Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Cikin mamaki yace: wannan kwalliyan fa sai kace wacce zata raka wani gwamna?

"Eh ai gwamna daman zan raka amma na cikin zuciyata" jameela tace.

Yanzu kam sai kasa kayanka sannan muje mu karya ko? Yace duk yadda kika fada haka za'ayi.



Ina so nayi amfani da wannan damar wajen mika gaisuwa ta musamman ga RUQAYYA ADAM Yar mutan Gusau Ki Huta Lafiya

KASH MU HADU A PAGE 008


&&AUREN WUCIN GADI&&

ýÿýÿýÿ Page 008ýÿýÿýÿ

Na



©Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga M=Square Nice Guys

Musa Lil-m'

Musa Yellow'

(Obidien)

(Ceceniya Police Barrack Gombe)



DON MASU KARATU

Imam Baqeer A.S Yace: ((...Dukkan Komai -Na Addini- Yana Cikin Littafin Allah Da Sunnar Annabinsa))

USULUL MINAL KAAFI J1/62



Ai kuwa dauko masa wasu kaya tayi wasu kufta blue da aiki zubin hannu suma blue an masa shige da bakin, ta na mika masa yana shiryawa kuma tana ta bashi labarai irin nasu na masoya da suka gama shaquwa da juna yana gama shiryawa ta riqe hannunsa kamar wani jariri ko mai koyan tafiya ta kaishi bakin dinning table, ta zaunar dashi.





"Ni yau ni zan baka abinci saboda ya zamo nina ciyar dakai kafun ka tafiya" jameela ce ta fada saboda tasan shi baya son ana bashi abinci kamar yaro karami.

"Shikenam tun da babu yadda na iya" haka sulaiman ya fadi hakan kamar wanda akayi wani galaba akansa.

"Hmm Muci kawai tun da baka so" ta fada tana mai bata rai.

Sai sulaiman yace: aa haba dan allah meye na kukan kuma ?

"Ni ba kuka nakeyi ba" ta fada tana mai basarwa.

Yace: to kiban abincin mana haba wasa fa nake miki haba sahiba muddin kikayi fushi dani yanzu na dole in fasa tafiyar nan saboda ba zanje wata uwa duniya ki daura min tunanin ki ba, bakin ciki ya kashe ni a can!

"Nina fada maka raina bai baci ba" tace.

Yace: to idan haka ne ki bawa mijinki a baki, ta hakan ne kawai zan yarda ranki bai baci ba!?

Matsowa tayi kusa da kurar da yake zaune ta bude ta gauraya masa gabansa kawai sai ta fara bashi, yakai loma daya sai yace: kefa ya bakya ci ?

"Ni ai ina gidan! Kai kuma da zaka tafi ta yiwu ma duk abun da kaci kafun shiga ya zazzage!

"A'a ban yarda ba kawai nima ki bani cokali ina baki a baki"

Hakan kuwa akayi daga baya tana bashi yana bata suna ta tadin soyayya.

Basu san lokacin da kowwanensu yaji ya koshi ba.

Wayar sace tayi ringing yayin da wani zikiri na larabawa ya cika falon sai yace: "Abokin ne ya kira"

Ya daga ya kara a kunnensa "Assalamu alaykum" sulaiman ya fada.

Musa ya amsa masa sai yace "haba sarkin soyayya ayya kana son komawa kuwa? "To meye ka gani" sulaiman ya fada.

"Naga baka neme ni bani yanzu har shida saura"

Sulaiman yace: Haba nasan zaka zo ko ban kira kaba.

"Sai ka fito mu tafi ai?

sai sulaiman yace: ka shigo dai mu fita tare. :

"To gani nan" yana kashe waya sai kawai yaji sallama nan take ya turo kofa ya shigo saka makon daman yana jiran zuwansa shi yasa bai ma kulle kofar shiga da kuma na falon ba.

Cikin girmamawa sukai musabafa sulaiman ne ya fara mikawa musa hannu suka gaisa, sai jameela ta dan rusuna kadan tace: Baban boy ina kwana?

"lafiya kalau" yace ya kuma amsa mata ne cikin kulawa da mutuntawa.

"Bari na kawo mata break fast" jameela ce ta fada tana fadan hakan kuwa sai ta juya da nufin tayi cikin kicin.

"Haba dan allah barshi ni ai bana karyawa sai 10" ki tambaye shi sai yayi nuni ga abokinsa.

"To shikenam"

ta fada daga nan ne sai sulaiman yace: mai sanyi zu ki zauna anan yayi nuni da wata 1 sitter sai yace: aboki na zauna kaima anan zamu yi wata magana yayi masa nuni da 2 sitter yana zama kuwa sai shima ya zo kusa dashi ya zauna.

Sai yace: daman ina sone in tuna muku abun da kuka sani musamman ma ke jameela, kin ga yau zan tafi na fada miki zanyi iya kokari na nan 2weeks zan dawo amma dan allah idan na tafi a iya tsawon yadda na kasance acan duk abun da yake damun ki kada ki boye ki tambaye shi akan komai na rayuwa bani da kokonto akansa idan kina da damuwa idan har bazaki iya fada masa ba ga kawarki maman sajjad ki fada zata iya sanar mishi?

Kaima abokina ga tanan sai yayi nuni da jameela yace: na baka amanarta ka kula da ita idan na tafi.

Sai musa yayi dariya yace: Haba abokina wannan ai bana tsammanin sai kayi mana wani tunatarwa akai!

"Ai kasan shi tunatarwa a har kullum yana amfanar mumini" inji sulaiman.

Jameela kuwa tun daya fara wannan zancen nasa ita kuma sai ta rasa meye yake damun ta ita ji kawai take gaban ta yana faduwa ta kuma kasa iya riskar meye yake damun ta, hakan yasa bata iya cewa komai ba.

Kawai ji tayi yace: sai ki tashi muje bakin terminus ko? Ko yau babu rakiyan ne? Musa ne ya fadi haka ai kuwa sai sulaiman ya amshe da cewa kai baka ga tayimin kwalliyan rakiya bane?

Ai naga kamar tayi wani jugum-jugum ne ko kuma kin fara tunanin kewa ne tun kafun ya tafi ?

Jameela tace: a'a haba sai kace yau ya fara tafiya?

"Sai ku tashi muje ko dan yanzu haka 6 saura kadan" inji sulaiman.

Jameela ce ta kulle gidan ta baya da kuba, a yayin da suka hau motar da musa ya dauko a gidan su sulaiman dan rakiya, sulaiman sai ya koma baya

"haba abokina dawo gaba mana" inji Musa.

Sai shi kuma yace: Idan na dawo gaba ita kuma matar tawa meye amfanin daukota kenam ?

" Allah ya shiryeka dai" inji musa.

Haka kuwa akayi musa na jan mota sulaiman da matarsa kuma suna ta hira irin na masoya da jinjina al-amarin rabuwar da zasuyi na sati biyu. Basu wani wuce dakika sha biyar ba sai gasu a cross din tsohuwar kasuwar gombe, musa baiyi wata-wata da suba ya shige cikin terminus ai kuwa sun isa da sa'a dan saura mutum daya ma motar ta cika nan take musa ya dauko kayan abokinsa da suke cikin karamar akwati ya kai masa but, a wannan lokacin ne aka rubuta masa rasit din biyan kudi take ya biya aka karbi number wayan abokin sa kamar yadda akan saba, karban numbern dan uwan mutum idan zaiyi tafiya.

Haka ya shiga motar sukayi bankwana yana dagawa abokinsa da matarsa hannu har motar ta shi suka tafi.

"To kema sai kizo mu wuce ko ? na kaiki gida"

tace: to tazo ta har ta shiga baya sai yace mata waye drivernki dan allah ki dawo gaba!

Tazo ta zauna da sulaiman ya lura kamar tana jin kadaici sai ya fara kawo mata labarai na gidan sa da sauran al-amuran rayuwa dan ya debe mata kewa.

Amma duk da hakan kawai yake take masa dan babu yadda ta iya ji ya zama dole amma daya bari ma shi da yafi mata a hakan dai ya kaita har kofar gida sukayi bankwana shi kuma ya wuce gidan su sulaiman da yake jekadafari dan ya mayar da motar ya kuma dauko mashin dinsa daya barta a gidan.



INA SAMUN KIRAYE-KIRAYEN JAMA'A A WAYA SABODA YAWA GASKIYA BAZAN IYA LISSAFO SUNAYEN SU BA AMMA SU SANI INA MUSU GODIYA INA SONSU DA FATAN ZASU NA MINI UZURI AKAN JINKIRIN FITOWAR RUBUTUTTUKA NA A KOWA CE RANA KAMAR YADDA NACE ZANYI NA GODE



KASH MU HADU A PAGE 009



&&AUREN WUCIN GADI&&

ýÿýÿýÿ Page 009ýÿýÿýÿ

Na



©Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Ummana Ta musamman

INNA ALTINE''

(Maman Suhairat)

(London Mai Dorawa Gombe)





DON MASU KARATU

Manzon Allah S.A.W.A Yace: ((Ya Aliyu Babu mai sonka sai mumini babu mai kinka sai munafuki))

RAWAHU MUSLIM







Komawan jameela gida ya zame mata kawar wani shiga kurkuku taga gidan gaba daya ya mata dubu sai tunane-tunane take tana kwance ta rasa tayi da nayi, sai taji kawai zata kira sulaiman dan gobe tana so taje wuni gidan su ko zai rage mata kewa akan tsananin zullumi da take ciki,

Ai kuwa sai ta kira shi yan bayyi ringing da yawa ba, ya daga wayar.

Ji tayi yace: masoyiya yanzu haka kina raina ina so na kiraki amma ban san meye zan fada miki shine na kasa nake ganin zan bari idan mun sauka lafiya zan kira ki!

"Ayya daman ina sone gobe inje wuni gidan mu dan rage kewa" jameela ce ta ke fada.

"Na sha fada miki cewa irin wannan dukka baki bukatar sai kin fadamin a zahirin gaskiya, you are free to do what you want i believed with your all behaviour, dan haka baki da matsala in dai anje a gaishe min da su umma da sauran yara.

"Nagode masoyi daka dauki 'yardarka gaba daya ka bani allah ya barmu a tare har gidan aljannah" jameela ce, ta fada.

" idan kuma zaki tafi zaki iya kiran garba ya kaiki a mashin ko ?

"Eh yadda kace haka za'ayi" ta fada

Yace: A'a yadda kike so dai.

"Yanzu kuna ina"

Yace: Eh yanzu haka mun iso yankin bauchi"

"Ayya to allah ya kaiku lafiya dan nabiyyur rahmati"

A tare suka ce: SALLAL LAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAHI.

Yace: Idan muka isa zan kira ki Bye.

Tace: Bye "I Love You"

Yace: "I Love You Too"

Sukayi ban kwana ai kuwa hakan yasa ta kara jin wani dadi na musamman bisa karfin guiwar da yake saka mata na nuna alamar ya yarda da ita dari bisa dari tana cikin haka ne sai bacci yayi awon gaba da ita da waje kusan 11 na rana.



*** ***** ***



Da kamar misalin 3:00pm musa yayi ta dialing numbern musa, amma sai dai tayi ringing shiru haka dai kuwa yayi ta try daga baya yaji ta a kashe hakan sai tasa yayi tsammanin ma watakila ya isa nema ya barta a caji ya tafi.

Da kamar misalin karfe karfe 5:30pm ne lokacin da musa yana kan hanyarsa ta dawo wa gida yaji an kirashi da bakuwar number, sai kawai ya daga ya kara wayar a kunnensa ai aikuwa sai yaji ance

"Assalamu Alaykum"

Mai maganar bai bashi damar amsa sallamar bama yaci gaba da cewa

"kaine Musa Abdullahi gombe Dan uwan Sulaiman muhammad deba wanda ya hau mota daga gombe zuwa kaduna da safiyar yau..."

Musa bai bashi damar ko da karasa maganar ba yake ce masa "nine nine nine"!!!

"Sunyi hatsari garin bauchi a hanyar su ta shiga yankin jos yanzu haka suna General hospital bauchi"

Ai kuwa sai ya ji maganar nan kamar saukar araduwa akansa sai ya gigice yama rasa ma meye zaice ya kuma rasa abun da zai fara yi, ai kuwa a haka sai shawarin kawai ya tafi jeka da fari yayi kawai dan ya sanar dasu abban sulaiman din yadda ake ciki.

Ai kuwa sai yaja mashin dinsa ya nufi anguwarsu gudu yake yana ta tunanin yadda al-amarin tafiyarsu zai kasance bai dauki wani dogon lokaci ba ya isa yana zuwa da yake ya saba kai tsaye yake shiga gidan yana zuwa gidan sai yayi sallama akan yana son yayi magana da abba umman sulaiman din nema da kanta Tace: ai Bai dawo gida ba.

Tace amma dai lafiya kam.

Kalau yace.

Sai yace to bari yaje zai kira sa a waya ai kuwa haka akayi yana fita ya kira shi a waya ya sanar dashi halin da ake cikin ai nan take alhajin sai yace: kasan ya za'ayi mubi komai a hankali mu bari gobe da asussuba mu tafi.

Amma yanzu zanyi waya da alhaji kasimu na bauchin akan yaje ya duba shi kafun mu taho, amma kada ka sake ka sanarwa da jameela da halin da ake ciki saboda kar kuma abun da sauki ta janyo mana wani abu dabam!.

Insha allah abbba bazan sanar mata ba. Ya fara sukayi bankwana ya kashe wayarsa.

Kawai sai ya kama hanyar gida yana zuwa sai ya samu iklima tana zaune tana karatun wani littafin addini na musamman na turanci mai suna "To be with the truthfull" wanda gaba daya ya dauke mata hankali gaba daya da alama tana kan wata gaba ta musamman ne a littafin yasa.

Sallama ya sake maimaita mata da karfi ai kuwa sai tayi firgigit ta duba sai ta ganshi ta amsa masa sallamar sannan ne ta fahimci cewa gaba daya wannan littafin ya tafi da hankalinta.

Zuwa kawai yayi ya zauna kusa da ita kadan sannan ya fara sakar zuci bai ce mata komai ba.

Daga nan ta fahimci akwai matsala ta juya ta fuskance shi gaba daya.

Tace: Baban sajjad lafiya kuwa naga ka shigo ba walwala ko dai an bata maka rai ne?

Yace: Gobe zamu tafi bauchi!

Kwatsam taji abun haka wani dabam

Tace: bauchi kuma meye zamuyi a can ?

Yace: sulaiman ne sukayi hatsari da mota a hanyarsa ta komawa gun aiki!

Sai kawai ta ajiye littafi ta fara Istirjai (INNA LILLAHI WA INNA ILAHIRRAJEEUN) Da fatan dai yana nan cikin koshin lafiya, ta fada.

"Kawai nima dazu yan Union suka kirani suke sanar dani halin da ake ciki amma wai sunce da sauki"

Amma na sanarma abbansu yace ba komai gobe zamu tafi da safe duk da kuma ya gargade ni akan kar jameela tasan halin da ake ciki dan haka kema na gargade ki akan kada ma wani dabam ya sani.



*** **** ****



Hakan akayi a gida lokacin da abba ya koma ya sanar da umma da sa'adatu da sauran yaran gidan akan halin da ake ciki ai kuwa sai suka fara koke-koke.

Nan take abba ya hausu da fada ya nuna musu ai ba rasuwa akace yayi ba balle suyi ta masa ihu a gida.

Ai kuwa sai ya gargade su akan kada jameela ko wani dabam, yasan halin da ake ciki.





KASH MU HADU A 010



&&AUREN WUCIN GADI&&

ýÿýÿýÿ Page 010ýÿýÿýÿ

Na



©Usman Umar Gombe &&

(Babangida Ustazu)&&

Call/WhatsApp

08137017208



Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Yayan

Anty LAMRATU M. LADAN wato

M. AUWAL M. LADAN''

(YAYA AUWAL)

(Byee pass Gombe)





DON MASU KARATU

Khalifa Omar bn Alkhattab Yace: ((Kada Ku Tsarkake Ni Da Abun Da Bani Dashi))

WASAYA WA NASA'IHUS SALIHIYN 12



Jameela kuwa tun lokacin data kwanta bata tashi ba sai wajen hudu saura, tana tashin ne sai taji gabanta yana ta fadu, kuma sai taji kanta yana wani irin sarawa, tana duba agogon bango kuwa sai ta fara fadin ((Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun)).

Nufin ta tashi ta daura alwala amma kuwa sai abun yaqi saboda ciwon kai din, sai tayi niyyar ta tashi tasha magani ai kuwa, kai kuwa a daddafe ta shiga cikin kicin ta bude Cooler irin yan madaidantan nan masu riqe zafi kadan ta sakawa kanta, sai taje ta ajiye akan dinning table sannan cikin karfin hali ta nufi bathroom taje ta dauro alwala, tana daukowa ta nufi daki inda first aid box yake ta dauko iya maganin da take tsammani zai sa taji sauki, ta nufi falo inda dinning table yake ta fara cin abincin bajin dadin abincin take ba amma haka take turawa dan ta samu maganin da zata sha ya tsaya a cikinta.

Abun da yake bata mamaki shine bata san dalilin yawan faduwar gaba wanda take yawan yi ba.

Da kamar kusan 5pm ta idar da sallolinta kawai sai mijinta ya fado mata a rai ta dauko waya ta kirashi shiru switch off kawai takeji sai tayi mamaki dan tasan ba halin sulaiman bane kashe waya, tunda tasan cewa wayar sa a cike take da caji kuma idan ta cika tana kaishi kwana biyu, kuma tasan yanzu ba lokacin sallah bane balle tace ko ya shiga sallah ne.

Watakila da yayi sallahr la'asar ne ya manta bai switch on na wayar ba.!

A haka ta tsaya ta da tunani taje ta kunna C.D Qira'a ta kunna na Alkhusary na suratul Maryama tana ji tana ta bibiya ko zata rage kuncin da yake damunta a cikin zuciya.



*** **** ****



Da asuban fari ne abba, musa da garba suka hau mota suka nufi hanyar bauchi musa ne yake musu Driving na motar amma baba yana baya garba kanin sulaiman yana gaba, tun bayan gaisuwan da akafi kafun a dau hanya babu wanda ya karayin magana ga dan uwansa, tafiya ta fara nisa a garin kashere suka ga ana ta shiga sallahr asuba abba yace: Su tsaya anan kasuwan suyi sallah sannan suci gaba da tafiya.

Hakan kuwa akayi suna tsaya ba tare da bata lokaci ba sukayi sallah suka daura tafiya ta alkaleri suka shiga.

Duk lokacin da suka hadu da road block abba ne yake musu magana da yake mutum ne mai cikar kamala hakan tasa basa bata musu lokaci, karfe takwas daidai sai ga su abba babban asibitin jahar bauchi nan take suka nufi fannin Emergency abba yana shiga sai yaje inda wata nurse take rubutu yace: madam barka da aiki ?

Tace: yawwa barka alhaji?

jiya ne akayi hatsari a mota daga gombe zuwa kaduna a gombe line amma sunyi hatsari a anan bauchi kuma nan akace an kawo su.

Tace: To ka duba duba kujerun waje zakaga wasu daga yan union ka tambaye su.

Nagode Abba ya fada ya juya su musa suna biye dashi a baya.

Yana fita sai yaga wasu mutum biyu da uniform na Yan union ya musu sallama suka amsa.

"Suna na alhaji muhammad deba nine mahaifin sulaiman wanda yana daya daga cikin wadanda suka taho a motar gombe line zuwa kaduna..." abba ya musu jawabi gamsheshshe Sai dayan yace muje ka duba shi suka shiga emergency abba yace a cikin duk wadanda aka kwantar babu shi.

To kenam yana cikin mutum hudun da suka rasa rayukansu a wannan hadari daya faru.

Musa yana jin haka ya fara fadin: Sulaiman ya rasu!!!

Yana fadan hakan sai ya wani mummunar hajijiya ta jashi nan take ya fadi yayi ta kuka mai tsuma ran duk mai sauraren sa, a lokacin ne garba ma ya durkusa yayi ta kuka sakamakon jin wannan labari mai mummmuna.

Yana kuka yana cewa: meye zan fadawa anty jameela idan ta tambaye ni akan yaya sulaiman, a lokacin da duk yan wannan gurin aka juyo da idanuwa kansu abba ne kadai baiyi kuka ba.

Yan union din suka cewa abba kaikam zaka iya komawa gida yanzu haka zamu wuce tare dashi da motar asibiti zuwa medical center gombe, a can zaku karbi gawarsa, abba yace dashi da waye suka rasu mutum hudun.

Suka ce masa: da driver ne da mace daya da maza biyu.

Abba ya juya kallonsa ga garba da sulaiman wayanda har a wannan lokacin basu daina kukan nan ba, abba ya fara rarrashinsu yana fadin: kuyi hakuri ubangijinsa ya fimu sonshi ya dauke shi, mu kuma mu masa fatan rahma da gafara ya jasu ya daura

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment