Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito da dan saurin sa, mantuwa yayi dan har ya kusa zuwa office ya tuna shine dalilin dawowar sa. Sarai ya ga Adam a compound din ya kuma san ganin shigowar sa ya hana shi shiga ciki amma sai yayi kamar be ganshi ba, yayi wucewar sa da dan saurin sa, bin bayan sa yayi suka shiga a kusan tare a lokacin tana zaune bayan fitar su Raihana tana amsa waya tana dariya cikin jin dadi, ganin Aryan a lokacin yasa ta yin saurin katse wayar tana fata da addu'ar Allah yasa be hadu da su Raihana da suke fita yanzu ba, dan ta tabbata idan yasan akwai wata alaka tsakanin su ba zai taba accepting dinta ba.

"Son me ka dawo yi?" Tace tana mikewa tsaye cikin yanayin rashin gaskiya

"Akwai abinda zan yi." Yace a gajarce yana hayewa saman da dan saurin sa, kallon Adam tayi da yake tsaye daga baya tace

"Ya hadu da su Raihana ne?"

Girgiza mata kai yayi

"Basu hadu ba, dan su ta gaba suka bi shi kuwa ta baya yake shigowa."

"Ok." Tace daidai lokacin ya dawo ya sake wuce su ya fice cike da sassarfa. Tsaki taja me tsawo bayan ya fita, bata son ganin sa tamkar yadda yaki jinin ganin ta, ta sani kuma tana da yakinin da za'a bashi damar kashe mutum daya a duniyar nan toh tabbas da itace kai tsaye, sai dai be sani ba, tsanar da tayi masa har ta ninninka wadda yake mata, dan ita baki daya rayuwar ta da tsanar sa ta ginu, fiye da yadda ta tsani mahaifiyar sa, shikuwa a baya ya sota, so me tsanani har baya iya bacci ba tare da ya ganta ba, ya mata irin son da d'a yake wa mahaifiyar sa ko ma fiye da hakan.

***Washegari ta tashi cikin shirin zuwa wajen aiki, ta shirya cikin shigar doguwar rigar atamfa A shape me gajeran hannu sannan ta dora NYSC jacket dinta a sama ta yi rolling mayafi medium akanta sannan ta dora pcap din a sama. Jakar ta, ta dauka ta tura takardar da sauran abinda zata bukata ta fito falon ta samu Adda Maimuna zaune tare da Abban su Amina, ta durkusa ta gaishe su sannan tace zata tafi, kudi ya dauko ya bata sannan ya saka mata albarka.
Har gaban gate din me napep ya kai ta, ta sauka ta karasa wajen masu gadin dake zazzaune a kan benci ta gaishe su sannan ya fada musu abinda ya kawo ta, ciki suka ce ta shiga ta hau sama tayi godiya ta wuce ciki. A reception ta samu wata mata zaune tana shigar da abu cikin desktop, matsawa tayi ta gaishe ta sannan tace mata sabuwar corper ce ita, takardar ta karba ta duba sannan tace ta hau sama office din oga Kamal, godiya tayi ta wuce zuwa saman tana dubawa har ta kawo office din nasa, Knocking ta yi akofar kad'an ta jira aka ce ta shigo sannan ta tura kofar bakin ta dauke da sallama, yana tsaye yana duba wasu takardu tare da head supervisors na company suna magana akan sells din da kowanne gidan mai ya kawo a satin gaba daya, shigowar ta yasa su tsayawa ta karaso ta dan russuna ta gaishe su kafin ta fadi abinda ya kawo ta ya rigata cikin sigar tsokana yace

"Corper we!"

Murmushi tayi ya nuna mata wajen zama yace ta zauna ta basu minti biyu, ta zauna suka cigaba da dubawa har suka gama, sannan ya tafi shi kuma ya zauna a kujerar sa sannan yace ta taso, ta taso tazo ta zauna ta gaishe shi ya amsa a sake da tambayar camp, ta amsa itama tana murmushi

"Ok welcome to Mukaddas and sons." Yace yana mika mata hannu ta bashi posting letter din tata

"Thank you." Tace ta mika masa cike da girmawa ya duba ya saka hannu a wajen da ya kamata ya saka sannan yace

"Bari na bawa Oga kwata-kwata ya saka hannu anan, bani minti biyu."

Ya mike kenan aka dan yi knocking sau daya kafin ya turo kofar ya shigo kansa tsaye

"Ina stamp din office dina?" Yace yana shigowa

"Gashi nan dazu aka kawo, sai kuma Faisal ya shigo zan kawo maka kenan, dama yanzu office din ka zanzo we have a new corper."

"I don't think muna bukata, reject her."

Yace ba tare da ya kalli ko in da take ba, ya dauki stamp box din ya juya zai fice

"Wait please , we need her saboda field din da ta karanta."

"Regardless! Just reject her please wahalar corpers din nan yawa ne da ita."

Yayi ficewar sa kawai, wata kwalla ce ta ciciko a idanun Raihana, ta tsani wulakanci a rayuwar ta, sai kace wadda tazo neman aljanna zaa wulakanta ta haka. Dawowa Kamal yayi ya zauna yana girgiza kai

"What a tough guy! Sorry please don't be offended, I'm coming."

Ya tashi ya fita da sauri, share kwallar tayi da bayan hannun ta, tana jin duk shaukin da take dashi na zama a wajen na gushewa.
A zaune ya same shi yana latsa computer as if nothing happens, ajiye masa takardar yayi a gaban sa yace

"Please sign and stamp here, idan kuma ban kai nayi making decision anan ba sai na sani."

Dagowa yayi ya tsaya da abinda yake ya kalle shi, sannan ya kalli takardar kad'an kafin yace

"Me yasa kake so mu dauke ta?"

"Haka kawai nake so, coz naga zatayi amfani, computer science ta karanta."

Be ce komai ba, yaja takardar gaban sa ya dauki biro yayi signing a wajen da ya kamata yayi sannan yayi stamp ya tura masa yana maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Dauka Kamal yayi ya fice shima be ce komai ba, bayan sa yabi da kallo ya girgiza kai karon farko da yaga me irin sunan ta

_"Raihana."_ ya furta a chan kasan makoshin sa, wani memory me matukar muhimmaci a rayuwar sa ya shiga yi masa yawo aka, ko suna wacce duniya a yanzu? Allahu a'alam.

***Zuciyar ta a chunkushe ta bar office din, sam bata ji dadin abinda ogan yayi mata ba, ko ba komai mutum ba abun wulakanci bane ba. Tana tafiya a kafa ta kusa karasawa titi wayarta tayi kara, ta kalli screen din ganin me kiranta ya sakata dauka da dan sauri ta daidaita muryar ta sannan ta gaishe ta

"Ok gani nan."

Tace cike da zumudita tura wayar a jakarta sannan ta tare napep tace ya kai ta KURMAWA. Motar ta, ta hango an yi parking dinta a chan gefe, ta sauka ta karasa ta danyi knocking, sauke glass din tayi tace ta shigo, ta zagaya dayan bangaren ta shiga, driver ya tashi motar suka nufi cikin prison din.

Jikin ta gaba daya yayi sanyi tunda taga an shigo ciki, a waje ta hangi mutane a layi masu son samun shiga ciki domin ganin yan uwan su, sai an fara baka takarda ka shigar da sunan Ka sannan ku samu shiga ciki shima sai ku zazzauna a wasu kujeru kuna jira har a zo kanku sannan ku shiga ciki bayan an baku tag kun makala a wuyan ku. Su kuwa kai tsaye suka wuce duk wannan layin har ciki sukayi parking, manyan gandurobobin ne suka fito suka tare su, suka dinga kwasar gaisuwa ita dai Raihana sai kallo take yi, ciki suka shiga kai tsaye zuwa wani office suka zauna sai gashi an kawo mata tag din an ce ta taso, cike da zumudi ta mike suka fita, ta hade hannun ta waje daya saboda yadda suke mata wani iri. Wani dan daki aka ce ta shiga ta zauna ta jira, ta na zaune akayi sallama ta juyo da sauri, bata san sanda ta fashe da kuka ba,ta tashi ta rungume shi cikin kuka

"Abby na."

"Uwata... Kece da kanki? Ke kadai? Masha Allah Alhamdulillah."

"Toh ya isa haka na, bar kukan ki zauna muyi magana, ya isa haka." Yace yana shafa bayan ta, shiru tayi ta zauna tana kallon sa cike da tausayawa

"Abby ina wuni?"

"Lafiya lou Raihanata, kece kika zo ganin abbinki da kanki?"

Gid'a masa kai tayi

"Basa so su zo dani kwata-kwata bansan me yasa ba."

"Basa so kiyi kuka ne, amma kullum suka zo sai sun nuna min hotonki sannan sai sun yi ta min hirarki."

"Abby yaushe zaka fito?"

"Saura kiris kinji? Ki cigaba da min addu'a, sannan ki rike min mutuncin ki a duk in da kika samu kanki, sannan duk runtsi karki ci amanar wadanda suka aminta dake, ki zama me riko da gaskiya da amana duk runtsi."

"In sha Allah Abby, zan zama me bin maganar KU."

"Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya baki sa'a a duk abinda kika saka a gaba dake da Yan uwanki, ki musu biyayya domin su ne iyayenki a yanzu da nan gaba ma."

"In sha Allah." Tace tana cigaba da kukan da ta dan tsagaita da, sun dan dau lokaci suna hira har sai da yayi mamakin dalilin da ya saka aka barsu suka dade haka, amma be kawo tunanin komai ba, suka sha hirar su sannan tayi masa sallama cike da kewar sa, ta koma office din farkon nan jikin ta a sanyaye. Kayan provision ta gani a zube ana maganar su, ta shigo

"Yawwa Raihana, gashi nan za'a bawa Abban ki, tunda zuwan bagatatan ne baki zo masa da komai ba."

"Nagode sosai Anty, Allah ya saka da Alkhairi."

"Amin Amin, officer bari mu koma, thank you so much, sai ka jini."

"Ba komai Hajiya, dan Allah a mika mana gaisuwa wajen Alhaji, muna shan abin arziki sosai sai dai fatan Allah ya kara girma da arziki."

"Ba komai." Tace suka fito ya rako su har mota suka shiga, sai da yaga tafiyar su sannan ya koma ciki.

Sanda suka hau titi sosai ne Hajiya Zeenat ta riko hannun Raihana, ta saukar da kanta k'asa cikin yanayin damuwa tace

"Ina cikin damuwa Raihana, damuwa me tsanani."

"Allah ya yaye miki damuwar ki Anty." Tace cike da tausayin matar me tsananin kirki da karamci

"Kina so ki san matsalar da nake ciki Raihana?" Gid'a mata kai tayi da sauri

"Ko da yake be kamata na dora miki nauyin damuwa ta ba, ke yarinya ce, amma inaso kiyi hakuri da taka tsantsan da halin Aryan."

"Aryan?" Tace tana kallon ta

"Eh Aryan, ina kyautata zaton kin hadu dashi yau a office da kike je."

"Shine oga?" Tace da sauri

"Shine, yana da zafin rai da wani irin hali, shine kadai damuwa ta a yanzu, ina kaunar sa tamkar yadda nake kaunar raina, sai dai..."

Sai tayi shiru kamar me tunani

"Shikenan Raihana, zamuyi magana wani lokacin kinji?"

"Tam." Tace a kasalance abinda yayi mata dazu ya dawo mata, lallai yana da babbar matsala idan har zai iya saka mace kamar Hajiya Zeenat a cikin irin damuwar da ta hanga a cikin idon ta.
A hanya suka sauke ta, tayi godiya ta tsaya jiran abun hawa, sai ga kiran Hamman ta, da sauri ta daga tana dan matsawa baya daga titin.

"Kina ina?" Dadah tayi maganar tana jin an daga

"Daadah na, yanzu nake neman abun hawa zan tafi gida, yau ce ranar farko da na fara zuwa in da akayi posting dina."

"Shikenan, ki kula da kanki kina zuwa ki kirani kinji?"

"Tom." tace muryar ta a sake ba tare da tayi tunanin komai ba.





*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

*RUMBUN QAYA*


Free Page 4

©® *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥

_____________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼♀️⛹🏼♀️⛹🏼♀️._*.


•••••••

Daga kansa yayi ya kalli kofar da akayi knocking kafin yace

“Yes!” Turowa yayi ya shigo fuskar sa ba yabo ba fallasa,yanayin sa Aryan ya kalla kafin yace

“Akwai matsala ne?” Girgiza masa kai yayi kafin ya zauna, sannan yace

“A ah, maganar da na saba dai kullum ita ta kawo ni yanzu ma, dan Allah ka rage zafi Aryan."

Bata fuska yayi yana duban Kamal din yace

"Me kuma nayi?"

"Yadda kayi ma yarinyar nan dazu, ba dadi."

"Ni ba abinda nayi mata, iya gaskiya ta kawai na fada corpers din nan basa da wani amfani."

"But ai be kamata ka fada a fuskar ta ba."

"Toh naji, wai ka santa ne?"

"A ah me ka gani?"

"Yadda kazo ka titse ni mana akan ta."

"Ni dai kawai ka yarda bakayi daidai ba, mata suna da rauni sosai, hakan zai iya effecting dinta."

"I don't believe you, they are very cunning, sun iya shedding crocodile tears."

"Banda Raihana." Yace yana murmushi

"Raihana?"


"Yes! Baka ga sunan ta a jikin takardar ta ba?"

"Ban karanta ba ai."

"Amma kayi signing?"

"Ina da wani option ne?"

"You are not nice wallahi, ai shikenan. Nace ta fara zuwa gobe sai ta dinga zuwa sau uku a sati,ta zauna a cash office muga abinda zata iya."

"Cash office? Why not reception? Ko su zauna dasu Zainab."

"A ah, karatun ta ya wuce haka nan, taje dai cash office din su yi aiki tare da su abdulhakeem."

Mikewa yayi ya dauki rigar sa da ya sakale a jikin kujerar da yake zaune ya dora ta a saman t-shirt din dake jikin sa, ya kwashi wayoyin sa ya zuba su a aljihu sannan ya kalli Kamal din da ya mike tsaye shima yana daukar wani file a saman desk din Aryan din yace

"Zan je naga Ya Nabeela."

"Kaga da ba dan wannan aikin da yake gaba na ba, da munje dan na kwana biyu ban shiga ba, nayi missing daddad'an girkin ta

"Muje mana, ba dadewa zan ba nima muna da meeting da shareholders da karfe biyu, so har ma dawo ma."

"Ok toh bari na dauko wayata a office."

"Ka sameni a parking lot." Yace yana yin gaba, suka fito a jere shi yayi k'asa shi kuma Kamal ya koma office dinsa ya dauko wayar sa ya rufo.

A harabar wajen ya same shi tare da Malam Musa suna magana akan sabbin motocin da suka siyo na mai wanda zasu iso anjima, gobe yake saka ran dawowar Daddy shiyasa ma zai yi duk kokarin sa wajen ganin ya kammala duk ayyukan da ya tafi ya bari. Hango Adam yayi ya fito daga dayan block din da yake kallon nasa, ya nufo su ya sakashi katse maganar da yake niyyar yi ta hanyar cewa

"Bari na dawo Malam Musa zamuyi magana."

Ya nufi motar sa, Kamal da ya fuskanci dalilin da ya sashi barin wajen yayi saurin bin bayan sa ya shiga motar, yaja suka bar wajen.

"Malam Musa biyo ni office."

Adam yace ya juya ganin sun watse ba tare da sun bari ma ya karaso ba, bin bayan sa Malam Musa yayi ciki yana ayyana abinda Adam din zai tambaye shi wanda ya saba tambaya a duk sanda ya gansu tare da Muhammadun suna wata magana.

***Wayar sa ya dago da tayi kara ya daga ganin Ya Nabila ce, sukayi magana ya ajiye yana maida hankalin sa akan tukin da yake yi. Kamal ne ya karya shirun da yayi ta hanyar sako maganar Adam

"Menene matsalar sa wai?"

Yace yana duban Aryan din da kansa yake kallon titi cikin yanayin da zai yi wuya ka iya tantance abinda yake ransa

"Matsalar sa ta wuce ni?"

"Allah ya kyauta, yaushe Daddy zai dawo?"

"Gobe in sha Allah, bansan ko daga goben zan sake shigowa office din ba a cikin week din, dan nima inaso na danyi wani aiki a office dina."

"Ka daure dai ka shigo please, shi kansa Daddy yanzu baya iya dadewa a company dole dai kai ne kasan dai ba za'a sakar ma Adam komai ba ko?"

"Kana mamakin hakan? Daddy yana ta shirye-shiryen bashi share me tsoka a company din."

"Are you serious?"

Dage kafadarsa yayi irin I don't care din nan sannan yace

"I'm serious, abinda suke ta planning kenan."

"Then me ka shirya?"

"Ban shirya komai ba, na gaji ma baki daya ta zuwa company wallahi, na matsu ayi a gama na cike wa'adin da daddy ya daukar min nayi gaba, be damen ba wajen nan ko kad'an, buri na daya ne kuma ka sanshi, so bana bukatar wata dukiya ko wani fame, su suke ta wahalar da kansu I'm willing to give everything in dai zan samu cikar buri na."

Murza saman goshin sa Kamal yayi cikin yanayin damuwa yace

"Nasan yadda kake ji, ka sani kowanne tsanani yana tare da sauki, in sha Allah komai zai wuce kamar baa yi ba, zaka dawo rayuwar ka tamkar yadda kake a baya, in sha Allah."

"In sha Allah, amma bana tunanin hakan Kamal,karka manta ina fama da PTSD (Post Traumatic Stress Disorder )."

"Na sani, amma zaka samu sauki in sha Allah, mu cigaba da addu'a sannan ka cigaba da ganin therapist dinka kana shan dukkan magungunan ka, zai wuce."

"In sha Allah!" Yace daidai lokacin suka karaso gidan, yayi horn megadi ya bud'e musu suka shiga ciki.

Amna ce a gaba Amaani na bayan ta cikin rige-rigen zuwa yi masa oyoyo, sune kananan yaran Ya Nabeela sai yayyane su biyu Affan da Hadiyya. Daga su yayi sama a tare cikin tsananin kaunar su, ya rungume su a jikin sa yana dariyar da ba zaka taba ganin yayi ta ba in dai ba yana tare da su ba. Sai da ya gama daga su sama sannan Kamal ya dauki Amaani shi kuma ya dauki Amna suka shiga ciki suna musu surutu.
Hadiyya da Affan na zaune sun saka Ya Nabeelan a tsakiya suka shigo, tashi sukayi su ma suka zo wajen su suka yi hugging dinsa sannan suka zauna duk suka mamuke masa.

"Ku barshi ya zauna mana sosai Affan, kun bi kun dabaibaye shi kamar yau kuka fara ganin sa, sannun ku da zuwa kanina."

Ta karashe tana kallon Kamal

"Sannu da gida Babbar Yaya."

"Sannu Kamal, ya gida ya aiki?"

"Alhamdulillah wallahi."

"Masha Allah."

"Small mom ina wuni?"

"A ah gama da yaranka, sai mu gaisa." Tace cikin sigar tsokana, murmushi yayi ya gyara zaman sa sosai yana daidai ta su suma sannan ya gaishe ta, ta amsa tana masa murmushi me dauke da kaunar da tausayi a lokaci daya, murmushin shima yake ta tashi ta kawo musu abinci sannan ta kora su Amna dakin su ta saka musu kallo ta dawo suka sake gaisawa sosai suka dan taba hira, ta dauko wasu takardu na maman su ta bashi ya bud'e ya dudduba sannan ya mikawa Kamal shima ya duba. Daga nan suka tashi sukayi mata sallama yaran suka rakosu har mota tare da ita, ya dauko musu chocolates dinsu a baya da ya manta da ita ya basu sannan suka koma office dan lokacin meeting din nasa ya kusa dan sai da suka kara sauri idan ba haka ba da ya makara.


***Tana fesa turare ta gama shiryawa Amina ta shigo, ta zauna tana kallon yadda tayi kyau cikin shigar riga da skirt na atamfa orange and mint green ta yafa orange veil wanda yayi matukar haska ta kasancewar ta fara sosai, tana son gayu a rayuwar ta duk da komai nata very simple ne amma tasan marching colours sosai shiyasa Amina take jinjina mata dan da gaske yar gayu ce ta bugawa a jarida, koman ta very unique and classy haka take yin sa. Tafa mata hannu tayi a saman fuskarta

"Meena wannan kallon fa?"

"Kin ganki kuwa Adda Raiha? Wallahi kayan sun miki kyau sosai, kar kije office kisa guys su dinga karo fa."

"Look at you, me wannan shigar yayi da har za'a yi karo, ni tsoron zuwa ma nake wallahi, boss din bashi da kirki ko kad'an, irin masu wulakancin nan ne kinsan masu kudi dangin mala'u."

"Allah? Wulakanci sukayi miki?"

"Bari kawai, dan tsabar wulakanci wai fa a gaban ido na yace wai ayi rejecting dina, hadda cewa wai corpers basu da wani amfani."

Dariya Amina ta fashe da ita ganin yadda Raihanan take tsuke fuska tana bada labarin

"Kice kin hadu da mara m, toh ya akayi kuma suka karbe ki?"

"Oga Kamal ne yaje ya same shi a office ko me suka ce oho, sai gashi ya dawo da takardar tawa anyi signing da stamp a jiki."

"Ok Allah sarki, shi me kirki ne Kamal din."

"A ah sosai wallahi, baki ga yadda ya dinga bani hakuri ba wallahi, har fa kuka nayi saboda takaici."

"Ai da haushi wallahi, sai kiyi takatsantsan dashi sosai, Allah ma yasa ba shine zai dinga baki monthly clearance ba."

"Da na kad'e har ganye na wallahi."

"Allah ma yasa dai ba shi din bane ba, dan ma dai an ce ba ma wani zuwa PPA din mutane suka ba."

"Ameen, idan ka hadu da supervisor me kirki ba, bari kiga na tafi yau farko kar nayi late nayi laifi."

"Sai kin dawo, ni sai rana nake da lectures ba ma lallai naje ba gaskiya."

"Ok." Tace ta zura takalmin ta suka fito a tare, taje tayi ma Adda Maimuna sallama sannan ta tafi.

Kasancewar safiya ce bata wani sha wahalar abun hawa ba, nan da nan sai gasu a gaban wajen, ta sauka ta biya ta shiga takawa zuwa ciki. Gaisawa sukayi da masu gadin wajen dan sun gane ta zuwan da tayi, ta wuce ciki kanta tsaye. Babu cikar ababen hawa a harabar wajen hakan ya tabbatar mata da ba'a gama zuwa ba ko kuma ma dai tana cikin farkon wanda suka fara zuwa a yau din. Cikin reception din ta shiga ta tarar da wani namiji shi kadai yana zaune gaban computer, matsawa tayi suka gaisa tayi introducing kanta yace ta hau sama ta jira zuwan Oga Kamal, saman ta hau babu kowa sai Zainab tana gyara tarkacen da yake kan desk dinta. Itama gaisawa sukayi ta bata wajen zama tana dan satar kallon ta dan jiya da tazo bata nan sun fita da su Samuel.
Tana nan zaune har aka dinga zuwa da kad'an kad'an, sai gashi wajen ya cika still dai tana zaune tana bin kowa da kallo tana jiran zuwan Kamal wanda take ganin kamar ba zai zo ba.

"Sir Aryan is here." Taji Zainab din ta fada daidai lokacin ta wani kamshin turare me sanyi da dadin kamshi a mamaye ilahirin wajen da suke. Takun tafiyar sa ce ta fara isowa in da suke bayan kamshin sa da ya gama karade wajen baki daya. Manyan kaya ne a jikin sa sabanin jiya da yake sanye da suit ash grey colour. Fuskar sa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment