Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi al'wala kana yayi niyar salla ya fara biyan sallolin da bai samu yayiba.
Shi kuwa Ya Adnan fita yayi ya tambayi inda zai samu abinda zai saya musu suci.
Wani k'aton Restaurant dake cikin asibitin wanda ana yin kalan abincin ko wanne k'asa,
Snacks and drinks ya samo musu sannan ya koma ya tallafawa Saifuddeen ya d'anci sannan shima yaci kana ya koma gefe ya konta bisa kujerun silver dake wurin.


Su Ahmad kuwa suna shiga taxi d'in suka cewa drivern ya kaisu hotel mafi kusa da asibitin,
to yace musu kana ya ja motar suka fita daga harabar adibitin tafiya kad'an sukayi sukaga ya ratsa cikin wani tamfatsetsen hotel mai azabar kyau da tsari na zamani,
suna fitowa Ahmad ya zubawa sunan hotel d'in idanu.
Hyatt regency Delhi, ido ya zubawa benayen da sukasha k'awanya da abubawan alatu na duniya,
da sauri Ahmad ya koma cikin motar kana ya kalli Driver tare da cemishi.
da ganin wannan hotel d'in zaiyi tsada, to in dai da akwai wani k'arami a nan kusa ya ka kaisu.
kai driver ya jujjuya mishi tare da mishi bayanin cewa babu wani hotel nan kusa in banda wannan sai wani dake gabanshi kad'an kuma duk tsadarsu d'aya,
ya k'ara da ce musu gwara kuma su kama wannan d'in zasu huta da biyan kud'in texi na zirga-zirgan zuwansu da dawowa,
ya shaida musu ko an bashi gado baza'a barsu su zauna dashi ba, dan akwai masu kula dasu.
jin haka yasa dole suka fito,
Direct reception d'in hotel d'in suka nufa,
suna zuwa Ahmad ya k'arb'a musu d'aki d'aya tare da biyan kud'in sati biyu duk da yawan kud'in ya bashi tsoro to amman ya zaiyi.

Key aka basu bayan an rubuta sunayensu da time and date na zuwansu cikin littafin ajiyan shige da ficen mutane.

Hayatuddeen ne ya ciccibi 'yar ma dai-dai ciyar jakarsu,
sannan yabi bayan Ahmad da d'aya daka cikin workers nasu da zai nuna musu d'akin da yake can saman bene na hud'u kasan cewar lifta ne cikin k'ank'anin lokaci suka isa,
suna isa ya bud'e musu k'ofar tare da juyawa ya fita,
suna shiga,
Hayatuddeen ya ajiye jakar hannunshi tare da zuwa gaban TV,
kunna tibin yayi sannan ya dawo ya zauna bisa lumtsuma-lumtsuman kujerun da sukayiwa parlour k'awanya,
ido ya lumshe sannan ya bud'esu yabi bayan Ahmad da kallo,
shi ko Ahmad bedroom ya wuce kai tsaye cikin bathroom ya nufa,
wonka yayi mai rai da lfy sannan yayi al'wala kana ya d'aura towel d'in daya samu a ninke sabo dal cikin ledsnshi ys farkeshi, komai na wurin sabo.
yana fitowa ya koma parlour ya d'auko jakar kayan nasu yazo ya dawo bedroom d'in k'ananan kaya ya saka fitowa yayi ya koma parlour gefen Hayatuddeen ya zauna tare da cewa.
"Je kayi wonka kazo muje mu samu abinda zamu ci,
mu kuma sayi sim card na k'asar tasu."
da sauran Hayatuddeen ya mik'e tare da cewa.
"To." shi kuwa Ahmad ido ya zuba mishi ganin yadda yake cilla kayanshi tsakiyar parlour,
baki ya bud'e ganin ya tsallake wondenshi a inda ya cireshi,
kuma ko a jikinshi ya nufi bedroom,
kai tsaye bathroom ya shiga bayan yayi wonka yayi al'wala sannan ya fito,
gaba d'aya kayan cikin jakar saida ya fiddasu ya zubesu bisa gado sannan ya saka wani wondo 3 quarter pink color sai rigarshi mai yankekken hannu white Color,
sosai kayan sukayi mishi kyau.

Shi kuwa Ahmad a fili yace.
"Wato haka Raliya ke fama da rigimar Autan Ummi."
dai-dai lokacin kuma ya fito tare da cewa.
"Na fito ya Ahmad muyi sallan muje muci abinci yunwa nakeyi."
cikin had'e fuska Ahmad yace.
"To wa zai tattara maka kayan daka watsar d'in?."
kai ya d'an longob'ar tare da cewa.
"Ni ban iya tattarewa ba ya Ahmad."
tsaki Ahmad yaja tare da cewa.
"Zaka ma koya ai, dan nima ban iyaba."
sai ya kuma fuskanci al'k'ibila ya tada kabbara ganin haka shima Hayatuddeen yabi bayanshi,
bayan sun idar da sallolin nasu ne suka sauk'a reception sukayi tambayar ta ina Restaurant yake nan aka kwatanta musu sannan,
suka nufi wurin suna isa sashin. Restaurant Ι—in.
Mathuramakrishna viswanathun.
Hayatuddeen ya isa gaban teburin da yaga an rubuta Africa food, gefe d'aya ya juya inda yaga ansa Nigerians food is ready,
sai kuma ya juyo jin Ahmad yana ce mishi,
"Ni ka amso min feesh roll,."
to yace sannan ya saya musu duk abinda suke buk'ata sannan suka juyo,
suna dawowa reception d'in suka gayawa ma'aikatan wurin cewa suna son sayan SIM card,
kud'in sukace su kawo zasu sayar musu dan suma suna saidawa,
nan suka basu kud'in layukan da kuma kati sannan suka musu register tare da karb'an woyoyin suka saka musu layukan sannan suka saka musu katin,
ganin tuni lokaci d'aya layin ya hau yasa suka haura d'akinsu.

Suna isa suka zauna a parlour sukaci suka sha,
ganin ko kad'an Hayatuddeen bai damu da kanshi dake watseba yasa Ahmad mik'ewa ya tattarusu ya shiga bedroom dasu,
nan kuma yayi arba da kayansu daya wancakalar
hannunshi d'aya yasa ya tokare k'ugunshi kana yasa d'aya ya dafe goshinsa tare da cewa.
"Wayyo ni Ahmad jikan Ahmad naga ta kaina da aka had'ani da wannan sangartaccen Ummin."
dole ya kimtsa komai.

Shi kuwa Hayatuddeen a parlour ana ya konta tuni bacci ya fara d'ibanshi.
Ahmad da ya gama tattara abinda ya watsanne ya dawo parlour ya tada Hayatuddeen tare da cewa.
"Ka tashi mu koma asibitin mana."
cikin gengyad'i yace.
"Ya Ahmad dare yayi sosai fa ka bari da asuba muje."
da wannan shawarar ya koma bedroom ya konta.
Dan akwai gajiyar tafiya tare dasu.

Washe gari suna idar da sallan asuba,
suka fito suka kama hanyar da zata sadasu da asibitin,
tafiya kad'an suka shiga cikin asibitin.

Daga bakin harabar wurin,
suka fara tambaya da tambayar suka samu suka isa har office d'in Dr Acash prasat dan dashi suke tambaya,
suna shiga cikin wurin suka hango Adnan zaune bakin mashigar inda suka kwana,
da sauri suka iso gunshi,
Ahmad ne ya fara bashi hannu,
bayan sun gaisa ne,
yace musu ana mishi wonka ne,
jin haka yasa Ahmad ya bashi SIM card d'in da suka saya mishi da key d'in d'akinsu ya kwatanta mishi yace.
"Kaje kayi wonka ka samu ka canza kaya ka kuma d'an ci abinci kafin ka dawo, wata k'il Dr yazo."
haka kuwa akayi ya amsa ya tafi,
su kuma suka zauna koda aka gama kimtsashi.
Hayatuddeen ne yaje ya samo mishi abinda zaici,
daga nan sukayi ta hira dashi har zuwa lokacin da Ya Adnan ya dawo,
nan sukayi ta zaman jira sai bayan azahar Dr Acash yazo,
haka sukayi ta bin layin ranar amman ina ranar basu samu damar ganinshi ba,

the next day ma haka sukayi ta bin layi, har kusa k'arfe biyar na yammansu sannan suka samu damar shiga.

Suna shigar da Saifuddeen Dr Adnan yabi bayansu,
d'aya daga cikin nurses da suka shigar da Saifuddeen d'inne ya nunawa Dr Adnan wurin zama,
bisa wasu kujeru guda biyu dake gaban wani babban table,
wanda d'aya sashin shi kuma kujera d'aya ce,
wacce Doctor Acash prasat ke zaune,
kekyawan ba indiye ne,
fayel d'in da Saifuddeen da nurse ta bashi ne ya fara bubbud'ewa yana duddubawa,
yayinda Dr Adnan kuwa ya zauna gabanshi,
sauran nurses d'in kuwa suke ta kiciniyar kontar da Saifuddeen bisa wani d'an gado dake gefen doctor.

Suna gamawa suka koma gefe suka zauna,

Da sauri Dr Adnan ya d'ago kanshi cikin mmki yake kallon Dr Acash da yake mishi mgna cikin yaren hausa.
"Tun shekaran jiya Dr Aliyu yace min kun iso,
kuyi hak'uri abin ne da yawa."
cikin nitsuwa Dr Adnan yace.
"Ba matsala, d'azu mukayi mgna da Dr Aliyu ma."
juyawa yayi ya kalli Saifuddeen dake konce a rigingine,
sai ya kuma meda dubanshi ga fayel d'in,
kana ya bud'e poldernsu ya fara 'yan wasu rubuce-rubuce kusan tsawon 4 minutes sai ya kuma ture takardun sannan ya jawo system dake gabanshi still rubuce-rubucen yayi, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Dr Adnan cikin bagwariyar hausarsa da zamanshi da Dr Aliyu ne yasa ya iya yace.
"Forko dai yanzu za'ayi mishi gwajin, X-ray CT scan MRI scanning wanda ko wanne d'aya N95,000. ne
sai kuma Surgery da ya kamata ayishi kan lokaci d'an yanzuma lokaci ya d'an fara ja,."
cikin gamsuwa da bayaninshi Dr Adnan yace.
"Surgery d'in kuwa zai kai nawane?."
kai ya d'an rusunar sannan ya d'anyi dube-dube a system d'in sannan ya d'ago kanshi ya kalleshi kana yace.
"N2.5 million."
A hankali Dr Adnan yace.
"Ba matsala a fara aiki."
mik'ewa yayi ya nufi gaban gadon da Saifuddeen yake a hankali yasa hannunshi ya fara jan 'yan yatsun Saifuddeen amman shiru bai kulaba a hankali ya fara bin k'afafunshi yana d'an lallatsawa still Saifuddeen baya ji bare ya bud'e idonshi,
sai yaci gaba da tattab'ashi tare da juyawa ya kalli Dr Adnan dake tsaye bayanshi cikin kula yace.
"Naga kurmane shi ko?."
kai ya gyad'a mishi da sauri,
cikin meda hankalin shi kan Saifuddeen yace.
"In ba matsala in kunada hali musa doctor kunne a cikin aikinshi mana."
jim kad'an Dr Adnan yayi kana ya d'an matso doctor Acash d'in tare da cewa.
"Dr kanaga zai worke ne?."
da sauri ya jujjuya mishi kai tare da cewa.
"Wannan ai sai Doctord Ι—in kunnen ne zasu bamu amsar nan in sun dubashi,
sai dai muna zaton zai worke tunda ba haifarshi akayi da kuramtarba ko?."
da sauri Dr Adnan ya gyad'a mishi kai tare da mishi d'an k'arin bayanin yadda ya samu larurar kuramta,
kamar yadda yayiwa Dr Aliyu a Abuja.
dawowa sukayi suka zauna bisa kujerun da suka tashi nan suka fara musanyan basira da shawara a matsayinsu na Doctors,
sosai Doctor Adnan ya k'ara samun haske a lamarin sashin aikinshi dan zama da kwararran Dr da yayi na awa biyu.
da yawa suna kwarafin cewa shi Dr Acash in an aka shigar da mutun ba'a fitowa da wuri,
shi kuwa k'a'idar aikinshi ne ya binciki marasa lfy da kyau a nitse ya kuma samu cikikken bayani daga bakin mara lfyar ko iyayenshi.
Shiyasa yake dad'ewa da mutane,
shiyasa kuma mutane ke son ya dubasu,
anan take ya kira wani doctor da yake kula da sashin kunne.
Ba jimawa ya shigo nan sukayi 'yan dube-dubensu,
daga bisani nan take aka fara aikin gudanar da gwoje-gwajensu.
Saida suka gama duba komai sannan aka fitar dasu,
aka kaisu room d'in da za'a kwantar dashi zuwa gobe in sun duba sakamakon awun nasu.
nan ya bawa Dr Adnan number shi cewa gobe in sunzo ya shaida mishi.

D'akin babba ne mai kyau gadaje biyu ne a cikin d'akin sai kujeru guda biyu ko wanne gado da kujera d'aya,
bayan sun gama komai nan suka zauna su dukan su uku Hayatuddeen yana gefen Saifuddeen,
Ahmad kuwa yana tsaye gaban Dr Adnan da yake musu bayanin yadda sukayi da Dr da kuma gwoje-gwojen da akayi da kud'ad'ensu.
ganin lokacin salla yayi ne sukayi al'wala sannan suka tafi masallaci, sukayi salla magrib nan suka d'an jira lokacin isha yayi, hankalin konce sukayi salla dan sun san akwai masu kula da Saifuddeen.

Bayan sun idar sun koma ne suka sameshi kwance amman an d'an d'aga kan gadon in ka ganshi zakace a zaune yake irin ya d'an jinginane,
da sauri Hayatuddeen ya zauna gefenshi tare da cewa.
"Sannu Hamma Saifuddeen ya jiki?."
kanshi ya jinjina alamun da sauk'i sannan ya kuma mishi mgna cikin body language yake tambayarshi ya labarin Ummi.
da sauri Ahmad yace.
"Ummi tana lfy tace a gaidaka."
murmushi yayi cikin jin dad'i sannan ya kalli Hayatuddeen dake cewa.
"Bari in kira Raliya video call sai ku gaisa da Ummin."
matsowa yayi kusa dashi ya zauna gab dashi kana ya kira Raliya sannan ya kaikace woyar tashi ya matso da kanshi jikin Hamman nashi duk suka fuskanci wayar.

A can gida Nigeria kuwa dai-dai lokacin Raliya na zaune gaban Ummi da take ce mata.
"Tunda sukaje basu samu damar ganin Dr bama, ni gaba d'aya hankalin na a tashe yake."
da sauri Raliya tace.
"Yauwa Ummi dama abinda ya kawoni kenan fa yanzu mukayi mgna da Ya Ahmad yace min yau sun samu ganin Dr kuma Alhamdulillahi duk gwajin da ake buk'ata anyi, zuwa gobe sakamakon zai fito."
ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi."
sai kuma tayi shiru jin Raliya na cewa yauwa gama Auta na kirana."
da sauri tace amsa kiran."
Da sauri tayi picking call d'in murmushi tayi ganin fuskar yan uwanta duk suma suna mata murmushi da sauri ta yunk'ura ta dawo gefen Ummi ta saita fuskarsu da fuskare wayar,
suna kallon junansu,
wani irin faffad'an murmushi Ummi tayi ganin fuskokin yaranta cikin happy tace.
"Alhamdulillahi babana ya jikin?."
kai ya d'an rausayar tare da yin yalwataccen murmushi,
Hayatuddeen kuwa cikin tankwara wuya yace.
"To wai ni kam bakuyi missing na bako kallifa Ummi ko ki kulani ninefa autanki."
dariya tayi har saida wushiryanta ya baiyana sannan tace.
"Nayi kewarka mana autana."
da sauri Raliya tace.
"Ni dai banyi kewarka ba dad'i ma nakeji na huta da tattaren kayanka yanzu gidanmu baya hargitsewa tunda ka tafi."
dariya yayi sosai sannan yace.
"Wayyo yarinya ai in ke kin huta mijinki bai hutaba yaseen watsar da komai nakeyi son raina Ya Ahmad ke tattaremin,
Yau da safe harda boxer na ya wonke min da zai wonke nashi."
da sauri yayi shiru tare dasa hannu yana shafa k'eyarshi da Ahmad ya bugi yana mai cewa.
"Wato kama maidamu bayinka nida matata."
cikin jin dad'i Raliya tace.
"Yauwa ya Ahmad buge minshi da kyau, kuma ka dena tattare mishi komatsanshi."
Saifuddeen kuwa hannu yasa ya jawo kan Hayatuddeen ya manna da kafad'arshi sannan yasa tafin hannunshi yana shafa mishi inda Ahmad ya d'an buge mishi.
murmushi yayi tare da cewa.
"Kada ya tattara mana ba sai muyi ta zama cikin dottiba."
cikin jin dad'i Ummi tace.
"Kai Autana ka fara girma fa ka rink'a womke guntayem wondunanka da kanka kaji ko?."
kai ya gyad'a mata sannan ya mik'awa Dr Adnan wayar cikin kauda kanshi yace.
"Barka da dare Ummi ya gida."
sunkuyar da kanta tayi cikin kunya irin ta surkai tace.
"Lfy lau Baban Adam ya mai jikin?."
A mutunce yace.
"Alhamdulillahi Ummi jiki da sauk'i yau mun samu munga likita,
nanda kwana biyu za'ayi aiki, ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai samu lfy."
cikin samun nitsuwa tace.
"Allah yasa."
Amin Amin sukace baki d'aya sai kuma tace.
"To ni kuma sai yaushe zan zo in dubashi?."
Da sauri Ahmad ya koma gefen Adnan d'in kana yace.
"Ummi ki kwantar da hankalin ki bari in an mishi aikin munga yanayin jikin sai kizo."
shiru tayi kamar dai bata gamsuba sai kuma Dr Adnan yace.
"Ki bari sai anyi aikin, dan nima in anyi aikin zan dawo,
in yaso in na dawo sai ki zo ko?."
a hankali tace.
"To ba matsala Allah ya bada sa'an aiki."
Amin Amin yace sannan ya kalli Raliya tare da cewa.
"Ina Faruq?." a hankali tace.
"Yana d'aki wurin Goggo Dada wai sai ta mishi tatsuniya daga nan duk sukayi bacci."
"Ki gaida min shi, gobe asabar yaje gida mana yayi hutun sati a wurin Mamanshi."
cikin nitsuwa tace.
"To ba matsala, ka gaida Hamma da jiki mun gode Allah ya saka ya bar zumunci."
Amin Amin yace sannan suka sallami juna.

Sosai Ummi ta samu nitsuwa da sukayi hirar.

Su kuwa suna gama woyar Ahmad ya gyarawa Saifuddeen konciyarshi,
dan ganin ya fara lumshe ido,
a hankali Ahmad ya kalli Dr Adnan tare da cewa.
"Ya Adnan kuje masauk'inmu kaida Hayatuddeen ku kwana bari ni in kwana dashi, kaje ka samu ka huta."
kasan cewar akwai gajiya a jikinshi yasa ya amince,
tare suka tafi shida Hayatuddeen shi kuwa Ahmad ya kwana nan wurin Saifuddeen.

D'aya gadon ya hau ya kwanta yana kwanciya Bappa Ali na kiranshi wanda shi kuma kawunshi ne yayan mahaifiyarshi da sauri ya amsa kiran.
"Salamu alaikum."

"Wa alaikassalam."

"Ina wuni Kawu Ali."

"Lfy lau Alhamdulillahi Ahmad ya jikin Saifuddeen?."

"Jiki da sauk'i Kawu yau mun samu munga Doctor."

"Eh haka dai Mudassir ke sanar min yanzu wai sunyi waya da Yayanshi Adnan."

gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"Na kira d'azu ai zan sanar maka to kuma sai naji layin naka baya tafiya."

"Eh lallai na rufe wayar ne, na tafi harami shiyasa."
Cikin nitsuwa yace.
"Kawu Ali sai yaushe ne dawowarku?."
"Saura mako guda, kuma in sha Allah ni daga nan saudia zan taho india".

"To Allah ya kaimu lokacin ya dawo daku lfy.
Kawu Ali a tayamu da Addu'a fa."
"In sha Allah, Ahmad zamuyi ta addu'a."

Daga nan sukayi sallama,
juyowar da zaiyi sai yaga Saifuddeen na rik'e da wayarshi,
a hankali ya tashi zaune kana ya mik'e ya taho gaban gadon,
lek'a fuskarshi wayar tashi yayi,
ido ya lumshe ganin karatun Qur'an yakeyi,
sai ya koma konta.

Shi kuwa Saifuddeen tunda Ahmad ya gyara mishi kinciyarshi,
ya lumshe ido ya fara bacci sai kuma ya fara mafarki inda yake ganin Zaleeha
tanata k'ok'arin son ganin fuskarshi daya rufe da tafin hannunshi,
shima kanshi ta tsakanin yatsunshi yake gane fuskarta,
ita kuwa sai tasa hannunta tana ta son ciro hannunshi daga fuskarshin amman ta kasa d'age hannun nashi,
ganin haka sai ta koma gefe ta zauna tanata kuka,
daga nan ya farka daga baccin.
To shiyasa kawai ya d'auki wayarshi ya fara karatu.

Shi kuwa Ahmad Warisu ya kira suka gaisa sannan sukayi saida safe.

Ya Adnan da Hayatuddeen kuwa da k'afa sukayi tattaki har cikin Hyatt kasan cewar ba nisa da asibitin.

Suna isa Ya Adnan yayi wonka,
yana fitowa Hayatudden ya mik'e ya shiga,
bayan sun gama shirin baccinsu ne,
Ya Adnan ya koma parlour ganin Hayatuddeen baiyi bacci ba, yanata charting da abokanshi da yawanci jikin Hammanshi suke tambaya.
Dan haka ya koma parlour dan yana son zaiyi waya da matarsa ya d'an kontar mata hankalin.
Sosai ya kontar mata da hankalin, sannan yayi bacci.

Washe gari bayan sun karya suka sayawa su Ahmad abinda zasuci sannan suka nufi asibitin.
Suna isa doctor na isowa, a tare suka d'anci abincin.
Tuni Dr Adnan kuwa ya kira Dr Acash prasat ya shaida musu suna kusa.

Suna gama woyar ya hangi Divia ta amsa kira sai kuma yaga ta nufi inda yake tare da ce mishi su shiga,
yana shiga suka tattauna da doctorn,
suna gamawa ya fita.

Yana dawowa wurinsu Ahmad yace.
"Har ka fito?."
"Eh na fito ya nuna min sakamakon gwajin da akayi ne,
ya kuma cemin gobe ne zasuyi aiki."

"To Allah ya kaimu." Ahmad ya fad'i yana gyara wuyan rigarshi,
Hayatuddeen kuwa Amin Amin yace tare da ajiye wayarshi kusa da kan Saifuddeen.

Washe gari kuwa k'arfe tara dai-dai na k'asar tasu.
Aka gama shirya Saifuddeen cikin shigar da akewa wad'anda za'ayiwa aiki,
tuni suma Doctors an gama shirya musu komai kayan aiki.

K'arfe goma dai-dai nurses suka shigo suka tura gadon Saifuddeen suka nufi wani corridor mai fad'i, a hankali Hayatuddeen ya bisu da ido da alamun karaya a idanunshi,
ganin haka yasa Ahmad ya jawoshi suka zauna kana ya d'an kontar mishi da hankalin.
Ganin ya d'an nitsune ya kira Ummi yace mishi tofa an shiga aiki ta tayasu da addu'a yana katsewa ya kira bappa Ali ya gaya mishi hakama su Salisu da Warisu duk ya gaya musu.

Shi kuwa Dr Adnan yana tare dasu Dr Acash dan shi a wurinshi kamar samun k'arin ilimi ne ace a gabanshi akayi aikin.

Suna isa d'akin da za'ayi aikin Saifuddeen yayi murmushi ganin Ya Adnan da irin shigar doctors d'insu,
shima Dr Adnan murmushi yayi dan yana jin k'arfin guiwa da karsashi daga ganin lafiyayyun kayayyakin aikinsu,
bugu da k'ari ga Dr Malik Khan shima dashi za'ayi aikin dashi.

Allurar bacci ko ince cire haiyaci sukayiwa Saifuddeen,
bayan sunga yayi lib alamun alluran sunyi aikinsu.

Nanfa suka fara aikinsu baji ba gani,
shiru kakeji ba magana ko tari basayi sai sautin AC da kuma d'an sautin injuna da d'an k'aran ajiye ababen aiki da sukeyi.

Surgery ba sauk'i kusan tsawon awa hud'u sukayi a kanshi,
sannan suka kammala komai,
canza mishi kayan jikinshi sukayi sannan suka canza mushi gado, kana aka turoshi tamkar gawa aka fito dashi,
ta gabansu Ahmad akazo aka wuce dashi,
mik'ewa sukayi suka fita daga wurin baki d'aya,
yayinda tuni su Ahmad suna biye dasu a d'aya,

Wani side dake can gefe suka shiga,
suna shiga wurin suka shiga wani babban parlour dake cike da kekunana da kuma d'an ma dai-daicin pharmacy kuma ga ma'aikata a cike da wurin.
Suna shaga wasu suka taso suka karb'eshi a hannun wad'an nan d'in,
wani d'aki suka shiga dashi dashi,
kuma basu hana su Ahmad shigaba sai dai suna shiga sukaga sun zuge wani k'ofa na glass sun shiga cikin d'an keb'an taccen wurin dake cike da,
na'urori.
Kontar dashi sukayi bisa gadon dake ciki sannan suka k'ara gudun AC tare da gyara mishi konciyarshi,
suna mgna amman su Ahmad bazasu jisuba.
suna gama kimtsashi sukayi d'aura mishi ruwa tare dasa ruwan allurai a ciki,
daga nan suka fito suka zo inda su Ahmad suke,
a nitse suka d'an musu bayanin cewar kada su yawaita hayaniya, kada kuma suce zasu shiga inda yake shida farkawa sai gobe iwar haka,
kada kuma su damu, su zauna na.
kai kawai suka gyad'a cikin gamsuwa da nitsuwa,
kana suka zauna a kujerun dake jere a wurin,
gaba d'aya Hayatuddeen ya kasa nitsuwa sai hawaye yaketa zubdawa da kyar dai Ahmad ke tausasa mishi zuciya.

A can kuwa ana fitar da Saifuddeen aka shigo da wani bature,
shima awa hud'u sukayi suna aiki a kanshi daga nan kuma,
suka firfito sai kuma gobe kasan cewar mutun biyu sukewa aiki kullum.

Suna fitowa Dr Malik da Dr Acash suka nufi can inda aka kontar da Saifuddeen
yayinda Dr Adnan ya bisu a baya,
suna shiga suka k'ara duddubasu da kyau sannan suka fito,
Nan Dr Acash ya kalli Dr Adnan cikin hausa yace.
"Kuje masauk'inku kada ku damu akwai masu kula dashi.
Dan koda kunza baza'a barku ku ganshiba ma'aikatanmu ne zasuyi mishi komai,
sai bayan sati d'aya zaku ganshi."

"To ba matsala Dr."
cewar Adnan kenan,
dole tasa suka koma masauk'insu.

Sai dai kullum zasu zo safe da yamma su ganshi ta cikin glass d'in.

Sosai ma'aikatan wurin suke kula da majinyatansu cikin iyawa da sanin makamar aikinsu,
tunda sun san irin mahaukatan kud'ad'en da suk'e karb'a a hannun 'yan uwan marasa lfy."

Yau kwana uku da yiwa Saifuddeen aiki Dr Acash ya nemi Dr Adnan ya bashi takardar daya rubuta wasu sabbin magunguna kala uku wanda zai shashu tsawon sati Ι—aya rak.
Yana fita ya wuce pharmacy koda yaje ya basu takardar suka gaya mishi kud'in maganin kai ya kad'a dan daya lissafa da kud'in Nigeria dubu d'ari huΙ—u da sattin da biyar ne harda d'ari uku.

Bayan ya saya ne ya bawa masu kula da shi d'in.
Ba b'ata lokaci suka fara bashi mgnin.

Tun randa aka fara bashi magungunan ya fara jin sauk'in nauyin da jikinshi ke mishi.

Randa aka cika sati da mishi aiki kuwa a ranar jirginsu bappa Ali ya iso India daga k'asar saudia.
kasan cewar da asuba suka iso,
kai tsaye masauk'insu Ahmad ya nufa,
saida sukayi breakfast sannan suka nufi asibitin.


Suna shiga Dr Adnan ya kira Dr Acash ya nema musu izinin shiga wurin Saifuddeen,
jin haka yace su jirashi yazo.

Bayan awa biyu ya iso kana shida kanshi ya musu jagora har cikin d'an d'akin glass d'in nan.

Suna shiga duk sukayi...!




By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 21*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



_09097853276 ta nan zaku turo katin mtn na300 kacal, ko kuma ku turo ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan no 09097853276_

~Hmmm Daga gobene free page ya Ζ™are kun cinye alakoronku~


Sukayi saurin k'arasawa gaban gadon da Saifuddeen ke kwance,
gaba d'aya fuskokinsu k'unshe da murmushi ganin yana musu murmushin.
Bappa Ali kuwa hannunshi yasa bisa kanshi yana shafawa tare da fara jero mishi tambayoyi cikin kula yake cewa.
"Saifuddeen ya jikin? Da sauk'i ko? ina ke maka ciwo?."
ido ya lumshe mishi alamun da sauk'i,
Ahmad da Hayatuddeen kuwa ido suka zura mishi ganin gaba d'aya ya rame

Please Login or Register in order to submit comment