Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(Ummu meenal)*


*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*


*Short story*

*page 21-25*


*WANNAN SHAFIN NAKUNE ❤ DANIDA MIJINA FANS*❤


Umma tana ganinshi hankalinta ya tasha tafara kuka lafiya affan meya sameta?
Shikanshi affan baesan meyake faruwa da itaba saboda haka bashida ansar da xai bata
Can yayi qarfin hali yace umma bara nakira baba yaxo da mota aje asibiti
Umma tace hi sauri kakirashi kada afra ta mutu
Kafin affan ya kira baba afra ta farfado tana fadin
Ruwa ruwa muryanta duk ta dushe da alama taci kuka harta qoshi
Umma cikin sauri ta dauko pure water tafasa tabata aiko tasha ruwan sosai ahankali ta koma kan cinyar umma ta kwanta ita kuma umma tasa affan ya dauko mata towel tana sawa cikin ruwa tana dafawa afra cikin ikon Allah xafin xaxxabin ya tafi
Shi kuma affan sai kiran wayar baba yakeyi Amma bai samuba daga qarshe ya tsaya yana kallon soyayya tsakanin umma da afra affan yayi murmushi cikin ranshi yace umma ko kinaso ko bakiso saikin rabu da ita nan da kwanakki kadan xataje makaranta
Ita kuma afra barci ta koma abunta sannan umma tace mashi Naga kamar jikinta da sauqi tunda tasamu barci kaje kasiyo mata magani idan ta tashi saita sha
Haka ya fita da niyyar siyo magani akan hanya ya hadu da wasu abokanansa suna ganishi suka fara
Ango ango
Cikin mamaki yace waya fada maku ni ango ne
Aliyu daya daga cikin abokanansa yace
Aini wlh baba ya burgeni da yayi maka haka ace kayita xama babu aure yanxu ko da yayi maka haka aiya kyauta
Affan cikin jin haushi yace idan banyi aure ba ina ruwanka kai bakayiba
Aliyu yayi dariya yace affan bakasan ni imar da take tartare da aure ba shiyasa amma yanxu ranar da aka kaimaka mata washe gari idan munxo xamuga canji
Affan yace Dan Allah kubarni da maganar auren nan ni wlh ba a son raina xanyi auren nan ba duk daga baba ne
Aliyu yace affan waiko bakada lafiya ne
Affan yayi murmushi yace kafi kowa Sanin lafiya ta Lau saboda idan sha awa na yatashi kai kake siyo mun magani
Aliyu yace ai yanxu matarka itace maganinka
Affan yace kai mexanyi da wannan yarinyar afra ce fa xan aura
Dariya sukayi gaba dayansu
Affan yace wannan yarinyar tayimun qarama ai sai inraba biyu
Dariya suka sake gaba dayansu


Ana saura sati daya biki mutanen xamfara sukaxo harda yayyen amarya da abokanan arxiqi aunty Asma u harda guxurinta na kayan mata sai dai umma ta hana abata a cewarta sai lokacin tarewa yayi
Afra kam tasha kuka harta godema Allah shima affan ya barwa Allah komai tunda dai ba fasa auren xa ayiba

Maganar kayan daki babu abunda aka siya sai lokacin tarewa yayi tunda yanxu karatu xata cigaba dashi bayan daurin aure
Ranar jumma a abokanan affan Sunxo har gidansu affan Sun iske gida ya cika da mutanen biki da qyar sukasamu suka shiga dakin ango Sun sameshi kwance ko tunanin me yake Oho
Aliyu ne ya dauko wata baqar leda ya bashi
Affan yace menene wannan?
Kayan daxakasa kaje daurin aure ne
Affan ya hade rai yace Kaga malam ni anfada maka xan tsaya sa wani sababbin kaya ne ni qila daurin auren baxan samu xuwa ba
Dariya sukayi abokanansa sannan shima affan yace
Ana daura aure xata kama gabanta Dan makaranta xataje ni kuma xanje bautar qasa

Ranar assabar misalin qarfe goma sha biyu dubban mutane suka shaida daurin auren affan da afra akan sadaki dubu hamsin inda ango yasha manyan kaya babu laifi ya dan saki fuska Amma a cikin ranshi ko kadan baya murna da wannan auren
Ita kuma afra tanajin labarin an daura aurenta da affan ta fara kuka sosai tana fadin nabani an daura mun aure da mugun mutum yau nashiga uku wlh baxan xauna dashiba tunsu aunty fatima suna bata haquri har Sun gaji Sun fara yimata fada
Aunty Asma'u cewa tayi
Afra bawai affan baya sonki bane halinki ne bayaso idan kin gyara halinki sai kiga kun xauna lafiya
Afra taqara fashewa da kuka tace ni banason Shi
Duk abunda takeyi affan yanajinta saboda masu karatu kunsan gidansu daya
Ran affan ya baci da kalamanta bawai Dan tace bata sonshi bane jin haushi a'a wai shi take kira da mugu lallai xataga mugunta
A hankali ya qaraso inda take yace
Ke nikike kira da mugu ?
Tayi shiru saita turo Dan madaidaicin bakinta
Bata saniba ashe su aunty fatima sun bar dakin lokacin daya shigo
Aiko gabanta ya fadi tayi saurin tashi da niyyar fita ya riqo hannunta yace
Ina xakije
Dakin umma
Affan yace ni kike kira da mugu ko?
Afra tayi shiru idanunta suka fara cicciko da hawaye
Ba tambayar ki nakeyiba? Waye mugu?
Nanma tayi shiru
Affan yace to tunda kince mun mugu xakiga mugunta baxakici gabada karatunki ba kuma sati na sama tarewa
Afra ta xaro idanuwanta ta dafe qirji tace
Dan Allah yaya affan kayi haquri wlh baxan sakeba Dan Allah
Murmushi yayi Dan dama wasa yakeyi mata
Bani kike cewa mugu ba
Natuba baxan qara ba Dan Allah tasaki sabon kuka afra kenan kuka baya mata wahala


*ummu meenal
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤

*NA MRS SADEEQ ( ummu Meenal)*



*DEDICATED TO AYSHA GALADIMA*


*short story*

*page 26-30*


*MASOYA NA A DUK INDA KUKE INA GODIYA SOSAI DA MASU SON NOVEL DINA DA MASU YIMUN MAGANA A PRIVET DUK INA GODIYA*

*TUKWICI GAREKI AYSHA*


Haka akayi taron biki lafiya dukda dai ba wani taron akayiba saboda cewa akayi sai a tarewa xa ayi taro
Amarya afra ta rame dama gata ba qiba gareta ita yanxu tunda an daura aure burinta ta cigaba da xuwa makaranta kada affan ya hanata dan tasan ba qaramin aikinshi bane
A bangaren affan kuwa yanacan dashida abokanansa sai xolayarshi sukeyi tun baya tanka masu harya fara maida masu
Affan yace ni cikin satin nan xan kaita makaranta a huta danni ko ganinta banasonyi
Bello daya daga cikin abokin affan yace haba malam ai dai yakamata kabari ka angwance a daren yau koba hakaba ya tambayi sauran abokanansu
Aliyu yace a a qara ta tafi tun yanxu saboda idan ya tare yaji yanda aure yake ai saiya tauye ma yarinya haqqinta yace baxata cigaba da karatunba
Affan duk firan da sukeyi yanajinsu haushi ya hana yayi magana


Yaune affan yaxo da transfer na makarantar afra yana fadawa umma angama komai ko yauma xata iya xuwa G G S S JIBIYA
Umma tace bangane ko yau xata iya xuwa ba ina kayan provision?
Yace umma bansan me take buqata ba kitambayeta
Umma tace ni xan tambayeta kenan daukarta xakayi kuje ta xabi abunda takeso
Affan yace umma taje dai ta siyo tunda ba mota gareni ba
Dan bakada mota shine baxakaje ku hau napep ba
Ran affan ba haka yasoba Amma babu yanda xaiyi dole ya amsa mata
Umma to tashirya anjima xamuje Mu siyo umma tace to Allah ya kaimu

Umma ta tashi taje dakin afra ta sameta tana sana an kuka umma tace haba afra wai har yanxu baxaki daina kukan nan ba saikin jawa kanki ciyo
Afra ta dago manyan idanunta da suka koma ja saboda kuka tace umma banason auren nan Dan Allah kice ya sakeni...
Umma ta rufe mata baki da hannunta tace kul na hanaki daga yau karki qara cewa affan ya sakeki kinsan babu kyau mace tace mijinta ya saketa
Afra ta rushe da sabon kuka tarasa ina xatasa kanta
Kishirya anjima xakuje kuyi siyayyan xuwa makaranta
Umma dawa xamuje ?
Da mijinki
Umma basai munje tareba kuma banason ya siya mun komai ke nakeson kisaya mun
Umma tayi murmushi cikin ranta tace bakyason abun hannun affan Amma kinason nawa lallai wannan qiyayyar tayi nisa
A fili kuwa cewa tayi a a afra affan shine wajibi ya siya maki baniba ita dai afra shiru tayi
Sai bayan lah asar sannan affan ya fito yacewa umma shidai ya shirya umma tace to kaje kagani ita ko ta shirya
Da kamar baxaijeba kuma saiya tuna mahaifiyarshi ce
Dakinta ya shiga ya sameta xaune da alama bata dade da gama sallah ba daga qofar dakin ya tsaya yace
Kifito mutafi
Ko kallonshi batayiba tace to
Nifa banida lokaci kina wani to idan xaki tashi kitashi kinma ci albarkacin umma
Haka ta tashi da hijabin da tayi sallah har sunkai bakin qafa afra ta koma tacewa umma umma mun tafi
Umma taji dadi a tunaninta Sun fara shiryawa ne tace to adawo lafiya
Dan Allah afra karkiyi rashin kunya kinsan dai da Wanda kuke tare
Batayi magana ba ta juya ta koma qofar gida ta iskoshi yana jiranta
Tafiya sukeyi babu mai magana cikinsu har suka samu napep suka shiga babu mai magana musamman affan da yayi kamar bada ita yake tafiya ba
A super market afra qin xaban komai tayi itama wai fushin takeyi (nidai nace afra ki sassauta fushinki kixabi kayan abinci mai rai da lafiya Dan bourding skul xakije)
Shi kuma affan gefe daya ya tsaya yana kallonta Dan shima yasawa ranshi cewa indai afra bata xabi abunda takesoba to shima baxai daukar mata komaiba ba wai Dan bashida kudin ba aa idan tana taqama ba ason ranta aka aura mata shi ba to shima ba ason ranshi ya aure ba Dan haka baxai xauna yana bata lokacin shi akantaba

Haka tagama yawonta cikin super market babu abunda ta dauka daga qarshe ma wajenshi ta dawo tace tagama yace ina kayan tace ita batason komai
Baiyi mata gardama ba yace to mukoma gida haka suka koma gida babu siyayyar komai

Suna shiga gidan umma ta gansu babu komai tace to ina kayan ?
Affan yayi saurin cewa
Umma munyi siyayya to bayan mungama sai muka hadu da wani kuma a makarantar yake shine nabashi kayan nace yakai mata makaranta kinga an rage kaya kenan umma tace to kasanshi ne affan yace sosai ma kuwa umma
Umma tace aiko ya kyauta yanxu saitaji da skull back da uniform
Affan yace hakane umma

Yaune afra xataje makaranta kuma affan shine Wanda xai kaita daga kaduna xuwa jibiya akwai tafiya Dan haka affan ya anshi motar baba xai kaita
Tunda safe afra take kukan rabuwa da umma ita kuma umma sai lallashi takeyi tana yimata nasiha
Kiyi haquri afra bafa wani dadewa xakiyi a makarantar nan ba iyaka wata uku ne
Umma yanxu har xanyi wata uku ban gankiba umma baxan iyaba
Umma tace kinsan xan rinqa xuwan maki visitin
Da qyar umma ta kwantar mata da hankali ta daina kuka
Haka suka kama hanyar jibiya tana cike da kewar umman ta
(Su afra haka xa aje makarantar babu provition?)



*ummu Meenal ce*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤


*NA*
*MRS SADEEQ (ummu meenal)*



*DEDICATED TO

*AYSHA GALADIMA*




*Short story*

*page 31-35*


*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA PRINCIPAL DIN MAKARANTAR G G S S JIBIYA ALLAH YAKAI HASKE A KABARINKI ALLAH YA JIQANKI DA RAHAMA DUK MASOYAN DANI DA MIJINA YACE AMIN YA ALLAH*



Haka suka isa qofar makarantar babu mai magana cikinsu saida aka kai dai dai qofar makarantar sannan afra tafara hawaye affan yayi kamar bai gantaba saida tagama kukanta sannan yace ta sauka afra ta tace
Baxan ganeba bansan kan makarantar ba tana kuka yace ina ruwana bake bakyajin magana ba har kinsa an daura mun aure dake ko to wlh sai kinyi Dana sanin aure na sauka narakaki badan halinki ba
Babu musu ta fito cikin motar ta bishi duk inda yaje haka suka kai har office din prinsfar hafsat mai mutunci basu bata lokaci ba prinsfer tabata class j s s 2 sannan takira wata daliba tace ta nuna mata hostel din j s s 2
Dalibar ta kalli afra tace muje na nuna maki dama antashi yanxu hostel xamuje afra tace to
Ina kayan naki na taimaka maki afra ta kalli affan sai taji hawaye Sun fara wanke mata fuska
Affan kauda kanshi yayi kamar bai ganta ba sannan tace banida kaya muje kawai
Affan ya tausaya mata sosai daga Sun tafi babu kaya har sunyi nisa ya kirata ya dauko dubu biyar ya bata yace ko xata nemi wani abun
Haka ta ansa harda godiya sannan ta juya tabi hanyar hostel
A dauramar baya ta sauka kuma post kwana dama duk kwana mutum hudu hudu ne sai tayi sa a lokacin da taxo hadixa aliyu jibiya tabar kwanar saita xauna a madadinta
Sai dai afra batasa komai a lokar data isko ba saboda babu kayan
Ko xaunawa batayiba sai taga yan hostel sun fara fita one by one kuma kowa da robarshi da alama dinning xa aje a anso
Afra kam ko robar ansar dinning babu kuma ga yunwa tafaraji Dan
Haka saita xauna akan gadon kwanar saboda yan kwanar basunan sunje dinning
Tana cikin tunanin gida sai taji hayaniya kafin ta dago kanta sai gani mutane tayi sunata wuceta dayake post kwana take
Wasu suce mata sannu wasu kuma su qyaleta wasu su shigo da waqa wasu kuma rawa anyi shinkafa da wake a dinning tana nan xaune saiga yan kwana Sun dawo
Sunyi mata sallama ta amsa
Daya daga cikinsu wadda ake kira nana bilki ita tafara yimata magana
Sannu sister
Yauwa sannu
Munyi baquwa ne inji maryam hamisu
Afra tayi murmushi tace eh
Nana bilki tace kai kyakkyawa kuwa
Tace nagode
Nan yan kwana suka bude lokarsu kowa ya dauko manja da yaji da mai star suna sawa a dinning kunsan dai daining ba dadi gareshi ba
A bangaren affan yanata shirye shiyen xuwa service sai dai har yanxu baisan inda xaije service din ba Amma ya shirya komai lokaci kawai yake jira

A bangaren umma tayi kewan afra sosai Dan har tanaji idan ta dawo baxata komaba sai dai kuma ba yanda xatayi dole ta haqura ta Barta ta koma indai tanason karatun afra

*G G S S JIBIYA*
Misalin qarfe biyar da rabi afra tana hostel kwance akan gadon nana bilki
Nana bilki tace afra kitashi muje dinning
Afra tace banida roba
Laaa bakixo da roba ba ?
Kai kawai ta daga mata alamar eh
Nana bilki ta dauko wata robar irin ta almajiran nan tace gashi
Haka afra ta anshi robar sukaje dinning
Wani uban layi suka isko suka tsaya a bayan layin Ana xubawa har aka kawo kansu tuwon tsakin masara ne da miyar kubewa busashiya
A hostel afra ta bude robar tuwon kamar tayi amai sai taga kowa yana Dan qara manja da maggi ita kuma batadashi
Sai a lokacin tayi danasanin daukar kayan provision din da sukaje shopping taqi dauka
Har tafara cin hakanan tunda batada komai kuma ga yunwa tanaji tanaci tana bata fuska kamar xatayi amai
Maryam hamisu tace wai sister haka kike cin abincin ne ?
Afra tace baxan iya cin abincin nan ba babu inda ake saida wani abu Dan Allah yunwa nakeji saboda ta tuna da kudin da yaya affan ya bata
Maryam hamisu tace akwai shop Amma ba a budewa saida rana ko idan antashi break fast kuma ba tuwo ko shinkafa ake saidawa ba
Afra tace me ake saidawa ?
Biscuit sweet madara cabin da sauransu
Afra tace gobe xaku kaini xan siya madara baxan iya cin daining ba
Sukace Allah ya kaimu
Nana bilki ita ta xubawa afra manja da yaji harda maggi a cikin tuwon sannan afra tasamu taci abincin shima kadan taci

*A KADUNA*
Service din affan ya fito Amma abun mamaki sai aka turashi G G S S JIBIYA 😨 wato makarantar su afra
Umma kam murna tayi sosai a cewarta xai Kula mata da afra*
Shikam affan hakan ba qaramin jin haushi yayiba saboda yana murna tayi nesa dashi gashi kuma yanxu Sun dawo kusa
Lokacin dayake fadawa su aliyu an turashi service a jibiya ba qaramin murna sukayi ba har xolayarshi sukeyi wai shima yanaso yana nuna bayaso
Aliyu yace nasanma har gida anbaka a makarantar
Affan yace to Dan anbani gida a makarantar sai akayi me?
Saika dauko matarka daga hostel kamaidata dakinka tunda a skull dinne Kaga da safe kushirya kushigo aria skull 🤣
Affan yace wlh kunfara kaini ga bango banason wannan game din babu abunda xanyi da wannan yarinyar Allah ya sauwaqe nafi qarfinta ya fada cikin fada😡
Aliyu yace idan xakaje sai kaje da maganinka kada jarabarka ta tashi ka afkawa yar mutane 😜
Affan Dan haushi ko magana yakasayi haka suka rabu suna xolayarshi
Ana gobe xaije service suna xaune da umma da affan sai nasiha take mashi
Dan Allah affan kariqe qanwarka amana karka biyewa halinta Kaga matarka ce kuma qanwarka Dan Allah ka Kula kuma ka Kula da karatun ta Dan Allah karka takuramata kasan dai yarinya ce
Affan yace ai umma dakinsu daban dakina daban sai skull eria ne kawai xamu hadu da ita
Umma ta dauko dambun nama tace gashi kabata kace ina gaisheta
Yace to xataji
Ranar da xai tafi saiga aliyu da mota yace shi xai kaishi jibiya
Affan yace xakaje dai gulma kawai
Ya tuntsure da dariya yace aa wlh Kaga bodar Niger nakeson xuwa to Naga duk hanya dayane shine nace bara kawai Mu wuce tare
Affan yace kai kasani kayi gulmar ka kagama
Cikin ikon allah sun sauka lafiya Dan aliyu har dakin affan ya rakashi sannan yayi mashi fatan alkairi ya wuce gaba
Shi kuma affan ya tsaya yana Dan gyare gyaren gurin Dan yayi qura sannan yaje ya kwanta saboda gobe Monday xaije fara xuwa karantarwa kuma ya gabatar da kanshi wajen dalibai. ......


*kubiyoni*
*ummu meenal ce*
[9/4, 4:29 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤


*STORY AND WRITING BY*
*MRS SADEEQ (ummu Meenal)*


*DEDICATED TO*
*AYSH GALADIMA*


*short story*

*36-40*


*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana baxan iya qirga sunayenku ba saboda kuna da yawa da masu bina pc suna nuna qaunar nevel din DANI DA MIJINA duk ina godiya muna tare🤝🏻*


Da asuba afra tana barci can cikin barcin taji ana tashinta kamar a mafarki ta farka sai taga duk yan hostel sun tashi itama tayi saurin tashi ta dora alwala danyin sallah asuba

A bangaren affan kuwa ya shirya cikin kayan nysc kayan ba qaramin kyau suka yimashi ba sai qwarjininshi ya qara fitowa saida ya gama shirinshi tsaf sannan ya fito xuwa area skull

Ita kuma afra bayan Sun gama share sharen su ta koma guri guda ta xauna saboda yunwar data dameta har wani jiri take gani batasan lokacin da tafaďa tunanin gida ba lokacin da tana gida umma har lallashinta take taci abinci Amma saita gadama takeci Amma yanxu gashi tana son abinci Amma babu sai dinning kuma sai 10am ake badawa kuma babu dadi uwa uba baxai isheta ba
Batasan lokacin da tafara hawaye ba sai kuma ta tuna lokacin da sukaje shopping da yaya affan yace ta xabi abunda takeso tayi banxa dashi yau gashi tana nema bata samu ba tana cikin tunanin ne sai taga wata mai irin kayan ta uniform taxo ta gabanta xata wuce afra tace
Sister Dan Allah xan tambayeki
Dalibar ta juyo tace inajinki sister
Afra tace Dan Allah inane shop ni baquwa ce bansan ko ina ba sai class da hostel yan kwanar mu kuma sun fita bansan inda sukaje ba
Dalibar tace eyyaa sannunki da xuwa ni sunana xainab gide kefa ?
AFRA
Xainab tace xomuje dama nima can xanje suna tafiya suna Dan taba fira har suka isa shop din
Afra ta dauko kudin da affan yabata dubu biyar ta siya madara da Milo sai bournvita da cabin ta siya suga daganan kudi ya qare baifi yan canji suka rage mata ba

*ASSEMBLY*
Principal tsaye a gaban assembly tana jawabi kamar yanda ta Saba dalibai suna sauraronta kamar a mafarki afra ta hango affan cikin kayan nysc saidata qara bude idanunta ta gani kodai mafarki takeyi aiko ba mafarki bane a xahiri ne sai taji principal tana gabatar da affan a matsayin malamin makaranta xai koyar da maths kuma a j s s 2 😳 ajinsu afra kenan
Principal ta cigaba da jawabi akan uncle affan tace dafatar dalibai xasu bashi hadin kai kuma suyi mashi ladabi da biyayya
Afra har cikin ranta taji dadi saboda taga na gida kunsan yan bourding da son ganin na gida😜
Cikin daliban j s s 3 taji wasu suna cewa wallahi kyakkyawa dashi ni ya burgeni afra sai tayi murmushi tace bakusan Waye yaya affan ba
Bayan an tashi break fast afra taje dinning har tabi kayi ta tuna da batada cup din karbar koko kuma gashi tanajin yunwa dama nana balki ce ta ara mata dayan cup dinta kuma an sace gashi yanxu tanason karbar koko babu cup
Kawai wata xuciyar tace kije wajen yaya affan ko xaki samu aiko batayi musu ba ta koma office dinshi da gudu knocking batayi ba tashiga office din saboda kada koko ya qare tana haki ta shiga
Shi kuma yana xaune lokacin ba a dade da kawo mashi waina ba sai tururi takeyi da xafinta taji nama da qashi xai faraci kenan sai ganin afra yayi tashiga a guje
Kallonta ya tsaya yanayi ita kuma ta sunkuyar da kanta qasa saida suka danyi mintuna haka sannan dayaga batada niyyar yin magana yace
Ke lafiya kika shigomun office babu sallama fuskar shi a daure
Afra cikin in in na tace
Am um Dan Allah naxo ka aromun cup xan karbi kunu kada ya qare
Saida dariya taxo mashi Amma gudun raini saiya qara daure fuska yace
Anfada maki ni sa ankine da xanxo da cup?
Ubanwa yace kishigomun babu sallama
Afra gabanta yana faduwa tace wlh yaya yunwa nakeji Dan Allah ka taimaka mun tafada tana kallon wainar gabanshi
Dan murmushi yayi ya fara takowa xuwa gurinta ita kuma tana ja da baya harta kai jikin bango dama shine wurin qofa
Cire mata hijabin yayi ya riqo gashinta da qarfi aiko ta saki ihu yayi saurin rufe mata baki da dayan hannunshi yace
Xaki qara shigomun office?
Girgixa kanta tayi alamar a a saboda ko magana baxata iya ba
Ke yarinyar nan Dan kin rainamun da hankali shine kikaxo wai in ara maki cup ko ?
Me kika maidani?
Hawaye kawai sukebin idanuwanta kukan ma yaqi fita
Saida yaga dama sannan ya saketa sannan yace duk Wanda ta fadawa xata gane batada wayo sannan yace ta fita tabar mashi office
Cikin kuka ta juya xata fita kuma saiyaji masifan tausayinta ya cika xuciyar shi koba komai matarshi ce dukda baya sonta haqqinshi ne ciyar da ita
Harta kai bakin qofa yace
Afra xo nan
Batajeba saita tsaya a bakin qofa
Yace umma tabani saqo inbaki gobe kixo ki karba
Batace komaiba saita bishi da manyan idanunta
Sannan yace bisimillah xokici waina kinci darajar aure
Afra cikin tsiwa tace baxanci ba (ni ummu Meenal nace abakin qofa xakiyi tsiwar kishiga ciki mana😀)
Affan yace xaki iya tafiya
Bata jira ya qarasa maganar ba ta rufe qofar da qarfi sannan taje dinning
Allah ya taimaketa ta hadu da xainab gide wadda sukaje shop tare ta ara mata cup tayi saurin shiga layi
Ankusa kawowa kanta Sai taga mutanen gabanta kowa ya kamata gabanshi ita kuma tayi tsaye saida wata tace mata sister koko ya qare
Kuka tafarayi sosai kitchen master yaxo yace lafiya?
Afra tace yunwa takeji
Kitchen master yace meyasa bakixo dinning da wuri ba
Afra tace banida cup
Kitchen master yace daga yanxu kinajin an buga dinning kiyi gaggawar xuwa inba hakaba baxaki samuba sannan ki nemi cup afra tace to

Afra suna gaban fanfo yau kwanasu antashi da matsalar ruwa basuda konasha kuma sun dade a fanfo Amma basu samuba dayake layi akeyi kuma har yanxu layin bai kai garesu ba kuma ga qishirwa tanaji haka taje ta kwanta da qishirwa Amma taci alwashin indai taje gida baxata dawo ba

Affan saida ya koma dakinshi sannan yaji wani sabon tausayin afra ya mamaye mashi xuciya yaji kamar yaje dakin ya daukota yabata abinci taci bai gama tunanin ba saiga wayar umma tashigo yayi saurin dauka tareda sallama umma

Please Login or Register in order to submit comment