Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ɗauki wannan kaza ki biyani kuɗin ta

Asabe da ciwo yaci karfin ta tace '' haba Hajara ina ne ina cin mataccan abu ni da ba arniya ba ki dai bawa ƙaren Haruna yaci...,

ke bana son iya shege wallahi dole ki ɗauki wannan kaza duk abin da zaki da ita kiyi da ita amma wallahi dole ki siya ban da ma zuciyar musulunci ba sai na karya miki kashin kafaɗa ba har ni zaki dinga bi da sharri to wallahi tun muna shedar juna ni dake kiyi gaggawar biyana kudin wannan kazar dubu bakwai na siye taci abincin dubu biyu dubu goma sha ɗaya kenan


nida bani nayi abin nan ba dan Allah kiyi hakuri ta faɗa tana ƙoƙarin tashi da kyar take jan kafar ta fusgota hajara tayi ta ɗauki kazar da shazali ya murɗe wa wuya tace '' maza biyani sannan kibar gidan nan ....,

zama tayi domin abin yayi mata dai-dai tace '' wallahi daman ba son fita nake ba..,

au haka kika ce to wallahi yau na lahira sai yafi ki jin dadi asabe

kan bala me yashi tab jajar ubancan ke kar kiga ina yi miki lumbu lumbu yan zunan zan choge kafata naci uban ki kowa ya sani fankan fankan bata kilishi

kai lallai matar nan kin raina min wayo yau zanyi maganin futsarar ki wallahi

mudai yi maganin juna nan fa fada ya kaure a tsakanin su haruna ne ya shigo yana tsalle hadi da rausaya yana cewa ku tasu babba ku tasu ku taso ba me raba ku haka ya dinga mai maita wa
ganin faɗan ya ƙara kamari ya canza salon waƙa wanda yafi wani ƙarfi ya cuci Dan uwansa wallahi ba wanda zan kira ya raba ku taya dan akuya zai yi fada da giwa yace zai ci riba

baƙaramin wuya suka bawa juna ba ba zato ba tsammani Hajara taji asabe ta gartsa mata cizo abin ka da ta samu tsoka ba ƙaramin shigarta cizon yayi ba ta kwalla kara ta sakita ba shiru tana sakin ta ta fara cewa

'' Hajara daman na fada muku faɗa dani babu riba wallahi amma kika toshe kunnuwanki ai gashi nan yanzu kinga uwar bari kin sakeni kaza kuma wallahi ko kobo bazan biya ba kije kine mi wanda ya kashe miki abar ki ya biya ki kiga idan be sace ki ba kin koma samfurin mucija da zani...,

Haruna kamo min ita wallahi ba zan yadda ba kaga fa a kirjina ta cije ni shegiya yar iska wallahi sai nayi maganin ki

kin dade baki ba Hajara, nace kin dade baki ba kana sakewa ka karaso nan wallahi sai na ɗauki iccen nan na saka maka a fuska shege da fuskar ka yawa kayi sujja a buhun gawayi...

kut ashe daman ina kallon ki kamar mutuniyar kirki ke ba ta kirki bace hmmm zan karaso ni kuma tafasasshen ruwan nan zan diba nayi miki wanka da shi..

fakar idanuwansa tayi, tayi wuf ta fita maza maza haruna ka bita kar ka barta ko bayan layin nan tayi bin ta yayi kafin ya cimmata har ta shiga gida dafa gwuiwowinta tayi tana haki tace

'' kuna ina dan Allah ku kawo min ruwa wannan bala'i har ina daga wannan sai wannan...,

a hankali baba da ba ta dade da dawowa ba ta dan leƙo da kanta dariya ce ta kubbuce mata ganin yadda asabe ta koma yawa wata rubabbiyar gwanda fuskar nan taci bleaching duk tayi ja sai zare ido take..

bayan ki asabe ga shazali nan zan sara miki gadon baya da gudu ta shiga dakin
ta dariya lami ta fara yi harda fati tace

'' gaskiya kin bani kunya asabe ina daban cin ki yake da sai ki tsaya ku dambatu ku buga yar kashi ke da shi...,

takaici ne ya kama ta tace '' yanzu baba dariya kike dan bake yakewa abin da yake min ba haba baba gaskiya haka be kamata ba..,


tura dauri gaban goshi tayi tana cewa dole fa shazali ya raina ki duk abinda da yake faɗa gaskiya ne bakya tara karuwai ko dazu ba dan daudu bane ya bar gidan nan?

shiru tayi duk ranta ba dadi ta gyara zama tana miƙe kafarta tace '' mufeeda mufeeda..,

ta tafi makaranta

makaranta kuma ban hanata bin duk hanyar da shegen yaron nan yabi ba kai wannan jaraba har ina anya kuwa ba asiri yayi mata ba tabi ta nane mai ala dole sai shi yasa ubanta ko da yake mahaifinta ke daure mata kinsan ranar nan da naje mahaifiyar cewa tayi ai itama ba ba son wannan alaƙa take ba ke kinga irin mutuncin da taci min kai gaskiya matar nan kwata kwata bata da mutunci wallahi inda yaje bata je shi ba

Shiru baba tayi mata tamkar da dutsai take magana

Wannan kenan


ASH gaskiya Hajiya ke faɗa maka ta kamata ka dawo kamar da ka gina sabuwar rayuwa mahaifina ya mutu na dena farin ciki ne

jingina yayi da kujera ya lumshe idanuwansa yace

'' har abada farin ciki na ya tafi Yasir..,

tab abin naka azeemun ne anya kuwa fatalwar nusaiba ba ita takama ruhinka ba

dariya yayi yace '' kome zaka faɗa saidai ka faɗa wallahi ko da yake ba kai kaɗai ba hatta Hajiya kallon da take min kenan..,

wallahi dole tayi maka nifa ban taba cin karo da labari irin naka na kabi Ka kwallafa mace ɗaya a ranka

file ya ɗago fara dubawa yace '' mubar maganar haka zanyi aiki...,

korata kake yi ko to bara na tafi gurin madam ta ɗebe min kewa cewar Yasir da yake danne dariyar da ta taso mai ganin yadda fuskar ASH ta canza

ajiye file din yayi yace '' ni ba korarka nake ba kawai dai nace maka zanyi aiki..,

okay ai kai daman duk maganar da za a taɓa marigayya ba sonta kake ba idan ka ƙara aure bawai yana nufin ka manta da rayuwar ta bane

dafe kansa ASH yayi yace '' ya Allah nifa bana son wannan zancen amma na lura ku kamar dadinsa kuke ji...,

sosai ma kuwa wallahi domin bamu da buri da ya wuce mu ganka yau kayi aure har da ya'ya buɗe baki yayi zai magana sai aka turo kofar da sauri dukkan su suka kalli kofar wani irin riga da wando ne a jikinta yawa fata ta saka kimono amma ita da babu duk ɗaya cikin iyayi tayi sallama

kau da kai yayi sannan ya amsa sallamar tata zama tayi ba tare da yaba ta izinin zama ba tace

'' ya ASH barka da yamma daga school nake nace Bara na kawo maka ziyara ko dan ba aunty nusaiba be kamata mu yar da juna ba...,

hankalinsa ya maida kan laptop dinsa yace '' yauwa...,

a takaice sam baya kaunar zuwan da ni'imatullah take mai a ce ko da yaushe tana hanyar office dinsa yana raga mata ne dan ita kanwar nusaiba ce step sister dinta ce mahaifinsu ɗaya

buɗe jakarta tayi ta fiddo da turare tace '' ga gift nan ka bawa intee..,

mun gode ki ajiye shi a nan ya faɗa yana ci gaba da kallon laptop dinsa cije lips din ta tayi ta ajiye turaren ranta duk a jagule kallon ta yasir yayi cikin takaici shifa wallahi bega dalilin da zai yarda yarsa me rawar kai ba ya kaita gaba da secondary batare da tayi aure ba..,

duk da abin da ni'ima take yi da halin mahaifiyar ta sam bata so ayi mata faɗa sai abin fa yarta ta ga damar yi gida ne na kishiyoyi kowa na son ya'yan ta ba kwaɓa balle harara ko wacce so take ace dan ta ne a gaba...

Ya yasir barka da yamma

barka dai ya faɗa yana ƙoƙarin tashi ba tare da ASH ya ɗagowa yace

'' ko zaki bi shi ina aiki ne..,

murmushin yaƙe tayi tace

'' okay ba damuwa sai ma ka sauke ni a hanya..,

a'a ba hanyar ki nayi ba

da sauri ta kalle sa tace '' ko kana tsoron aunty zee ta gammu..,

ai tasan ni daga ita ba ƙari domin ta tattara komai da ake so mace ta gari ta kasance

kai ta jin jina ta mai da kallon ta kan ASH tace '' na tafi..,

okay Allah ya kiyaye hanya

Ba tare da ta amsa ba ta fita duk ranta a bace har gurɗewa take dafa bango tayi ta saita kanta ganin kamar mutane na kallon ta kullum cikin daɗin baki mom take Mata amma ba wani ci gaba yau ma ba irin wankan da ba tayi ba da magunguna ga kwallin da ta saka idonta har yaji yake mata amma ta daure ta cije gashi ba amfani...

fita farfajiyar ma'aikatar tayi ta dauko wayar ta da take man a gaji tsaki ta ja ganin sunan jameel ta mai da wayar fita waje tayi ta tsaya a titi tana tarar a daidai ta duk wanda ta tara ko kallon ta ba yayi sai dai yayi gaba abin tamkar haɗin baki

gajiya tayi ga uwar rana da take dukan kanta wata jeep ce ta tsaya fara kal da ita sauke glasses din motar tayi ɗauke kai ni'ima tayi kallo saurayin ya ke binta da shi yace '' hy...beb..,

ɗagowa tayi ta kalle sa ranta a haɗe ta ƙara kau da fuska yace '' be kamata mace kamar ki tana tsayuwa a kan titi ba idan ba zaki dabu ba ki shigo na rage miki hanya ko ma na kai ki inda zaki..,

malam a kwai damuwa zaka iya tafi Nagode

haba beb karfa tun kafin ya ƙarasa ta ɗaga masa hannu tace '' dan Allah zaka iya tafiya nace maka bazan hau ba ana dole ne..?,

domin payment zaku biya ta wannan account ɗin 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay

500
Mutanen nijar kuma za su biya katin moov na 300fcfah

Sannan ku turo da shedar biya ta nan 09061890481

UWAR GAFALALLU

OUMYASMEEN

EPISODE 16-17


PERFECTLY PEN'S


Ba'a dole amma ranar nan tana dukan ki ni daman temaka miki zanyi tunda kin ki shikkenan yana gama faɗin haka yaja motar sa yayi gaba mai da hankalin'ta tayi kan titi sarai ta gane sa me wankin mota ne a bayan makarantar su haka kurum ta daukarwa kanta kara da kiyashi cikin ikon Allah ta samu napep hawa tayi ta fara danna wayar ta kamar daga sama taji danshin huƙa a wuyanta me satar wayar yace

'' dan ubanki kawo ta kona farke miki ciki..?,

jikinta har rawa yake haka ta miƙa wayar nan sannan yace

'' zo ki fita tun kafin na ci uwar ki...,

fita tayi ba ƙaramin dana sani tayi ba da bata bi wannan me wankin motar ba tsorata tayi dan haka a kafa ta dinga daɓawa tana tafiya har ta isa gida a jikace ra isa tana shiga ta wullar da jakar ta ta rushe da kuka da sauri mom ta shi go tace


'' ke rufe min baki kar maƙiyana suji suyi dariya me ya faru faɗa min..?,

yan kwatar waya na haɗu da su suka sace min waya ni wallahi wannan duk be dameni ba mom inda nake wallahi ya ASH be kalla ba balle yasan nazo

wai shi wanne irin mutum ne duk kudina da nake ɓatarwa ya tashi abanza kenan

kuka ta ci gaba da shi tace '' ai wallahi duk daddy ne ya jawo mana lokacin da ta mutu da yace gani ai ba zai iya yi mai musu ba kuma komai zai zo da sauki amma yanzu ga shinan ya jiƙa mana aiki sai ɓatar da kudade muku ba wani labari...,

ai wallahi daddy ki ban san wanne irin mutum bane sai fa dana kwarkwanta mai har gamshashshen bayani nayi mai yadda zai fahimta amma fur yaƙi

share hawayenta tayi tace '' ai da ace su waheeda ne da tuni ya yarda kullum a gidan nan sai dai adin ga tauye mu...,

bar su ni'ima akwai ranar ƙin dillanci wallahi dan wallahi malam gobe da nisa yace min na gab da mallakar komai na daddy dan haka yanzu na zage dan tsai

kwantar da kanta tayi a jikin gado idanuwanta na zubda hawaye kallon ta mom tayi tana. shafa kanta tace

'' kiyi hakuri insha Allahu komai ya ku san zuwa karshen dole ya aure ki ko yaƙi ko ya so ai jidda mutuniya ta ce dazu ta bar gidan nan na ƙara jadda da mata manufata...,

da sauri ta ɗago tace '' me tace..?,

ci gaba tayi da shafa mata kanta tace '' cewa tayi yanzu maganar da suka gama yi da Hajiya kenan amma bata ,bata amsa ba sai cewa tayi Allah ya zaɓa mai wacce tafi zama alkairi a gare shi...,

da sauri ni'ima ta tashi tace '' bamu da wata matsala da ta wuce Hajiya wallahi tun farko da ta nuna mai gani yana jin maganar ta ai ba zai ƙi ba..,

ke karki damu aure fa kamar anyi shi an gama ne wallahi kar ki sakawa kanki damuwa idan har ina doran ƙasa ko na sati uku ne sai ya aure ki

rungumeta tayi tana murna dariya itama mom tayi tana shafa gadon bayanta ta ci gaba da cewa ai idan sun san wata basu san wata ba dole ya kaso kanshi gare ki har shi a wa zai dinga wulakanta min ke

cikata tayi ta shiga dakin ta ta kwanta tana kallon ceiling har ta hangota a jikinsa kai ranar wanne irin farin ciki za tayi daga gani fa jarumini ƙara limshe ido tayi tana jinta a wata duniya ta dabam jin sallamar saudat ta miƙe zaune shigowa tayi ta nemi guri ta zauna tace

'' besty ina ta kiranki amma shiru bata shiga...,

wallahi haɗuwa nayi da yan satar waya ni'ima ta faɗa tana cire dan kunanta da kimono din da take jikinta

kawata kice yau kinga tashin hankali.. cewar saudat da take zaune kusa da ita

dariya ni'ima tayi tace

'' idan aka ce tashin hankali ɗaya kenan toni idan akwai abin da yafi tashin hankali na shiga ke kinga wuƙar da suka sakamin a wuya... wannan ita ake kira da gayawa jini na wuce..,

tab ni da nazo muyi hira ashe haka ba zata samu ba wallahi na ra inda zan saka kai na wallahi kuma kin san ba wanda nake mu'amalla dashi kuma daman ke kika nuna min wannan hanyar

haɗe rai ni'ima tayi tace

'' ban gane ba kafi ni na koya miki daman idan kin ga mutum yayi abu shi ya saka kansa zai yi amma bani na koya miki ba daman can ina sa wannan burin a zuciyar ki samun dama ne baki ba ni wallahi na gaji yanzu ma a makaranta sai da wata ta gama kwakulata tas sannan ta barni nazo gida zan huta ke kuma ki zo tun wuri kisan inda dare yayi miki ki kama wata ko kwa daidai ta..,

matsowa kusa da ita tayi tana dafa kafadar ta tace '' dan Allah ki tausaya min yi ɗaya...,

maza maza yi ina bani da lokaci
da sauri saudat ta kalleta tace

'' au ba zaki taya ni ba..?,

harara ta galla mata ta kai saudat ta gyaɗa tana cewa haka ma na gode wallahi fasha ta , ta fara lungu da sako..,

wa'iya zubilla a haka har ta biyawa kanta buƙata a tare sukai wanka suka fito mahaifiyar ni'ima na zaune a parlour ɓashar bata san me ke faruwa ba

koda suka fito ko wacce ta shiraya tamkar wani abu be shiga tsakani ba suka ci gaba da hirar su , suna tafi da shewa sai da aka kirawo sallar isha sannan ta bar gidan
dawowa tayi daga rakiyar da tayi wa saudat tace

'' mom yau naga kamar baki abinci ba...?,

ke ina zanyi iya ni da ba kirkina ba na dan adana ma samu dan abun ɓatarwa a bikin ki

zama tayi tace '' ni wallahi yunwa nake ji gaskiya ki nema mana mafita..,


wacce mafita zan nema miki yau daddy ki dubu nawa ya baki

nafa ci abinci a makaranta ta faɗa tana turo baki gaba

to yanzu ma saiki ƙara fito da wani kudin kici abinci wallahi bazan iya ba idan bikin ki ya tashi ba wanda zai temaka min kowa gani yake ina auren me kudi basu san ba abin da nake amfana da shi ba

shiru tayi mata bata ƙara cewa komai ba

TUDUN YOLA

a hankali yake tafiya da ita cikin wheelchair har ya ƙaraso da ita parlour kura mai ido tayi tana kallon ta murmushi ya sakar mata itama mai da mai tayi cikin sarkewar murya tace

'' abbey yaushe zaka kai ni gurin ummina...,

limshe ido yayi ya buɗe a lokacin ɗaya ba tare da ya ɗauki dogon lokaci yana limshe idon ba yace

"insha Allah zan kawo miki ita kinji ki dena damuwa...,

maida hankalin'ta tayi kan Hajiya kafa mata ido ba ko kiftawa kallon ta Hajiya tayi tace

'' intee na me ke damun ki...?,

idanuwanta ne suka cika da hawaye tace ''kullum abbey ce min yake zai kawo min ummina amma yaƙi Hajiya ki sa shi ya kawo min ita shi kaɗai yasan inda take ko..?,

karki damu dole ya nemo miki ita ci gaba da kallon ki baki ga cartoon ake ba

kallon tv din tayi sai kuma akai sa'a wanda take so ake haskawa na MASHA AND BEAR dariya ta dinga yi tana kauna sukan sataka a cikin farin ciki mara a dad'i

Wannan kenan

Assalamu alaikum Assalamu alaikum gyara kwanciya tayi bata amsa sallamar ba sai da hajara gwuicho ta gaji dan kanta ta shigo tana wura hanci tace

" Sannun ki ishashiya kin samu guri in kwanta kina ji ina sallama amma kikai burus to wallahi sai kin biyani kazata...,

Shazali shazali fito ka biya ta kazar ta gaban hajara ne ya yanke ya waɗi ba shiri ta matsa baya jin shiru kamar ma karya asabe take amma don tsaru ba dan tsoro ba sai ta tsaya a bakin kofa da yace ku let tace chus tace

'' Allah isaka hunu zaki kirawo daga ƙabari wallahi sai kin biyani...,

Shazali ana zagar maka uba hajara gwuicho ce yana kwance ne a daki tun dazu ya dawo dai-dai amma jin ana zagar mai uba ya fito yana muzurai da sauri hajara ta bawa ƙafarta himma tayi gaba

dariya ce ta kusan kubbucewa asabe amma sai ta danne gudu tashin hankalin shazali baya son dariya ga shi gidan shiru ba kowa ita ka daice sai mufeeda da take cikin daki tana karatun Alkur'ani

Dan haka sai ta saita kanta batare da yayi magana ba ya fita dai-dai shigowar sumy bashi hanya tayi ya fita sannan ta shigo tana cewa wallahi kyenta a haɗa kudi akai kawu shazali asibiti su garkame shi kinga abin da ya fita yana yi yau kina ga ba wanda ya zauna a kofar gidan nan

.sumy kenan gidan nan ko gadon ubanane ai na barsa wallahi infa dole ce ke zaune da ni a gidan nan yaufa sai da nayiwa kaina ruwan zafi wallahi


zama tayi tana cire mayafin ta tace

'' momcy ruwan zafi kuma..?,

wallahi bazan miki karya ba ke kinga ciwon da kafaɗuna ke yi ai wallahi na ci a zaba

Allah ya kyauta ga wannan hajiyan Dubai tace na kawo miki

buɗe food flask din tayi zaro ido tayi tana ɗaukan cinyar kaza ta zoga tana cewa wallahi wannan mata tana gatan tani ga soyayyar kazar nan tayi dad'i wallahi

gyara zama tayi tace '' momcy ai ba ƙaramin jin dadina take ba..,

kai masha Allah haka akeso wannan abu yayi dad'i wallahi mufeeda fito aciki arziki dake

ajiye kur'anin hannunta tayi ta fito tace

''momcy gani..,

fukafuki ta dauko ta miko mata tace '' ungo gashi nan ba dan halin ki ba..,

ɗan murmushi tayi tace '' wallahi nagode bana ci..,

wata dariya tayi tana buga cinya tace '' wallahi kinyiwa kanki ta ƙara auki..,

juyawa tayi ta koma daki baza ta taɓa cin abin da ya fito daga hannun sumy ba tun da tasan daga in da ya fito komawa daki tayi ta ci gaba da karatunta baba ne ya shigo da leda sallama yayi da sauri baba lami ta fito daga daki ashe tana ciki luf tayi gudun tashin hankalin shazali tace


'' yauwa gwara da ka dawo da wuri wa'yannan munafukan ina ji suna gulmar shazali shima zai dawo na faɗa mai ko wacce ta a cikin su ya fasa mata kai ta kiyaye yi da shi..,

wani yawu me kauri asabe ta haɗeye tana zare idanuwa ji tayi ta shiga wata duniya ta daban kardai baba da gaske take yau tasa ta kasa bacci lafiya domin muddin shazali yaji wannan zance tofa wallahi me raba su da shi sai Allah

Sumy ce tace

'' haba baba daga magana zamu kai shi a nema masa magani sai kuma kice muna munafurcinsa kinga duk maganar nan bata kai haka ba ga wannan nan zo kici..,

ganin uban nama a cike ta zauna tana fara gutsura cika bakinta tayi ko tsayawa tauna ba tayi haka ta dinga ci magana take amma maganar bata fitowa miƙa musu ledar baba yayi da sauri ta amsa tana buɗe wa ganin shinkafa da wake ta turawa asabe tace


'' waike asabe wacce irin mace ce ba ladabi ba biyayya balle sanin ya kamata mijin ki ya dawo ba sannu da zuwa kin tsaya kina kallona..,

baƙin ciki ne ya ishe ta ba gwara ta faɗawa shazali ba duk abin da ya ga dama yayi musu idan ya so ta kulle kofar ta ta cinye kayar ta amma shine sumy ta bata ga baba da karnene duk tabi ta kanainaiye flask din cikin takaici ta zura hannu zata dauki wata tsoka da sauri baba ta riƙe hannunta tare da gallamata muntsini ta ture shi gefe

ko kayan da baba ya zo da shi ba ta tsaya ɗauka ba ta shiga daki ai tashin hankalin shazali ba yau suka saba gani ba Allah ya saka ya shigo ya rutsa su yaci ubansu..,

Momcy dan Allah zaki bani kuɗin sauka

banza tayi mata ta nemi guri ta kwanta ƙara mai maita maganar mufeeda tayi a fusace tace

'' mu feeda bani da kuɗin sauka dan haka kiyi hakuri gaba kya yi idan ubanki ya nemi abin yi duk bashi ya jaja mana zama a gidan gado ba baka da sakat kai Allah ya kawo karshen ta'addancin shazali ya mutu kowa ya wuta yau za ta nayi kafata ta cire ba zara ƙara moruwa ba..,

Momcy mutuwa fa kikace

mufeeda kinga laifina ne da har zaki shiga tashin hankali irin su shazali mutuwar su ita ce hutu..,


DOMIN FARA PAYMENT

ZAKU BIYA TA WANNAN HANYAR

8141785374

AMINA ALHASAN MUHAMMAD OPAY

KU TURO DA SHEDAR BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN

UWAR GAFALALLU

OUMYASMEEN

EPISODE 18-20

Gaskiya hakan be dace ba yanzu idan baba taji ba zata ji dadi ba

dan ubanki kar taji dadin ba ita taka wo mana jaraba gida ba yau idan na faɗa miki tashin hankalin da shazali ya saka ni a jiki ba zai musaltu ba mufeeda har cewa yayi zai tura kaina a wuta shikkenan ya kashe ni ya mai da ku marayu

Zaro ido mufeeda tayi tace

''kullum abin nasa ƙara tsamari yake Allah ya yaye mai..,

ki dinga haɗawa da idan zai sami sauƙi Allah ya bashi lafiya idan ba zai samu sauƙi ba Allah ya ɗauki ransa mu huta wannan jaraba har ina duk a kaina abin ya ke ƙarewa...

balla yayi da tinkiyar baba lami ta saki wani gigitatcan ihu da sauri asabe ta, tashi ta kulle kofa tana cewa Allah isaka ya fasa mata kai ta mutu kowa ya wuta yinin yau na yi shi cikin tashin hankali ne ba wanda ya zo siyan wiwi kowa yana tsoron shazali

sumy ta dake tsakar gida tuni ta miƙe zata gudu yace

'' yi zaman ki wannan tinkiyar da kike gani yar iskace tana ɗaya daga cikin karuwan da asabe take tarawa..,

ikon Allah aikuwa ta cancanci duka gwara ka ballata

da sauri baba ta fito tace

'' shazali me tinkiyar nan tayi maka kake neman naƙasta min ita...?,

banza yayi mata ya wuce garbati da haladu suka shigo garbati yace

'' asabe reza faka faka zo kafin wannan mara M din yayi mana cin kai yasin ina gab da zura kanshi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment