Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don Allah ki sassauta mata mana kowanne bawa baya wucce qaddararsa kece kike fada mana haka kullum...." Katseshi tayi da cewa “wlh idan Habibatullah bata bacemin daga qwayar idona ba saina tsine Mata ta qara tambadewa ta lalace gabadaya"
Miqewa Habbatullah tayi idanunta na shararar da hawaye tace “indai hakan yayi miki nima yayimin Addah amma ki sani duk halin dana tsinci kaina a ciki nan gaba babu hannun Pappa kece me ruwa da tsaki domin kema uwar da kika haifeni kin gujeni kin qyamaceni Addah bazanji ciwo ba kuma bazanji haushi ba idan mutanen duniya gabadaya zasu qini"




Tana gama fadin haka ta juya ta fice da sauri ta dauki akwatin ta tana kallon gdan tana kuka a ranta tanajin anya kuwa ita ba yar tsuntuwa bace, biyota Ibrahim yayi ya riqe akwatinta yace “wlh babu inda zata Addah saidai ke ki tafi tunda ke kinsan inda zaki ita kuwa fah Ina ta sani hannun wa zata qara fadawa? Haba haba Addah wannan rashin adalci ne kiji tausayinta mana a yanda take dinnan ga dare yariga yayi"
Qwacewa tayi tace “wlh tallahi saina fita daga gdannan Ibrahim gara ta kwana cikin salama koda ni zan kwana a saman juji nasani duk yana cikin qaddarata"
Ficewa tayi da sauri Ibrahim yabita yana roqonta ta dawo ta tsayar da Napep ta sanya kayanta ta juyo ta dafa kansa tace “kada ka damu qanina zan shiga cikin garin Gombe zan nemi gida na kama kafin Addah ta sauko nayiwa kaina dakai da Addah alqawarin bazan qara aikata wani abu na sabo ba insha Allahu ka tayani da addu'a kaji?" Hawayensa ya share yace “amma aunt...." Rufe masa baki tayi tace “nafi buqatar farin cikinta da nawa kaima kayi biyayya da farin cikinta kaji Addah tariga ta rantse idan na samu gda zan fada maka sai kazo ka gani"




Kudi ta zaro masu yawa a Jakarta ta basa tace “ka kula da kanka kafin muyi waya kaji qani na" Napep din ta shiga tana hawaye tana daga masa hannu shima yanayi yana daga mata harta qule, sunyi tafiya me tsayi kafin su fito gari da yake darene qofar wani hotel yakaita ta sauka ta biyasa ta shiga ta kama daki suka bata mukulli ta shige ciki tayi wanka ta fada gadon tana rera kukanta me ban tausayi tanajin wayarta tanata ring amma takasa duba ma wayene saboda ji takeyi kamar ta kashe kanta ta huta da wannan quncin rayuwar, tambayar kanta takeyi ita yaushe zatayi farin ciki ne a rayuwarta?.........






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[7/29, 9:18 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI* ✈️

*PAID BOOK*


_Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200_

_Account number_

_0255526235_

_Fauziyya Tasi'u Umar_

_GTB_

_Ko katin waya MTN ta wannan number_

_09013718241_

_Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi  daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria._


*Episode 30*

 

*END OF THE PART ONE*

 

Ta jima a kwance tana tufkawa da warwarewa kafin ta miqe ta dauro alwala tayi nafila raka'a biyu ta me neman gafarar ubangijinta a bisa laifukanta da suke bibiyar rayuwarta.
Wannan dare bata kwanta ba sai bayan sallar asuba ta koma ta kwanta tanajin zuciyarta tanayi Mata zafi tashin hankalinta shine batasan inda zata nufa ba babu inda tasani a cikin garin gombe balle tace zataje, tananan kwance har azahar tanata juyi wayarta da take charge ta qara bugawa tayi qarfin halin miqewa daqyar ta dauko wayar tayi murmushin yaqe tace “Ibrahim Ina cikin aminci kayi hqr kaji don Allah duk ranar da Addah ta sauko ta yafemin ta yarda da qaddarata a matsayin tata ka fadamin kaji..."



Ta qarasa maganar cikin shassheqa numfashi Taheer ya furzar yace “yanzu kina ina?" Saurin sauke wayar tayi saboda ko muryarsa bata qaunar ji shine sanadin faruwar komai, tsorone ya kamashi.
Itakuma ta manna wayar a qirjinta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi wannan rana azumin dole tayi kiran duniya Taheer yayi mata taqi dauka sai bincike suka shiga Allah yasa dan Napep din daya daukota na gidane shine yayi masa Jagora har hotel din ya bashi kyauta me kauri ya shiga ciki Koda aka kirata aka sanar da ita mijinta yazo cewa tayi batada appointment dashi.



Saida ya tashi hankalinsu sannan suka rakashi dakin nata yayi knowking bugu biyu ta taso tunaninta  abinci aka kawo mata da hijjabinta qato har qasa ta bude, ja tayi da bsya da sauri tana danna qofar ya riqeta da sauri ya danna ya shiga ya mayar ya rufe yana kallonta cikin tsananin qaunarta da tausayin kansu ya matsa gabanta ta janye tace “don Allah ka tafi Taheer wlh banason ganinka banaso Taheer kaje kawa...."
Cafkarta yayi ya hada bakinsa da nata tanata qoqarin qwacewa shikuma yana qara shigewa jikinta har suka zube a gadon ya janye da sauri yace “ohhhh meye yasa zakiyimin haka habeey zuciyata tana gurinki ke kuma kina qoqarin turamin takaici da wanne zanji ne ya kikeso nayi"


Janyewa ta sakeyi tace “nikuma banason ganinka na tsaneka ya zanyi na cireka cikin qaddarata tunda na hadu dakai qaddarorina suka qara tsanani Taheer nasan badon shegen cikin nan nakaba da mahaifiyata bazata qyamaceni hakaba shikenan itama ka dasa Mata tsanata a kunnena akan idona Addah take cemin ta tsaneni na fice Mata daga gdanta inba hakabs ta tsinemin Taheer nikam nashiga ukuna waye zai soni waye zaiji tausayina..."
Matsawa yayi sosai numfashinsu na bugun juna yace “duk duniya nafi kowa sonki wlh har mahaifiyarki nafita sonki habeey bazan taba gudunki a cikin hayyacina ba kiyi hqr nasan nine silar faruwar komai nima a cikin qaddarata kike"



Shiru yayi na wani dogon lkc kukanta na dukar masa zuciya ya janyota jikinsa ya sanya hannunsa ya shafa cikinta yace “bakici abinci ba kin barmin baby da yunwa ko?" Numfashi taja ta miqe ta diro daga gadon yayi murmushi da yawan Mata ciki muni yake sanyasu itakuwa gwanarsa wani sihirtaccen kyau ta qara, wayarsa ya dauka ya fita ya jima yana waya da Hajiya Dije kakarsu ta wajen uba bai boye mata komai ba yana kuka ya zayyane mata komai itama cikin tausayin kanta da jikokinta tace.
“Kowanne bawa baya wucce qaddararsa Taheer ka kawomin ita har zuwa lkcn da zuciyar mahaifiyarta zatayi sanyi haqiqa yarinyar tana buqatar kulawa idan aka qyaleta ta qara fantsama duniya bazataji kira ba saboda zata cigaba da daukar bata da wani me tausayinta a duniya"



Yaji dadi sosai na yarda kakar tasa ta fahimceshi yanzu ne hankalinsa zai kwanta yakuma ji da rikicin cikin gdansu, abinci ya nema Mata ya dawo ya tararta ta fito a wanka tana tsane jikinta da towel saida numfashinsa ya dauke saboda wani yanayi daya shiga yayi saurin juyawa ya fice saboda baison sake sanyata cikin damuwa yanzu nutsuwa tafi buqata.
Saida ya daidaici ta gama sannan ya dawo ya tarar da ita a saman sallaya ta idar da sallar La'asar ta dago sukayi ido hudu yayi mata murmushi yace “kinfi kyau kina murmushi Hurul ainiy" qasa tayi da kanta ya matsa ya zauna yace “kiyi marnege da wannan Grandny tanacan tana shirya Miki tuwon alkama miyar danyan kuka nasan baby na zaiso tunda shi babansa yakeso"




Kallonsa takeyi har ya bude abincin ya debo a cokali yakai bakinsa ya tauna sannan ya matsa gabanta ya kamo kanta ya dagota ya juye mata a bakinta ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi yayi ya hada mata tea tanacin abincin tanashan tea din tana kallonsa saida ta qoshi ya qyaleta ya miqe ya fara hade mata kayanta yana zubawa a akwatinta babban ta matsa gabansa tace “ina zamu Taheer nayiwa addahta alqawarin bazan qara zina ba a rayuwata don Allah kada kace zaka mayar dani gdanka ka massheni kamar matarka"




Dagowa yayi ya kalleta yace “nima nayi alqawarin bazan sake tursasaki kiyi abinda bakiso ba a yanzu nutsuwarki nafi buqata Habeey azare zan kaiki gdan kakata wacce ta haifi babana nasan Zaki samu rayuwa me dadi anan har zuwa lkcn da Zaki haihu sai muyi aure mu raini babynmu cikin kulawa da soyayya nasan Granny zata soki saboda ta taba ganin hotonki a wayata ta qare miki kallo tace kina mata yanayi da wani data sani koda yake tace da yayan Abbanmu Sahabi kike mata kama"
Zama tayi tana kallonsa har ya dauki kayan ya fita ya sake dawowa ya kamo hannunta yace muje ko?"




Batayi masa musu ba suka fita ya bude mata suka shiga suka dauki hanya lkc zuwa lkc yana kallon yanda tayi tagumi hannu biyu tana sharar hawaye, basu isa Azare ba sai bayan isha sosai yabi wata hanya.
Itadai gabanta sai faduwa yakeyi saboda tunanin me zataje ta tarar acan din, parking yayi a gaban wani gda babba gaban get din gidan cike da almajirai sunata karbar abinci, yayi horn masu gadi suka bude masa ya shiga Granny tana tsaye a saman bene ta hangosu yana fito da kayan itakuma ta koma gefe ta zauna a saman wani dutse tanata sharar hawaye gabanta naci gaba da faduwa.
Tsugunnawa yayi a gabanta yace “inada tabbacin bazaki taba samun matsala anan ba My Habeey shiyasa na kawoki ki saki ranki kiyi rayuwa me dadi, kamota taji anyi ana cewa "yo karma ta saki ran nata mana basai na qwanqwashi kanta ba" dariya yayi itakuma ta kwantar da kanta a kafadar Granny tanajin gabanta na tsananta faduwa itama Granny faduwa gabanta yakeyi ta shafa kanta tace “ki kwantar da hankalinki kinji Habibatullah insha Allahu zakiyi farin ciki zakiji dadin rayuwarki a gaba farko rayuwarki qunci qarshenta walwala da farin ciki dawwamamme" a haka suka shiga ciki Granny tana cewa“Taheer yanzu babarka ta kirani take fadamin kana neman bijirewa auren Saudat........"




_Tashin hankali kunji fah wata sabuwa Taheer zaiyi aure, wacece Saudat da zai aura? Meye ya San gaban Granny da Habeey ya fadi lkcn da sukayi arba da juna? Shin wai Taheer ma zaiyi biyayya kuwa wa zabin iyayensa? Wannan amsoshin sai a DUBAI PART TWO._



_Wannan shine qarshe part one na wannan lbr wadanda suka ruga sukayi subscribe dani akan lbrn bandaku masu so nan gaba zaku biya kudinku ta wadannan hanyoyin dake sama_



_Zakujini Shiru na kwana uku Ina cikin wani uzuri ne insha Allahu nan da kwanaki ukun zamu dora daga inda muka tsaya_





*UMMUH HAIRAN CE...✍️*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment