga aji malamin physics ɗinsu ya shigo kowacce ranta a haɗe sabida sun tsani physics, banda Samha wacce kamar ita kaɗai yake yiwa karatun saboda yanda ya bada attention ɗinsa wajen koya mata,sai kusan ƙarfe goma ya fita duk suka tashi daga kwanciyar da sukayi wasuma harda bacci......




Suna cikin cin abinci wata yarinya ƴar jss three tazo ta ce" Aunty Fateema wai kije inji director" ɗora hannu ta yi aka ta ce " nashiga uku ni Samha, ok tafi zanje" juyawa yarinyar ta yi ta tafi sannan ta miƙe ta ce" i'm coming" suka ce "ok".......






Zama tayi bayan ta gaishesu ya ce".Fateema me kika yanke akan maganar mu ta jiya?" numfasawa ta yi tana wasada fingers ɗinta ta ce" Sir na amince, amma banda shiga rayuwata ta makaranta" murmushi ya yi ya ce" good masha Allah yanzu zai dinga yi miki magana amma bawai wacce zatasa a gane ba kinji" ta ce" toh" kallonta ya yi yana cute smile ya ce" that means kin amince Fateema?" ɗaga kanta ta yi ta kalli Yazeed ta ce" Eh na amince" ya ce" thank you Samha i promise u will never regret" tashi ta yi ta ce"Allah yasa " sannan ta yi waje. Murmushi ya yi ya ce" gaskiya friend na gode sosai da wannan ƙoƙarin wlh yarinyar tayimin" dariya mai Fata ya yi ya ce" ai ka huce haka awajena " daga haka suka cigaba da hirarsu..........




Tashin su kenan daga islamiyya suna tafiya itada Zahra ta ce" najefa na ce masa na amince, amma.ina tsoro Zahra kaga Daddyna yaji" murmushi Zahra ta yi ta ce" karki damu Samha in sha Allah Daddy bazai jiba kuma kema kaga ki bari ki faɗa soyayyarsa kiyi komai a sannu sabida kinsan bawai soyayyar gaskiya bace" ta ce" in sha Allah, ni wlh baima burge ni ba " girgiza kai ta yi ta ce" u'un kar kice haka saboda ba kisan sanda zaki fara sonsa ba kinsan so babu ruwansa da mutum ya yi maka gwanda a kiyaye" dariya ta yi ta ce" wannan ai kece malamar soyyaya irin wannan tsara zance haka" harararta ta yi ta ce"banza ƴar iska bansan rashin mutunci" dariya ta yi suka jera suka cigaba da tafiyarsu........



Kusan one week kenan suna tare kuma babu laifi sun ɗan saba dashi yauma suna tsaye suna hira ya kalleta ya ce" wai love yaushe zamuyi aure?" murmushi tayi ta ɗauke kanta ya kamo hannunta ya ce" plx mana ko sainaje na yiwa Daddy kuka?" batasan sanda ta fashe da dariya ba tana nuna kanta ta ce"nii, ƴar gidan ubana, so kake Daddy ya ce nada ina karatun gabaɗaya ko?" dariya shima ya yi ya ce" daina karatu kuma?, toh yanzu yaushe zamuyi plx?" kwaɓe baki ta yi ta ce" nikam karabu daniii " dariya ya yi sosai ya ce" wow Love irin wannan shagwaɓa haka, kinsan kuwa inason mace shagwaɓɓiya irin sexy ɗinnan sweet". turo baki ta yi tana kallon wani wajen ta ce" ni dai sai anjima kada a nemeni" batayi auneba taji warm lips ɗinsa a bakinta,wata zabura ta yi zata gudu ya riƙeta gam yana cigaba da abinda yake, kusan 2mins sannan ya saketa yana sauke numfashi da gudu ta tafi batareda ta juyoba...



Riƙe kansa ya yi ya ce" oh my god mena aikata haka?" lokaci ɗaya ya yi wani murmushi sannan ya shafa kansa ya yi gaba.......




Tana zuwa hostel ɗinsu ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta sannan ta fito daidai nan su Lubna suka shigo. Kallonta sukayi ganin yanda fuskarta ta yi jajur duk ta kumbura, da mamaki Zee ta ce" Balarabiya what's wrong?" murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce" me kika gani?" wani kallo tayi mata na kin rainan hankali sannan ta ce" babu komai" Lubna ta ce" haba calm down kinsan dai Samha bata shawara da kowa banda Zahra saboda haka abar maganar" harararta Zahra ta yi ta ce" toh tunda kunsan hakane sai kubar maganar plx" cigaba da wata hirar sukayi cikin nishaɗi da annashuwa......




Da daddare as usual bayan sun kwanta Zahra ta ce" Samha ɗazu mene ya sakaki kuka?" zama ta yi ta bata labarin duk abunda Yazeed ya yi mata, sosai Zahra ta yi mamaki sai kuma ta ce" plx Samha karki saka wani abu aranki kuma karki sake kula shi saboda daman ni ban wani yarda dashiba" ta ce" that is the reason why tun farko banyi accepting ba saboda irin wannan mutane basu jin tsoron Allah" Zahra ta ce" wlh fa shiyasa tun farko nace karki zurfafa a cikin sonsa kin san maza" ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce" amma fa Zahra ina sonsa da gaske wlh, bansan yausheba amma inajinsa a raina sosai" baki buɗe Zahra ta ce" subhanal lahi amma Samha shiyasa nayi warning naki a kan kada kiyi zaton soyayya kuke " hawaye na sauka a kan fuskarta ta ce" wlh Zahra i don't know yaushe hakan ya sameni ba kawai naji ina sonsa kuma sosai wlh" Zahra ta ce" toh Allah ubangiji ya yaye miki Samha" ta ce " Ameen " sannan suka cigaba da hira kafin bacci ya ɗaukesu........




Tunda ya koma gida yake tunanin Samha shi kaɗai yake murmushi a haka har bacci ya ɗaukeshi.....




Zaune ya tadda Alh. Mai Fata bayan sun gaisa ganin yanayinsa ya ce" ya Yazeed lpy kuwa?" girgiza kai ya yi ya ce" wlh ba lafiya ba....." plx ka taimakeni" numfasawa ya yi ya ce" gaskiya Yazeed bazan iya ba saboda babu yanda za'ayi mahaifinta ya yarda kuma itama yarinyar kasan bazata yarda ba kawai ka haƙura idan kuma ka matsu toh akwai mata sai wacce ka zaɓa" da damuwa ƙarara a fuskarsa ya ce" wlh bazan iya haƙura da Samha ba coz yarinyar ta haɗu kuma wlh urgent nakeso saboda kasan ni banason daɗewa" shuru ya yi sai kuma ya ce" nikam nayi iya yina sauran kuma ya rage naka" tashi ya yi ya miƙa masa hannu sannan ya ce" sai ka jini" ya yi murmushi ya ce" oll the best" ya ce" thanks" sannan ya yi waje.........



Tundaga wannan ranar bata sake haɗuwa da shiba duk yanda zaiyi dan su haɗu sai ta kauce masa dukda itama ta yi missing ɗinsa sosai amma ta yi iya bakin ƙoƙarinta ganin ta manta shi amma abun ya faskara banda Zahra dake sake lallaɓarta a haka kusan two months wanda har cuta saida ta yi amma ba'a faɗawa Daddynta ba. Yauma ya kasance zasu fara second term examination suna zaune suna karatu banda Samha wacce ta rame ta yi baƙi, dafata Zahra ta yi ta kalleta da damuwa ta ce" wai Samha bazaki cire Yazeed a ranki ba?, yanzufa exams zamu fara gobe ya kamata ace kin daina tunaninsa haka don Allah kiyi concentrating a kan exams ɗinki kinji" gyaɗa mata kai kawai ta yi ta ɗauki littafinta ta buɗe sannan itama Zahra ta zauna ta cigaba da karatun........



Fitowarsu kenan daga exams ɗin suka zauna ƙarƙashin wata bishiya suna discussing akan jarrabawar kamar ance ta ɗaga kanta ta hangoshi yana nufuso ji tayi gabanta ya yi wani irin faɗuwa ganin inda take kallo yasa Zahra ta kalli direction ɗin ai kuwa sukayi ido huɗu dashi wata uwar harara ta maka masa ya yi kamar bai ganiba ya yi gaba abinsa. Kallon Samha ta yi ganin har sannan bata daina kallon inda ya bi ba yasa ta ce" Samha dan Allah dan Annabi ki manta da Yazeed a rayuwarki plx" ta faɗa tana goge mata hawayen fuskanta ba tareda ta ce komai ba........




Da sallama a bakinta ta shiga office ɗin director'n dalilin kiranta da yasa a kai, amma ga mamakinta sai taga Yazeed zaune suna hira hakan yasa ta tamke fuska babu alamar dariya ta ce" good day Sir" ya ce" how are yhu?" ta ce" fine" nuna mata kujera ya yi ya ce" have a sit" zama ta yi tana kallonsa alamar neman ƙarin bayani. Ganin irin kallo da take masa yasa ya ce" abokin ƙawarki ne yasa a kiraki" kallonta Yazeed ya yi ya ce" Zahra inason ki taimakeni ne gefe ɗaya kuma ki taimaki ƙawarki" da mamaki ta ce" wani irin taimakone wannan?" ya ce"........." a wani fusace ta kallesa ta miƙe ta na nunasa da yatsa ta ce" wlh har abada nida aikata wannan abun bazan taɓa iya cutar da wani bare kuma Samha har ƙarshen rayuwa babu wannan *TSAKANINMU* wlh danaci amanar Samha gwanda na mutu a yanzu wlh" tana gama faɗin haka ta juya sai dai kafin ta kai ƙofa ya ce" idan baki bani haɗin kai ba wlh kece zaki fansheta sai ki zaɓa da ki sami dukiya da rayuwa mai kyau fiyeda ta gidanku da kuma bani haɗin kai" tunda ya fara maganar ta ke kallonsa har ya gama banda hawaye babu abunda ke zuba daga fuskarta ta ce" wlh kome zaka yimin bazan taɓa aikata abunda kake muradi ba" ta yi fitarta ta banko ƙofar, juyawa ya yi ya kalli Mai Fata ya ce".....







*Kada ku manta Tsakaninmu book two isn't free, it's 400#, 300# For the first 20 people, you can start making your payment via 9086030007 Hauwa lawan opay, evidence via 09086030007 thanks yhu*






_Written by_
*Nanameera*



_Tauraruwar royal Star ce✍️_
[2/13, 22:37] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


🌹*TSAKANINMU*🌹

*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


*Haɗaka palace*

_Page 25&26_


_______Tana zuwa hostel ɗinsu ta zauna ta yi shuru tana tunani sosai abun ya ɗaure mata kai ace musulmi baya tsoron Allah to wazaiji tsoro?, tana cikin wannan tunanin ne Lubna ta shigo, zama tayi kusada ita ta ce" Zahra lafiya naga kinyi shuru haka?" numfasawa ta yi sannan ta ce" wlh wani abune yake tunkaromu plc ku tayamu da addu'a kinji" ta ce" in sha Allah amma karki saka komai aranki saboda kinga muna exams kar ki waɗi" ta ce" in sha Allah, tncs sis" harararta ta yi da wasa ta ce" banson gulma" sukayi dariya duka.......



Sosai jarrabawa ta ɓoyesu kowa ba shida abunyi sai karatu dan ko hirar arziki ba su yi kuma har sannan Zahra bata faɗawa Samha abunda Yazeed ya cemata ba a haka har suka kai final paper.......



Fitowar su kenan daga ajin kowacce sai murna take ta gama jarraba, dubawa Zahra ta yi taga babu Samha hakan yasa ta cewa su Zee" plc ina Samha?" Lubna ta ce" kinsan da wuri ta fito maybe ta tafi hostel" ta ce" to kuzo mu tafi plc" Zee ta ce" chaɓ mu dai sai munyi yawo ke ki tafi" ta ce" toh " sannan tayi hanyar hostel ɗinsu su kuma sukayi gaba.......



Tana shiga ta tarar bata ciki hakan yasa ta zauna dan tunaninta tana toilet, kusan 10mins amma shuru babu Samha babu labarinta ta miƙe taje ƙofar banɗaki tana kwankwasawa ta ce" Samha wai me kike a banɗakin nan?" shuru taji hakan yasa ta ɗan tura ƙofar amma ga mamakinta sai taga babu kowa a ciki. Tsaki ta yi ta ce" aikin banza ko ina tayi ohoo?" sannan ta juya zata fito taji tayi karo da mutum, da sauri ta yi baya tana
ɗago kanta tayi ido biyu da wani wanda ita batace ga kalarsa ba ta buɗe baki zatayi magana ya fesa mata wata powder sai gata a ƙasa sumammiya.....



A hankali ta fara buɗe idonta har ta buɗesu tanyar wata zabura ta yi ganinta a kan wani royal bed ƙato, batasan sanda ta fashe da kuka ba amma daga gefenta sai taji kukan wata daban, juyawa ta yi sukayi ido biyu da Samha wacce a ka ƙuƙƙule da sarƙa kamar wacce tayi sata banda kuka babu abunda take, itama Zahra volume ɗin kukanta ta ƙara suka dinga kukansu babu mai rarrashinsu......



Buɗe ƙofar da su kaji anyi yasa suka kalli ƙofar a tare, shigowa ya yi yana wani irin murmushi na zallar mugunta yana kallonsu, tsagaitawa su kayi da kukan suna binsa da kallo na tsananin mamaki musamman Samha. Ɗora ƙafarsa ɗaya ya yi akan gadon yana kallon Zahra ya ce" yaya dai Zahra'u?, meyasa nayi warning ɗinki baki jiba?, na baki kuɗi wanda da yanzu ke babu ruwanki a cikin wannan maganar amma kika ƙi, har saida kika fusatani nayi aikin da kaina kuma a yanzu zan fanshe duk irin zagin cin mutuncin da kika yimin a gaban ƙawarki"da sauri suka kalleshi a tare lokaci ɗaya suka sake fashewa da sabon kuka cikin dashewar murya Samha ta ce tana haɗa hannayenta alamar roƙo" dan Allah dan Annabi Yazeed kada ka cutarda Zahra wlh batada laifi it's my fault dan Allah ka rabu da'ita ta tafi idan yaso ni kayimin duk abunda kakeso kaji dan Allah" ta ƙarashe maganar tana sakin wani raunataccen kuka, cikin kuka itama ta ce" wlh A'a duk laifina ne dan Allah ka rabu da Samha wlh duk abunda kakeso zan maka amma ka barta" kallonsu ya yi duka sannan ya fashe da wata dariya irin ta muguntar nan sannan ya ce" karku damu ɗaya bayan ɗaya zanyi kunji" yana gama faɗin hakan ya zare singlet ɗin jikinsa, ganin da gaske nema yake ya yi tsirara yasa duka suka kifa kansu suna kuka. Basu sake shiga tashin hankali ba saida taga ya hau kan gadon banda kuka da kiran sunansa babu abunda Samha keyi dan ita Zahra ta rigada tayi give up na mutuwarta tanaji tana gani haka ya rabata da budurcinta hankalinsa kwance lokacin kuwa tsabar tashin hankali Samha numfashinta banda janyewa babu abunda yake ta sowa ya yi zai yo kanta daidai lokacin aka buɗe ƙofar ya juya yana kalla..........



Da wani irin gudu ya shigo yana kallonsa da mamaki da kuma tashin hankali yake cewa" Yazeed meyasa zakayi haka?, me yarinyar nan tayi maka dan Allah?, wannan ma ai haukane so kake a rufe makaranta ta?" kallonsa ya yi ya ce" idan har baƙatata zata biya ai shikenan" tsaki ya yi ya tafi gurin Samha ganin yanda taketa kokawa da numfashinta ya warware duk ɗaurin da yayi mata sannan ya kama hannunta suka fito........





Kai tsaye asibiti aka wuce dasu amma duk wannan bidirin da ake babu wanda ya sani a cikin makaranta, kusan two days kafin Samha ta dawo daidai a nan likitoci suka tabbatar da tanada ciwon zuciya. Shigowa sukayi asibitin ya zauna gefenta yana kallonta ya ce" Fateema ya jiki?" ta ce" ina Zahra?" girgiza kai ya yi yace" ta tafi gida kuma kema babanki yazo ɗaukarki amma dan Allah dan Annabi inason abunda ya faru ya zama sirri wanda bazaki tonaba har abada, bawai saboda Yazeed A'a kiyi saboda Allah" tana goge hawayen fuskarta wasu na sake zubowa ta ce" koda ban faɗawa kowa ba ka sani Allah ba azzalumin bawansa bane kuma wlh sai ya hukuntaku ka saka wannan a ranka" tashi ta yi ya ɗebo kayanta suka fito.........




Zaune suka tadda Daddy ya yi sallama da director n sannan suka kamo hanya, sunyi nisa ta kalleshi ta ce" Daddy " ya ce" na'am" tana kallonsa ta ce" Daddy bazan koma wannan makarantar ba har abada wlh bazan koma ba a mai dani makarantarsu Saima kaji" da mamaki ya ce" lpy Samha?" ta ce" kawai Daddy wlh bazan dawo ba" sanin halin gaddamarta yasa ya ce" shikenan Allah yasa hakane mafi alkhairi" ta ce" Ameen" sannan suka cigaba da tafiya........
*wannan kenan*

Banda kuka babu abunda Saima keyi itama Samhan kuka take cikin rauni ta ce" wlh Saima ban taɓai miki baƙin ciki ba hasalima burina bai wuce naga kinsamu kyakkyawar rayuwa, wlh Saima duk duniya babu wanda ya kaini sonki ko su Daddy ji nake da kyar su fini, wlh ban taɓa ƙinki da Yazeed saboda wani abuba sai wannan, kuma.......... Rufe mata baki Saima ta yi tana kuka kamar ranta zai fita amma takasa maganar hakan yasa ta tashi zata tafi amma bata kai bakin ƙofa ba jikake timmm ta waɗi ƙasa, da gudu Samha ta yi kanta cikin tashin hankali t ce".........





*remain 4pgs na gama book one and book isn't free its 400#,300# For first 20, eighting slot remaining make your payment via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence' via 09086030007whatsapp only*






_Tauraruwar royal star ce✍️_https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


🌹*TSAKANINMU*🌹

*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


_Haɗaka palace_


_Page 27,28,29&30_


*End of book one*

*I Dedicated this page to TSAKANINMU Fans group wannan page ɗin nakune Allah ya barmu tare*



__________Da sauri ta ɗauketa ta ɗorata kan gadonta da kyar sannan ta fita da gudu dan sanarwa Mommy amma sai ta samu Mommy batanan hakan yasa ta yi tunanin shiga ɗakinta dan ta ɗaukar mata drugs ɗinta ta bata....




Tana shiga taje wajen bedside drower ta ɗauki magungunan kamar ance ta juya kawai ta kalli gefen pillown ta ganin wani sachet ɗin maganin yasa tasa hannu ta ɗauko dan a zatonta maganine, batasan sanda ta zauna ba saboda tsananin tashin hankalin daya ziyarceta naman jikinta har wni rawa yake tunaninta ya tsaya cak Shin me Saima take da wannan maganin?ta tambayi kanta, kusan two minutes sai kuma ta tashi ta fita daga ɗakin tanajan ƙafa........



Zaune ta tadda ita ta jingina da jikin gadon banda tunani babu abunda take dan kwata-kwata batasanma Samha ta shigoba har ta zauna gefenta ta taɓa sannan ta kalleta a firgice Samha ta ce" Saima kin san ni i'm ur sister saboda haka duk duniya babu wanda ya kamata ki dinga shawara sai ni, saboda haka please kada kimin ƙarya me kike da wannan maganin?" ta faɗa tana nuna mata sachet ɗin. Cikin wani sabon tashin hankali ta buɗe bakinta amma ta kasa maganar sai kuka ganin yanda take kuka yasa jikin Samha ya yi sanyi ta rungumeta ta ce" kiyi shuru twinny ki faɗamin what wrong wiz u wlh bazan faɗawa kowa ba" ɗagowa tayi ta kalleta ta ce" da gaske bazaki faɗawa kowaba ?" ta ɗaga mata kai. Miƙewa ta yi daka kwancen ta kamo hannunta tana facing ɗinta ta ce" twinny i'm sorry, i'm very sorry wlh ban taɓa zaton haka zai faru dani ba sanda kike faɗamin ban saurare ki ba sai Yanzu da babu abunda faɗawar zai amfanamin, wlh twinny nayi danasani bansan haka yakeba, ban ɗauka so yake ya cutar daniba banji maganarki ba saboda ƙawa data ruɗeni gashi yanzu natashi cikin tutar babu ni ban auri wanda nake soba kuma yanzu ko wanda bana soma bazai aureni ba, bansan me zan faɗawa su Daddyba wlh bansani ba, ji nake inama Allah ua ɗauki raina na huta da irin wannan ranar" ta ƙareshe maganar tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, itama kanta Samhan kuka ta ke dan ko bata faɗa mata ba tagane inda zancen nata ya dosa, tana goge hawayen fuskarta ta ce" tun yaushe?" ta ce" tun randa nace miki zani birthday gidansu Aleeya wanda kuma a zahiri Yazeed ne ya gayyacemu birthdayn bayan munje ganin yanayin wajen yasa nace nidai mu tashi mu tafi amma sai ya ce bari ya kawo mana abun sha wanda tunda nasha bansan inda kaina yakeba sai da na farka na ganni a asibiti kima ya yimin gargaɗin karna kuskura na faɗawa kowa idan ba haka ba ya yimin video kuma zai sakeshi kowa ya gani" ta faɗa tana cigaba da kukanta kamar ance Mommy ta mutu. Sabida mutuwar jiki Samha kasa cewa komai ta yi amma deep down ji take inama taga Yazeed yanzu da wlh sai ta kasheshi idan yaso itama a kasheta, shuru kowannensu ya yi suna tunanin mafita musamman Samha kusan 10mins sannan ta ce" karki kuskura Mommy ta ganki a tsukinnan koda zaki fito ki dinga sake hijab saboda kai tsaye zata gane, sannan karki ce mata bakida lpy kome ki keji ki faɗamin zan miki please Saima coz bansan ya zata ɗauki al amarinba kuma kinga ta nada depresion to kaga aje ya tashi more espicially Daddy zani wajen Zahra zamusan abun yi amma this time around dole sai an hukunta Yazeed" ɗago kai ta yi da sauri ta ce" twinny ya ce zai watsa video na please ki taimake ni" kamo hannunta ta yi ta ce" karki damu kinji nasan me zanyi kedai ki tabbata kinyi abunda na ce miki" gyaɗa mata kai ta yi ganin yanda jikinta ya ɗauki zafi yasa ta ce" ki kwanta bari na dafa miki abinci kici sai kisha magani" komawa ta yi ta kwanta ita kuma ta tashi ta fito dan shiga kitchen.......








*Ethopia*

Zaune suke gefenta suna taɓa hira sosai yaji daɗi dan rabonda suyi hira da ita har sun manta tana murmushi ta ce" Abu Azaad idan na mutu wa zaka aura?" kallonta ya yi sai kuma ya ce" please Zaheera banson irin wannan maganar wane ya ce miki mutuwa zaki yi?, yanzu ba gashi kina samun sauƙi ba kuma maganar ma kirasa gaban wa zaki yi sai Azaad wannan ai ba daidai bane" murmushinta mai kyau ta yi ta ce" i'm sorry kawai

Please Login or Register in order to submit comment