Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin zazzaɓi da ciwon kai da suka kawo mata cabka lokaci guda.
Agaban tankamemen gate ɗin gidansu dake cikin New G.R.A ta tsaya da motartata tare da danna wani ɗan siririn horn, Malam Kalla me gadi ne ya wangale mata gate ɗin, yayinda ta tura hancin motar tata cikin gidan, ko parking mai kyau yau batayi ba haka ta fito daga cikin motar, kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, don acanne kaɗai take da yaƙinin samun nutsuwa, cikin muryarta da ta dashe ta yi sallama, Unaisa da Unaid yaran Yaya Ahmad ne keta wasa acikin tsakiyar falon, suna ganinta suka taho da gudu cikin ƙaunarta su duka sukace.
"Oyoyo Aunty Zaleeha!"
cikin yanayin sanyi daya rusketa haɗi da rashin kuzari tashafa kayinsu kana ta zuge zip ɗin jakarta, kasancewarta uwar mak'ulashe da shan zaƙi hakan yasa sam bata rabo da abubuwan zaƙi dangin su chocolate's da sweet's, chocolate ta basu sannan ta nufi ɗakin Mamy nan tabarsu sunata murna.

Sallama ɗauke abakinta tashiga ɗakin Mamy'n,
Mamy dake zaune abakin gado tana ninke kaya ta amsa mata cike da kulawa tana me dubanta.
"Sannu da hutawa Mamy!" tafaɗa tana me ajiye jakan hannunta kana ta sanya hannu ta zare mayafin dake jikinta.

"Yauwa Zaleeha sannu da dawowa ya aikin?".
cewar Mamy tana mebinta da kallo.

"Lafiya". tafaɗa ataƙaice kana ta faɗa kan gadon Mamyn blanket taja ta rufe jikinta dashi.
Cikin damuwa haɗi da kulawa Mamy tace .
"Yadai Zaleeha bakida lafiya ne?"
cikin muryarta dake neman sarƙewa tace.
"Mamy kaina ke ciwo, sannan zazzaɓi na damuna!"

"Subahannallah! kinsha magani kuwa?".
Mamy tafaɗa aɗan rikice tana mai taɓa jikin Zaleeha'n, aikuwa nan taji jikin yaɗau zafi zau.
Kai Zaleeha ta girgiza alaman batasha ba, tashi Mamy tayi tare da cewa.
"Bari naje na kawo miki abinci da magani kisha inyaso idan yayanku Ahmad yashigo sai ya kaiki asibiti"
Mamy na fita Aunty Lubna matar Ya Ahmad tafito daga cikin toilet ɗin dake ɗakin Mamyn, jikinta duk ruwa da'alama alwala tayi, ganin Zaleeha akwance lulluɓe da bargo yasanyata cewa.
"Lafiya kike kuwa Zaleeha duk wannan uban zafin shine ke hadda lulluɓuwa".
Zaleeha da zazzaɓi yasake cin ƙarfinta ta ɗago idanunta ta kalli Aunty Lubna'n sai kuma ga hawaye shaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta.
Ganin hawaye na fita daga idon Zaleeha yasanya jikin Aunty Lubna yin sanyi, zama tayi akusa da Zaleehan tare da sanya hannu ta dafa kanta cikin kulawa tace.
"Kuka kuma Zaleeha? share hawayenki kinji komai yayi tsanani yana tare da sauƙi ki sawa ranki jarumtar yadda zaki fuskanci k'addararki!"
Kai Zaleeha ta girgiza mata tare da kife kanta akan cinyan Aunty Lubna'n cikin dasashshiyar muryarta tace "Menene laifina Aunty Lubna? meyasa kowa agidannan bazai yarda cewa inada wanda nakeso ba, sannan kuma ba aljani bane kamar yanda suke tunani, mutum ne shifa kamar kowa, Inasonsa! Aunty Lubna Inasonsa!, bansan meyasa kowa yaƙi fahimtan hakan ba hatta Ya Ahmad ɗina ma fa shima kallon bansan me nakeyi ba yakeyi mini gani yake wai ba mutum nake soba aljan ne!".
shiru tayi da maganan tare da ƙara sautin kukanta.
Cikin lallashi haɗi da tsananin tausayinta Aunty Lubna ta sanya hannunta ahankali take shafa bayan Zaleehan, cikin son kwantarwa da Zaleeha hankali tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha ki kuma kwantar da hankalinki, nafahimci yanda kikeji kuma insha Allah zaki gansa harma kuyi aure dashi kidaina kukannan kinji shalelen Ya Ahmad ɗinta!".
Wani irin sanyi kalaman Aunty Lubna suka sauƙarwa Zaleeha acikin zuciyarta, take taji son matar Yayan nata ya ƙara shiga ranta, nan tasoma ƙoƙarin share hawayenta harma da sakin murmushi, Mamy ce ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da plate ɗin abinci da kuma magani, kasancewar taji sanyi acikin ranta bisa kalaman da Auntyn nata tayi mata hakan yasanya ta ci abincin saidai ba sosai ba magani tasha inda tayi alwala tayi sallah bata bar kan sallayan ba saida tayi sallan isha, anan ɗakin Mamy ta kwanta, mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa, ana idar da sallan Isha kuwa saiga Abdussalam yayiwa gidan dirar mikiya, koda Mama taji zuwan Abdussalam nan tashiga zazzaga masifa wai Zaleeha batajin magana tayi baƙo me mahimmanci kuma taje ɗakin uwarta tabiyu tayi zamanta, koda akaje ɓangaren Mamy ƙiran Zaleeha nan aka iske tana bacci, inda Mamy ta shaida cewa bata da lafiya ne, haka Abdussalam ya koma gida batare daya samu ganin Zaleeha ba, Mama kuwa ba irin faɗa da maganganun da bata faɗa ba ita kaɗai taketa ɓaɓatun ta harda cewa wai Mamy ce ke zuga Zaleeha akan kada taso Abdussalam, haka tayita aikin baƙin ranta ita kaɗai awannan daren dai Zaliha aɗakin Mamy ta kwana.

***

Alhamdulillahi yau kwanan su Saifuddeen uku da dawowa Nigeria, inda acikin kwanaki Ukunnan sauƙi kullum ƙara samuwa yake ga Saifuddeen yana mai ci gaba da shan sabbin magungunan da aka loda mishi.
sannan kuma acikin kwanakin kullum gidan nasu cikin karɓan baƙuncin mutanen dake zuwa gaisuwa yake,ciki kuwa hadda matar Alhji Sani, da kuma Matar Alhaji Kabiri da Mommyn Hisham.da kuma matar Alhaji Adamu Hajia Kingi damn k'anwarta Aunty Kubra yar kasuwa ce mai zuwa Dubai sari kayan k'awa na mata, time to time da ita Ahmad ke zuwa sari, suma sunzo sun duba jikin Saifuddeen inda Ummi taji daɗi sosai.

Ranan yau takasance laraba kuma yaune ranan da Ishaq ya sanar da Saifuddeen cewa Zaleeha zatazo gidan nasu na nakasassu don gudanar da shirinta mai suna BABU NAKASASHE SAI RAGO, hakan yasa tun safe yau Saifuddeen yatashi yanajin kansa cikin wani irin shauƙi yayinda yakejin zuciyarsa wasai.

Ɓangaren Zaliha kuwa kwana biyu kenan yau bataje aiki ba sakamakon ɗan jinyan da tayi, amma yanzu Alhamdulillah jikin nata yayi sauƙi sosai, yayinda kullum Aunty Lubna ke ƙara kwantar mata da hankali, hakanan yau tatashi tana mejin faɗuwar gaba yayinda takejin zuciyarta na tsinkewa akai akai haka dai ta kawar da duk wani abu da takeji ta shiga shirya kanta don zuwa gabatar da shirinta.

Fitowarsa daga wanka kenan lafiyayyar skin ɗinsa sai fidda daddaɗan ƙamshin tsadadden sabulun wankansa, zaune yake agaban mirror yana shafawa jikinsa mai, yana kammalawa ya shiga gyara ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ta sauya gaba ɗaya kamanninsa na da, taƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini. Wata dakakkiyar shadda me kyau da tsadan gaske wacce take da kalan skay blue ya sanya, sosai shaddar ta amshi jikinsa inda tayi bala'in da cewa da white skin ɗinsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar wacce jikinta ke ɗauke da ratsin sky blue yasanya, yayinda aƙafansa kuwa yasanya lafiyayyun takalma sau ciki ƙiran kamfanin bally suma kalar sky blue garesu hakan yasanya haɗuwar tasa ta ƙara bayyana, bakaɗan ba Saifuddeen yayi kyau yayinda kyakkyawan sajensa keta ƙyalli, tsadadden turarensa me daɗin ƙamshi ya fesa ajikinsa take ɗakin ya gauraye da ƙamshinsa, agogonsa ƙiran kamfanin rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa na dama, wayarsa ƙirar iphone ya tura acikin aljihunsa tare da sarrafa kekensa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Daddaɗan ƙamshin turarensa shiya ja hankalin su Ummi da Hayatuddeen da kuma Raihana dake falon suka dawo da kallonsu garesa, "Wow Hamma Saifuddeen ka ganka kuwa? Wallahi Hamma na baka taɓa yin kyau irin na yau ba!!".
Hayatuddeen yafaɗa cikin santin kyawun da yaga hamman nasa yayi.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen tare da duban Ummi cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan wai maganan da Hayatuddeen yafaɗa gaskiya ne?
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"A kullum a koda yaushe kai kekyawa ne koda bakayi wonkaba bare kolliya.
to ya kake zato idan kayi kwalliya to sai kayi kyau tamkar balarabe.
kaga kenan sharrin Hayatuddeen ne kawai dama tuncan kai kyakkyawane!"
Dariya gaba ɗayansu suka sanya banda Saifuddeen wanda shidai saidai yayi murmushi.
Cikin yabawa da kyawun da yayi Raihana tace.
"Hammana wallahi kayi kyau sosai".
murmushi yayi mata tare da yi mata alama kan cewa ya gode, Hayatuddeen kuwa cikin azarɓaɓi ya ciro wayarsa hoto yashiga ɗaukan Hammannasa yana me cewa ya samu na sawa a status da kuma Instagram.
jin haka Raihana ta amshi wayar tare da yi musu hoto shida Ummi da Raliya data shigo yanzu. Sunyi kyau matuk'a duk suna murmushi Ummi ta d'an roggofo kanshi.

Cikin body language ɗinsa yayiwa Ummi bayanin inda zaije, fatan Alkhairi Ummi tayi masa tare da cewa.
"Adawo lafiya".

Har bakin mota Hayatuddeen ya raka hamman nasa yayinda da kansa ya sauƙa akan kujeransa ya shiga cikin tsaleliyar motarsa ƙiran mercedes benz, agidan baya ya zauna sannan Hayatuddeen ya sa mishi weelchair d'insa a but yayinda Sule driver ke tuƙasa...

Tana gama shafa mai ta ɗauki tsadaddiyar hodan ta ta goga akan fuskarta, tana gama shafa hodan ta ɗauki black eye pencil ɗinta ta goga acikin manya manyan idanunta dake matuƙar gigita masu kallonsu, pink lipstick ta goga akan ƴan ƙananun laɓɓanta, yayinda tayi amfani da Mascara wajen miƙar da tulin eye lashes ɗinta, ita ba mace bace wanda take da yawan cika meckup akan fuskarta hakan yasa bata ƙara komai akan fuskarta ba bayan wannan ɗan kwallian da tayi.
Wani haɗaɗɗen lace wanda yaji dinkin riga da sket maroon colour wanda keda ratsin golding ash ta sanya, sosai kayan suka amshi jikinta inda sket ɗin ya bayyana haɗaɗɗiyar surar jikinta da kuma cikakkun hips ɗinta, parking dogon gashinta tayi atsakiyan kanta tare da zama akan stull ɗin mirror tashiga tsantsarawa kanta ɗaurin ɗan kwali, wani irin haɗaɗɗen ɗauri tayiwa kanta wanda yaƙara bayyana kyawun shigar nata, wata ƴar siririyar sarƙa golding ash ta sanya awuyanta tare da liƙa ɗan kunnensa me kamar manne akunnenta, wani takalmi me tsananin tsini da kyau wanda keda kalan lace ɗinta ta sanya aƙafafunta tare da ɗaukan wani vail shima maroon colour ta yafa ajikinta, baƙaramin kyau Zaleeha tayi ba ita kanta yau kyawunta ya ɗauki hankalinta, turarenta dake rikita maza ta fesa tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta me kalan kayanta ta riƙe ahannunta, wayarta tariƙe aɗayan hannun nata tare da car key ɗinta kana ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa take taku ƙwas-ƙwas hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance, cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo".
Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace.
"Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?".
Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce ne".
Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon, da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa.

Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu,
cikin had'e fuska yace.
"Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?."
ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido.
cikin yin rau-rau da ido tace.
"Ya Habu bazan sake ba."
kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida.
Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi. Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan.

Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot, daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta.
Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta, addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon, mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!".
Murmushine yafaɗaɗa akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace.
"Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?".
Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani.

Yau da wani Gurgu zata gudanar da shirin nata don haka tuni ta tafara ƙoƙarin soma yi masa tambayoyi kamar yanda tsarin shirin nata yazo dashi, ko mintu 10 ba ayi da fara shirinba a hankali taji wani irin ni'imtaccen iska na ratsa ko ina dake jikinta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta,
lumshe idanunta tayi sakamakon wani irin daddaɗan ƙamshi da taji ya ratsa cikin hancinta ya kuma cakuɗa da numfashinta, wani irin mimmiƙewa taji tsikar jikinta nayi, wani irin sanyi me daɗine taji yana kusanto ta tamkar wanda ake hurosa, hakan yasanya akasalance ta kai dubanta ga inda takejin kamar tanan sanyin ke fitowa, dai-dai lokacin shikuma ya shigo cikin wajen, zaune yake akan kekensa fuskarsa na fitar da annuri haɗi da ƙyallin kyau sajenshi yayiwa fuskar k'awanya mai jan hankali.
Wani irin duka da harbawa zuciyar Zaleeha tayi, yayinda ta kafesa da idanunta masu rikita maza, cikin nutsuwa yake sarrafa kekennasa wanda kuɗinta kaɗai ya isa yasai wani gida, sam ya kasa ɗauke kyawawan idanunsa daga kan kyakkyawar fuskar da yajima yana bege dason gani, wani irin yawu Zaleeha ta haɗiye wanda ya tsaya mata amaƙoshi, zata iya rantsewa bayan mutumin daya taimaketa bata taɓa ganin wani kyakkyawa aduniya ba bayan wannan mutumin dake zaune akan kekensa in dai ido da idone, cikin tsananin dauriya da kama ajinta bawai don ta ƙoshi da kallonsa ba ta kawar da idanunta gefe, ƙarasowa cikin babban falon yayi tare da tsayawa adai dai inda Ishaq ke zaune,
A fakaice ta D'angelo kalle fararen yatsun hannunshi da yaketa musabaha da mutanen nasu da suka kewayeshi tamkar sarki a fadarsa,
ƙamshinsa kaɗai yasanya Ishaq ganesa, nan ya ɗauki wayarsa ya rubuta masa saƙo kamar haka.
"Gafa Zaleeha nan tana gudanar da shirinta wani sati dakai za ayi".
Murmushi kawai Saifuddeen yayi tare da yiwa abokin nasa rubutu inda yace.
"Allah ya kaimu,"
kana shiko Ishaq ya gyara zama tare da cewa.
"Zaleeha ga aboki na kurman da na tab'a gaya miki naje Indian dubashi da jiki."
ba tare da ta kalleshi ba tace.
"Ayyah."
Shiru yayi tare da kafeta da idanunsa kowani motsi da zatayi tare da bugun zuciyarsa yake tafiya amman da yake ya iya sarrafa kanshi babu mai ganewa sai ita da takejin kwayar kekyawan idanunshi na yawa a surar jikinta.
Hakan yasa gaba ɗaya nutsuwarta ce tayi ƙaura daga jikinta, cikin rashin kuzarin dayazo ya lulluɓeta haka take gudanar da shirin, ɗan ɗago da mayan idanunta tayi da niyar satan kallonshi karab idanunsu suka haɗe dana juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, sakamakon wani irin shock da taji acikin jikinta, gaba d'aya taji wani abu na dark'efe kwayan idanunta,
bayan kamar minti 7 tasake ɗago da kanta don ta dubesa still idanunsu ne ya sake sarƙewa acikin najuna, sake yin ƙasa da kanta tayi aranta tana cewa.
"Na shiga uku waye wannan kuma ne wai da yazo ya hanani sukuni, irin wannan kallo saikace maye hegen gurgu mai jajayen kunnuwa, dama ai ance gurgu yafi mai k'afa iya shege!".
bayan kamar 8 minutes a hankali tasake ɗago kanta, har yanzu dai kallonta yake baya ko ƙiftawa sai dai ya rage girman idanun nashi, ɗan jim tayi tare da yin mgnar zuci.
"OK tsaurin ido ko tam zanyi mgninka yanzu".
kana itama ta tattaro tsaurin idonta da jarumta ta tsaida kwayar idanunta cikin nashi kwayar idanun,
dib-dib taji zuciyarta na bugawa da k'arfi-k'arfi kuma da sauri,
wani irin kwarjini da haibar fuskarsa da surarshi suka cika mata idani cikin one second ta janye idanunta cikin idanunshi da sauri ta maidasu akan surar kansa zuwa gefen sajenshi, ganin bai ɗauke nasa idanun daga cikin nata ba yasanya ta sakar masa harara tare da murguɗa masa baki, wani irin dariyane ya kama Saifuddeen don sosai hakan da tayi ya ƙarawa fuskarta kyau, lumshe idanunsa yayi yana mejin wani abu ya dark'afe ƙahon zuciyarsa.
Adaddafe haka Zaleeha tagama gabatar da shirinta inda gaba d'aya kallon da Saifuddeen ke mata ya dagula mata lissafi, ita sam batason yawan kallo musamman ma shida ya kafeta da ido kamar zai cinyeta kuma idanun nashi wani haiba suke dashi na musammam.
a hankali taja gajeren tsaki tare, kallonshi a fakaice kana tace.
"Maye kaci Kanka!."
ido ya lumshe a hankali dan ya gane me ta fad'i mishi,
ita kuwa hararanshi ta kumayi kana taci gaba da aikinta.
Shi kuwa Saifuddeen cikin lumshe ido da shak'ar sassanyar iskar AC mai cike da k'amshi a ranshi yace.
"Uhummmm bazan ci kaina ba in sha Allah ke d'in dai zan c...!




Duk fa masu bin labarin nan kunsan sashi sashi muke binshi, to da ganin yanzu kun san mun shigo wani sashi na musamman kuma. Wasan yanzu zai fara.
Dan Allah da darajar iyayenmu da girman Al'arshi Kada ki fitarmin da littafi na, in kin fitarba ba sai nace Allah ya isaba ko inyi zagi da tashanci ba damn tijar maguzawa ba, No da Allah isasshene kuma shi yana sane daku in ni bana sane daku, kuma shine zai mana hisabi. Dan haka ni bazan zageku ba bare in zagi iyayenku, dan nasan darajar nawa iyayen ko k'abilata bana so a zaga bare iyayena shiyasa bazan zagi iyayen wasuba🤗🤗🤗

BY


*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:56 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*


*Page 26*


*NA*

*AISHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Lumshe ido yayi tare da yin magana a cikin zuciyarshi.
"Uhmmm bazanci kaina ba insha Allah keɗin dai zan ci!".
Sake ɗago idanunsa yayi ya watsa mata su, ita kuwa Zaleeha daketa ƙoƙarin tattara kayan aikinta ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, duk da cewa ba kallonsa takeyi ba amma tabbas tanajin idanunsa na yawo ajikinta,  tana gama haɗa kayan aikin nata taɗan ɗago da kanta,aikuwa idanunsu ne ya sake sarƙefe acikin na juna, 
"Anya wannan ba maye bane!".
ta kuma faɗa cikin ƙasa-ƙasa da murya tana me wurga masa harara da kyawawan idanunta.
Lumshe idanunsa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa dake beating, tabbas yau yasamu nutsuwa irin wacce yajima bai samu ba, bakomai ke tafiya da hankalinsa ba face yanda take kaɗa idanunta wajen hararansa,  harshe yasanya ya ɗan lashi red lips ɗinsa, yanaji ajikinsa inama da yana da damar da zai kusan tota garesa, tabbas daya jawota jikinsa yayiwa wannan bakin tsiwannanta shan tom-tom.
  hand bag ɗinta ta rayata abisa kafaɗanta tare dakai dubanta ga jama'an dake gabanta, sallama tayi musu akan cewa zata wuce, cikin takunta dake matuƙar ɗaukar hankalin maza ta tako harzuwa inda Ishaq yake,  ƙarasowanta garesu yayi dai-dai da kusan ɗaukewar numfashinsa sakamakon daddaɗan ƙamshinta daya samu cakuɗa da numfashinsa, cikin wani irin kasala ya lumshe beautyful eyes ɗinsa.
Saura bai wuce taku huɗu ba ta ƙaraso garesu ta tsaya cak tare dayin ƙasa da kanta, sam batajin zata iya kallon cikin idanun Saifuddeen dan wata azababbiyar fitina take hangowa cikin kwayar idanshi mai kama da maganad'isu haiba da kwarjinshi yana sa zuciyarta cikin wani yanayi, hakanan ƙarasowarta garesu ya haifar mata da faɗuwar gaba yayinda ƙirjinta ke duka da sauri-sauri.
Cikin tausasa murya ta dubi Ishaq daketa faman murmushi kamar yana ganinta,
  "Malam Ishaq nizan wuce sai kuma idan munsake haɗuwa wani sati Idan Allah yakaimu!"
Murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa, inda ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Saifuddeen cike da ƙaunar Saifuddeen ɗin yace "To  bari nai miki rakiya  Malama Zaleeha, amma fa wani sati kishirya don kuwa baƙonki na musammanne, abokina Saifuddeen kenan!".
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya daki zuciyar Zaleeha cike da haushinsa ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa harara, inda still ta kamasa yana kallonta,  "Nasani ae dama kallona kake maye kawai!".
tafaɗa cikin ƙasan maƙoshi tana me mulan-mulan da bakinta, 
Murmushin daya ƙara bayyana zallan kyau da kwarjininsa yayi, sarai ya fahimci me take faɗa cikin ransa yace.
"Zakisan kuwa ni maye ne na gaske duk randa kika shigo hannuna!".
Sake gayara zaman jakarta akan kafaɗarta tayi inda ta juya cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta nufi hanayar da zai fitar da ita daga cikin falon, tare da Ishaq suka jera suna tafiya, suna ɗan hira sam idan kaga Ishaq bazakayi tunanin makaho bane.
Da wani irin kallon So, haɗi da shauƙi tare da zallan k'auna Saifuddeen ya bita, komai nata abun burgewane, idanunsa ne suka sauƙa akan tsararren hips ɗinta da cikin salo suke juyawa, saurin lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa, don kuwa wani irin harbawa yaji jikinshi da zuciyarshi sa nayi,  wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da buɗe idanunsa, dai-dai lokacin ita da Ishaq suka fice daga cikin falon,   murmushi yayi tare da ɗan sanya hannu ya shafi lafiyayyen sajen dake kwance akan fuskarsa.

Sannu ahankali gaba ɗaya mutanen dake cikin falon suka soma watsewa kowa ya kama gabansa.

Har bakin motarta Ishaq ya rakata, inda sosai taji daɗin rakiyar tasa, cikin muryarta dake nuna jin daɗin rakiyar tasa tace.
"Godiya dubu Malam Ishaq!".

Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.
"To Malama Zaleeha kigaida mutanen gida!"

Da "To" ta amsa masa, kana ya juya yakoma inda yabar Abokinsa Saifuddeen.

Murfin motar  ta buɗe ta shiga  tare da murza mata key,  dai-dai-ta tsayuwar motar tata tayi, cikin tuƙinta me ɗauke da nutsuwa ta fice daga cikin harabar ofishin ƙungiyar ta (Jonapwd), cikin salo take murza kan steering motar tata,  tunaninsa ne ya faɗo cikin ranta, hakan yasa ta saki wata ƴar siririn tsuka tare dayin ƙwafa, cike da haushin irin kallon daya dinga yi mata ta murguɗa baki tare da yin guna-guni acikin ranta inda tace "Mutum gurgu sannan kurma amma sai shegen sa'ido, no wonder akace gurgu kafi me ƙafa iya shege!".
tafaɗi haka adai-dai lokacin da take shan wata kwana.

Ishaq na dawowa cikin falon, ya iske Saifuddeen wanda ke zaune cikin matsanancin shauƙinta.
Hannayen Saifuddeen ɗin Ishaq ya riƙo cikin nutsuwa yace.

"Saifuddeen kaga Zaleeha ko, tana da kirki sosai sannan akwai nutsuwa atattare da ita, sam kyawunta baisakata yin ɗagawa ba".
Murmushi Saifuddeen yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya rubutawa Ishaq saƙo kamar haka.

"Nayaba da hankalinta matuƙa ishaq, saboda hakane ma na zaɓeta a matsayi. Matar aurena uwar ƴaƴana in Allah ya yarda,
ba dama nace maka nasamu matar aure!".

Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace.
"Wai kana

Please Login or Register in order to submit comment