Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kuma Sai Dariya Yake Cikin Tsananin So Da Kula.

Basu Tsaya A Ko Ina Ba Sai Anguwar Dawaki Da Yake Zagaye Sukayi Suka Fara Zuwa Gidan Su Jameela, Tun Daga Kofar Gida Da Yara Suka Ganta Sai Suka Ruga Da Gudu Suka Nufi Cikin Gida Suna Cewa Ga Adda Jameela Ga Adda Jameela Kasantuwar Jameela Mace Ce Mai Son Yara Shi Yasa Idan Yaran Anguwa Suka Ganta Sai Kaga Suna Dauki Saboda Sun San Zata Basu Wani Abu In Zata Tafi.

Cikin Nitsuwa Ta Sauka Daga Kan Mashin Tace: Mai Sanyi Sai Mushige Ko Cikin Kulawa Da Zolaya Yace: Sai Ki Fara Yin Gaba Tace: Naki Din, Sai Dai Mujera Mu Shiga A Tare In Har Bazakayi Gaba Ba.

Dakyar Dai Ta Yarda Tayi Gaba Suka Shiga Cikin Gida, Su Jameela Bawani Babban Gida Bane Kawai Dai Irin Gidajen Nan Ne Na Rufin Asiri.

Ta Masa Rakiya Har Falo Ita Kuma Umma Tana Ta Masa Sannu Da Zuwa Mutanen Kaduna Shi Kuma Gogan Sai Ya ke Yake, Suna Zama Yara Kanen Jameela Ameer Da Surayya Suka Zo Suka Durkusa Cikin Girmamawa Suka Gaishe Da Adda Jameela Da Sannan Suka Juya Zuwa Musa Sukace: Yaya Musa Ina Kwana Cikin Zolaya Yace: Bazan Amsa Gaisuwar kuba Saboda Bakwa Zuwa Gidan Addan Ku.

Caraf Sai Surayya Ta Cafke Maganar Tace: yaya Shekaran Jiya mafa Munje Tun da Safe Sai La'asar Muka Dawo Lokacin Baka Gida ?

Sai Ya Juya Gun Jameela Yace: Addarsu Anyi Haka ?

Tace: Eh Anyi Haka Yallaboi

Yace: To! Meye Yasa Baki Fada Min Ba Tace Na manta Ne Sorry!

Take yasa hannu a aljihu ya ciro dari biyu ya basu sukaiwa yaran da suke waje akan su raba suka fita suna ta murna sunsan suma zai basu wani ba idan zai fita.

Ana Cikin Wannan Muhawara Ne Sai Umma Ta Shigo Falon Da Suke Zaune Cikin Girmamawa Musa Ya Zube Kasa Yace: Umma Ina Kwana ?

Cikin Kulawa Tace : Masa Lafiya Kalau Ya Aiki Ya Mutan Kaduna ?

Yace: Lafiyan Su Kalau Umma,

Sai Jameela Tace: Umma Ina Kwana Ta Amsa Mata Sai Take Tambayar Ta ina Abba Tace: Ya Fita Kasuwa Tun Karfe Takwas Dan Yace Za'a Sauke Masa Kaya Yau.

Suna Gama Gaisawan basu wani dadewa ana tadi ba na wasa da barkwanci dan sun kai kusan dakika ashirin da daya sannan Sai Sulaiman Yace: Umma Mukan Zamu Tafi Sai Wata Rana Amma Daman Ina Sone Na Fada Miki An Kusa Gama Mana Gidan Mu A Kaduna In Da Zamu Koma Tare Da Jameela Cikin Murna Umma Tace: Tace Nayi Murna Sosai Amma Kafun Ku Tafi Da Kun Tsaya Na Muku Ko Dan Abun Da Zaku Taba.



Caraf sai jamela ta amshe ta da cewa, haba umma kina nufin banyi masa abun karyawa bane muka fito?

Da yake ita Umma mai wasa da dariya ne sai tace: aa ina nufin ku tsaya kuci dafaffen girkin ba shiririta ba ?

Sai jameela tace: umma kina nufin shiririta nake mana a gida kenam?

Ban fada miki ba nikam, umma ta fada.

Shi kuma sai yake yake yana dariya a haka dai muka tashi zasu tafi.

Sai sulaiman yace: umma zan dawo ko mu dawo tare saboda zanyi sati biyu anan garin kafun na koma amma idan abba ya dawo kice masa ina gaisheshi kuma zamu dawo gaisheki shi.

Umma tace: Insha allahu zaiji dama kunyi hakuri ko nakira muku shi a waya yazo ku gaisa.

Aa umma ba komai zamu dawo dai inji jameela tana maganar tana dariya.

Haka zasu fita sai ya zare dubu uku dari biyar-biyar ne sabbi ya mikawa jameela yace: ki bawa ummana ta sayi goro,

Tana karba kawai sai taje karkashin filon umma ta ajiye su umma tana gani babu yadda ta iya saboda kusan haka jameela take mata dan idan da zaace umma karba zatayi da sai dai su wuni su kwana amma bazata karba ba.

Nagode, allah ya saka umma tace, tana nan a zancen ta sai ga surayya da ameer sun dawo suna ta tsallen wasa da murna nan take ya ciro 200 Ya bawa surayya da ta nuna bazata karbaba saboda idon umma amma sai jameela ta miqawa ameer wanda shi shiru-shiru akan ya kaiwa umma tana musu canji na kudin taran makaranta, ya karba.

Sai inna ta fara yiwa jameela masifa akan meye yasa take haka ita kuma ta wuce gaba, sulaiman kuwa yana ta baiwa umma hakuri cikin raha sai kawai suka fita.



Kafun su hau mashin din ne yace: sai JekaDaFari ko ?

tace: sai yadda kace, nima bama wannan ba ina sone na kara maka godiya akan yadda kake karrama iyaye na da mutunta su kuma kake musu alkhairi... bai bari ta kara saba yace dakata wato ke kina ganin iyayenki ba iyaye na bane ko meye, wallahi kina bani mamaki idan ban yiwa naki ba waye zan yiwa, hakan ma dai nasan cewa babu abun da nayi ina fatan har na samu karin mukami a gun aiki buri na in biyawa umma da abba kujeran hajji saka makon yaba tukuici.



INA NEMAN UZURI DAGA MASU KARATU AKAN CEWA WAYAR DA NAKE RUBUTU DA ITA TA SAMU MATSALA AMMA INSHA ALLAH BAZAN WUCE KWANA UKU BA KOMAI ZAI JARU,

INA SONKA FATANA KUCE INA NISHADANTAR DAKU



KASH MU HADU A PAGE 005


&& AUREN WUCIN GADI &&

Page 005

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Addata

Ayshfat Muhammad Galadima

(Momi) '''



(Federal Lowcost Kusada Ministry of Agric/Fadama II Gombe)



TSARABAR MAKARANTA

Manzon Allah S.A.W.A Yace:

(( [[Lallai Nina Bar Muku Khalifofi(na) Guda Biyu AlQur'ani... Da Iyalan Gidana -AhlulBayt-...]] ))

MUSNAD AHMAD







Basu wani dade suna tafiya ba saboda ba wani tazara bace mai nisa daga dawaki zuwa jeka da fari, Suka iso gidan su Sulaiman.

Babban gida ne wanda babu yabo ba fallasa shigewa sukayi cikin gidan take yana gaba tana binsa a baya suna tattaunawa suna dariya irin na masoyan da suka shaqu da juna, sallama yayi aiko khadija ce ta fara gane shi tace, "Waalaikussalam"

Aikuwa sai ta ruga da gudu ta fada dakin maman su tace: umma! Umma!! Umma!!!

"Haba meye ne kina ta kiran mutum kamar wata makahuwa" Umma ta fada tana hada fuska.

"Yaya sulaiman ne yazo, da anty jameela !!!"

"Haba khadija shine kike ta kwalamin kira to ya fada min daman tun shekaran jiya kafun ya dawo" umma tace

"Haba umma yaya baki fada min ba kuma" khadija tace.

Kafun umma ta bada amsa, kawai sai sukaji sallamar sulaiman ya shigo daki.

Umma ce ta amsa tana musu maraba lale da zuwa.

Ita kuma khadija kamewa tayi tasha mur a gefe guda har sulaiman ya zauna suka gama gaisawa da umma.

"Meye yasa mu 'yan gatan umma ne kam... ta share yayanta, Haba Dija Kaya bakisan ta gida ba..." sulaiman yayi ta mata maganganu dai na tsokana.

Juyowa tayi tace: haba yaya yanzu zaka dawo baza ka kirani a waya ka fada min ba, sai dai ka kira umma ita ma ba fadamin tayi zaka dawo ba sai yanzu take fadamin.."

Caraf sai jameela ta cafke maganar da fadinta "Rabu da ita daman bata ma ko zuwa gidan yayan nata..."

Haba anty wancan satin ba naje ba. Khadija ta fada

Amma ai ya dade shi yasa

Tace: to shikenam zan na zuwa shikenam

"Shikenam" shima yace.

Daga nan ta juyo ta gaishe shi ya amsa yana mai fara'a.

Ta juya sashin anty jameela ta gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska ta amsa mata.

Daga nan sai yake tambayar umma ina umma sa'adatu da sauran yaranta.

Sai umma tace: sun tafi kuma auren wata yar uwarsu a kumo duk dama gobe zasu dawo.

To umma kinsan fa na kusa komawa ko kaduna ya kamata idan na tashi ko mawa na tafi daku gaba daya gidan nan aje ayi walima na mussamam.

"Ai kai ma kasan wasa kake dan kai ma kasan babanka ba bari zaiyi ba mu tattare gaba daya mu tafi gidanka dan mune sarakunan masu hankali.

Sai dai kawai wasu yara suje daga baya manya suje ko da bayan walimar komawa din ne.

To shikenam Umma amma dai ban so ba.



Daga karshe dai sulaiman tashi yayi ya tafi gurin abokinsa ya bar Jameela tayi ta taya khadija aikin gida sukayi ta wanke-wanke da girki.

Ana cikin haka jameela ta shiga daki ta tattaro kayan sawan umma wadanda sukayi dotti umma tana ganin haka tace aa wallahi ban isa na wahalar da surukata ba, da ker da ji6in goshi amma ta yarda saboda zakin baki da iyayi yasa ta dauko sabulu daman kala uku ta gani da alamar an saka ta wanke su tas suka fita ta shanya a lokacin ne abincin da suke dafawa tare da khadija ya karasa dahuwa ta sauke khadija ce ta raba aiko san ta saka muku jalof din taliya da waken a tire na umma dabam Sannan na yaya sulaiman dabam.

Aiko sai umma ta tubure akan allanfir sai an hadasu suci su ukun tare hakan kuma akayi kasan tuwar umma dattijuwa ce wacce babu ruwanta ga kyan hali shi yasa kullum jameela take gode wa allah akan yadda allah ya bata umma uwar miji saliha.





ASALIN LABARI

Alhaji muhammad deba shine asalin sunan babansu sulaiman asalinsa dan garin deba ne na karamar hukumar yamaltu deba, a can ya taso amma sai sana'ar sa ta kasuwanci ta dawo dashi cikin garin gombe tun lokacin sulaiman yana yaro dan shekara shida kafun daga baya ya kara aure bayan kasuwancinsa na dilan manja a babbar kasuwar gombe ta bunkasa.

Ya auro sa'adatu wacce yar ubangidan sace da yayi masa silan bunkasar kasuwancinsa, a shekarar daya auro tane matarsa ta farko ta sake haihuwa ya mace wacce taci sunan mahaifiyarsa wato khadija.

Ana nan dai har sulaiman ya fara makaranta a jalowaziri primary school ya gama karatu har matakin NCE amma a gurin babansa yake zuwa yana taya shi aiyuka a shago shi kuma baban yana bashi wani abun kashewa kuma yana daukar nauyin karatunsa,

Alakar musa da sulaiman ta faru ne tun suna makarantar kwana da sukayi tare a garin pindiga amma asalinsa dan tudun wadan gombe ne.



A lokacin da musa ya tashi yin aure babban abokinsa shine sulaiman inda a wannan bikin ne allah ya hada jameela da sulaiman har maganar aure ta shiga tsakani.



Iyayen jameela ba wasu masu hali bane sosai amma mahaifinta alhaji kabeer mai tireda ake ce masa yana manyan shaguna guda biyu a kasuwa na saida kayan masarufi, matarsa daya ita ce asma'u yayansu uku jameela suhaima ameer amma sun samu ratan shekaru a tsakaninsu sosai da addarsu jameela.



Sulaiman ya samu aiki ne a hukumar wutan lantarki kuma yayi sa'a an dauke shine da takaddunsa na dan babban matsayi ma ya samu saboda yana da wanda ya wuce masa gaba.

Daga fara aikin ne babansa ya saya masa gida akan yayi aure ya kawo matar nan daga baya idan yana da raayin zama acan ya iya gina musu gida a can ba musu kuwa ya yarda.



Ya auri jameela auren ya tara jama'a sosai saboda har abokan aikinsa daga kaduna ma sun samu halarta auren jameela ya kafa tarihi wanda baza'a mance dashi ba a dawaki saboda daruruwan mutanen daya tara duk da cewa shi angon ba dan siyasa bane ko kuma hamshakin dan kasuwa.



YAN UWA MASU KARATU INA DA WATA BUKATA TA MUSAMMAN KUMA TA ALKHAIRI A GURIN ALLAH INA FATA ZAKU TAYA NI ADDU'A AKAN ALLAH YA BIYA MIN BUKATATA! !!

KASH MU HADU A PAGE 006


&& AUREN WUCIN GADI &&

Page 006

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208





Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Mai Gida

Mal. Kabiru Keji Tela Gombe

(KEJI BOOK SHOP) '''



(Bakin Cross Tsohuwar kasuwar Gombe)







DON MASU KARATU

Imam Ja'afarus Sadiq A.S Yace: (( [[Duk Wanda Ya Kosar Da Makiyinmu-AhlulBayt- Hakika Ya Kashe Masoyinmu]] ))

MA'ANIL AKBAR



Murna ce ta kara zamowa biyu wanda a rana ta biyu wato ranar wuni matar musa ma ta haifa masa wani kyakyawan yaron gwanin ban shaawa, nan take kuwa ranar bakwai yaron yaci sunan Sajjad, bayan suna ne da jameela da sulaiman sukaje gidan musa sai tadi ya fara nisa lokacin tana riqe da yaron tace: baban boy wannan yaron wani irin suna ka sanya masa mun san dai akwai sajida mace amma ban san ana sanyawa namiji irin wannan suna ba ?

Sai sulaiman yace: "ina ruwanki ko kuma so kike kiyi masa shishshigi ki bari mana kema idan kin samu naki kisa masa duk sunan da ki kaga ya fi miki ?

"Aa haba aboki daga tambaya ai ni ta tambaya ka bari na bata amsa kawai" musa ne ya fada yana dariya.

"Yanzu kam kai ka sani daka biye mata.

sai ya fara da ce mata ai kinsan nana fadima tana da 'ya'ya guda uku ko?

"Eh" tace.

Kuma akwai sayyadina hassan da sayyadina hussaini wanda aka kashe a karbala.

"Ni ban san wannan ba" jameela tace.

Ya kamata koda wikipedia ki hau kiyi searching na wannan kisan, a takaice dai yana da yaro wanda shi daya ne ba'a kashe ba a inda aka kashe sayyadina hussain, to shi sunan yaron aliyu babansa kuma hussaini dan aliyu dan abiy dalib, to shine saboda tsabar yawan ibadarsa sai yan uwansa sharifai suke masa laqabi da Assajjad Ma'ana mai yawan Sujjada wato ibada kenam, Da fatan kin fahimta?

"Na fahimci wani abu amma zan kara bibiyan wikipedia kamar yadda ka fada mini dan ina son ina sanin tarihin magabata" jameela ta fqda tana dariya.

Suna isowa daf a zancen sai jaririn ya tashi yasa kuka kawai sai Iklima tace: bani dana dan baki san darajar shiba tunda baki haifa ba.

"Eyey ba komai nima kwana nawa ne, ai kamar yau nima zanyi yaro kam" ta fada tana mika mata shi a lokacin sai ta juya ga sulaiman tace masa: "Ko ba haka bane angona" da alamar wasa.

"Can ta matse muku keda kawarki..."

"af yanzu fa tara tayi!" Inji sulaiman yana duba agogo

"eh mana to sai meye, ko a daji kake" musa ya tambaya.

Nan take iklima ta mikawa musa jariri tace masa bari mu shiga ciki mu tattauna da kawata, bata ko jira amsa ba ta ja hannun jameela uwar daki.

"Mata mata mata Babu mai iya muku sai allah" sulaiman ne ya fada yana dariyar mamaki.

Iklima taja jameela daki da dauko mata wasu turare na hayaki dana shafa irin nasu na mata a cikin abun da bai wuce dakika shabiyar ba ta kara koya mata wasu muamala na musamman da yadda ake tarairayar miji da salon kwanciya kala-kala.

Anan ne ta fahimci cewa lallai wanda yayi gaba yayi gaba ne a harkar zaman aure.

"Ke kam ki sake matar mutane mana haba kina ta mata musu lokaci..." taji muryan musa ne.

"Gamu nan dai baban sajjad muna hanya, mun ma gama" iklima ta jawo jameela suka shigo falon.

Tashi sukayi gabaki daya suka raka su har bakin inda motar da sulaiman ya karbu aro agurin babansa saboda yawon ziyara na musamman, a hakan sukayi ban kwana tare suka fito daga anguwar kasuwan mata suka wuce unguwansu na byefass.



*** *** ***



Haka dai rayuwa tayi ta dadi a tsawon hutun wata daya da sulaiman yake sun sha soyayya tare da matarsa na qin karawa kamar bazasu rabe ba, tun daren washe gari zai koma jameela ta shiga yi masa kuka akan kada ya tafi a lokacin da abun ya fara yaw ne sai ya kamota ya rumgumeta a jikinshi ta yadda suna iya jin numfashin juna.

Yana cewa: " haba masoyiyata farin cikin raina abar alfaharina ki sani kece kadai a zuciya ta babu wata nima a gaskiya ban so ace nayi nisa dake ba, dan bani da wani buri da ya wuce na zauna tare dani kina shayar dani madara da zuma na soyayyarki, ban san wata 'ya mace ba bayan ke, ki yarda dani bazan kusanci wata ba bayan ke ki karfafai guiwa ta akan neman halal, ko so kike na ginawa wuta naman iyalina da wuta, ko so kike na daina"

Nan take ta fara kuka tana cewa: fadin wallahi ni bana son inji kana kiran wuta dan wallahi bana son allah ka shiga wuta, amma muddin duk yadda rayuwa zatayi damu inaso ka kasance tare dani karka gujeni kada ka kini wallahi ina sonka irin son da uwa bata yiwu danta.



KASH MU HADU PAGE 007


&& AUREN WUCIN GADI &&

Page 007

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Matasan Aduwa

Sulaiman Terry-g'

(Dan Oga)

Isa Shadulin'

(Isa Chairmo)

Bunu'



(Baban Bariki)

(Aduwa Biyu Kasuwan Mata Gombe)



DON MASU KARATU

Manzon Allah S.A.W.A Yace: ((Ku Sanyaya Abinci, Dan Babu Albarka A Cikin Zafin))

TIBBUN NABAWIY S11



To ki kwantar da hankalinki na ma fasa yin wata dayan sati biyu zanyi ko angama mana ko ba'a gama ba gwanda na kaiki can ko a wani gida mu zauna tun da bana tsammani za'a wuce wata daya za'a karasa aikin yana isowa nan ne a zancensa, sai jameela ta janye jikinta daga nashi ta fuskance shi da kyau ido sha6e-sha6e da haweye tace: kayi mini alkawari bazaka dade ba?

"Eh nayi alkawari, amma kuma naga kamar baki yarda" ya fadi hakan ne a yayinda yake kura mata ido dan fassara sirrin zuciyarta.

"Ta amsa na yarda mana Mai Sanyi na"

A fannin jameela tana jin hakan amma ta kasa nitsuwa duk da cewa sulaiman bai taba mata karya ba a mu'amalarsu na zaman auren kai tun ma kafun ya aure ta.

Da yaga kamar tana cikin kokonto sai shi kuma ya matse bai nuna mata ya fahimci hakan ba, sai ma kawai ya jawota jikinshi ya fara sarrafata da irin salon soyayyarsa na musamman ana haka har ta gama dauke wuta, har sukayi abunda sukayi bayan abun da ya faru ne ya samu tayi bacci shima ya kwanta maimakon yayi bacci sai yayi tunane-tunane akan yadda yake tausayawa matar tasa idan har baya nan duk da cewa baya zarginta kuma bai taba jin zata iya cin amanar saba duk da yadda take nuna tsananin damuwar ta akan tana rabanshi kusan kullum, a haka yayi ta irin wannan tunanin har sarkin barayin bauchi ya sace shi yayi sama dashi.





*** *** ***



Kiran asuban fari jameela ta tashi taje ta dauko heater ta daura musu ruwan zafi bai dauki wani tsawon lokaci ba ya tafasa ai kuwa nan take ta shiga tayi wanka tana fitowa kuwa sai ta jira ta tsantsame sannan ta nufi cikin kicin ta kunna gas cooker nan take ta debo fulawa gwangwami uku ta dauko kuka ta gauraya guri daya ai kuwa sai ta dauko ruwan kanwa wanda ta masa gora na musamman daman sai kawai ta saka ta fara gwabawa ai kuwa ruwa yana tafasa ta fara jefa danwake yan kanana, tana gama jefawa sai taje ta dauro alwala tayi sallah raka'a biyu na nafila, a karkashin zuciyarta kuma tunanin tafiyar mijin tane fall a zuciyarta data idar da sallahn sai tayi ta addu'a akan allah ya kaishi lafiya ya dawo lafiya.

Ai kuwa da gudu-gudu sauri sauri taje ta samu har dan waken data daura ya dago sama alamar ya nuna kenam, saukewa tayi ta koma dakin ta samu mijinta yana ta bacci da yake yana fada mata idan ta riga shi tashin asuba ta tashe shi, ai kuwa tana zuwa ta haye kan gadon ta kwanta a kusa dashi a hankali ta daura bakinta a setin kunnensa sai ta fara hura masa iska a hankali, nan take sai ya canza numfashi sai ta kara kura masa ta yadda yafi na farkon sai take ce masa "mijina wannan shine kadai lokacin da zaka baiwa ubangijinka a cikin sa'annin da kayi kana bacci"

Ji yayi kamar a mafarki nan take ya tashi cikin nitsuwa ya fara gabatar da adduan tashi daga bacci, yana gamawa ya bita da salati, yana dubawa sai ya ganta a gabansa ya sun banci kumatunta sannan tace masa: are you ready to bath?

"Yes dear" yace mata yana dariya.

"To tashi kaje ko in daga ka in kaika!" Ta fada cikin raha.

"Ke da bakya cin abinci ma yaushe zaki iya dagani" ya fada ya tashi ya nufi bathroom yana zuwa yaga ruwa mai dumi baiyi mamaki ba ya dauka ya fara wanka.

Ita kuma sarkin ayyuka cikin kicin ta nufa ta ta shirya musu danwaken nan ta yanka musu koyi a sama ta sanya kabeji wanda tun jiya ta saye shi saboda tafiyan mai gidanta, ta kaishi dinning table ta ta shirya komai da duk abun da za'a bukata.

Yana fitowa sai ya ganta tana tahowa yace: sarkin ayyuka sannunki ko?

Ta amsa da yawaa ta dauko masa jallabiya cholate colour da wanda ta bashi ya saka ya koma ya dauro alwala ya tafi masallaci, dan a wannan lokacin wasu masallatan ma sun fara sallah.

Nan take jameela taje tayi sallahn asuba a dakinta, tana idarwa sai tayi ta addu'o'i dabam-dabam akanta da mijinta musamman da takeji gabanta yana yawan faduwa daga ta tuno da tafiyar mijin nata duk da hakan yana faruwa take Uzbini (Auzubillahi...) da neman tsarin ubangiji.

Komawa bathroom ta sakeyi ta cancara wani sabon wanka na musamman ta shirya tayi kwalliya na musamman dan raka maigidanta ai kuwa ta hadu dan a wannan wankan ne duk wasu rukunai na kyawunta suka kara bayyana ta wani kashe dauri ta ta dauko jakan da sulaiman zai tafi da ita ta kara kade masa ai kuma tana cikin wannan halin sai taji sallamar mijin nata sai kuwa ta amsa cikin kulawa.

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment