Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya kaita makwancinta ba kin fara ay bata mata yarinya ki ji tsoran Allah asiya .


Kinga malam a yimin shiru ban saka dakeba kuma ban ambaci sunan jikar kiba balle ki ce zaki fadamin baka,kema ban hanakiba idan ki ka dauketa kika rike,umman aisha fashewa da kuka tayi ta na cewa,yanzu asiya ni kike fadawa wadannan bakaken maganganun,yanzu idan uwarkice zaki fadamata haka,wallahi ni ba uwata ba saidai uwarki, innalillahi wa inna ilahirraju un,umman asiya ta dafa kan zuciyarta da hannu daya ,saigata a kasa ta fadi macecceya,mima ce da Amrish suka karaso dagudu suna jijigata suna kuka suna rokonta dan Allah tatashi,kada ta mutu ta barsu.

Dagudu mima taje ta kirawo babansu a gurin zaman makoki tana rabar tamasa abinda ke faruwa ,yana zuwa ya fashe da kuka ,yana cewa yanzu asiya abinda kikai kin kyauta kenan shikkenan,kema ki tattara kayanki ki tafi gidan ku nasake ki saki 2 "kuma ayanzu na keso kitattara kayanki ki barmin gidana,"kutumar ube wallahi ba ka isaba saboda na zagi wannan matar ,itafa tai abin zagin ,kodan tafadi tamutu Allah yayi daman lokacin ta yayi,, wallahi babu Inda zanje na fadamaka zama a gidanka daram,jitai Wani gigitaccen mari a kuncinta wanda yay sanadiyyar giftawar taurari daga idonta cikin bacirrai ta juro donganin wace takadiriyar ce tayi gangancin marinta ,wazata gani mima ce da Amrish sai huci suke ,suna kokarin dukanta malan ya dakatar dasu ya futa ya sanar wa da mutane mutuwar maman ayshat.



Cikin awa biyu aka gamaiwa umman Ayshat komai aka tafi kaita,gidanta na gaskiya.


*Mima kiyi hakuri dolene yasa zantafi bazan iya jure irin wannan abinda anty asiya keyiwa babanmu ba ,komenene yafaru nasan duk saboda nice,zan tafi inason kiyi hakuri sannan kada ki manta dani aduk inda kike,bazan hanaki kiyi kukaba Mima nasan kina sona kuma kinshaku dani dolece tasa zan bargidan nan naje na nemi inda iyayena suke, tana gama fadar haka ta juya ta futa rabar mima a dakin tana faman kuka.


Itako AMRISH tana futa ta miki hanya tai ta tafiya batare da tasan inda zata jeba,tafiya take tana zama tana hutawa,tana cigaba da tafiya har yamma tayi likis ,tana tafe a hanya ga wata masifaffiyar yunwa da take damunta,wasu zafafan hawaye ne suka zibomata,zuciyarta kunshe da bakinciki kala kala,tabbas tana ji ajikinta iyayanta suna raye basu mutuba,amma abin tambayar shine ,ina suke ,a ina zan samesu ,me hakan yake nufi meyasa zasu min haka,satoni akai,kodai basa sonane suka yardani gaba ki daya wadannan tambayoyin bani da amsarsu ,kuma bani da wanda zai bani su?


Karfe 6 da rabi aka dawo daga kai umman Ayshat makabarta,malan ahmad ne ya shiga gida domin ya ga lafiyar su AMRISH saidai kash yana shiga dakin Mima kawai ya tarar ta saka kanta a tsakan kanin kafafunta sai kuka take,cikin sauri da damuwa ya karasa inda take yace Mima, meyasa meki waye ya dakeki,ina AMRISH din .lokaci daya ya watsowa Mima wannan tambaya da ita kanta bata san inda AMRISH take a yanzuba,cikin kuka ta ce ,baba yaya AMRISH ta tafi, yatafi!!!!!! Tatafi ina? Ya fada a gigice, tace tatafi ta nemo iyayanta bazata sake dawowa ba tatafi ta barmu baba,ta kara fashewa da kuka, sharaf malan ahmad ya zauna a kasa zuciyarsa na masa zafi da ciyo,afili yashiga sumbatu yana cewa,yanzu da tatafi inane zataje, AMRISH batasan kowaba sai mu"batada kowa daga Allahn da ya halicceta sai mu da muke rukonta,Allah ne kadai yasan suwanene iyayanta,sannan shi kadaine yasan sunaraye ko sun mutu da kuma dalilin da yasa suka jefar da ita,innalillahi wainnailaihirraju un AMRISH ina kikashiga ,ya dafe kai.



AMRISH kuwa darene yayi sosai a hanya babu komai babu kowa a kan titi sai yan tsirarin motoci dake giftawa,sai kuma ita da take neman mafaka,ta kwanta, juye juye tashiga yi tana neman gurin dazata kwanta,can ta hango wata gada doguwa me girman gaske,ga mutane nan duk a kwan kwance,harda ma mata almajirai, da sauri ta nufi kasan gadar ta nemi gefan wata mata ta kwanta ,ta lumshe idonta amma fa ba bacci takeba.


Sukuwa su Mima da Malan ahmad babu wanda ya runtsa kowa a cikinsu tunanin halinda AMRISH take ayanzu suke,Allah sarki bayin Allah.


Tananan kwance a gurin duk tabi ta rude saboda yadda saurayen gurin ke gasamata cizo.sai soshe soshe takeyi gashi bata da a bun dazata lulluba,hijabinta ta ciro ta lullube jikinta ta kwanta a dandaryar kasar wajan,tana shashshekar kuka kasa kasa,tana rokon Allah ya kawo mata dauki,bakaramin kuka taciba daga bisani kuma bacci barawo ya dauketa,tashiga baccinta harda munshari.sosai tasha bacci batare da tasan gari ya wayeba,tana tsaka da baccin taji saukar ruwan sanyi a jikinta ,a furgice amrish ta tashi tana muzurai,ta daga idonta suka hada ido'' wani mutumine tsoho tsaye dauke da botuki a hannunsa,fuskar sa a tamke yace? Ke'' uban mekike a nan gurin tun dazu,waya fada miki ana kaiwa haryanzu ana bacci a nan ,tashi ki huce tunda gadar bata ubanki bace,yadaka mata tsawa,ta mike da sauri ta zura jijabin ta duk a jike ta huce ta gefansa.magana ya sake yi yace'' shegun yara irin kune ''yayan bariki ''ya'yan titi,aykin bamza iyayanku suje sugama iskancin su azo a hayfeku'' metstsssss yayi tsaki ya juya,wani mutumin ne ya karaso yace,malan tanimu me kakeyi ne,wayata tabaka haka kake fada. Uhm hannu malan sile,waccan ''yar karuwan nake,kaganta dai kamar wata saliha,uhmm kai malam tanimu,ay ina mamakin ganin su masu kyau,wallahi nima mamakin nake,idan kaga ''yayan shegu kai kace susuka halicci kansu,'''yan iska ya'yan gaba da fatiha.

Duk abinda suke fa蓷a amrish na jinsu, batace komaiba ta cigaba da tafiya hawaye na zuba a cikin idonta .tana faman rawar sanyi duk jikinta a jike,tana tafe ta na lumshe ido bata kula ba har tai karo da wani katon duste ta hantsila duk ta kurkurje ,takalmin da ke kafarta kuwa ya dade da tsinkewa ,zama tai a gurin ta karka de kayanta ,ta shiga juye juye bata samu abin da zata daure takalmin ba,can kuma sai ta hango kellen a tamfa ta dakko ta daure takalmin'' sannan ta saka taciga ba da tafiya batare da tasan in da zataba'' Amrish dai ta rasa makama kuma tarasa mafita,gashi ko abinci ba taciba har yamma ta farayi ,duk tabi ta gala baita,ji take kamar ta kashe kanta ta huta,wani dan silaf ta hango me dan tudu a can gefe,ta matsa kusa da shi ta zauna,ta hada kai da gwywa sabida kukan ma ya daina fitowa,sai dai kukan zuci''' tinani tashiga yi shin ita wacece suwanene iyayanta"ko dai ita dagaske shegiyar ce ba da aure aka haife ta ba, innalillahi wainnailaihirraju ta runtse ido tana ambaton sunan Allah' a ran ta tana cewa Allah isa ba haka bane.


Tana nan zaune a gurin tana tunanin yadda za ai ta samu a binci taci ,kawai sai ta hango wata babbar makaranta wato University,ta manyan mata makarantar"ya'yan masu fa蓷a a ji, wasu "yan matane tsaye a jikin wata mota kirar kasar chana su uku,sai maza guda biyu, gaba ki dayansu a tsaye suke suna shan yogot da mutufain suna murmushi,da alama dai masoyane.

Amrish tashi tayi da 茩er ta karasa gurin da suke,dauke da sallama a bakin ta tace" assalamualaikum ,tayi sallama tafi sau biyar amma babu wan da ya amsa mata sallamar,ko kallo bata ishe suba, nafisace ta kalli, daya daga cikinsu da alama itace shugabar ta fiyar ta su domin duk tafisu kyau,gashi taci wasu tsigalallun kaya riga da wan do ko hula babu a kanta''' sai gashinta da ya zubo a bayanta, tace BIHAR wai wannan kazamar gurin watazo, BIHAR ce ta juyo ta kalleta tace ,ke zan tambaya dan kinsan duk dangin mu babu kazami ko talaka,ballan tana "ya'yan titi.jin wannan bakar maganar da aka ya ba mata ne yasa amrish ta runtse ido ta bude, tana sauraran duk ciutuncin su, dayar mesuna yasmin ce ta juyo tace, ke mekike bukata kin zo kin samu a gaba? Murya na rawa amrish ta ce tai mako zaku bani kamar yadda Allah ya tai makeka. Dan Allah ku taimaka min da abinci yau kwata kwata ban ci abin ciba. Dariya suka kwashe da ita daga su har samarin nasu ,har da bubbuga kafa suna nuna ta da hannu, da ga bisani kuma bihar ta juyo a fusace ta wanke amrish da mari hagu da dama tace,ke "yar gidan mutsiya ta duk ranar da kika sake bari mukayi ido hudu dake wallahi na rahira sai ya fiki jin dadi,shegiya ubanki ya bamu abincinne bar nan gurin,hhhh behar ay daga gani ma wannan bata da uban in kika bibiya haihuwar kan hanya ce'' ''yayan shegu, cewar nafisa ,ita ko amrish jiki a sanyaye ta juya ta nufi inda ta ke,ta koma ta tusa kanta a tsakankanin 茩afafuwan ta ta shiga rera kuka kamar wadda za a yanka.


________Abangaren su malan Ahmad da mima kuwa unguwanni da lunguna da sako babu inda basu duba ba amma basu ga amrish ba,babu amrish babu labarin ta haka suka koma gida ,ran kowanne su a jagule, Asiya ce tace uhm kuyi kugama dan nan gidan ba na zaman "ya'yan shegu bane ,na zaman ya'yan sunna ne tayi tsaki ta shige daki,itako mima dakin ummanta ta shiga gaba kidaya sai dakin ya zame mata tamkar jeji me duhun gaske Allah sarki mima.



Tom amrish fa dare ya farayi haryanzu tana zaune akan wannan silaf din,idonta ya kada yayi jajur ya kumbura sumtum, tarasa yadda zatai gashi babu gurin kwana ,babu inda zata kwanta ,sai a gurin nan ta kwanta ta runtse idonta''amma da ba bacci ta keba kwai tunanin rayuwar da zata fuskanta nan gaba takeba.

Haka amrish ta cigaba da kwance a gurin abin tausayi ita kadai kwallin kwal a waje baiwar Allah ,babu kowa sai gaushin karnika,sai ita kuma da take kwance,amrish dai bata samu tai bacciba sai karfe 3 na dare kuma shima karfe uku na daren bacci barawane ya dauke ta amma badan wai tana so tayi bacci ba.

Tom washe gari amrish tana zaune a kan silaf din cikinta sai murdawa ya keyi ,sabida tsananin yunwar da take ji ko iya tashi bata yi sabi da yunwa,tanan a gurin jikinta duk yayi sanyi ga zazza蓳i dayake neman rufeta sabida tsananin yunwar da takeji ,kwanciya ta a gurin ta runka burgima hawaye na Zariya a kuncinta ta na ta burgima a dan daryar gurin saboda yunwa,tun tana iya burgima har ta dawo ta kasa daga ko hannunta'' sai dai hawaye kawai da yake bin kuncinta,. Tana nan kwance a gurin wani yaro karami wan da bai huce shekara 14 ba a duniya ,ya karaso gurin ya ga amrish a kwance ko hannunta'' ba ta iya dagawa, dasauri ya matso ya fara magana yana cewa lafiya'' me yasameki ki tashi, Itadai amrish bin sa kawai da kallo take amma ta kasa magana sai dai kuka, a hankula ta bude bakinta har rawa yake tace'' yunwa nakeji ka taimakeni zan mutu,, bejira karasa War taba ya zura a guje,wani shago,ya sayo mata buredi da shayi ya kawo mata, gani yayi bazata iya tashi ba hakanne ya sa ya dagota ya jingina ta jikin silaf din ,yashiga bata ruwan shayin da buredi '' har ta koshi,idonta taf da hawaye ta dago tace'' Nagode Allah ya taimake kamar yadda ka taimake Ni, murmushi kawai yayi mata yace Amin ,sanan ya tashi ya cigaba da tafiya.ita ma tashi tayi duk da lokacin jikinta be gama dawowa daidai ba,amma ba laifi ta ji dan karfi a jikinta.

Zaune suke a gaban likitan ,kowannen su atsorace yake,da irin kallon da likitan ke musu,jiki a sanyaye wata dattijuwar mata tace,likita mesakamakon yace, uhm sai dai kukara hakuri,amma wanan karanma haka yanunamin baku da wata ma tsala daga ke har me gidanki, wallahi bansan matsalar da ta hana ku samun haihuwa ba, Hajiya asma,U ce ta mike ta na tafe tana shara hawaye,har ta karasa gaban motar su,haka shima mijin nata baritar sulaiman Muhammad,kana kallon fuskarsa zaka iya karanto damuwar da take kan fuskarsa.ahaka suka shiga mota suka dauki hanyar zuwa gidan su dake cikin G.R.A suna isa megadi ya wangale musu get suka shiga, parking space suka nufa sukayi parking,sanan kowannensu ya fito ,suka nufi cikin harabar gidan, tundaga falon gidan BIHAR ta karaso da sauri tana cewa'' wai mom ita kuka tafine kuka barni, nasan cewa akan rashin haihuwar nan ne,wai ku bazaku hakuraba ,kuyi hakuri da Ni din kawai haba'' gaba dayansu bawan da yace mata uffan suka wuce suka barta a gurin tana faman surutai.


Gaba ki dayansu daki daya suka shiga mom ta zauna a gefen gado ta na sharar kwalla,dady ya karaso ya zauna a gefanta,ya bude baki zai mahana tayi saurin dakatar da shi dacewa bana bukatar rarrashinka,mugu kwai azzalumi,haba asma, U yanzu gabar da kike dani hartakai ki kira mijinki da azzalumi,menayi miki,abune yariga yafaru kuma arashin sani ,sama dashekara goma 17 amma ki kasa mantawa Ni kaina nayi na dama wallahi lokacin sharrin shaidan ne da kuma kuruciya da Allah ki daina damuwar nan haka,hmmm na daina damuwa ko,Allah sarki ka da kamanta'' ako da yaushe Ni din uwace,me rauni da tausayin ''yayan ta,kai kuma fa ubane mara tausayi mara imani ,wallahi sulaiman bazan taba ya fe maka ba katashi ka futarmin daga daki ko Ni na tattara kayana ba koma gidanmu,an sorry kiyi hakuri dan Allah zan fita abin bekai ga hakaba'' amma ina Dada tuna tar dake ki yi tunani akan karan kanki Ni mijinki ne idan baki daina fushi da niba maka'ikum rahama suna fushi dake. Sannan ya tashi ya futa.


Tom dady yana futa bihar ta shigo dakin da sauri,ta cewa mom'' am momy kinyi baki,a hankula mom ta bude runannun idonta tace,bihar wacece?momy mom ayyuf ce, okay kice ga ninan zuwa,tom juyawa tai ta nufi hanyar da zata wadata da falon gidan , fuskar ta dauke da murmushi tace anty zainab tana zuwa, okay thank you my daughter zaki iya tafiya,tom mom tana tafe tana satar kallon ayyuf dake zaune,shiko ayyuf bemasan tanayi ba zuciyarsa nacan tunanin inda amrish ta shiga saboda yaje gidan malan ahamad gaisuwa ya tambayi mima ina amrish take sanar masa duk abin da ya faru,tun daga lokacin ya kasa sukuni a kullum tunanin inda zai ganta yakeyi. Momy ce ta fito fuskar ta babu yabo ba fallasa tace sannu da zuwa anty zainab yauwa ta mike tare da rukota ,tana cewa,meyake faruwa ne ? Kuka tasake fashewa dashi tana cewa,anty kema kinsan akan zunubin da mijina ya aykata a shekarun baya,shine haryanzu yake bibiyar rayuwarmu,bangane shike bibiyar rayuwar kuba, eh mana tundaga lokacin da sulaiman ya aykata zunubi mafi muni game da kyau yar da Ubangiji ya bamu ,tun daga ranar ko batan wata bansake yiba .anty ayanzu bani da da kokuma jika,kinsani bihar ba ''yata bace agidan marayu muka dakkota,meyasa bazan ji babu dadi ba,Allah shai dane banice silar fadawa wanan halin da muke cikiba,tana gama fadar haka ta fashe da kuka,etako Hajiya zainab rarrashin ta tashiga yi da yimata wa,azi akan kaddara me kyau ko mara kyau nan tafara nusanshe da ita akan duk abin da tagani ya faru a rayuwar baya kaddara ce ba yin kanku bane.haka dai suka cigaba da hirarsu har lokacin tafiyar Hajiya zainab yayi suka yiwa Hajiya asma U sallama suka tafi.


Tom abangaren Amrish kuwa tana tafe a hanya tana faman goge gumi ga jikinta sai wani irin wari yake ,ita konta batason warin da takeyi gashi duk inda taje neman tai mako sai an hantare ta akoreta,ko kuma ayi mata kallon mahaukaciya kowa da kalar zagin da yake Binta da shi,Allah sarki baiwar Allah,duk inda ta je ta tsaya muddum da mutane a gun sai am toshe hanci sabi da warin da takeyi, idan tayi fitsari babu tsarki idan kuma tayi kashi shima babu ruwa,ballanta na kuma uwa uba salla da wanka,tara san inda zatace ta tsoma rayuwar ta taji dadi,tarasa gata,ayanzu amrish harro kon Allah take akan yayi gaggawar daukar rayuwar ta ta huta,bazata iya cinye wanan jarabawar ba,gashi tuntana tafiya takalma ta har sun sude tsabar yawo a unguwa unguwa lungu da sako titina titina,da bin kasan gada domin kwana,sai da takai ta kawo harta kafarta tafara taba kasa,bayada ta iya haka ta cire takalmin ta yar dasu ta samo jarkar lemo ta kukkulla tsumma a jiki ta saka duk da bata jin dadin tafiya da jarkar amma ya ta iya yafi ta dinga taka kafarta haka.


________tafiyarta tacigaba dayi da jarkar a kafarta amma ina sai taji wahala take sha'' ta gwammace ta cire jarkar ta cigaba da tafiyarta a haka babu takalmi duk da tasan zata ji zafin taka kwaltar.

Tom haka rayuwar amrish ta cigaba da gudana kullum a wahale'' yau ta kwana a karkashin gada gobe kuma kwana a bakin kwata'' jibi kwana a karkashin bishiya.

Yau ma kamar kullum tana tafe a hanya hijabin nan nata yayi dukun dukun'' ga shi ya kode bakine amma har yafara dawowa ruwan toka tsabar wahala da datti'' itako doguwar rigar da ke jikin ta'' ta atamfa ta wani kode ta jeme, bama ka iya tantance zanen jikin atamfar' wasuko guraren duk sun yage, eta kanta fatar jikin ta ta dafe tayi duhu sosai'' duk wannen kyau da Amrish ke dashi ya zama tarihi ayanzu ko dani ce na ganta sai naji tsoro dan zan dauka mahaukaciya ce,bazan yi tunanin tana da hankali ba ,musamman yadda kafarta tayi kurji__kurji tayi faso'.

Tana tafe akan titin yaran unguwa suka shiga Binta suna tsokanar ta mahaukaciya mahaukaciya.bata ko kallon in da sukeba'' da abin dai ya dameta sai ta fashe da kuka ta durkusa guywoyinta a kasa,ta daga hannunta,sukuwa yara da suka ga haka sunzata Dukansu zatai'' kawai suka tarwatse kowa yayi ta kansa, amrish ko yadda ta daga hannun nan addu,a ta shiga yi tana cewa'' Allah kasan komai,Ni baiwar kace '' me tsananin bukatar taimakon ka,ya Allah ka tausaya min duk da bansan wane zunubi na aykata ba har rayuwata ta kasance a haka'' kowa guduna yake,babu me sona'' babu me kula dani ,ada nasan ina da gata, ayanzukuwa nazama mujiya acikin mutane,wadda nake kallonta a matsayin uwa a gareni,tatafi ta barni, Allah ka ceceni, ka tausaya min'' idan kuma mutuwa ce hutu a gareni Allah kau gaggawar daukar rayuwata,ta sauke hannunta tana rusa kuka kamar ranta zai fita,ta kwanta a gurin tana burgima tana jan numfashi kadan kadan yana sama''sama.sai da takai ta kawo duk mutumin da zai huce saiya tsaya ya kalleta,wasu su jijjiga kai alamar tausayawa'' wasukuma suce Allah ya bata lafiya'' wasu kuma suyi dariya su huce abun abin tausayi sai wanda ya gani.



____________KADUNA____________

Kwance yake a kan katafaran gadonsa me kyau da ado' gefe guda kuma shishace da kwayoyin maye duk a zube a gefe, ya lumshe idanunsa masu 蓷auke da zarazaran gashin idonsa me launin ruwan toka,hancinsa dogone like biro'' bakinsa kuwa ba a magana wajan kyau da haduwarsa,jinake kamar naje na lasheshi, doguwar suma gareshi launin baki amma ba baki can ba'' dogon namijine kana ganinsa kaga cikakken namiji me kyau da kwarjini da karfi kamar damisa'' gaba ki daya ilahirin gabobin hannunsa a murde suke ga tafkeken kirji me dauke da kwantacciyar suma bakakirin a kwance sai kelli take'' ABER kenan farine tass me cikakkiyar asali masu dukiyar da babu kamar ta duk fadin garin Kaduna. Abu biyune ya kasance cikas a rayuwar sa shine'' ya kasance yana shan shisha da duk wasu kwayoyin da suka shafi hanyar bugar da mutum,abin da ya saka ABER ke shan wannan kwayoyi shine'' ABER yana da tsananin sha,awa wadda har ta zamemasa tamkar cutarwa ce a rayuwar sa'' hakan neyasa ABER ya nemi taimakon abokin sa deen akan wannan masifar da ta addabesa,nan danan abin ya bashi shawara akan ya din ga shan kwayoyi zasu rage masa sha,awar da yake ji,,babu musu ABER ya yadda da maganar abokin sa deen dan yana tunanin shawara me kyau deen ya bashi'' a hankula a hankula ya na shan kwayar har ta bi jikinsa yanzu babu wan da ya isa ya dakatar da shi akan shayeshayensa. Wannan kuma shine babban burin mahaifiyar deen da kuma shi kanshi deen din,wato su tarwatsa rayuwar ABER.



ABER yana kwance yaji an fara noking din kofar, sai da aka jima a kwankwasa wa tukunna ya bude baki da 茩er ,murya a sanyaye,kalar ta ''yan shayeshaye a lamun ya sha ya bugu,yace'' a shigo,cikin hanzari aka murda aka shigo, wanene wani matashin saurayine me kyau kai da kaganshi kaga ABER dan bakaramin kama suke ba ban bancin shine abin ya dan tasa sosai shikuma wannan yarone be huce shekara 19_20 ba, da sauri ya karasa gurin sa ya shiga cewa'' ya ya ABER me ya sameka haka dan Allah ka daina shan wadan nan abin babu kyau'' Ni kai na na san ba halin yaya na bane shaye shaye' na san ka da ilimin addini da na boko dan Allah yaya ka dawo asalin GENERAL MUHAMMAD ABER YUSUF jarumin namiji mefada aji'' sannan me ayki da tunani me kyau,me tausayin talakawansa,dan Allah yaya ka canza wannan ba dabi,ar yayana bace. A hankula aber ya fara magana gami dacewa'' YAZED' yayanka ya mutu Ni ba yayanka bane,wancan ganaral Muhammad aber Yusuf ya mutu ,yanzu dan giya dan mayene a gabanka YAZED' ban san meyasa ba nakasa hana kaina yin wannan abin,dan Allah kanina ka tayani da addu,a insha Allah zan daina, hawayen dake fuskar YAZED'ne suka karasa gangarowa,yarasama me zaice kawai sai ya rungume aber ya saki kuka yana tunanin halayen aber a da.

Ammi dake tsaye kofar dakin aber tana jin a binda suke fa da zuciyarta ta karye ta fashe da kuka,ta koma dakinta a guje ta fada kan gado tashiga rera kuka,me sauti.



KANO

Mima ce zaune a kofar dakin ummanta gaba ki daya a bin duniya ya dameta,tamarasa mezatai komai ya lalace mata,gaba daya duniya ta koma mata kamar makabar ta,ga tarasa mahaifiyarta me sonta da kwaunarta ''wan da ya fita so ya rabata da ita,ga kakarta itama ta rasu'' gakuma''yar,uwarta amrish me son ganin farincikin ta itama ta rasa ta har abada,gashi yau kwana uku kenan tanemi mahaifinta ta rasa,hatta gidan da yake aiki taje,sai ta tarar Hajiya zainab ta tashi daga gidan ga basaya,ayanzu daga ita sai Asiya suke zaune,kullum da kalar azabar da Asiya take bata,wahala kala kala tana shan su agurin Asiya,mima dai takoma abar tausayi bata da ayki kullum sai kuka.



Kaduna************


Ammi ce zaune a falon har zuwa yanzu kukan take '' babu kowa a gefanta jikake ko ina tsit ...

Gani tai kukan bazai ka ramata kumau ba''hakan yasa ta tashi ta nufi dakin ABER ta murda kofar ta shiga dauke da sallama a bakinta.


Kai tsaye kusa da aber ta zauna inda shikuma YAZED'ke gefan sa na dama yana share kwalla,sabi da kada ammi ta gaya yana kuka zuciyarta ta karye itama ta fara kukan...


Murya a sanyaye ammi ta fara magana ta ce'' ... Babana?''

Aber ne yana daga kwance yace'' na'am ammi.....

Ammi ce takara cewa'' yanzu babana kana ganin hanyar da ka dakko itace mafita a gareka?'' haba babana meyasa zaka canza d'abi'unka na kirki?'' wadan nan abin da kake yi bazai karamaka komai ba dan Allah babana idan ma wani abunne ya sauya maka ra,ayi wannan hanyar ba me kyau bace?''


Aber ne ya fara magana' hawaye na zuba daga fuskarsa yace'' ammi?.. kin Sanni

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment