Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kamal yace cikin rashin jin dadin abinda Aryan din yake wa yarinyar, ya rasa dalilin sa kuma ai ba haka yake wa su Zainab ba, ba kuma itace corper ta farko da aka fara kawo musu ba. Ajiye cup din tayi ta raba ta gefen su ta fice ranta babu dadi. Tana fita Kamal ya tura kofar ya dawo wajen sa

"Why are you like this dan Allah? Why are you soo mean to her? Me tayi maka?"

"Babu abinda tayi, aiki tazo ba gulma ba naga, me yasa zata zauna taana fada maka laifi na."

"Tsakani da Allah baka kyauta ba, ka kira ta kace tazo, bayan kasan ka samu paper din."

"Bayan na kiratan ba."

"Then you should have call her again kace ka ganta."

"I forgot."

"Anya? Anya kuwa?"

"Me?"

"Ban gane maka ba kwata-kwata."

"Ba zaka taba ganewa ba kuma ba."

Ya bud'e kofar yayi ficewar sa.

***Ko da ta fito daga kitchen din bata tsaya ko ina ba, tayi ficewar ta dan ba zata iya zama ba, yayi masifar bata mata rai yau din nan, me ya dauki kansa? Me yake ji dashi? Ta manta shaf da kiran da Hajiya Zeenat tayi mata kuma duk shi ya rikitata,sai da taji wayar ta na kara ta tuna tana ciro ta taga Hajiya Zeenat din ce.

"Dan Allah Anty kiyi hakuri wallahi mantawa nayi ban kira ba."

"Ba komai 'yata, nasan ba zaki da gangan ba, ya aiki?"

"Lafiya Lou, ina wuni?"

"Lafiya alhamdulillah, dama kira nayi naji babu wata matsala ko? Ina nufin bangaren Aryan kinsan halin nasa sai hakuri."

Kamar me jiran kiris, kawai sai ta ji hawaye na sakko mata, ta share su cikin muryar kuka tace

"He's very rude Allah Anty, ya tsaneni bansan me nayi masa ba."

"Subhanallah, me ya faru?"

"Bansan me nayi masa ba, komai nayi ban iya ba, a gabana sai yayi ta fadamin magana, ni wallahi na gaji."

"Nasan zai aikata fiye da haka, amma dan girman Allah kiyi hakuri, kiyi hakuri a madadin sa, kiyi hakuri."

Jikin ta ne yayi sanyi jin yadda Hajiyan take bata hakuri, har sai da taji nauyi da kunya, taji dama bata fada mata ba.

"Ya wuce in sha Allah, ba zan sake damuwa ba ma duk abinda zai yi mun saboda ke Anty."

"Nagode sosai Raihana, nagode."

"Ba komai."

"Akwai wata alfarma da nake nema a wajenki Raihana, wani taimako nake so kiyi min dan hakan ne kadai zai taimaka Aryan ya rage wannan halin nasa, taimakon sa zanyi amma baya so kowa ya taimaka masa, yana da yar matsala ne wadda ba kowa ne ya sani ba, kuma baya shan magani ko kad'an, duk da bani da hujjar hakan saboda ya toshe duk wata hanya da zamu gane amma ni nasan baya sha din, akwai in da yake boye su, tun wuri gwara a shawo kan matsalar kafin abun yazo yafi karfin mu, tunda bani da wata shaida shiyasa na kasa yin komai akai, dan ko nayi yunkurin fadawa Alhaji sai na kasa saboda zai bukaci shaida, shiyasa nake so ki taimaka min mu ceto shi daga fadawa cikin wahala. Dan Allah Raihana "

"Bana jin akwai abinda zaki nema a wajena na kasa yi miki in sha Allah, zanyi komai dan ganin kinyi farin ciki."

"Nagode sosai Raihana, nagode zan neme ki idan an kwana biyu, zaki ji abinda ya kamata kiyi ta nan bangaren ki."

"Shikenan, Allah ya rufa asiri, nagode."

"Amin nice da godiya."

Dariya suka kwashe da bayan ta ajiye wayar,

"Wawuyar yarinyar halin ta sak na mahaifiyar ta, dama ai barewa bata gudu danta yayi rarrafe."

"Yaro be san wuta ba sai ya taka ai Hajjaju, ke din duniya ce in dai ta wannan fannin ne."

Dariya suka kara yi a tare.

"Da alamu tarihi ne zai maimaita kansa."



*RUMBUN K'AYA*๐Ÿ”ฅ

*DAUDAR GORA*๐Ÿ”ฅ

*IDON NERA*๐Ÿ”ฅ

*A RUBUCE TAKE*๐Ÿ”ฅ

*KI KULANI*๐Ÿ”ฅ

*_uhmmmm_*๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*โ˜บ๏ธโ˜บ๏ธ

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*๐Ÿ”ฅ



RUMBUN QAYA*


Page 8

ยฉ๏ธยฎ๏ธ *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F9Fgin7INwl2MLGe0vpoEh

๐ŸŒน KUDI KE KIRA

๐ŸŒนDon Neman Karin Bayani a Tuntubi Wannan number..

๐Ÿ”ฅ 09112842587

๐ŸŒนKo kun San akwai Wasu 6oyayyun damar Maki Wanda tun waccan shekarar data gabata mutane suke cin moriyar su..???

๐ŸŒน An shirya wannan program din don canza Tsarin kasuwancin matasa da Mata Zuwa kusuwancin zamani

๐ŸŒน Inda za'a koyar da Mata sanaoi iri daban-daban

๐ŸŒนKamar yadda Sunan Shirin yake wato KUDI KE KIRA... tabbas za'a koya muku yaya ake Kiran kudi su zo kuma su zauna har su dinga Kiran 'yan uwan su...Ta hanyar koyar daku hanyoyin Neman su da kuma yadda za'a dinga kashe su

๐ŸŒน Business sai da Traffic is a game of Numbers Dole Sai da jama'a...shin ta yaya ake Nemo jama'ar? Right Target audience sune jama'ar ku

๐ŸŒน Kullum kuna sana'a Babu customers..?? To Albishirin ku za'a koyar daku building contacts yadda zaku Kawo mutane what's app din ku...Hatta yadda Zaku hada file na contacts Gain Yana cikin Abinda za'a koyar a wannan Training din..

๐ŸŒน Cikin abubuwan da za'a koyar na sanaoi kadan daga ciki sune...Skin Care products, graphics, digital marketing, Gyaran jiki na sudan da chad, turaren wuta,na daki,na tsugunno,na tsinke,humra,body lotion, cream,izal,airfreshner, oils perfumes, wardrobe Balls, Sabulun wanka, Sabulun wanki,hypo,etc

๐ŸŒน Program din zai kasance cikin yare guda biyu wato Hausa da Turanci za'a kammala Shirin cikin Kwanaki goma in Sha Allah Stay Turn

๐ŸŒนBayan kammala Training din

๐ŸŒนZaki Sami certificate na shaidar kammala kyauta

๐ŸŒนBa Sai kina da Data ba...kina yin Register kungiya Zata baki Data kyauta har ki kammala Training din

๐ŸŒนZasu yi Miki website design kyauta

๐ŸŒนZasu koyar dake Kasuwanci Kyauta irin Wanda kika zaba

๐ŸŒนZasu yi Miki Logo na company ki kyauta

๐ŸŒน Goggle my business account kyauta

๐ŸŒนTallata muku kayan ku a yanar gizo kyauta

๐ŸŒนZaku Sami Product guda daya Kyauta da kungiyoyin suka tanadar Muku don Gyaran jiki da magance matsalolin Infection da saukar da niima ( Maganin Herbal ne 100%Natural )

๐ŸŒน Yiwa Business din ku CAC Register kyauta

๐ŸŒน Yadda zaku Sami Rancen Kudi,ko nawa mutum ke bukata ku juya kuyi business ku maidawa kungiya kudin ta ( da yawa suna da ideas na business amma Babu Jari..don haka wannan babbar dama ce ayi amfani da ita don dogaro da Kai)

๐ŸŒน Kadan Kenan daga cikin Abinda program din ya kunsa mu kasance cikin group don samun Sauran bayanan Masu yawan gaske

๐Ÿ’ฒayi Sharing Link din don sauran Mata su amfana da wannan Shirin



_________โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ข


***A gajiye likis ta koma gida, ga uwar yunwa ga ranta da yake a chunkushe, ko abincin kirki kasa ci tayi duk da yunwar da take ji ta zauna shiru tana bitar abinda ya faru dazun. Wajen la'asar ta tashi ta je dakin Adda Maimuna ta tambaye ta abinda za'a dafa da daddare duk da ba ko yaushe ne take shiga kitchen din ba amma in dai tana nan, tana taimakawa sosai ayi duk aikin da za'a yi da ita, ba zata zauna ta lafe komai sai dai ayi mata ba, irin wannan zaman gundurar masu gidan kake yi shiyasa take shiga ayi duk abinda za'a yi da ita, ta lura kuma hakan na faranta ran Addan shiyasa ma take sake dagewa wajen ganin ta zauna lafiya dasu a dan zaman da zatayi.
Tuwo tayi miyar kubewa daf da magriba ta gama ta gyara kitchen din tas, sannan ta dora indomie dan bata jin cin tuwon kawai gashi kuma tana jin yunwa tunda da rana bata wani ci abincin ba. Tana cikin cin indomie din Oga Kamal ya kirata, ta daga da yakinin dalilin da ya saka shi kiran nata. Hakuri ya bata akan abinda ya faru dazun ya kuma yi kokarin nuna mata sam hakan ba halin Aryan din bane ba, shi kansa be san dalilin da ya saka yayi acting haka toward her ba,amma sam tsakanin sa da ma'aikatan ba haka bane ba. Ta dai ji shi ne ba wai dan ta yarda ba, dan ita bata ga duk abinda ya fada din ba,tunda dai ita be mata ba.
Tattare wajen tayi ta kai plate din kitchen ta dauraye shi sannan ta dawo falon ta samu su Muhammad suna kallon ball ta zauna kawai dan idan ta koma dakin ma babu abinda zatayi, ga Amina yau ba ta dawo ba ta tsaye gidan Anty Saliha babbar yayarsu watakila ma ta kwana a chan.


***Rashin neman sa da Daddy be yi ba jiyan sai ya zata ya manta ya cigaba da sabgogin gaban sa, yana raba kafa yaje nasa office din yaje na gida, baya shigowa gidan sai dare sosai kuma dan baya son abin magana, haka kuma da safe da wuri yake ficewa ya wuce gidan sa ya karasa shiryawa a chan daga nan ya tafi aiki, haka yakeyi a kwana biyun sai dai yau yana shigowa sai ga Daddy a falon k'asa shi da Adam da tarin takardu a gabansu daga gani wani muhimmin aikin sukayi tunda har suka kai wannan lokacin, ji yayi kamar ya juya amma babu hali dan sun riga sun ganshi. Karasowa yayi ciki ya durkusa ya gaida Daddyn wanda ya amsa masa idanun sa na kan wata takarda sannan yace ya zauna. Kallon juna sukayi shi da Adam kafin ya zauna yana zubawa takardun ido yana son fuskantar dalilin zaman nasu.

"Kai da nace ka sameni da daddare shikenan sai kayi batan dabo? Yau kwana uku."

Shafa saman sumar kansa yayi, ya dan yi yak'e kad'an

"Ya tabbata a gidan dai kake kwana, ni ne dai baka son haduwa da, sai ka shigo late ka fice da safe ko?"

"Ba haka bane ba."

"Toh Ya ya ne? Har yanzu maganar nan ce Muhd? Ba zaka hakura ba ko?"

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, dan be zaci Daddy zai dauko wannan maganar ba a irin wannan lokacin, be taba kawo hakan ba da ya gwammace ya fasa shigowar da ya gansu, ko yayi wata karyar da zai samu ya zille.

"Ya kamata ka sani, ban amince kayi wani abu akai ba, na fada maka ba tun yau ba, ka bar wannan maganar kawai amma na lura kamar baka ji, abinda ya riga ya wuce ya wuce, tsaurara bincike ba zai taba haifar d'a me ido ba."

"Dan haka bana so, ka bar maganar nan na fada maka, ka barta tunda ba akan ka aka fara mutuwa ba, ba kuma zai zama na karshe ba, kana gani nayi iyakar kokari na akan case din, kuma an tabbatar da kanta ta kashe kanta, binciken Yan sanda, likitoci da duk kwararru akan fannin ya tabbatar da haka, akan kishi? Toh me kake so nayi kuma akai? Ko ban iya ba kaine ka iya?"

Kansa a k'asa zuciyar sa na wani irin harbawa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, ya dinga jin wani irin tashin hankali na bijiro masa, maganganun da ya tsani ji a rayuwar sa, ace wai ta kashe kanta da kanta, wanne marar tunani ne zai yarda da hakan? Ta ya ya kishi zai saka ta kashe kanta? memory din abinda ya faru ne ya shiga dawo masa filla filla. Muryar ta radau tana neman taimako, cikin tsananin wahala da galabaita. Sunan sa da take kwalawa ya shiga yi masa amsa kuwwa, tamkar a lokacin take kiran sa, tamkar a lokacin komai yake faruwa, idanun sa ya runtse, ya hango ta kwance a cikin jini, cikin tsananin jinin da be taba ganin irin sa ba, Ammin sa a kwance, an mata yanka irin wanda ake wa rago! Jikin sa ne ya hau rawa sosai, gumi ya shiga keto masa, Adam ne ya fara lura da halin da yake ciki, yayi saurin ankarar da Daddy dan tun sanda ya fara masa magaar be ko kalle shi ba, zabura yayi cikin tsananin tashin ya watsar da takardun hannun sa, sukayi kan Aryan din suna kwalla kiran sunan sa.

"Kira Dr, kira likitan sa Adam, innalillahi."

Wayar sa ya ciro da sauri ya shiga dialing number likitan da yake duba shi, ringing daya ya dauka dan har yana shirin kwanciya ma dan be dade da shiga gida ba.

Suna tsaye akan sa suna kokarin bashi taimakon gwaggawa Dr ya karaso, ya taimaka musu aka karasa saka masa nebuliser dan dama gashi asthmatic toh da irin hakan ta faru sai numfashin ya soma yin sama. Kusan minti talatin zuwa awa daya sannan ya fara samun daidaituwar numfashin sa dama kan sa. Rufe idon sa yayi ruf, yana jin maganganun su akan sa da yake masa wani irin ciwo.
Har kusan ukun na dare suna tare a dakin sa harda Hajiya Zeenat, dan nan aka maidashi, yana jin yanayin damuwar da Daddyn yake ciki fiye da duk wata damuwa da ya taba shiga akan ciwon nasa, me yasa yanzu ya nuna damuwar sa sosai? Me ya sauya daga sanin da yayi wa Daddyn na rashin kulawa da damuwa da abinda ya shafe shi? Be san dalilin nuna masa soyayyar ba, bayan be same ta a lokacin da yake da matukar bukata ba, a lokacin da ya chanchanci a jashi a jiki a nuna masa soyayya, sai yanzu? Da ya girma ya mallaki hankalin kansa? Baya bukatar wannan soyayyar, baya bukatar kulawar zai iya kula da kansa tamkar yadda yayi a baya. Suna fita daga dakin ya tashi da k'yar dan jikin sa baki daya babu kwari ya fice daga dakin ya sakko k'asa, ya isa dakin masu gadi ya taso daya daga cikin ma'aikatan gidan yace ya kaishi gidan sa, a daren nan da komai haka suka tafi. Suna isa ya ce masa ya zauna ya karasa kwana anan kawai ya shige ciki yana jin kamar ana daddatsa masa cikin jikin sa saboda wani irin mugun sanyi me hade da zazzafan zazzabi da ya rafke shi a lokaci daya. Gabannin asubah zazzabin ya dan sake shi kad'an, ya tashi da k'yar dan dama ba baccin yake ba. Alwala yayi yana fitowa daddy na kiran wayar sa, be daga ba dan yasan kila dakin sa yaje duba shi da asubah yaga baya nan shine dalilin kiran, bashi da wani bayanin da zai bawa Daddy bama shi da karfin jiki da na zuciyar da zai iya magana dashi, musamman da ya zama duk abinda ya fada ba zai iya ce masa a ah ba. Raka'atanil fajr yayi ya zauna a saman daddumar har zuwa lokaci ya tashi yayi subh sannan ya koma ya sake kudundunewa a cikin blanket. Bacci ne ya dauke shi me karfi cikin yanayin da shi kadai yasan abinda yake ji.





RUMBUN QAYA*


Page 9

ยฉยฎ *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

****Karfe tara ya farka daga nannauyan baccin da ya dauke shi, bashi karfin zuciya da na gangar jiki amma hakan ya tashi da k'yar, yayi wanka ya shirya sannan ya kira Kamal yace yazo ya dauke shi dan baya jin zai iya driving. Ba'a dau lokaci ba sai gashi ya iso, ya fito yana tafiya wadda ya sa Kamal din karasowa da dan sauri yana kallon fuskar sa

"Are you ok ?"

Gid'a masa kai yayi, ya wuce shi zuwa wajen motar, bin sa yayi cike da mamakin karfin hali irin nasa. Bud'e masa motar yayi ya zauna a hankali sannan ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar gidan. A hanya be ce masa uffan ba, kansa jingine da jikin kujerar ya rufe idon sa ruf dan ma baya so Kamal din ya ishe shi da tambaya, he's so weak dan hatta heartbeat dinsa ya sauya.

"Aryan!"

"Um." Yace ba tare da ya bud'e idon ba

"Baka jin dadi, let go back please."

"Haka nace maka? Na gaji ne kawai."

"Gajiya? Me kayi da safen nan da zai saka ka gajiya,?"

"Ba sai ka sani ba."

"Ai saboda babu shi din ne ma, sanin da nayi maka baka kwana a gidan nan idan har ba wani abu bane ya faru ba, kai da Daddy ne ko? Dan nasan baka saka damuwar Adam a ranka balle har ta dame Ka."

"Kamal please, let talk about it some other time."

"Ok, be strong please."

Yace masa cike da tausayawa, kafin ya maida kansa kan titin ya cigaba da tukin sa ransa duk babu dadi.

Ko da suka isa company be fito daga motar ba, har sai da ya dauki wasu yan dakiku saboda yadda yake jin kansa na juya masa, da k'yar ya cije ya zuro kafar sa ya fito dan yayi ma kansa alkawarin ba zai taba bari hakan yayi affecting dinsa ba, amma kuma daga yadda yake ji yasan yana gaf da breaking alkawarin da yayi ma kansa nan kusa. Jerawa sukayi zuwa cikin building din Kamal na biye dashi a kusa kusa dan tsoron yanayin da Aryan din yake ciki. Har sai da ya kaishi office dinsa ya tabbatar ya zauna sannan ya wuce nasa da niyyar kiran Dr ya samu bayanin abinda ya faru dan yasan ta yadda zai iya kulawa da Aryan din. Be taba jin da gaske Aryan yana bukatar mace a tattare dashi ba sai yau, yana bukatar macen da zata zamar masa tamkar bangon da zai jingina dashi, tabbas zai rage abubuwa da yawa yasan, sai dai wacece zata iya zama da Aryan din da halin sa? Da ciwon sa? Da damuwar sa? Da shariyar sa? Wacece zata jure duk wannan? Dole sai dai wadda take tsananin so da kaunar sa fisabillillah, ba wai dan wani abun duniya ko fame ba, wadda take jin da gaske yana da bukatar a jashi a jiki, a nuna masa tsantsar soyayya, irin wadda ya rasa, wadda zatayi masa soyayyar uwa da danta, tayi masa soyayyar miji da mata. Tunanin sa ne ya katse sanda yaji Dr Ma'aruf din ya daga wayar, suka gaisa ya tambaye shi abinda ya samu Aryan din, yasan waye Kamal a wajen Aryan din shiyasa be boye masa komai ba, har ma da abinda ya kasa fadawa Daddyn, wanda ya sake tsoratar da Kamal din sosai.

System ce a gaban sa yana rike da mouse yana scrolling sai dai har ga Allah be san abinda yake dubawa ba, ga tarin bayanai nan da duk wani abu da yake da bukata a ranar amma ya kasa aiwatar da komai, lekowa Kamal yayi ganin sa a haka ya sashi zuwa office din su ya tarar da Raihana tana zaune babu abinda take dan babu aiki sosai a ranar saboda rashin zuwan Aryan din da wuri, dole sai ya gama dubawa idan ma akwai aikin zai aiko mata dashi ta mail ko ya kirata tazo ta karba. Gaishe shi sukayi dukka a karo na biyu sannan yace ta taso ta dan dafa musu shayin nasu. Ok tace ya fita ita kuma ta wuce kitchen din. Akwai komai da zata bukata nan da nan ta hada abinda zata hada ta dora, ta tsaya a kitchen din har ta gama sannan ta dauka zuwa office din Kamal din, tayi Knocking kad'an a kofar sannan ta tura, waya yake ya kalle ta sannan ya kalli kayan hannun ta

"Kai mana office din Aryan please, thank you."

Yace bayan ya dan zare wayar daga kunnen sa yayi maganar sannan ya cigaba da wayar, bata so ba dan ita bata ma san ya shigo yau ba duk da tasan babu abinda zai hanashi shigowar amma rashin jin duriyar sa yasa ta sakankancewa da be zo din ba. Tana kokarin karasawa office din nasa zainab ta taso da sauri ta tare ta

"Oga yace baya bukatar kowa a office din sa yau."

"Oga Kamal ne yace na kai masa."

"Bani na kai masa da kai na."

Wani kallo Raihana tayi mata,ta rasa dalilin takura mata da yarinyar tayi, gashi ita kuma sam ba'a nuna mata iko da gadara, wanda taga alamun dabiar Zainab din ce, murmushi tayi mata kad'an sannan tace

"Karki damu bari na mika masa."

Tayi wucewar ta, ta barta a tsaye a wajen cike da mamakin yarinyar.
Kan sa ya dora a saman table din bayan ya dan ture system din, sai da ta shigo sannan ya dago, tayi saurin janye idon ta daka kallon sa ganin yadda nasa suka kad'a sosai, kallon kayan hannun ta yayi har ta karaso ta dora su saman dan madaidacin table din dake gaban couch din.

"Good morning Sir."

"Menene wannan?" Yace bayan a amsa gaisuwar a ciki ciki dan ita bata ma ji ba

"Sir Kamal ne yace a kawo nan."

Juyar da kansa yayi gefe da yaji kamar ya makale masa, sannan ya sake dawo dashi tunanin taimaka masa ya fado masa

"Have a seat."

Ya nuna mata wajen zama, dan jim tayi kafin tazo ta zauna a daaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table din nasa ta dayan side din, turo mata system din yayi gaban ta, sannan a hankali yace

"Ki duba min wannan."

Kallon screen din tayi, sai taga same aiki ne da wanda ya saka ta kwanaki .

"In kin gama dubawa ga mails dinsu nan kasa sai ki tura."

"Ok."

Tace ta shiga aikin, yanayin maganar sa tayi mata kama da ta mara lafiya sosai, dan babu wannan zafin a maganar haka kuma babu nacaccen kamshin nan nasa da kullum yake mamaye baki daya ilahirin building din. Kamar ta bud'e baki ta tambaye shi ko akwai matsala ne? Dan tana jin sautin numfashin sa na fidda wata yar kara, sannan tana jin kamar jawo numfashin yake ta karfin gaske. Amma kuma tace masa me? Tasan yanayin sa zai iya bata amsar da zata gwammace dama bata yi tambayar ba. Wayar sa dake saman table din ce ta dinga kara amma yayi biris kamar bashi ake kira ba, so take ta dago taga yanayin da yake ciki amma sai ta kasa dan cike dake da shakkar sa. Tura kofar ya sakata kallon kofar, sai dai ganin wanda ya shigo ya saka gabanta faduwa, fuskar sa ce ta washe ganin ta, ya karaso yana maida kallon sa kan Aryan din da shigowar sa ta saka shi yunkurin mikewa amma kasancewar bashi da karfin jiki sai ya kasa.

"Me ya kawo ka?" Yace muryar sa a shake wadda take kara tabbatarwa da Adam weakness dinsa, shafa saman kansa yayi yaja kujerar dake gefen ta Raihanan ya zauna sannan yace

"Baka duba wayar kane? Daddy yana ta kiranka tun asubah, shi ya turo ni, na duba masa kai."

"Tunda ka ganni sai ka tafi ko"

"No ai ban gama ba,zai kira yanzu sai na hada ku." Yace yana zaro wayar sa da ta soma ringing ma tun kafin ya dire maganar, dagawa yayi

"Eh daddy yana office, eh toh gashi nan dai bari na bashi."

Ya cire wayar ya mika masa, wani kallo Aryan din yayi masa kafin ya karbi wayar ya saka handfree ya dorata a saman table din

"Aryan kana jina?"

"Ina kwana?"

Yadda yayi maganar ya saka Raihana kokarin mikewa ta bar musu office din dan ita bata gane yadda abubuwan suke ba.

"Seat down!"

Yace mata yana zare idon sa akanta, komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta. Yadda yake maganar da yadda yake amsawa wanda aka kira da Daddy ne ya daure mata kai, shi kowa haka yake masa kenan? Har mahaifin sa ma?

"Yan mata aiki ake yi ne?"

Adam ya fada yana karyar da kansa hade da wani irin kallo, kallon da yake hana mata sakat idan yayi mata shi dan ta tsani a rayuwar ta yawaan kallo musamman irin wannan da kana gani zaka tabbatar da abinda mutum yake nufi.

"Umm." Ta bashi amsa tana sake kankan da kanta dan ita gaba daya zaman wajen ya ishe ta.

Wayar sa Aryan din ya garo masa bayan ya gama maganar, ya dauka yana mikewa

"Babu kyau wulakanta mahaifa dai, baka ga yadda hankalin sa ya tashi ba, amma kamar ko a jikin ka."

Uffan be ce masa ba, yayi masa wani banzan kallo kawai ya ja siririn tsaki, dama kuma Adam din yasan ba zai tanka masa ba, kuma dama be yi don ya tanka masan ba, yayi ne duk dan saboda aikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment