Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi kyau sosai, tare sukayi breakfast dinsu cikin sha awa ita kanta afra har mamakin kanta takeyi yanda takeson affan da kishin shi har cikin ranta

*BAYAN WATA DAYA*
Affan cikin jin dadi yake fadawa umma cewa yasamu aiki a NNPC farin ciki wajen umma da afra baxai fadu ba afra ta rungumeshi tana murna sosai shi kanshi Affan din murna yakeyi





*taku ummu Meenal*
[9/10, 7:37 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤






*STORY AND WRITING BY MRS SADEEQ* (Ummu meenal)




*DEDCATED TO*
*Aysha galadima*





*short story*
*81-85*




Anyima afra scanning babu wata matsala sai dai Sun hango Dan qaramin ciki 11 days shine silar ciyon Maran dayake damunta
Affan ba qaramin dadi yaji ba daya duba resoult din yaga ciki 11 days wato 1nyt dinsu tasamu ciki kenan cikin jin dadi yacewa Dr xan iya ganinta yanxu ?Dr tace babu matsala kashiga tana barci saboda anbata maganin amai kuma ansa mata drip saboda aman da tayi ya galabaitar da ita
Affan ya shiga dakin da afra take kwance sai yaga ta Dan rame kadan kuma ta qara haske ya duqa dai dai Dan qaramin bakinta yayi kissing dinshi a fili ya furta I lv u hannunshi yasa wajen maranta yaji Maran a lafe kamar babu komai a cikinta dadi yaji yana ratsa shi musamman daya tuna akwai dan shi ko yarshi
Bata farka ba sai wajen qarfe biyu bakinta a bushe tace ruwa xansha ai bata qarasa cewa xatasha ruwa ba affan yayi saurin bata ruwan a baki saida ta qoshi sannan ta kauda fuskarta affan ko xama baiyi ba ruwan da tasha ta dawo dasu saida ta amaryar da ruwan tas affan ya rasa mexai mata yaji wani irin tausayinta ya kamashi ji yake kamar yadawo da cikin jikinshi
Saida ya gama gyara wajen da ta bata da amai sannan yaje ya kira Dr yace yaxo afra tayi amai Dr yayi murmushi yace affan kayi haquri shi aman mai juna biyu ba lokaci guda xai tsaya ba sai a hankali saboda haka idan kaga tayi amai ba matsala affan yace Dr yanxu babu wani magani da xa a bata Wanda xaisa aman ya tsaya?
Dr tace gsky babu duk abunda xamuyi mata munyi so a hankali aman xai tsaya kayi haquri
Affan ya shiga dakin da afra take tana ganinshi ta kauda kanta alamun batason ganinshi affan ya duqa gabanta har qasa yace Dan Allah afra kiyi haquri ki yafemun nasan na bata maki rai ban kyauta maki ba kiyi haquri wannan duk ya wuce Mu shiga sabuwar rayuwa mu tarairayi babynmu da yake cikin ciki kafin yaxo duniya mu bashi tarbiyya......afra bata jira affan ya gama maganarshi ba ta ce me kake nufi yaya? Cikin tashin hankali ' affan yace kinada ciki na kwana goma sha daya 11 days. ..
Afra ta Dora hannu a kai 🙆🏼‍♀ tace na shiga uku yaya ka cuceni tana kuka sosai
Affan yace ban cutar da ke ba kiyi haquri ki fahimce ni
Afra cikin kuka tace wlh baxan xauna da cikinka ba karatu xanyi Dan wlh saina xubar dashi
Affan yasa hannu ya toshe mata baki yana cewa
Koda wasa banason kiqara cewa xaki xubar da cikin nan ciki da ubanshi kice xaki xubar banason jin wannan kalmar
Afra ta buge mashi hannu tace wlh saina xubar nace banaso
Affan kam cikin xuciyar shi kamar garwashi yanaji kamar ya dauketa da Mari Amma yana ganin idan yayi haka ya qarawa kanshi laifi ne gurin afra
Qara duqawa yayi har qasa ya riqe mata kafafuwa yace Dan Allah ki daina cewa xaki xubar da cikin nan kinsan Allah bayaso afra ta maka mashi harara ta sauka daga kan gadon tasa hijabinta tace ni baxan xauna asibiti ba xan tafi staff quaters Dan baxan xauna ina jinya akan cikin nan ba
Affan ya riqe ta yace babu inda xakije sai an sallameki afra ta saki ihu affan dayaga xata Tara mashi jama a sai ya qyaleta yaje yace abashi sallama
A qafa AFRA take tafiya dayake babu nisa tsakanin asibitin GADA da cikin makarantar jibiya shi kuma affan yana bayanta yana lallashinta Amma kamar yana xugata da haka har suka isa cikin staff din afra tana shiga daki ta Kifa kanta kan katifa ta rushe da sabon kuka affan ya dagota yana bata haquri har cikin ranshi bayason kukanta Amma afra bata daina kukan ba
Har cikin dare afra fushi take da affan ya dauko mata maganinta Amma taqishaa affan yace to wlh baki isaba ko dire dure sai nayi maki
Afra dataga affan da gaske yake xai mata dure saita anshi maganin tasha sannan ta kwanta barci

Tsakiyan dare affan ya tashi yayi alwala yayi sallah yana roqon Allah ya dai dai tashi tsakaninshi da matarshi sai wajajen asuba sannan ya kwanta saboda yanason ya shiga class da safe
Da asuba shi ya hada masu break fast saida tayi wanka ba laifi taji dadin jikinta kuma ta saki ranta saboda ta tuna hanyar da xatabi tayiwa affan baqin ciki Dan haka ta saki jikinta taci abinci sosai
Affan sai murna yakeyi a xatonshi daina fushin.
Affan ya shirya yacewa afra shi xai tafi class afra tace saika dawo ya fita yana murna bai kawo komai a ranshi ba
Affan ya fita babu dadewa afra ta rushe da kuka tace mugu kawai saita dauko wayarta ta kira xulaihat tana kuka hankalin xulaihat ya tashi dataji afra tana kuka xulaihat tace lafiya kike kuka ?afra tace na shiga uku Dan Allah kitaimakeni, xulaihat tace taimakon me? Afra cikin kuka tace wai ciki gareni ...ta qarasa ,maganar cikin kuka xulaihat tace alhdlh ai ba abun kuka bane afra ki kwantar da hankalinki xaki haihu lafiya... afra ta katseta da cewa so nake kiyimun text din maganin xubar da ciki Dan Allah
Xulaiha tace ke bakida hankali ne kinsan abunda kike fada kuwa,
Nasani wlh baxan iya xama da cikin nan ba ya hanani karatu na sannan kuma ya hanani naje xamfara kuma yanxu ace inada ciki wlh baxan iya ba
Xulaiha tayi lallashin duniyar nan Amma afra taqi haqura tace ita saita xubar
Xulaiha ta lura afra da gaske takeyi saboda fushin da tayi Dan haka cikin ranta tace xata yimata wayo saboda idanma bata turo mata maganin ba to xataje ta nemo dan haka ta yanke shawarar bara tayi mata wayo , xulaihat ta tambayi afra cikin sati nawa ne? Afra tace 11 days xulaihat cikin ranta tace oh rabo kenan dan haka tayi mata text din wani magani Amma bana xubar da ciki bane wannan maganin yana kariya ne Dan kada ciki ya xube musamman idan ciki yana qarami
Ita kuma afra ta xaci da gaske ne harda murna kuma tunaninta ya tsaya ina xata samun maganin ?wata xuciyar tace kije babban cames xaki samu tayi tsallen murna tanajin dadi dama akwai kudin da umma ta bata lokacin da xasuxo Dan haka bata tsaya bata lokaci ba ta Sanya after dress da gyalenta ta fita
A hanya tasha wahala sosai amma bata samuba saida ta shiga cikin garin jibiya a wani babban cemis ta samu tayi murna sosai wannnan tayi saurin dawowa staff saboda taga lokacin dawowar affan ya kusa
Bayan ta dawo ko xaunawa batayi ba ta dauki maganin tasha har guda biyu sannan ta kwanta tana jiran taji ciki ya xube
Tayi awa daya da Shan maganin Amma shiru babu abunda ya faru har affan ya dawo cikin babu alamun xubewa
Shikam Affan daya sameta kwance ya dafa kanta yace injin ba Jikin bane ta kwabe mashi hannu affan yace wai lafiya daxu Naga kina fara a yanxu kuma Naga kin daure ko jiki ne?
Afra xatayi magana cikin tsiwa affan yasa bakinshi cikin nata yana tsotsa kamar ya samu sweet wani mugun haushi taji ya qara bata sai tafara hawaye affan ya lashe hawayen yana qara rungumeta a jikinshi afra tace nifa ka qyaleni affan yace babu abunda xanyi maki
Har dare afra tana xuba ido taga ciki ya xube Amma bai xube ba duk tabi ta tayar da hankalinta har affan yaso yagane akwai damuwa a tare da ita amma saiyayi tunanin mayb dan bai barta taje xamfara bane lokacin da xasu kwanta afra a qasa ta kwanta affan yayi yayi da ita ta hau gado amma taqi wai baxata kwana dashi ba yace to ki hau katifar ni xan kwanta a carfet afra tace ita baxata hau katifa ba dole ya qyaleta ta kwanta a carfet . Wajen qarfe biyun dare dayake lokacin damuna ne kuma afra tana tsananin tsoron tsawa gashi ruwan yau da tsawa akeyinsu duk ta takure tanajin tsoro saita tuna lokacin gida idan Ana ruwa maqale umma takeyi yau gashi ita kadai tana cikin tunanin ne taga walqiya ta haske dakin batasan lokacin da ta hau katifa ta rungume affan ba saiga tsawa anyi cikin tsoro ta qara rungumeshi tana fadin yaya tsoro nakeji affan ya qara rungume ta ya fara rabata da sleeping dres dinta ya sarrafa afra shi son ranshi sai asuba ya Barta
Da asuba tare sukayi wanka affan ya hada masu break a cewarshi kada ta wahar mashi da baby Dan haka da kanshi ya hada masu sai da suka qoshi sannan ya tafi class harda manna mata kiss a goshi
Bayan ya fita afra takira xulaihat a waya tace ita cikin har yanxu bai xube ba xulaihat tace ai dama ba lokaci guda xai xube ba tayi qoqari ta shanye maganin saita shanye xai xube, aiko suna gama waya afra ta qara dauko maganin ta qarasha .......










*ummu meenal*
[9/10, 7:37 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤








*STORY AND WRITING BY MRS SADEEQ*(Ummu meenal)




*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
G.W.F


*Home of gorgeous,intelligent and expert writer's, we the best among the rest*


Https://www.facebook.com/
Groupsgorgeouswritersforum/
1726580770789237/


*DEDICATED TO*
*Aysha Galadima*



*aunty maimuna ýar mutan kazay ina tayaki murnar kammala buk dinki mai suna 💞MEELAT💞 tamu*
*Allah ya qara daukaka da qwarin ido kai harma da xaqin hannu*



*short story*


*page 91-95*




Cikin afra yana wata hudu affan ya kammala gidanshi gidan yayi kyau sosai yanxu sai tarewa ranar laraba Dan haka kayan da xa sa gidan kamar su gado da kayan kitching affan yaba odar su a Dubai
Ita kuma umma tace sai anyi bikin tarewa walima kenan abba yace basai anyi komai ba su tafi Allah ya bada xaman lafiya Amma umma tace yakamata ayi abba yace to ayi biki lafiya
Kayan da affan ya siyo a Dubai kaya ne nagani na fada Dan gsky kayan sunyi kyau sosai baxaka gane kayansu ba saida akaje akayi danki jere sannan kayan suka qara haske gidan

Ana saura kwana uku tarewa saiga affan ya shigo gidan da kayan akwati set biyu ne dayan poupule ne sai dayan pink kala hamsin ne takalmi kala goma ne sai sauran tarkace kowa yana fadin kayan sunyi kyau
WASHE gari mutanen xamfara sukaxo sun yaba sosai da sukaga kayan afra saima dasukaje gidan afra da yake kinkinau ne sunga aljannar duniya sai dai kuma Muce Allah yabada xaman lafiya
Ana gobe bikin tarewa afra taje kaiwa affan abinci dakinshi affan yana ganin afra ya tuntsure da dariya afra cikin shagwaba ta tsaya qofar dakin tà turo qaramin bakinta tace
Me nayi maka kakemun dariya?
Affan yace kawai kin burgeni ne kinga yanda kika qara kyau kuma ga Dan cikin ki nan ya Dan fito cikin yayi maki kyau sosai
Afra ta harareshi tace. Babu wani ciki yayi mani kyau kawai kace kana dariya kajamun abun kunya munyi aure ban tare ba nasamu ciki ko
Affan ya qarayin dariya yace
Aa madam ki rufamun asiri ba haka nake nufi ba ya rufe bakinshi saboda wata dariya yakeson qarayi
Afra cikin fushi ta ďan duki faffadar qirjinshi tace Dan bakasan yanda yan xamfara da sukaxo suke mamakina ba wai ashe ciki gareni ta qarasa maganar kamar xatayi kuka
Affan yace to ai ba haramun bane ladama kike samu kuma nayi maki alqarin idan kin haihu xaki cigaba da karatunki a KASU kuma idan xa ayi jarabawa xakije kirubuta
Afra taji dadi sosai ta rungumeshi tana godiya
Ranar tarewa afra tasa wani swis les baqi yanada xanen fulawa ja dinkin ya matuqar ansar jikinta idan kaganta kamar kasaceta ka gudu. Gida kam ya cika da mutane sai kace yaune aka daura auren
Affan yasa wata dakakkiyar shadda ubansu affan ba baya ba wajen kyau da qwarjini Dan haka shima ya hadu sosai
Affan daya shigo gidan yaga afra sai yaga takoma mashi sabuwa yaji ya qara sonta har ya qosa dare yayi a kai mashi matarshi .

Da daddare misalin qarfe Tara na dare afra tana dakinta itada yan uwanta na xamfara umma tace akirata duk da afra affan ya koyar da ita komai na rayuwar aure Amma saida gabanta ya fadi saboda rabuwa da umma Amma bayanda xatayi ta tashi taje kiran da umma take mata jikinta babu qwari ta samu umma xaune kan kujera afra ta xauna gefenta tace umma gani
Umma ta dafa kan afra tace Allah ya maki albarka inason nafada maki wata magana
Afra ta sunkuyar da kanta qasa Dan har tafara hawaye
Umma taci gaba da cewa . Inaso kisani afra aure ibadane kiyiwa mijinki ladabi da biyayya ki girmama mijinki kuma kiyi haquri a cikin xaman aurenku.....ai tuni afra ta fashe da matsanancin kuka itama umma takasa cigaba da nasihar saboda kukan da yakeson xuwan mata sai shi abba ne yace akira affan.
Nasiha mai ratsa jiki abba yayima afra da affan ba afra ba har affan din jikinshi yayi sanyi Amma hakan bai hanashi murna ba.
Lokacin da abba yacewa affan ya dauki matarshi su tafi afra ta riqe umma tana kuka sosai da qyar aka banbare afra Jikin umma.
Afra tana kuka tashiga mota aliyu ne yake Jan motar afra da affan sune bayan motar basu tsaya ko ina ba sai qofar gidan affan
Har cikin gidan aliyu ya shiga da motar affan ya riqo hannun afra suka shiga cikin babban falon gidan







*kuyi haquri da wannan ba yawa saboda bana gida ban xauna sosai ba muna hidima ne*




*ummu meenal ce🖊*
[9/16, 6:18 PM] Aysha Galadima: *❤❤❤DANI DA MIJINA❤❤❤*

❤❤❤


*Short Story*


*STORY AND WRITING BY MRS SADEEQ*(Ummu meenal)




*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
G.W.F

*Home of gorgeous,intelligent and expert writer's we the best among the rest*


Https://www.facebook.com/
Groupsgorgeouswritersforum/
1726580770789237/


*WANNAN SHAFIN NAKUNE 'YAN KLASS OF TWENTY THIRTEEN GROUP💞, KUYI YANDA KUKAGA DAMA DASHI*


*DEDICATED TO*
*Aysha Galadima*


*page 96-100*

*END*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Sallah sukayi raka a biyu sukayi addu Dan samun xaman lafiya da yaqi da shaidan a xaman aurensu
Afra kanta yana kallon qasa saboda har yanxu kukan takeyi affan ya jawota jikinshi ya rungume yana lallashi saboda yasan halin afra idan ta fara kuka tana dadewa tanayi da haka har ya samu tayi shiru
Yau affan jin kanshi yakeyi kamar sabon ango sai nan nan yakeyi da afra ita kuma afra sai qara narkewa takeyi tana zuba shagwaba da haka harya fara rabata da kayan jikinta itama afra ta anshi saqonshi da kanta ta manna bakinta cikin nashi abunda bata taba yimashi ba lokacin da suna gida affan ya qara rudewa ya sakar mata komai na ragamar rayuwanshi dan shi ta kasheshi da dadi yasa hannayenshi akan dukiyar fulaninta yana murxasu son ranshi gashi kuma Sun qara girma da haka sukayi gado( ni dai babu ruwana da ganin qwaf saina fita naja masu qofar)

Washe gari afra ta tashi qarfe bakwai tayi komai na aikin gida ta hada masu breakfast ta aje a dinning ta jona booner gidan ya dau qamshi ga sanyin Ac afra taje ta samu affan tashin shi kenan daga barci yana kan gado bai ma sauka ba tana tafiya tana rangwaďa shi kuma ya bita da kallo harta Iso gabanshi kan jikinshi ta xauna tace
Muje kayi wanka ko yaya
Affan ya harareta yace nifa yanxu yakamata kicanxa mun suna
Afra ta harareshi da wasa tace to mexance
Yace kixabi sunan da yadace dani kuma mai dadi yana maganar yana kashe mata ido
Afra ta qara shigewa jikinshi tace idan nace hubby na yayi ?
Affan ya rungumeta yana cewa yes yayi na gode my heart.
Da taimakon afra affan yayi wanka ita ta goge mashi ruwan jikinshi ta towel
A dinning afra tayi serving dinsu affan yanaci yana santi sannan ta xuba mashi haddaden kunun gyada yanasha yana samata albarka

*bayan wata biyar*
Cikin afra ya shiga wata Tara affan sai nan nan yakeyi da ita cikin ba qaramin girma yayi ba ita ko umma cewa tayi yakama a dawo da afra gida Amma affan ya hana yace Ayita addu a Allah ya raba lafiya. A lokacin afra har taxana jam
Ranar Monday cikin dare afra ta tashi da ciyon Mara sosai hankalin affan ya tashi sosai yayi saurin kiran umma dan ya fada mata umma tana ganin kiran waya cikin dare gabanta ya fadi ta dauka affan yace umma afra ce ba lafiya yanxu xamu tafi asibiti umma tace kayi sauri kutafi nima ganinan xuwa
Da qyar afra take tafiya saboda ciyon da maranta yake mata har ta shiga mota affan ya shiga shima yaja mota da gudu sai asibiti
Basu bata lokaci ba aka shiga da ita Labour room
Affan kam ya rude sosai Dan lokacin da umma ta Iso taga damuwa sosai sai itace take bashi haqur akan insha Allah xata sauka lafiya affan yace wlh umma tausayi take bani ta wahala sosai
Umma tace kai dai kayi mata addu a insha Allah xata sauka lafiya affan yace Allah yasa
Qarfe biyar na asuba afra ta haifi santalelen yaronta mai kama da affan komai nasu iri daya fari kawai babyn yafi affan
Lokacin da nurse take fadawa affan cewa afra ta haihu lafiya saida yayi Sujjada saboda farin ciki Dan har nurse din saida yabata kyauta
Murna kam ai baxata fadu ba gun affan da umma. Dan lokacin da ya shiga dakin Hutu ya dauki jaririn ya rungume yanajin sonshi har cikin ranshi sannan yayi mashi huduba da sunan mahaifinshi umar

Bayan an sallamesu gidan umma suka wuce kowa yanata murna kuma duk Wanda yaga babyn sai yace yana kama da affan
Bayan kwana uku da haihuwa affan ya shigo da akwati seat yawanci kayan baby ne Dana mamanshi kowa yanasa albarcin bakinshi
Ranar suna sa da raguna biyu affan ya yanka mutanen xamfara kam sunyi murna sosai kuma anyi shagali sosai
Washe garin suna afra tana kwance da babynta wanda suke kira *ARYAN* Sai kuka yakeyi affan ya shigo dakin ya samu afra tana kwance tasa atamfa super ruwan ganye green sai aryan dayake gefenta yana kuka affan yayi saurin daukanshi yace haba my heart bakijinshi yana kuka?
Afra tace wlh yaron nan ya cika tsotsa yanxu yagama Shan nono kuma wai yanxu nema yakeyi
Affan yace my heart kitaimaka kibashi yasha so yake yafiki girma
Afra cikin shagwaba tace ni dai gsky sai anjima xan bashi
Affan yaxo daf da afra yasa hannunshi cikin rigarta ya dauko Aryan ya ciro nonon ya sawa Aryan nonon a baki sannan yace banason kibarmun yarona da yunwa Dan haka ki kiyaye
Shi kuma Aryan yasamu abunda yakeso sai tsotsa yake sosai da yake yaron akwai wayo kuma yanada girman jiki Dan lokacin da sukayi arba in saika rantse Dan wata uku ne

Bayan arba in affan yacewa afra yakamata taje xamfara dama yayi mata alqawarin saita haihu Dan haka da kanshi ya kaita afra murna take xataje gida dan lokacin da affan yayi parking din mota da gudu ta shiga gidan dama ansan da xuwanta gida ya ruďe da murna sannan aka kaisu dakin Hutu aka kai musu abinci a can
Saida suka kammala cin abinci sannan affan yace shi xai tafi jibi xaixo ya dauketa
Afra tace haba hubby na yaushe rabon da inxo kuma kace kwana biyu xanyi ni wata daya xanyi
Affan yace xakisa yanxu injuya dake idan kikace kiyi wata
Da qyar affan ya bari afra tayi sati daya
Yan uwa da dadi afra ta shiga cikin Dangi inda ta dade bataje ba kowa sai murna yakeyi kuma tunda ta tafi ake bata kayan mata anyi mata kaxar amare tasha tsimi da gumba harta gaji
Bayan sati daya saiga affan da sassafe yaxo daukar afra sai kace Wanda ya kwana a hanya dama ta shirya kayanta Dana Aryan basu bata lokaci ba suka juya sai kaduna
A hanya affan yake cewa afra shifa ya gaji da xamanta gidan umma gidanshi xai wuce da ita
Afra ta marairaice Dan tasan halin affan ba qaramin aikinshi bane ya wuce da ita gidanshi tace Dan Allah hubby na kayi haquri kar ace munyi rashin kunya
Affan yace gsky na gaji da kwana ni kadai
Afra kamar xatayi kuka tace ni dai wlh kunya nakeji ina gidan umma ina wankan jego kuma kace xaka kaini gidanka
Affan yace ai kingama jego tunda kinyi arba in
Da qyar afra ta lallashi affan akan ya haqura ya kaita gidan umma tunda ta kusa komawa ita kanta tayi kewar mijinta sannan ya haqura ya kaita gidan umma
Bayan Sun dawo da kwana biyu umma kamar tasani tace affan ya dauki matarshi ya tafi da ita gida dama affan jira yakeyi dan haka bai bata lokaci ba ya dauketa da kayansu ya Maida gidanshi
A daren saida affan ya kusa sumewa Dan dadi yanata sa mata albarka washe gari ya biya masu aikin hajji afra tayi murna sosai tace nikam nayi sa ar miji Allah yabarmu tare Allah ya qara daukaka shima yana murmushin jin dadi yace amin sannan suka qara fadawa duniyar ma aurata

*BAYAN SHEKARA BIYAR*
Afra ta xama babbar mace Dan yanxu tana karatu a *KASU*
yanxu yaranta uku Aryan sai amina taci sunan mahaifiyar afra suna kiranta *MEENAL* ta uku taci sunan mahaifiyar affan suna kiranta *HANAN* yanxu duniya tayi masu dadi basuda damuwa suna xaune lafiya kowa bayason bacin ran kowa...........


*ALHAMDULILLAH*
*Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa ina roqon Allah kura kuren dayake cikinshi Allah ya yafe mun*

*Sai kun sake jina a sabon littafi na mai suna *BANSAN ITA BACE*




*Taku ummu Meenal*🖊

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book

Please Login or Register in order to submit comment