Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane me kake nufi duk inda aka haɗa hanya da shege sai ya nuna halinsa yanzu zan maganin ka

Ku dakata kafin ku fara faɗa nan magajiya bamu kuɗin mu kunsan shege ba bakon mutum ɗaya bane

nacin'ye bazan bayar ai ka bari mu shiga daga ciki tun anan za kai min zancan kuɗi to bazan bayar ba na cinye sai ku yan kani ku kwaɗan'ta namana ku cinye sai na bayar

haka kika ce....?,

gyara damarar kugunta tayi ta daure tamau ta kama kugu tace"dinana haka nace ku a kan kuɗi baku da sanayya yawa wacce zan gudu....,

magajiya kinfa saba yanzu zaki ficiccike akan karya kice kin cinye ni kuwa wallahi kobo na bazai ciwon kai ba sai kin bani

ta masar ya faɗa yana haɗe rai

tab jar'uban can lallai na yarda duk wani dan bariki kunama ne yau Shekara nawa muke tare da ku na taɓa cinye muku hakkin ku bani nace ku rakani ba zan baku wallahi yanzu nace bazan biya ba ta zauna sai abin wani sarkin bani ba

Kinga karki nuna mata tashanci har karkashin gada na kwana yau ko da aljanu kike yawa wallahi sai kin bamu kuɗin mu yar hau..

da hallacan kuyi shiru motar hisba naga na yowa nan

auzubillahi kuskure bakin ka da hypo wannan ai jamana masifa ne rabi dan ku kun tafi kurkuku shine ba'aza wayi gari ba kuyi zancen jami'an tsaro to wallahi saidai a kama ku ASHO ya faɗa yana mai da hukar'sa shiga cikin gida sukai amma zuciyar magajiya ta kasa nutsuwa kuɗin su ta zaro ta basu tace

"kai ASHO ciro hukarnan in ma zuwa sukai kama mu ba kayan laifi a jikin mu karkarinta wa'azi zasu yi mana in yayi hutar duniya to su bama aikin share masallaci da jin wa'azi.,

cire wa yayi yana cewa kuma fa haka ne

ai su ba kamar wayancan marasa imanin ba nifa wani daki da aka kai ni wallahi bana gane dare balle rana

wallahi shi ya saka nake yiwa kaska Allah ya isa

Dinana ga babban wanda za kai wa Allah ya isa wancan me kama da Yahudawan farko dan anyi kidnapping ɗin matar ka ba bincike sai ya kama mu gamu ya'yan talakawa bamu da yancin kan mu...

gabansu ne ya wadi jin sallama da kyar magajiya ta iya amsa sallamar tasu wasu matane su ka shigo da hijabi da tambarin hisba a jikin hijabin'ta sai a lokacin falmata ta fahimci uwani bata gidan haka ma kahu cikin karfin hali magajiya tace "sannun ku...uwanin bata nan...,

a'a gurin ku muka zo

jingina tayi a jikin bango ta harɗe kafa tace " da alama dai maƙiya sunyi aiki to ina jin ku..shaf shaf ku faɗi abin da ya kawo ku...,

kallon kallo aka shiga tsakanin jami'an hisba Idcard ta ciro tace "sunana hauwa ali me allo ni jami'ar hisba ce an toro ni domin mu kai ku hisba..,

daka daka waya aiko ki kin faɗamin abu a dubu gwara ki mini gwari gwari yadda zan gane ko ba haka ba dinana....?

baiwar Allah ki tsaya mana ta karasa maganar mana

ke ma matemakiyar tace ko kuma yar karere ai bake nayi wa magana ba ita nayi wa

ganin yarinyar bata da kunya tayi shiru ci gaba da bayanin'ta tayi tace "mutanan unguwa sun kai ƙarar ku....,

yanzu kuma na fahimta ina zancan ki ya dosa sunan wa dawa sukai muku list domin ni gidan nan cika yake maƙil fiye da tunanin ki sana'a nake nake rufawa kaina a siri yan baƙin ciki masu hassada sunkai muku karanta shine za kuzo ku yayi me mu yawa wasu kayan wanki ku zuba a mota yanzu dai ni zaku kama dan su wa'yannan ba ruwansu buƙata ke kawo su

ai dukkan ku ake ce mu kama da yan daudu uku da dan ɗaba ɗaya sai ke

lah ha'ilaha illallahu shikkenan dinana na shiga uku yanzu ina na kama hisba

kaji banza gyara bakin ki ta masar mene bamu gani ba gurin Dass aka kai mu fa ABUJA BIRNIN TARAYYA

kora masa dai ai mu an shamu mun warke billahilazi rabi ya faɗa yana turo dauri gaban goshi....

kunga mu tafi ai wannan harka bata gardama bace mu tafi magajiya ta faɗa tana yin gaba binta sukai har gaban motar su ashe da maza suka zo shiga motar sukai ta gumi magajiya tayi ta fara tunanin rayuwar'ta ta baya har a ka zo bata sani ba sai ji tayi tamasar ya taɓa'ta yace "munzo..,

fitowa tayi suka mara mata baya har office ɗin oc akai kai su zama sukai suna jiran ikon Allah hankalin ta masar a tashe yake sai zare ido yake domin wannan ne karon'sa na farko shiga hannun hukuma shi kuma daman asho ai dan hannu ne yasha shiga basu an kare ba sai ji sukai tamasar ya fashe da kuka cikin mamaki kowa ke kallon sa ya ɓara baki yawa ƙaramin yaro har da bubbuga ƙafafuwa

kai da kata wannan wane salo ne faɗa mana in da futa muma sai muyi dinana ya faɗa yana dafa kafaɗar'sa

be kulasa ba ya ƙara runtumewa da kuka ta gumi magajiya ta zare tace "zakai shiru ko kuma wallahi mu naɗa maka duka wannan wanne irin iskanci ne...?,

O.C ne ya shigo kujera ya ja ya zauna hannu ta masar ya shanye yawa irin lalurarrun mutanan nan wa'yanda suka sha ruwan mahaifa yana dalalar da yahu mamaki ne ya kusan kashe su magajiya tace "dinana kaga wani sabon barikanci....?,

uhmm magajiya in kana da rai kashe kallo

gyaran muryar da O.C yayi sai suka bashi nutsuwar'su da hankalinsu annu'ar buɗe taro yayi sannan ya ƙara da cewa al'ummar wannan ungowa ta kofar mata yakasai da zango sun kawo mana koken su akan ku musamman ma ke da kike tara yan iska wannan bashi ne karon farko da suka kawo mana karar ki ba mu nan gurin da kuka gani hukunci muke cikin tsarin addini in Allah ya temaka har shiryuwa mutum yake daman haka muke so mu zama sanadin shiryuwar al'umma kai Sheikh Ibrahim al Bashir ciro min dan kwalayan kan su da zanin su ya faɗa yana nuna su rabi Allah ya jada ranka kamar wannan bawan Allah bashi da lafiya
maƙe murya ta masar yayi yace 'kar ka sake ka taɓa ni kana taɓa ni zan cire maka hanjin cikin ka....,

salati su magajiya sukai dinana yace "innalillahi gani tsohon makirci wallahi lafiya yake....,

kwantar da hankalin'ka ai munan da ka gan mu muna da maganin komai musamman ma masu cutar aljannu kamar yadda na faɗa muku kusan cewa hisba aikin Allah ce abin da Allah ya ce Annabi yace shi muke yi

buga cinya rabi yayi yace "uhmm gaskiya fa domin abin da sani yayi ya kone min ruwan kaiii wallahi...,

yanzu ya Sheikh kai shi gurin da ake ruƙiya kafin mu gama da wa'yannan

wata ƙara ya kwalla tamkar zata fasa musu dodan kunne ya ƙara karkacewa yace "kuna ganin abin namu wasa ne kana takowa sai na cire maka jijiyar ƙwaƙwalwar ka....,

ganin kamar zai raina musu hankali O.C ya tashi ransa a ɓace ya ɗauki wata zabgegiyar bulala ya zabgawa ta masar gantsarewa yayi cikin haɗe rai O.C yace "ya sunan ka...?,

cire ɗan kwalinsa yayi yace"SANI BADAMAS HALLIRU...,

zama O.C yayi yace"yanzu ku za a kirawo iyayen ku domin su san halin da kuke ciki ke kuma ki kawo saurayin ki a daura muku aure domin kyahun mace sittirar ta gidan mijinta...

da sauri magajiya ta ɗago yau take ganin ikon Allah yawa wani uban'ta yana ginda ya mata sharadi abin da bata gane ba shine yan unguwar tasu cewa sukai tana zina ko me lallai ta koma zata ci uban dukkan wani munafiki da munafuka gyara zama tayi tace "Allah ya ja da ranka ni bani da saurayi kuma duk wanda ya kawo muku wannan karar to fa ɗan hassada ne ranka ya dade da wannan sana'a nake ci na ciyar da iyayena ni bana shaye shaye bana duk wata harkar banza ina kara mutuncin kai na ko ba haka ba deeni.....?,

dinana da jikinsa ke tsuma yace "eh wallahi muma tayata aiki muke tana biyan mu kaf cikin mu ba wanda salla take huce shii wata ran ma mu muke share masallaci RABI'U da kake gani har janmu salla yake babban limami ne ASHIRU (ASHO) kuwa har koyar da ilimin addini yake SANI almajirin'sa ne shine me share majalisi

O.C ɗagowa yayi tun da yake wannan hukuma yau shekara ashirin be taɓa cin karo da manyan yan iska irin wa'yannan ba ga kalami basa kama mutun sai sun yi kwakkwaran bincike tukunna suke kama mutum yau anfi wata ana kawo musu karar wannan shu'umin GIDA har mai gidan yanzu sai sun kirawo gama rubutunsa yayi ya miƙawa ya Sheikh yace "ka miƙa wa su liman sannan ka tsaya ko wanne a cikin su yabaka number ɗin mahaifinsa....,


ba musu kowa ya karanto ci gaba da tagumi tayi gaban ta na dukan uku uku zama ai tashin hankali aka ce sai tayi aure ita yanzu ba aure a jerin abin da tasaka a gaba....

fita yayi bayan ya gama amsa

UNGUWAR KOFAR MATA


Malam surajo bansan ya zanyi da yarinyar nan ba akan auran nan a duk binciken da kayi nayi yaron nan bashi da aibu duk macen da ta same shi ta more

ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zama yace "yanzu dai ka kirawo su kace su turo duk wani sauran abu kabar min a hannu na ga wayon da kak mata na cewa auran hucin gadi ne kaga in ka ɗaura basai ya sake ta ba zan zauna na fahimtar da yaron wannan abin da yayi tamkar jahadi yayi sai uwani ta ci gaba da sana'ar tata...,

ajiyar zuciya ya sauke yace "tom shikkenan yanzu bani da kuɗi a wayata aramin wayar ka.....,

bashi waya yayi kiran number MUZABFAR ya shiga yi har ta katsai ba a ɗaga ba kira uku yayi mai be dauka ba ya ajiye wayar yace "in ya gani zai biyo number idan ya kirawo sai kai mai bayani...,

to Allah dai ya shirya mana yaran nan ka haife su ne baka haifi halin su ba kullum addu'a nake amma abin na ASHIRU tamkar tiri

ka ci gaba da yi addu'a bata waɗuwa ƙasa banza abin nasa da sauki wallahi tunda baya ɗaukar kayan mutane

lallai kam Assalamu alaikum

gaban kawu ne ya waɗi ganin jami'an doka ya kuma tuna maganar da FALMATA tayi mai na zata bashi kudin belin'su da kyar ya iya amsa sallamar su gaisawa sukai ɗaya daga cikin su yace "sunana malam sulaiman Yusuf ni jami'in hukumar hisba ne....,

Innalillahi malam surajo yaran nan sun sake jawo min wani tashin hankalin wallahi aurar da ita zanyi na huta wannan tashin hankali har ina tun da nake ko gurin yan bijilanti ban taɓa zuwa ba sai gani har nine da zuwa Abuja babbar headquarter D.A.S.S.......✍️

Bazan gaji da baku nishaɗi ba😂😂😂😂😂😂

Laifin dad'i.....

ALHAMDULLAHI ayau na gama book 2

Domin ci gaba da karanta littafin nan ku ci gaba da payment ɗin ku gobe zan shiga BOOK 3 insha'Allah

zaku iya biya ta wannan hanyar 8141785374 AMINA ALHASAN MUHAMMAD OPAY ₦500

KU TURO DA SHEDA TA WANNAN NUMBER 09061890481
yan niger zaku dauki katin AIRTEL 300fcfah ku toro ta wannan number 09061890481

Dan giram Allah in baki yi niya ba karki min magana







An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment