Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiyarta da tashi,dan in akwai matsala a maganceta tun da wuri.

Duk inda sukaje amsa ɗaya ce dukansu basa da kwan haihuwa,sede suyi haƙuri,bazasu taɓa haihuwa ba.

Tashin hankalin da Rayhan yake ciki yafi na lokacin auran Safna,rungume jameela yayi suna ta kuka gwanin ban tausayi,cikin kuka Rayhan ke faɗin"Ya Allah na karɓi laifina,ka bani a baya nayi butulci,ya Allah ka yafemin,nasan wannan hukunci ne daga gareka,Allah na tuba"yasake rushewa da kuka.

Kowa a family ɗinsu seda ya tausaya musu jin sakamakon nasu,ga Rayhan ya koma kamar wani taɓaɓɓe akan yara,na kowa so ike,yaran ƙannensa da kanshi yake binsu har gida yayi wasa dasu yakai musu tsaraba me tarin yawa.

Sosai yakeson ganin safna domin ya nemi yafiyarta.data ɗanta ,dan yasan hakkinsu ke bin sa.

*Bayan shekaru huɗu*

Safna ce ke tattakawa a lambun gidansu,yayin da Farhan ke tallafe da ita,sakamakom tsohon cikin da take ɗauke dashi haihuwa ko yau ko gobe.

Cikin yasamu ne asanda Farhan yagama fidda tsammanin ze sake haihuwa,kwatsam Allah ya nuna ƙarfin ikonsa akan hakan.

Ba farhan ba ita kanta Safna murna take da samun cikin,kulawa ta gidan duniya de wannan ciki yana ganinsa,dan har likitoci masu kulawa da cikin mahaifin Farhan ya turo gidan wanda ko yaushe suna gidan kulawa da me ciki.

In safna ta tuno lokacin cikin junior har kuka take,danshi sam besamu gata ba,amma wannan gatan har yayi yawa.

tun cikin na ƙarami ba abinda baa siya ba na haihuwa,ɗakuna biyu shaƙe suke da kayan yara na sawa dana wasa,kai abun se wanda yagani.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/27/21, 5:18 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*khadeeja Abdul tamasu soba,(labour GGASS T/WADAN DANKADAI 2011 CANDY) takatulu na gaisheki,ashafamin kan babana Muhammad,Allah bar mana zumunci amin amin*

*page 50*

Yau tun safe safna ke naƙuda,hankalin kowa yatashi na gidan,burinsu Allah ya sauketa,lafiya farhan ji yake kamar ya amshi ciwon.sabida firgicin daya ke ciki ko magana baya iyawa.

Bata haihu ba,se azahar bayan angama shawarar yimata cs,Allah yasa ta haihu da kanta.inda tasamu ƴan uku biyu maza se mace ɗaya,wayyo Allah zo kuga farinciki gun Farhan da iyayensa,ji suke safna tayi musu komai,

Rungumeta Farhan yayi ajikinshi hawaye na bin idonshi,cikin kuka yake faɗin"tunda na aureki safna komai nawa yasauya,ba abinda zansa hannuna akai bezamemin alkhairi ba,kin kawomin sauyi da dama arayuwata,safna ina miki son da ni kaina bansan adadinsa ba,aduk lokacin dana rasaki safna wallahi nima rayuwata tazo ƙarshe"

Da sauri ta ƙanƙameshi ajikinta,tana wasa da gashin kanshi,tace ahankali"Kadena faɗin haka mijina,nice kazamewa alkhairi,makarantu nawa ka gina? asibitoci nawa ka gina?,gidan marayu nawa ka gina? duka a ƙasata da ƙauyena,duk dan sabida ni,kafini komai amma kazaɓeni in zama matarka,Kasoni kaso komai nawa,ni me zancewa Allah in ban godeba,samunka a matsayin uban ƴaƴana alfarmace daga rabbana,ina tsananin ƙaunarka mijina"

Haɗe bakinsu yayi guri guda,kasancewar su kaɗaine a ɗakin,yaɗan samu natsuwa,sannan ya saketa.

Bayan mejego tayi wanka ta kimtsa,tuni aka yiwa yaran wanka,sannan aka miƙosu ga mahaifiyarsu domin susha nono.

Na biyun ta fara ba yasha ya ƙoshi sannan ta ɗauki ƙaramar itama ta bata tasha ta ƙoshi.

Rufe nonon tayi ta miƙe,da sauri Farhan shima ya miƙe riƙe da yaron na farkon yana kallonta yace"shi wannan me yayi da bazaki shayar dashi ba,?shi kika fara haifa amma kika ba sauran shi baki bashi ba?"

Murmushi tayi,ta shafe gefen fuskarsa tace cikin kirsa"taya zan shayar da ɗan da banawa ba?kaima kasan baze yiwuba"

Cikin rashin fahimta yace"Anya safna baki samu matsala ba kuwa, taya zaki haifosu su uku,kice ɗaya ba naki bane,to na waye in ba naki bane?"

Miƙa hannu tayi ta amshi yaron,sannan tace"zo muje kaga mahaifiyarsa"tana kaiwa nan ta juya ta fice daga ɓangaren nata rungume da yaron Farhan na bin ta abaya kamar bindi,

Sosai yayi mamakin ganin ta murɗa ƙofar falon shehnaz,ta shiga.

Koda suka shiga,sautin kukanta suka jiyo acan ciki ɗakinta,tana kuka tana faɗin"ya Allah ka azurtani da samun miji na nunawa ƙawa,amma kuma baka bani haihuwa ba,tsawon shekaru goma sha biyu da nayi da aure,ya Allah abokiyar zamana ita kabata haihuwa har kai mata ƙari,banyi fushi ba ya Allah ka sassautamin zafin kishina inje jikinta mu zauna lafiya ko renon yaran ne ta dunga bani,Allah kasanyayamin zuciyata"tasake rushewa da kuka,

Tsaye suke abakin ƙofar suna kallonta,idanuwan safna na zubar da kwalla sosai shehnaz tabata tausayi ganinta zaune kan abun sallah ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah.

A hankali safna ta taka ta isa gareta ta tsuguna agabanta sannan tasaka mata yaron akan hannunta,da sauri shehnaz ta buɗe idonta ta saukeshi akan safna,cikin rashim fahimta ta dubi hannunta,jinjiri,se faman tsotson hannunsa yake,kamar farhan yayi kakinsa sabida tsabar kamar da sukeyi.

Rungume yaron tayi da sauri ajikinta sannan ta dubi safna tana kuka tace"wallahi bazan cutar miki da yaranki ba don Allah ki barni ko renonsu ne in tayaki,wallahi ina matuƙar ƙaunarsu"ta sake rushewa da kuka.

Safna itama kukam take da kyar tace mata"ƴaƴanki ne kema,kinma fini iko dasu,wannan dana kawo miki,ba baki shi ne duniya da lahira,banaso ko bayan raina yasan cewa ni na haifeshi,shiyasa ko shayar dashi bantaɓa yiba,na baki ki shayar dashi,kuma ki zaɓa masa sunan da kike ganin yadace dashi"tana kaiwa nan ta miƙe ta fice daga ɗakin ,azabure shehnaz ta miƙe rungume da yaron,tayi kudu tayi arewa tayi gabas da yamma tama rasa inda zata.

Idonta ne yasauka kan farhan dake tsaye bakin ƙofa yana hawaye gami da murmushi akan fuskarsa.
Sabida tunda yake be taɓa ganin farinciki a tare da shehnaz irin na yau tunda ya aureta.

Allah yasani har gobe yana sonta,kuma beson abinda ze dameta sede itace taƙi kwantar da hankalinta,shiyasa shima yafita sabgarta.

Da gudu ta ƙarasa jikinshi ta rungumeshi shima rungumeta yayi,cikin kuka take faɗin"kai taka hurul inin tun aduniya aka fara baka ita,safna ƴar aljannace Farhan,wallahi ina sonta nima,ina sonta,ya Allah duk ranar da zuciyata ta ayyanamin in cuceta ko in cuci wani nata Allah kai gaggawar ɗaukar rayuwata kamin in aykata hakan"

Sosai take kuka tana kallon yaron da shima zuwa yanzu ita yake kallo dan kukan nata yafarkar dashi.

"nagodewa safna data samin NOOR ɗina cikin farin ciki"cewar farhan ya sumbaceta a goshi.

Yaronne ya fara kuka,agigice shehnaz ta zabura da gudu,ta sake dawowa da gudu gun Farhan wanda duk tausayinta ya gama kamashi,kamata yayi ya zaunar da ita gefen gado.

ƙin zama tayi tana faɗin"ina zan zauna yarona na kuka,ka faɗamin mezan mishi yayi shuru"

"nono yake so,kinga in baki zauna ba taya zaki bashi yasha?"cewar farhan cikin tausayawa.

A sanyaye ta zauna,ta riƙe yaron tana bin farhan da ido,sabida tunaninta taya zata bashi nono ita daba ruwan nonon gareta ba.

A hankali farhan ya ɓalle botir ɗin gaban rigarta,sannan yaciro nonon daga bra ɗinta,sannan ya gyara mata ruƙon yaron,sannan yadubeta yana murmushi yace "to maman baby abashi yasha"

Ɗan ran ƙwafawa tayi,nonon yazo dede setin bakin yaron ayko carab ya amsa yafara tsotsa.

Da sauri ta runtse ido hawaye na bin idonta na farinciki,tana faɗin "Ya Allah"

Duk da ba ruwa a nonon haka yay ta tsotsa.Safna ce ta dawo ɗakin ɗauke da magungunan dake sa ruwan nono zuwa koda baka taɓa haihuwa ba ta miƙawa farhan tana murmushi tace"yau fa ayki yasamu masu yinshi,to ga maganin ruwan nono nan,aba mejego,"

Gaba ɗaya suka tuntsure da dariya,ta juya ta fice daga ɗakin.

Magungunan yaba shehnaz tasha,sannan ya bar ɗakin,baayi awa biyu cikakke ba nonon yafara kawo ruwa sabida kyau da nagartar maganin.

Shehnaz ji take kamar tana aljanna,sanda taba yaron nonon taga yana zuwa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/28/21, 9:19 AM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*51*

Ɗakin safna ya nufa,yasamu ta fito daga toilet kenan,rungumeta yayi ajikinshi kamar wani ze ƙwace masa,yace"bazan iya miki godiya ba sede in miki addu'a Allah ya saka miki da mafificin alkha'iri,nagode sosai da wannan namijin ƙoƙari"

Rungumeshi itama tayi tana murmushi.

Huɗuba yayiwa yaran da sunan Mahaifansa macen da namijin,sannan yaje yayiwa na Shehnaz huɗubar shima da sunan Mahaifin Safna,suna kiransa musaddiq.

Kayan yaro yaɗan ɗiba aka kai part ɗin shehnaz kamin gari ya waye ya siyo masa nashi shima asa a ɓangaren shehnaz ɗin.

Gun safna ya koma yasata dole seta masa abinda ze ɗan samu sa'idar rashimta kusa dashi,ga jego ga soyayya abun se gurin su farhan.

Ya jima a ɓangaren safna kamin dare yayi ya koma sashin Shehnaz.

A can yaga bidiri gurin farim shigar uwa,dan fafur taƙi yarda Farhan ya hau mata kan gado,se tureshi take tana faɗin"Gadon yamana kaɗan,gaskiya kar aje gun bacci ka dannemin yaro,ni ka kima ɓangarenka kawai jego fa nakeyi"ta faɗi hankalinta kwance.

Dariya farhan yayi sannan yace"aymin afuwa bazan danneshi ba maman baby,abarni in kwanta duk na gaji."Ya langaɓe mata kai.
Da kyar ta amince ya hau gadon bayan ta kafa masa sharruɗa na kwana a gadon nata.

Sosai farhan abun ke bashi dariya,koda dare yayi ya buƙaci kwanciya da ita,tsalle tayi ta dire ita jego take yi,ɗanta beyi kwari ba,duk yadda farhan yaso fahimtar da ita ƙin fahimta tayi.dole ya ƙyaleta ya kwanta.

Har bacci ya ɗaukeshi ta ɗaka masa duka abaya,ya farka afirgice,a zaune take damfanfam riƙe da jinjirin,fidar yaron ta nuna masa akan madubi tace ya ɗan miƙo mata zata bashi ruwa😄

Haka badan yasoba ya miƙe yaje ya ɗauko mata ya kawo mata,yakoma yaci gaba da baccinsa me daɗi.

Cikin bacci yaji ta kuma ɗaka masa dukan,a firgice ya farka,wannan karon wiper akasa shi miƙowa akan madubin again😄

Kwanciya yakumayi yaci gaba da baccin,can cikin baccinsa yakuma jin ta ɗaka masa wani dukan,yana buɗe ido yace "mezan miƙo muku?"ya faɗi cikin takaici.

Murmushi tayi sannan tace"dama zan nuna maka murmushin da yake ne yana bacci,wallahi harda ɗan sauti murmushin"ta faɗin cike da nishaɗi.

Gwajab ya koma ya kwanta,ya lumshe ido,bece mata komai,ba haushi taji dan haka wani dukan ta sake kwaɗa masa tace"kai kaji haushi,kar ka kalla ɗin"😄

Ranar farhan seda yayi danasani tafi dubu na kwana a ɗakin na Shehnaz,dan in motsi yaron yayi seta tasheshi ta nuna masa,kan gari ya waye kuwa an sauya wa yaron kaya so uku,wai datti suke shiyasa take sauyawa.

Asubar fari Farhan ya fice a ɗakin idonsa cike da baccin da be samu damar yi ba

Muje zuwa

Surbajo for life
11/29/21, 1:15 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*52*

Shehnaz ko ko baccin ma bata ji,ita data kwana azaune.
Farhan be fito ba se misalin ƙarfe goma na safe,yayi wanka ya kimtsa,idanunsa har yanzu akwai ragowar kumburi na sauran bacci.

Ɗakin shehnaz ɗin yafara shiga,a tsaye take saɓe da ɗanta a kafaɗa tana ɗan masa waƙoƙi cikin harshen larabci,tana ganinshi tace"yauwa habibi jeka gun Safna kace ta baka soson wankan baby zan masa wanka,"

Dama yasan zaa rina ko gaisawa bata bari sunyi ba ta fara aykenshi.
Haka ya juya zuwa part ɗin safna yana mita.

Safna na ganinshi ta taso ta rungumeshi,fuskarta ɗauke da faraa.
Duban tsanaki tai masa sannan tace"Me kuma yafaru naganka da ido luhu luhu kamar fanke?"

Tsaki yayi sannan yace"nifa kin haɗani da jidali wallahi,ita bata huta ba nima bata barni na huta ba"daga haka ya kwashe bidirin da akayi jiya,amma banda ƙin yarda ya kusanceta sabida wannan sirrinsune,ya sanar da safna.

Safna dan dariya har ƙwarewa takeyi,farhan ne ya katseta da cewa"yanzuma aykoni tayi,tace kibada sabulu"

Dariyarce ta sake kubcewa safna wannan karon harda tari take dan dariya.

Haka ta ɗauko ta miƙa masa tace"to Abu musaddiq,agaida ummu musaddiq"

"zan kamaki ne"ya faɗi sanda ya fice daga ɗakin.

Inda ya barta nan ya sameta ya miƙa mata sabulun ya nufi kujera da niyar zama da sauri ta dakatar dashi da cewa.

"Habibi ina towel ɗin babyn fa?"

"sabulu kawai kikace"yabata amsa.

"to kai yaro ne da zakace sena lissafo komai,ay kasan akai wanka zaa tsane jiki,ni dan Allah kai sauri ka amso min"

Wayyo Farhan yaga takanshi,juyawa yayi yakoma gun safnar,yana buɗe ƙofar ya tsaya bece komai ba.

Dariya tayi sannan tace"Abu musaddiq me ummu musaddiq ɗin tace abaka?"

"towel"ya bata amsa agajarce.

Zuwa tayi ta ɗauko ta bashi tana gimtse dariya dan taga acike yake taf.

Yana zuwa yasamu ta cire masa pampers tun kan ya zauna ta miƙo masa yakai dustbin🤣

Bece komai ba ya amsa ya fice,basuyi aune ba sejin ƙarar motarshi sukayi ya fice daga gidan😄dan abun ya isheshi.

Banida caji ne se anjima zaku jini

Muje zuwa

Surbajo for life
11/29/21, 1:18 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Page 53*

A karo na farko da shehnaz da safna suka zauna guri guda suna hira har da dariya.
Zaune suke a babban falon gidan suna hira,bayan sallar la'asar.

Yaran kuma suna ɗaki suna bacci,shehnaz da ƙyar ta iya baro nata ɗan aɗakin,hankalinta gaba ɗaya yana gunshi.

Sallama Farhan yayi ya shigo falon,amsawa sukayi gamida masa sannu da zuwa,

Fuska a haɗe yaje ya nemi guri ya zauna,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana mazurai.itade safna tun shigowarshi takeson yin dariya take dannewa sarai farhan ya lura da ita amma se yayi kamar beganiba.

Shehnaz ce tace"yauwa habibi,ɗazu daka fita musaddiq..."ay be jira ta ƙarasa ba ya miƙe da sauri yabar falon,zuwa part ɗinshi,wato ita bata ma fahimci fushi yakeba,wani laifin ma take shirin ɗorawa.

Ganin ya bar gurin ne safna ma ta miƙe zuwa sashinta,shehnaz tafi kowa murna da watsewar dan ita kamar akan ƙaya take tafison zama kusa da ɗanta.

Farhan be sauraresu ba se tara na dare,ɗakin safna ya fara shiga.akan gado take yayin da Ayman da Aymana,ke baccinsu acikin gadajensu.

Dariya ta shiga ɓoyewa dan tana ganinshi dariyar ta taso mata.
Ayko kanta yayi ya wawurota,tsilli tsilli tayi da ido,
Hadeta yayi da jikinshi sannan yace"mahaukaci na koma ko,?shiyasa kikemin dariya,kinga baby wallahi ki fita idona in rufe"

Kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi,sannan ta sa masa kukan kirsa.
Kiɗimewa yayi yashiga rarrashinta,a ruɗe yace"kune kuka cajamin kaina yau,ita ta aykoni ke kisani agaba kina dariya,da wanne zanji "

Ƙara shiga jikinshi tayi tana kukan,taƙi magana.rasa yadda zeyi da ita yayi dan haka janta yayi suka kwanta agadon,yashiga ayka mata sakonni masu wiyar fassarawa.lib tayi ajikinshi,kuka ya ƙare,seda ya tabbatar ta ware sannan ya ƙyaleta,ya gyara kwanciyarshi akan gadon ya janyota jikinshi.

Ganin sha ɗaya na dare ta wuce ne yasa safna cewa"dare fa yayi Abban musaddiq,kaje tana jiranka"

"ay shehnaz in zan shekara ban jeba bazata damuba matuƙar musaddiq na tare da ita,kuma in naje wallahi bazata barni in runtsa ba,kawai ki barni in kwana anan,dan mu dama bamusan wani wai baa kwana ɗakin mejego ba se tayi arba'in"

Duk yadda safna taso yatafi ƙin yarda yayi dole ta ƙyaleshi.

A nan ya kwana baccinshi harda munshari,ita ko shehnaz rashin zuwan nashi sosai yay mata daɗi,dan ita yanzu a matsayin takura take kallon zuwanshi gunta,tafiso taganta ita kaɗai da babinta.

Haka rayuwarsu taci gaba da garawa cikin so da ƙaunar juna,

Yaran nada shekara guda,Farhan ya shirya musu tafiya zuwa nigeria,harda shehnaz da junior da Ayman da Aymana,da safna,da musaddiq ɗan gidan mummy kamar yadda suke masa kirari sabida son da shehnaz take nuna masa.

Tuni doctor Amina tayi booking na maaikata guda biyar ta turasu sabon gidan da farhan ya gina dominshi da iyalinsa a garin na Abuja,domin su fara gyaran gidan.

Safna tafi kowa murna da tafiyar kodan taje gun baffanta da dangin mahaifiyarta.

Da misalin ƙarfe bakwai na safuyar yau jirginsu ya ɗaga zuwa nigeria,

Muje zuwa

Surbajo for life.
11/29/21, 1:18 PM - Ummi Tandama😇: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Billy shantally tawa ni kaɗai,alharin Allah ya kai miki keda ahalinki baki ɗaya,ina ƙaunarki nima sosai,Allah ya barmu tare cikin aminci*

*Page 54*

Koda suka iso,doctor Amina suka samu tazo ɗaukarsu a danƙareriyar mota jeep babba,se motocin jamian tsaro daga gomnati,kasancewar Farhan yarima me jiran gadon mulki.

Doctor Amina rungume safna tayi tana kukan farincikin sauyin data gani tattare da safnar,dan yanzu gaba ɗaya ma hausarta ta koma kamar tame koyon hausar,dan tun zuwanta dubai inde ba waya zatayi dasu baffa ba to zata iya ƙirga hausa ko sau nawa tayita,sabida babu mejin yaren se ita kaɗai

Gidan su aka kaisu wanda ya gaji da haɗuwa,Bayan kowa yayi wanka ya kimtsa,sukaci abinci sannan doctor tai musu sallama kan gobe zata dawo,ay ga mamakin doctor tana fitowa wajen gidan motar Rayhan tagani a fake yayinda shi kuma yake tsaye yana jiran fitowarta.
Da kamar ta wuce shi amma seta tsaya ƙarasowa yayi da gudunshi.

Buɗe ƙofar tayi ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa.

"barka da safiya likita"cewar rayhan yana murmushi.

"barka de Rayhan,ya gari,me kakeyi anan ne?"doctor ta buƙata.

"Likita ke na biyo sabida naga tahowarku dasu Safna tundaga airport,naje raka iyalina zata umara,zan juyo naganku,shine na biyoku,don Allah doctor ki taimaka ki haɗani da safna da mijinta in nemi yafiyarsu badan ni ba doctor"ya ƙarasa maganar hawaye na bin kumatunsa.

Sosai tausayinshi yakama doctor,dan haka cewa tayi ya jirata,ita kuma ta juya cikin gidan.

Su safna sunyi mamakin ganin ta sabida ta musu sallama ta tafi.
Farhan ne ya dubeta yana murmushi,yayinda musaddiq ke kan ƙafarsa yana wasa yace"sarkin mantuwa me aka manta kuma?"

Ɗan yaƙe tayi sannan tace "kana da baƙo a ƙofar gida"

Sosai Farhan yayi mamakin maganar amma be kawo komai ba ya miƙe bayan ya sauke musaddiq ɗin yabi bayanta suka fita.

Besan Rayhan ba,dan haka be gane ko waye ba seda suka iso gabanshi,doctor tace"am very sorry ranka ya daɗe,wannan shine tsohon mijin safna wato rayhan"bata ƙarasa ba Annurin dake fuskar Farhan ya kauce,da sauri Rayhan ya zube agabanshi ya riƙe ƙafafunsa yana kuka yace"don Allah ku barni haka base kun hukuntaniba,Allah yagama muku sakayya tun tuni,gafararku nazo nema kaida matarka,bana nufinku da kowanne irin sharri"kukan dayaci ƙarfinsane yasa yakasa ci gaba da maganar.

Tausayinshine ya mamaye zuciyar farhan,hannu yasa ya kamoshi ya rungumeshi ajikinshi yana dukan bayansa alamun rarrashi.

Ganin kowa yazo shigewa kallonsu ake ne yasa yaja hannun Rayhan ɗin zuwa cikin gida,doctor na binsu abaya.

Kai tsaye falon gidan ya nufa dashi,bakunansu ɗauke da sallama,Azabure safna ta miƙe jikinta ɓari yake kamar ɗan mazari,tsorone ƙarara a fuskarta dan haka cikin kuka take faɗin"me kazo yi gurin mijina,me nayi maka,don Allah karka rusa min farincikin daban taɓa mafarkin samu ba,kabar rayuwata nima na jima da barin taka kamar yadda ɗa ke baro cikin mahaifiyarsa,ina ƙaunar mijina,wallahi ka zamo sanadin rabani dashi bazan yafe maka ba"Farhan ne ya ƙarasa inda take ya janyota jikinshi,ta kwantar da kanta a ƙirjinshi tana faɗin"baby banida alaƙa dashi,wallahi ban gayyatoshi nan ba"

Bayanta yake shafawa a hankali dan ya lura duk a firgice take,"calm down baby,ba wani abu ya kawoshi ba haƙuri yazo baki ki natsu pls"

Se a lokacin safna tasamu natsuwa,dan ita da tunaninta ɗan auran nata yazo ya girgiɗe mata.

Rayhan wanda kishin ganin safna ajikin wani ba shiba ya gama nuƙurƙusar zuciyarsa duƙawa yayi agabanta yace hawaye na bin idonshi.

"safna ki gafarceni,na cutar dake gashi cikin ruwan sanyi Allah na miki sakayya,nayi aure amna likitoci sun tabbatar mana da cewa daga ni har matata bazamu haihuba,sabida bamuda kwayoyin haihuwa,tun muna magani har mun haƙura,don Allah ku gafarceni ko zan samu sassauci azuciyata"

Farhan wani tausayin Rayhan dinne ya mamaye ko ina na jikinshi,tabbas rashin haihuwa,masiface dake hana bawa runtsawa,sabida shima yashiga wannan halin abaya shi kaɗai yasan ya yaji a lokacin.

"Nayafemaka duniya da lahira,Allah ya yafe mana baki ɗaya,haihuwa kuma ina muku adduar Allah ya baku"cewar safna.

Farhan kamo hannun ayman da aymana da junior yayi ya tsayar dasu gaban Rayhan,yace"wainnan ƴaƴanane da Safna ta haifa min,harda wancan( ya nuna musaddiq wanda shehnaz ta ɗauke abunta ta riƙe tunda taga ya fara kami yaran)a cikinsu ka ɗauki guda ɗaya na baka duniya da lahira"

A kiɗime Rayhan yake kallon Farhan,yanaso ya tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiyo masa.gyaɗa masa kai yayi gamida sake tura yaran gabanshi .

Rayhan bin kyawawan yaran yayi da kallo,hawaye na bin idonshi,a hankali ya ɗora hannunsa akan junior gami da jansa jikinshi ya rungume,shima junior ɗin rungumeshi yayi,yana faɗin "Abba kadena kuka,babba baya kuka inji ummina"cikin harshen turanci.

Ƙara rungumeshi yayi ajikinshi yana wani sabon kukan akaron farko ankirashi da sunan mahaifi saɓanin uncle daya saba ji abakin ƴaƴan kannensa dana abokansa.

"dama nakane,dan haka kaje da kayanka mun bar maka duniya da lahira,kaddarace ta gifta wacce kuma ta wuce"cewar farhan yana murmushi.

Rayhan kama ƙafar Farhan yayi yana kuka yakasa magana,ganin hakanne yasa Farhan ɗaukar junior ya miƙa masa yace"Tashi kuje Allah tayaka ruƙo"asanyaye ya miƙe ya ɗauki junior,wanda se farinciki yake ko alamun damuwa babu aranshi.bare ayi zaton zeyi kuka.

Koda ya ɗago ya dubi safna wacce ke kuka,bece komai ba illa haɗa hannayensa dayayi guri guda alamun godiya.

Haka ya fice ɗauke da junior ajikinshi,doctor Amina na binsa a baya.

faɗawa kan kujera safna tayi ta rushe da kuka me tsuma zuciya,Allah ne kaɗai yasan son da takewa junior,gashi yanzi anrabasu.

Shikanshi Farhan ɗin dauriya yayi dan kaf ƴaƴansa yafison junior,amma dama haka Allah tace in zakayi kyauta kayi da abunda kafi so.

Ɗaukarta yayi cak suka wuce ɗaki,tana rusa masa kuka,shehnaz kanta tausayin safnar taji,dan haka jan ayman da aymana da musaddiq tayi suka wuce nata ɗakin.

ɗakinshi ya nufa da ita,se cigaba take da kuka tana kiran junior ɗinta.

Akan gado ya ajiyeta sannan shima yahau gadon ya janyota jikinshi yayi mata rungumar da zatayi shuru dan kanta,ayko baa jima ba tayi shuru ta koma se lumshe ido take,a hankali ya dubeta yace"Allah ya miki baywa ta koina,mw isa akan ƙaramin abu zaki tashi hankalinki,nasan Rayhan baze taɓa cutar miki da ɗa ba to meye abun kukan,ni kinma bani kunya,ke da nakewa kallon jaruma ta"ya ƙarasa maganar yana lakace mata hanci.

"to ni baby ay kyautar ce kayi bakayi shawara dani ba"tayi maganar a ashagwaɓance.

"sanda kika kyautar da musaddiq shawara kikayi dani?"ya tambaya yana ƙoƙarin zuge zif ɗin rigarta.

Murmushi tayi bata bashi amsa ba ta koma ta kwanta akan gadon ta sakar masa linzamin.

Cire rigar yayi,ya janyota jikinshi ya shiga shafa boobs ɗinta ta gefe,yayinda ya manna bakinshi akansu,yashiga surcking ɗinsu,ba tun yau ba ta hanashi ganin shayarwa take amma fafur yaƙi denawa.

Hannu yakai can ƙasan marar ta ya shiga ayka mata sako me wiyar fassara,safna kukan daɗi tasa mishi a haka tashiga rage masa kayan jikinshi,itama sakon tafara tura masa ta hanyar kamo joy stick ɗinsa tana ɗan mulmulawa,gamida pressing,gaba ɗaya ta birkita masa lissafi,kamar yadda shima ya birkita nata,shi kuka ita kuka ahaka ya cilla kwallonsa araga.

Basu samu natsuwa ba seda suka kwashe awa guda da rabi suna abu ɗaya,dan Farhan akwai dogon zango,tun safna na raki har ya koyar da ita ta saba.

Kwanansu biyu da zuwa suka nufi ƙauyen sara.

Babu wanda beyi murna da zuwanta ba,har matan babanta,kowa nan nan yake dasu,
Baffa har kuka yayi da ganin safnar wacce tazamo silar arziƙinsa.

Babu inda basu zaga ba adangin na safna,kyaututtuka suka rabawa kowa,ga maƙudan kuɗaɗe da suka rabawa jamaar gari,kowa se son barka.

Satinsu guda suka koma Abuja cike da kewar juna,dan maimuna da kuka suka rabu da safnar.

Rayhan kusan kullum seya kawo junior,amma abun mamaki shi junior ɗin beson zuwa,yafison yakaishi gurin iyayen shi Rayhan ɗin.

Iyayen Rayhan da ƴan uwansa har gida sukazo sukayiwa Safna godiya da Farhan.
Zumuncine ya ƙullu atsakaninsu,ranar da jameela ta dawo daga umara tasamu labarin sunyi ɗa har suma seda tayi dan farinciki.

Har gida yakaita tayi musu godiya.

Rayhan da jamila ko ƙuda basa so ya taɓa junior,in kana ƙaunar ɓacin ransu to kataɓashi,ko office Rayhan yaje be iya zama har yatashi be dawo gida yaga junior ba sannan ya koma.

Watan su safna biyu a nigeria suka koma dubai,safna ɗauke da ɗan ƙaramin cikinta,wanda farhan ya ɗauki son duniya ya ɗora masa kamar baa taɓa masa haihuwa ba.

Ayman da Aymana kuwa gidan iyayen Farhan ɗin aka kaisu,dama sosai suka ji ɗacin kyautar musu da junior da yayi.

To muma Anan muna fatan Allah yasauki safna lafiya da sauran mata masu ciki amin summa ammin.

*ALHAMDULILLAHI*

A nan wannan littafi na AURE DA HAIHUWA ya kawo ƙarshe,
Darasin dake ciki Allah bamu ikon ayki dashi.

Kuskuren dake ciki Allah yabamu ikon gujewa aykatashi.

mu kasance tare cikin sabon littafina me suna TAYI MIN ƘAƘANTA dan ganin wainar da ake toyawa.

Taku har kullum

Zahra Surbajo.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne

Please Login or Register in order to submit comment