Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MUZABFAR yayi Allah yayi mai gane mutane dan haka lokaci kalilan ta gane su cikin tashin hankali yace

"Ranka ya dade badai ku tayiwa wannan diɓan albarkar ba dan girman Allah ku rufan asiri kar saka a kama'ta kuyi hakuri....,

Runtsai ido ASIF yayi ganin babban mutum yana me wannan magiyar da sauri MUZABFAR yace

"A'a baba wajan'ta muka zo a bokina na rako....,

da sauri ASIF ya buɗa baƙi zai magana KAWU yace

"Allah ya saka lafiya....ba kamasu kuka ƙara zowa kuyi ba....,

Ji ASIF yayi yawa ya ɗora hannu aka ya kurma IHU ko yaji dad'i gashi kamar an kulle mai baki ya kasa magana be tsinke da lamarin MUZABFAR sai da yaji yana ce baba daman wani babban lamarine ya kawo mu baba alfarma muka zo kai mana tun lokacin da kuka bar Abuja muke so muzo amma aiyuka summana yawa ASIF yana son yar gurinka FALMATA mun zo tambaya Allah isa ba aimata miji ba

suman tsaye ASIF yayi ya kasa tantance me kunnuwan'sa suke ji mai muryar KAWU yaji yace

"Babbar magana yanzu dai ga wayata ku samin number ku zan neme ku inde na gama bincike...,

da sauri MUZABFAR ya amsa ya saka mai sallam sukai mai suka shiga mota har a wannan lokaci ASIF yaka sa tantance me ke shirin faruwa me i saka be dakatar dashi ba....amsar da ya kasa bawa zuciyar'sa kenan
har suka isa gida ba wanda ya ƙara magana fitowa yayi ya shiga shashin nasu kiciɓus yayi da HAJIYA a kofar shiga part ɗinsa tana zagaye da waya a hannu da sauri ta juyo tace

"Kai kuwa ASIF ina kasamu gun shiga tun dazu hajiuya kattime me dalilin aure wannan wacce gidan tv suke tallan'ta ta kawomin zuƙa zuƙan mata ka zaɓa amma shine kake ƙoƙarin watsa min ƙasa a ido na kirawa wayar ka tana faɗa min wani shirman banza.....,

MUZABFAR da shigowar'sa kenan dariya zancan Hajiya ya basa yace

"Hajiya Allah ya bar mana ke....,

Amin inda gaske kake kai kuma na dawo kanka dan wallahi bazan laminci ka zauna da wacca juyar'ba ba tare da ka auri me kwan haihuwa ba.....ga kanan marabar ka da gauro kaɗan'ce kamata yayi lokacin da zaka tawo ka tawo da me zubin taliya yar murji amma ka tawo kai kaɗai ni shigo ka zaɓa ka darje....

dabara ce ta waɗo mai yace

"Hajiya yanzu daga gunta nake....,

washe baki tayi tace

"Dan Allah nasan Baka karya da gaske....daga gun jikartawa kake hakane MUZABFAR....,

Eh Hajiya

Shiga Hajiya tayi ɗaki ba tare da ta ce musu komai ba shiga part ɗin'sa yayi shikuwa muzabfar sai ya gano karshen wannan chapter dan haka bin Hajiya yayi dariya ce ta kusan kuɓucce mai dannewa yayi ganin yan mata sunci ado sun fi su goma sha wayyo Allah rigimar Hajiya ko salla bata yi..,

da sauri Hajiya kattime me dalilin aure tace

"Zaɓi ka darje ko wacce da ka ganta nan kwalin degree ne da ita wannan ita kuma master's degree ne da ita ta nuna wata tasha fenti a fuskarta sai taunar chingum take a ƙa'idar ungiyar mu photo muke bayarwa a zaɓa so lokacin da tayi min magana ta dauki number ta ne a television ne daga cewa babban mutum ne kai shi ya saka ma na kwaso su muka tawo akwai zaurawa a cikin su amma wallahi zam zam suke ciki da waje yasha gyara baza ma kace anyi ba ga yar shela can sabuwa ce fil Ranar auranta mijinta ya mutu....

kurɓar lemon da Hajiya ta saka yar aikin'ta ta kawo mus da snacks ta gutsire cake ta ƙara korawa da lemo tayi fari da idon'ta tare da yarfe hannu awarwaron da ta saka suka bada wani sauti tace

"Dan samari zaɓa ka darje wallahi zasu zame maka aljihu kai saboda tsabar biyayya zasu iya kwantawa kabi ta kansu domin sun horu ba ƙaramin training na yi musu ba danni ba yau na saba harkar nan ba na dade a cikin'ta....

Zaro ido MUZABFAR yake tabbas Hajiya ta ɗebo abin da yafi karfin masifar'ta koya zasu kaya da wannan yar duniyar tab......

Nima zan so inga yadda zasu kaya

*akwai rikice fa hmmm kudai Ku ƙarasa payment domin jin yadda zata kaya yau na buɗe paid group WA yanda suka biya zasu gansu a ciki.....*

Sauran page 5 na gama book 2

09061890481

Only WhatsApp

Nainarh kid's:.captain Ayusherh
Queen Kainat:.shiryayyiyar kaddara
Oumyasmeen:.gidan magajiya



*GIDAN MAGAJIYA*


EPISODE 41-42


Ina me dalilin Aure ajiye kofin hannunta tayi tace
"Ranki yadade gani...,
Hajiya tayi tace
"ina me baki hakuri yaron nan yace min yana da wacce yake so ....,
Hajiya ban gane mekika ce ba haɗa rai Hajiya tayi tace
"Abin da kunnuwanki suka ji miki shi nace....,

tab wallahi baza ta saɓuba saida na kashe uban kuɗi ki zomin da maganar banza kar ki ganki uwar manyan mutane narantsai da Allah yanzun nan sai mu lakaɗa miki duka iya karkarinta ace an kai mu gidan yari wannan kuma ba yau muka saba shigar'sa ba ya zame mana tamkar ɗakin uwar mu in banda rainin hankali na tako tun daga Sokoto na tawo kice min wai kun fasa muna dura a garin na ko hutawa bamuyi ba muka yo nan....

Ke daka tamin amma ke dai anyi mara mutunci ki dubeni tsofe tsofe dani ki dinga faɗan wannan magana bakya tsoron Allah ya kwashe miki albarka

Sannu uwata nace sannu uwantale wallahi ku daka ta nawa ne abin da kika kashe....?

MUZANFAR ya faɗa kama kugu tayi tace

"Dubu dari uku domin jirgi muka hau....,

Okay bani account number din ki karanto mai tayi ya saka ba dadewa ta ga alert tashi sukai ba wanda yayi wa Hajiya sallama ƙasa tafiya nabeela tayi ji tayi baza ta iya barin gidan nan ba Hajiya kattime ta roƙo hannun ta domin tasan damuwar'ta tace

"Mu tafi zaki gwada min son zuciyar ki....,

ba yadda ta iya haka ta bisu tashi Hajiya tayi zata shiga bedroom dinta dariya ce ta kubbu cewa MUZABFAR ya dinga yi harda riƙe ciki leƙowa Hajiya tayi tace

"Innalillahi MUZABFAR kardai kaima ka haɗu da wannan ciwo na zamani mental processing da naji a radio....,

be cemata ƙala ba ya fita shashin'sa ya nufa tura kofa yayi kamar yadda yayi tsammani haka ce ta faru tana zaune ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa ta na kallo agogo my juyowa tayi tace

"Habibty 11:39 fa .....?,

rungumeta yayi yace

"Zance...?,
Dariya tayi tace

"Masha Allah ina picture kanwar'tawa nunamin....,

Wayar'sa ya zaro ya shiga cikin gallery din'sa ya miƙa mata dariya tayi ta rankwashe shi aka tace

"Wannan photo na ne ai na kanwar'tawa nake nufi.....,

amsar wayar'sa yayi yace

"Tunda baki yarda ba shikkenan....,

dariya tayi tace

"Uhmm...,

ABUJA OSOKORO


Kamar an jefo'ta haka ta shigo cikin gidan tana haƙi sai zare ido take tana wai waye domin yau taga bala'i ganin idon'ta hurjanjan ta shigi cikin dakin mahaifiyar ta da sauri hajja ta tashi tace

"A'isha lafiya tun dazu nake neman ki amma wayar ki a kashe kin ɗaga min hankali.....,

kasa magana tayi sai ruwa da take cewa miƙo mata tayi ta sha bude wardrobe tayi tana zuba kaya a akwati..

A'ishah lafiya kike haɗa kaya tamkar wacce za tayi hijira....?

Hajja gidan mijina zan koma ni wallahi na fasa auran wannan shegen mutumin ɗazu kinga tujarar da matarsa ta aiko akai min har da cewa zata buga sunana a jarida da photo na ai kinga ta kunyata ni a idon duniya harfa barazana tayi min da rayuwata

to shi yanzu Allah isaka be sakeki ba

Hajja ko ya sakeni wallahi sai ya mai dani

yanzu dai ki bari sai gobe kya tafi dare yayi 12:00 fa

Hajja da zafi zafi ake bugar karfe gwara natafi tun da zafin abin Abuja ba kamar sauran garuruwan ce ba a kwai tsaro zan isa lafiya ina zuwa zan faɗa miki kar ki damu ta faɗa tana jan akwatin ta

Allah ya tsare ki

Amin hajja ta ɗaga labule tafita inda ta ajiye motar'ta ta nufa buɗe'ta tayi ta saka akwatin'ta ta rufe za gayawa tayi wajan driver ta shiga kye tayi mata ta tashi horn tayiwa me gadi ya buɗe mata get ta fita hawa kan titi tayi zuciyar'ta cike da tunani kala kala har ta isa gida horn tayiwa masu ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ne ya fito riƙe da bindiga a hannunsa ganin ita ce sai ya koma ba dadewa sai gashi me gadi ya buɗe get ɗin....

shiga ciki tayi da gudu daidaita parking din'ta tayi ta fito ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya zo ɗaukan akwatin'ta yayi har kofar da zata sada ta da floor'ta ya ajiye mata da yake yasan dokar ogan'nasa dauka tayi ta shiga ajiye akwatin tayi a floor ta zuba ta gumi....tana tunani

KANO N.N.D.C QUARTER

tunda ya shigo ya kasa zaune ya kasa tsaye ya rasa abin yi ko dan Hajiya ya yi AURE amma wannan ta dace da ta zama uwar ya'yansa.....?wacce irin tarbiyya za ta bawa ya'yansa anya kuwa ba auran yarjeniya zai yi da ita ba in Hajiya taga yayi auran hankalin'ta ya kwanta nan da wani lokaci ya sake'ta tunda bisa dukkan alamu zata yarda da wannan agreement ɗin da haka yayi shiga toilet ya yi wanka ya dauro alwala canza kaya yayi ya saka pyjamas farare tas da su shinfiɗa daduma yayi ya tada sallah bayan ya idar ya ɗauki Alkur'ani me gir ya suma karantawa sai wajan karfe biyu ya ajiye ya kwanta....

Kiran sallar farko a kunnan magajiya dan haka da sauri ta tashi ta kunna fitila da yake a kwai huta zama tayi ta zuba wata uwar miƙa tashi tayi ta fito kiciɓis tayi da kawu ya fito zai tafi masallaci kallon'ta yayi ya shige ya fita alwala ta ɗauro bayan ta gama ta koma daki salla aka tada binsu tayi har aka idar tana idarwa ta fito ta soma haɗa kayan sana'arta ruwan wanka ta ɗora tana jiran yayi zafi ta dauka tayi wanka

kamar anjefo rabi ya shigo yana haƙi sai zare ido yake kallon sa tayi tace

"Lafiya...?,

Wallahi Allah magajiya ido huɗu muka haɗa da wannan na Abujan yanzu ya zoge glass ɗin motar sa shi da wani kardai dawowa sukai su kashe mu na shiga uku wayyo Allah baba

tashin hankali ba'a saka maka rana jar uban'can mun shiga uku da gudu ta shiga bayi zaman dirshin rabi yayi ya zuba ta gumi yana cewa nima da zanyi kashi da nafi kowa murna sai ringing yake a ciki na dinana ne ya shigo da M.P a hannunsa sai tashin ƙiɗa take yi kai kace kana club ɗin lagos ko kallon inda rabi yake beba ya sami guri ya ajiye MP sa yana tiƙarrawa yana cikin rawa....

yaji rabi yace "bazan hanaka rawar'ka ba wata kila wannan ce ta karshe da za kayi idona idon'su wallahi mu suke nema kashe ƙidan yayi yace

"Rabi me kake faɗa ne haka....?,

Kuka ya rushe da shi ya fyece majina da zanin dake jikin'sa yace "wallahi in kaci bashin wani kaje ka bashi haƙuri ya yafe maka bilahillazi idona idon shugaban DASS...

innalillahi ƙiyamar mu ta tsaya shikkenan kai Allah ka tsinewa KASKA banda asarar dubu biyun mu da mukai bamu da zaman lafiya ana yi mana bita da kulli ka duba fa ka gani wannan dubu biyu kudin abinci na kwana biyu kenan

Amma kai dinana anyi mara hankali wallahi muna ta rayukan mu da lafiyar mu kana ta dubu biyu to ai kasan hanya jeka ka karɓo

wallahi magajiya aini kinga na rasa bakin magana in banda tsabar rashin mutunci da rashin sanin ciwon kai muna ta lafiyar mu ina batun wasu kuɗi

KAWU ne ya fito daga daki yace

"Rabi'u deeni falmata lafiya kukai jigum jigum kamar wa'yanda a kaiwa mutuwa...?,

Wallahi Allah KAWU da wannan tashin hankali gwara in mutuwar ce ayi munsan mutum ya mutu in ma

Bata ƙarasa abinda tayi niya ba RABi ya goge hawayen'sa yace

"Wallahi gyara zancan ki wanne irin gwara mutuwa saidai in kece zaki mutu amma ni wallahi bayan zuba yaushe nazo duniyar da har zaki dinga batun mutuwa ana zaune kalau......,

Dan girman Allah rabi ka zauna kayi jiran duniya anya kuwa dinana ba ƙarya yazo ya faɗa mana ba muka hau kai muka zauna mutumin da har jiniya ake mai shi ya gani....?

gaskiya kam nima sai yanzu nayi tunanin haka kallon su kawu ya tsaya yi ya rasa gane baƙin zarar gashi kuma sunƙi faɗa mai......

yanxu dai makaryaci kuka ɗauke niii....

duk abin da zuciyar ka ta baka shi muka ɗauke ka ɗan rainin hankali botiki ta dauko ta juya ruwan ta tace wa dinana ya wanke mata tukunya ya zuba mata ruwa ya ɗora rabi kuma ya fara feraye doya

gama wankan tahi ta fito shiryawa tayi cikin doguwar riga ta atamfa ta chokalo dauri gaban goshi sai kamshi take zubawa fara haɗa kullin waina tayi wata uwar sallama suji anyi gaban rabine ya waɗi yace

"Shikkenan aikin gama ya riga ya gama innalillahi tun huri nace mu gudu kuka ƙi ai ga irin'ta nan....,

da hallacan yi mana shiru dinana liƙa kaga suwaye..?

Kafa na fiki ke mana ki leƙa kika suwaye

Ni kake faɗawa haka dinana kafin ta ida zancen ta tuni rabi yafara kokarin ɗanewa kan katanga da sauri dinana ya riƙo shi yace

"Wallahi ba'inda zaka kuka ya fashe dashi yana cewa MAGAJIYA duk shi ya saka mu a wannan tashin hankalin son zuciyarsa ne yayi yawa shi yasa ka har ya kai mu muka siyi sofaffin layi shine da wasu ƙafafuwan'sa yawa kwarashi za ka gudu ka bar mu ai ba kafa ya fi mu ba .....,

da sauri ta tashi ta ƙara riƙo ɗaya kafar ta rabi tace

"Zaka sauko ko sai na karya maka ƙafafuwa...?,

Ku dakata wannan abin fa ba dole nayi muku ba zaku cika ni kusai nayi muku rashin mutunci ya faɗa yana muci muci da ido alamun ba'arziki

Assalamu alaikum

wa'alaikas...kafin KAWU ya ƙarasa tuni sun cika RABI shima saukowa yayi suka rufe wa KAWU baki kasa ƙasa rabi yace

"Mun shiga uku kawu wa ya aike ka amsa wannan sallamar da ba aminci a tattare da ita....,

kallon su ya shiga yi yana tunanin anya kuwa lafiyar su ƙalau dinana ne ya gane haka yace

"Wallahi kawu duk kallon da za kai mana saidai kayi mana dan kuwa yau muna cikin rashin nutsuwa da tashin hankali rabi ne yace yaga shugaban mala'ikun duniya.....

asho ne ya shigo yana rangaɗa sallama da alama abuge yake nuna su yayi da danya tsa cikin maganar maye yace


"Amma ku anyi kafurai kuna jina ina sallama ba me amsawa saboda baku ga uwar motar da na tawo da ita ba..,

wata uwar ashar magajiya ta yi mai tana cewa amma kai anyi dan iska wallahi ashe daman kai kake wannan sallama ka saka mu a tashin hankali zo ka fita wallahi baza ka zauna min a gida ba yau tunda bada kuɗin ka nake haɗawa na biya haya ba

yau nake jin wani sabon isanci akai kafuri sama dakai wallahi Allah sai ka tashi kabar gidan nan dan kwal uba......

wallahi ko baki rantsai ba sai ya bar gidan nan dan durin uwa daukan sa zanyi aka na fitar dashi kai Allah ya tsinewa shaye shaye ga yarda ya saka mu a halin ha'ula'i cewar rabi

sosai kawu yake dariya sai yanzu ya fuskanci inda suka dosa ba wanda ya biya ta kan kawu sai uwar tujara suke zubawa asho zaman dirshan yayi yana cewa Wallahi bazan fita ba

Chak dinana ya dauke sa a kafaɗa gantsara masa cizooo yayi a huya ba shiri ya sauke sa yace

"rabi zo ka duba min ba allura ya caka mini ba a huya dan Allah zo ka duba mini...

Kai rabi kar ka kula shi zo ka ɗauke shi ka fita da shi

hannu kika fini kina gani dai abin da ya yiwa dinana ni kuma da yake gani mara hankali sai na kara ɗaukan sa kinga abin da yafi cizo zai mini yan shaye shaye ba'a raba su da makami haka kurum ki saka a kai ni lahira ban shirya ba

rufe min baki ina ka taɓa ji sai mutum ya shirya ake kai shi ƙabari kar kayi mamakin yau kawayi gari ka ganka a tsakanin tukwane

Haba uwani kina a matsayi na uwar mu kina cewa na mutu gaskiya hakan be dace ba

Rabi'u kenna ita fa mutuwa bata sallama ya kamata Ku nutsu ku san abin yi kaga shigar matan nan da kake Allah ya hana ya kuma tsinewa duk me yi

Allahu akbar uwani ashe kin iya tafsir ban sani ba anan dai baki da rabo tafi masallacin bola ko kya sami wanda zai iya ɗaukan wa'azin ki cewar ta masar da ya shigo rataye da haka a hammata da dankwali yana juya shi a hannu.....

Ku dai ku cigaba da yin payment ₦500 lokaci yana ƙaratowa sauran pages 4 na book2 gama

8141785374 Amina alhasan Muhammad opay

Ku turo da shedar biya ta wannan number

09061899481
Dan Allah in ba siye zaki ba karki min magana masu yi min magana ace ASLM dan Allah ku tafi kai tsaye game da abin da ya kawo ku




GIDAN MAGAJI YA

EPISODE 43-44

TA'MASAR UWANI kike fadawa haka zoka fita ko na karya maka kashin muƙamuƙi..
ɗamara yaci yace

"Billahillaziii ba inda zanfi'ta ita baki ga abin da take faɗa ba sai nawa zama daram yana me naƙuɗa.....,

tab gaskiya ya raina ki kina faɗa yana faɗa wallahi magajiya zan faɗa miki gaskiya ki koma magajiyar ki tada faɗan nan da kike yafi naɗa sannan dole na kai ki gurin malam me ishimawee ya duba miki ƙasa a ga ko akwai wanda yasa ka miki hannu domin wannan rainin da akai miki da walakin gora a miya ya faɗa yana buga cinya game da harfe hannu.....

tab sannu macuta ni za ku kai a cinyewa kuɗi a banza tsaya kuji wallahi duk macan da take kai kuɗi domin amallake mata miji to wallahi sunan kwakwalwar'ta dooosa haƙuri da iya magana da kyautatawa datarairaya da son yan'uwansa shine babban magani banda ka rainani ka mai dani kidahuma shine kake min zancen wani malami kai ka kiyayeni

Rabi tamasar kuzo mu ɗauke wannan mahaukacin dan wallahi tunda ya sani gudawa a wando saboda cizon da yayi min

Wallahi maza sun ƙare a duniya shine mu muna mata kake'so mu mu tayaka ɗaukan sa haram wallahi haram

da hallacan rufemin baki shegu kawai wa'yanda Ubangiji ya tsine musu.....

be ƙarasa ba suka rufe shi da duka ku daka'ta wallahi bazan laminci wannan iya shegen ba kawu zo ka raba su ga doya'ta tana kokarin dauhuwa kar su naɗa musu duka su kasa yi min aiki.....


wallahi ba zamu yadda ba kullum aibata mu yake kawu ba ruwanka ina ganin mutuncin ka a matsayin ka na uban mu na bariki

icce magajiya ta ɗauka tayo kansu ɗoɗanawa ta masar tayi a ɗuwawu ihu ya saki tuni suka fita a guje harda dinana da ya garzatsawa rabi cizoo sun zata kunama ce ta ciji tamasar ya saki wannan razanan nan niyar ƙarar da ya zunduma haɗe da ihuuuu binsa sukai har asho ashe iskancik nasa na karya ne....

dariya magajiya tayi tana cewa kawu anya kuwa suna da hankali

gyara zaman kur'anin dake hannunsa yayi ya ci gaba da karatu be kulata ba a zuciyarsa kuwa nema musu shiriya yake

kai ta gyaɗa ta koma kan kullin wainar'ta gefe kuma wutar da ta dora doya tana ta ci tun dare daman aka yo mata markaɗe.....

*****

haɗa kayan'sa ya cigaba dayi yau yake so ya koma Abuja gobe kuma ya koma baƙin aiki...

Asif daman ba hutu kazo ba kwana biyu kawai za kai ka tafi

zuge akwatin'sa yayi yace uhmmm sanin halin aminin'nasa amma dan haka ya ja baƙin'sa yayi shiru zama ya gyara yace

"baka tambaye ni ya hajiya tayi da me dalilin aure ba....?,

bani da business da'ita

hmmm haka kace da fa ban kuɓutar da kai ba ta hanyar kaika gidan magajiya da tuni dole ka zaɓa a cikin yan matan da Hajiya ta kawo maka

matsar da akwatin yayi ya riƙe mai huyan riga yace

"bana so in gwada training akan ka da tun a jiya na zubar maka da haƙora ce maka nayi ina son'ta da zaka haɗani da baban'ta kasan ina ganin ƙimar'sa bazan iyayi mai musu ba bazan kuma ina karyata ka a gabansa saba da girmana ina zaune kai zaka nemo min matar aure....,

cika shi yayi ya naushi iska yana cewa wallahi narasa dalilin da a lokacin ban tsayar da kai ba daga shirman da kake shirin aikata min

aikin gama ya gari ya gama da wallahi wannan maganar ɗazu hajiya take sanarwa da su abba kafin mu gama breakfast yanaji yana cewa ma zai neme ka ka faɗamai inda yarinyar take domin basa so a dade

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abin da ya shiga maimaita wa ya ci gaba da cewa kasan kuwa yarinyar nan bazata taɓa yarda da aurena ba ka duba ranar da suka bar Abuja ta kwayar idanuwanta ina iya hango tsana'ta a cikin idonuwanta


tashi yayi yace

"to Allah in alkairine auran Ka da ita Allah ya haɗa sai kaga an sami rabo....,

banza yayi mai har ya gama shirinsa na tafiya Akram ne ya shigo ya dauki kayan nasa shi da ayman tare da zu huce gurin Hajiya ya fara shiga tana zaune tana lazimi macece me son ibada baka rabata da jan carbi sallama yayi amsawa tayi cikin sakin fuska tsugunawa yayi ya gaisheta yace "Hajiya zan koma....,

to nima fa binga zanyi domin tuni na saka a haɗamin kayana na gaji da zaman garin nan gwara na tafi yawon buɗe ido

da sauri ya ɗago salati ta saki tace"au bazan bika kake nufi ba ko yaya...? da kanka yana ƙasa yana wanda yayiwa sarki karya da yake kaji zan bika shine ka ɗago tafiya fa ba fashi nida yar jikalleta inga wanda ya haifeni a cikin ku ya hanani.....

Hajiya kiyi hakuri zan aiko a tafi dake amma yanzu bazan iya tafiya dake ba jirgi zan hau ba mota ba ba ai miki booking ba

kai muzabfar dauko min jakata na rataya ga akwatina can hansai ta faɗa maka inda ta ajiye min ita
bata jira me zai ce ba ta ci gaba da cewa hansai hantsai fitowa matashiyar buɗurwar tayi ta ɗurƙusa wayi tace

"Gani Hajiya.... Alhaji barka da zuwa....,

yauwa yace mata kamar dai ko da yaushe kinga ba gaisuwa na kiraki ki mai ba bana son tsohon kinibibi gaisar da uwar miji a kasuwa buɗe kunnan ki kijini bana son a sami problems kwanaki nasaki ki haɗamin kaya zani Abuja na fasa to shi zaki dauko min su

Hajiya kince na mai da su har abada ba zaki ƙara zuwa Abuja ba tunda annuna miki iyakar ki


Salati ta shiga yi tana goge kwalla da mayafin'ta tace "wallahi muzabfar karyar wannan yarinyar tana bani tsoro karfa wata ran ayi sama damu in Ubangiji ya gaji da halinta kasan me kan uwa da habi yake sai anje can a tantance yau she na faɗi haka da badan na dauko amanar'ta daga kauye ba wallahi yau ba'a binda zai hanani na maida ita yarinya sai shegiyar karya yau she na faɗi haka muzabfar ka duba min wannan zance...?
yanzu dai Hajiya kiyi hakuri mantawa tayi

bakin gyelanta tasaka ta goge idanuwanta tace

"ba dole nayi hakuri ba...,

ke hansai bata hakuri

Hajiya dan Allah kiyi hakuri

jeki Allah ya yafe mana baki ɗaya amin ya Allah ASIF ya faɗi haka

tashi tayi ta bar gurin ganin Hajiya ta manta da wannan zancan ya tashi yace

"Hajiya Allah ya ƙaddara saduwar mu....,

kai ta gyaɗa mai ba tare da tayi magana ba
binsa muzabfar yayi suka shiga yayiwa kowa sallama sannan ya shiga mota muzabfar ya ja su har airport badadewa jirginsu ya tashi.....


Abuja

tun da safe take cikin zullimi dan bata san tarbar da ASIF zai mata ba zai yi murnar dawowar'ta ko zai nuna mata halin ko in kula tun tana irga mintinan fitowar'sa har ta koma kirga awannin zuwa yanzu tabbatar baya garin ko kuma baya ƙasar domin in dai yana gari zai fito musamman ma da safe in ya dawo daga massalaci zai zauna yaji damuwar ma'aikatan gidan yau gashi har karfe 12:30 ba alamun'sa cikin sauri ta tashi

Please Login or Register in order to submit comment