Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ta ƙare a gidan yari ba batun cin ma muradin rayuwa.....

yan zu a ƙasar nan ilimi na nema yafi karfin takala ga matsin rayuwa takai ta kawo yanzu zaka ji fara shi in anjima ya tashi ga man fetur din nan a ƙasar mu ake haƙoshi amma yana nema yafi karfin talakawa hutar lantarki daman ba'a maganar'ta......yan handama da baba kere sunyi oder sola suna so ta tafi in da tsayuwar huta ba batun siyan huta me amfani da hasken rana.....

ganin wayan nan ire-iren tunanin za suyi mai yawa ya fara neman ɗauki gurin Ubangiji yana tasbihi belt ya saka sakamakon ji dayayi an sanar jirgi zai tashi a hali jirginsu ya fata tafiya har ya ɗaga sama.........

Unguwar kofar mata*

Ashe gida rahama ne tab ai sai yau na tabbatar da haka dinana da nayi bacci cikin kwanciyar hankali kai Allah ya sakama mana nifa ba fuskar da na tsana a duniya sama da wannan me kama da bishiya


Dariya dinana yayi yace

"Yanzu dai besan kina yi ba tawo muje in raka ki Abuja sai ki faɗa mai.....,

Banza tayi mai rabi ne ya sheƙe da dariya yace

"Na'rantsai da Allah da kuwa in ta shiga ba zata fito ba sai sun ya galgala naman ta ai ni a gurin na gane Ni dan iskan karya ne ina washe garin mu ka kwana kana ga zuwa yayi cikin wannan cel din da ke kallo mu ya harbe wani....,

zaro ido magajiya tayi tace

"Kace har kisa yana yi haba shi yasaka Ubangiji ya ɗauke mai rahamar fuskarsa ba rahama a fuskar sa ko ɗaya nifa daman can baya burge Ni mutane suyi ta yaban'sa ai shi adalin shugabane.....,

Magajiya nifa nayi mafarki mun sha biki ya aure ki dinana ya faɗa yana danne dariyar'sa

Wainar da ta zuba mai ita ta fara ƙoƙarin juyewa da sauri ya saka hannu ya ɗauka yace

"Ya kyauta da zobe...?,

harara ta watsai mai kahu da yake zaune yana jin su yace

"Allah ne ya rufab asiri da tuni dani za a kama..,

Allah ya rufa maka asiri kahu bulama da kaga baƙin tashin hankali wallahi baka da rabon fige kazar hawala da ka dauki darasi mai girma.....

Hmmm Allah ne ya fidda a'e daga rogo

Dariya dukkan su suka saka ban da magajiya da tun da abin da dinana ya faɗi ya ɗauke mata annurin fuskarta

Radio ya ware kamar kullum domin jin labaran duniya ya tarar ma har an kusan gamawa sai karashe A wata majiya me karfi a yau ne shugaban hukumar Dass zai kawo ziyarar ba zata kano in zai taya gwamnan jihar Kano buɗe sababbin aikin da yayi.....
Garin nan ya cika da masoyan sa domin tarbar'sa duk da be sanar da zuwan'sa ba a safiyar ranar Laraba ne aka kai mai hari gidansa da ke Abuja osokoro ya fito yayi kyakkyawan martani in da ya zargi manyan kasar nan da sahun'su akai mai hari duba da ce wa duk tsaron dake abuja har akawo mai hari ba tare da an kama ko da ɗaya daga cikin su ne...

Inda ya kara da cewa indai akan yaƙi da masu mugun laifi ne saidai a kashe shi yasan ya tafi akan hanya me kyau

da sauri magajiya ta kashe Radio tace

"Haba kahu yanzu abin da mutumin nan yayi mana be baka baƙin ciki ba har ka tsaya jinsa daman sun fasa kan shege kowa ma ya huta....,

karɓar Radio sa yayi yace

"Yau nake ganin ikon Allah Ni nasaka su suyi maganar nan falmata.....? Baki ga mutuncin da mutumin nan yayi mana ba motar sa ya bayar a kawo mu...,

Juyawa tayi ba tare da tace mai kala ba sajan bala ne ya shigo shi da kufur Musa washe baki magajiya tayi tace

"Yau jami'an doka ne a gidan nawa....,


Gujera suka samu suka zauna kufur musa yace


"Munji kin dawo ai dole mu zo jaje kullum sajan bala kwana yake baya bacci masoyiyar sa na hannun wayan nan mutane....,

da hallacan rufe min baki bindiga ce a hannun su bindiga ce a hannunku me saka da kuka ji haka baku zo ba kun karɓo mu ai wallahi sajan bala yanzu na gane ko na aure ka baza ka iya kwato min yanci ba me isaka ba zaka kai su kara ba ai naga kai ma kakine jikin ka duk kan ku matsayi ɗaya gare ku a son da nake maka yanzu ko rabi babu...


Haba sweet a gaban wa'yannan yan hana ruwa gudu kike maganar nan ai sai suyi dariya kalle ki zukekiyar mace in narasa ki ai na shiga wani hali

Wata uwar buɗa rabi ya saki yace

"Chasss anayi muna jin dadi kai ashe zan ga wannan rana....,

Sakar baki su kufur sukai sajan bala yace

"Kai Wa kake wa wannan maganar...,

kama ƙigiya yayi ya kauda kai yace

"Da wanda ya tsargu.....,

lallai so kake kayi kwanan cel

Dariya ya sheƙe da'ita yace

"aini yanzu nafi karfin cel KO kaman ta inda naje dinana kora mai bayani ai wallahi yanzu bana kallon ku a matsayin wasu jami'an tsaro malam jeka Abuja kaga yadda ake jami'an tsaro....ba irin kuba yan kuci ku bamu....,

Wata uwar buda aka saki da sauri suka bada attention domin ganin wazai shigo ɗaga labulan buhun da suka saka suka rufe kofar su ashe shagari ne yaci uban dauri ka kamar gwaggwaro baƙin nan yaci jambaki sai sheƙi yake.....

Jar'uban can sweet rabi ke nake gani ko gizo idona ke min ta masar ya faɗa yana taɓe baki yawa yaga kashi


ta uwar yan sa ido nice dai kema wallahi baki haɗu da gamon ki ba da duk wa'yan nan hannayen'ki da kike shanyawa yawa ganyen da ake so ya bushe tuni zaki dawo da shi dai-dai

buga cinya yayi ya gyara ɗaurin zanin'sa yace

"Allah ya rufa min asiri ba dani kukai harƙallar kuba da tuni dani za aci wannan kwakwar ta huya.....,

Dinana ne yace

"Ai ta masar munga tashin hankali mabayyani ke cikina har wani karta min yake saboda tashin hankali....na rasa inda zan saka kaina..inji dadi...,

Kama haɓa ta masar tayi tace

"Kuce sunci ubanku la'ada waje....,

ɗaya kenan magajiya ta bashi amsa

kujera ya samu ya zauna nan fa labari ya barƙe tsakanin su kahu ma ya bada nasa labarin.....

*Aminu kano international airport*

A hankali yake taka matattakalar jirgin yake sauko wa yayin da akwai motoci wa'yanda suke jiran'sa tuni yan jaridu suka fara ɗaukan sa ƙara saukowa yayi tuni bodyguard suka rufa mai baya yana gaba suna binsa abaya da sauri jidda ta ƙwalawa hajiya kira tace

"Hajiya yaya yazo kano zo ki gansa....,

Ke bana son rashin arziki in nazo naga ba haka ba Alkur'an uwar'ki halima sai ta sani.... domin ba dama ku ga mutum a kwance sai kun kirkiri abin da zai saka ya tashi...✍️


*Kuyi hakuri da wannan ba yawa*

*GIDAN MAGAJIYA*

EPISODE 33-34

Tashi jidda tayi zata fita ganin hajiya na neman karyata ta bayan ta gani da idon'ta karo suka ci da ya akram da sauri ta ja baya tace

"Kai hakuri ban kula ba...,

Shigo wa yayi ya zauna cikin haɗe girar sama da ta ƙasa yace"yau she zaki kula tun da ba hakan kika saka a ranki ba...,

Innalillahi ga mala'ikan yara na biyu yazo wato kai dai akram wallahi baka da kirki kai kenan kullum faɗa da yara to bazan lamin'ta ba tunda bakai ka haifar min ita ba ko uwar da ta haifi jidda naga ta saka mata ƙawon zuƙa irin na ka tun zan mata wankin babban bargo ko da yake kai fa dan gidan jummai Dubai in bakai ba ai Allah ya tambaye ka kaf cikin yan uwan mahaifiyar ku ita ka ɗai ce me sanyi sauran daga Attahiru sai hita jummai Dubai kuwa ai ita transformer CE ta fito tana gyara zanin ta tana faɗar haka

ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yayi yace

"Hajiya duk wannan abin da kike basu san kina yi ba Bara in kira miki aunty jummai ita ce dai-dai dake wallahi....,

Dun gurai mai kai tayi tace "ja'iri ce maka akai ina tsoron jummai Dubai ai wallahi yawon siyasa kaɗai zata nuna min amma ba dai iya faɗa ba kai wai fa a haka zamanin mu yayi sanyi da kai karya kake ka faɗa min zaka kirawo min jummai Dubai wace ita wace ita a siyasar Sardauna fa shugaban ƙasa ya riƙe irin nada ba na yanzu ba kuma a mulkin soja nan da kawai ɗorawa ake an zaɓa ko ba a zaɓa ba abin da sukai niya shi sukai na goga da manyan mutane Akram share hawaye tayi tace

"Allah ya jikan Sardauna yasa can tafi nan kaga komai nasa Asif ya dauko har jan halinsa Asif na da shekaru goma sha biyar ya mutu muka baro Lagos muka dawo nan da zama kasan fa Asif ni na raine shi saboda mahaifiyar ku wallahi shashashar uwa ce tana fa jin naƙudar sa amma tana zaune ita da Maryam ita ma wata kashu in ba kashu ba tafa girmi Fatima ai zata iya fuskantar wannan hali take ciki...ko

zama tayi domin ta ji daɗin bada labarin tuni daman jidda ta fita ta ci gaba da cewa ina baka labari dai suna zaune sai da ciwo yaci karfin'ta dariya ta sheƙe da ita tace

To naƙuda kanwar uwar'ta ce harira fara share hawaye marayam tana ta zuba ni daman banyi tunain ma zata iya haihuwa da kan'ta ba domin har madarar yara na tanada tun da naga alamun cikin bafa ta ba ri ana ganin girman cikin kullum cikin hijabi kai abu yakai abu ta fara kuka haka maryam ta sanar dani da sauri na fito daman bacci naƙe da ido ɗaya.....

Samin ta nayi a lokacin mafaya ma ta fashe kan ɗa yana kokarin tawowa da sauri na ɗagata nanuna Mata yadda za tayi yar banzan nan har da dogon wando a jikin'ta uban wace mata ciki in ya tsofa ana sa wando haka naci re mata shi cikin ikon Allah sai ga Asif a tafin hannuna ya duro Ni na saka mai ASIF nakuma hana a can za mai suna tunda Sunan Alhaji ya ɓata kowa sardauna shine ya maye gurbin sunan......

Kai in takaice maka dogon labari domin sai mu kwana munayi mahaifiyar ka tun da ta haifi Asif bata fiye bashi abinci ba da ya fara neman lalacewa tuni na dawo dashi gurina nake kula da shi har ya girma na saka shi a makarantar sai ta haife ka tare sukai haihu da matar kahun ka mamy kuke ce mata Kowa rana ɗaya kai da Ayman ita daman izzatu juya ce sai wayan nan sauran yaran suka biyo baya su inteesar jidda fa'iza basma mudai asalin mu yan kasar nijiyar ne buzaye ne daga ni har mahaifin ku zama ya kawo iyayen mu kano muka kafa tushe me girma mun taso da arzikin mu babban sojane sardauna Asif Hammad shine a salin sunan sardauna amma mutane da dama ko azamanin da yayi soja A sardauna ake ce mai.........mun yi rayuwa me dad'i ba faɗa ya rayu cikin iyalansa da ya'yan'sa ya ga wasu daga cikin jikokin'sa sannan Allah yayi mai rasuwa sanadiyar ciki me tsanani Allah ya jikansa da rahama

kamar ance ta ɗago ashe duk surutun da take earphone ne a kunnan'sa pillow case ta ɗauko ta maka mai cikin faɗa tace

"Zaka ci kaniyar'ka akram ni zaka maida Radio ka saka wa'yannan abubuwan ka toshe kunnan ka ina baka labarin rayuwar ku...,

Cire earphone yayi yace

"Haba hajiya ba ina jin kiba baki ji nace amin ba..,

zo ka fitar min a gidan uwar...ka fatima kace amin ɗin yanzu ana tambayar tarihin rayuwar ka wallahi waɗuwa zakai domin baka sani ba dan nema zo ka fitar min duk ɗuwawun ku ya goge min yadin kujera ni'anya kuwa ba tusar da kuke min a kujera ba take koɗar min da yadi nidai ba arana sukai ba amma jiyar da suka koɗe to yau kaje ka siyomin wasu Turkiyya nake so kuma.....


Assalamu alaika da sauri ta ɗago jin muryar da baza ta taɓa mantawa da ita ba komai shekarun da ta ɗauka bata ji muryar ba tace

"Wa'alaikassalam Sardauna kai ne ashe gaskiyar jidda da tace ta ganna Ka a TV..... Sannu da zowa me gidana...?,

Ƙara sowa yayi ya cire takalmin'sa ya zauna gaishe shi ta yayi zama tayi ta amsa yaya ina huni kazo lafiya

Cikin mamaki ya kalli Akram yace

"Lafiya qalau daman kana nan....?,

Dan sosa ƙeya yayi yace

"Eh wallahi sai yau zamu tafi nida Faisal da Ayman...,

Kai ya gyaɗa yace

"Yayi muku..kyau...,

tashi yayi zai fita hajiya ta riƙo kafar'sa tace

"Munafukan banza sai da nace zan fada maka suka ce ka sani shi kuwa daman wancan rasa kunyar ba'a magana da ashar ya shigo gidan nan an rufe mai gida yar gold ta hana shi shiga ya tafi guesthouse ya zauna....na kirata na ci mata mutunci shegiya yar gidan fakirai jikan nawa za tayi hawa haka kai ma ina ciki da kai ina maganar auran da nace kayi in baka samu ba zan wanke maka jidda na kawo maka..ita....,

da sauri Akram ya jiyu zuciyar'sa na tsananin bugu haka Asif da har cire glass yayi yace

"Jidda kuma hajiya....?,

Wallahi tas zata zauna in da rabo ma saidai ka wayi gari ka ganta da ciki ai ita mace bata kaɗan ba'a raina'ta ta faɗa tana cika kafar Akram da kyar ya iya ɗaga ƙafa ya fita gyara zama Asif yayi yace

"Maganar da ta kawo ni kenan na samu amma sai mun ɗan ƙara fahimtar juna gudun samin matsala sai in fada miki...,

yayi haka ne domin ya kaucewa maganar hajiya me zai yi da jidda kanwar kanwar shi washe baki tayi tace

"A ina take....?,

tsintar baƙin'sa yayi ya furta Maiduguri bawai dan ya shirya faɗar haka ba tamkar sunan daga kasan zuciyarsa ya fito kamar daman yana kwance a zuciyarsa jiran maganar ya ke ya furta

Masha Allah Masha Allah kace shuwa zaka ɗauko mana....?,

kai ya gyaɗa haɗa rai tayi tace

"To kaɗan gare ka fara gyaɗa kai magana nace kai min bance kai min zancen kurame ba....,

shiru yayi mata be ce mata komai ba dauko wayarsa yayi yana danna wa kiran A'isha ne ya shigo be ɗaga ba haka ta dinga kira hajiya na zaune tana kallon ikon Allah can tace mai kana jii wayarka na ringing kaƙi dauka ashe daman kana sane kake ƙin dauka sai kace wai aiki ne yayi maka yawa sannu saƙago wanda baya hutawa....


tashi yayi ya ciro damin kuɗi ya ajiye mata a gaban'ta yace

"Zan shiga ciki mu gaisa....,

dauka tayi tana shi mai albarka ya fita wajan mamy ya fara shiga jidda yake zaune ta tashi tace

"Yaya sannu da zuwa....?,

yauwa yace ya zauna mamy ce ta fito tana washe baki matar uncle hamza tace

"Yau babban mutum ne a gidan namu...,

Murmushi yayi yace

"Ina huni na same Ku lafiya...?,

Zama taji a hannun kujera tace

"Lafiya qalau alhmdllh ya A'ishah yi ce ko tana lafiya...qalau,,

Alhmdllh lafiya qalau jidda ce ta dawo da tiry a hannun'ta ajiye mai tayi a gabansa ajiye kuɗi yayi yace sai an jima

Da sauri mamy tace "badai tafiya zakai ba ba abin da ka saka a bakin ka...?,

Eh wallahi Nagode ya faɗa yana miƙo mata kuɗi amsa tayi tayi mai godiya da fatan gamawa da duniya lafiya amsawa yayi da amin tun kafin ya shigo labari yajewa Hajiya jamila zuwansa dan haka tuni tafara ƙoƙarin aiwatar da shirinta saidai ta nemi maganin ta rasa sosai take neman inda ta saka amma ina nema take tana cikin nema taji sallamar sa duk A.C da take aiki a dakin nata amma ta jiƙe sharkaf da gumi fitowa tayi tana zare ido tace


"a'a dan albarka ne a gidan namu...?,

sam matar jinin'sa be haɗu da ita ba dan yaƙe yayi yace

"Na same Ku lafiya...,

Hhh eh wallahi lafiya qalau ya hanya

Alhmdllh kuɗi ya miƙo mata amsa tayi tace

"Badai tafiya zakai ba ko wani abu baka sha ba....?,

tashi yayi yace "nagode ya saka kai ya huce.....,

dafe Kai tayi tana baƙin cikin rashin ganin wannan magani malamin ta yace shi ake kira da ƙare magana tana saka mai sai ya hauka ce......

*_Allah ka saka mufi karfin zuciyar mu_*

`Amin ya Allah`

Shashin izzatu ya nufa saidai tana kokarin fita kamar kullum dai waya take mayafin'ta na kafaɗa jin kamshin turarensa da baya ɓoya ta ɗago gyara annurin fuskarta tayi ta cire waya a kunne tace.......

"A'a Asif kai ne a garin namu...?,

takaici ne ya ishe shi me hali baya fasa hali daman abba zai gane ya sama mata aiki da yawon banzan nan da take tunda bazai iya hanata ba yace


"Eh na same kula lafiya....,

Lafiya qalau alhmdllh gashi ka same Ni zan tafi asibiti kanwar kawata aka kwantar a international wallahi ba abin da batayi min ba wannan kawar tawa shine ba wanda zai zaunar mata da rana sai Ni...

Allah ya bata lafiya

Amin tace tana kallon aljihun'sa da yake kokarin fito da ƙuɗi fito da su yayi ya miƙa mata da sauri ta amsa tana kirgawa tace

"Hhh kace yau in fita jaka'ta da nauyi kasan yanzu mahaifin naka yayi ritaya sai kana dan temakawa saboda haka yanzu nake neman jari da zan dinga juyawa kafin pension dinsa ya fito abubuwan sai hakuri sun canza....,

Okay zan duba ya faɗa yana shige ta gyara mayafin tayi tace

"Kar ma ka duba me fuskar shanu...kawa nitsaya mutum tamkar bishiya kamar arzikin ka ace ka bani dubu hamsin wacce bata huce kwandala ba a gurin ka..,

jaka ta rayata ya tafi tana mita yawa wanda yayi mata dole ta amsa...

Da sallama ya shiga shashin mahaifiyar tasa da sauri inteesar ta fito daga kitchen tace

"Wa'alaikassalam yaya sannu da zowa ina aunty Aisha....,

Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun alfarmar dake floor yace

"Yauwa ina umma...?,

tana sama bara in kirawo ta kafin ta rufe baki sai ga umma ta fito cikin wani hadaddan swiss lace blue black da adon flower golding Sai zabga ƙamshi take abin ka da jikin fulani ba zaka ce ta haifi Asif ba hannayen'ta sunci jan kunshi ga sarƙar gold a huyanta da hannunta ƙarasa saukowa tayi da sauri ya sauko ƙasa yace

"Ina huni....,

Zama tayi tace

"Lafiya lau kunzo lafiya...,

da sauri ya ɗago yace

"Lafiya qalau ni kaɗai nazo....,

bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen bata dade ba ta dawo jera kayan da ta dauko tayi akan dinning table tace

"bisimallah kaci sa'a yanzun nan na gama abincin rana ....,

ba musu ba ya tashi buɗe flask din Dan gidan voccum lafiyayyan alkubus ne buɗe na miyar yayi vegetable soup ce kamshine ya daki hancin'sa zubawa yayi daidai yadda yasan zai iya ci ya fara ci ƙarawa yayi ga kunun aya yaji kayan haɗi ga sanyi haka ya din ga cii......text ne ya shigo wayar sa buɗawa yayi na aysha ne tace

"Asif kana daukan magana ta kamar wasa a da naso auran Ka amma a yanzu bana so ana dole ne ka sake Ni na wallahi na shirya tsab duk da a bin da kake taƙama na fika....juya kawai..zan je in auri me haihuwa irina

gogewa yayi ya ajiye wayar'sa ajiyar zuciya ya sauke in aka ce mai A'isha zata aika ta mai haka tofa zai ƙaryata.....

*Littafin nan A 50 zan gama book 2 domin payment din book 3 zaka iya biyan ta wannan account din*

*8141785374 Amina Alhasan muhammand opay ₦500*

*Ka turo da shaida ta nan 09061890481*

*dan girman Allah in Baka shirya ba kar kayi min magana*


*GIDAN MAGAJIYA*

(Oum-yasmeen)

*I'm not worried about insulting you the rooster that Allah intended to fight with, even if he is being bullied, he will do it......*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


EPISODE 35-36

Book 2


Zai karyata hakan amma abin da ya lura kamar akwai wanda yake daga gefe yana zugata to waye....? bashi da me bashi amsa tissue ya dauka ya goge baƙin sa saki gyatsa tashi yayi dai-dai da fitowar umma huce shi za tayi yace

"Na gama zan tafi...,

Kallon'sa tayi tace

"To Allah ya kiyaye hanya..,

ba Abuja zan koma ba zan dan jima anan zan tafi dakina ne

Shiru tayi tana nazari tukunna ta kalli ɗan'nata cikin tausayawa be yi sa'ar mata ba ko lokacin da yace zai aure Ita dai cewa tayi Allah ya sanya alkairi dan sautari tasha kama shi yana yiwa kansa Allura ta rage feeling ta hanashi ya koma shan magani irin su Asif ba'a so su jima ba tare da mace ba....dan akwai wani ciwon ciki da yayi yawa ya mutu ajiyar zuciya ta sauke tace

"to... Allah ya kai mu lokacin tafiyar taka..,

Amin yace fito da kudi yayi aljihunsa ya miƙa mata amsa tayi ta sanya masa albarka wani sanyiyaji ya ratsa fita samin hajiya yayi tana zaune tana kallo ga jidda a gefen'ta sannu da zuwa tayi mai hajiya tace

"Ga abincin ka na saka jidda ta dafa maka danni yau banyi niyar cin abinci ba.....,

naci ya faɗa a takaice haɗa rai hajiya tayi tace

"Wannan fa da nasaka aka girka maka...?,

cikin gajiya da maganar da Hajiya ke saka shi yi tunda yazo yace

"Hajiya nafa ƙoshi....,

fita yayi yabi ta wata karamar kofa dake kallon wajan dining din turawa yayi ta buɗe corridor ne da yar baranda an ƙawata shi da flowers masu kyau har wani kamshi suke fiddawa ta cikin baranda ya shiga wani waje ga wata ƙatuwar glass door turata yayi tuni ta buɗe wani haddadan floor ne me kyau da tsaruwa dafa kansa yayi lokacin da ya tuna be fito da briefcase dinsa ba tana mota mutane sun gajiyar da shi tun da ya sauka ya huce government House sai da aka gama taron ya dawo haɗi da buɗe wani sabo. Aiki da gwamnar yayi na gina sabuwar gada wayar sa ya dauko ya kirawo Akram bugu ɗaya ya dauka cikin bada umarni yace


"Akram kazo dakina ka karbi key ka ɗauko min briefcase dina a cikin mota...,

Cikin girmamawa yace"to....,

Kashe wayar yayi yana kallon ko ina na dakin yana tuna rayuwar'sa ta yarinta sallamar Akram ce ta dawo dashi da ga dogon tunanin da ya waɗa ɗagowa yayi ya amsa ya mi ƙamai mukullin amsa yayi ya juya be wani ɗauki dogon lokaci ba sai gashi ya kawo mai amsa yayi ya ajiye yace

"Thanks...,

kasa kasa yawa me ciwon baki indai halin yaya ne inda sabo sun saba shi haka yake tashi yayi ya kulle bedroom ya shiga sai kamshi yake zabgawa da sauri ya fito..... yace

"Hajiya badai yaran nan ne ba suke gyara min ɗaki....?,

Wannan yaron ne Ubanka ne kabiru ke gyarawa ta bashi amsa a gatsai domin dazu ya ɓata mata rai da yaƙi cin abinci.....

komawa yayi ba tare da yace komai ba dan yasan yace zai biyewa Hajiya akwai matsala ita haka take so..

bedroom ya shiga ya fara cire kayan sa daga shi sai boxer ya shiga toilet cire boxer yayi sakarwa kansa shower limshe idanuwan'sa yayi da sauri ya buɗe sakamaƙon ganin fuskar falma'ta tanayi mai gizo......

Sauri yayi ya gama wankan Saboda ya tara gajiya yana fitowa kaya kawai ya ja blanket addu'a yayi sannan ya ƙarasa lulluɓa ya kwanta na dade'wa bacci yayi awan gaba da shi........

`Unguwar kofar mata`


Ina magajiya take da sauri magajiya ta ɗago ta kalli kofa wata mata ce da dattijuwar mace kallo ɗaya tayi musu tasan bada arziki suka zo ba tace


"Gani ko naci ban biya ba....?,

Ƙarasa shugowa sukai matar tace mata ke saurara tsohuwar kilaki zuwa mukai in ja miki kunne akan mijina

tashi magajiya tayi ta sheƙe da dariya tace

"Baki ƙarya ba danni nan da kika ganni tatatciyar yar iska ce duk da abin da kike zo dashi tofa ki shafa fatiha kin'samu dai-dai da kugunki......,


Ba shakka mama kinga ko ashe labarin da aka bamu zan zo na tarar da haka

tafi magajiya tayi tace

"Gaskiya tsohuwa sun cuce ku basu baku daidai ba....,

Salati tsohuwar nan ta saki tace

"Bilkisu bala ya dauko miki ruwan dafa kanki...,

Sai yanzu ta ɗauki haske ashe matar sajan Bala ce bilkisu tace

"Wallahi kika sake kika shigo gidana wallahi zaki ga bala'i da tashin hankali ganin idon ki.....,

to ai baki san nice bala'in ba da masifa har tashin hankalin duk nice ke je kijawa mijinki kunne ya fita harka ta inhar kin isa dashi ko da yake yace fa baki iya tarbiyya ba zai auro me mai wa ya'yansa tarbiyya ba irin ki ba tunda nima gashi nagani ba a sami tarbiyya tun daga gida inban da rashin tarbiya ace uwa ke rako ya' gurin

Please Login or Register in order to submit comment