Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kinsan wane aber' kin fi kowa sanin halayena ammi'' wallahi da ina da yadda zanyi na daina datuni na daina'' ammi kingafa mutanen da suke min kallon mutumin kirki gaba kidaya mutuncina ya zube a idon jama'a'' kowa ya gujeni yanzu kema ammi kin yarda na zama 蓷an shaye' shaye'..... Aber ya sa hannu ya goge kwallar da ta gangaro sannan ya kamo hannun amminsa ya ce'' ammi ki tayani da addu'a insha Allah zan warke.


Ammi ce ta goge hawaye da majunar dake kan hancinta ta ce'' kayi hakuri babana ,nasani bada saninka ba'' nasan bazaka zama hakaba'' akwai abin da ya sameka? Duk da bana zargin kowa a kai amma Allah shine yasan komai,kuma nasan yana gani'' insha Allah zaka samu lafiya babana'' kuma addu,a inan ina yimaka bana gazawa ko dai dai da rana daya ne ka cigaba da hakuri.



Yaya mun fiso muga ka kwantar da hankalin ka' ''.. yadda muma namu hankalin zai kwanta,kadaina yawan saka damuwa a zuciyarka ''Allah ya baka lafiya yayana.yazed ya fada tare da mikewa ya futa daga dakin.


Zaune yake a dakin sa yana shan apple'' yana murmushi gefansa kuma wata dattijuwa ce ke dariya kamar wata tababbiya'' tana cewa,ay nake fada maka'' deen wallahi kamar yadda na kuduri niyya'' sai na ga bayan zuri'ar Yusuf ''indai ina raye saina sanya yusufa yayi kuka da idonsa...


Hhhhhh mom barni da su,ay kibari kawai'' ko iya ciwon da muka sa boka ya dasawa ABER ya isa,ya sa Alhaji Yusuf ya hadiyi zuciya ya mutu' ''amma naga mutuminnan haryanzu shiru kakeji' da alama dai yana da ta wakkali da yawa'' sai mun canza wata hanyar mom''


Uhm bar ''yan iska'' ay wallahi tun da na dau alkawari saina cikashi tukunna zan samu sassauci.....

Mom karki damu,Ni kawai yanzu jira nake yayiwa wata yarinyar feyde,yadda zamuji dadin tarwatsa rayuwar ''yan bura uba,amma haryan zu naji shiru...


Ay ammi'' ke hana shi fita amma da nasan tuni ya yiwa yara da yawa feyde'' angaya maka banza na ce boka ya dasamasa sha'awa,hmmm....


Okay'' shikkenan ni zan fito dashi''bari na rashi naje gidan dan yau kwana biyu ban je na dubashiba.


Kutumar ubanka??'' dubiyar uwar me zakaje'' dalla zauna mu yi solving din matsalar mu'' muda dora masa ciwo muda zuwa dubiya Allah ya kiyaye'' tana magana tana hararar deen.

Kash'' mom bazaku ganeba duk wannan acikin ta kune'' idan bana zuwa dubashi sai a fahimci wani abu.. kin gane idan kuma ina zuwa babu wan da zaiyi zargin wani abu da muka aykata musu.



Oh '' to nagane saika dawo ammafa kada kafiye zakewa'' na fada maka.

Okay' babu damuwa mom saina dawo ya tashi ya futa.



Kwance take a gindin bishiyar man mararta sai ciwo take tana murda mata'' sai aikin faman rike mara take tana runtse idonta tana cewa''' wayyo Allah na' innalillahi Allah Ubangiji ka kawomin dauki'' tana fada tana hawaye'' tana runtse ido alamar zafi da radadin da takeji a mararta.


Tana tsaka da wannan yanayin ta jiyo abu yana zubowa a wan donta'' cikin sauri ta saka hannu ta dago wandon nan take taga jini'' alamar al'ada ta farayi'' ita bata saniba.

Nan take hankalin amshi ya tashi' tashiga furta kalmar Innalillahi wainnailaihirraju'un shikkenan na kade, wannan jinin mene a jikina haka'' meye ya sameni ne nashiga uku,waye zai taimakeni.. kuwa ya tsaneni' ' bani da gata kowa guduna yake,mena aykata haka?'' wane zunubi ne me girma na aykata,tun da nazo duniya nake shan wahala'' shin wanene zai taimakeni'' tana kuka tana saka hannu a kanta tana cewa waye yayimin haka...

Allah sarki batasan komai ba, Bama tasan menene ake nufi da al,adaba,babu uwa babu'uba babu dangi babu gata.rashin uwa babbar masifa ce'' rashin uwa babban tashin hankaline haka kuma kaddara ce'' Allah ya jikan iyayan mu wadan da suka mutu..muma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani.


Darene ya tsala sosai gari yayi shiru. Inda Alhaji sulaiman ke kwance a lallausan gadon sa' yana shan baccinsa hankalin sa kwance yana shan A.C. a furgice ya mike sakamakon mummunan mafarkin da yayi'' ya ganshi a cikin wutar ja hannama ana babbaka naman jikinsa '' yana ihu yana neman taimako,amma babu wan da ya zo taimakon sa,sai wata yarinya da take gefe jikin ta a malkwade,ko ina nata ana kashe yake,kumfa na futa daga bakin ta tana cewa a cigaba da gana masa azaba,bazata yafemasa ba''....

A jiyar zuciya Alhaji sulaiman yayi ya zauna a kasa ya hada kansa da gywa ya saki wani marayan kuka yana cewa'' nashi ga uku natsani kaina,yana tsaka da wannan kukan,saga Hajiya asma U ta shigo a guje tana kuka,tana cewa'' Alhaji ?'' Alhaji kataimakeni wallahi bina take,duk in da naje sai ta biyo NI tana
kira na da mama''Alhaji kataimakeni.....



Da sauri alhj sulaiman ya mike, yarukota,ya tallafota sosai ya fara rarrashinta.


Ki yi shiru Asma'u babu komai'' ki kwantar da hankalin ki.maza fadamin me kika gani?''


Alhaji kawai ina kwance naga nayi mafarkin wata yarinya'' jikinta duk babu kyaun gani,,gashinta kwarkwata da tsutsotsi,ajiki,kayan jikinta marasa kyau,naganta a dokar daji tana ta kuka tana kirana,tana mikomin hannu tana cemin'' nazo,shinena tashi zumbur ina salati,kawai na kalli gefena sai na ganta a tsaye fuskar ta dauke da hawaye na jini tana cewa intaimaka mata zata mutu... Alhj abin ya tsorata Ni ''


Alhj sulaiman ne ya fara magana cikin kidaina da damuwa yace'' ki kwantar da hankalin ki Asma'u nasan duk wannan abin Ni naja miki''bake kadai kikai wannan mafarkin ba nima nayi irinsa'' sai dai nawa yafi naki muni'' domin Ni a wutar jahannama na ganni a na babbaka naman jikina,tabbas na aykata zunubi me girma '' amma lokacin ban mallaki hankalin kainaba, ya Allah ka yafemini.ya fashe da kuka abin tausayi''

.
_____K___ADUNA_____

Deen yana futa daga gidansu kaitsaye gidansu aber ya nufa'' yana zuwa megadi ya bude masa get ya shiga, kaitsaye bangare ABER ya shiga '' ya bude kofar falo bega kowa ba''kawai sai ya shige bedroom din aber a nan yasa meshi a kwan ce yana ta burgima a kan 馃洀锔� bed babu tambaya sabi da yasan meke da munsa ba komai bane face sha,awa...


Deen ne ya zauna a gefansa ya tauna lebe yace'' sannu G.M '' shidai aber be cemasa komai ba saima juyawa da yayi ya rike mararsa yana cewa''' wash wash deen zan mutu kataimakeni .sorry G. M'' bansan tayadda za ai na iya tai maka makaba' na fada maka hanya dayace na samomaka zankadediyar yarinya ''ka sauke bukatar ka a kanta amma kaki waikai musulmi to ay gashinan zaka mutu a banza'' uhmm naji ka samomin Indai har zan samu sassaucin abin da nakeji''....


Okay amma fa a kwai ma tsala daya'' wace matsala kenan deen? Matsalar itace'' an ce kada a Barka ka futa sani da irin wannan matsalar,

A,a to ka kawo yarinyar gidan nan.

No aboki bazayyuwu ba,, dolene sai na samo hanyar da zamu futa don yarinyar ma sai na nemo...

Okay to shikkenan ina sauraronka zuwa gobe''

Yauwa a bokina kokari fa da kazauna kanka ya kulle cewar deen.sannan ya tashi ya masa sallama ya tafi gidan ,zuciyarshi cike fall da farincikin ya ci nasarar tafarko,saura aykatawa. Daganan kuma yasan yagama da rayuwar ABER ya gama tarwatsa a halin alhj Yusuf me tama''


__k__ANO_


Ke dan uwarki ba magana nake miki ba'' wallahi mima idan kika sake na taso sai namiki lahani'' shegiyar yarinya kawai, maza gawanki na can wallahi sai kin wankeshi....


Dan Allah anty Asiya ki barni banajin dadin jikina.


Kutumar uba Ni ay dadin nakeji'' to bari jiki kina 茩atuwar basamudiya bazan zuba miki ido na kalleki ba''hmm Bama ki da hankali mima........


Babu yadda mima ta iya haka ta mike'' ta debi wankin ta farayi'' ba ita ta gamaba sai karfe uku na rana.


Dakin Asiya ta nufa ta ce anty nagama'' okay maza ay wahala bata kare ba yarinya ga shara can dauki tsintsiya kifara..
To anty zanyi amma dan Allah inason ki fadamin ina babana yake?'' a fusace Asiya ta mike tace'' ke Ni zaki dinga fadawa wadannan maganganun ''to bansani ba ko zan sace shine?'' na tabbatar uban nan naki ba yaro bane ballan tana ace ya bata, kawai dai baya son kine be damu da keba'' daman uwarki yake kauna kuma ta mutu.

A,a anty wallahi baba bazai taba tafiya ya barniba'' kuma na tabbata yana sona,nasan duk inda yake a yanzu yana tunanin halin da nake ciki''


Oh'' sannu shugaban marasa kunya, wato harni zaki kalli tsabar idona kina fadamin bakaken magana ko'' to tunda kince yana nan kuma yana sonki'' saiki bishi,tana fadar haka ta tunkuda mima waje'' kije kada na sake ganin wannan fuskar taki a kofar gidannan shashashar yarin ya kwai,tayi tsaki tare da tura kofa tasa sakata.

Tun da Asiya ta rufe kofar mima ta zube a kasa kan guywoyinta ta fashe da kuka'' tare da tunano rayuwarsu da suka gudanar da iyayanta a cikin gidan'' tabbas haka rayuwa take juyawa bawa a duk lokacin da wata kaddara ta zo masa' me kyau ko akasin haka'' yanzu dai kuduba kamar ba a halicci A'isha da malan ahamad a gidan ba Dukansu yanzu babu su''haka amrish itama yanzu babu ita'' sai mima da itama anty Asiya ta koreta a yau zata bi duniya.



______AMRISH______
Tunda amrish ta zube a gin din bishiyar tana kuka bata ga kowa ba kuma bata samu taimakon kowaba'' gashi haryanzu jinin be daina fito mataba, babu yadda. Ta iya haka ta tashi ''tacigaba da tafiya tana tafe tana rike mara''har ta iso bakin titi,wata motace ta yanko a million sora kadan ta bige akaja burki keeeeee. Nacikin motar ne suka fito suna balbala mata Bala'i,, itako da 茩er ta iya daga jajayen idon ta ta ce kuyi.... Zuciyar ta ce ta fara bugawa da sauri saka makon wadan da ta gani, behar ce da kawayen ta wadan nan guda biyun. Hanyar guduwa ta shiga nema sani da tunawa da tayi da kashaidin da suka mata na cewa kada ta sake bari su kara ganin wannan kazamin jikin nata....


Allah sarki sotake ta gudu amma ta gaza tafiya saka makon al,adar da takeyi, cikin Muryar tausayi da hawaye a fuskarta'' ta shiga basu hakuri,amma ina bihar kataso wa ga ban ta sukai suka rufeta da dan banzan duka,,sai da sukai mata lilis sannan suka shiga mota suka ja suka cigaba da tafiya, suka barta a nan gurin sai burgima take tana kuka.


Sai da Amrish ta gama jinyar jikinta sannan ta tashi ta baro bakin titi' ta shiga cikin jama,a duk in da ta huce bin ta ake da kallo ana toshe hanci'' itako ko ajikinta, yunwa ce ta fi da minta'' wata me abinci ta hanga ana tayi mata layi'' ana sayan abin cin'' da sauri ta karasa gurin tashiga cewa''' a tai maka min, dan Allah ku taimake Ni kamar yadda Allah ya tai makeku yunwa na keji'' wani saurayi ne ya juyo tare da toshe hancin sa yace'' ke bar nan gurin'' kaza ma kawai baza a tai makeki ba, ay Amrish da jin haka ta fashe da kuka,ta saka guywoyinta a kasa tafara rokon su'' dan Allah ku daure ku tai makeni, kada ku hanni abinci ku tausaya rayuwata,, wani yarone ya karaso gurin ya ce anashi a binci aka bashi'' sai ya dauka ya bawa amrish'' yace ta je taci'' nan danan amrish ta shiga yi masa godiya ta koma gefe ta hau laima kamar bata ta蓳a cin abinci ba a duniya ,, atake jikin mutanen gurin yayi sanyi.....


Momy ban san meyasa nake ta tunanin halin da take ciki a yanzu ba momy ina mutukar tau sayin amrish bamusan halin da take ayanzuba.

Uhm ayyuf kenan'' Ni kaina nadamu da yarin yarnan'' gashi tsawan kwanaki malam Ahmad ya daina zuwa ,shikadai ne zai iya sanar damu dalilin da yasa amrish ta bar gida.


Ah to momy mu je gidan su mana mu tambaya ina tunanin hakan sai yafi ko'' eh to kakawo shawara ayyuf babu da muwa idan Allah ya kaimu gobe sai mu muje mu duba ko'' okay babu damuwa momy Allah ya kaimu.



Abangaren deen kuwa'' da murna ya isa gidan su yana washe baki kamar gonar auduga'' momnsa ce zaune a falo ta kurawa T.V ido tana kallon tashar arewa 24, a lokacin suna haska Film din labarina, ta na da ga zaune ta hakince sai zabga murmushi'' take,sai taji sallamar deen'' Muryar shi dauke da fara,a ya zo ya rungume ta yanacewa''momy anyi nasara momy burinmu ya kusa cika.

Bangane me kake nufi ba?'' akan me kakemin magana haka,kafahim tar dani my son kasani a duhu fitar dani a harke''tana magana tana wawware idanunta irin salansu na "yan duniya.

Deen ne ya ce'' momy ABER ya yadda zai bini muje domin ya sauke sha'awarsa akan koma wacece. What ''wai dagaske kake my son ?'' Allah momy da gaske nake ba wasaba yanzuma daga gidan su nake.


Na yarda my son'' Amma fa ba anan gizo wake sakar ba ''kana tunanin za a Barka kafita da aber daga gidan nan kuwa,?'' hmm mom kenan ay mungama yanke shawarar idan dare yayi'' zamu fita sai mu dau hanya, okay nagane to amma anan Kaduna zaku samu yarinyar ?'' a'a mom ki gane mana,ba anan ba,Kano zamuje'' ay ni bana so ya samu yarinya me hankali '' nafison ya samu wadda bata da cikakken hankali'' ko kuma mahaukaciya, yadda idan ya aikata akan mahaukaciya za,a yan kemasa hukuncin kisa'' kuma kinga ba a garinan bane balle yaci albarkacin Alhaji Yusuf akyleshi' Kano zamu' kuma kinsan kazo basu da wanda zai tai makesu can .


Wata uwar dariya momy ta farayi'' kamar wata ta蓳abbiya ,sabida tsabar jin d谩din labarin dan nata, sai da tayi dariya me isarta sannan tace'' kay ashe ba a banza ba'' wallahi yan zu na tabbatar kai jini nane'' yanzu kam na tabbatar kasha a nono'' katashi kaje ka kwanta ka huta Ni hakan ma kabiyani, Allah ya yimaka albarka.


Tom abangaren Amrish kuwa'' rayuwa ta cigaba dayi ita kadai babu me sonta'' kowa gudun ta yake'' yarinya tazama kamar matacciya a idon mutane'' babu me tun tudar rayuwarta '' babu me taimaka mata.

To yauma kamar kullum tana zaune a gindin bishiyar nan ta ha蓷a kai da gwywa tana rusa kuka kamar ranta zai fita, yanzu kam tagama sallama rayuwata a duniya,gashi tana so ta mutu amma ubangiji ya rubuta ba zata mutu yanzu ba, daman tun tuni Allah ya tsara sai tasha bakar wahala aduniya.

Ita kan babu abin da yafi bata tsoro sai jinin da tagani wancan satin,duk ya bata mata jikin ta da kuma kodaddiyar atamfar' dake jikinta'' wannan zubar jinin a jikinta yasa mutane sun kara tsanar ta,dan yanzu ko hucewa ta zuyi tagaban mutum wala mace ko namiji sai an rufeta da duka ko a Korea ta 'sabi da tsabar tsanar ta da kymarta da ake yi....


Yanzu kam ta 蓷an samu hankalin ta ya kwanta kadan, sabi da ta daina ganin zubar jinin yanzu ya tsaya cak'' kuma gashi batasan jinin menene ba.

To'' da misalin karfe 5 na yamma deen ta shirya tsaf ya nufi gidan su Aber ,a bakin get din gidan yayi parking din motar sa,sai ya kwan kwasa megadi ya bude,cikin dabara da salo irin nasu na ''yan duniya deen ya farayiwa megadi dadin baki har da bashi kudi Naira dubu dari 2 kawai dan ya bari sufita da aber '' haka ko me gadi ya yar da sakamakon yaga ruwan kudi sai murmushi''ya ke ya wangale wa deen kofa ,shiko deen wayarsa ya dakko ya danna number wayar aber ta fara ruri, kira daya aber ya daga tare dacewa'' hello my friend ka karaso na?'' eh kafito ina waje, okay'' to babu damuwa ganinan ya kashe wayar ya dakko damin kudade biyu ya sa a aljihunsa sannan ya dau bargo ya dora a kan gado yadda bazakai tunanin ba mutum ciki ba,sannan ya dakko wayar da ya fito.


Tun da aber ya fito zuciyarsa ke harbawa tana bugawa da sauri' amma haka ya daure ya cigaba da tafiya har ya karaso in da deen ke tsaye a jikin mota''yana zuwa basiyi watawataba suka shiga mota suka fara tafiya'' har suka dauki hanyar zuwa Kano.

Su Aber dai basu isa Kano ba sai karfe 10 na dare ,alokacin babu kowa sai haushin karnuka ko ina jikake shiru,sha,awar aber ta tashi ,nan danan fa rashiga ruke mara ya na cewa wash deen tai makamin zan mutu, take yashiga antawo sukwata addu,a dake bakin sa yana cije le'be tana fitar da iska,can kuma da abin ya tsanan ta kawai sai yasaki kuka,yana kiran sunan deen,shiko deen futayayi daga cikin motar yana waige waige'' ko zai samu wata yarinyar alokacin'' duk da shi zuciyar sa bataso hakan tafaruba yaso ace mahaukaciya suka samu,yadda za afi ragargaza aber''amma kash bega kowaba.


Yana tsaye a gurin har lokacin yana waige'' waige saiga amrish ta taho jata huce domin zuwa gindin bishiyar nan ta kwanta'' .

Deen ya kella ido a kanta' atake yasaki wani murmushin mugunta yace hahaha aber kashi ga uku.................


Gani yayi Amrish ta fara Ni sa daga ina da suke'' hakan ne ya sa yayi sauri ya bude murfin motar,ya shiga yiwa aber magana yana cewa'' G.M katashi'' nasamo yarinya katashi,ay da jin haka aber ya mike ya fito'' yana magana daker yana cewa" deen ina take, magana nakefa ina take ko sai na mutu ne'' deen ne yace hatacan a tayi kasan bishiyun can'okay to me muke jira mukarasa gurin mana.

Tafiya suka farayi'' deen yana gaba aber a baya har suka karasa daidai gurin da Amrish take.

Itako amrish tana kwance ta rufe idonta taji tsayuwar mutane a kanta da sauri ta mike shiga zare ido tana binsu da kallo'' gaba kidaya tabi ta rufe ''domin bata saba ganin irin wadannan mutanen ba''

Musamman ma aber dake kama da ''yayan 'larabawa, sai ta Gansa kamar aljani'' dan tun da take bata ta蓳a ganin me kyau irinsaba,hana rantsuwa dai taga wan da yake da kwatan kwacin irin kenshi shine,ayyuf amma ban da shi babu wan da ta taba gani.


Jiki babu kwari tashiga ja da baya sabi da, rashin samun abincin da za taci yasa duk jikinta babu kwari,daman da 茩er ta iya karasowa gindin bishiyar.

Murya na rawa ta ce suwaye ku?''
Me nayi muku dan Allah kada ku cutar dani.

Deen ne ya karasa ya caf ko ta tare da rike hannayen ta guda biyun yace'' G.M bissimillah'' Amrish ce tashiga kurma ihu tana cewa'' dan Allah kada ku cutar dani ku barni'' meyasa baku da imanine me nayi muku'' dan Allah ku rabu dani bani da kowa a duniyar nan amma sabi da tsabar rashin imani kuzo zaku ketani'' dan Allah ku bari kada ku aykatamin haka.

Shiko aber gaba ki daya ji yayi bazai iya ay kata zina ba'' kai yashiga girgizawa alamar ba zai iya ba,murya na rawa aber yace deen kacika ta bazan iya ba,bazan iya aykata wannan babban zunubin ba''


Mom ce zaune a gurin boka suna ta asira asirinsu.
Bokane yace Hajiya in dai ba ku yar da an tura ma yaron nan aljanin da zai tun zurashi ya aykata abin da mike so ya yiba'' bazai yiba.

To kenan boka me yaka mata ayi masa?''

Kawai kuyar da a tura masa bakin aljanin da zai sashi ya yi zina.

Hhhh okay babu damuwa zaka iya fara aykin ka..

Nan take boka ya fara aykinsa yana tsubba tsubbansa ,sai ga wata kura ta taso me cike da wasu bakaken abubuwa suka nufi hanyar arewa .

Aber kam yana tsaye a gaban Amrish yana cewa deen ba zai iya aykata zinaba wannan 茩urar tazo ta dakeshi,ta huce,atake ya rufe idon sa ya bude su akan Amrish dake kwan ce tana rokon su su keleta,ta fada kanta,shiko deen ganin faruwar hakan yasa ya dan kau da kai ya saki murmushi domin yasan wannan ba aykin kowa bane sai na momynsa.


Aber kam hannu yasa ya funcike ya gulallen hijabin dake jikinta'' SAiga ko daddiyar Atamfar ta wadda ta dade aduniya ta bayyana,wadda ja daya ABER yayi mata ta yage tun daga sama harkasa.

Atake suffar jikin ta ya bayyana musamman ma nonon ta da suka cika sosai kamar zasu fashe, Allah yayi halitta a jikin Amrish sai dai babu gyara.

Cikin mintuna 茩alilan aber ya gigice ya fita a hayyacina sa 'yana matsar kirjinta kamar Allah ya ai koshi,atake jikin Amrish ya mutu''nan danan ta gama saddakar wa rayuwar ta ba,abakin komai tajeba,dan a yaune tagama tabbatar da zancen anty Asiya da na mutane da suke cemata ita ''yar shegiya she ba ta hanyar haure aka haife ta ba'' yan zu gashi wani yana kokarin keta mata haddi'' tana tsaka da wannan tunanin hawaye yana zuba a kan fuskar ta,taji Aber ya Keta mutuncinta da darajar ta ta ''ya mace,ay batasan san da ta kurma uban ihu ta sume agurin ko motsi batayi ''ta koma tamkar matacciya.


Wannan aljanin da aka turowa aber yana cika aykinsa ya futa daga jikin Aber da duk wani sihiri da yake jikinsa,besan menene daliliba komai na jikinsa ya dawo yadda yake'' haka zalika sha,awar nan ya dai na jinta sai yake tunanin kamar mafarki yakeyi,yasalam me na aykata ne haka,Rufa idon sa yayi ya bude ko zai ganshi a rundunar sojiji na kasar TAILAN amma ina sai yakara ganin shi a gaban Amrish kumama yana aykata Alfasha da ita abin da Ubangiji ya haramta' da yarasa me zaiyi kawai sai ya fashe da kuka kamar ransa zai fita wa'iya zubillahi.


Shiko deen daga lokacin da yaga aber ya rufe idonsa ya cika amrish ya koma cikin mota. Sai da ya fahimci aber ya tabbatar shikadai ya aykata wannan ayka aykar sannan ya fito yana cewa G.M'' wai ina kashi gane daga cewa zakai futsari kuma sai kabar ni acikin mota ni kadai..

Aber ne yayi saurin cire abarsa daga gaban Amrish,ya dakko hijaf dinta ya rufa mata'' sannan ya ce deen kagani yafada murya na rawa.


Deen ne ya karaso gurin in da kasan besan mene ya faruba yace. Innalillahi wainnailaihirraju'un G.M me ka aykata haka me nake gani?'' innalillahi wainnailaihirraju yanzu Aber karasa wadda zaka aykatawa feyde sai mahaukaciya'' me taimaka''anyako Kanada imani ,sai ya saki kuka,yana cewa wallahi aber na yi danasanin saninka amatsayin abokina kuma 蓷an uwana.

ALLAH sarki aber ne ya karaso gabansa ya fashe da kuka yana cewa dan girman Allah deen kayimin rai'' wallahi bansan na aykata hakanba kuma bansan meyakawo mu nan ba'' dan Allah kada kataramin mutane ka taimaka,ya karasa maganar yana kuka.tare da juyawa yana kallo kekkewar fuskar Amrish wadda tadade da kumbura tsabar kuka.



Innalillahi wainnailaihirraju'un Alhaji zata kasheni. Wallahi bina takeyi tana cemin'' ta tsaneni'.....

Ya isa haka asma,U '' ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment