Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunsa akan kafadunsu kamar wasu kananan yara ya nufi bakin inda aka ake parking mototi.

Sai wani daga cikin yan union din da alama shine babbansu yace: alhaji idan ba damuwa na hadaku da wani mana yayi driving naku tunda shi drivern naku ma ga halin da yake ciki.

Babu ko musu abba ya amince.

sai ya juya ga daya daga cikinsu yace: Ya'u ka jasu kawai mu zamu taho a motar asibiti mu hadu kawai a can.

Nan take sukayi musayen

Number saboda idan sun iso medical center zasu iya kiran abba su sanar dashi.

Yau ya karbi mota da yake tsohon driver ne tafiya yake a titi cikin kwanciyar hankali kuma yake gudu basuyi awa daya ba kuwa sai wayar musa ta fara ringing.

Baiyi niyyar dauka bama sai yaji abba yace: ba kiran ake yi a wayan wani ba ya daga mana.

Ai kuwa yana duba numbern wanda yake kira, sunan JAMEELA Ya gani baro-baro a kan sensorn wayar ai kuwa sai ya kara rushewa da sabon kuka yana fadi: (Meye zan fadawa jameela akan sulaiman ta fahimta)

Sai abba ma yaji wani hawaye na tausayin jameela ya sirnano masa.

Ya ciro handkecip ya goge hawaye.

A lokacin wayar jameela ta katse.

Ko minti daya baiyi da katsewa ba, wayarsa ta kara daukan ringingtone abba yace: ka sakata a silent amma karka daga dan idan ka amsa zata iya fahimtar halin da ake ciki gwanda ka bari har sai mun koma gida daga baya kawai tasan komai zaifi.

Baza mu sanar da kowa ba sai mun koma gida.

Shi kansa dan union din sai da tausayi ya kama shi, shima yayi ta musu nasiha.



*** **** ***



Da kamar misalin karfe daya suka isa gida ai daman umman sulaiman tayi ta kiransa taji ya kashe tasan cewa akwai matsala, ai suna shiga gida sai jama'ar gidan yanayin sulaiman da garba ne ya fassara musu halin da ake ciki.

nan take Abba yace: To sai dai muyi hakuri sulaiman kam wanda yafi mu sonsa ya karbesa, Allah ya masa rasuwa sakamakon hatsarin da sukayi a wani jeji a garin bauchi.

Nan take gida ya hautsune da kuka ummansa daman tana cikin daki amma tana jin duk abun da yake fada, su kuma yaran gidan sai gidan ya gauraye da kuka da ihu, ihunsu har ya ankarar da yan unguwar halin da ake ciki inda suka ringa shigowa dan jin meye yake faruwa

Kafun kace meye labari ya karade anguwar gaba daya.



JAMA'A BA JAMEELA KADAI AKA YIWA RASHI BA NIMA ANTYNA #LAMRATU_M_LADAN TA RASU INA NEMAN ALLAH YA JIKANTA



KASH MU HADU A PAGE 011

&&AUREN WUCIN GADI&&

Page 011

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



I dedicate this page to my heart desire Balkisu S.A Chilo





DON MASU KARATU

Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Karanta Iyali Daya Ne, Daga Abubuwa Biyu Masu Sauki...))

NAHJL BALAGHA 4:564 H142





Jameela ta tashi ne a yau cikin wani irin yanayi na daya ciwon kai na biyu kuma ta kasa samun nitsuwa akan tana so taji shin mijinta ya isa lafiya ne, haka nan dai ta dafa indomie miemie guda biyu saboda ta karya, tana dafa abincin tana ta try na numbern sulaiman amma baya tafiya, gabanta sai kara faduwa yake amma ta kasa amintarwa da ranta ce cewa mijinta yana cikin wani hali ma balle ta darsa a ranta ya rasu ta dauko zata ci kuwa ai tana farawa kuwa sai taji bazata iya ci ba sakamakon yadda kirjinta yake bugawa.

Kawai sai ta ciro waya ta fara neman wayar musa akan ko yana da labarin abokinsa ya isa lafiya kuwa, haka kuwa akayi har sau biyu bai daga ba hakan yasa ta yanke shawarar ta kira iklima dan ta tambaye ta.

Har sai da ta kusa yankewa sannan sai iklima ta daga kamar ba komai.

Tace: Assalam kawata!

"Wa'alaikumus salam..."

Iklima tace: wato sai yau kika tuna dani ko? Ta fadi hakan amma tana ta kokarin boye abun da ta sani na rasuwar mijin nata!

Jameela tace: ai na kira baban boy bai daga ba har sau biyu nace to bari na kiraki ko zaki hadani dashi?

"Ayya ai ya tafi Bauchi yau da asuba amma yau zai dawo insha allah" inji iklima.

Jameela tace: ayya to kina da labarin ko jiya sulaiman yayi waya da baban boy?

"A'a wallahi bai fadamin ba amma dai yace min ya rakashi kuma ya kaiki gida daga baya" inji iklima.

Jameela tace: amma dai idan har kunyi waya ki tambaya min shi kice tun jiya bamu yi waya dashi ba amma yace masa ya kira ni.

"To shikenam sai anjima"

Bata bari ta bata amsar tambayarta ta ba, ta datse :wayan, hawaye ne ya cika idon iklima fal tana allah allah su karasa maganar saboda kar ta fara kuka ta fahimci akwai wani abu a kasa.

Haka nan dai kuwa ta fara tausayawa halin da jameela take ciki.



*** **** ***



Da kamar misalin karfe 1:40pm ne suka kira alhaji suka sanar dashi cewa an dauko gawarsu sulaiman da wadanda sukayi hatsari suka rasu tare yanzu haka suna Medical center gombe, zai iya zuwa su ganshi, nan take alhaji ya kira yace garba ya kira masa jameela a waya yana kiranta ya mika masa.

Ringing daya tayi jameela ta daga tace: Assalamu alaikum Garba.

"Bashi bane abbansa ne" abba ya fada.

Jameela tace: Abba ina wuni?

"Lafiya kalau jameela yanzu ina so kizo gida nan jekadafari ki same ni ina jiranki" abba ya fada.

Jameela tace: Abba lafiya kuwa?

"Lafiya kizo dai ki same ni" abba yana fadan haka ya kashe wayarsa nan.

Sai kawai ta fara cewa allah kasa dai ba wani abu bane ya samu sulaiman.

Da yake a lokacin tayi sallahn azahar kawai dauko hijabinta tayi ta sanya ta kulle gidan ai kuma da yake basu da tazara da titi sosai tana isowa bakin titi sai taga wani mai napep ta tare shi tace malam jekadafari zaka kaini yace: dari a hamsim zaki biya da yake tana sauri ko musu babu ta hau tun a keke napep din ta ciro dari biyu ta bashi yace: hajiya ba 50 naira fa.

Tace: babu komai ka rike kawai.

Yayi ta godiya da saka mata albarka.

Nan take suka iso gidan kawai fita tayi ko waiwayan mai napep din bata yiba, ta shiga gidan cikin gudu-gudu sauri-sauri ai tana shiga sai taga bakon yanayi sai ta hango garba da sulaiman suna zaune a gefe daya.

Ita kuma kanwar sulaiman wato khadija tana ganinta sai kawai ta rushe da sabon kuka sai sauran yan gidan suka dauka sashen matan ta nufa ta fuskanci inda khadija take.

Tace: khadija meye ya faru ki fadamin mana? Karki barni cikin rudu a lokacin ne umma ta jiyo sautinta daga daki sai ta fito, ta kama hannun jameela jameela abun da bata taba gani ba a rayuwarta da umma shine taga umma tana kuka, umma tace: jameela hakuri zamuyi allah yayiwa sulaiman rasuwa sunyi hatsari a hanya.

Nan take jameel 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~a taji duniyar na juyawa tace: a'a ba sulaiman dina baka, aa umma tana fadan haka ta sulale daga jikin umma ta fadi sumammiya.



*** **** ***



Duru-duru take gani tana bude idonta taga ashe ummanta ne a gefe kuma khadija ce, khadija tana ganin haka ta ruga da gudu tayi waje tana kiran yaya musa, basu dade ba kuwa sai gasu sun shigo tare, tace: musa ka fada min gaskiya wai da gaske ne mijina ya rasu ta fadi hakan ne cikin kuka mai tayar da hankalin mai saurare.

Shima kukan ne ya sake kama shi yace: jameela allah yayi wa sulaiman rasu yanzu haka gawarsa tana wannan asibitin ta fara kuka rikitar da mai saurare ummanta ta fara rarrashinta.

Nan take ta fara cewa ita kan sai an kaita taga mijinta, sukayi ta rarrashinta akan an rufe gurin sai gobe za'a masa sallah sai dai ta bari sai gobe, ana cikin hakan sai ga abbanta ya shigo, irin tsananin damuwar da take ciki yaki ya buya ga abban nata, shine yasa baki akan ta bari sai gobe kafun a masa sallah zata ganshi haka ta hakura tayi ta kuka khadija ma zama tayi a gefenta tana taya ta kukan dukka mutanen wannan dakin gaba daya hankalinsu ya koma ga su jameela kowa sai tausaya mata yake musamman idan sukaji watan ta shida da aure mijinta ya rasu.



Haka nan dai jameela ta nuna ta damu akan a sallamesu a asibitin ana sallamarsu kuwa da kusan karfe goma dan a lokacin ne ruwan da aka daura mata ya kare, sulaiman ya dauke su yayi hanyar gidansa da ita tare suka kwana da ita, sannan ya mayar da su ummanta gida ya biya ya maida khadija gida.



Haka nan dai jameela ta kwana tana kuka idan ta gaji sai ta tashi tayi sallah iklima tayi matukar tausaya mata akan halin data shiga haka har gari ya waye jameela haka taki taci komai da kyar da sidin goshi ta yarda ta dan sha shayi ba ko madara, hakan ma dan musa yasa baki ne,

Da kamar karfe bakwai garba musa ya dauki mashin ya kai jameela har gidan su abba taga gidan ya cika babu masa tsinke tun daga matayen anguwa wasu kuma yan uwa da abokan arziki na kusa, ai kuwa suna shigowa sai sabon kuka jama'a suka fara ai itama kuwa sai tayi ta kuka tana cikin kukan ne sai sukaji ance to za'a shigo da sulaiman motar asibiti tazo.

Haka aka mammatsa aka shigo da shi a makarar asibitin aka kaishi daki jameela tana ganin an wuce dashi dakin da garba yake kwana ta shiga tana ganin an ajiye shi sai tayi birki a lokacin ne, ta tsaya ta hange shi a cikin likkafani tana kure masa ne ai kuwa sai ta fadi ta kara suma.

Haba wa ai sai gida ya kara hautsinewa da hayaniya.



KASH MU HADU A PAGE 012


&&AUREN WUCIN GADI&&

Page 012

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



I dedicate this page to my arabic student of Mahdi Scout Fudiyya Ceceniya yashin Dam gombe





DON MASU KARATU

Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Tsoron Allah Shine Shugaban Dukkan Halaye))

NAHJL BALAGHA 4:613 H404



A wannan karon ma dai kamar wancan lokacin tana farkawa daga dogon suman da tayi sai ta duba gefe da gefe sai kawai taga umma faty kanwar mahaifiyarta tana zaune a gefen gadon tana jinjina irin halin da jameelan take ciki, a gefe kuma kawarta ce ikilima matar musa, da kuma khadija wacce bata cikin hali mai dadi.

"Ina miji na? da gaske ne mijina ya rasu? Na rabu dashi kenam har abada?" Haka jameela ta rinka sanbatu,

Wannan kukan kamar kara alerting din khadija ya itama ta sake fashewa da sabon kuka tare da sheshshekar hawaye.

Umma faty tana ta bata hakuri tana ce mata: yanzu ashe jameela da iliminki da hankalinki da girmanki kina so ki afka cikin sabon ubangiji kina nuna fushinki akan abun da allah ya kaddara miki na rashi, ni bazan hana ki kuka ba saboda kuka yana rage bakin ciki na radadin rashi, amma na tambaye ki shin yarda da kaddara alkairi da akasin sa baya cikin akidar musulmi? Ko kuma kina sone ki nuna kinfi ubangiji son bawansa wanda ya kaddara masa rasuwa?

Ki fada min shin kin ubangiji sonsa ne, kuma kina tuhumar ubangiji akan Adalcinsa ne?

Ki fada min kawai.

Da ta sata a gaba sai da tace: a'a?

To, ki bar kuka ki fawwala dukkan al'amarinki ga allah shine kadai mai yaye bakin ciki a duk lokacin da musiba ta samu mutum.

Maganganun da umma faty ta mata na nasihohi ba karamin tsumata yayi ba tare da khadija da ikilima wadanda a sashi guda suna kuka ne kawai dan tausayin jameela a wancan lokacin.

"To yanzu umma faty yanzu kina ganin yanzu a duniyar zan iya samun kamar sulaiman ne kuwa lallai nikam ni nayi rashi wanda bana tsammani zan mai da gurbinsa" jameela ta fada tana share kwalla.

Sai umma faty ta rufe bakin ta tace: haba jameela karka fadi haka yanzu ke kina tsammanin wayonki ne ya baki sulaiman din ko da kin sanshi, to ki mai da al'amarinki ga allah zai kawo miki abun da yafi shi..."

Jameela dai kawai jinta take tun bata yarda har tazo tana ganewa, da yake umma faty ta kasance mai tarin ilimi da hikma dan wanda take aure babban malami ne na addini, kaga kenam ko da ba tayi karatu ba akwai tsammanin haka balle daman ita din ma ba kanwar lasa bace.

Hakan kuwa akayi alal a qalli sai da su jameela sukayi kwana uku sannan aka sallame su a wannan asibitin haka sukayi ta zaman takaba tare da ikilima da umma faty ai kuwa sai gaisuwa ya zama biyu da ta'aziyya da gaisuwar maras lafiya, gaske a cikin ran jameela cike yake da mamakin wasu jama'ar da take gani na musamman wadanda bata tsammanin sulaiman ya sansu ai kuwa haka daga garuruwa dabam dabam ana zuwa gaisuwa idan anje gidan su na jekadafari sai azo gidansa na byepass a gaishe da matarsa, tsawon wannan lokaci.

A ranar safiyar bakwai ne na rasuwar sulaiman sai musa ya tara taro na musamman dan karantawa marigayin al-qur'ani da niyyar allah ya kai masa ladan ya gafarta masa, akayi kunu da masa aka raba raba sadaka da neman allah ya gafarta masa, haka kullum musa yake kawo matarsa da dare kuma ya koma dare ya dauko ta.



*** ***

****



Haka nan jameela taso ta koma gidan tun bayan kwana arba'in da rasuwar mijinta amma babanta ya tubure yace sai ta karasa iddanta duk sannan ta dawo, hakan kuwa akayi ta zauna a gidan ba saka turare ko mai mai kamshi aka hanata saka lalle ko wani ado na musamman na mata tsawon wata hudu da kwana goma na iddanta, ga tunani na rashin mijinta ga kuma an hanata kwalliya ko wani ado na mata hakan yasa ta canja jar fatarta ta wani dishewa ta kara rama kai kace ba ita bace jameela idan ka santa a baya.

A lokaci da dama ikilima tana kokarin ta bayyanawa jameela akan cewa daina wasu ado da kwalliya ga mai takaba wannan wani gargajiyanci ne na yan mazhaba ba wai daga allah yake ba ko daga annabi.

Sai jameela tace: to ai wannan shine al'adarmu kuma na tabbata yadda abbana ya zafafa akan wannan abun muddin yazo ya taras ko labari ya riske shi, ba karamin matsala zamu samu ba dashi?

"Sai kici gaba da zama cikin kuncinki ke daya" ikilima ta fada mata tana mata dariya.

Haka dai tana dawo wa gida ne abbansu sulaiman yaje ya samu abbansu jameela ya dauki wasu kudade makudai yace: wannan shine tumulin takaba na jameela.

"Haba alhaji duka wannan ai yayi yawa.

yace: a'a baiyi ba gaskiya wannan haqqin tane.

"Allah ya saka alhaji shi kuma sulaiman allah ya gafarta masa zunubansa mu kuma idan tamu tazo allah yasa mu ciki da imani" abban jameela ne ya fada.

Haka dai suka rabu suna yiwa juna jajen abun da ya faru na sannan sukayi sallama da juna abban su sulaiman ya nufi gida da motarsa daga nan kuma abba ya shige gida...?



**** **** ****



KASH MU HADU A 013



(Meye Kuke Tsammani A Idan Musa Yace: Zai Auri Jameela ya hada su da ikilima) ???


&&AUREN WUCIN GADI&&

Page 013

Na



Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



I dedicated this page to my mentor Aunt/sister

SHAFA'ATU S.A CHILO

(Bundu Wailaru Gombe)





DON MASU KARATU

Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Farkon Addini -shine Saninsa -Allah-...))

NAHJL BALAGHA H1



Bayan abban ya shiga gida ne, umma ta fara masa maganar ko waye yazo yace mata: Baban marigayi ne, amma ki kira mini yarinyar nan!

"Jameela! Jameela!! Jameela!!!" Umma take ta fada a yayin da ta nufin dakin da jameela take.

Tayi ta kwalla mata kiran ne a lokacin tana sallah shi yasa bata amsa ba, umma tana shiga dakin sai ta ganta tace: to idan kin idar abbanki yana kira, tana fadan hakan kuwa sai ta koma ta sanarwa da abba sannan ta zauna a gefen sa a kan taburma.

Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai ga jameela ta fito ta durkusa ta masa sannu da dawowa ya amsa cikin fara'a sannan ya mata nuni data zauna a gefen ummanta, ai kuwa tana zama sai abban nata ya fara cewa: Yanzu haka alhaji muhammad deba ne yazo min wato baban marigayi mijinki sulaiman, sannan ya bani wannan yace hakkin kine a baki, kudi ya ciro masu yawa a leda ya bude ya ajiye a gabansa.

Tun bai karasa maganarsa ba jamela ta fara hawaye taso ta boye kukan iya karfinta amma ina sai da kukan ya bayyana.

"Yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba akan tuno da mijin kiba, duk da cewa kuka wata alama ce ta rahama da nuna soyayya akan wanda mutum ya rasa, duk da cewa kuka yana rage bakin ciki amma baya taimakon shi wanda akayi kukan danshi ba, kawai addu'a tana amfanar mamaci a kowani hali..." abba ne yayi ta mata wannan maganar hakan yasa jikinta yayi sanyi kalau, sannan sai ya karasa tuna mata da maganar kudin da aka kawo mata.

Tace: abba bana bukatarsu tun da babu abun da na nema na rasa komai kana mini kawai ka rike su bani da bukatarsu gaskiya.

"A'a jameela wannan hakkin kine kawai dai kice masa ya ajiye miki su nan da wani lokaci tun da zaki iya bukatar su ko wani lokaci" umma ne ta fadi hakan inda tana maganar tana fuskantar jameelan.

Jameela tace: to abba ka ajiye su agunka!

yace to shikenan jameela allah ya miki albarka tashi kije ciki, ai kuwa hakan tayi ta shiga ciki.

Ta kunna wayarta ta hau yin sana'ar kullum (facebook) tana hawa kuwa sai taga ikilima a online hakan yasa ta mata sallama har ta roketa akan ta taimaka tazo mata su wuni man ta nuna mata ba komai idan har gobe abba ya barta zata zo.



**** **** ****



Da washe garin ranar talata ne wanda yayi kwana goma na dawowar jameela gida da safe ta nufi dakin abba dan ta gaishesu a lokacin da su yusra kuma sun maida bacci.

"Assalamu alaikum" jameela ta fada.

"Wa'alaikumus salam" kara so mana, abba ne ya fadi hakan bayan ya gane muryarta.

Tana shigowa ta durkusa ta gaishe shi da fulatanci ya amsa cikin kulawa da nuna soyayya, sai jameela tace: abba ina sone yau naje ziyara gidan su kawata iklima matar musa!

"Jameela baki da matsala zaki iya zuwa amma ina kara miki nasiha daki lura da kanki kada ki tsaya sauraran maza a layi duk da nasan ba halin ki bane

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment