Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta a k'asa tace ku shigo ciki inji malam.

Shide kunyar ta na k'ara sa mishi sonta a zuciyarshi, ansawa yayi,sannan suka biyota a baya har zuwa d'akin.

Dardumai ne shimfid'e a ciki,Dan haka zama su kai,Maimuna dama tuni ta nufi gidan su tasa k'aninta ya kwaso kayan abincin shi da abokinshi suka kawo inda su Farhan d'in suke.

A kunyace Safna ta zuba musu abincin,sannan ta mik'a gabansu tace "ga abinci kuci kunsha hanya",

Murmushi Rayhan yayi sannan ya kishingid'a yace"Nide se in a baki za'a bani zanci in ba haka ba nak'oshi"

A kid'ime ta zaro ido tana kallonshi,kan kace kwabo idanun ta sun kawo ruwa,cikin shagwab'a da muryar kuka tace"ka rufamin asiri,bansan ya Nisan garin Ku yake ba, amma ana fad'in se an wuce jihohi uku kan aje,taya zaka yo wannan tafiya kace ba zaka ci abincina ba,kuma fa tun safe nake had'a maka"ta k'arasa maganar cikin turo D'an k'aramin bakinta gaba.

Tunda ta fara magana hankalin Rayhan gaba d'aya ya koma kanta,sonta da sha'awarta ke shawagi a zuciyarsa,yadda yake son matarshi ta aure ta kasance haka safnar sa take.cikin sigar rarrashi yace "is ok baby na,wasa fa nake miki ni na isa in k'i cin abincin gimbiyata,share hawayenki kar haisam ya raina min ke tun yanzu"

Dariyar da haisam ya yine yasa ta mik'e ta fice daga d'akin da D'an gudunta,bin bayanta Rayhan yayi da idanu,ji kake makwat ya had'iye wani miyau daya taru masa abaki.

Koda suka gama cin abincin alwala su kai suka je masallaci su kai sallah sannan suka jero da malam zuwa cikin gidan.d'akin soron suka shiga.

Cikin girmamawa suka gaisa da malam sannan suka gabatar da Kansu Wanda haisam ne kewa malam bayani shi Rayhan yayi shuru alamun jin kunya.

Bayan dogon bayani malam ya gano gidan kakannin Rayhan dake daura farin sani ya sansu,amma sabida jawa y'arsa k'ima se yace.

"Naji duk bayanin ku kuma na gamsu da shi,zan yi bincike game da hakan in na ga ba wata matsalar na amince in daura aurenka da mamana kamar yadda ka buk'ata zan sa ka turo magabatan ka bayan na kammala binciken,Allah yay muku albarka"

Amsawa sukai da "Amin baba mungode Allah ya k'ara girma"sallama yay musu sannan ya fice daga d'akin,

Bayan fitar malam ba'a jima ba safna ta shigo kanta a k'asa alamar jin kunya,fuskarta d'auke da murmushi.

Guri ta samu ta zauna,bata jima da zama ba maimuna ta shigo,suka shiga hira dasu haisam,cike da wayewa haisam yace"maimuna muje ki nunamin kan garinnan naku,ko nima zanyi arba da y'ar fillon da zata saci tawa zuciyar "murmushi maimuna tayi sannan ta mik:e suka fice daga d'akin.

Shuru ne ta ratsa d'akin tun bayan ficewar su haisam,Safna tayi k'asa da kanta se wasa take da abun hannunta.
Cikin tattausar murya yace"na takura ki da yawa ko baby na?"cikin murmushi ta girgiza kanta alamar ba haka bane,murmushi yayi ya mik'e daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna Wanda har jikinsu na tab'a juna,tsorone da firgici tsababa a idon safna,ya lura da hakan.

Murmushi yayi sannan ya sa hannu ya kamo hannunta,da sauri ta d'ago ido tana kallonshi,tana k'ok'arin kwace hannun Nata amma be bata damar hakan ba,a hankali ya furta,"Safna bazan tab'a cutar dake ba,ni din masoyinkine,amma naga ke kamar baki yarda dani ba,ko me yasa?"a hankali tace a d'an daburce "ba haka bane"

Matso da fuskarshi yayi sosai kusa da ta ta yana kallon idanuwan ta da shanyanyun idanuwan sa yace can k'asan mak'oshi "to yaya ne?"

Kasa magana tayi illa runtse idanun ta da tayi,Dan bazata iya jure kallon kwayar idanuwan sa ba

.murmushi yayi sannan ya saketa ya Dan matsa daga kusa da itan sannan yace "to oya bud'e idanun naki dodon ya matsa daga kusa dake"

Haka de yay ta jan ta da hira tun tana kin amsawa har tazo ta saki jiki dashi suka sha,hira.

Sai da aka idar da sallar isha'i sannan yay mata sallama bayan ya jibge mata kwalayen tsarabar da yayo mata,gami da bandir din kud'i dubu ashirin.duk yadda taso ya tafi da kud'in fafur yak'i,dole tasa ta amsa Dan har yayi fushi,.

Haka suka rabu cike da kewar juna,daura zasu su Kwana da safe su wuce abuja.


Muje zuwa


Surbajo for life
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*Zahra Surbajo*




*Page 7*




Cikin k'ank'anin lokaci Malam shi da Amininsa Baban maimuna suka je binciken waye Rayhan har garin Abuja.bayan sun gama binciken usulinsa na Daura.

Cikin ikon Allah ko ina beda nakasu,hakan sosai yayiwa malam dad'i Dan yana son Rayhan d'in.ya yaba da natsuwarsa.

Cikin sati guda mahaifin Rayhan da aminansa suka zo nemawa Rayhan d'in auren Safna, duk wani Abu na al'ada sun gabatar dashi inda aka sa ranar auren sati uku masu zuwa,Wanda shi Rayhan d'in Sam be so asa da nisa haka ba,Dan amatse yake da son mallakar matarshi.

Suko matan malam habaici da zagi da mugun fata game da auren na Safna ba Wanda basu yi ba,ita de Inna sabuwa ido tasa musu,a zuciyarta kuma ta na bin y'ar tata da addu'a.

Duk wani gyaran Amarya k'anwar innarta da ke daura ne tai mata,
Tuni Amarya ta fito a amaryarta.

Ko ina a garin na Sara gulmar auren na Safna ake yi,inda ake ta yamad'id'in auren kud'ine,shi yasa aka yi saurin tsaida lokaci.

Malam ma toshe kunnensa kawai yayi Dan maza ma ba'a barsu a baya ba gurin gulmar auren na 'yarsa

*********

Rayhan matashine D'an kimanin shekaru 33 da haihuwa,farine amma ba tas ba, dogo ne, me D'an jiki Wanda ba za'a kirashishi lukuti ba,dirarrene ta kowanne tsagi,
Fuskarshi zagaye take da kwantaccen sajen daya dace da zubin fuskarsa,

Rayhan mutum ne me ilimin boko da islamiyya sabida yayi dace da iyaye nagari Wanda suka bashi tarbiyya.

Ko kad'an sharholiya bata cikin tsarinsa a natse yake,shiyasa yake yawaita yin azumi Dan kame kansa


Mahaifinsa Alhaji Hashim D'an kwangilane,Wanda ya tara dukiya me yawa,matar sa D'aya,Hajiya Hafsa wacce takasance y'ar kasuwa dake saro kaya daga k'asashen waje ta kawo gida Nigeria ta siyar.
'Ya'yan su uku biyu mata d'aya namiji Wanda shine Rayhan d'in,kuma shine babba,sauran k'annensa ne,nuzula da jawahir,Wanda yanzu haka suna jami'a suna karatu.

Rayhan yayi karatu a k'asar England, inda yayi karatu a fannin kasuwanci,Wanda shine abinda yafi burgeshi shiyasa ya zabi fannin.

Koda ya kammala ya dawo gida, mahaifinshi mak'udan kud'ad'e ya bashi Dan ya fara gudanar da kasuwancin,in da be yi k'asa a guiwa ba yasa hannun jari a harkar saida man petur,sannan ya gina gidajen mai guda uku nashi nakanshi Dan jin dad'in gudanar da kasuwancin.

Tunda ya kammala karatu kullum burin iyayensa yayi Aure sabida shekarunsa na tafiya,shima yana da burin hakan se de wacce ze aura d'inne be gani ba.

Mahaifiyarsa da k'annensa sunfi kowa murna da jin ze yi aure,Dan haka suka shiga shirya lefe nagani na fad'a Wanda za'a kai gidan su Safna.

Wannan kenan

************

Ranar jumma'a dubban mutane suka halarci garin na Sara domin shaida auren Safna da Rayhan, Wanda ya kafa tarihi a garin na Sara.
.Wanda manyan 'yan kasuwa da jami'an gomnati,da masu fad'a aji suka halarci d'aurin Auren.

An d'aura auren akan sadaki naira dubu D'ari,Wanda ango Rayhan bakinsa Sam yak'i rufuwa ko ina ka waiga makad'a da marok'a ne ke ta aykinsu.

Tuni an gama shirya Amarya wacce tai kuka har ta godewa Allah, Dan tare da 'yan d'aurin Aure za'a tafi da ita,bayan malam yay mata nasiha game da zaman Aure.

Kuma malam ya hana kowa zuwa rakata,a cewarshi d'orawa mijinta d'awainiya za'a yi,

Haka aka fito da ita tana ta rusa kuka,motar da ango ke ciki aka sa ta,direba ya ja sauran motoci suka Mara musu baya.

Koda ta shiga motar d'ago ido tayi Dan taga waye a kusa da ita,carab idonta ya shiga nashi yana mata murmushi, fad'awa jikinshi tayi ta ci gaba da kukanta.

Rungumeta yayi sosai a jikinshi yana sakin wata ajiyar zuciya, wani Abu ke taso masa tun daga tafin k'afarsa zuwa tsakiyar kansa, a hankali ya shiga rarrashinta cikin murya me dad'i,yace"kukan na menene baby,haka?"cikin kukan take kai masa k'arar malam kan hana rakota da yayi.

Bayan ta ya shiga shafawa yana hura mata iska a kunne,Wanda sannu a hankali kukan ya gudu,sautin numfashinta da yaji ya sauya ne yasa ya fahimci bacci tayi.

Murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciyarta a jikinshi ta yadda ba zata wahala ba,sannan ya maida kallonsa gaban motar,ido suka had'a da haisam dake Jan motar ta glass, ayko ya tuntsire masa da dariya,sannan yace"baba kode transit zamu yi a hanya ne kad'an maida miyau kan mu wuce?"duka Rayhan ya kai masa. Ya goce dariyar dukansu sukeyi.


Muje zuwa

Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*Zahra Surbajo*



*Hauwa'u Muhammad Danjuma NBS keffi,Duk k'awar da ta dace da k'awa aminiya irinki to ta hau gado tai bacci,Dan inde da ranki da lfy bazaki bar damuwa ko b'acin rai ya iso gadon baccinta ba,Allah yasaka miki da Alkha'iri farin cikin da kike sakani ni da D'ana yusuf bamu da abun biyanki,Allah ya d'aukaka darajarki Dan halak be mance halacci akanki na tabbatar da haka*



*Page 8*


Da isha'i suka Iso gidan Rayhan dake Abuja, gidane na alfarma Wanda ko a mafarki Safna bata tab'a ganin kanta a cikinshi.
Ba kowa a gidan se su da suka shigo yanzu,Dan Abban Rayhan hana kowa zuwa yayi shima yace a bari se ta Kwana biyu a zo.

Haisam na sauke su yay musu sai da safe bayan ya mikawa Rayhan kaji da madarar da suka siyo a hanya, ya ja motar ya fice daga gidan,yana tsokanar Rayhan, Safna tsayawa tayi a harabar gidan duk se taji ranta ba dad'i ganin shima danginshi ba Wanda yazo tarbarta.
Rayhan d'inne ya matso inda take ya kama hannunta ya ja ta a hankali zuwa cikin gidan,inda take tafiya a hankali kamar bazata ba.

Be a jiyeta a ko ina ba se akan gadonta Wanda ya gaji da had'uwa,a sanyaye ta zauna kanta cikin mayafi a k'asa.

Muryarshi ce ta katseta daga tunanin da take inda yace "zani d'aki in kimtsa kema ki samu kid'an watsa ruwa kamin in dawo,ga toilet nan acikin d'akin"ya fad'i yana lek'a fuskarta, da sauri ta kara sunne kanta k'asa,lakace mata hanci yayi sannan ya fice daga d'akin.

Bayan fitar shi ta jima zaune sannan ta mik'e ta shige toilet d'in,suman tsaye tayi ta tsaya tana k'arewa toilet d'in kallo,,to in banda abun Rayhan taya zata iya amfani da toilet d'in,da ta rasa yadda zatayi kawai sai ta dawo d'aki tai zamanta.

Rayhan be jima ba sosai ya dawo sanye cikin farar jallabiya data bi fatar jikinshi ta kwanta lub.hannunshi rik'e da ledojin da suka shigo dasu d'azu,

Da sallamarsa ya shigo d'akin,sosai yay mamakin ganin ta inda ya barta tun d'azu,ajiye kayan hannunshi yayi,sannan a hankali ya taka ya isa gareta,gefenta ya zauna,sannan yasa hannu yacire mayafin dake kanta,da ike ba d'ankwali hakan yaba gashinta da yasha gyara damar bayyana se shek'i yake.

A hankali ya janyo ta jikinshi,yay mata mafaka a k'irjinshi,sannan yasa hannu a hankali ya cire ribbon d'in da aka kama mata gashin dashi,hakan yaba gashin damar bazuwa har kan k'irjinshi,wani niimtaccen kamshi yaji ya bugu hancinshi daga gashin Nata, zib d'in rigarta ya fara nema a hankali ya fara zuge shi,da sauri safna ta dago manyan idanuwanta tana kallonshi,hure mata idon yayi sannan yasa hannu ya gyara mata gashin kannata,daya zubo mata a fuska,yace yana d'aga mata gira, "wankan zan miki tunda nace kiyi kin k'i"
A kunyace tace"ba k'in yi nayi bafa,toilet d'in ne ban gane kanshi ba shiyasa"

Se alokacin ya tuna daga inda ya d'auko safna,dole bazata iya amfani da toilet d'in ba matukar ba bayani yay mata ba.

Murmushi yay mata sannan ya k'arasa zuge zib d'in,yana fad'in"ba komai ni ay tunda na dawo se in miki wankan"ya k'arasa maganar,yana cire mata hannayen rigar,Wanda hakan yaba albarkar k'irjinta damar bayyana,
Safna kasa hanashi tayi,sabida a fad'an da aka mata a gida ance yin hakan sab'awa Allah neπŸ˜„hakan ne yasa ta barshi yake yadda. Yaga dama da ita.

Rayhan Ido ya k'ura musu yana kallo,se yake ganin abun kamar a mafarki wai shine zaune da Safna ba Riga ajikinta,a matsayin mata da miji,a hankali ya mik'a hannu ya rungumota zuwa jikinshi yana sauke wata ajiyar zuciya,yace can kasan makoshi"baby komai naki me kyau ne,Allah yasani beauty inason mace me cikar halitta kuma se gashi Allah ya bani full options"sunne kanta tayi a k'irjinshi Dan ita gaba d'aya kunya ce fall idanunta.

Da kyar ya sake ta sannan yaja hannunta zuwa toilet d'in ya nuna mata komai sannan ya fito,nashi d'akin ya koma, yayi tsarki ya d'auro sabuwar alwala Dan ta d'azu ta lalaceπŸ˜„


Safna wanka tayi sannan ta d'aura alwala,ta d'auro tawul ta fito,Wanda fitowarta yay daidai da shigowarshi.

K'asa tai da kanta tana wasa da hannunta,kallo d'aya yay mata yaji yana shirin b'ata sabuwar alwalarshi yasa ya dauke kai da sauri.

Ma'ajiyar kayan sawa dake d'akin yaje ya bude ya d'auko mata wata rigar bacci Dede guiwa se dogon hijab na sallah da zani empty da zata d'aura.

Kayan maminshi ce tasa aka tanajesu tun kan su tare.

Gabanta yaje ya mik'a mata kayan sannan ya juya mata baya, rigar tasa sannan ta zame tawul d'in jikinta se rawa yake ta d'aura zanin ta saka hijab d'in,rab'awa tayi ta gefenshi ta wuce inda taga ya shimfid'a dardumar yin sallar.


Muje zuwa.



Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*Zahra surbajo*



*Page 9*



Bin bayanta yaje yayi suka tada sallar,
Koda suka idar addu'o'in zaman lafiya da samun zuri'a dayyiba yay musu sannan yajanyo ledojin da ya shigo dasu,yafito musu da nama da madarar dake ciki suka ci suka sha,Wanda safna tayi Nata da taimakon Rayhan d'in.

Safna brush tayi tazo ta kwanta,yayin da Rayhan seda yagama kashe wutar ko ina sannan yabi bayanta,

Ganin shi kwance daga shi se gajeren wando agefenta shi yafi komai sata rud'ewa,se mutsu-mutsu take a gadon ta kasa baccin.

Hannu ya mik'a ya janyota gaba d'aya jikinshi,,yay mata rumfa da faffad'an k'irjinshi, sannan yasa hannu yana gyara mata gashin kanta,a hankali yace
"Me ya hanaki baccin babyna?"

Akunyace tace "ba komai"

K'ara matsarta yayi yace"kode ni kike buk'ata ba?"
Da sauri tace"ni wallahi ba haka bane"tayi maganar kamar zatai kuka.

Murmushi yayi me taushi,sannan ya had'e bakinshi da nata ba tare daya ce komai ba.
A hankali yake tsotsar bakin Nata cikin salon da Safna ba zata iya jurewa ba,hakan yasa take ta mutsu mutsu,yayinda gefe guda kuma ta lumshe ido alamar tana amsar sakon.
A hankali ya cire bakin nashi akan nata yace cikin dusasshiyar murya yana kallon fuskarta,"baby ni bazakiyi kissing d'ina bane ko ko bakyason Wanda ni nake miki ne?"ya k'arasa maganar yana shafo gefen Boob's d'inta.
Girgiza masa kai tayi gami da b'oye fuskarta a k'irjinshi.

Kyaleta yayi yaci gaba da sarrafata yadda yake so,tun bata maida martani har tazo tana biye masa.

Wannan dare Safna ta gurzu a hannun Rayhan ta yadda ko hannu bata iya d'agawa,se ido dake zubda kwallar danasanin biye masa da tayi.

Da kanshi ya taimaka mata ta gyara jikinta,se lallab'ata yake kamar kwai,yana sa mata albarka.

Pain killer yabata,sannan ya d'auketa cak zuwa dakin shi inda ya kwantar da ita yana ta lallab'ata har tai bacci.

Farin cikin da Rayhan yake ciki baze iya misaltashiba,Dan da kyar yay bacci.


Koda gari ya waye safna kunyar Rayhan d'in take ji ba kad'an ba,Dan ko magana ta kasa yi masa,shi ke janta da hira gamida tsokana.

Zaman Rayhan da Safna zamane na tsantsar so da k'aunar juna,danginshi na sonta itama haka.

Rayhan mutum ne meson haihuwa shiyasa ya kwallafa rai kan son ganin Safna tasamu ciki Wanda tsawon shekaru hud'u na auransu hakan be samu ba,

Safna na zuwa university, shekarar k'arshe take tana karantar mass communication, matsalar rashin haihuwarta itama yana damunta.

Hakanne yasa suka fara yawon Neman magani Wanda kullum basa gajiya.

A wannan tsukunne Allah yayiwa mahaifin Safna rasuwa,sosai tai kukan rashin mahaifinta,ga tausayin mahaifiyarta wacce bata da isasshiyar lafiya sakamakon ciwon zuciya dake damunta.

Rayuwar bata mata dad'i,ganin tayi nesa da mahaifiyarta bare ta taimaka mata, a k'ok'arin Rayhan naganin ya kwantar mata da hankaline ya d'aukar ma innar tata y'ar ayki dake kulawa da ita.

To a yawon Neman maganine suka had'u da doctor Amina har k'addarar sauya kwayoyin dashen haihuwar ta fad'a musu.

Muje zuwa



Surbajo for life.
11/14/21, 12:44 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*Zahra surbajo*



*Page 9*



Bin bayanta yaje yayi suka tada sallar,
Koda suka idar addu'o'in zaman lafiya da samun zuri'a dayyiba yay musu sannan yajanyo ledojin da ya shigo dasu,yafito musu da nama da madarar dake ciki suka ci suka sha,Wanda safna tayi Nata da taimakon Rayhan d'in.

Safna brush tayi tazo ta kwanta,yayin da Rayhan seda yagama kashe wutar ko ina sannan yabi bayanta,

Ganin shi kwance daga shi se gajeren wando agefenta shi yafi komai sata rud'ewa,se mutsu-mutsu take a gadon ta kasa baccin.

Hannu ya mik'a ya janyota gaba d'aya jikinshi,,yay mata rumfa da faffad'an k'irjinshi, sannan yasa hannu yana gyara mata gashin kanta,a hankali yace
"Me ya hanaki baccin babyna?"

Akunyace tace "ba komai"

K'ara matsarta yayi yace"kode ni kike buk'ata ba?"
Da sauri tace"ni wallahi ba haka bane"tayi maganar kamar zatai kuka.

Murmushi yayi me taushi,sannan ya had'e bakinshi da nata ba tare daya ce komai ba.
A hankali yake tsotsar bakin Nata cikin salon da Safna ba zata iya jurewa ba,hakan yasa take ta mutsu mutsu,yayinda gefe guda kuma ta lumshe ido alamar tana amsar sakon.
A hankali ya cire bakin nashi akan nata yace cikin dusasshiyar murya yana kallon fuskarta,"baby ni bazakiyi kissing d'ina bane ko ko bakyason Wanda ni nake miki ne?"ya k'arasa maganar yana shafo gefen Boob's d'inta.
Girgiza masa kai tayi gami da b'oye fuskarta a k'irjinshi.

Kyaleta yayi yaci gaba da sarrafata yadda yake so,tun bata maida martani har tazo tana biye masa.

Wannan dare Safna ta gurzu a hannun Rayhan ta yadda ko hannu bata iya d'agawa,se ido dake zubda kwallar danasanin biye masa da tayi.

Da kanshi ya taimaka mata ta gyara jikinta,se lallab'ata yake kamar kwai,yana sa mata albarka.

Pain killer yabata,sannan ya d'auketa cak zuwa dakin shi inda ya kwantar da ita yana ta lallab'ata har tai bacci.

Farin cikin da Rayhan yake ciki baze iya misaltashiba,Dan da kyar yay bacci.


Koda gari ya waye safna kunyar Rayhan d'in take ji ba kad'an ba,Dan ko magana ta kasa yi masa,shi ke janta da hira gamida tsokana.

Zaman Rayhan da Safna zamane na tsantsar so da k'aunar juna,danginshi na sonta itama haka.

Rayhan mutum ne meson haihuwa shiyasa ya kwallafa rai kan son ganin Safna tasamu ciki Wanda tsawon shekaru hud'u na auransu hakan be samu ba,

Safna na zuwa university, shekarar k'arshe take tana karantar mass communication, matsalar rashin haihuwarta itama yana damunta.

Hakanne yasa suka fara yawon Neman magani Wanda kullum basa gajiya.

A wannan tsukunne Allah yayiwa mahaifin Safna rasuwa,sosai tai kukan rashin mahaifinta,ga tausayin mahaifiyarta wacce bata da isasshiyar lafiya sakamakon ciwon zuciya dake damunta.

Rayuwar bata mata dad'i,ganin tayi nesa da mahaifiyarta bare ta taimaka mata, a k'ok'arin Rayhan naganin ya kwantar mata da hankaline ya d'aukar ma innar tata y'ar ayki dake kulawa da ita.

To a yawon Neman maganine suka had'u da doctor Amina har k'addarar sauya kwayoyin dashen haihuwar ta fad'a musu.

Muje zuwa



Surbajo for life.
11/14/21, 12:44 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*Zahra Surbajo*

*Page 10*

Watanni biyu doctor Amina ta kwashe
Neman Rayhan a waya amma bata shiga,
Ji take yi kamar tai hauka, gaba d'aya ta fice daga hayyacinta,bata gane komai.kullum addu'arta Allah ya basu ikon dawowa gareta.

A nasu B'angaren ko Rayhan da safna,suna can k'asar Germany inda Rayhan yaje domin gudanar da wani kasuwanci.

Tunda doctor Amina ta shaida mishi Safna Nada ciki ya d'auki son duniya ya d'orawa cikin,kulawar da yake ba Safna ko kanshi be bawa ita.

Duk wani fata da burin shi akan cikin ya d'ora shi,hakanne yasa yay alwashim duk ranar daya koma Nigeria ze yiwa doctor Amina kyautar da bazata taba mantawa ba.

Watansu biyu ya kammala abinda ya kaishi,Dan haka suka fara shirin komowa gida,
Safna ce ta matsa kan su koma d'in sabida rashin lafiyar mamanta,amma shi a so samunsane se ta haihu ze maido ta gidan.

Ta Lagos suka sauka,sannan suka hau wani jirgin zuwa Abuja, suna sauka a airport suka tarad da direba yazo d'aukarsu.


'Yan uwan Rayhan sosai sukai murna da dawowar tasu,game da cikin jikin safna kuwa,har walimar samuwarshi suka shirya.

Satin su d'aya da dawowa Rayhan yace Safna ta shirya suje su kaiwa doctor Amina ziyara,sannan aduba masa lafiyarta Dana abun da ke cikinta.

Cikin nishad'i da jin dad'i suke takawa a harabar asibitin zuwa office d'in doctor Amina,
Zaune take a office d'in,tana tunanin hanyar da zata sada ta da Rayhan, taji an matsa k'ararrawar Neman izinin shigowa.

Bata son kowa yazo inda take a halin yanzu,amma rashin sanin ko waye yasa ta bada izinin shigowa,a zatonta Mara lafiya aka kawo.

Shigowarsu office d'in yasa doctor mik'ewa a razane tana kallonsu, bakinta har rawa yake wajan ambatar sunanshi,
"Rayhan!!!"

Murmushi yayi gami da samun guri suka zauna,yace"surprise ko?"

A hankali doctor ta koma ta zauna bakin ta bud'e tana kallonsu kamar a mafarki.

"Doctor ya ayki,ya kuma akaji da jama'a,kin ganmu se yau"cewar Rayhan fuskarshi d'auke da murmushi.
.baki na rawa doctor tace"Alhamdulillahi Rayhan, na kusa haukacewa gurin neman ka"ta 'karasa maganar cikin damuwa.

Maida hankali shi yayi gunta sosai ya gyara zama sannan yace"da akayi ya ya doctor kike nemana?banganeba"

Glass d'in fuskarta ta cire sannan ta share hawayen da suka zubo mata,tace"matsala aka samu yayin gudanar da aykin dashen da aka yiwa safna"

A razane Rayhan da Safna suka d'ago ido suna kallonta,bakin safna har rawa yake tace"doctor wacce irin matsala kuma,?don Allah kimana bayani"

File d'in komai ta d'auko,sannan ta mikawa Rayhan da sauri ya fara dubawa,ita kuma taci gaba da masa bayani.

"Yayin gudanar da aykin aka samu matsalar sakamakon kamanceceniya ta suna da kuke dashi kai da Farhan, cikin dake jikin safna Rayhan ba naka bane na Farhan ne,kai kuma kwayoyinka da a kasa ma matarsa basu sa tayi cikin ba"daga haka de ta kwashe komai ta sanar dashi,gamida had'a hannayenta guri d'aya alamar Neman afuwar kuskuren da aka samun.

D'ago ido yayi yana kallon likitar cikin alamar rashin yadda da abinda tace, ganin hakane yasa doctor d'aukar Qur'anin dake gefenta,kasancewar tana da alwala tace cikin kuka"na rantse da duk wata gaskiya dake cikin wannan littafi me tsarki gaskiya na sanar daku"

Yanke jiki da safna tayi ta fad'ine yasa su waigowa gareta a razane sukai kanta suna kiran sunanta.

Da sauri doctor ta kira ma'aikata aka shigo da gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa zuwa wani d'akin inda doctor tashiga k'ok'arin ceto rayuwarta.

Rayhan samun Kansa yayi da kasa bin bayansu ya zube a office d'in doctor Aminar yana danasanin amincewa da yin dashen da yayi tun lokacin da aka bashi shawarar yin hakan,wannan wacce irin mummunar k'addara ce tabbas a matsayinsa na musulmi dole ya yarda da hakan.

Runtse idonsa yayi wasu zafafan hawaye suka shiga zubo masa,da ya rasa ta ya ze tsaidasu.

Yana nan zaune doctor ta shigo,tace"ta farfad'o,kai take son gani yanzu"

D'ago ido yayi ya kalli doctor d'in yace a sanyaye,"zanje gida in dawo ki ci gaba da kulawa da ita,"daga haka yasa hannu a aljihu ya d'auko kudi ya ajiyewa doctor d'in,sannan ya juya ya fice daga office d'in.

Cikin rashin fahimta doctor tabi bayansa da kallo har ya fice.


Muje zuwa


Surbajo for life.
11/14/21, 12:44 PM - MY MTN 2: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AURE DA HAIHUWA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*Zahra Surbajo*



*Gidan suna naje yau aymin uzuri*


*Page 11*



Jiki a sanyaye doctor ta koma gun Safna ta shaida mata ya fita amma yanzu ze dawo,
Sosai Safna tai mamakin tafiyar Rayhan batare daya zo yaga halin da take ciki ba,
Amma seta boye damuwarta,ta runtse ido tana hango rayuwar da zata yi da cikin da ba na mijinta ba agidan auranta.

A nashi bangaren Rayhan gida ya koma,yana shiga dakinsa ya shige ya kulle kansa aciki,fadawa kan gadonsa yayi sannan ya rushe da kuka tamkar karamin yaro.

Seda yaji kansa ya fara ciwo sannan ya yi shuru,yaso yaje yaga halin da Safna take ciki amma yakasa yin hakan sabida zafin da zuciyarshi ke masa.

Wasa wasa seda Safna ta kwashe sati guda a asibitin ba Rayhan ba dalilinsa,safna tayi kukan har ta godewa Allah, ko wayarshi ta kira be dauka,dole tasa doctor Yi mata allurar bacci akai akai,sabida gudun kar ta haifarwa kanta matsalar da zata shafi Dan dake cikinta.

Doctor ce ke jinyarta da kanta har zuwa ranar da ta warware.

Shigowa dakin doctor tayi fuskarta dauke da murmushi, take kallon Safna dake zaune gefen gadon tayi tagumi.

Karasowa tayi ta zame mata

Please Login or Register in order to submit comment